x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 10 - KANA NAKA ALLAH NA NASA complete document

  • 27001 words
  • 30000 words
  • Out of 66841 words

Category: Love Stories

Views 305

25 Aug 2025
Start ads
After Image Ads
na samu cikin da nake sai na ji sam bana son samu a tsukun nan sai bayan bikinki kada yazo yamun cikas."

Dariya nayi nace.

"Mu dai muna so koma da yaushe ne, fatanmu Allah ya kawo lafiyayye kuma mai albarka. Kinma tuna mini akwai wani magani da na ji ance in dai anyi ana dacewa, nace zan gaya miki ki gwada ."

"Gaya mini amman bazan yi yanzu ba sai bayan biki."

"Ai kwa kin yi kaɗan wallahi yanzu zaki yi tun da ba mu san san da rabon zai zo ba."

"Hakane kuma, ina ji gaya mini in sha Allah zan yi fatanmu Allah yasa a dace."

"Amin. Ganyan mangwaro ne kullum ki tsinki guda bakwai ki samu farar albasa 'yar madai daiciya ki rabata biyu sai kisa a ciki ki haɗa ki tafasa idan ya tafasa ki barshi a rufen kar ki buɗe sai washe gari da safe kafin ki ci komai ki tace ki sha, haka zaki dinga yi tsawan kwana talatin in sha Allah za'a dace duk da dai komai rabo ne."

"Tom Allah yasa na iya sha."

"Zaki iya in sha Allah."

"To Allah ya shige mana gaba ."

"Amin ya Rabbi."



#BRBEBEE'ARTH



Wattpad@Rashuna



KANA NAKA
(Allah na nasa )


19

"Shi yasa na so an ɗaura mana aure kinga hankali kwance babu wani tunaninki da missed ɗinki da zai dame ni, amman gashi tun yanzu har na fara kewar ki."

Lumshe idanuwana nayi na warasu akan farar kyakkyawar fuskarsa kafin nace.

"Abin da ba wani jimawa za kayi ba, kamar yau ne fa za kaga Nazo ɗaukar ka a airport ka dawo, kuma zamu na yin waya har vidio call ma."

"Baza su gamsar da ni kamar yadda zan ganki a zahiri ba kina wasa da soyayyar da nake miki Najj, har ga Allah na ƙagu na jiki kwance a nan."

Ya kai ƙarshen maganar yana nuna ƙirjinsa,kautar da kai na yi cike da kunyar maganarsa shi kam ya saki wani kafirin murmushi mai sauti kafin yace.

"Ina jin zan yi kusan wata guda fa, so nake idan na dawo na dawo gaba ɗaya ni da Jidda kuma sai ziyara."

"Nima in sha Allah da azumi zanje umara, idan Hajji tazo shima za ni in sha Allah,yanzun ma ji nake kamar na bi ka."

"Me yasa tun tu ni ba ki mini wannan maganar ba?wallahi da ba abin da zai hana tafiyarmu tare."

Murmushi na yi kana nace.

"Ta ya kake tunanin tafiyarmu za ta yuhu bayan ba'a riga an bikinmu ba?"

"Ta yadda na yadda Abba ya yarda da ni, kuma gidan da zamu sauka ba ni kaɗai ne ciki ba akwai MU'AZZ da matarsa za ki iya zama a nasu phart ɗin."

"A lallai su ji daɗin iskanta ni ba."
Na faɗi hakan a cikin raina,a fili kuma cewa na yi.

"Wai ya ma akai EL ya riga ka aure ne?"

"Saboda ya fi ni jaraba."

Ya faɗa kansa tsaye cikin raina nace.
"Na shiga uku, shegiyar tambayata."
Ban dawo daga wannan kunyar tawa ba na ji yace.
"Tawa jarabar ba ta tashi ba sai ranar da idanuwana suka fara sauka a kanki, a nan na ji cewar tabbas na shirya aure na kuma samu matar aure."

A daidai nan muka ƙarasa gurin da aka tanada dan yin parking cikin aitport,dama yasa na kawosa ne yau jirginsu zai tashi zuwa ƙasa mai tsarki domin har haɗo abubuwansa masu muhimmanci ya yi kuma cuku cukun samun transfer aikinsa zuwa nigeria, amman yana gama parking na yi saurin buɗa murfin motar na fice, to wannan kayan kunyar da ya jibga mini sam na ji ban son haɗa ido da shi, ina fita ya saki murmushi kana shima ya fito yaiwa motar key ya zago ta in da nake tsaye na kifa kaina jikin motar.

"Mu shiga ciki, so nake sai kinga tashin jirginmu zaki koma."

"To kaje zan biyo bayanka."
"Na ƙi wayon."
"Dan Allah."
"Ok na ji, amman wallahi ba ki isa ki haramta mini ganin kyawawan ƙwayoyin idonki ba, don ni ba haka na shirya mana sallamar da zamui ba, nai tunanin zan ɗan samu huge haka ko ɗan kiss."

Murmushi ya saki ganin yadda nayi kamar zan shige cikin motar saboda kunya kana ya juya ya fara tafiya, sai da naji takun tafiyarsa sannan na juyo na take masa baya.


Kafin tashin jirginsu ya yiwa El waya ya gaya masa lokacin da jirgin nasu zai sauka kafin ya kashe wayar.
Sai da naga tashin jirginsu kana na juyo gida cike da kewarsa da ta fara damuna tun yanzu, dan ba ƙaramar shaƙuwa muka sake yi bayan saka ranarmu, shi ke kai ni makaranta ya ɗauko ni, ya saka ni yi masa girkuna kala kala ina yi yana taya ni sannan in na gama mu ci tare.


SULAIMAN

A airport ɗin ya samu MU'AZZ yasan dama za'a yi haka dan mutum ne da ba ya saɓa alƙawari, idan kace masa takwas to a nan takwas za tayi masa, ba ya bari a jirasa kuma ba ya son jira.

"Yau ina jelar taka ne?"
"Ta na hospital."
"Lafiya?"
Sai da ya Fara yatsina fuska kafin yace.
"Aiki aka mata?"
"Toh subhanallah,me ya same ta?"

Tattare naman goshinsa yayi guri ɗaya yana yamutsa fuska, sarai Sulaiman yana ganinsa,yasan me zaice ya gaji da magana danma shine yake amsa masa tambayar da shiru zai masa.

"Idan baka son magana sai ka bawa mutum cikakkiyar amsar da bazai kuma maka wata tambayar ba."

Sai da ya juya kan motar suka fara ƙoƙarin fita daga cikin airport ɗin kafin yace.
"Mahaifa aka cire mata, Pls bana son kowa ya ji maganar ta tsaya iya tsakaninmu."

Ba ƙaramin girgiza zuciyar Sulaiman tayi ba da jin furucin El ɗin, ya buɗe baki sau shurin masaki da nufin yin magana amma ya kasa furta ko da kalma ɗaya, duk da yasan ko da ya sake maganar ba lallai ya tanka shi ba yadda yaga ya ƙara tamke fuska fiye da yadda daa take a ɗaure, taɓe baki yayi kafin a ransa yace.
"Rayuwarsu ba tashi ba, tun da haka suka zaɓawa kansu ai shike nan, amman yana tausayawa Zareenah, ba komai yake jiye mata ba nan gaba, domin kuwa dukkaninsu basu da tabbacin abin da zai faru a gaban."



EL MU'AZZ

Yana ajiye Sulaiman ya juya zuwa asibitin da aka yiwa Zareena aiki tun da ya doso ɗakin da aka kwantar da ita yake jiyo muryar mahaifiyarta tana ta masifa, dan haka ya dakata bai shiga ciki ba.

"Kin cuci kanki Zarina, kin wulaƙanta rayuwarki, ba baki nake miki ba amman ina da yaƙinin akwai ranar da zata zo sai kin zubar da hawayen nadamar abin da kika aikata,nadamar da zata kasance mara amfanin a gare ki, wallahi da na san abin da zaki aikata kenan bazan barki ba, amman saboda kada na hana shiyasa kuka ƙulla kuka rufe ke da mijinki da mahaifinki, saboda duk ƙwaƙwalwarku ta kifaye ce, idan shi baya son jikokin ai ni ina so ke kaɗai Allah ya mallaka mana ai dole zamu so ganin wani abu da ya fito daga gareki amman soyayyarki ta rufewa mahaifinki ido ya kasa gano hakan ai shikenan,duk zakui nadama ranar da shi mijin naki ya buƙa ci haihuwa ya kawo wacce zata haifa masa."

Tun da ta fara faɗan ba ta faɗi kalmar da ta girgizata ba irin kalmar nan tata ta ƙarshe ai kwa ta saki wani uban ihu haɗe da faɗin.

"Ammi dan Allah kada ki mini baki, ya riga yayi mini alƙawarin bazai mini kishiya ba,in fact ban yankewa kaina wannan hukuncin ba sai da yayi mini wannan alƙawarin."

"Zarina kenan, gata da soyayyar da aka baki yasa sam ƙwaƙwalwarki ba ta aiki,idan El yayi miki alƙawarin bazai miki kishiya ba shi ke da ikon kansa?
Ko kwa tafiyar rayuwar a tafukan hannunku take?
Ko kwa daga sama ya faɗo?
Idan shi ba ya buƙatar 'ya'yan ai iyayansa zasu so ganin jininsa ko kwa zuba muku idanu zasu cigaba da yi?"

Wani gumi ne ya zirarowa Zarina ta shiga kurma uban ihu iya ƙarfinta, mahaifinta da ke gefenta ne a zaune ya shiga rarrashinta haɗe da rufe Ammi da faɗa ta inda ya shiga ba ta nan yake fita ba,duk da jikinsa yayi sanyi da maganganunta, amman ai baici tazo tana gaya mata wa'yannan magan ganun ba a yadda ake buƙatar lafiyarta yanzu, shi fa soyayyar Zarina na rufe masa idanu a abubuwa da dama wan da sam baya lissafi yake biye mata su aikata wani abun,kamar dai yanzu da haka ta kasance.

Ƙarar turo ƙofar da aka yi yasa Zarina buɗe idanuwanta da ta rintse tana kuka Abie na faman rarrashi, akan EL suka sauka daman tasan shine saboda jin mayataccen ƙanshinsa da ya kaiwa ƙofofin hancinta ziyara.
"Yauwwa bie, zo dan Allah ka gayawa Ammi ta daina yi mini baki, kayi mini alƙawarin baza ka mini kishiya ba, kuma baza ka gayawa mahaifanka cewa na cire mahaifata ba."
Lumshe idanuwansa yayi kafin ya warasu akan Ammi, kamar bazai magana ba kafin can kuma yace.
"Ammi dan Allah komai ya wuce."

Numfashi ta sauke me nauyi kafin tace.

"Ai shike nan, na bar wannan maganar daga yau, dama ai shishshigi na ne tun da ba'a saka da ni ba."

"Afuwa Ammi, mun yi kuskure."

"Ya wuce."

Ta faɗa tana jin ciwon abin da Zarinan ta aikata, ciwon da ta tabbata bazai taɓa warkewa ba, da ace tana da wasu yaran to ta tabbata abin zaizo mata da sauƙi to ba bu Zarinan dai ita ce wacce ta kassara rayuwarta dan ita da haihuwa hai hata hai hata.
Ta rasa wannan makauniyar soyayyar da Abie ke wa Zarina da har tasa yake biye mata a dukkan abin da ta nuna tana so ko da ba akan daidai ba ne, duk da kasancewar ta ƙwara ɗaya da Allah ya basu ba ta cancan ci irin wannan soyayyar ba mai rufe idanuwa, ba haka ta so tarbiyyantar da 'yarta ba ko kaɗan sai dai ba yadda za tayi da Abie da yayi uwa yayi makarɓiya da kuma samun goyan bayan Zarinan tun da komai za tayi mata ita a gurinta a zuwan takura ne.

SULAIMAN

Yana shiga sai da ya fara kiran wayar Najj suka ɗan taɓa hira, kafin ya kira Mommy da Daddynsu ya sanar musu ya sauka lafiya,har lokacin ransa maƙale yake da abin da kunnuwansa suka jiye masa EL ya faɗa yana tausayawa Zarina har ga Allah don ta El me sauƙi ce don san da ya buƙaci haihuwa yana iya rufe idonsa ya kawo wacce zata haifa masa, sam ya rasa in da suka aro wannan halin yahudancin su da ke tsakiyar birnin makka cikin larabawa,musamman Zareena da ta kasance haifaffiyar garin tun da shi El zuwo ne, sam rayuwarsu kamar ba wa'yanda ke cikin larabawa ba idan kuna jin labarin rayuwar sakewa to ita EL MU'AZZ ALIYU FANDA ke gudanarwa da matarsa ZAREENA TAHIR ABDUSS SALAM.

Wanka yayi ya gasa jikinsa sosai da ruwa Mai zafi, bayan ya shirya kansa cikin shigar shan iska kana ya bi lafiyayyen gadonsa ya haye ya hau baccin gajiya,dan ya gaji da damuwar Zarinan da ke ganin daidai ta aikatawa rayuwarta ya azawa kansa.




ku kallla."Fatma tace da 'yan tawagarta, gaba ɗayansu kuwa suka juya idanuwansu ya sauka akan Sajda,tana taku ɗaiɗai cike da yauƙi da yanga wan da ya zame mata jiki domin kuwa duk in da gayu yake Sajda tasan gayu ta kuma san ta kansa. Abin da ya bawa su Fatma mamaki ba komai ba ne sai yadda Sajda ta samo mayafin da ya mugun shiga da leshin da ke jikinsu gaba ɗaya,anko ne na class mate ɗinsu, sun zaga kasuwanni da dama haɗe da super market suma da dama amma basu samu mayafin da ya mugun shiga da leshin ba kamar yadda na Sajda ya shiga, abin da suke gudu ya faru (Sajda ta fisu ɗaukan wanka) Har ta gifta su ta ankara da yadda suka zuba mata ido kamar su cinyeta ɗanya, basa shiri shiyasa bata shiga shirginsu, su kullum burinsu su fita ɗaukar gayu amman hakan ya gagara saboda ta fisu sanin takan gayun.
"Lafiya dai ko na ci muku bashi?"
" Muna mamakin yadda akai kika samu mayafin da muka gama karaɗe kasuwanni da dama ba mu samu ba."
"Hmm shine matsalarku?"
"Eh"
"To matsalarku tazo ƙarshe in sha Allah zan haɗa ku da NEEHAL COLECTION daga yanzu wahalar neman mayafai ƙare muku da yardar Allah, dan nima tun da aka haɗa ni da ita na huta, duk mayafan da ake so ana samu a gurinta ko wani irin kala ne, kuma masu kyau da ɗaukar ido cikin farashi mai sauƙi."
"Au wai kina nufin mayafin na gida ne ?"

"Eh mana ɗan hannu ne."

Amma ta iya mayafai maza maza haɗa mu da ita dan baza mu shiga gurin bikin nan ba sai da irin mayafin ki muma mu ƙure gayu.

https://wa.me/message/AD4MDTQJLXIRD1

Ku bi wannan link ɗin zai kaiku in da zakui magana da NEEHAL COLECTION daga yau matsalar mayafai ta ƙare muku zaku samu duk kalar mayafan da kuke so cikin farashi mai sauƙi ina mai tabbatar muku zaku ji daɗin muamala da ita.

Ga masu bukatar a tallata musu hajarsu kofa a bude take cikin farashi mai sauki.
#09037093702/08082007142
#BR

[10/1, 10:01] RASHUNA: BEBEE'ARTH



Wattpad@Rashuna



KANA NAKA
(Allah na nasa )

20

ZAREENA TAHIR ABDUSSALAM
'Ya ɗaya tilo gurin mahaifinta TAHIR ABDUS SALAM (Abie)da mahaifiyarta OUMAIMA OUMAR (Ammei)wan da haifafun Saudi arebia ne za kuma mu iya kiransu larabawan garin.
Sai da suka shekara goma da aure kafin Allah ya basu cikin Zareena,murna da farin cikin da suka shiga ba ya misaltuwa,yayin da haihuwarta tazo musu da buɗi na alkhairi,domin kuwa dukiyar Abie haɓɓaka ta dunga yi kamar ana ƙara izzata,ɗan kasuwa ne wan da yayi fice cikin ƙasashen duniya,kuma gogaggen ɗan bokon da ya wadatu da ilimi ya ratsa shi,wan da hakan yasa yake rayuwarsa tamkar ba balaraben saudiya ba domin kuwa al'adun yahudu da nasara sun shiga jikinsa sun zauna daram wan da zamu iya cewa a gurinsa Zareena ta kwaso nata ɗabi'un.


Wannan buɗi da ya kuma samu a haihuwar Zareenah shi ya kuma makantar da shi a soyayyarta, ba ya ji ba ya gani duk abin da ta nuna tana so sai yayi mata shi ko da ba ya ra'ayin hakan, a haka ya raineta a kuma hakan ta tashi, wan da hakan ke soya ran Ammei domin kuwa ba haka ta so tarbiyyantar da tilon 'yar tata ba, amman rashin mafita ya saka ta kawo ido da kunne ta zuba musu,domin kuwa ba ta samu goyen baya gurin Zareenan ba,ita Zareenan gani take Ammin takurawa rayuwarta take saboda ba ta sonta Abei yafi sonta da ƙaunarta.

Daga pre nursery har zuwa seneor secondary tayi su ne a CALCUTA.Wani babban birni a arewa maso gabacin india.
Daga ita sai nanynta Hussa suka tafi dan Amminta tace babu abin da zai sakata barin ƙasarta ta haihuwa,idan har makarantun da ke cikin Saudiya basu wadacesu ba to itama babu in da zata bi su.

Ba ta da wani buri da ya huce bayan gama secondary ɗinta ta tafi HONG KONG domin cigaba da karatunta domin kuwa tana matuƙar son ƙasar,suna yawan zuwa yawon shaƙatawa da Abei idan ya kawo musu ziyara anci sa'a kuma lokacin suna hutu.
Babu abin da ke burgeta irin abubuwan ƙayatarwa da bugewarsu ba ma kamar Repulse bay hotel da Aberdeen hotel in da zaka ga kifi mai rai irin wan da kake so daga wani tabki da ke kusa a dafa maka shi nan take ba tare da ka ƙagara ba, sai dai kuma shigowar EL MU'AZZ cikin rayuwarta ya sauya mata wannan burin daga ranar da ta fara ɗora idanta a kansa daga ranar taji zata iya ajiye ko wani buri ne domin ta kasance tare da shi.

Tashi tayi idonta na mata ciwo da ƙaiƙayi dama kuma tun tana yarinya tana fama da ciwon idon sai dai kuma yakan jima bai tasar mata ba,to dama anwa Abie ɗinta kwatancen likitan idon da ya fara aiki a Muwadda hospital cike da ƙwazo da nasara har yace zai kai Zareenan ya duba idanuwanta ko za'a dace,sai kuma gashi yau ta tashi da ciwon idon dan haka ya ɗauketa suka nufi asibitin.

Kasancewarsa sanannen mutum babu wani jira ko dogon layi suka shiga office ɗin SULAIMAN ALIYU FANDA,yayin da EL MU'AZZ ALIYU FANDA ke cikin office ɗin yana duba masa idonsa da yau ya tashi yana masa matuƙar ƙaiƙayi,sanye yake da wata arniyar jallabiya blue da ta ƙara haska farar fatarsa ta kuma yi masa masifar kyau,sai kuma baƙar p cap da ta bada damar bayyanar kyakkyawar sumar kansa wacce daga gani kasan ba ƙana nan kuɗaɗe take lashewa gurin gyaranta ba.

Bayan gama duba idon nasa da Sulaiman ya yi ya sanar masa idonsa ba shi da wata matsala, may be dai ko jiya ya daɗe bai bacci ba kuma ya zubawa kansa ruwan sanyi.
Tabbas jiya ɗin ya daɗe bai bacci ba yana ta aiki akan cumpuiter, kafin can cikin dare kuma yanayinsa ya sauya gaba ɗaya,wata gigitacciyar sha'awa ta addabi rayuwarsa wacce bai taɓa tsintar kansa a cikinta ba duk da fahimtar kansa da yayi yana cikin mazaje masu yawan buƙata,tsarewar Allah da kiyayewar sa ce ta kawo shi yau gurin kaucewa dukkan matan da ke bibiyar rayuwarsa.
Sai da ya sakarwa kansa ruwa mai matuƙar sanyi ya kuma daɗe yana sauka tsakiyar kansa kafin ya samu ya ɗan ji dama dama wan da yake tunanin hakan ne ya haddasa masa ƙaiƙayin idon.

"Ka sha wannan maganin bayan ka ci abinci sai ka ɗiga wannan a idanuwan naka sai ka kwanta ka samu bacci sosai, dan Allah yau kar ka fito ka samu ka huta sosai yadda zaka samu sakewa."

Fara maganar Sulaiman ce ta dawo da shi daga zancen zucin da ya tafi ya lumshe idonshi ya warasu kaɗan akan fuskarsa kafin ya miƙa hannunsa ya karɓi magun gunan da Sulaiman ɗin ke miƙo masa a daidai nan kuma Abei ya murɗa handle ɗin ƙofar
End Ads