x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 20 - KANA NAKA ALLAH NA NASA complete document

  • 57001 words
  • 60000 words
  • Out of 66841 words

Category: Love Stories

Views 300

25 Aug 2025
Start ads
After Image Ads
tahowa da gawarsa."
Abin da kawai yace kenan ya kashe wayar haɗe da kife kansa ya fashe da sabon kukan da ya zo masa.

Momy kam.
"Innalillahi wa inna ilaihir raji'un."
Ta ambata haɗe da zubewa daɓas a kasa a zaune,yayin da su Abba su ka yo kanta da tambayar lafiya me ya faru?

"Sulaiman,Sulaiman Sulaiman"

Kawai take ambata,ruɗewa da tashin hankali ma yasa ta manta ba ta ambatar sunansa.

Da ƙyar ta iya furta musu cewar.

Sulaiman ya rasu,ta zube a sume a gurin yayin da maganar ta sauka a kunnena a gangaro gadon da nake kai za'a shiga thearter da ni,gab gab jikina ya hau wani irin mazari da kyarma yayin da suka ƙara hanzarin shiga da ni cikin ɗakin,sai dai kuma ana shiga da ni ɗakin ragowar 'yar da ke cikina ta keta ƙasana ta fito,itama kamar 'yar uwarta da wani irin azababban kuka ta fito,kukan da ya zarta ko wani kukan da kuka san ana haifar jarirai da shi,dole su koka kam,sun duro duniya a marayu,a ranar da mahaifinsu ya bar duniyar.

Ina haihuwa na dinga wata irin jijjjiga,wan da da ba dan taimakon gaggawar da aka ba ni ba tsaf zan iya rasa hankalina da tunanina,ko kuma ido ko kunne,wai ashe idan aka yi jijjiga wani ruwa ne ke tsartuwa a ƙwaƙwalwa,idan ya bi ta ido shine ake rasa ido,idan ya bi kunne shima a rasa kunne,idan ya bi ta cikin ƙwaƙwalwa a rasa hankali da tunani.

Sai da na kwana uku kafin na samu kaina,jaririyar ma sai madara aka dinga ba ta,dan ɗayar tun a ranar ta koma,saboda wahalar da ta sha a ciki kafin ta fito,komai na jaririyar Momy ce ke mata,ba ta yadda ta bawa kowa ita,tana jin kamar riƙe yarinyar a jikinta ke rage mata kewar rashin Sulaiman a duniyar,yaron da ta kwana da sanin duk cikin 'ya'yanta ta fi sonsa da ƙaunarsa,kamar yadda ya fi dukkanin 'ya'yanta nuna mata so da kulawa.

Sai da na ƙara sati biyu a asibitin suka tabbatar da lafiyata ta ko wani ɓangare bayan dogayen tasa tasai da muka sha.Sai damuwa da kunci kuma wannan na rashin da ya same ni ne dole sai a hankula zan warware.Gwaggo ce ta zauna da ni sai bayan sadakar bakwai Momyn ta zo Gwaggon ta koma gida,sai a ranar na ɗora idona a kan jaririyata,a kuma ranar na fara shayar da ita Nono,da sauri kuwa ta kama ta fara sha,ta ji abin da ba ta taɓa sanin a kwai shi ba,yawancin jarirai sukan fara saninsa a ranar da suka duro duniya ita ko sai da ta kwana tara kafin ta san shi,tausayinta ne ya dabai baye ni,hawayen da dama a kusa suke suka wanke fuskata,na hau kuka da shesh sheƙa na tausayin kanmu,ga ta dai ta duro duniya a marainiya,kamar yadda nima na kasance,bam-bamcinmu ni mahaifiya na rasa ita mahaifi ko wani irin ƙalubale za ta fuskanta cikin rayuwa?
Wannan Allah ne ya barwa kansa sani,sai dai zan ta yi mata addu'a daga yau har zuwa ranar da numfashina zai katse akan koma wani ƙalubale ne zai fuskanci rayuwarta yasa ya zo mata da sauƙi.

Kallon Momy na yi da duk ta faɗa ta zabge,dan mutuwar nan ta mata duka ba na wasa ba,ƙarfin hali kawai ta ke.
Nace.
"Momy wani suna aka saka mata?"

"Ai ina tunanin an barta da Khadijan ne kawai,ba'a yi mata yanka ba,mun bari a sallame ki tukunna."
Momy ta faɗi haka ne;saboda ranar da aka yi haihuwar ta kira shi ta gaya masa an samu mace, buɗar bakinsa sai cewa yayi.
"An samu Khadija ke nan."

Wannan Momy ta riƙe ta ke ganin a barta da Khadijan kawai,yayin da na girgiza mata kai nace.
"Asiya sunanta Momy,da shi za'a yi mata yanka,saboda ya sha gaya mi ni cewar yana son ya ga ya haifi mace ya saka mata Asiya,ya kirata da Ammi saboda yana matuƙar son sunan da duk wata mace me sunan,kuma a duk 'ya'yan da Allah ya ba shi duk wacce ta yi katari da samun sunan za ta ga so da soyayya da kuma zallar gata in sha Allah,amman kasancewar UMMANMU ba ta raye idan muka fara haihuwar mace Khadija zamu saka mata,idan wata ta biyo baya ita kuma sai mu saka mata Asiya."

Ɗagowa na yi na kalli Momy idona cike da hawaye na ce.

"Yanzu to ya na ina Momy?Bare mu haifi wata macen mu saka mata Asiyan,dan haka wannan da Allah ya raya mana sunanta Asiya zamu kirata da Ammi,idan Allah ya ci gaba da bamu aron rayuwar,za mu cika rayuwarta da soyayya da gata,ko don mu cika masa birinsa a bayan ƙasa ta rufe masa idanuwansa ko Momy?"

Na kai ƙarshen maganar muryata na karyewa kafin kuka ya ci ƙarfina,rungumo ni Momy tayi jikinta tana gyaɗa mini kai,dan itama kukan da take ta riƙewa ne ya gaza riƙuwa,ya hanata furta ko da kalma daya.
Kuka nake sosai a jikinta,tana shafa bayana haɗe da share nata hawayen da suka ƙi riƙuwa.

MU'AZZ

Bai taɓa tunanin a kwai rana irin ta yau da shima zai ji so da ƙaunar ganin jininsa a duniya ba,sai yau ɗin da Sulaiman ya turo masa hoton jaririyar da aka haifa masa da sunan tasa ce,mallakin Bro ɗinsa,a take zuciyarsa ta buga da ƙaunar yarinyar ya ji ba shi da wani buri da ya wuce ya ji yarinyar a hannunsa,dan haka a take ya nemi flight ɗin da zai sauka Nigeria washe gari,wan da daa Calcuta zai je gurin Zareenah da bayan dawowarta daga India ta tafi wani course ɗin na shekara biyu a ɓangaren aikinta na Ghynic saɓanin wancan da taje akan karatunta na Bussiness da ta samu ta kammala shi shima.
Ya samu jirgin da zai sauka Nigeria amman sai ƙarfe huɗu,bai damu ba,saboda ya san a washe garin dole zai isa Nigeria,hakanma zai ba shi damar har haɗa abubuwansa dan zai ɗebi kwanaki kafin ya dawo Saudiya,sun ba shi hutun aiki har na tsayin wata uku,dan haka daga can Nigeria Calcuta zai huce gurin Zareenah dan yayi kewarta ba kaɗan ba.
Sai dai kuma a washe garin komai ya canja,me makon tafiyar farin-ciki da zumuɗin ganin 'yarsa sai yayi tafiyar damuwa da baƙin cikin ba zai ga ko gawar ɗan uwansa ba,tun da ya tabbata kafin ya ƙarasa nigeriar ma an kai shi.
Mutuwar Bro ɗin nasa ta gigita rayuwarsa fiye da yadda alƙalami zai rubuta,ashe rabuwar ƙarshe su ka yi zuwan da su kai saudia? Da ga ranar da ya kai su airport daga ranar ba zai ƙara sauke idanuwansa a kansa ba a she? Sai dai video call ɗin da su ka yi,ya tuno maganarsu ta ƙarshe a jiyan bayan ya turo masa hoton Babyn ya ke cewa.
"A daa kullum ina kwana ina ta shi da tsoron cikin,Daddy,Mommy,Mu'azz,Nassrin ko waye zai riga yin gaba,ma'ana ko waye zai riga mutuwa?sai Najjwa ta ƙaru cikin tsoron nawa,yau kuma ga ƙaruwar Baby na samu,ga wata can ko wani suna gumurzun isowa duniyar,amman dukkanku ina fatan ku ga gawata ba dai ni naga ta ku ba,don bansan wani irin hali zan shiga muddun na rasa ɗaya daga cikinku ba."

"Mu ga shi nan ka tafi munga taka gawar ba tare da ka san halin da zuƙatanmu su ke ciki ba."
Ya kai ƙarshen maganar yana goge hawayen da ke ƙara zirarowa bisa fuskarsa da tayi jajir saboda kukan da ya ƙi tsagaita masa ko kaɗan.

Tun isowarsa Nigria jin Babyn da Bro ɗinsa ya tafi ya bar masa a jikinsa kaɗai ke sanyaya masa zuciyarsa,shi kansa be san wani irin gata da soyayya zai bawa wannan jaririyar ba,a sauran tsayin rayuwar da za ta rage masa a gaba ba.Haka suke fama da Momy ya zo ya ɗauka ta biyo shi ta karɓe,har yau da suka taho asibiti ba tare da saninsa ba shine ya biyo bayanta.
Tsaye yake yana binsu da kallon yadda suke kuka,ba tare da sanin wanzuwarsa a tsaye ba,wan da shi kansa a lokacin sai da idonsa ya kaɗa,amman bai bawa hawayen damar fitowa ba,duk da sau tari ba damarmu hawayen ke jira ba su na zuba ne bisa raɗin kansu a wani lokacin,dan wani zubin duk yadda muka kai ga son zubarsu basa bamu haɗin kai.

Gyaran murya yayi kafin mu ankare da tsaiwarsa a gurin kana yace.
"Momy ke da za ki rarrashe ta,sai ki biye mata ku dinga kuka?a fa gadon asibiti take,me kike tunani da Doctor ya shigo ya tarar da ku a haka?
Haƙuri za mu ƙara Momy,kuka ba zai mana maganin komai ba,ya fi buƙatar add u'armu yanzun sama da komai,damuwa da ƙuncin da zamu shiga ba zai masa maganin komai ba."

Jinjina kai Momy tayi,duk da shi kansa a muryarsa ta ji yadda zuciyarsa har lokacin a karye ta ke,domin kuwa mutuwar Sulaiman ta karya musu zuciya gaba ɗayansu,sauƙin da aka samu wannan Babyn tana dishashe musu wani gurin tun da dai Gurbin ido ba ido ba ne.

Washe garin da aka sallame ni aka yiwa Ammi yanka,tun a nan na tabbatar da ba ƙaramar 'yar gata za'a yi ba.
Abba shanunsa da ban,ga na Daddy shima,ga kuma na babanta Mu'azz,shi Ku ma Baffa raguna tiƙa-tiƙa,ga na Miqdad abokin Man shima ya kawo manyan raguna bayan uban kayan da ya jubgo mata.Duk aka haɗa aka yanka,a ka yi sadakarsu tare da fatan Allah ya raya mana Asiya Sulaiman Aliyu Fanda(Ammi)

A ranar ne Safiya tayi ƙundun balar tunkarar Momy,rabon da su saka juna a ido tun ranar da Safiyan tayi nasarar fitar da Momy daga gidanta.
A 'yan kwanakin nan cikin nadama da da na sani ta ke,domin kuwa abin da ta aikata za ta iya cewa be amfaneta da komai ba,duk ta in da aka je aka dawo Momy ke da nasara a kanta ba ita ba.
Ba ta auri Aliyu dan dukiya ba,don za ta iya cewa mahaifinta ma ya fi shi arziƙi nesa ba kusa ba,ta aure shi ne saboda so da ƙaunar da ta ke masa,amman abin da ya fara sanyaya mata jiki shi ne;ganin irin katafaren gidan da Momy ta ke ciki,bi ma'ana da ta yi nasarar fitar da ita daga gidan nan,sai ta auri wani attajirin da dukkan alamu sun bayyana sai dai su goga kafaɗu da Aliyu ba dai wani ya fi wani ba,ga 'ya'yan da ta tsira da su wan da ita sai da ta bada mahaifar da zata ɗauki cikinma kana ta samu nasarar shigowa gidan ,dan haka ta ke ganin duk in da aka je aka dawo Momy ke a sama ita a ƙasa wanwar.

Abu na biyu da ya ƙara sanyayar mata da jiki,kwaɗaituwa da son ganin jininta da Allah ya jarabci zuciyarta da shi,al'halin babu damar samu yanzun,haihuwa ba bu mahaifa abu ne da ba zai taɓa yuyuwa ba,dan haka ta ke ɗan ɗanar ɗaci da baƙin cikin abin da ta aikata,ta fara da na sani da kuma zazzafar nadama,dan ta fahimci haƙƙin Momy ya fara bibiyarta,dan kullum cikin mugayen mafarkai ta ke,dan haka ta samu Daddy ta warware masa ta yadda a ka yi ta auresa ko ta samu ta rage wani nauyin zunubin.
Ga mamakinta Daddy sai ce mata yayi.

"Tuni na riga na fahimci hakan Safiya,ture ta aurenki da na yi,don wannan kan iya faruwa ba tare da wani asiri ba,amman ace da wannan bakin nawa na furtawa Hasiya saki,abun a jinjinawa ne,da kuma ayar tambaya a kai.Duk da hakan ma zan iya kiran rabuwarmu tsananin rabo da kuma zazzafar ƙaddarar haihuwar towince ɗin nan,dan haka ni ba ki da damuwa da ni don tu ni kika shiga cikin alfarmar rigar mahaifinki,don magiya da roƙon da yayi mini a kanki ne kawai ke riƙe da igiyar aurenki ba cin haka da tuni na daɗe da tsintsinkata,dan haka Hasiya ya kamata kije ki nemi yafiya ba ni ba."

Tun tuni take son zuwa ta nemi yafiyar Momy amman nauyi da kunyar Momyn ke daƙilar da ita,har aka yi mutuwar nan da ƙaruwar da aka samu ta kasa zuwa,duk da so da ƙaunar jaririyar da Allah ya jarabci ruhinta da shi,sai yau dai ta yakice kunyar
ta zo tunkarar Momyn gaba da gaba.

Momy ba ta jaa da nisa ba tace ta yafe mata,Allah ya yafe mana ba ki ɗaya,ko yanzu dai Allhamdlillah ta san itace da nasara.

Kaya ninki guda ta kawowa Ammi,masu kyau disigners kala-kala,haka ma Daddy ya ƙara jibgo mata wasu kayan bayan wancan da ya kawo mata,tun a yanzu dai ina da yaƙinin ba za su bar Ammi tayi kukan rashin Uba ba,sai dai rashin mahaifi kawai,dan da alamu baza su barta ta ɗanɗani ɗacin maraici ba.

Idan har Ammi ta zo hannuna to nono zan bata,duk wata hidimarta Momy ce akan gaba,idan ba ta hannunta ta na hannun Babanta Mu'azz,wan da sam ya ƙi komawa yace bai san ta yadda zai yi rayuwa a ƙasar da ba Ammi ba.Ranar da ta cika wata ɗaya a duniya har da yanka mata cake tsabar taya ɓera ɓari,to ban da taya ɓera ɓari yarinyar da ke kwance ba ma ta san duniyar da ta ke ciki ba aka yankawa cake?har da wani in sha Allah ya fara kenan duk watan duniya sai ya yanka mata cake a haka har ta yi wayon da za ta fahimci abin da ke faruwa.
Su Baba Mu'azz masu 'ya kenan,ba dama ya ji kukanta tuni zai gigita ni,wa taran ma tsare ni yake sai na bata mama a gabansa,ji yake kamar ya zira hannu ma ya ciro ya bata,a kwai ranar da yayi a gaban Momy ai kwa ta fatattake shi tana ta faɗan kamar a kansa aka fara haihuwa,idan jaririyar ya ke so ya je 'yar bokon matarsa ta haifa masa,ita wannan ko me yayi halalinsa ce.
Yau ma haka kawai ta ke ta zunduma mini kuka,na rasa me yake damunta ga Momy sun fita da Abba,Nasrin kuma ina tunanin sun yi bacci ita da twince,dan da tuni suna naniƙe da Ammin,shi ko Mu'azz yau sam ban sanya shi a idona ba,kuma ban yi tunanin zuwa gurin Gwaggo ba,sai da naga kukan ba na ƙare ba ne duk ta firgita ni kana na miƙe ko hula ban nema na sakawa Kaina ba tsabar a firgice na ke.

Ina ƙoƙarin fita shi kuma ya sako kai,mu ka yi karon da nayi taga taga Zan faɗi yayi azamar sanya tafukan hannunsa ya taro mu gaba ɗaya cikin faffaɗan ƙirjinsa sai ji kuke ɗif kukan Ammi ya ɗauke sai zuciyoyinmu da ke buga da wani irin sauri,sai jin muryar Momy muka yi a kanmu tana faɗin.
"Subhanallah,Mu'azz me ye hakan nake gani?"
Cire ni yayi daga jikinsa haɗe da karɓar Ammi da ke hannuna wacce ta ci gaba da tsanyara kuka kamar me jiran maganar Momy ta ba ta umarni,bai ce komai ba sai Ammi da yasa a kafaɗa ya na girgizawa ga Momy kuma ta tsare mu da ido.

Ƙasa na yi da kaina kafin nace.

"Momy ba fa wani abu ba ne,fitowa zan yi ina ta sauri zani gurin Gwaggo Ammi ta ishe ni da kuka mu ka yi karo,na tafi zamu zube ƙasa shine ya taro mu."

Jinjina kai tayi tana mayar da kallonta kan Mu'azz ɗin da ke ta faman jijjiga Ammi har an samu kukan nata ya fara yin ƙasa,fuskar nan a murtuke ransa yana suya,shi be san me Momy ta ke nufi da shi ba,me zai nema a gurin matar wansa? ban da ma da Ammi a tsakani me zai haɗa shi da ita,bai ma ga abin da zai zaunar da shi a ƙasar ba har yanzu.
Takawa yayi cikin takun nan nasa na ƙasaita zai bar ɗakin.
Momy tace.
"Idan tayi bacci ni za ka kawowa ita."

Buɗar bakinsa sai cewa yayi.

"Momy ki fa kwantar da hankalinki ɗakin nanne dai ba Kya so na shigo,to na daina shiga in sha Allah,ni ban ma ga abin jan hankali jjkin bazawarar 'yar taki da kike ta kaffa kaffa da ita,ni da nake da Balarabiyar mata me zanyi da wannan?"

Ya kai ƙarshen maganar yana wani mele baki.

"Ko ma dai meye kada na ƙara ganin ƙafarka a ɗakin nan,'yata kuwa ke da abun jan hankali ba wannan ƙemashashshiyar matar taka ba."
Ni ko bakin gado na kai zaune,maganganun nan nasa biyu suna mun suya a rai,bazawara,ko ma dai meye wansa ne ya mayar da ni bazawarar,jikin mudubi na je ina ƙarewa halittata kallo,tuni majigin hoton matarsa ya fara yawo a idona,tabbas kam ta fi ni kyau a fuska nesa ba kusa ba,ni kuma na fita kyahun jiki,dan nikam ko ta ina a cike nake masha Allah,ga fatata na samun gyara kullum cikin sulɓi da shaiƙi ta ke ta na ɗaukar ido,amman shi ne zai ce babu abun jan hankali a jikina,ƙwafa na yi haɗe da jan tsaki cikin takaici.

Washe gari Ammi ta ta shi da zazzafan zazzaɓi,babu shiri muka nufi asibiti da ita,kafin mu ƙarasa asibitin har suma ta fara yi tsabar zafin zazzaɓin,duk kuma wani treatment da aka bata zazzaɓin sam yaƙi sauka kafin a yi mata gwajin da aka gano abin da yasa mata wannan zazzafan zazzaɓin,ciwo ne a cikin jininta duk shi ya jaza mata wannan zazzaɓin,a kuma shawarar da likitocin suka bamu shi ne a mata juyen jini,insha Allah ciwon ya barta kenan.
Tu ni Mu'azz ya fara mana shirin tafiya Saudia,don ya kafe cewar sai a can za'a yi mata,to da yake duk an yadda da ingancin asibitin kuma fatan lafiya ta har abada a ke wa Ammin shiyasa kowa ya bashi a manna.

Kwana biyu tsakani jirginmu ya ɗaga ƙasa me tsarki,har da Momy da Abba,da Zuwaire,Daddy da Aunty (Safiya)washe gari suma zasu biyo bayanmu.
Motar da ta ɗauke mu direct asibitin ta sauke mu,tu ni aka shiga bawa Ammi kulawa musamman da aka ga Mu'azz a matsayin mahaifinta.Daga nan aka kwashe mu zuwa gida dan mu huta,dan basa buƙatar masu jiyya,suna da ma'aikatansu masu kula da marasa lafiya babu ha'inci,dan haka a shawarce suka bamu mu bari sai zuwa gobe ma dawo kafin nan duk wani gwaje-gwaje an mata,an gano dukkanin wata matsala.

Ni dai kam ranar kasa bacci nayi,juyi na dinga yi a
End Ads