asabar kenan a ranar na fara zuwa makarantar;Irshadul ad'fal al'muhajurun k'ofar na'isa lokon mak'era.
Makarantar akwai karatu sosai ga k'ok'ari su na yin boko,islamiya,makarantar dare da ta allo,dala'ilu.
Dala'ilun muka shiga muke zuwa ranar al'hamis da juma'a,dare kuma muka shiga ta nan unguwarmu indabawa kenan,anan muke zuwa har ta magariba,karatu muke sosai,mun fanso duka littafan da ake koya mana.
Gwaggo ta ji dad'i sosai ganin yadda na mayar da hankali kan karatuna,duk silar k'awan cenmu da Nauwa,tace mana.
"Ai irin k'awancen nan ake so,Allah ya shi muku al'barka ya rabaku da kaidin k'awaye."
Mukace
"Amin Gwaggo"
Tace."Bara na baku wata addu'a wacce ma'aiki ya umarcemu da mu dinga yawaita yin ta,dan kariya daga aboki makiri ko k'awa makira."
Mukace."Muna saurarenki Gwaggo" Ta fara karanta mana muna rubutawa kamar haka:
"Allahumma inni a'uzu bika min khalili makirin;aina'u tariyani,wa k'albuhu yar'ani,wa'in ra'a hasanatin dafa'aha,wa'in yara saiyi'atun az'aha."
Fassara.
"Ya ubangiji ina neman tsari daga aboki makiri;wanda babu ya ni a idonsa,a zuciyarsa kuma ba haka ba ne,idan kyakkyawan abu ya same ni sai ya yi bak'in ciki da hakan,idan kuma mummuna ta same ni sai ya yi farin-ciki da haka yaje ya na yad'awa mutane."
Kwanci tashi har mun shiga jss3,karatu muke sosai ba kama hannun yaro,kullum da yamma sai yayan Nauwara ya yi mana lesson na boko da na islamiya hakanne yasa a boko da islamiya mu ke d'aukan ta d'aya da ta biyu,idan ita ta yi ta d'aya to ni zan yi ta biyu,haka in ni na yi ta d'aya to ita za ta yi ta biyu.
Tun ranar da Abbana ya kore ni daga gidanmu ban k'ara marmarin zuwa gidan ba,shima kuma babu ruwansa da lamarina ko gidan Baffa yazo ba ya nemana nima sai na ja jikina duk tsananin so da k'au
nar da nake masa haka na hak'ura tun da ba ya maraba da ni anman kullum na yi sallah sai na yi mishi adduar Allah ya kar kato da hankalinsa kaina,sannan naiwa mahaifiyata da kakata da dukkanin wanda suka rigamu gidan gaskiya,Allah ya jik'ansu ya gafarta musu. Tunda na yi wayo nake tambayar Abbana dangin Mamana yake ce mini suna can sierraleon idan na k'ara girma zai kaini nace,to su me yasa basa zuwa yace mini shima bai sani ba,nace ni to ina son na gansu tun da ban san Mamana ba.
Tun a lokcin da mukai zancen yaso ya bibiyi dangin Maman nawa,yasan halin rayuwa ne ya hana su lek'oni dan bai kamata ya watsar da dangin Khadija ba don k'asa ta rufe mata idanu,anman Allah bai nufa ba har Mama ta zo ta kar katar da hankalinsa da tunaninsa akanta da 'yarsa su kawai yakewa kallon ahalinsa.
Kwatsam ina tsakar gida ina shara sai wasu mutane suka yi sallama suka shigo sai na amsa musu nace su shiga d'aki Gwaggon na ciki,ni dai naga sai kallona suke a raina ina ta zancen ko su waye oho?Suka shiga itama Gwaggon ba ta gane su ba,bayan sun gaisa suka ce da Gwaggon.
" 'Yan uwan matar Alhaji Bashir ne da ta rasu."
Gwaggo tace. "Auho ai ban sanku ba shiyasa,Allah ya yi mata rahama. Najwa zo ga 'yan uwan mahaifiyarki"
wurgi na yi da tsintsiyar hannuna na rugo d'akin da gudu sai kuma na tsaya ina kallonsu ina turo baki kafin nace.
"Bama zan kulaku ba,sai yanzu kuka tuna da ni,dan kunga babu idon Mamana."
Nakai k'arshen maganar ina share k'walla,d'aya daga cikinsu ce ta janyo ni jikintta tana lallashina.
"Kiyi hak'uri ba da gan-gan muka k'i zuwa ba,yanayin rayuwa ne ya saka.Inna da Kawu kullum cikin zancen ki suke musamman shi da bai tab'a ganinki ba,sun yi tunanin Babanki zai dinga kai ki suna ganinki tun da ya hana su ke,sai gashi an d'ibi wannan shekarun ba tare da ya kaiki ko sau d'aya ba,kuma idan an kira wayarshi ba'a samu,yanayin jikinsu ya hana su zuwa anman sunce mu rok'i Baban naki akan ya kai musu ke tun da bai zama lallai ya yadda ki bimu yanzu ba."
Kuka na fashe da shi a jikinta tana cigaba da lallashina had'e da tambayar kukan me nake? Cikin shashshek'ar kuka nace.
"Kukan dad'i nake yau naga ahalin mahaifiyata tun da ita ba'a bani damar ko da sanin fuskarta ba sai a hoto,anman yau da na ganku ji nake kamar ita ce a kusa da ni."
"Allah sarki Aunty Khadija,Allah ya gafarta mata." Cewar wacce ke rik'e da ni, muka amsa gaba d'aya da Amin,kafin na mik'e na fita ina cewa.
"Bara na kawo muku ruwa."
Bayan fita ta ce suke tambayar Gwaggo Hajiya Aisha take gaya musu ta rasu,suka dinga jimantawa suna bin bayanta da addu'a.
Ruwan na fara zuba musu a faranti na kai,bamu da lemo da yake dukkanmu ba ma shan lemo me gas sai dai mu had'a kunun aya ko zob'o Baffa yafi son su,to yau kuma duk ya k'are dama a yau d'in muke shirin yin wani,dan haka Gwaggo ta bani kud'i na amso musu kunun aya da zob'on. Gidan su Nauwa na fara zuwa da murnata na gaya mata yau dangin mahaifiyata sun zo,aikam ta taya ni farin-ciki tare muka fito muka je muka siyo musu zob'on da kunun aya muka zarto gidanmu,na d'auko farantai na zuba a kai na kai musu,na d'auko wani farantin na shiga d'akin Gwaggo na ciko shi da dambun naman kaza da yake mu ba ma rabo da dambun nama Baffa da Gwaggo duk suna son shi,gani nima mayyarsa ko abinci zan ci sai na zuba a kai,na kai musu,na gabatar musu da Nauwa suka gaisa sosai suna yaba hankalinta da nutsuwarta.
Yau ba batun zuwa islamiya dan aiki ya kacame mun danma Nauwa ta taya ni sai da muka kusa gamawa sannan ta tafi da cewar za ta dawo.
Dambun couse-couse muka yi da co-slow sai soyayyen kifi,sai kunun aya da zob'o,sai da na yi wanka na yi sallar azahar kana na zubo musu na zubawa Gwaggo nima na zuba na ci,ina jinsu suna ci suna zuba santi suna mamakin 'yar k'arama da ni haka na iya girki,Gwaggo na k'ara kuzanta musu yadda nake da himma a komai ba ma a girki ba don tun dawowa ta gidan na hana ta aikin komai,komai ni nake sai dai wani zubin ta kama mini ko kuma in ina makaranta sai ita ta yi.
Da naga har bayan la'asar Nauwa ba ta dawo ba sai na zuba mata dambun na cewa Gwaggo. "Bara na kai mata."
A lokacin su kuma sun d'an kwanta su huta.
Na zo daidai da zan shiga gidan nasu muka yi kacib'is da Yaa Muhd na tsuguna har k'asa na gaishe shi ya amsa kafin yace.
"Har kinzo? Gashi yau ban jin zamu samu damar yin lesson,sai dai zuwa gobe in Allah yasa zamu gani.". Nace.
"Allah ya nuna mana goben"
Yace.
"Amin."
Na shiga ciki,sai dai ban sameta ba Umma ke cemin ta tafi Islamiya,ta gaya mata 'yan uwan mahaifiyata sun zo ni bazan samu zuwa ba,a raina nace.
"Nauwa mayyar islamiya."
Na bawa Umma dambun na juyo gida muka zauna da su muna ta hira,sai a lokacin suka ce "Ba ki tambayemu sunayenmu ba." Nace "To ai kune ba ku gayan ba."
Gwaggo tace.
"To ke ba sai ki tambaya ba banda sokanci irin na 'yar fari."
Na k'arashe mata da. "Kuma auta ba."
Dariya muka saka gaba d'ayanmu kafin su fara gayan sunansu, d'aya tace sunanta Maryam,d'ayar Halima,sai Hafsa,Hafsan itace k'anwar mahaifiyata,su kuma 'ya'yan yar mahaifin mahaifiyata.
Nan dai muka cigaba da hira har suke cemun an kusa bikin autar su mahaifiyata nace.
"Aikam zan zo,dama saura wata biyu mu yi juniour candy in nazo sai na yi kusan wata biyu ko uku duk na zaga dangi."
Suka ce.
"Da kwa Inna da Kawu sunfi kowa farin-ciki."
Nace.
"Wai su waye Inna da kawun ne?"
Aunty Hafsa ce tace.
"Babarmu da Babanmu." Nace.
"Kakannina kenan?" Tace. "Eh" Aikam na saki wani ihun murna zanje naga kakannina ashe suna raye wayyo,ji nake tamkar mahaifiyata aka cemun tana raye tun da ita na riga na d'ebe tsammanin ganinta sai a aljanna idan Allah ya had'a fuskokinmu.
Nace.
"Aunty Hafsa Abba yace ba a k'asar nan kuke ba,ya akai kuka iya hausa?"
Tace.
"Ai Innarmu bahaushiya ce ita ke yi mana hausa shiyasa muka iya."
Nace.
"Ku yi mini yaren naku na ji."
Aikwa suka hau yi mini ina kwasar dariya ina auna suma da ace ba su iya hausa ba haka zasu ji nawa harshen,Allah buwayi kenan gagara misali.Allah mai gari bam-bam.
Sai da su Aunty Hafsa suka kwanan mana biyu kana suka tafi,d'an kwana biyun da mukai munyi sabo sosai,Abba yazo sun gaisa sun gaya masa sak'on su Inna yace dai su nema masa afuwar su ina yin juniour candy shi da kansa zai kawo ni in sha Allah,shi ya biya musu kud'in jirgi da sha tara ta arzik'i suka koma suka barni da kewa.
Na gayawa Nauwa muna yin juniour candy sai sierealoan,duk da jikina ya yi sanyi da Abba yace shi zai kai ni kar abun ya kuma shiri ricewa, duk da na k'udiri aniyar saka Mallam ya matsa masa.
Nauwa tace.
"Dama Baba ya barni sai mu tafi tare." "Eh wallahi,ki tambayesa Allah yasa ya barki."
"Amin to,zan gwada,anman kinsan halinsa." "To ga wata shawara"
"Ta me fa?". "Ki gayawa Yaa Muhd sai ya tambaya miki." "Cib'b'in ina naga fuskar tunkararsa Naj? Ba fa ya sakar mana fuska ko kad'an,ko lesson d'in da yake mana albarkacin ki na ci."
"Ki jimin sharri,ga abu a sarari kowa yasan albarka cinki nake ci zaki wani ce haka,to ni a suwa kare da gudun layya? Ni abinda na fuskanta Yaa Muhd ba ya son raini, don kinje kin rok'eshi babu abinda zai miki."
"Ke duk fa abin ki bazan tunkari Yaa Muhd ba gara na gayawa Umma ta rok'a mini Baban."
"Mtssss! ga hanya mafi sauk'i muka tsaya bawa kanmu wahala."
Dariya muka saka tare da adduar Allah ya nuna mana lokacin.....
Kwanci tashi asarar mai rai;idan bai aikata abin kirki ba,abin da zai d'ibi ladansa a lahira ba.
Har mun gama juniour candy,dama tun da muka fara zana jarabawa nake gayawa Malam ya tunawa Abbana muna gama jarabawa zai kaini sierealeon,kuma ya siya mana waya ni da Nauwara,tun da tafiyar ma tare da ita zamui dan ta gayawa Ummansu tun tuni ta tambayar mata Baban nasu kuma ya barta yace.
"Ai Najwa ce ba a hana Nauwara bin ta ba,k'awancensu ya zarta k'awance sai dai a kira shi 'yan uwan taka."
Sai gashi kuwa muna gama zana jarabawar Abba ya fara mana shirin tafiyar,da yake yanzu naga yana d'an shiga lamarina dan ba kuga d'inkin da ya mana ba ni da Nauwa,ga kuma sababbin wayoyinmu masu kyau,duk da sai da muka sha fad'a da takara gurin kowa kafin a bamu wayar musamman Yaya Muhd don cewa yayi muddun ya samu d'aya daga cikinmu da kula samari sai ya yi mana hukuncin da ba mu tab'a tunani ba,shiyasa muka k'udiri niyar kiyayewa duk dama Allah bai yimu masu rawar kan kula samari ba dan ko mazan ajinmu bama shige musu sabanin wasu da har soyayya suke a tsakaninsu.
Ranar lahadi mun gama shirinmu,mun had'a komai namu sai zumud'i muke da zirgillo da yake washe gari litinin zamu tafi.Baban su Nauwara shima yayi mana sababbin d'inkuna,Yaa Muhd ma ya siya mana dogayen riguna masu kyau,Gwaggo ma ba a barta a baya ba tayi mana dambun nama mai yawa da miyar kaji tace mu tafi da su Baffa kwa addu a ya bi mu da ita dan babu abin da kuma muke nema. Washe gari jirginmu ya d'aga sai sierealeon,ba mu sha wata wahala ba da yake da Abba a tare da mu tun da ya riga da yasan ainiyin garin da suke a cikin sierea d'in sai gamu har k'ofar gidansu mahaifiyata,sai da k'walla ta ciko idanuna na d'auketa da hannuna ba tare da ko Nauwa ta farga ba,abin da kuma ban sani ba Abba yana ankare da ni shi kanshi jikinsa wani mugun sanyi yayi yana jin tamkar ya aikata mugun zunubi,ya tabbata ya yiwa Kadija babban laifi ace tun mutuwarta sai yau da take da shekaru goma sha uku zuwa sha hud'u sai yau ya tako mahaifarta,bai dubi mahaifanta da ya shaida cewar tafi k'aunarsu akan karan kanta ba.Yana da tabbacin da zab'i aka bata ya tabbata baza ta tafi ba tare da ta wadata su ba yadda ko bayan ranta baza su yi kukan rashi ba,sai dai kuma da yake tsarin tafiyar rayuwar gaba d'aya ba a tafukan hannunmu yake ba tsarin na Allah ne,yadda yaso hakane yake kasancewa baka isa ka canja komai ba.
Ji ya yi yana mugun kunyar had'a ido da mahaifanta,lura da ya yi ya barmu a tsaye yasa shi kallona yace.
"Ku shiga Najwa nan ne gidansu mahaifiyar ki,sai ku shaida musu ina k'ofar gida."
Da sallama muka shiga cikin gidan,da wata fara sol d'in dattijiwa muka fara cin karo zaune a tsakar gida itace kuma ta amsa mana sallamar mu,ina ganinta a jikina naji itace kakata saboda kama da suke da mahaifiyata,nima kuma mahaifiyar tawa nayo sak sai dai na d'ebo zubin Abba kad'an.
Da fara'arta tace mu shigo dan daga ganinmu tasan ba 'yan garin ba ne bak'i ne,sai dai kuma ta k'ureni da ido tana ta kallona,murmushi na saki kafin nace.
"Abin kunya kaka ta kasa gane jikarta."
"Ta ya za'ai na kasa gane jinin Khadijata?A tun shigowarku sai da jikina ya bani Khadijata ce ta dawo."
Janyo ni jikinta ta yi ta rungume had'e da fashewa da kuka tana kiran sunan Kawu.
Gyaran muryarsa muka fara ji yana fitowa daga makewayi a gabanta ya shiga anman ta mance ta ma yi tunanin yana d'aki,shima fari ne anman ba can ba yana da jiki duk da tsufan da ya cimmasa.
Hannu ya d'aga sama yana wa Allah kirari da godiya da ya bashi aron rai da numfashi har sai da yayi tozali da jinin Khadija,kafin ya k'araso in da muke shima ya rungume ni cikin jikinsa,muryar Nauwa naji tana.
"Naj munfa bar Abba a waje."
Kafin na yi magana Kawu yace taje tace ya shigo.
An gaggaisa an tambayi bayan saduwa tare da neman afuwarsu na nemansu da bai yi ba suka nuna babu komai,komai nufi ne na Ubangiji idan bai nufeka da yi ba komai damun da abin zai maka a zuciya ba ka isa ka aiwatar da shi ba.
Abba bai wani jima ba yayi musu sallama ya tafi anman yace su bani Accaunt number na tura masa zai sako musu sak'o,wata bak'ar jaka da na yi tunanin tasa ce itama yace na bawa su Innan sak'onsu ne a ciki,sosai suka dunga masa godiya.
Bayan tafiyarsa ne nake cewa Inna.
"Ina su Aunty Hafsa?"
"Ai duk suna gida jansu,bara Fatima ta dawo sai ta raka ku ko gidan Hafsan ne kawai zuwa gobe in kun huta sai ku fara zaga dangi. Tun d'azu na aiketa kin jita shiru tamkar maye yaci shirwa,ta yuhu tana can gidan Hafsan,da ta sama muku wani abun kun ci."
"Da yake ma ba yunwa muke ji ba mun ci cake da coffe a jirgi."
Ina rufe bakina sai ga sallamar Fatiman.
"Inna na jima ko?Wallahi..."
"Wallahi me?"
Inna ta yi saurin katse ta.kinje kin yi zamanki gidan Hafsa zaki zo kimin dad'in baki,ga baki nafi awa hud'u da aiken ki sai yanzu zaki kwaso k'ananun k'afafuwanki ki taho mini kina Inna wallahi."
Fad'a sosai Inna ta dinga mata duk da yarensu mudai sai saurare ba ji muke ba.sai can Fatin ta kallo in da muke zaune baki ta saki tana kallona kafin tace.
"Inna na canka"
Innan ba ta dai ce mata komai ba sai ta kalle ni tace.
" 'Yar Aunty Khadija hakane?"
Gyad'a mata kai na yi aikwa ta yi wata sufa ta rungume ni tana murna kafin tace.
"Ashe dai da gaske su Aunty Hafsa suke da suka ce zaki zo? Ba yadda ban yi ba su taho da ni da zasu zo anman suka k'i wai kud'in jirgi nace su saka ni a maleji ko boot Aunty Maryam tace Uban wa yace miki akwai maleji a jirgi?"
Dariya muka saki gaba d'aya dama tunda tace meleji muke rik'e dariyarmu ni da Nauwa,nace. "Aunty Fati ga 'yar uwata Nauwara."
Tace. " 'Yar uwarmu zaki ce,nima ta zama 'yar uwata daga yau.'Yar uwarmu kunzo lafiya,ya hanya?"
"Lafiya Alhdlillah Auntynmu."
Cewar Nauwa.
Inna ce tacewa Aunty Fati ta tashi ta raka mu gidan Aunty Hafsa ta sama mana abin da zamu ci dan in tace Aunty Fati ta mana shiririta zata tsaya har mu jigata da yunwa dan tasan hali.
Sai da Aunty Fati ta fara kwashe mana kayanmu ta shigar mana da shi d'akinta kana muka nufi gidan Aunty Hafsa babu nisa,zo kuga murna gurin Aunty Hafsa da ta ganni ai abun bazai fad'u ba, wannan zuwa ba zato ba tsammani dan ba su tab'a tunanin Abban zai kawo ni ba.
Ashe bayan tafiyarmu Mama sai ta nufi gurin bokanta saboda ganin yadda Abbana ya kashe mana kud'i ni da dangin mahaifiyata,ya kuma tafi kai ni da kanshi,alamu ne na farrak'un da aka mana ya fara sakinsa shiyasa taje a sabunta shi,wanda da ta san abin da zai faru da ko da kud'i ba taje ba sai dai kuma idan ajali yayi kira babu abin da ya isa ya dakatar da kiran dole ka amsa ba ma kasan sanda zaka amsa kiran ba.
Da murnarta da farin-ciki ta baro gurin bokan da ya sanar mata muddun ta yi turaran da ya bata Abbana ya shak'a to an mana farrak'un da ba wanda ya isa ya warwareshi ko shi karan kansa ne.Wannan farin-cikin shi yabi ya isheta take tuk'inta cikin kwanciyar hankali ba tasan ajalinta yana k'ara kusantota ba domin kuwa nata shirin take Allah kuma yana nasa rayuwa da mutuwa tafiyarsu gaba d'aya a hannunsa yake anman wani zubin sai tunani da hankulanmu su gushe.
Hatsari suka tafka mai muni babu kyan gani wanda ya yi sanadiyar mutuwar Mama a nan take