x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 9 - KANA NAKA ALLAH NA NASA complete document

  • 24001 words
  • 27000 words
  • Out of 66841 words

Category: Love Stories

Views 309

25 Aug 2025
Start ads
After Image Ads
fara ƙullawa a leda, ban ji motsinsa ba sai maganarsa kawai naji.

"Bari nazo na taya gimbiyata ƙulli."

Harara nai masa ta wasa kafin nace.
"Wace wai gimbiyar taka?"
Yace "Ke mana,ko ba gimbiyata ba ce?"
"Eh ba ita bace,gimbiyarka ai sai mai jan kunne.". "Ke kuma kore ne da ke?" "Eh mana baka gani ba."
"Ban gani ba sai dai in yanzu ki nuna mini ya faɗa yana matsowa daf da in da nake tsaye ɗan ja baya nayi ina zaro idanuwa, murmushi yayi yana komawa inda yake daa a tsaye.
"Ina so zamui wata magana, amman kafin nan sai na cika cikina da alalarki ma ɗan karan daɗi."
"Tun kafi kaci har kasan zai yi daɗi?"
"Eh mana, ai tun daga ranar da na soma cin girkinki nasan babu wani abu da hannunki zai sarrafa bai yi daɗi ba,musamman wannan alalar da tun daga ido zata fara baka sha'awa."
Ina zubawa yana ƙullawa a haka har muka gama, dan bance komai ba shima kuma bai ƙara magana ba har na ɗora ya tafi masallaci sallar la'asar ɗin da aka kira nima na nufi ɗaki dan gabatar da tawa sallar.

Ina zuwa na tarar ya dawu sai ga shi ya shigo a hanzarce akan na zuba masa ya tafi da shi Daddynsu ke kiranshi, food flask na ɗauko mai kyau na zuba masa na ɗauko jug na zuba masa lemon kwakwar da baisan da shi ba,kana na saka masa cikin wani kwando mai matuƙar kyau.
"Na gode."
Yace da ni bayan ya karɓa ya juya ya fita,Momy na sakawa nasu a cikin food flask na bawa Zuwaire kana na ɗebi namu ni da Gwaggo dan nasan tana mutuwar sonshi shi kwa Baffa bai dame shi ba haka ma Abba, nima dai ba wani damuna yayi ba amman indai na ganshi zan ci.



"""Yau na tashi da zuwa gidan Nauwwa na gama shiri na tsaf naiwa Baffa da Gwaggo sallama kana na nufi sashin Momy itama nai mata sallama nasan Abba ya fita tun da banga jelarsa ba Hadi, shi na sakawa jelar Abba saboda duk inda kaga Hadi to ka tabbatar Abba yana gurin.
Inawa Momy sallama na fito sai gashi munci karo da Yaa Sulaiman da fara'arsa ko gaisawa bai bari munyi ba yace.
"A'a gimbiyata ina zuwa kuma?"

"Gidan Nauwwa zani,ina kwana?"

"Lafiya lau,kin tashi lfy?"
"Alhdlillah."
"Haka dama nake son ji,duk da idanuwana sun tabbatar mini hakan, bara na shiga mu gaisa da Momy sai na fito muje na huta da ƙorafin Nauwwara."
"Ok tom a fito lafiya."
Motata na buɗe na shiga na zauna ina addu'ar fita daga gida da ta shiga abin hawa can sai gashi ya fito."A motar ki zamui tafiyar kenan?"
Sai da ya faɗi hakan idanuwana suka sauka akan wata arniyar farar motar da ta gaji da haɗuwa."Ba matsala muje a motar taki,amman fitowa zaki dan ni mace bata jana a mota." Kallonsa nayi a raina nace."To ranar nan da na jaka fa?" kamar yasan abin da nake faɗi a raina yace.
" Ranar nan ma akasi aka samu."
Fitowa kawai nayi na zaga na shiga ɗaya site ɗin shima ya shiga ya ja muka tafi, ina kwatanta ta masa hanyar da zai ɗauka da zata kaimu Gaida unguwar da aka kai Nauwwa kenan, mun kusa isa sai ga kiran wayarta."
"Hello Sis kin taho?" Abin da ta fara faɗi kenan."
"Eh na ma kusa ƙarasowa."

Ba mu fi minti ishirin muka ƙarasa ba sai gamu har ƙofar gidan Nauwwa, ina tura ƙofar gate ɗin naji a buɗe take na tura na shiga da sallama da gudu ta fito ta ɗane ni muka hau murna kafin nace.
"Ke fa ba ni kaɗai ba ce."
"Ke da waye to?"
Ta faɗa tana kallon bayana alamun tana neman wanda muke tare."

"Yaa Sulaiman ne ."
"Ok, yaji gori kenan? Kice ya shigo."

Juyawa nayi na fita yana jingine jikin mota ya harɗe hannuwansa a ƙirji, kafeni yayi da ido yana sakar mini murmushi, irin kallon da Yaa Muhd yake mini irinsa naga yana mun,nan take jikina yayi sanyi na isa gare shi har lokacin kallona yake da ƙyar na iya furta "Ka shigo" Nai gaba ya biyo bayana.


Mun jima muna hira gaba ɗayanmu kafin ya mana sallama ya tafi akan sai ya dawo ɗaukata. Bayan ya tafi ne Nauwwa ke ce mini. "Anya kwa Najj ya Sulaiman ba sonki yake ba?"
"Me kika gani?"
"Takun tafiyarku mana kamar masoya, zuwan da yayi mini ma na tabbata albarkacin ki na samu."
"Ba haka ba ne,ke da kike 'yar uwarsu ko babu ni dama zai zo miki."
"Hmmm haka dai kikace amman na tabbata akwai wani abu a zuciyarsa idan babu a taki zuciyar kuma zaki ce na gaya miki."

Sai wajen biyar kana yazo ya ɗauke ni muna tafe muna hira jefi jefi kafin can naji yace.
"Tun ranar da idanuwana suka fara sauka akan hotonki zuciyata ta doka miki da wani irin ƙarfin da ya zarce yadda take bugawa a ko da yaushe,a sanda kuma idanuwa suka sauka a kanki a zahirance ai sai ta mutu gaba ɗaya cikin tsumammiyar soyayyarki."

Da sauri na ɗago kai muka haɗa ya kashe min ido da ɗage gira ɗaya kafin yace.
"Kin yi shiru."
"To me zance ?"
"Au ba ki san abin da ma zaki ce ba."
"Eh"
"Ok to bara na gaya miki abin da zaki ce cewa zaki nima tun ranar da na fara ganinka zuciyata ke ƙaunarka."
Idanuwa na zaro waje kafin nace.
"Cabf"
"Au baza ki faɗa ba kenan?"
" Kaga dan Allah ka buɗen mota na fita." Dan har mun iso gida yayi parking sai ya sawa motar lock.
"In dai kina son fita sai kin gaya mini abin da na faɗa miki."
Shiru nayi, shima yayi shiru na ɗan lokaci, na ɗago zan magana muka haɗa ido da shi nai saurin kautar da kaina gefe,murmushi yayi mai sauti kafin yace.
"Najjwa ko ba kya sona ne?"
Yadda yayi maganar sai naji kamar ta Yaa Muhd,a raina nace.
"Wace mace zaka cewa kana so tace bata sonka?"
"Najjwa magana fa nake kinmun shiru."
"To ai ni ban ce ba na sonka ba."
"Kina sona ke nan?."
Sunkuyar da kaina nayi ina wasa da zoben hannuna,bin hannun nawa yayi da kallo kafin yace.
"Ɗago kanki zan gani cikin idanuwanki."
Sai na kuma yin ƙasa da kaina sosai.
" Ki ɗago ko kuma na ɗago ki,baza ki ɗago ba tam bara ki gani ."
Da sauri na ɗago ganin ya kawo hannunsa gare ni dariya yayi kafin yace .
" Yarinya da kar ki ɗago."ya buɗe motor yace.
"Je ki tun da na gani cikin ƙwayar idonki."
"Babu abin da ka gani wallahi."
"Yarinya kada ki hana zuciyarki abin da take so,tun da kin ƙi faɗe na gani cikin idanuwanki da suka gaza ɓoye abin da ke ranki."
"Hmmmm haka dai kace."

"To ya ne?"
Fita nayi daga motar nai ɓangaran su Gwaggo na rabu da shi dan bani da abin da zance masa...


#BR
[9/25, 10:49] RASHUNA: BEBEE'ARTH



Wattpad@Rashuna



KANA NAKA
(Allah na nasa )


18


"Ku kallla."Fatma tace da 'yan tawagarta, gaba ɗayansu kuwa suka juya idanuwansu ya sauka akan Sajda,tana taku ɗaiɗai cike da yauƙi da yanga wan da ya zame mata jiki domin kuwa duk in da gayu yake Sajda tasan gayu ta kuma san ta kansa. Abin da ya bawa su Fatma mamaki ba komai ba ne sai yadda Sajda ta samo mayafin da ya mugun shiga da leshin da ke jikinsu gaba ɗaya,anko ne na class mate ɗinsu, sun zaga kasuwanni da dama haɗe da super market suma da dama amma basu samu mayafin da ya mugun shiga da leshin ba kamar yadda na Sajda ya shiga, abin da suke gudu ya faru (Sajda ta fisu ɗaukan wanka) Har ta gifta su ta ankara da yadda suka zuba mata ido kamar su cinyeta ɗanya, basa shiri shiyasa bata shiga shirginsu, su kullum burinsu su fita ɗaukar gayu amman hakan ya gagara saboda ta fisu sanin takan gayun.
"Lafiya dai ko na ci muku bashi?"
" Muna mamakin yadda akai kika samu mayafin da muka gama karaɗe kasuwanni da dama ba mu samu ba."
"Hmm shine matsalarku?"
"Eh"
"To matsalarku tazo ƙarshe in sha Allah zan haɗa ku da NEEHAL COLECTION daga yanzu wahalar neman mayafai ƙare muku da yardar Allah, dan nima tun da aka haɗa ni da ita na huta, duk mayafan da ake so ana samu a gurinta ko wani irin kala ne, kuma masu kyau da ɗaukar ido cikin farashi mai sauƙi."
"Au wai kina nufin mayafin na gida ne ?"

"Eh mana ɗan hannu ne."

Amma ta iya mayafai maza maza haɗa mu da ita dan baza mu shiga gurin bikin nan ba sai da irin mayafin ki muma mu ƙure gayu.

https://wa.me/message/AD4MDTQJLXIRD1

Ku bi wannan link ɗin zai kaiku in da zakui magana da NEEHAL COLECTION daga yau matsalar mayafai ta ƙare muku zaku samu duk kalar mayafan da kuke so cikin farashi mai sauƙi ina mai tabbatar muku zaku ji daɗin muamala da ita.


****"""""Ina shiga toilet na faɗa na watsa ruwa kana na ɗauro auwalar sallar magariba don naji an fara kiraye kirayen sallar.
Sai da na shirya kana na gabatar da tawa sallar kafin na fito falo, yanzun ma falon tsit kamar ɗazu da na shigo, nasan Gwaggo na ɗaki tana lazimi sai bayan sallar isha zata fito, shi kuma Baffa yana masallaci sai bayan an idar da sallar isha yake dawowa.
Ficewa nayi zuwa sashen Momy sai kuma muka haɗu da Yaa Sulaiman yana ƙoƙarin shiga,ganina da yayi yasa shi dakatawa har na ƙaraso in da yake tsaye.
" Ki tanadar mun abinci ba me nauyi ba, zanje na dawo kin ji amaryata."
Bai jirayi cewata ba ya shiga motarsa ya tayar yabar harabar gurin.

A kichen na samu Momy tana hada hadar ɗora girki,da sallama na shiga kafin nace.
Momy me ake dafa mana ne?"
"'Yar halak zancen ki nake a raina, ina cewa yau Nauwwa ta ƙwace mana ke, Abban ki har ya fara faɗan kinsan idan ba dole ba baya son ki dinga kaiwa magariba a waje."

"Ai tun kafin magariba na shigo ina sashen Gwaggo, wallahi Abba ya zama mafaɗaci Momy duk wannan matar ta cuce mu ta sauya mana shi."
Na faɗa ina turo baki gaba, murmushi Momy tayi kafin tace.
"To ai faɗan nasa akan gaskiya yake yinsa Najjwa, meye amfanin mace budurwa takai magariba a waje idan ba dole ya zama ba?"

"To ai da fa Momy ko me zanyi Abbana ba ya mini faɗa wallahi kafin tazo ta shiga tsakaninmu."
"A lokacin ba kya abun faɗan ne, yanzu kuma ba kiga kin zama budurwa ba."

Taɓe baki kawai nayi don naga alamun Momy bayan mijinta kawai take bi dan haka na kau da maganar a tsakaninmu ta hanyar faɗin.

"Momy ba ki bani amsa ba me zaki dafa ne?"

"Abbanki zan yiwa jalof ɗin taliya da vegitables nd arishi nd fish."

"Aikam wannan daɗin bazai huce mu ba, muma a saka sanwar da mu."

"Ke da wa kuma?"

"Ni da Yaa Sulaiman"

Kallon da naga Momy na mun yasa ni jin kunya nai saurin ficewa daga kichen ɗin,ba tare da na nemi tayata ba dan nasan ba barina za tayi ba, dan muddun Abbana yace ga abin da yake so ba ta barin kowa yayi masa sai ita,sai dai kuma in tana cikin wata lalurar, tana matukar kula da Abbana shi yasa nima nake sonta.
Murmushi Momy tayi ta bi bayanta da kallo kafin a saman laɓɓanta ta furta.
"Allah ya tabbatar da alkhairi."
Duk da a ƙasan ranta MU'AZZ take son aurawa Najjwan amman kana naka Allah na nasa tun da ga shinan har Son ya ƙyasa Najjwan ta yuhu dama can Allah ya rubuta shine mijinta dan haka zata cigaba da bin bayansu da addu'a da kuma fatan alkhairi.

A falon Momy na samu Nasrin da twince, dama su na shiga gani don yau nayi missing ɗinsu over.
Ina ɗaukansu suka shiga yimun dariya na biye musu ina ta musu wasa muna dariya cike da nishaɗi, sai ga Yaa Sulaiman ya shigo ya nemi guri ya zauna kafin yace.
"Nasrin ɗauko mun ruwa.". Tace "To" haɗe da miƙewa, bayan ta kawo masa ruwan ya sha ya kalleni yace.
"Ina abincin?"
"Momy ce take yi ba ta ƙarasa ba."

"Ok". Yace ya tashi ya fita ɗauke da Nimra a hannusa ya bar Neehal a gurina ina ta ɗaukarmu a hoto."
"Yauwwa Aunty Najjwa bara na kira miki Yaa EL ɗin yau ku gaisa."
Kafin nace komai har ta danna masa vidiocall, ashe ta juyo da wayar saitin da nake ni banma sani ba muna ta wasanmu da Neehal mun gama hotunan, kamar ance na ɗago kaina idanuwana suka sauka a kansa, kallo ɗaya nayi masa nayi saurin kau da kaina zuciyata na wani irin bugu na miƙe
ɗauke da Neehal na bar gurin, duk da naji Nasrin na cewa." Aunty Najjwa Yaa EL ɗinne fa kizo ku gaisa."

Ta ina zan iya tsaiwa mu gaisa? Mace ce fa akan cinyarsa yana zaune shi kuma kamar an dasa shi, idanuwansa a lumshe, rigar da ke jikinsa ta bayyana kyakkyawan ƙirjinsa mai cike da gargasa sai shaiƙi take tana walwali daga dukkan alamu ba ƙaramin kuɗi take lashewa gurin gyaranta ba.

Tsawar da ya dakawa Nasrin ita ta dawo da hankalinta kan wayar.
"Nace miki ina son gaisawa da wata ne?"

Girgiza mishi kai tayi tana ƙifƙifta ido kafin tace." Yaa ba fa wata bace Aunty .."

"Ban tambaye ki ko wace ita ba, kika sake yi mini irin haka sai nazo har nan na sassaɓa miki kamanni wallahi, sha sha kawai."
Yakai ƙarshen maganar yana huci, daga dukkan alamu tashin da Najjwa tayi ya ƙona masa rai a gurinsa kamar wulaƙanci ne da raini Nasrin ɗin ta janyo masa.

Zarina kuwa farin ciki ne ya dabaibaye zuciyarta tana ƙara jin yadda da mijinta akan ko wace mace ta kwana da sanin ta sha kan ko wace mace a kansa tayi kwanar da bata jin ko shekaru nawa wata za tayi tana tafiya baza ta cimmata ba.

"Aunty Zarina pls ki bawa Yaa haƙuri."

Nasrin tace da Zarina haka dan shi ya lumshe idanuwansa tasan kuwa tun da yayi hakan bazai sake magana ba."

"Ok Nasrin, amman kada ki sake, tun da kinga yayan naki ba ya so."

"Bazan sake ba in sha Allah."
"Yauwwa 'yar gari haka nake so, ni babyn hannunuta ce ma ta birgeni yarinyarta ce?"

Kafin Nasrin tayi magana ya disconnected ɗin kiran, dan bai gaya mata Momy ta haihu ba, ba mamaki wannan parrot ɗin ta gaya mata.

Sai bayan sallar isha ya kirani, lokacin nayi sallata nayi shirin baccina ina kwance kan gadona Mai laushi tunaninsa nake kan maganar da mukai ɗazu kiran nasa ne ya katse mini tunanin nawa.

"Ina main falor."

Abin da yace da ni kenan ya katse kiran,miƙewa nayi na sanya hijabi kan doguwar rigar baccina kana na fito, tun da na fito yake bina da kallo har nazo na shige kitchen.
Tana cikin warmer Momy ta ajiye mana na ɗauki plate na zuba masa har lokacin da ruwanta ba ta ƙame ba sai tiriri take tana zuba ƙamshin cyrry da spices ɗin Rashuna dan Momy ba ta da gurin siyan curry da spices sai a gurinta, yana da matukar daɗi da ƙamshi curryn ya bada wata iriyar kala mai kyan birgewa.
(Idan kema kin shirya siyan naki ga numberta nan akwai kyau akwai sauki da kuma inganci. 09037093702)

Center table na janyo har zuwa gabansa na ajiye plate ɗin a kai har lokacin idanuwansa a kaina, juyawa nayi na ɗauko ruwa da lemo da cup na ajiye masa,kallona kawai yake ko ƙifta ido ba ya yi saitin fuskarsa na kai tawa na hura masa iska sanyayya, lumshe idanuwansa yayi saboda ƙamshin sweet new ibon da ya doki hancinsa, maganar da nayi ce ta saka shi buɗe idonsa.

"Zan iya tafiya?"

Wani kalar kallo ya watsa mun kana yace.
"Zauna mu ci abincin tukunna."
"Ai ni na ci nawa."
"Ban yadda ba, ki zauna ko kuma na ɗora ki kan cinyata na baki."

Babu yadda na iya da shi haka na zauna muna cin abincin dukkanin idanunsa suna kaina har muka kammala, na kwashe kwanikan na kai kitchen zatona in na dawo zan tarar ya tafi sai na tadda shi a tsaye kallonsa na tsaya ina yi yace.
"Rakiya zaki mun."
Cikin shagwaɓa nace.
"Ni dai bacci nake ji."

Bai ƙara magana ba ya ja hannuna ina ta neman fisgewa amman na kasa har sai da muka je bakin motarsa ya saken.

Juyo da fuskarsa yayi saitin tawa yace.
"Good night,sweat dream with me,I love u."
Janye fuskata nayi zan juya na tafi ya janyo hannuna sai da ya jefe ni da kallon love kana yace.
"Ba ki isa ki tafi ba ki bani amsa ba."
Turo bakina nayi nace.
"To me zan ce?"
Ɗan jan bakin nawa da na turo yayi kafin yace.
"Cewa za ki ilove u too."

Duk nuƙu nuƙuna sai da ya saka na faɗa kana ya sake ni, nayi sashen su Gwaggo da gudun tsiya.



Idan wani ya bani labarin zan kuma buɗe zuciyata ga wani bayan Yaa Muhd a take zan ƙaryata,sai gashi wai nice yanzu muke shan soyayya da Yaa Sulaiman, soyayya mai zafi mai tsayawa a zuciya, yana ganin ya samu karɓuwa gurina yaje ya sanarwa Daddynsu da yake shima burinsa a yanzu Sulaiman ɗin yayi aure dan haka ya karɓi maganar da muhimmanci cike da farin ciki da zaƙuwa,ba ɓata lokaci suka zo suka sami Abbana tun da abun za'a iya cewa ya zama na gida ba wani tsayawa bincike bincike, daga zuwa tambayar aure nan take Abbana ya basu,a take kuwa shima Daddynsu ya ajiye dubu ɗari biyar kuɗin aure da saka rana, ba'a dai saka ranar ba aka bari a ji ta bakin angon.
Shi Yaa Sulaiman a yadda ya so nan da wata ɗaya na roƙe shi alfarmar ya ƙara wata uku a kai ya zama huɗu zuwa lokacin mun gama makaranta, to sai kuma aka saka wata biyar masu zuwa idan mai duka ya kai mu.
'Yan uwa da abokan arziƙi sun yi matuƙar farin cikin saka mana ranar da aka yi, farin ciki kuwa da zaƙuwar zuwan lokaci ba kamar Nauwwa da Nasrin har sun fara shirye shiryen abubuwan da za'a gudanar lokacin bikin, Nauwwa har da cewa.
"Wallahi duk tsananin son
End Ads