x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 1 - KANA NAKA ALLAH NA NASA complete document

  • 1 words
  • 3000 words
  • Out of 66841 words

Category: Love Stories

Views 303

25 Aug 2025
Start ads
After Image Ads

An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

[3/9, 23:27] FaShuNa: BEBEE'ARTH


Watpad@Rashuna


KANA NAKA2024
[Allah kuma na yin nasa]

1
SHIMFID'A
Alhaji Bashir Sunusi babban d'an kasuwan da yayi fice cikin birnin kano dama wasu garuruwan da dama har ma wasu k'asashen wajen yakan lek'awa akan harkokin kasuwancinsa.Mutum ne me karamci da sanin ya kamata, me kuma tausayin na k'asa da shi da taimakonsu gwargwadon iyawarsa yakan kuma fitar da hak'k'in Allah cikin dukiyar da ya hore masa akai akai.Yana da matarsa Khadija mace Mai kirki da sanin ya kamata ta rik'e iyayanshi da danginsa tamkar nata, su takewa kallon nata mahaifan sabili da nata iyayan sun mata nisa suna can sierraleone tun daga can ya aurota.Ba ta samu haihuwa da wuri ba sai da suka shekara biyar da aure kuma Alhamdlillh ba ta fuskanci matsala daga ko wani b'angare ba kamar yadda wasu sukan tsangwami wanda Allah ya jinkirtawa samun haihuwa ko kuma bai bashi ba kwata kwata, bayan ba laifinsa bane bashi da ikon bawa kansa abinda Allah bai bashi ba, ba zab'insa ba ne ba kuma son ransa bane yadda yaso hakane yake kasancewa ga duk yadda yaso rayuwar bawansa ta kasance,ita RAYUWA tafiyarta ba a hannumu yake ba,da a hannunmu yake da ta zama ba rayuwa ba kenan.

Kyautar tagwaye duk mata Allah ya basu sai dai Usainan ba ta zo da rai ba.Ansha shagalin suna sosai, wasu daga cikin 'yan uwanta sun zo Alhj Bashir ya tura musu da kud'in jirgi kasancewarsu ba wasu masu k'arfi ba.A ranar sunan da daddare Allah ya amshi ran Khadija ciwon cikin lokaci guda kafin ma a tafi asibiti rai yayi halinsa.Wannan mutuwa ta Khadija ta daki ahalinta yadda bakwa zato, Alhaji Bashir k'arfin hali kawai yake anman shi kad'ai yasan yadda yake jin rashin Khadija cikin rai da zuciyarsa, macece wacce ta iya tafiyar da shi cikin ko wani hali,Allah ya jik'anta ya gafarta mata,muma in tamu tazo Allah kasa mu cika da kyau da imani Amin.

Iyayanta sun zo,mutuwarta suma ta bugesu yadda bakwa zato."Ana murna an rabu lafiya ansha shaglin suna,ashe namu muke Allah ma yana ta nasa shirin,Allah ya jik'anki Khadija halayenki na gari su biki."
Kalaman mahaifiyarta kenan da take cikin jimamin rashin d'iyarta,kasancewarta ta fari a gurinsu mai sonsu da k'aunarsu da kyautata musu a ko da yaushe.

Bayan an share zaman makoki iyayanta da zasu tafi suka rok'i da ya basu Hassana (Najwa) anman Alhaji Bashir ya sakawa idonsa toka ya hanasu, don ko kod'an ba ya k'aunar yayi nisa da wannan jaririyar da ta cika zuciyarshi da k'aunarta da tausayinta tayi nisan da bai jin ko wasu yaran ya kuma samu zasu cimmata bare har su zarta ta,to kwa ta ya zai iya bayar da ita a tsallake garin nan da ita ama bar k'asar da ita gaba d'aya? Ba yadda ba suyi ba anman ya hana su haka suka tsallake suka tafi cikin k'unar zuciya, yayin da mahaifiyarsa taci gaba da rainan Najwa, dama tun mutuwar tana gurinta,itama bata da wani buri sai na cigaba da rainon jikarta,wacce take jin kamar ta k'wace dukkan wata soyayyar jikokin da zata samu a nan gaba.


Sai da Najwa ta shekara shida kana Alhaji Bashir yayi aure shima saboda matsantawar mahaifansa ne,anman in ta shi ne haka zai zauna har lokacinsa yayi yaje ya tadda Khadijansa a can suci gaba da rayuwar da ta yanke musu a duniya.
Anan bayan layinsu ya samu wata bazawara mai suna Kubrah, auranta mutuwa yayi da kuma 'ya a tsakani mai suna Zainab kuma ita ke rik'on 'yarta, dan hakama bayan auransu Alhaji Bashir yace ta taho da Zainab d'in,murna gurin Kubrah ba'a magana.
Bayan wata biyu da tariyarsu Mahaifiyarsa ta rasu, sanadiyar hakan rik'on Najwa ya dawo hannun Kubrah, wacce mutuwar kakarta mai sonta da k'aunarta ya tab'ata yadda bakwa zato sai da aka had'a mata da taimakon rubutu kana aka samu sauk'in wasu abubuwan.

Kubrah mace ce mai son zuciya da makirci, a gaban Alhaji Bashir nuna tsantsar soyayyar Najwa take, kamar yadda yake nuna mata soyayya wani zubin har finma hakan, anman a bayan idonsa 'yarta kawai ta sani, babu ruwanta da sha'anin rayuwar Najwan .

Yayin da Baffa mahaifin Alhaji Bashir ya sake aure, saboda zama shi kad'ai d'in babu dad'i,Gwaggo tana da kirki sosai wani zubin Najwan a gurinta take samun sauk'i don in ba sani kayi ba cewa zakai itace ainihin kakarta.


Wannan Kenan.


_______

Sauri nake na kammala shirin makaranta kada su Zainab su tafi su barni don sun saba mini hakan a duk sanda Abbana yayi tafiya duk randa na makara gurin shiryawa sai dai na fito na tarar sun tafi sai dai ranar na hak'ura da zuwa makarantar don ko nafi kowa naci Mama baza ta bani kud'i na hau mota ba.
Saurin nawa ya tashi a banza dan kwa Mama ce ta shigo d'akin namu.
"Ki tub'e uniforme d'innan ki fito ki mini wanke-wanke aiki yaiwa Haulatu yawa."

"Mama makarantar fa?"

"Waye yace ki zauna lak'ak'I har a tafi kai Zainab?Dan haka ki cire uniforme ki fito yau ke zaki taya Haulatu aikin gidan nan."

"Anman Mama kinsan ban iya wanke....." Kafin na k'arasa tasa hannu ta dakar mini bakina.
"Ni za kicewa baki iya ba? Mara kunya mara mutumci ki fito kiyi tun kafin na miki duka a gidannan tunda Uban naki da ya d'aure miki k'ark'ashi baya nan."

Ina kuka na fito haka na gwajajjab'a shi na barshi anman fa sai da nasha duka wai kwanukan basu fita ba.

A haka naci gaba da rayuwa cikin gidan mahaifina,agola ta fini daraja anman a bayan idonsa, dan Abbana yana matuk'ar k'aunata bai had'a k'aunata da komai ba duk da baya nuna mana bam-bamci ni da Zainab anman ko hakan Mama bata dubaba taci alwashin sai ta raba tsakanina da mahaifina yadda zasu fi samun sake ita da 'yarta......


#Bebee'arth
#Rashuna
[3/9, 23:27] FaShuNa: BEBEE'ARTH


Watpad@Rashuna


KANA NAKA2024
[Allah kuma na yin nasa]

2

Gurin wani boka a wani luluk'in k'auye da taji labarinsa gurin k'awarta ta shirya ta tafi ko rakiyar k'awar ba ta nema ba saboda rik'e sirrinta,dan ta sha jin k'awayen dake cin amanar wanda suka bud'a musu sirrinsu.
Bayan ta gurfana gabansa ta zayyana mishi abinda ke tafe da ita sai ya bata k'ullin magani akan taje ta barbad'a akan abincin Abbana idan yaci shi zai taimakawa aljanin da zai tura masa shiga jikinsa ya sauya masa tunani tare da dasa masa tsanata mai tsanani da kansa zai kore ni daga cikin gidan.
Nan ta karb'a tana godiya tare da ajiye masa kud'in da ya buk'ata harma da k'ari don ba k"aramin mahaukatan kud'i take samu gurin Abbana ba.

Bayan ta dawo gida ta bar bad'e abincin Abbana da wannan garin maganin da boka ya bata,a ranar Abbana bai kirani munci abinci tare ba saboda yayi dare kuma a tunaninsa nayi bacci,nankwa idona biyu shi nake zaman jira don Mama ta hanani abincin saboda tunda na dawo daga makaranta na tafi gidan Baffa (Kakana) sai yamma na dawo shine ta hanani abincin dare wai bani da abincin gidan tunda ba anan na yini ba.

Bayan sati da faruwar hakan na fara ganin wasu sauye -sauye daga Abbana,kwata-kwata babu ruwansa da lamarina,abincin da yake kirana muci ma ya daina,ranar da naje gurinsa kuwa daka mini wata uwar tsawa yayi yace na fice na bashi guri,tsoro da firgici suka hanani motsawa daga inda nake sai hawaye sharrrr suka biyo kuncina,Mama ce tai magana.
"Baza ki fita ba mara kunya mara mutumci kin tsare mutane da idanuwanki a tsaitsaye na marasa d'a'a."

Ta hankad'oni waje na fad'i goshina ya fashe na dinga kuka amma Abbana ko kallon gurin da nake bai yi ba bare ya yi magana, na mik'e ina kallonsu suna cin abincin har da Zainab,ina ganinta tana mini gwalo,na tashi na nufi gidan Baffa.

Ina zuwa gwaggwo ta tare ni da tambayar.
"Lafiya me ya faru?"

Ina kuka na gaya mata.

"Allah yana ji kuma yana gani."

Abin da tace da ni Kenan, ta d'auki hijabinta muka je camix akai mini dresing a gurin da ya fashe kana muka dawo gida tana ta mun sannu.Sai dare sannan ta rakani gida,tun daga wannan rana na daina zuwa gurin Abbana shima kuma ba ya nemana ko wani abu zai sayo sai dai ya sayowa Zainab ban da ni,aiki kuwa ina shansa tuk'uru ta kori masu wanke-wanke da shara,kullum sai na yi kafin na tafi makaranta, wani zubin har makara nake a zaneni Zainab tai tamun gwalo,duk da k'arancin shekaruna anman wuya ta sakani na koya dan in ban yi ba baza ta bani abinci ba kuma ta hanani zuwa gidan Baffa bare na samu na ci a can.

Ina da shekaru tara a duniya na gama primary,anman duk wani aikace -aikace na gida na iya,girki ma ina koya,domin tana sakani dafa 'yan k'ananin abubuwa haka. Ita a ganinta mugunta take mun ni kuwa ba ta san dad'i nake ji ba, gata take mini 'yarta take wa mugunta.
An sama mana makarantar Amina memorial, muka fara zuwa ni da Zainab, kullum da abincinta take tafiya me rai da lafiya,ni dama tuni aka dad'e da yayeni da tafiya da abinci wataran ma ba na ci nake tafiya saboda kan nazo ci sun azazzaleni in kuma na tsaya ta saka a tafi kai Zainab kuma baza ta bani kud'in mota ba,ko na jira ya dawo baza ta bari ya kaini ba,inda Allah ya taimakeni idan na samu zuwa gidan gwaggo tana bani biscuit ko cin-cin da lemo sai na saka a jaka su nake samu wani zubin na ci.
Mugunta dai iri-iri Mama ta iya ta maida ni bora a cikin gidan Abbana ta maida Zainab mowa cikin gidan Abbana,har gulmata Zainab suke da k'awayenta,wani zubin sui ta tsokanata bana kula su randa kwa suka kaini k'arshe na kama Zainab d'in me zuga su nawa dukan tsiya na kuma ce ta shiga hankalinta ni ba sa'ar yinta bace, ita dake zaune k'ark'ashin mahaifina tana cin arzik'i, dan kawai tana da uwa ne a bakin murhu nima dan Allah ya anshi tawa ne ba tare da ko fuskarta na shaida ba,na tabbata da tana raye da zan samu sauk'in wani abun.
Da muka komo gida ta zayyanawa Mama aikwa nima ta kamani tamun lilis tace.
"Ko maganar banza na k'ara gayawa Zainab sai na bar cikin gidan bayan dukan mutuwar da zata mun, kumu Abban nawa da nake tak'ama da shi bai isa yayi wani abu akai ba."
Tun daga wannan lokacin ko me Zainab zata mun bana kallonta bare na tanka mata......



#Bebee'arth
#Rashuna
#09037093702
[3/9, 23:27] FaShuNa: BEBEE'ARTH


Watpad@Rashuna


KANA NAKA2024
[Allah kuma na yin nasa]

(3)

A haka muka cigaba da karatu har zuwa sanda muka yi jarabawar canjan aji,nice na yi ta d'aya Zainab kwa ta goma ta yi,da muka kai gida Mama ta 'kwace ta saka biro ta mayar da sunan Zainab jikin nawa ni kuma ta mayar da sunana jikin na Zainab d'in kana ta nunawa Abba aikwa ya dinga murna yace.
"Ai nasan Zainab d'ita mai 'ko'kari ce ita kwa waccan jakar sai taje ta yi ta jakan cinta."
Mota sabuwa fil ya bayar da sabon driver ana kai Zainab makaranta ita kad'ai, ya siyo mata yari da sar'ka na gold kyautarsa ta k'ok'arin da Zainab ta yi. Mama murna ya bi ya isheta haka ma Zainab sai tsalle ta ke ta na mun gwalo ta na kirana jaka mara 'ko'kari,hawaye ne me zafi da rad'ad'i ya wanke mini fuska na futo daga cikin gidan dan ji na yi ya yi mini wani irin zafi.

Gidan Baffa na nufa na zayyanawa gwaggo abin da ya faru ina kuka tace.
"Ki yi ha'kuri Najwa,Allah yana ji kuma ya na gani,da sannu zai bi miki ha'k'kinki,yanzu tun a duniya Allah ya ke fara hisabi,itama ta haifa kuma za ta gani a k'waryar shanta in sha Allah tun da rayuwar ai ba a tafukan hannunmu take ba."


Mun koma makaranta mun shiga jss 2.Wata rana ina zaune a harabar gidanmu ina tsifar kai sai ga Abbana ya dawo,na nufe shi da sauri ina masa sannu da zuwa had'e da 'ko'karin kar'bar jakar hannunsa ya kawo mun wata mangarar da ta saka na yi gefe na zube a 'kasa,sai na ta shi ina kar kad'e jikina aikwa sai jin saukar bahagon marinsa na yi a kuncina."
"Ni kike karkad'ewa jiki tsabar kin raina ni? Tabbas na yadda da maganar Kubra k'awayen banza sun fara bud'a miki ido to yau d'in nan zan rufe miki idon gaba d'aya."

Ya janyo wayar wuta ya hau zabga mini,dukana yake ko ta ina, Mama na gefe ita da Zainab suna ta mun darinya ko tazo ta ceceni bare ta bada ha'kuri,sai da ya fasfasa mini jiki kana yace na fice masa daga gida, kada ya k'ara ganin k'afata a cikin gidansa,haka na fice ina kuka mai tsuma zuciya,Mama kwa farin-ciki ya isheta yau burinta ya cika na bar musu gidan ita da 'yarta yadda zasu fi cin karansu ba babbaka.

Gidan Baffa na nufa na zayyana ma Gwaggo abin da ya faru,ruwan d'umi ta d'ora ta gasa mini jikina tana ta mitar yau sai ta zayyanewa Baffa dukkan abinda ke faruwa a gidanmu.
Baffa na dawowa ta zayyana masa duk abubuwan da suka faru a baya da kuma na yau d'in,fad'a ya dinga yi akan me ba'a sanar masa tun a lokacin ya d'auki mataki ba Gwaggo ta dinga bashi ha'kuri,ya kira Abbana a waya yace yazo gida ya samesa ya dinga masa fad'an dukan da ya yi mini, dan ina kwance zazab'i ya rufe ni sai da Gwaggo ta kaini asibiti.
"Kace ta bar maka gidanka ko? to ka rubuta ka ajiye idan kaga Najwa ta bar gidannan to sai dai in auranta aka yi ko kuma bana numfashi.Kuma in zaka tashi tsaye kan wannan makirar matar taka to, in ba haka ba nan gaba har ni sai ta shiga tsakaninmu dama mace indai ba ta kirki bace ko d'akin mahaifiyarka ta shiga sai ta san yadda ta yi ta rabaku."

Shi dai Abbana hak'uri kawai yake ba shi,saboda yadda yaga Baffan ya d'auki zafi fiye da yadda yake zato.


Tun daga wannan ranar na dawo gidan Baffa da zama.Sai da na yi jinyar sati biyu na murmure,na k'ara haske da kyau tsabar hutu da jin dad'i kana na koma makaranta.
'Yan ajinmu sai tambayata su ke wai ciwo na kwanta ko kwa hutu dai na d'auka? Saboda sunga yadda na k'ara kyau da cikowa nikwa sai dai kawai na yi musu murmushi.

Babu wanda ke shiga harkar wani tsakanina da Zainab,dama kowa k'awayensa da ban bencinmu ma ba d'aya ba,ni ina tsakiya bencin farko,ita tana gefe benci na kusan biyar.

Koma wata gidan Baffa sai k'awan cenmu da Nauwara ya k'ara k'arfi kasancewar anan bayan layin su Malam take,sai muke tafiya tare mu dawo tare,wannan ya k'ara mana shak'uwa da k'aunar juna,ta dinga mini nacin na shiga islamiyarsu,hakan yasa na gayawa Gwaggo,ita kuma ta gayawa Baffa ya bani kud'i na siyo form na yanko uniforme muka kai d'inki duk tare da ita a nan unguwar rimaye.(Unguwarmu da na baro kenan)

Ranar da muka karb'o d'inkin washegari ya kama
End Ads