kuwa duk in da gayu yake Sajda tasan gayu ta kuma san ta kansa. Abin da ya bawa su Fatma mamaki ba komai ba ne sai yadda Sajda ta samo mayafin da ya mugun shiga da leshin da ke jikinsu gaba ɗaya,anko ne na class mate ɗinsu, sun zaga kasuwanni da dama haɗe da super market suma da dama amma basu samu mayafin da ya mugun shiga da leshin ba kamar yadda na Sajda ya shiga, abin da suke gudu ya faru (Sajda ta fisu ɗaukan wanka) Har ta gifta su ta ankara da yadda suka zuba mata ido kamar su cinyeta ɗanya, basa shiri shiyasa bata shiga shirginsu, su kullum burinsu su fita ɗaukar gayu amman hakan ya gagara saboda ta fisu sanin takan gayun.
"Lafiya dai ko na ci muku bashi?"
" Muna mamakin yadda akai kika samu mayafin da muka gama karaɗe kasuwanni da dama ba mu samu ba."
"Hmm shine matsalarku?"
"Eh"
"To matsalarku tazo ƙarshe in sha Allah zan haɗa ku da NEEHAL COLECTION daga yanzu wahalar neman mayafai ƙare muku da yardar Allah, dan nima tun da aka haɗa ni da ita na huta, duk mayafan da ake so ana samu a gurinta ko wani irin kala ne, kuma masu kyau da ɗaukar ido cikin farashi mai sauƙi."
"Au wai kina nufin mayafin na gida ne ?"
"Eh mana ɗan hannu ne."
Amma ta iya mayafai maza maza haɗa mu da ita dan baza mu shiga gurin bikin nan ba sai da irin mayafin ki muma mu ƙure gayu.
https://wa.me/message/AD4MDTQJLXIRD1
Ku bi wannan link ɗin zai kaiku in da zakui magana da NEEHAL COLECTION daga yau matsalar mayafai ta ƙare muku zaku samu duk kalar mayafan da kuke so cikin farashi mai sauƙi ina mai tabbatar muku zaku ji daɗin muamala da ita.
****"""""Kamar ita ya gani a zaune a bakin titi,dan haka sai ya dawo da baya da baya dan gasgata zatonsa, ita ɗince kuwa, glass ɗin motor ya zuge kafin yace.
"Ina neman afuwa gurin gimbiyata,ya akai kika fito cikin ruwa yana dukanki? da kinyi zaman ki cikin makarantar Zan zo har nan na ɗaukeki."
Jin muryarshi ne yasa na ɗago kaina, dan nai tunanin motocin da ke tsayawa domin rage mini hanya ne wani ya tsaya shiyasa ko motar ban ɗaga kai na kalla ba,bare har na gane motata ce.
Ta shi nayi da sauri na zaga ta ɗaya ɓarin dan wallahi gaba ɗaya a tsantsame nake da jikina,na buɗe motar na shiga, kafin ya ja motar mu fara tafiya shiru babu wan da yayi magana a cikinmu, sai da ya fara tsayawa a wani pharmacy ya shiga ya fito ba tare da nasan me ya yo ba kana muka ƙarasa gida.
"Ki shiga ciki, ki tabbatar kin yi wanka da ruwa mai zafi sosai,sannan ki ci abinci ki sha wannan maganin." Yakai ƙarshen maganar haɗe da miƙo mini ledar da naga ya fito da ita daga pharmacyn nan, ashe abin da ya siyo kenan, ko bai faɗa ba dama ina shiga wanka ne abu na farko da zan fara yi da ruwa kuma mai zafi sosai kamar yadda yace.
"Na gode." Nace da shi bayan na karɓi ledar."
Har na nufi hanyar da za ta sada ni da sashin su Gwaggo naji yace.
"Ba ki ji ba."
Waigowa nayi ina zubawa fuskarsa ido.
"Gwaggo na can tare da Mommy an mata cs an ciro tagwayen yara masu tsananin kama da ke."
Wani tsellen murna na daka na dire na manta a gaban wa nake ma, kafin na narke fuska nace.
"Amman shine Yaaya da mu huce can,Abbana ya sani?"
"Abba ya sani ba mamaki ma yanzu ya ɗauko hanya.Ke kuma nasan idan muka je baza ki yadda mu taho akan lokaci ba,ni kuma bazan iya jure barin ki da jiƙaƙƙun kaya ba,ki shiga ciki kiyi abin da nace kafin nan in sha Allah na dawo sai mu tafi."
Ai da gudu na kwasa nai ciki yayin da yayi murmushi ya juya kan motarsa ya fice dama al ready yacewa gate man ɗin kar ya rufe.
Gidansu kai tsaye ya nufa, wankan shima yayi da ruwa mai zafi sosai kana ya fito, ya na cikin shiryawa a ransa yace bari ya kuma gwada wayar EL dan tun ɗazu yake kiransa ba ta tafiya, yanzunma ta tafi amman ba ai peaking ba, jim kaɗan kuma sai gashi ya biyo bayan kiran amman shi vidio call ya kirawo sa, barinta yayi ta katse dan baya son yin vidio call da EL ɗin ba don komai ba sai don rashin kunyarsu daga shi har bayahudiyar matarsa, ta yuhu yanzu ma haka tana kan jikinsa amman yake kiransa, ya rasa me yasa sam EL bai san wata aba kunya ba, ko da Momy zasui waya ba ruwansu daga shi har Zarinan tana kan cinyarshi wani zubin ma tana shashshafa shi, sai da Momy ta mishi ta tas akan hakan tace idan har yasan yana tare da Zarina kada ya ƙara gigin kiranta vidio call.
Tana katsewa yabi bayan kiran sai gashi ya ɗaga cikin cool voice ɗinsa yace.
"Helo Bro ya?."
"Lafiya ya gidan ya Madam ?"
"Alhmdlillah,ya su Mom?"
"Suna lafiya sai dai Mom ɗince a kaiwa cs."
"Subhanallah, me ya sameta,tsakani da Allah shine har akai cs ɗin babu wan da ya gaya mini?"
"To ka damu da ita ne?"
"Wani irin magana kake Bro? Nikwa na dam u da Momy, kaima kasan abin da ya hana ni zuwa nigeria har yau, amman ƙarshen watan nan zamu shigo in sha Allah,tun da Zarina ta samu hutu.Ka gaya mini wani ciwo aka cirewa Momyn?"
"Ba ciwo aka cire mata ba, yara aka ciro mata har guda biyu duk mata."
"Kana nufin haihuwa Momyn tayi?"
"Ƙwarai kuwa."
"Haba dan Allah,haba dan Allah,yanzu tsakani da Allah Momy ta mana adalci? Da girmanmu yanzu ace wani an haifar mana ƙanne, dama da Daddy ta haihu abun zai fi zuwar mana da sauƙi, wlh nama fasa zuwa nigerian kuma ka gayawa wannan yarinyar wallahi ta sake ta kirani ta nuna mini fuskar yaran da ita da su zan haɗa na ci ubansu wallahi,wannan abun kunya har ina? Tsakani da Allah na wani ce babarmu ta haihu,ai wallahi ba wan da zai ji mutuwar sarki a bakina. "
"Allah ya shiryeka EL,idan zaka shiryu,amman ni ka sani bana jayayya da ikon Ubangiji, ina matuƙar farin-ciki da wannan haihuwa ta Mommy, dan Allah kai ta zama a saudiyya har mahadi ya bayyana dama mun tattara mun barwa Zarina da danginta kai,nima ƙarshen watan nan zan shigo na haɗo komai nawa na dawo gida suma naci gaba da bauta musu.Kuma ni ba ɗan aikenka ba ne sai ka kirata da kanka kai mata kashedin."
Yana kawowa nan ƙit ya kashe wayar.
Yana shirin shiga mota aka kunno kan motar Daddy, dakatawa yayi har sai da drivern ya daidaita parkin ɗin motar kana ya ƙarasa ya buɗewa Dady motar ya fito suka gaisa kana ya gaya mishi haihuwar Momyn tasu, sai da yayi ɗan jim kafin kuma yasa albarka tare da fatan Allah ya bawa Momyn lafiya. A kunnen Nasrin da ta jiyo dirar motar Daddy ta fito tararsa duk sukai maganar, ai kwa tana karasowa gurin da suke tsayen ta dirawa Daddyn magiya da shagwabar ya barta taje ta gano Momyn nata sai kwa taci sa'a yace ta bi shin suje, tuni ta hau tsallan murna,dama a shiryanta ta fito babu wani abu da zata koma dauka dan haka kawai suka shiga mota suka taho.
NAJJWA
Ina shiga wanka na fara yi da ruwa mai zafi na gasa jikina sosai kana na ɗauro auwala,bayan na tsane jikina sai na fara gabatar da sallar la'asar ɗin da ta kufce mini, ina idarwa na shirya kana na nufi ɗakin Baffa naje mukai ta murnar ƙaruwar da muka samu,kafin can ya tambaye ni sautin rogonsa, wallahi na manta amman sai kawai nace masa. "Hadari ne ya haɗo shiyasa ban samu masu rogon ba duk sun nemi gurin fakewa,baza kaje ganin twince ɗin ba ne?"
"Abbanki nake jira."
"Wani Abban? Ai wallahi ba mamaki can asibitin zai zarce, gara ma kazo mu tafi tare yanzu Yaa Sulaiman zai zo."
Ina rufe baki na jiyo dirin motarsa sai lokacin na tuna ban ci abincin ba ma bare na sha maganin, da hanzari na ta shi na nufi kicthen, ai duk tuwo na tarar a kitckicthen ɗin Gwaggon Baffa na shinkafa ita na dawa kuma duk ba wan da nake ƙaunar ci ga lokaci ya ƙure bare na dafa ko indomei ce, kawai sai na ɗauki 'yar ƙaramar farar roba na zuba dambun nama a ciki, na buɗe fridge na ɗauki lemo da ruwa kana na nudi ɗakina wayata da ledar maganin kawai na ɗauko na fito tun da da hijabi a jikina kawo lokacin har ya shigo suna hira da Baffa.
" Na gama muje."
Tare suka miƙe shi da Baffan sukai gaba na bisu a baya. Nasrin naga ta fito daga gaban motar nace.
'A'a kaga su Nasrin an kasa zama anyi ƙanne."
"Ke dai bari Aunty Najjwa abun ba'a magana."
"To ta naga kin fito."
"Yi zamanki wlh zamu shiga baya ni da Baffa."
Na nuno mata Baffa da ya tsaya suna magana da Garzali mai wanki."
"Ki taimaka ki shiga in ba so kike yau Yaaya yayi farfesuna ba."
"Tom shikenan taho mu shiga bayan ga Baffa nan shi ya shiga gaban."
Nace da ita haka bayan na hango tahowar Baffan, na buɗe gidan bayan muka shiga bayan na ɗauke kaina daga kallon da yake mini.
A cikin motar muka ci dambun naman ni da Nasrin kana na ɓalli magun gunan na sha. A can asibitin muka tarar da Abba, na kalli Baffa ina dariya kafin nace.
"Kaga abinda nake gaya maka ko? Ni wlh har na fara kishi da wa'yannn yaran yanzu shikenan sun ƙwace mini fada gurin Abbana."
Dariya Abba yayi yace."Ai ba su kai isar da zasu ƙwace miki fada ba 'yar kaɗan na tsikara musu."
Dariya nayi kafin muka shiga ɗaukar jariran duk wan da ya ɗauka kamar kar ya bawa wani. Baffa faɗi yake.
"Yadda kuka san Najjwa tana jaririya."
Nan da nan asibiti ya ɗinke da jama'a ana ta murna da san barka, na kira Nauwwa ma wajan sallar Isha sai kwa gata rabon ta ci tsiren mandawari dama tace nacewa Baffa tayi missing ɗin shi yanzun ma ni na cewa Baffa yasa a kawo mana tsiren da youghort har yana tsokanata da.
"Nan ɗinma partyn zaki haɗa kenan,sai kinsa an tattaroku gaba ɗaya an sallama lokaci bai yi ba."
Kwanan Mommy huɗu a asibitin aka sallamo ta,nan ma dai 'yan barka aka cigaba da cin cirin don zuwa,'yan biyu sunyi farin jini kowa na sonsu da ƙaunarsu. Ranar suna an sha shagali an watsa naira Abba ya saki bakin aljihu sosai,haka ma Baffa da Yaa Sulaiman,ɗinkunan da na dinga sakawa ina shiga ina fita ke kyace nice me jegon.
Ni na zaɓi sunan da za'a dinga kiransu da shi Hassana Neehal,Usaina kuma Nimra haka muke kiransu da shi,had a ƙatuwar calendar da akai mai ɗauke da hotonsu haka aka saka sunayen nasu a jiki.
Ni nake rainon ƙannena da Gwaggo ta musu wanka zan kwashe su, sai idan sun buƙaci abincinsu zan kaisu gurin Mommy ko kuma idan zani makaranta.
Zaune muke a falo ni da Momy muna hira, Neehal a hannuna Nimra kuma na hannunta,sai ga Abba da Yaa Sulaiman sun shigo Abba yace.
"Kaga 'yar gidan Abba da takwararta."
Nai murmushi yace.
"Ki shirya yau zaki baƙo." Gabana ne naji ya yanke ya faɗi ,cikin sanyin murya nace.
"Abba baƙo kuma?"
#BR[9/25, 10:49] RASHUNA: BEBEE'ARTH
Wattpad@Rashuna
KANA NAKA
(Allah na nasa )
17
"Ku kallla."Fatma tace da 'yan tawagarta, gaba ɗayansu kuwa suka juya idanuwansu ya sauka akan Sajda,tana taku ɗaiɗai cike da yauƙi da yanga wan da ya zame mata jiki domin kuwa duk in da gayu yake Sajda tasan gayu ta kuma san ta kansa. Abin da ya bawa su Fatma mamaki ba komai ba ne sai yadda Sajda ta samo mayafin da ya mugun shiga da leshin da ke jikinsu gaba ɗaya,anko ne na class mate ɗinsu, sun zaga kasuwanni da dama haɗe da super market suma da dama amma basu samu mayafin da ya mugun shiga da leshin ba kamar yadda na Sajda ya shiga, abin da suke gudu ya faru (Sajda ta fisu ɗaukan wanka) Har ta gifta su ta ankara da yadda suka zuba mata ido kamar su cinyeta ɗanya, basa shiri shiyasa bata shiga shirginsu, su kullum burinsu su fita ɗaukar gayu amman hakan ya gagara saboda ta fisu sanin takan gayun.
"Lafiya dai ko na ci muku bashi?"
" Muna mamakin yadda akai kika samu mayafin da muka gama karaɗe kasuwanni da dama ba mu samu ba."
"Hmm shine matsalarku?"
"Eh"
"To matsalarku tazo ƙarshe in sha Allah zan haɗa ku da NEEHAL COLECTION daga yanzu wahalar neman mayafai ƙare muku da yardar Allah, dan nima tun da aka haɗa ni da ita na huta, duk mayafan da ake so ana samu a gurinta ko wani irin kala ne, kuma masu kyau da ɗaukar ido cikin farashi mai sauƙi."
"Au wai kina nufin mayafin na gida ne ?"
"Eh mana ɗan hannu ne."
Amma ta iya mayafai maza maza haɗa mu da ita dan baza mu shiga gurin bikin nan ba sai da irin mayafin ki muma mu ƙure gayu.
https://wa.me/message/AD4MDTQJLXIRD1
Ku bi wannan link ɗin zai kaiku in da zakui magana da NEEHAL COLECTION daga yau matsalar mayafai ta ƙare muku zaku samu duk kalar mayafan da kuke so cikin farashi mai sauƙi ina mai tabbatar muku zaku ji daɗin muamala da ita.
****"""""
Sai da ya haɗe fuskarsa tsaf dan kar ma na kawo masa wani ƙauli da ba'adi,kafin yace.
"Eh baƙo nace,ko shima zaki kore shi ne?"
Wani tsoronsa da shakkarsa ne suka shige ni kamar lokacin Mama Kubrah.Girgiza kai nayi ƙwalla na cika idanuwana, sai kuma ya sasauta fuskarsa kana yace.
"Ko a kwai wan da kuka daidaita da shi ne?in ya so sai na dakatar da wannan."
"Babu" Nace da shi kaina a ƙasa dan hawayen da ya taru na neman saukowa a kuncina.
"Saka miki idon da nayi ba shi ke nufin na rabu da ke akan abin da kika zaɓawa kanki ba, saboda mijinki ya mutu sai kice baza ki kuma wani auren ba, to kin butulcewa Ubangiji kenan, kuma kina tuhumarsa kan ɗauke miki miji da yayi kenan,bayan ke kanki kin san rayuwar taki aro ya baki, idan lokacinki yayi ko second baza ki ƙara ba.kafin ke nawa aka yi ? Ni kaina na ishe ki misali mutuwar mahaifiyarki ba shi ya hana ni ƙara wani auren ba duk tsananin son da mukewa juna haka na haƙura na kawo wata cikin rayuwata, dan haka bana son jin wani zance ki buɗe zuciyarki ku fuskan ci juna da Abbas."
"Tom in sha Allah Abba ba za a samu wata matsala ba."
Na faɗa ina ƙara yin ƙasa da kaina dan naga wannan Abban bazai karɓi duk wani wargi da zan kawo masa yanzu ba,duk da banjin zan iya buɗe zuciyata ga kowa a yanzu amman ya zame mini wajibi gurin cika umarnin Abban sai dai kuma ban san ta ya ya ba.
Sulaiman kuwa mutuwar zaune yayi jin bayanin da Abba kewa Najjwa,to dama Momy ba ta sanar masa ba kenan? In kwa hakane bazai zauna ai masa sakiyar da babu ruwa ba,soyayyar Najjwa ba ta shige shi da wasa dan haka Allah ne kaɗai yasan lahanin da za tayi masa muddun ya rasa ta.Abba na tashi ya take masa baya har zuwa ƙawataccen falonsa,sai a lokacin Abba ya ankare da shi.
"A Sulaiman ice dai ko lafiya?"
"Eh to lafiya dai za'a ce Abba" ya faɗa yana ɗan sosa kai,zama Abba yayi yana maiwa Sulaiman nuni da shima ya zauna,zama shima yayi yana yin ƙasa da kansa kafin yace.
"Abba dama cewa nayi to idan baƙon Najjwa yazo ni kuma yaya za'ai da ni?"
Kyakkyawan murmushi ne ya kubfcewa Abba kafin yace."Ai ban gane hausar taka ba dama can kana son Najjwan ne?"
"Ehh Abba.". Ya bashi amsa yana ƙara yin ƙasa da kansa."
"Aikam ka kusa ƙauran baki,Allah yaso ban amsa masa ba nace zan fara tun tuntuɓarta na ji ko da wanda suka daidaita,shigowar da nai kiran yaron zan na bashi damar fara zuwa yau ɗin sai kuma ga taka maganar,a zahirin gaskiya naji daɗi gida ba ta ƙoshi ba ai ba'a kai dawa ba, zan kira shi na bashi haƙuri kai kuma sai ka fara kafa gwamnatinka sai nace Allah ya bada sa'a ya kuma tabbatar mana da alkhairi amin."
Farin ciki mara iyaka ne ya ziyarci zuciyarsa ji yake kamar Najjwan ce ta amshi soyayyarsa,duk da ƙasan ransa yana ta tunanin dalilin da yasa Mommy ba ta sanarwa Abba da maganar soyayyarsa ba da tuni yana ji yana gani Najjwan zata yi masa nisa.
Godiya yaiwa Abban ya fito har lokacin muna zaune ni da Mommy tana tayi min nasiha cike da lallashi,dan Abba na barin gurin kukana ya fito fili na kasa tsayar da shi,yi yayi kamar baiga hawayen da nake sharewa ba ya nemi furi ya zauna yana sauke idonsa kan Momy dake yunƙurin miƙewa yace.
"Mommy Alala nake so."
"Ga ƙanwarka nan ta yi maka."
Ta faɗi hakan tana ƙoƙarin barin falon zuwa falon Abba."
Juyo da kallansa yayi kaina.
"Zaki yi min?"
"Me zai hana?"
"Nima bansan abin da zai hana ɗin ba."
Murmushi nayi saboda yadda yayi maganar ya bani dariya.
Zuwaire 'yar aikin Momy na saka ta wanken wake tun da ba sai an surfa ba a ɓarje yake wanke shi kawai za'ai, na ɗora ƙwai a wuta da hanta, na fasa kwakwa na ɓare dabino na cire ƙwallayen na wanke nai blandin ɗinsu, zuwa lokacin Zuwaire ta gama wanken waken ta gyara attaruhu da albasa ta zuba a ciki, sai nace ta bayar a kai mini markaɗe saboda yafi laushi akan nayi a blanda.
Kafin a kawon markaɗen na haɗa lemon kwakwar da yasha uban madara na saka fridge,ƙwai da hantar duk sun dawu na yayyanka su,ana kawon markaɗen na haɗa
ƙullin na