cewa Zuwaire.
"Ba ni cup."
Cikin wani accent ɗin murya,tamkar ba da yaren hausa yayi maganar ba.
Jiki na rawa ta ɗauko glas cup ɗin ta ɗauraye shi ta saka hankici me kyau da tsafta ta goge shi kana ta miƙa masa, ansa yayi ya tako zuwa gurin da na ajiye youghort din ya buɗe ya tsiyaya kana ya juya ya bar kichin ɗin na bi bayansa da kallo zuciyata na mugun harbawa.
A falon dai na kuma tarar da shi a tsaye yana siping ɗin youghort ɗin a gayance,kallo ɗaya na yiwa gurin da yake tsaye na fice da sauri,na rasa wannan masifar da tasa zuciyata ke harbawa wannan bawan Allahn.
Tun daga wannan ranar ban ƙara saka shi a idanuwana ba dan yini nake a makaranta kaina ya ɗau zafi,mun fara exxam,idan na dawo kuma sashin Gwaggo nake zama ita kanta Momy yanzu ba sosai take ganina ba musaman da Abba bai dawo ba har yanzu,Yaa Sulaiman kuma bai samu zuwa ba har yanzun shi ma, aiki sosai ya sha masa kai har weak end ɗin ba shi da lokacin kansa,sai dai muyi waya da video call yana ta gaya mun irin tsananin kewata da yayi.
A mugun gajiye yau na shigo,direct sashin Momy na nufa dan gajiyar baza ta barni tsinanawa kaina komai ba,ga matsiyaciyar yunwa ina ji,sashen Gwaggo kwa ba 'yan aiki tace ba ta so shiyasa kai tsaye na yo sashen Momyn.
Tun daga bakin ƙofa nake ƙwallawa Zuwaire kira, bayan na cire hijabin jikina da da hular kaina da ta bawa kwantacciyar baƙa wuluk ɗin sumata bayyana, kan kujera na zube bayan na bawa Zuwaire abubuwan duk da na cire da jakata nace ta kai mun ɗakina ta kawon ruwa mai sanyi kuma.
Muryar Momy na ji ta na.
"A'a Najjwa duk gajiyar ce?"
"Wallahi Momy na gaji,duk jikina ciwo yake."
"Ayya sannu."
Ta faɗa tana neman guri ta zauna idonta ya sauka a kansa tace.
"A'a kai kuma yaushe ka shigo?"
Maganar da tayi ne yasa ni kallon in da idonta ke kalla na ganshi a hakimce idanuwansa a lumshe.
Wallahi ban lura da shi ba, na dai ji zuciyata na harbawa da sauri da sauri,ɗauke idanuwana nayi daga kansa ban dai ji me yacewa Momyn ba, hankalina yayi kan Zuwaire da ta kawo mun ruwan da na buƙata na karɓa na ɓuncine murfin na kwankwaɗe kafin nace ta anso mini dambun nama gurin Gwaggo ta haɗo mini da lemo sai lokacin na ji Momy na cewa.
" Aikam yau ba'ai girki a gidan nan ba sai da daddare nace tayi mana dambun couse couse,in zaka jira to in baza ka jira ba bara Zuwairen tazo sai ta ɗora maka wani abun."
Muryarsa ƙasa ƙasa na ji yace.
"No barshi kawai."
"Dama to ba yunwar kake ji ba."
Bai ce komai ba sai idanuwansa da ya mayar ya ƙara lumshewa.
Zuwaire na kawo mun dambun naman na karɓa na fara ci kamar wata mayunwaciya ina korawa da lemo.
"To ko dambun naman za'a kawo maka?"
Girgiza mata kai yayi ba tare da ya buɗe idanuwansa ba.
"To ai shikenan sai kaje kai ta baƙin ranka kai kaga zaka iya."
Daga haka ta tashi ta bar falon, ta nufi ɗakin Nasrin dan jiyo kukan Neehal da Nimra a lokaci guda,abin da da wuya kaji suna kuka a lokaci guda.
Sai da naji na dawo daidai kana na miƙe zan bar falon bayan na mayar da hulata kaina.
"Ki taimaka mini da kunun nan."
Ban nuna na ji shi ba naci gaba da tafiyata, sai ji nayi caraf an riƙo hannuna.
Murya na rawa,saboda wani electrification da ke zagawa cikin jini da jijiyata, saboda faruwar abin da bai taba wanzuwa cikin rayuwata ba nace.
"Me ye hakan?"
"Plss yau babu abin da na iya ci."
"To ka sake ni."
Na faɗa ina rintse idanuwana saboda baƙon yanayin da nake karɓa a jinin jikina.
Cikin wata kasalalliyar murya yace.
"To zaki mun?"
Bansan san da na ɗaga masa kai ba,aikuwa a take ya sakar mini hannun na nufi kichin ya take mini baya.
Guri ya nema ya zauna yana danna waya har na gama kunun na zubo masa shi a mug yana ta tiriri, na ɗauko na nufo gurin da yake zaune idonsa akan waya yana sakin murmushi kumatunsa na lotsawa.
Zan iya rantsuwa ban taɓa ganin mutumin da murmushi yaiwa kyau ba kamarsa,sai naga kamanninsa da Actor ɗin nan na film ɗin india ya ƙara bayyana.(Jhon Abraham ) Ban aune ba ya ɗago kai mukai two eyes nayi saurin janye nawa idanuwan bayan ya ɗagemun gira, kafin yace.
"Wannan kallon fa?"
Ƙasa nayi da kaina cike da kunya nazo na ajiye masa kunun zan bar kichin ɗin,kamar ɗazu sai ji nayi ya sanya hannunsa mai tau shi caraf ya damƙen hannu, baki na rawa nace.
"Wai meye haka, kasan hakan fa bai dace ba."
"Me kike kalla a jikina."
"Ni ba kallonka nake ba."na faɗa ina turo baki gaba.
"Idan kina son na sake ki wallahi sai kin gaya mini abin da kika kalla a jikina."
"Nifa na gaya maka ba kallonka nake ba, naga ma ido muka haɗa,kaga kowa ma ya kalli kowa ai."
Na kai ƙarshen maganar ina yamutsa fuska, dan har ga Allah ni kaɗai nasan yanayin da nake ji a jikina, sai mutsu mutsun ƙwace hannun nawa nake amman ko motsi bai yi ba sai lumshe idanuwansa da yayi ya ɗauki kunun da ɗaya hannun ya fara sipping a hankula.
"Ga fa Momy nan zuwa,dan Allah ka sake ni."
Buɗe idanuwansa yayi sai cikin nawa muka ƙurawa juna ido zuciyata na mugun harbawa.
"Ai na fi son tazo ta ganmu a hakan, sai na gaya mata cewar, kallona kike tayi shine kikace ni kike so ba Sulaiman."
Gaba ɗaya idanuwana na zaro waje da suka nuna alamun tsoratar da na yi, wan da hakan ke ƙarawa idanuwana kyau kafin nace.
"Ni fa wallahi ba kallonka nake ba,kawai dimple ɗinka ne ya burge ni."
"Ok kina son shi ne ?"
Gyaɗa masa kai nayi,yace.
"Ki min magana da baki Hajiya ni ba kurma ba ne."
"Ehh". Nace ina turo baki gaba haɗe da kautar da fuskata gefe.
"Tun da kina son abina,nima ai kina sona."
"Ni dai wallahi ban ce ba." Na faɗa cike da shagwaɓa ina diddire ƙafafuwa kamar wata ƙaramar yarinya, wan da ni bansan ma nayi hakan ba."
"Bina kawai yake da kallo, kafin ya lashi leɓansa na ƙasa,cikin ƙasa da murya yace."
"An jima ki haɗa mini coffe zanzo na karɓa."
Gyaɗa masa kai nayi alamun na ji shi,ganin yana kallona kuma bai sake ni ba yasa nace masa.
"To."
Ina faɗa kuwa ya sake ni haɗe da lumshe idanuwansa yaci gaba da sippisig ɗin kununsa yayin da na fice daga kichin ɗin da mugun sauri....
"Ku kallla."Fatma tace da 'yan tawagarta, gaba ɗayansu kuwa suka juya idanuwansu ya sauka akan Sajda,tana taku ɗaiɗai cike da yauƙi da yanga wan da ya zame mata jiki domin kuwa duk in da gayu yake Sajda tasan gayu ta kuma san ta kansa. Abin da ya bawa su Fatma mamaki ba komai ba ne sai yadda Sajda ta samo mayafin da ya mugun shiga da leshin da ke jikinsu gaba ɗaya,anko ne na class mate ɗinsu, sun zaga kasuwanni da dama haɗe da super market suma da dama amma basu samu mayafin da ya mugun shiga da leshin ba kamar yadda na Sajda ya shiga, abin da suke gudu ya faru (Sajda ta fisu ɗaukan wanka) Har ta gifta su ta ankara da yadda suka zuba mata ido kamar su cinyeta ɗanya, basa shiri shiyasa bata shiga shirginsu, su kullum burinsu su fita ɗaukar gayu amman hakan ya gagara saboda ta fisu sanin takan gayun.
"Lafiya dai ko na ci muku bashi?"
" Muna mamakin yadda akai kika samu mayafin da muka gama karaɗe kasuwanni da dama ba mu samu ba."
"Hmm shine matsalarku?"
"Eh"
"To matsalarku tazo ƙarshe in sha Allah zan haɗa ku da NEEHAL COLECTION daga yanzu wahalar neman mayafai ƙare muku da yardar Allah, dan nima tun da aka haɗa ni da ita na huta, duk mayafan da ake so ana samu a gurinta ko wani irin kala ne, kuma masu kyau da ɗaukar ido cikin farashi mai sauƙi."
"Au wai kina nufin mayafin na gida ne ?"
"Eh mana ɗan hannu ne."
Amma ta iya mayafai maza maza haɗa mu da ita dan baza mu shiga gurin bikin nan ba sai da irin mayafin ki muma mu ƙure gayu.
https://wa.me/message/AD4MDTQJLXIRD1
Ku bi wannan link ɗin zai kaiku in da zakui magana da NEEHAL COLECTION daga yau matsalar mayafai ta ƙare muku zaku samu duk kalar mayafan da kuke so cikin farashi mai sauƙi ina mai tabbatar muku zaku ji daɗin muamala da ita.
Ga masu bukatar a tallata musu hajarsu kofa a bude take cikin farashi mai sauki.
#09037093702/08082007142
#BR
[10/19, 21:18] RASHUNA: BEBEE'ARTH
Wattpad@Rashuna
KA NA NAKA
(Allah na nasa )
25
Ina shiga ɗaki na jingina da ƙofa ina mayar da numfashin da bansan ina riƙe da shi ba haɗe da danne saitin da zuciyata take da har lokacin take harbawa.
Rintse idanuwana nayi na buɗe kafin na furta .
"Ya Allah."
Cikin ƙasa-ƙasa da murya,kafin na ji ringing ɗin wayata ya karaɗe ɗakin,idanuwana na wurga ina neman in da Zuwaire ta ajiyen jakata dan nasan wayar na ciki,aikuwa na hangota kan mirro na ƙarasa da sas sar fa dan kar wayar ta katse.
Ina ganin me kiran na saki murmushi kana nayi peaking da sallama a bakina ya amsa mini da sanyayyar muryar nan tasa kafin yace.
"An dawo daga makarantar?"
"Ban jima da shigowa ba a gajiye,so samu na yi wanka na gasa jikina amman ƙanin nan naka ya tsayar da ni,sai yanzu na shigo,ina shigowa kana kira."
"Ayya,amman Bro bai kyauta ba da ya tsayar mun da ke, yanzu kije ki yi wankan kafin a kira sallah, ko kuma ki bari ayi sallar tun da magaribar ta kawo kai,idan an idar da sallar sai ki wankan, bayan sallar isha zan kira in sha Allah yau mu kwana akan waya."
"Ok tom Allah ya bamu iko."
"Amin cwty."
Daga haka ya kashe wayar ina mamakin ko tambayata abin da ƙanin nasa ya tsayar da ni yi bai yi ba, mutane kala kala a rayuwa, yadda na fuskanci Yaa Sulaiman yana da matuƙar sauƙin kai,rayuwarsa yake me sauƙi,duk da baiwar wakin da Allah yayi masa hakan ba ya damunsa,duniyar sam ba ta dame shi ba,ba shi da tsauri da jin kai irin na ƙaninsa ko kaɗan,halinsu ma ba su zo ɗaya ba,a kyahun sura ma Yaa Sulaiman zai iya ɗara Mu'azz sai dai Mu'azz ya nuna masa gogewar fata da gayu, da kuma buɗewar jiki, dan da ganin Mu'azz siffar sa irin ta ƙarfaffun mazan nan ne ka na ganinsa kasan ya na ɗaga ƙarfe. Amman fa ba ina nufin Yaa Sulaiman ba ya gayu ba,shima yana zuba nasa gayun amman kana ganin Mu'azz kasan ba ajinsu ɗaya gurin gaye ba.
Sai da nayi sallar magariba kana na shiga wanka na gasa jikina da ruwan zafi sosai kana na fito na mutstsika mai na saka khumra na fesa turare, na ɗauko doguwar rigar baccina na saka na saka hula na fito daga ɗakin, dan na fara jiyo rigingimun su Neehal.
Suna falo da Nasreen ta barbaza musu Kay an wasa a gabansu,wannan ya cafo wancan wannan ya cafo wancan suna ta zuba gwarancinsu.
"Exxam ta saka Nasreen ta ƙwace mini rainon twince ɗina."
Murmushi Nasreen tayi kafin tace.
"Kina gama Exxam ɗin kuma ki tattara ki tafi ki barmu tare ba."
"Wa ya gaya miki?ai ƙafata ƙafarsu."
Na kai ƙarshen maganar ina ɗaukar Nimra dan itace kusa da ni aikwa ta hau washen baki.
"Ai wallahi Momy baza ta iya kyautar twince ba,tuni fa suka ƙwacen fadata,yadda kika san a kansu ta fara haihuwa."
"Ta fara haihuwa ko suka fara haihuwa? Ai kin cire Abban,dan ni tuni na sallama musu tawa fadar."
"Au Najjwa har da ke kema?"
Mu ka ji muryar Momy tana nufowa gurin.
"A'a Momy suɓutar baki na yi."
Na faɗa ina dariya.
"Shi kenan kinwa kanki na fasa baki ya yen nasu ."
Sigina Nasrin ta yi mun haɗe da alamun cewar dama na gaya miki baza ta iya baki ba, sai ji mukai Momy tace.
"To munafuka, ko dan ke ai na bawa Najjwa ya yen twince."
Murmushi nayi yayin da Nassren ta turo baki gaba tana.
"Kai Momy nice munafukar?"
Momyy ba ta saurareta ba sai Zuwaire da ta ƙwalowa kira yayin da Zuwairen ta fito daga kicin da sauri ta nufo in da Momy ke zauna ta duƙa haɗe da faɗin.
"Gani Momy."
"Ba'a gama abincin ba ne?"
"An kusa saura ƙiris."
"Ok to maza a hanzarta."
Sai da na jira Zuwaire ta ƙarasa girkin, dambun couse-couse ne da ya ji vegetables da hanta,aka ɗora soyeyyen kifi da coleslow a kai ga ginger drink a gefe,sai da na cika cikina kana na gudu sashen Gwaggo dan na ƙudirci bazan haɗa masa coffe ba shiyasa na gudu kar ma yazo ya same ni a nan dan sam wallahi bana son haɗuwarmu dan ni kaɗai na san abin da nake ji a jikina."
A falo na zauna ina danna wayata, tv na ta zubar gadonta, nasan Gwaggo tana ɗaki tana lazimi sai kuma anyi sallar isha ta gabatar da ita kana zata fito, shi kwa Baffa yana masallaci dan in ya fita sallar magariba dama sai bayan isha yake shigowa wani zubin ma sai ya kai goman dare bai shigo ba idan sun zauna da dattijan unguwar.
Ina nan zaune aka kira sallar isha na tashi na shiga ɗaki na ɗauro auwala na gabatar da tawa sallar na daɗe ina addu'a da nemawa mahaifiyata da kakata rahama gurin Ubangiji tare da dukkan wan da suka rigamu gidanmu na gaskiya kafin na shafa.
Takwas daidai kiran wayar Yaa Sulaiman ya shigo wayata.
Video call yace mini zai kirani ya kashe, jin hakan yasa ni barin hijabin jikina, na hau kan gado haɗe da ɗaukar remort na ƙara ƙarfin Acn.
MU'AZZ
Tun kunun madarar nan babu abin da ya yadda ya sakawa cikinsa,saboda yau yasan yana da coffee ɗin da zai saukar masa da nutsuwa, dan sai ya fanshe na kwanakin da bai sha ba.
Tara da rabi daidai tayi masa cikin harabar gidan Momyn,yayi parking ya fito cikin ta kun nan nasa na ƙasaita ya nufi cikin gidan,knocking biyu yayi Zuwaire tazo ta buɗe cikin yanayin baccin da ya fara fusgarta, tana ganin shine ta bashi hanya haɗe da risinawa tana gaishe shi duk da ta san ba lallai ya amsa ta ba,a tsakiyar falon ya tsaya yana ƙare masa kallo,yayin da Zuwaire ta risina a gabansa tace.
" Momy tun bayan sallar isha tayi mana sallama ta shige, Nasrin kuma ba ta da ɗe da shiga ɗaki ba,wa za'a yiwa magana?"
"Ɗayar "
Ya bata amsa yana mayar da bakinsa kamar ba shi yayi maganar ba kafin idonsa ya sauka akan tangameman hotonta da ke manne a bangon falon.
Zuwaire kuwa ya barta cikin tunanin wa yake nufi,kamar kuma ance ta kalli saitin da yake kalla sai idonta ya faɗa kan hoton Najjwa, lalle gayen nan ɗan rainin wayo ne Najjwan ce bai san sunanta ba ko ya,ko kuma kawai rainin sens ne?
"Najjwa za'a kira?"
Jinjina mata kai yayi, yayin da tace.
"Aikam ina to ta riga kowa bacci a gidan nan,dan tun ɗazu ta yiwa kowa sallama ta tafi sashen Gwaggo yau can zata kwana."
Ranta cike da mamakin me zai yiwa Najjwan yake nemanta da wannan daren.
Juyawa yayi ya fice daga falon yayin da Zuwaire ta mayar da ƙofa ta rufe.
Kansa tsaye ya nufi sashen Gwaggo babu tunanin komai a kansa sai kawai Najjwa ta bashi coffe ɗinsa.
Murɗa handle ɗin ƙofar yayi ga tsammaninsa kuma sai ta buɗe yasa kai cikin falon, tsit falon yake an kashe komai ban da fitilu, tsayawa yayi cak yana ƙarewa falon kallo ba tare da yasan me zai yi da ya kawo ƙafafuwansa nan ɗin ba.
Najjwa
Ba'a je ko ina da fara vidio call ɗin ba na gaji da zama,kwanciya kawai nake biɗa nace ya kashe vidio call ɗin ya kira ni voice call kawai,yace shi sam bai gaji da ganina ba shiyasa ma in sha Allah sai ya yakice wannan weak end ɗin yazo ganina, nace.
"Ni dai kam har ga Allah na gaji da zaman."
Dan ni dai kam idan har an gan ni a zaune aiki nake,ko a makaranta ko kuma in naci abinci ina son ya tsirgan bayan hakan nikam ko da yaushe a kwance nake, Gwaggo ta kan ce mini me karyayyan ƙugu."
"Ya zan yi da ke Gimbiyata? Ai dole na bi umarninki."
Yana kawo ƙarshen maganarsa ya kashe vidio call ɗin kana ya kira muka ɗora daga in da muka tsaya bayan na kwanta kan tausassan gadona ina mimmiƙewa, muna cikin wayar na ji ƙishirwa ta kama ni sai lokacin na tuna ma da na ci abinci ban sha ruwa ba lemo nai ta ɗaɗɗaka, miƙewa nayi na fito muna cigaba da wayarmu.
Duk da na ji bugawar ƙirjina ban kawo cewar shine a gurin ba tun da nasan me zai kawo shi nan a wannan daren?
Tafiya nake hankalina ba ya kan hanya yana kan wayar da muke da Yaa Sulaiman sai kawai na ji nayi karo da mutum, a razane na ɗago dan ganin waye idona ya sauka a kansa,baki na buɗe zan saki ihu cike da mugun tsoron da yayi sanadiyar fitowar idanuwana dan ni tunanin da ƙwaƙwalwata ta bani aljani ne yayi suffarsa ya zo mini, hannu yasa ya riƙo ni ganin ina yin baya kafin ya saka tattausan hannunsa ya toshe mini bakina dan hana sautin ihun da nayi niyar kurmawa fita, yana jin kamar ya saukewa idanuwana kiss sabo da yadda sukai matuƙar yi masa kyau,tun ba yau ba yasan idan na tsorata idanuwana na yin mugun kyahun da ke ƙayatar da shi.
"Ina coffe ɗin nawa."
Ya faɗa yana sakina dan ya san tun da yayi magana na dawo cikin nutsuwata, sai lokacin na bi wayata da kallo in da tayi gefe ta kife, ƙarasawa na yi in da ta kife dan dukkan alamu Yaa Sulaiman