x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 4 - KANA NAKA ALLAH NA NASA complete document

  • 9001 words
  • 12000 words
  • Out of 66841 words

Category: Love Stories

Views 287

25 Aug 2025
Start ads
After Image Ads
rabuwar Mommy da Daddynsu Nasrin."

Nace. "Cabf!lallai ta yi hak'uri mutum yana zaune a gidansa wata tazo ta fidda shi saboda rashin tausayi da imani."

"Wallahi kuwa,dan ma na tak'aita miki labarin anman tarin bak'in cikin da Mommy ta k'unsa Allah yayi yawa da shi."

Nace. "To ina 'ya'yan nata ,har yau ba su gama karatun ba ne?naga ban tab'a ganinsu ba."

"Sun gama. Shi Yaa Sulaiman likita ne a b'angaren ido,Yaa El kuma a b'angaren zuciya kuma sun kama aiki a can asibitin Jiddah saboda k'wazan su a fannin abin da suka karanta,bayan kammala karatunsu Yaa Sulaiman ne kawai yazo,Yaa El kwa tun da yaji labarin abin da ya faru tsakanin Mommy da Daddy yaji nigeriar ma ta fita a kansa a can yayi zamansa har ya kama aiki da asibitin Muwadda,shekarar da ta wuce aka yi bikinsa da Zahrah,ance haifaffiyar Jiddan ce,shi ya sa ma acan aka yi bikin sai su Mommy ne suka je can, Yaa Sulaiman ne dai har yau bai aure ba."

"Ikon Allah,kuma kince shi ne babba."

"Eh,ance akwai tazarar shekaru uku tsakaninsu."

#Bebee'arth
#Rashuna
#09037093702
[3/9, 23:28]BEBEE'ARTH
[5/9, 20:36] RASHUNA: BEBEE'ARTH


Watpad@Rashuna



KANA NAKA
(Allah na nasa)


9

Naga kirkin Mommy Hasiyya sosai da Nauwa ke bani labari,tun bayan tare warta ta so na koma gurinta Baffa ya hana,anman yakan barni naje na yini na dawo.
muna sss2 mukai saukar karatun alqur'ani,an mana hidima sosai yadda kasan bikinmu ake,Aunty Fati da Aunty Hafsa duk sunzo sun mana bajinta sosai.
A haka rayuwa taci gaba da mik'a mana har zuwa sanda mukai candy muna da shekaru 17 amman har lokacin ba ma kula samari saboda kullum fad'an Yaa Muhd akanmu kenan anman duk da haka sai an biyomu har gida,ai ta aike nak'i fita Gwaggo tai tamun fad'a nace"
Nifa Gwaggo ba yanzu zan aure ba."
Tace.
"Sai zuwa sanda na yaye ki ba."
Sai kuma mui dariya dukanmu a tare.

Yammaci ne mai dad'i,iska na kad'awa mai ratsa jini da jijiya garin yayi dad'i luf luf gwanin saha'awa sakamakon ruwan saman da aka yini ana tafkawa tun daren jiya.
Kwance nake a d'aki ina tunanin yau kwananmu biyu ba mu had'u da Nauwa ba, tun ranar laraba da muka rabu bayan an tashi daga islamiya (da yake har bayan saukar tamu muna zuwa ana mana wasu littattafan kuma mukan shiga wasu ajujuwan muna koyar da su)sai kawai na mik'e na d'auki hijabina har kasa na cewa Gwaggo bara naje gidan su Nauwa tace sai na dawo na gaisar mata da Ummansu nace.
"Zata ji."

Tun fitowa ta daga gida wani saurayi yake ta bina a baya dan ban sanshi ba a layinmu a haka har sai da ya cimmani yamun sallama na amsa don nasan muhimmancinta daga haka yaci gaba da zuba zancensa nidai ina zuwa gidansu Nauwa nai shigewata ban tsaya ba,na rabfka sallama shiru babu wan da ya amsa na kuma yi nanma dai shiru har na fara tunanin juyawa sai ga Yaa Muhd ya shigo na gaishe shi had'e da tambayarsa ko su Umma basa nanne ? yace.
"Umman ce dai bata nan anman Nauwara yanzu zata dawo na aiketa,ashe kece kika shigo wani mutum yace nai masa sallama da ke."

"Ya fiya naci wallahi,tunda na fito yake bina ban kulasa ba,dan Allah kace masa an bayar da ni."

"Meye tukuicina ?"


"Me kake so"

"Ke."

Ya fad'i hakan da wani salon murya yana jifana da narkakkan kallon da yasa jikina d'aukar rawa nai k'asa da kaina.

"Uhmmm ko baza ki bani ba?"

Yanzun ma da wata narkakkiyar murya yayi amfani da ta saka jikina d'aukar d'umi gaba d'aya,Allah ne ya taimake ni Nauwara ta shigo,yana jin sallamarta ya juya ya nufi d'akinsa had'e da cewa ta kawo masa abinci da aiken nasa d'aki.

"Naj daga gidanku nake Gwaggo tace mun kina nan."

"Wallahi kuwa ,naga kwana biyu bamu had'u ba shiyasa na tako na taho."

"Kedai bari,Umma ce bata nan shiyasa kika jini shiru,yanzu ma Yaa Muhd naje sayowa awara gidan Lami shine na biya, ni ina tausayawa matarsa da aikin awara ace mutum kullum sai yaci awara,abinci ma bazai ci ba sai da ita kuma baicin ta sayarwa Umma ke masa,yanzu ma dan yaga uwar bari ne Umman bata nan shiyasa yace naje gidan Lami na sayo masa,nifa ina ga ita ke saka shi ciwon cikin nan."

"Idan kin gama munafuncin nawa sai ki zubo abincin ki kawon."

"Na shigesu, Naj dan Allah bari na zuba ki kai masa,in ba haka ba na kad'e har ganyena."

"Aikam nima bada ni ba,kinga hucewata kar a had'a da ni a laifin da ban aikata ba."

Ina kawowa nan nai fitowata ina jinta tana kwalon kira nai kunnen uwar shegu saboda ban son Yaa Muhd ya kara ritsa ni.

Da daddare har na kwanta sai ga kiran wayarsa na d'aga had'e da sallama ya amsan hade da cewa kin kWanta ne?

Nace "Eh"

"Na sakaki tunani ko?"
"Uhmmm"

"Naga za'amun sakiyar da babu ruwa ne,ance mun samari tururuwar zuwa gurinki suke,kar naje wani d'an k'walisan yamun wuuf da ke ya barni da ciwon zuciya,kinga kuwa ai gara asirinta ya tonu da a barta da ciwo."

"aikuwa dai"

"Yauwa 'yar gari,to yaa an karb'i tayin nawa ko kuwa?"

Shiru nayi domin kuwa bani da abin cewa ni kaina bazan ce ga halin da zuciyata ke ciki a kansa ba.

"Najwaa kinyi shiru kice wani abu mana dan Allah."

"Uhmmm"

"Bari dai na barki mayi waya da safe naga alamun bacci kike ji"

"Toh Allah ya tashemu lafiya."

"Ammin."



Tun daga wannan ranar kullum sai ya kirani safe rana dare ban ankare ba lokaci guda muka fara gudanar da soyayya mai zafi a tsakaninmu,kwata kwata na janye k'afata zuwa gidan su Nauwa duk nacin kwa da take mun san da kwa ta gano soyayya muke da Yaa Muhd sai cewa tayi.
"Munafuka shiyasa kika daina zuwa gidanmu ashe,Allah sarki wata yarinya zata bautu da dafa awara."
Ita taje ta tseguntawa Ummansu sai kwa gata har gida tazo bikona wai Yaa Muhd bazai shiga tsakaninmu ba har yanzu ban canja daga 'yarta ba sai wani matsayi da na k'ara samu.

Soyayyarmu da Yaa Muhd tai nisa sosai ,ana cikin haka muka fara zuwa school of nursing Abba ya siya mana mota iri d'aya sak,fara k'al mai kyau da d'aukar ido. Yaa Muhd ya koya mana.Karatunmu yayi nisa sosai Yaa Muhd ya samu lecturing a BUk aka kawo kud'ina aka saka shekara guda sati d'aya da kawo nawa aka kawo na Nauwara wani Najeeb ne anan bayan layinmu yake aka tsayar da rana lokaci d'aya da namu.

Ranan wata asabar Faisal d'an ajinmu ya shigo unguwarmu sai ya kirani akan zai k'araso mu gaisa nai masa kwatance nace to na kwatanta masa kuwa sai gashi yazo.
Faisal yana da kirki sosai ga k'wak'walwa zan iya cewa shine zakaran ajinmu shiyasa nake kula shi don sosai tamu tazo d'aya kuma ina mugun k'aruwa da shi.

Muna tsaye k'ofar gida muna gaisawa d'aga idon da zan kawai naga Yaa Muhd a gabana,wani kallo ya jehomun kafin ya girgid'a kai ya shige cikin gidan.

"Idan na canka Yaa Muhd ne."
Cewar Faisal na d'aga masa kai.

" A bashi hak'uri,bari na gudu sai ranar monday idan Allah ya kaimu."

"Allah ya nuna mana,na gode ka gai da gida."

Daga haka na juya na shiga gida, yana zaune suna tab'a hira da Gwaggo a tsakar gida nai sallama suka amsan sallamar a tare, kafin ya mik'e yaiwa Gwaggo sallama ya fita na bi bayansa tunanina zai tsaya anman d'an mutumin nan ko waiwayowa bai yi ba,na dawo jiki a salub'e na shige d'aki raina ba dad'i sam, sai ga Nauwa ta kirani a waya.
"Hello Sis yau lafiya kuwa ?"
"Ina kwa lafiya Yaa na fushi da ni."
"Mtsss har kin fad'ar min da gaba na zata wani abu ne."
"Wani abu ne mana fushin fa masoyi na kasa jurewa har sai da na zubda hawaye.". "Lallai a gaisheki soyayya manya to me ya had'a ku ?"

"Faisal ne yazo muna cikin gaisawa sai ga Yaa Muhd din shiyasa ma ko gurinki ban kawo sa ba."

"Au kishi ne,ki rabu da shi idan ya gaji zai sakko."
"Ai wannan yayan naki akwai kishi, cewa fa yayi idan mukai aure sai dai na ajiye makaran tata bani ba shiga kasuwa ke duk inda nasan zanyi cud'anya da maza na soke kaina a zuwa gurin inma ina shaawa."
"Kuma kika yadda?". "To ya na iya tun da ina son abina.ke ni burgeni yayi ma ina son namiji me kishin iyalinsa wasu mazan suna bani mamaki kwata kwata basa kishin matansu wai su nan wayewa wayewar banza wani ma sai yace matarsa baza ta saka babban mayafi ba sai karami dan kar abokansa su rainata suce bata waye ba kiji dan Allah kawai jahilci,ki duba zamanin Annabi Muhammad (S.A.W) matan aure basa fita sai da daddare saboda kar aga kalar tufafin dake jikinsu anman mufa yanzu wata kwalliyar ma da zata yi ta tafi unguwa ba ta yiwa mijinta a cikin gida,ta gwammace na waje su gani akan mujinta ya gani wan da idan ya gani ne yaji dad'i za'a bata lada.
Ki duba ki gani mune zuwa kasuwa mu cud'anya da maza,makaranta ko gurin aiki duk cud'anya ce da maza,wata macen idan kika ji tana hira da abokin aikinta tana babaka dariya ina to ko da mijinta bata wannan hirar kuma duk zunubi muke kwasarwa kanmu ke wannan zamanin sai dai kawai Allah ya kyauta.Dan haka komai Yaaya yace mun indai bai sab'awa addini ba zan yi shi da gaggawa."
"Lallai yayi yayi matar Yaaya na yadda kina matukar son Yayan nan nawa irin wannan wa'azi haka."

"Nidai kawai kije ki bashi hakuri ban san iskanci ." "Najwa kema wasa kike Ina naga fuskar tunkararsa?" "Gwadawa zaki kinji." "Ke ni sai anjima duk kin k'ararmun da kati." To sai me? ai kune kati keda ke da Jibson guda."Bata ban amsa ba ta kashe wayarta sai naci gaba da neman layin yaa Muhd ga mamakina sai na jisa a kashe, sai na tura masa sak'o game da alakata da Faisal da zuwan da yayi kana na kashe wayar gaba d'aya dan banga amfaninta ba....
[7/3, 21:22] RASHUNA: BEBEE'ARTH



Wattpad@Rashuna



KANA NAKA
(Allah na nasa )


10

Washe gari da rana bayan na yi wanka nai sallar azahar,sai na d'auki wayata na kunna a tunanina ko Yaa Muhd ya neme ni ko yamun reply.
Tana kunnuwa tex ɗin Nauwara ya fara shigo mun wanda yazo mun tare da faɗuwar gaba Dass!
Da hanzari na buɗe na fara karantawa kamar haka:
"Asalam. Najj na kira wayarki ban samu ba dama Yaa Muhd ne ba lafiya,mun kai shi asibiti amman yanzu mun dawo muna gida jikin nasa da sauƙi."

Ina gama karantawa ba shiri na miƙe na zari hijab na fito Gwaggo na samu a falo ta bawa TV hankalunta gaba ɗaya, ni kuma abin da bai ɗaɗani da ƙasa ba kenan,kallo ba, sam ba ma shiri da shi barni dai da danna waya zan iya yini ko abinci ban nema ba indai da waya a hannuna.
" Gwaggo bara naje gidansu Nauwa Yayane wai bashi da lafiya."

"Ayya ki masa sannu,kafin anjima da daddare nima ki rakani na dubosa."

"Tom in sha Allah zai ji." Kana nasa kai na fice.

KO da naje gidansu Nauwa duk suna zaune a tsakar gida,sai a lokacin naji matsananciyar kunya ta kama ni,na taho zugui zugui duba saurayi gidan surukai.
Ina sussunne kai dai cike da kunya na gaishe su,in da Allah ya taimaken Nauwa ba ta mun I ya shege ba tace kawai na taso mu shiga ciki.

Babu wan da yace ƙala cikinmu har muka shiga ɗakin Yayan, yana kwance idanuwansa a rufe da mukai sallama muka shiga,ba kuma tare da ya buɗe idon ba ya amsa mana sallamar.
A sanyaye nace. "Yaya ina yini?"
Ya buɗe idanuwansa a hankula kana ya amsa min da: "Lafiya lau Najwa,ya kike?"
"Lafiya lau Alhmdlillh,ya jikin naka?" "Jiki da sauƙi sai tunaninki da ya hana ni sakat.Najwa bazan iya dogon fushi da ke ba,wannan ma ni nasan azabar da na sha.Kishi ne ya turniƙe ni shi yasa na ƙi saurararki kwata-kwata."

"Maganar ta huce kai shiru ka koma ka kwanta."
"Ai dama na samu shiyasa nai maganar,
ɗazu ina son yin maganar na kasa, idan cikin nan nawa ya fara ciwo ji nake kamar mutuwa zan yi Najj."
"Yaya ka daina zancen mutuwa,in Allah ya yarda ba yanzu ba."

"To Allah yasa,domin kuwa zan so yin rayuwa mai tsayi tare da ke,sai dai kuma KANA NAKA ALLAH NA NASA,nasa kuma shine gaskiya Naj,ba yadda muke so komai yake kasancewa ba,faɗar mutuwa ai ya zama dole domin kuwa dukkanin rai sai ya ɗanɗani ɗacin mutuwa, Ƙanwata mu da ake son mu tuna mutuwa a rana sau saba'in in ka tuna sau goma ma ai kayi da yawa amman ana samun wan da ko sau guda baya tunawa da ita a rana ."

"Nidai dan Allah mu bar zancen mutuwar nan gabana faɗuwa yake."
"Ai ko ba mu yi zancanta ba idan lokacinmu yazo dole ta ɗauki rayukanmu, sai dai kawai muyi fatan dacewa."

"Gaggo na gaisheka."

"Ina amsawa. Ina sonki Najj,ina son yin rayuwa da ke,ina son ki haifa mini yaran da zasu zamo sanyin idaniyata sai dai kaish!a jikina nake jin wannan ciwon bazai barni ba sai ya karni, domin kuwa duk binciken likitoci sun kasa gane me yake haifar mini da wannan ciwon,kinga kuwa in ba ciwon ajali ba wani ciwo ne za'a kasa gane kansa? Duk da dai ƙawarki tace awara ke saka mini ko?"
Me makwan amsa sai kawai na saka masa kuka sai kuma ya hau lallashina cikin sanyin murya, nace. "To ai kaine ka ƙi barin zancen mutuwar kana ƙara saka mini tsoro a raina,bayan ka kwana da sanin ban haɗa ƙaunarka da komai ba, rashinka bani da masaniyar iya illar da zai mini a rayuwa,cuta ba mutuwa bace ta yuhu na rigaka yin gaba."
"To ki yi shiru na daina kin ji?"
Na ɗaga kai.
"To kimun murmushin nan naki mai sanyi mai saka na manta dukkan wani ƙunci."
Ban san san da ƙawataccen murmushi ya kufcewa fuskata ba.
"Ko ke fa ,har na ji saidah,kinsan me? "
"Sai ka faɗa." "Wallahi ɗazu kafin ku shigo bacci nake ji amman tunaninki yamun kutse ya hanani sakat,amman kinga yanzu wani nishaɗaɗɗan bacci nake ji idanuwana har wani lumshewa suke,zuciyata tayi fresh ga wani nishaɗi da nake ji duk domin kasancewarmu guri ɗaya, shin kema kina ji?"
"Hmmm!Fin ma hakan ina ji"
"Da gaske kuwa?" "Ko shakka babu." Nauwa ce ta katse shi da abin da yake son faɗa da sallamarta muka amsa ta dube ni haɗe da faɗin "To sai ki fito yayi baƙi kin wani zo kin shantake a ɗaki wai ke me saurayi."
Murmushi nayi haɗe da faɗin. "Wai ma da yaushe kika bar ɗakin nan?"
Ba dole na fita ba kun mayar da ni kamar gunki kuna hirar love." Ba fa na son iskanci ki daina mun haka kar Umma ta ji ."
"Da kin san da Umman kika zo kika rashe wai ke saurayi ba lafi...". Yaya ne ya katse ta cikin kausasshiyar murya da faɗin.
"Dalla kin ishe mu da surutu ki faɗi abin da ya kawo ki ki gaba."

". 'Yan wajen aikinku ne sai kuma Momy Hasiyya."
"Shine kuma don raini kika tsaya zubar zance dallah je kice su shigo."
"Allah ya huci zuciyarka."Kana tayi saurin ficewa.

Miƙewa na yi,ya narkar da idanuwansa a kaina.
"To ni zan huce,anjima in sha Allah zamu zo da Gwaggo sai na ƙara ganin jikin naka."
"To masha Allah Allah ya kai masoyiyata gida lafiya.". "Amin,Allah kuma ya bawa Masoyina lafiya."
Muka ce "Amin." A tare kana na fito.

Kaina a ƙasa na ƙarasa gurin da su Umma suke muka gaisa da Momy Hasiya tana mun ƙorafin bana son zuwa bayan tsakaninmu bai taka kara ya karya ba, na rufe bakinta da in sha Allah zan dunga zuwa kana nai musu sallama na fito.
Ji nayi kamar ana bina a baya,juyawar da zan yi ashe Nauwa ce ta biyo ni taƙoƙarin saka hijabi." Shine kikai tahowarki na shiga ɗauko hijabi."Sorry ƙawalli ai ban sani ba."
Sai da ta raka ni har ƙofar gida, muka daɗe a tsaye muna hira kana mukai sallama ta juya.

Da daddare mun koma ni da Gwaggo jikin nasa da sauƙi,mun daɗe muna hira Gwaggo sai gajiya tayi ta tafi ta barni mai makon ta aiko Nauwa ta kira ni,ƙarshe dai sai mara lafiyan ne ya rakani har gida tunda jikin nasa da sauƙi sosai.



Kwanci tashi gurin Ubangiji babu wuya wai har lokacin bikinmu ya zo,shiri muke babu kama hannun yaro,ta fannin Abba babu abin da bai siya mana ba,kaya na alatu na more rayuwa babu wan da bai siya mana ba.Momy Hasiya kwa ɗebe mu tayi zuwa gidanta tana mana gyara na musamman,dama tun biki saura wata ɗaya muke zuwa Rashuna collection ana mana gyaran jiki fatarmu ta murje tayi kyau tayi sulɓi tana glowing.

Biki saura sati,ko ta wani ɓangare an gama hallaruwa dole aiwa Abbana kara,nice ta fari nice auta nice dankalin turawa hhhh haka ma su Umma ma dole a musu kara bikin fari zasu yi kuma na mace da namiji
Su Aunty Hafsa da Aunty Fati tuni suma suka hallara aka fara gudanar da biki cikin kwanciyar hankali. Ranar juma'a mukai dinner,asabar akai perty ranar lahadi kuma aka ɗaura mana aure, ranar da abubuwa guda biyu suka gauraya cikin rayuwata suka hautsina mini 'yar ƙaramar kwanyata (Farin-ciki baƙin-ciki ) Ranar da ban jin zata gogu cikin tarihin rayuwata domin kuwa tayi matuƙar kokawa da numfashina...



Wattpad@Rashuna
[8/11, 08:20] RASHUNA: BEBEE'ARTH



Wattpad@Rashuna



KANA NAKA
(Allah na nasa )

11

Da yamma ana ta shirin kai ni gidan Yaa Muhd jikina yayi sanyi kwata-kwata ban jin daɗinsa ga kuma gabana da yake ta yawan faɗuwa wani zubin har sai na saka hannu na danne ƙirjina kana zan ji daɗi. Wayata dake gefena a ajiye ce ta shiga ruri ban yi ƙasa a guiwar ɗagawa ba ba tare da ko sunan wan da ya kira na gani ba tsabar yadda nutsuwa ta fara barina.

"Shi kenan mun shiga uku mun rasa Yaa Muhd."
Abin da kunnuwana suka jiyo mini kenan na yi saurin janye wayar daga kunnena dan ganin waye ma ya kirani domin kuwa ko ƙwaƙwalwata
End Ads