x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 19 - KANA NAKA ALLAH NA NASA complete document

  • 54001 words
  • 57000 words
  • Out of 66841 words

Category: Love Stories

Views 297

25 Aug 2025
Start ads
After Image Ads
abin da ke hannuna,suma suka haɗo mu da tsaraba rigijib muka rabu cike da kewar juna.

A abuja muka sauka,ya koma bakin aikinsa,watanmu uku a can na matsa masa da ni gida nake son zuwa,gashi a lokacin shi kuma yana tsaka da aiki dan yana da marasa lafiya sosai,da ya gaji da nacina haka ya sako ni a jirgi,kafin ya samu sauƙin abubuwa ya biyo bayana,duk da yadda yake jin zai yi mugun kewata musamman ta fannin abinci,dan shi kam ba me yawan buƙata ba ne,nima kuma a lokacin ba sanin kan abun nayi ba,duk tsayin lokacin da zai ɗauka kafin ya nemi ni ba damuwata ba ce,dan a wahala na ɗauki abun da takurawa.


Idan kuka ga Yaa Sulaiman a yanzu ba za ku gane shi ba,ya canja sosai yayi ƙiba jikinsa ya buɗe tun a wata rana da muna kallo nace mishi ina son namiji me buɗaɗɗan jiki,ma'ana namiji me ƙarfaffan jiki,irin aftawan indiya da zakuga jikinsu ya buɗe sosai,duk da shi ba me ra'ayin ɗaga ƙarfe ba ne amman da jin wannan magana tawa sai gani na yi ana shigo da kayan motsa jiki cikin gida,ɗaki guda ya ware aka danƙaresu kala kala masu kyau da tsari na zamani,sai gashi lokaci guda jikinsa ya fara wani irin buɗewa ya ƙAra fito da cikar zatinsa da ilhama.

A zaman wata huɗun nan da muka yi da Man,bazan iya cewa ga wani abu da yayi mini na bacin rai ba,duk abin da na nuna ina so ko ba ya so zai yi mi ni,zai takura kansa ni ya faranta mi ni,duk da ance sai zama yayi zama ake gane halin juna amman ina da yaƙinin Man a ko da yaushe zai yi kokawa da ɓacin raina,mutum ne simple ga daɗin zama kamar yadda Momy ta taɓa faɗa mi ni.

Kamar laulayi jirana yake na sauka kano ya sako ni a gaba,na fara wani irin azababban laulayi,in da Allah ya taimake ni a gidanmu na sauka,nan Gwaggo da Momy suka shiga kula da ni,tamkar su cire mini ciwon su mayar jikkunan su,musamman da result ya fito na asibiti cewar ina ɗauke da juna biyu har na tsayin wata uku,murna da farin ciki gurin su ba'a magana.Man sai da ya zo yayi kwana ɗaya ya koma saboda ayyuka sun haɗar masa,farin ciki kuwa ba sai an tona zuciyarsa ba kamar ya ɗauke ni ya haɗiye ni tare da abin da ke cikina ya ke ji,Allah ya cika mishi burinsa ya dasa mishi ƙwansa a mahaifar Najjwa za ta haifa masa jininsa shima zai ga jininsa kamar yadda yake tsananin buri da fata.

Yau da lafiya gobe babu,na yi sati a asibiti na yi sati a gida,duk na bi na ƙare ba na ce na lalace ba,saboda fatata a murje take,tayi wani irin kyau ta na sheƙi a haka dai aka gurgura har cikina yayi wata bakwai kana na samu lafiya,ko da yaushe Man ya na hanya,idan yazo ya ganni sai ya koma,wani zubin ya kwana wani zubin kuma a ranar yake juyawa,har sai da Abba ya hau shi da faɗan sintirin da yake ya yi yawa ya je ya mayar da hankalinsa kan aikinsa tun da anan ɗin ga su dukkaninsu a kaina ana samun laulayin nawa yayi sauƙi zan komo Abujar amman duk da haka Man ya kasa jurewa kullum cikin kiran waya amman sai ya mayar da zuwan nasa duk sati.

Ga Daddynsu shima a tsaye yake a kaina,duk wani faɗi tashi na laulayin cikin da nake da shi ake yi,duk wani abu na kwaɗayi da sha'awa na masu ciki ya na kan hanyar kawo mi ni,wani zubin sai dai kawai na ji ya kira wayata akan na aiko a karɓo mi ni abu kaza gashi a ƙofar gida,idan jikina da ƙwari na taka da kaina naje na anso,idan kuma ba ƙwari sai na tura a karɓo mi ni.
Kamar yau da ya kirani cewar ga shi a bakin gate na turo a amsar mi ni saƙona,kasancewar jikin nawa da ƙwari yasa na saka hijabi na fita da kaina,don mu gaisa,dan nasan shi kansa zai fi son na fito da kaina dan yaga yanayin jikin nawa ko hankalinsa ya nutsu guri guda,ba shi da wani buri da fata da ya wuce ganin fitowar jikan nan nasa lafiya,jikan da yake jin babu wani wan da zai zo daga baya da zai kai shi ko ya kamo shi ko kuma ya zarta shi a zuciyarsa.

Shi ko Daddy tare su ke da Safiyya sun je dubo mahaifinta ba shi da lafiya,shine ya biyo da su nan domin ya bawa Najwa saƙon gashin kazar da ya san ta na matuƙar so da ƙauna a fara wannan laulayin nata,haɗe da tatacciyar madara me sanyi da garɗi.

Tun tsaiwarsu a bakin gate ɗin gidan Safi ya ke bin gidan da kallo,a kyau da tsari da girman gidan sai dai su zo ɗaya da wan da take ciki ba dai wani ya fi wani ba,tana cikin ƙarewa gidan kallo Najjwa ta fito tinƙis tinƙis cikin tafiyar masu ciki,gabanta ne ya yanke ya faɗi kafin wani irin yanayi ya dabaibayeta muryar bokan da taje gurinsa ne ya faɗo mata a rai,ko kuma tace matsafi don da haka ya dace ba boka ba.
"Zai aureki,za kuma ki mallakeshi har ki samu nasarar fitar da uwar gidansa daga gidan,ta hanyar abu guda ɗaya da muke buƙata daga gareki ba tare da ko sisin ki ba."

A lokacin idonta ya rufe,zuciya da ruhinta sun cika da so da ƙaunar ɗan mutan Fanda,ba ta da wani buri da ya wuce na auransa ko ta halin ƙaƙa,sonsa take ƙaunarsa ta ke dan haka ba ta damu da abin da za ta rasa ba muddun zai aureta ta kuma rayu da shi muddun rai.
Dan haka ta matuƙar ƙagauta ta ji me wannan matsafin ke buƙata a gareta,duk girman abun duk kuma illar da zai yi mata daga baya zata bayar muddun dai zata rayu inuwa guda da ɗan mutan Fanda.

"Mahaifarki muke buƙata,bi ma'ana babu haihuwa tsakaninku da Aliyu Fanda."

Matsafin ya gaya mata haka bayan ta uzzura masa da son jin abin da su ke buƙata a gurinta.

Ajiyar zuciya ta sauke wacce ba ma ta san tana riƙe da ita ba,bayan jin a bin da suke buƙata a gurinta,ashe abinma me sauƙi ne,ita ba haihuwa ko tarin dukiya zai kaita gidan Aliyu Fanda ba sai zallar so da ƙauna,ƙaunar da ba ta taɓa tsintar kanta cikin yiwa wani ba sai a kansa,ba ma ta san cewar akwai buƙatar ɗa namiji a wani sassa na jikinta ba sai ranar da ta fara ɗora idonta akan Aliyu Fanda,duk wani boyayyen feiling da emotion suka bayyana kansu,don haka ko me za ta rasa muddun rayuwarsu zata gauraya guri guda da Aliyu Fanda ko me zai biyo baya me sauƙi ne,don haka babu tunanin komai ta mallaka musu mahaifarta ba tare da tunanin akwai zuwan rana makamancin ta yau ba da wani emotion zai bayyana kansa a gareta akan haihuwa.

Ba ta taɓa tunanin akwai zuwan wannan ranar ba bare har ta bayyana a gareta a kurkusa,ashe za ta so haihuwa,a she itama zata so ganin jininta? Tun da duk in da akaje aka dawo shi Aliyu yana da nasa 'ya'yan tun da gashi yanzu ma jika yake shirin fara ɗauka.



Ganin na samu lafiya Abbana yace Man yazo mu tafi,duk da Momy ta so a barni sai bayan na haihu Baffa da Abbana suka kafe akan babu wannan zancen,ai yaron yayi matuƙar ƙoƙari,idan cikin nawa ya isa haihuwa in yana ra'ayi ya dawo da ni gida na haihu a gabansu, da ƙyar suka barni ganin sunan Nauwwa da ta haifi ɗanta namiji Najif ya yiwa Yaa Muhd takwara,irin farin cikin da na tsinci kaina bazai musaltu ba,wannan yaro kuwa ya ga so da ƙauna da bajinta iri-iri ta ko wani ɓangare.

Bayan sunan da kwana biyu Man ya zo washe gari muka juya Abuja muka gina sabuwar rayuwa me kyau da inganci,na wani irin maƙale masa kamar cingam,ko be neme ni ba zan kai kaina,kuma ko ba ya ra'ayi haka zai biye mini mu lula duniyar masoya,wani zubin ko ya rigani samun nutsuwa ba ya barina sai ya nema mini nutsuwar nima,kuma ba na shiru da bakina bare na cuci kaina,mijina ne babu kunya a tsakaninmu,idan ba shi ba babu me biya mun buƙatata idan kuma ba a halaka zan jefa kaina ba,Allah ma ya kiyaye amin.

Ban taɓa sanin haka abun yake da daɗi da nishaɗi ba sai a 'yan kwanakin nan,don ni a wahala na ɗauke shi sai ga shi yanzu na zama wata irin fitinanniya ko nace jarababbiya,dan ban taɓa tunanin ina cikin jerin mata masu buƙata ba sai yanzu,ko kuma ciki ne ya saka mini ban sani ba dai.

Duk da dai Nauwwa ta taɓa ce mini ko wace mace da irin halittarta,wasu matan a zuwan namiji farko garesu ma suke sanin kan abun,wasu kuma sai sun ɗebi watanni kafin su gane shi,wasu sai sun haihu,wasu sai suyi haihuwa nawa ma kuma suce miki babu wani abu da zasu ɗorar a wannan harkar dan haka abin dai ya danganta da halittar da Allah (SWA)ya yiwa mutum babu wata magana ƙwaƙƙwara sai yadda kika samu kanki.


EDD na na gab da cika Momy ta uzzurawa Man sai ya maido ni gida,ni kaina ba son tafiyar nake ba,don duk da cikina ya tsufa sosai kamar ƙara mini jaraba a ke,amman tun da Momy ta matsa babu yadda muka iya haka muka ɗunguma muka nufi kano tare da ɗumbin siyayyar Baby,duk da a scaining ance mana mace ce,komai unisex ya siya,dan yace bai yadda da abin da suka ce ba sai ranar da Babyn ya diro duniya yayi tozali da shi ko ita.

Mu na zuwa mu ka tarar da wani jibgin siyayyar Babyn,ba ga Momy ba ba ga Abba ba,dan nikam na rasa tsakaninsu wa ya fi zumuɗin ganin jikan nan? Duk da Momy tun akan Mu'azz ta so samun jika,dan ko yau ma sai da ta kuma tambayar Man cewa.

"Wai nikam har yau Zareenah da Mu'azz ba za su yi karatun ta nutsu ba,su haƙura da bokon nan su fara tunanin ajiye iyali ba?"

Yau dai kam Sulaiman ya ji bari ya warwarewa Momy komai,ko an samu ta daina saka rai da samun jika ta gurin Zareenah,duk da alƙawarin da ya yiwa Mu'azz cewar maganar za ta tsaya tsakaninsu amma dai kam yau sai ya warwarewa Momy gaskiyar magana ko ta cire rai zuciyarta ta huta.

"Zareenah fa tun kwanaki ta cire mahaifarta Momy,ina ganin tunanin samun jika daga garesu ya tsaya daga yau."

Momy da ke zaune sai da ta miƙe tsaye ta na salati da sallallami.

"Amman wannan yarinya ta cuci kanta,dan bazan ce ta cucemu ba,dan wallahi summa tallahi aure zanwa Mu'azz,Allah ya sauki Najjwa lafiya don muddun ya sake ya tako ƙafarsa ƙasar nan,bazai koma ba sai da mace wallahi."

"Momy kina ganin hakan masalaha ce? Dan ina ganin hakan kamar zai karya zuciyar Zareenah, dan yayi Mata alƙawarin bazai mata kishiya ba,wa kuma kike ganin za ki aurawa Mu'azz har da za ta iya zama da shi?"

"Idan Zuciyar Zareenah mutuwa za ta yi ba karyewa ba ta daɗe ba ta mutu ba,don wallahi sai na yiwa Mu'azz aure da duk macen da ta kwanta mini a rai,dan wannan ne zai saka Zareenah ta gane kuskuranta da kuma dukkan wata mace me ƙaramar ƙwaƙwalwa irin tata da zasu yadda da maganar namiji,basa duba cewar ba ka isa ka tsarawa kanka rayuwa ba yadda Allah ya so hakan ke kasancewa ko yayi mana daɗi ko akasin hakan.Abu Ɗaya da mace za ta riƙe a rayuwa shine;Kishiya ƙaddara ce,idan tana cikin ƙaddararki ko ba ta ciki allƙawarin namiji babu abin da ya isa ya hana ko ya saka,ki sakawa ranki bai zama lallai ki rayu ke kaɗai da mijinki ba,duk kwa tsayin shekarun da zaku ɗiba,tun da gashi nan ana yi muna gani sai mace ta cire rai da tsammanin za'a yi mata kishiya sai a ɗauko mata ɗanya sharaf,dan haka abin da ya fi miki ki cirewa ranki tsammanin kishiya har sai ranar da kika rasa numfashinki ko ya rasa nasa, don wallahi ko ƙur'ani ya dafa kan cewar bazai miki kishiya ba kada ki yadda bare har ki rasa wani sassa na jikinki saboda shi,don lokacin da zai karya miki zuciya raga raga sai dai a taya ki jimami daga gefe don babu me jiye miki ɗacin gubar da ya shayar da ke sai me ƙaramar ƙwaƙwalwa irin ta ki."


Har na ƙara sati biyu akan EDD na haihuwa shiru kike ji,sau biyu Man na zuwa tun bayan cikar EDD nawa amman shiru har ya koma ban haihu ba sai a yau na tashi da matsanancin ciwon baya da mara,a washe garin komawarsa Abuja kenan.

Cikin iko da ƙudira ta Ubangiji na fara naƙuda,naƙudar da da nasan haka take,da ni kaina ban gama shiryawa fitowar Babyn a yau ba,da kuma nasan ƙaruwar da na samu zan yi rashin wani abu kuma da ban shirya samun ƙaruwar ba,sai dai kuma ba'a tara sani da Ubangiji,ba kuma shirinmu yake dubawa ba,nasa shirin shima yake kuma nasan shine daidai da rayuwarmu.

Ƙarfe takwas daidai na dare jaririyar ta keta ƙasana ta fito haɗe da canyara kuka me azabar ƙarfi da ya gauraye Asibitin gaba ɗaya,wan da hakan yasa Gwaggo,Baffa,Momy,Abbana,Daddy faɗin.

"Alhamdlillah."

Cike da yalwar farin ciki.

Sai dai kuma ciwo ya dawo baya ashe yara biyu ke cikina wan da Allah ya ɓoye abunsa bai bawa ko likitocin damar sani ba sai yanzun,sai dai kuma har zuwa wayewar gari shiru kike ji Allah bai raba mu ba,dan har an kira Man a waya,tare da tura masa hoton ɗaya Babyn a wayarsa,amman kuma halin da nake ciki bai bawa zallar murna da farin cikin wannan kyauta da Allah yayi masa bayyana ba,ya barta tari guda a zuciyarsa,amman kwana yayi yana kallon hoton Babyn me matuƙar kyau da shiga rai.
Son samu ya samu flight ɗin da zai sauka kano,amman sai washe gari ƙarfe tara na safe,ban da yanayin da ake ciki na rashin tsaro da lafiyar ƙasa da ba abin da zai hana shi nufar kano a wannan daren,amman haka ya haƙura ya kwana yana juyi da kallon hoton jaririyar da ta shiga ransa ta zauna,wacce har ya saka hoton kan sciring ɗin wayarsa.
Daga ƙarshe kuma ya raya daren yana nemawa Najjwa sauƙi gurin rabbus samawati,dan jikinsa sanyi yayi ƙalau ya ji ya na tsoron rasa Najjwa,ya kwana ya na roƙon Allah ya rabata da abin da ke cikinta lafiya.


Takwas daidai ya fito zai nufi airport,dan har lokacin sun yi waya da Momy tace masa har yanzu dai shiru,ana shirin shiga da ita thearter, hankalinsa ne ya ƙara ɗunguma ya tashi, ya ji zuciyarsa tana tsintsinkewa,ga lokaci sam ya ƙi yin gudu,ji yake kamar yayi tsuntsuwa yayi fiffike ya ganshi gaban Najjwa da ke gumurzun sama musu Baby.

Miqdad ya kira shi a waya cewa,gadon nan da ya bawa Malls ɗin nan order an kawo shi,ya biya ya karɓa in yaso sai ya huce da shi,da har zai cewa Miqdad ɗin ya je ya karɓar masa,shi yanzu ba a nutse yake ba,amman sai wata zuciyar tace kawai ya je ya karɓa tun da ta wajen zai wuce.

Zuwan da da ya san abin da zai tarar a gurin da bai je ba,da yasan zuwansa gurin ba zai ba shi damar ɗaukar jaririyarsa a tafukan hannunsa ba,bazai ba shi damar ganinta ido cikin ido ba,da ko da wasa bai kuskura ya tunkari gurin ba,sai dai kuma ba a tara sani ga Ubangiji.

Har ya karɓo gadajen,ya taho yana murmushin da ya tsaya iya laɓɓansa dan har lokacin a tsintsinke yake jin zuciyarsa,ba komai ya saka shi murmushi ba sai hasko twince ɗinsa da yayi akan gadajen.
Gado ne na yara me kyau da tsari da ɗaukar ido,duk nisan in da kake idan yaro yana kuka za ka ji yana fitar da sauti me kukan yara,haka idan ƙofar ɗakin a buɗe take ka danna wani remort a hannunka gadon zai zo har in da kake.

Al'amarin ya faru ne ya na gab da fita daga Mall ɗin borm me matuƙar ƙarfi da illa ya ta shi da shi tare da dubban jama'a da suka zo Mall ɗin,dan Mall ɗin babba ne sosai duk
faɗin garin Abuja babu Mall ɗin da ya Kai shi kyau da inganci da girma da tsari tare da samun costomers,dan ba wannan ne karo na farko ba an sha kawo musu hari Allah ya na kiyayewa,sai gashi yanzu magautansu sun samu nasara duk kwa kula da tsoron da aka kafa a mall ɗin,Allah ya riga ya rubuta hakan sai ya kasance babu wayo babu dabara.

Hankali tashe Miqdad ya nufo Mall ɗin bayan ya ga sanarwar,fatansa da burinsa bai wuce Allah yasa hatsarin bai ritsa da Sulaiman ba.
Sai dai kuma ina Addu'arsa ba ta amsu ba,yana zuwa yayi tozali da gawar Sulaiman,ko ƙwarzane babu a jikin gawar fuskarsa ɗauke da yalwataccen murmushi,rungume gawar yayi a jikinsa haɗe da fashewa da wani irin kuka me ɗaci ya na ɗorawa kansa alhakin mutuwar Sulaiman,dan da bai kira shi cewar yazo ya karɓi gadan na,da hakan ba ta faru ba,da tuni ya na nan ya na shaƙar iskar duniya.

A motarsa da ya barta can tsallaken titi ya samu wayar Sulaiman ɗin,Momy da ke last call ɗinsa ya dannawa kira,a lokacin suna cike da taraddadin za'a shiga da Najjwa thearter dan cire ragowar abin da ke cikinta.
Ta na ganin kiran Sulaiman ɗin ta ɗaga cike da alhini,da kuma jin wata sabuwar faɗuwar gaba da ta same ta.

Da jin muryar wani ya na sallama ba ta Sulaiman ɗin da ta tsammata ba,zuciyarta ta buga wani irin tsalle a ƙirjinta.

"Ɗazun nan borm ya tashi da Sulaiman,Allah ya riga ya karɓi abunsa,in sha Allah yanzu zan yi cuku cukun
End Ads