ya turo ya shigo Zareena biye a bayansa idonta bai fara sauka a ko ina ba sai akan Mu'azz wan da zuciyarta tai wani irin bugun da ba ta taɓa ji tai mata irinsa ba lumshe idonta tayi ta kuma sauke shi a kansa a daidai lokacin shi kuma ya miƙe ya cewa Sulaiman.
"Thanks."
a saman laɓɓansa kafin ya fara takunsa na cikakkun maza zai bar office ɗin ba tare da ya kalli fuskan wanda suka shigo office ɗin ba, yayin da Zareena tai mutuwar tsaye tana binsa da kallo,ganin yana ƙoƙarin barin office ɗin ba ta san san da bakinta ya furta.
"Hey." Ba ganin ko juyowa bai yi ba bare ya nuna ya jita yasa ta saurin zuwa ta sha gabansa yana gab da isa bakin ƙofar,a jikin ƙofar ta jingina ban da haka kusacinsu zai yi kusa sosai duk da haka suna jiyo ƙamshin turaran junansu da ya fara saukar musu da kasala,barema Zareena ta ji labari dan ƙamshin turaran El ɗin ya taimaka ƙwarai gurin ƙara matar mata da jiki da jin ƙaunarsa na narkar da jini da jijiyarta.
Bugu zuciyarta ke yi tana tsalle a ƙirjinta amman haka tayi ƙundin balar miƙa masa kyakkyawan farin hannunta dan idan ta bari a yau ya kubfce mata ba ta san inda zata samo shi ba wanda hakan ke nufin hautsina kyakkyawar rayuwar da take gudanarwa.
"ZAREENAH TAHIR ABDUS SALAM."
Ta faɗa tana ƙarewa kyakkyawar fuskarsa kallo,idanuwansa ya sauke a kanta wanda har lokacin basu koma ainihin yadda suke ba,cike suke da buƙatar wanda zai ɗebe musu abinda suke ji cikin jini da jijiyarsu.
Kallonta yake sosai kallon da bai taɓa yiwa wata mace makaman cinsa ba ko don halin da yake ciki ne,ko kuma kyahun Zareena da kyahun surarta ke fisgarsa oho?
Zareenah kyakkyawa ce sosai kyawun da yakai a kira shi da kyau,kyawun da ta yo gadonsa gurin iyayanta har ta so ta zarta su a kyau,farinta har wani shaiƙi yake yana ɗaukar idon mai kallonta.
Har ta fara sarewa zai kulata ganin yadda yayi bakam da ita,kallon da yake mata ma ba ta ankare ba saboda na ƙasan ido yake mata sai dai tana jin yadda jikinta yake mata rawa sosai,yayin da Abie da Sulaiman suka zuba musu ido suna ganin sarautar Allah.
Kyakkyawan farin hannunsa wanda ke cike da gargasa baƙa wuluk tana zuba shaiƙi ya miƙo mata yayin da ta saki kyakkyawan murmushin da ya bayyana kyawawan haƙoranta farare tasss da suka ƙara ƙawata kyakkyawar fuskarta ta sanya hannuta cikin nasa wanda a lokaci ɗaya suka ji sauyawar yanayin jikinsu musamman ma shi da yake cikin halin buƙatuwa dan haka da sauri ya zare hannunsa daga cikin nata kamar anai masa dole ya furta.
" EL MU'AZZ ALIYU FANDA."
Murmushi tayi kafin ta furta.
"Nice name."
Ta buɗe hand bag ta ciro wani kyakkyawan kati ta miƙo masa,kamar bazai ansa ba sai da ya gama shan ƙamshinsa kafin yasa hannu ya ansa, can ƙasan maƙoshi ya furta."Ba ni hanya na wuce."
Tana bin fuskarsa da ke kuma matar da ita cikin soyayyarsa ta lokaci guda ta matsa ta bashi hanya kafin ta furta.
"Pls ina jiran kiranka."
Ba tare da ya nuna alamun ya jita ba yasa kai ya bar office ɗin yayin da Sulaiman ya sauke ajiyar zuciya cikin ransa yace.
"Ki ma godewa Allah da kika samu ya saurareki har ya haɗa hannu da ke daga dukkan alamu shima yana da interest a kanki."
Ita ko Zareena gurin Abei ɗinta da ke tsaye ta nufa ta rungumesa haɗe da lumshe idanuwanta cikin kasalalliyar muryar da soyayyar El ta saukar mata da ita tace.
"Abei ina son shi,wallahi Ina ƙaunarsa Abei ka ji zuciyata."
Ta kamo hannunsa ta kai saitin in da zuciyarta ke mugun bugawa.
"Subhanallah, ina burin karatun naki Baby?"
"Na ajiye shi daga yau Abei aure nake so ba da kowa ba kuma da shi,idan yaso karatun ya biyo bayan komai."
Numfasawa yayi, kafin yace.
"To zauna likita ya duba ki tukunna idan munje gida ma ƙarasa maganar."
Murmushi tayi a ranta tana jin daɗin wannan ciwon idon da yayi sanadiyar haɗuwarta da El kafin ta ƙarasa gaban kujerar da aka tanada dan zaman mara lafiyar da zai gana da doctor, yayin da Sulaiman da Abei ke gaisawa yana masa bayanin ciwon Zareenan ita kuma idonta ya sauka a in da sunan doctorn ke rubuce.
Sulaiman Aliyu Fanda. nan tayi rewending sunan da El ya gaya mata.
"El mu'azz Aliyu Fanda. Murmushi tayi yayin da ta fahimci 'yan uwa ne da wannan likitan ko ba komai ta samu yaƙinin ko bai kirata ba tana da tsanin da zata hau ta lalubo shi.
Magani itama ya bata na sha da na ɗigawa ya kuma ce ta rage ta'ammali da ruwan sanyi,dan kwa gwana ce gurin wasa da ruwan sanyi,duk tsananin sanyi wanka ma da ruwan sanyi take kuma duk wani abu na sha ba za ta sha miki shi dalan dalan ba sai mai matuƙar sanyi shiyasa wani zubin Ammi takan kirata da kwaɗuwa gurin son wasa da ruwa,dan zata iya wuni cikin swiming ba tare da damuwar komai ba.
A mota ban da zancen El babu abin da takewa Abei,suka je gida ta ɗorawa Ammi ma har sai da ta gaji ta hau ta da faɗan rashin kamun kai da kunyar da aka san ɗiya mace da ita.
Sai da Abei ya shiga ciki ya nuna mata cewar ai ba laifi ba ne don mace ta nuna tana son namiji da zata hauta da faɗa ai ba kanta farau ba kuma kanta ƙarau ba asali ma sunna ta daɓɓaka tun da hakan ya faru da Annabi Muhammad (S.A.W) da matarsa ta fari Sayyadatuna Nana Khadija.
Tun daga nan ta kawo ido ta zuba musu kan lamarin El da shi da 'yar tasa dan taga alamun anan ɗinma bayanta zai bi gurin yi mata auren da ta nuna tana so duk kwa tsananin so da burin zurfaffan ilimin da zai bawa Zareenan da ya ci a kanta....
"Ku kallla."Fatma tace da 'yan tawagarta, gaba ɗayansu kuwa suka juya idanuwansu ya sauka akan Sajda,tana taku ɗaiɗai cike da yauƙi da yanga wan da ya zame mata jiki domin kuwa duk in da gayu yake Sajda tasan gayu ta kuma san ta kansa. Abin da ya bawa su Fatma mamaki ba komai ba ne sai yadda Sajda ta samo mayafin da ya mugun shiga da leshin da ke jikinsu gaba ɗaya,anko ne na class mate ɗinsu, sun zaga kasuwanni da dama haɗe da super market suma da dama amma basu samu mayafin da ya mugun shiga da leshin ba kamar yadda na Sajda ya shiga, abin da suke gudu ya faru (Sajda ta fisu ɗaukan wanka) Har ta gifta su ta ankara da yadda suka zuba mata ido kamar su cinyeta ɗanya, basa shiri shiyasa bata shiga shirginsu, su kullum burinsu su fita ɗaukar gayu amman hakan ya gagara saboda ta fisu sanin takan gayun.
"Lafiya dai ko na ci muku bashi?"
" Muna mamakin yadda akai kika samu mayafin da muka gama karaɗe kasuwanni da dama ba mu samu ba."
"Hmm shine matsalarku?"
"Eh"
"To matsalarku tazo ƙarshe in sha Allah zan haɗa ku da NEEHAL COLECTION daga yanzu wahalar neman mayafai ƙare muku da yardar Allah, dan nima tun da aka haɗa ni da ita na huta, duk mayafan da ake so ana samu a gurinta ko wani irin kala ne, kuma masu kyau da ɗaukar ido cikin farashi mai sauƙi."
"Au wai kina nufin mayafin na gida ne ?"
"Eh mana ɗan hannu ne."
Amma ta iya mayafai maza maza haɗa mu da ita dan baza mu shiga gurin bikin nan ba sai da irin mayafin ki muma mu ƙure gayu.
https://wa.me/message/AD4MDTQJLXIRD1
Ku bi wannan link ɗin zai kaiku in da zakui magana da NEEHAL COLECTION daga yau matsalar mayafai ta ƙare muku zaku samu duk kalar mayafan da kuke so cikin farashi mai sauƙi ina mai tabbatar muku zaku ji daɗin muamala da ita.
Ga masu bukatar a tallata musu hajarsu kofa a bude take cikin farashi mai sauki.
#09037093702/08082007142
#BR
[10/3, 20:47] RASHUNA: BEBEE'ARTH
Wattpad@Rashuna
KANA NAKA
(Allah na nasa )
21
KANA NAKA FREE NOVELL NE.
Yanzu nake typing nasa shi yasa wani zubin kuke samun delay kafin nayi post saboda abubuwan rayuwa aka ce yau da gobe ta fi ƙarfin wasa Ma su buƙatar compleet ni kaina ba ni da shi ku biyo ni a sannu har mu cimma ga cinyewa mu siɗe gaba ɗaya.
Da ƙyar ta ga wucewar kwanaki biyar tana jiran tsammanin kiran waya daga El amman shiru kike ji tamkar maye ya ci shirwa.A kwana na biyar ɗin ne ta kasa jurewa haƙurinta ya gaza ta nufi asibitin Muwadda.
Direct office ɗin Sulaiman ta nufa, ta same shi ba ya tare da marasa lafiya, yana dai rage aiki a computer ɗinsa,sai da ta zauna akan kujerar da ke gabansa kana ya ɗago kansa ya sauke idonsa kan fuskarta, sarai ya gane ta, amman kwanakin da ya basu ai bai idda cika ba, ko kuma ba ta samu sauƙin idon ba ne?
Ya tambayi kansa,ya kuma bawa kansa amsa da..
"Bari dai to naji me ke tafe da ita ta bakinta."
Hannu ta miƙa mishi su gaisa, ya girgiza mata kai,dan shi irin wannan gaisuwar idan ba da namiji ɗan uwansa ba ba ya yadda yayi da kowa.
Murmushi tayi dan ta gane nufinsa kafin tace.
"Ya ka ke, ya aiki?"
"Lfy Alhmdlillah, da fatan dai ba idon ne ya matsa miki ya sakaki dawowa ba?"
Girgiza kai tayi kafin tace.
"Wannan karan zuciya ce ta matsa mini Doctor,ido tuni ya warke dan na ji daɗin maganin da ka bani sosai."
"Alhmdlillh to haka ake so,amman kuma nan ba sashen masu ciwon zuciya ba ne,idan kika fita daga nan ki tambayi ɓangaran masu ciwon zuciya idan kinje sai ki tambayi office ɗin EL MU'AZZ ALIYU FANDA in sha Allah yadda na baki maganin ciwon ido kika ji daɗi zai baki na ciwon zuciya ki ji daɗinsa fiye ma da haka."
Wani murmushin zallar jin daɗin abun da yazo mata a sauƙaƙe ta saki,kafin ta tashi cike da zumuɗi tace.
"Na gode Doctor, ina da yaƙinin idan na ganshi ciwon zuciyar zai raba ni da ita gaba ɗaya. Allah ya baka abin da kake so duniya da lahira."
Tana kawowa nan ta bar office ɗin cike da karsashi.
Bin bayanta yayi da ido cike da nazarin maganarta sai lokacin ma ya tuna abin da ya faru tsakaninta da EL ɗin ranar nan,ta yuhu abin da ya kawota kenan ta kuma same shi cikin sauƙi.
Kai tsaye ta murɗa handle ɗin ƙofar office ɗin nasa ta shiga wani sanyayyen ƙamshi ne ya doki hancinta da ya samar mata da nutsuwa kaɗan kafin ta sauke idonta a kansa nutsuwar ta zo mata gaba ɗaya.
Sanye yake da wasu arnayen suit blue da sukai matuƙar dacewa da farar fatarsa, ina ga dai ya fuskanci yadda blun abu ke yi masa kyau shi yasa yake saka shi, dan siririn glass ɗin idonsa ma blue ne da yayi matuƙar ƙarawa fuskarsa kyau, fuskar nan a haɗe ba wani annuri yana rubutawa mara lafiyar da ke gabansa magani a jikin kati, kyakkyawan farin hannun nan nasa mai cike da gargasa ɗaure da wani arnen agogo blue shima sai ɗaukar ido yake.
Lumshe idonta tayi ta buɗe ta fara takowa cikin office ɗin cike da kuzari da shauƙin soyayya, a kan ɗaya kujerar da ke gabansa ta zauna haɗe da sauke wawuyar ajiyar zuciya ganin ko in da take bai kalla ba yanawa mutumin da ya rubutawa magani bayani.
Ko da ya gama da shi bayan ya fita ma wata mata ce ta shigo, haka ya dinga duba marasa lafiyarsa ba tare da ya nuna alamun wanzuwarta a gurin ba, ita kam hakam bai dameta ba sai morewa kallonsa kawai take zuciyarta na sanyaya da farin ciki.
Can da ta ji ƙishi ta tashi ta nufi in da ta hango fridge ɗinsa yake ta ɗauko gorar ruwa da lemo da ɗan ƙaramin cup, kan table ɗin da ke gabansa ta ajiye cup ɗin ta tsiyaya masa ruwan kana ta kai gorarr bakinta,sai da ta shanye ruwan tass kana ta cilla gorarr cikin kyakkyawan duthbin ɗin da ke gefenta ta ajiye gorar lemon akan table ɗin dan sai ta ji ruwan kawai ya wadace ta,ga mamakinta sai taga ba komi a cup ɗin da ta tsiyaya masa ruwan,wani murmushin jin daɗi tayi kana ta buɗe gorar lemon shima ta tsiyaya masa.
Wata balarabiyar budurwar yarinya ce ta shigo kyakkyawa da ita, yana duba file ɗinta ita kuma tana ƙare masa kallo, yayin da Zaeenah ita kuma ke kallonta, can taga kallon ba na ƙare ba ne tayi gyaran murya kafin tace.
"Malama kallon ya isa,wannan kallo da kike masa ai ya huce na ƙaidar musulunci,ki kama kanki,kar ki kai shi gurin da ba shi da matsuguni dan wallahi ba ciwon zuciya ba ko ciwon mene ne sai dai ya kashe ki dan baki da matsuguni a gurin nan."
Ba tace mata komai ba sai ƙasa da tayi da kanta har ya gama duba file ɗin nata yayi mata 'yan tambayoyi ya rubuta mata magani.
Tana fita ba tare da ya ɗago kai ya kalli Zareena ba yace.
"Ashe ke da kike ta kallona hakan bai wuce ƙaidar musulunci ba?"
Murmushi tayi da suka nuna jerarrun farare tass ɗin haƙoranta,ashe duk abin da take ya na ganinta yake marmazewa, kana tace.
"To ai ni da ban."
Sai da ya gama duba marasa lafiyan kaf tana zaune tana danna waya ko kuma ta ajiye wayar ta zubawa fuskarsa ido tana ƙare masa kallo cike da so da shauƙin ƙauna.
"Doctor saura ni, nima a duba tawa zuciyar Plssss."
Ta faɗi hakan idonta a kansa.
Sauke birkitattun idanuwansa yayi masu cike da buƙata a kan kyakkyawar fuskarta,kyanta na fusgarsa,halin da yake ciki na gaya mishi tabbas Zareena tazo a daidai ka aureta kawai ka wutawa kanka wahalar da kake sha kullum cikin dare idan har kana son kaucewa aikata saɓon Allah.
Duk da yana ganin yayi ƙarami da aure (A cewarsa ba fa ba tawa ba )a yanzu dan bai shirya masa ba dududu shekarunsa 25 amman jaraba ta saka dole yayi aure yanzun idan har yana son zamansa lafiya musamman yanzu da Zareena tazo ta ƙara birkita masa rayuwa,kullum sai tazo office ɗinsa tun daga wannan ranar, kuma ba ya iyawa idonsa shamaki a kowata kusurwa ta jikinta hakan ya ƙara dagula masa lissafi fiye da baya ma dan haka ya tsayar da matsayar auranta kawai ya huta.
Sulaiman ya gayawa shi kuma ya gayawa Daddynsu, cike da farin ciki kuwa suka zo shi da yayyansa suka nemawa El auran Zareena gurin Abei ɗinta, ba'a wani saka lokaci da yawa ba saboda roƙon Mu'azz dan haƙurinsa na kai ga gazawa musamman yanzu da har rungume juna suke kuma hakan yazo yana damunsa.
Dududu wata guda aka saka, tun da ko wane ɓangare jiƙe suke da naira shirin aure a wata guda ba wahala zai musu ba.
Momy ta so Sulaiman ɗinma ya shirya suyi auransu lokaci guda, amman yace kawai taci gaba da masa addu'a har yau bai samu zaɓinsa ba. (Ashe zaɓinsa na nigeria, nigriar ma cikin garin kano, kanon ma cikin badala.)
An sha biki na kece raini na al'adu da ban da ban, a nan saudiya aka sha bikin dan su Mommy nan suka zo aka sha bikin gaba ɗaya, washe garin da aka kai amarya suka cala yawon shaƙatawa in da suka fara sauka a HONG KONG.
Ita wannan ƙasa wacce har yanzu tana ƙarƙashin Ingila,girmanta kamar sukwaya mil ɗari uku da tisiin da takwas ne,kuma mutanen cikinta zasui milyan biyar mafi yawancinsu kuma mutanen sin ne.
Babban birninta shine VICTORIA birni me ban sha'awa da dogon tarihi da suna cikin duniya.
Shi wannan tsibiri yana kusa da centon,wani ɗan kogi ne me faɗi kamar rabin mil ne ya rabasu da china,ko da yake akwai 'yar. gintuwar sashin ƙasar a gefen tsibirin, Hong Kong tana nuna halayen china dan tafi ko wana gari na kudu maso gabacin Asia yawan mutanen Sin.
Kuma wannan tsibiri wan da yake da ƙauyukansu a gefensa yana da abubuwan ban sha'awa da zai nunawa maziryarta.
Saboda ƙawatattun gaɓuna da yawan mutane sukan zo wannan tsibiri daga garuruwa masu ni sa dan yawan shaƙatawa.
Ma fi yawancin saye saye a wanna ƙasa akan yi shi ne kwoloon a ƙetaren ruwa wan da ake ƙetarewa a kwale kwale.
Mu'azz ya ɓarji amarcinsa son ransa yayin da Zareena ido ya raina fata dan ta wahaltu a hanunn El ainun.
satinsu guda a hong khong suka cala Calcuta in da tayi karatunta, ta kai shi tsadaddun makarantun da tayi in da ya ƙara jinjinawa so da ƙaunar da mahaifinta ke mata.
A calcuta ma sati guda suka yi kana suka nufi BANGHOK shima sukai sati guda kana suka wuce.SINGAPORE.Ɗaya daga cikin ƙasashen da suka haɗe suka yi tarayyar malaysia.
Sun isa wannan birni bayan tafiyar sa'a biyu saman tekun india, a wannan tsakanin ne aka nuna musu yadda ake saka wata irin riga wacce ake kira Life Jecket saboda ko wani haɗari zai abku,amman dai sun isa Singapore lafiya bayan tafiyar kamar mil ɗari tara da tamanin daga Banghok yayin da suka sauka a wani rantsatstsan hotel mai suna Ruffles Hotel.
A nan sai da suka yi sati biyu cur suna yawan shaƙatawa da ɓarje amarci kafin su nufi babban birnin MALAYSIA watau Kuala Lumpur.
Sun isa Kuala Lumpur bayan tafiyar sa'a ɗaya da minti biyar, kuma nisan wannan tsakani mil ɗari uku da hamsin ne kurum.
Ita wannan ƙasa watau Malaysia tarayya ce ta ƙasashe masu mulkin kansu kamar guda goma sha huɗu.Mutanen wannan ƙasa kuwa ana kiransu Malays,waɗan da kuma mafi yawancin su musulmai ne.
Sun sauka a wani ƙasaitaccen hotel wan da ake kira Jalon Clifford.
Sai da suka yi wata guda cur kana suka fara shirye shiryen komawa.
A daren washe garin da zasu koma ne bayan ta fito daga wanka ta zauna