x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 21 - KANA NAKA ALLAH NA NASA complete document

  • 60001 words
  • 63000 words
  • Out of 66841 words

Category: Love Stories

Views 292

25 Aug 2025
Start ads
After Image Ads
gado,daga ƙarshe na ɗauro auwala na kaiwa Allah kukana akan ya bawa Ammi lafiya,wannan aikin da za'a yi mata Allah yasa a yishi cikin sa'a da aminci,domin kuwa Ammi ke dishashe wani gurbi da rashin Man ya samar da shi,dan haka rashinta ban san iya illar da zai yi mini ba,amman a tsorace nake wallahi,zuciyata a tsintsinke take da wannan ciwo na Ammi.

A bin da likitocin suka ce shine;zasu bata treatment na sati biyu,in sha Allah ba za ta ƙara fama da zazzaɓi ba,bayan sun ɗorata akan drugs,kuma a shawarce kar ayi nesa da ita har zuwa nan da shekara ɗaya,daga nan za'a kuma yi mata gwaji idan ciwon ya barta ba sai anyi aikin ba,idan kuma yana nan dole sai anyi mata juyen jini amman fatanmu kafin lokacin ma ciwon ya barta in sha Allah.

Jin haka yasa Momy tunanin ta yadda za'ayi su bar Najjwa a hannun Mu'azz,hanya guda ce ta hanyar igiyar aure ta sarƙafu tsakaninsu shi ne hankalinsu zai fi kwanciya,ba wai tana zargin Mu'azz ba ne,ba kuma don ba ta yadda da shi ba ne,shaiɗan take gudu,wan da ko ya ya ya hango mitsitsiyar ƙofa yasan ta yadda zai yi ya shiga,musamman yadda ta san al'adun turawa sun jima da kama Mu'azz ɗin,dan haka maganin kar ayi kar a soma,aure za ta saka a ɗaura musu kafin ma su tafi su barsu a cikin ƙasar,ita za ta iya cewa ma tsuntsu uku ta jefa da dutse ɗaya.
Na farko shine,samun damar barin Najjwan da Ammi a hannun Mu'azz hankali kwance ba tare da tunanin wani abu ba.
Na biyu,ta cimma da ɗaɗɗan burinta na haɗa a ur an Mu'azz da Najjwa.
Na uku,ta cika burinta da alwashin yiwa Mu'azz aure da ta ci,wan da mutuwar Sulaiman ta saka ba ta bi ta kan hakan ba.

Abba ta fara samu da maganar,in da kai tsaye shi ma ya amince da shawarar da ta kawo,sai dai kuma yace ta fara shawara da Daddynsu Mu'azz ɗin,shima zai kira Baffa ya ji ta bakinsa,duk da yasan babu wan da zai yi gociya da wannan shawarar amman jin ta bakunansunma yana da daɗi.

Kamar yadda kwa Abba yayi hasashe ba'a samu wata togaciya ga ko wan ne ɓangare ba,Yaya Ladi ce ma da suka yi waya da Daddy yake sanar mata ta fara tseguminn ya za'ayi su aurawa Mu'azzz matar matacce,bayan ta ji cewar kafin Sulaiman akwai wanda aka ɗaura musu aure ya rasu,yanzu ga Sulaiman ɗinma ya rasu salon shima Mu'azz ɗin su rasa shi.

Maganar tata ta kaɗa Daddy har ya so yin togaciya ga auran nasu,sai da Safiya tayi ta lallama shi cikin magana me daɗi da nuna masa babu me kashewa da rayawa sai Allah,a haka ƙaddarar Najjwan ta zo,rabon haihuwar Ammi shi ya kashe mijinta na farko,wanda ta kuma yuyuwa rabon haihuwar wasu yaran tsakaninta da Mu'azz ne ya kashe Sulaiman,kuma ba mamaki idan ka matsa ba za'ayi ba rabon ya kashe ka,kaga ayi bayan ranka in dai hakan a rubuce yake.

Tuni jikin Daddy yayi sanyi,musamman da ya kwana da sanin rabo idan ya rantse babu abin da ba ya sakawa,dan haka tuni ya sallama,aka ɗaura auran HASSANA BASHIR SUNUSI (NAJJWA) da EL MU'AZZ ALIYU FANDA ba tare da jin ta bakin ko ɗayansu ba,wan da Momy ta ɗauki alhakin hakan ta kuma roƙi kar wan da ya sanar musu yanzu,idan ta ga dacewa da yuyuwar su sani za ta sanar musu.

Sati biyun da aka ɗibarwa Ammi yana cika aka sallamemu muka dawo gida,kwana ɗaya su Momy suka ƙara suka juya,ganin yadda jikin Ammi yayi kyau sosai,aka bar mini Zuwaire don ta tayani hidimar Ammi da kuma zaman gidan tun da matar gidan ba ta nan.

A haka rayuwa ta miƙa mana a Saudiya,tun muna nuna baƙunta a zaman gidan har muka zo muka saba sosai,duk in da na ke son zuwa ga driver nan ya ajiye mana,duk da ni yawan fitar tawa ma Masjidul Haram ne,dan ko kaɗan ba na gajiya da zuwa da yin ɗawafi ina kai kukana gurin da za'a share mun,a bani abin da na roƙa har da yi mini ƙari,in roƙawa Ammi lafiya ba tare da an mata juyen jinin ba,na kuma roƙawa Ummana,Yaa Muhd,Mann ɗina rahama da yafiyar Ubangiji tare da sakamakon gidan aljanna.
Ko kaɗan a raina ban jin sha'awar sake aure,musamman idan na tuna maza biyu na binne,ban jin a kwai wan da zai kuma yin gigin aurena,amman kuma idan yin wani auren ya na ƙaddarata bazan yi jayayya da ita ba,zan roƙi Allah ya bani zaman lafiya da kwanciyar hankali,ya kuma bamu tsayin rayuwa da duk wanda ya zaɓa mi ni,ya kuma saka ni zan riga shi mutuwa ba wai ya tafi ya bar ni ba,don ban san wata iriyar illa hakan zai haifarwa zuciyata ba,na kuma san na shiga bakin duniya kenan,duk da yanzun ma ba'a rasa masu yi da ni ba,suna manta cewar ni kaina bani na zaɓi hakan cikin rayuwata ba,a haka nima ta zo mini wanda su kansu ba su huce hakan ta faru da su ba,tun da duka tafiyar rayuwar ba a tafukan hannuwanmu su ke ba,ta na hannun Rabbi izzati yadda ya so hakan ke faruwa babu tsimi babu dabara.

Girkuna nake yi mana Kala-kala masu rai da lafiya,idan ya na nan na saka Zuwaire ta jere masa nasa akan dining har da coffee wan da muma ya fara kama jikinmu a zamanmu cikin saudiyar nan.Sai na kwana nawa ban saka shi cikin idona ba,saboda da na daidaici lokacin dawowarsa in na shige ɗaki ba na fitowa,sai na bar Zuwaire da Ammi a falo wacce na san dole sai ya buƙaci ganinta,don wataran ko muna ɗaki ni da ita sai ya turo Zuwaire ta ɗauko masa ita,rashin saka shi cikin idanuwan nawa shi ne samun lafiyar zuciyata da ta dawo da harba masa fiye da daa ma,idan na ganshi wani irin feiling ne ke motsawa a dukkan wata gaɓa ta jikina,shiyasa na ke kaucewa ganinsa sai kuma ranar da tsautsayi ya haɗa mu.

Kamar yau da Ammi ta tasar mi ni cikin dare da rigimar yunwa,duk da ba ta fiya tasar mini ba,ba ma ta tashi shiyasa ba na ajiye mata komai,yau kam sai da ta sakani ɗaukota muka nufo kicin,na zaunar da ita na shiga haɗa mata abincinta,sai gashi ya shigo kicin ɗin ,gurin da na zaunar da ita ya nufa kai tsaye yana dariya haɗe da faɗin.
"Hey prity."
Kamar yadda shi ya ke kiranta,tuni ta ɓangale masa baki ta na miƙo masa 'yan hannuwanta,ɗaukarta yayi suka hau juyi a kicin ɗin suna ƙyaƙyata dariya,zuwa lokacin na gama haɗa mata abincin na juyo ina kallonsu cike da sha'awa,kafin na ɗauki wayata ina duba miss call ɗin Miqdad,da bansan lokacin da ya kira ba,zuwansa uku bayan komawarsu yana zuwa ganin jikin Ammi,kuma ko wani zuwa da kaya niki-niki zai zo mata,na sakawa da na ci da na wasa,kuma kullu yaumin sai ya kirani a waya don ya ji lafiyarta,wataran sau biyu wataran sau uku,ko kuma ya kira vidio call na haɗasu,tun ba ta waye shi ba har ta waye shi shima ta na ɗaga masa 'yan hannuwanta ta na ɓangala mishi dariya.
Jin yadda ƙirjina ya ƙara ƙarfin bugu,da kuma jin ƙamshin turaransa dab da ni yasa ni ɗago kaina idanuwana suka sauka kan farar kyakkyawar fuskarsa,kallonsa nake kamar wani magnent ko kaɗan na kasa janye idanuwana daga kansa,zuciyata na mugun bugawa da sonsa da ƙaunarsa da kuma wani bala'i da ya same ni na jin feiling a kansa daga ko wata gaɓa ta jikina.
Bowl ɗin da na haɗa mata abincin ya ɗauka ya juya zuwa kan dining ɗin da ke kicin ɗin ya jaa kujera ya zauna ya fara peading ɗinta.
Da ƙyar na iya janye idona daga kansa na taka a hankula zan bar kicin din cikin matuƙar sanyin jiki,yayin da maganar da yayi ta dakatar da ni daga niyar fitar da nayi.

"Ina nawa Abincin? Nazo ban tarar da komai akan dining ba,kuma yunwa na ke ji sosai,kin sabar mini da naki abincin shiyasa ban riƙo komai ba na shigo."

Ni sai a lokacin ma na tuna ban ajiye masa komai ba,saboda yau tun rana da Zuwaire tayi mana girki ba mu sake girki ba,ragowar muka ci da daddare saboda yadda tayi mana daɗi,wake da shinkafa dama nace tayi mana da ganyayyaki sai dafaffan ƙwai,to na sanshi ba lallai yaci ba shiyasa ban ajiye masa ba,kuma nayi niyar haɗa masa coffee mantawa nayi.

Juyawa nayi ba tare da nace komai ba dan ko na buɗe baki ban jin zan iya wata magana a yadda nake jin yanayin jikina.
Coffee na haɗa masa,sai na zubo masa tsadaddun biscuit ɗin da yake uban jibgewa da sunan na Ammi ne,wanda ƙarfin cinsa Zuwaire ce tun da ni ba damuna yayi ba.

Niyata ina ajiye masa na juya na bar kicin ɗin amman ya tsayar da ni da cewar na jirasa ya gama,kafin ya gama ɗin tuni Ammi tayi bacci a jikinsa.
Ya na gaba ina binsa a baya har zuwa ɗakin nawa,nayi tunanin zai tsaya a bakin ƙofa na karɓeta tukun,sai naga ya murɗa ƙofar ya shiga na mara masa baya haɗe da cakewa daga bakin ƙofar ina jiran fitarsa dan na mayar da ƙofar na rufe.

Kwantar da ita yayi a kyakkyawan gadonta me laushi,ya rufa mata tattausan dubert kana yayi mata addu'a ya tattofa mata,ya juyo cikin takun nan nasa wanda nake jinsa tamkar haɗe suke tafiya da bugun zuciyata,yana isowa dabf da ni ya jaa ya tsaya haɗe da zubawa fuskata ido,aka ci sa'a nima shi nake kalla idanuwanmu suka gauraya guri guda.
Da duk kallon da nake masa da yadda nake jin wani sabon failing a kansa yana motsawa a dukkan wata gaɓa ta jikina,ban ankara ba ashe ya ƙara yo gab da ni sai jin saukar muryarsa na yi yana.
"Yau kurma kika zama ne? Kwatata ban ji muryarki ba."

Ɗan firgita na yi,jikina ya ɗauki mazari kamar wacce aka sakawa shocking."

"Lafiyarki kuwa?"

Ya faɗa yana ƙara kusantowa daf da ni,ya fi ni tsayi sosai,tuni ƙamshin turaransa ya ƙara birkitar da ni,chymistry yaci gaba da aiki a jikina.haɗe da sanya hannunsa a dokin wuyana,lumshe idanuwana nayi haɗe da jin saukar hannun nasa a ko wata gaɓa ta jikina.
"Naajjj lafiyarki kuwa?"
Ya kuma tambaya,yana kuma shafa hannuwansa akan dokin wuyan nawa wanda yasa ni wara idanuwana cikin nasa ina jin taruwar ƙwallar masifar da ta fitineni cikin jikina,kuma duk shi ya ƙara haddasa mini hakan,na kusantowarsa gareni da sanya tafun hannunsa kan dokin wuyana yana shafawa.
Ba zance ga ta yadda na tsinci kaina cikin faffaɗan ƙirjinsa da nake matuƙar so da buri ba,koma meye zan ce shaiɗan ya taka rawar gani gurin cimma muradin gaɓɓan jikina,wata iriyar kyakkyawar runguma na yi masa,ina mimmiƙewa a jikinsa duk wanda ya ganni a wannan lokacin yasan ba cikin hayyacina nake ba,umarnin zuciya da gaɓɓan jikina kawai nake amsawa.
Shima kuma baiyi ƙasa a guiwar karɓata ba yana ƙara fitinar jikina da zazzafan romance ɗinsa da ya fara kwance 'yar ƙaramar ƙwaƙwalwata.
Yayin da na ji saukar bakinsa a kan nawa kuwa tuni muka gigice muna ƙara gigita kanmu,wato wani irin soft mouth to mouth kiss da Mu'azz yake mini tamkar zai raba ni da harshena baki ɗaya,gaba ɗaya ya gigice ya fita daga hayyacinsa,cikin salo da ƙwarewa ya ke ƙara birkita mini 'yar ƙaramar kwanyata.
Cikin wani salon da ban taɓa tunanin akwai irinsa ba yake kissing ɗina,ban samu damar hana shi ba,saboda ni kaina ban san inda kaina yake a lokacin ba,domin kuwa yau ce rana ta farko da hakan ta haɗa ni da wani aka kuma ci sa'a ba kowa ba ne sai muradin zuciyata.

Ƙarar kiran wayarsa cikin wani ringtone me daɗi ya fara dawo da mu cikin duniyar da muka bari,muka lula wata can da ban,bayan kiran farko ya katse,na biyu da ya shigo yayi silar farkar da mu gaba ɗaya,zame jikina nayi haɗe da durƙushewa nan bakin ƙofar cikin kunya,nadama,takaici,da kuma jin haushin kaina,ina jin ƙarar rufe ƙofarsa alamun ya fita na tashi na nufi toilet,na sakarwa kaina ruwan sanyi ko zan ji dama-dama,dan harlokacin lamarin ƙara ta'azzara yake a jikina,na kai ƙololuwa gurin son a biya mini buƙatata a cire mini abin da ya fitine ni a cikin jikina.
Sai da na ji ɗan dama-dama kana na tsarkake jikina na fito,saboda yadda naga na jiƙe na san wanka ya wajaba a kaina,kana na fito,rigar bacci kawai na saka na lallaɓa na kwanta ina jajjera ajiyar zuciya kamar wacce tayi mugun aiki ta gaji,tare da ambaton astagfirillahil azim cikin muguwar nadama.


Da ƙyar ya kai kansa ɗaki shima yana har haɗa hanya,tambayar kansa yake garin ya hakan ta kasance musu?
Shi dai kawai yasan ya ji yana buƙatar jin damuwarta,zai iya cewa tun daga lokacin da ta faɗo jikinsa ya rasa control ɗinsa gaba ɗaya daga jin tudun ƙirjinta a jikinsa,dama kuma me neman kuka ne aka jefe shi da kashin awaki,a mugun buƙace yake shiyasa ma ya shirya zuwa calcuta gurin Zareena,ya kuma zaɓi can a matsayin in da shima zai yi course ɗinsa na tsawon wata shida akan dashen zuciya,dan ya gaji da watangaririyar da yake shi ka ɗai,ba ya son matsa mata,rayuwar da ta zaɓawa kanta tana ganin hakanne daidai da ita,amman har ga Allah yana cutuwa da rashinta kusa da shi,gashi hakan har ya kusa affecting ɗinsa aikata aikin da na sani,abin da Momy take guje musu in da ya aikata da wani idon zai kalli Momyn? Har yana faɗin 'yar tata bata da abin jan hankali,ga shinan yanzu ba hankalin nasa ta ja ba, susuta shi tayi ta birkita masa tunani gaba ɗaya.

Toilet ya nufa kai tsaye,be bi ta kan kiran wayar da Zareenah ke faman doko masa ba,ya jefa wayar kan gado haɗe da jan siririn tsaki,rana ta farko da ya ji mugun jin haushin Zareenah akan tafiyar da take ta barshi,sai dai shi ya bita duk in da take ba damuwarta ba ce.
Ruwa ya sakarwa kansa me mugun sanyi,kafin ya tsarkake jikinsa ya fito daga toilet ɗin ya na jin ɗan dama-dama.

Washe gari busy ya zama sosai,saboda gobe ne idan Allah ya kaimu tafiyar ta sa,dan haka abubuwa suka haɗu suka cuɗanye masa.
Sai dare ya shigo gidan tun safe da ya fita,addu'arsa Allah yasa Ammi ba ta yi bacci ba,dan shaf ya manta yau ne take cika wata bakwai a duniya,dan haka riƙe da cake ɗinta ya shigo da niyar ya sanya Zuwaire ta ɗauko masa ita,amman kuma be san me yasa da ya tarar da falon tsit ƙafafuwansa suka kwashesa suka nufi ɗakin Najj ba?
Be sani ba ko matsuwar da yayi ya sanya Ammi a idonsa ne?
Ko kuma son ka sanya mahaifiyar Ammin a ido ba.
Wata zuciyar ta ba shi amsa da hakan,siririn tsaki ya jaa yana murɗa ƙofar ɗakin ya shiga,da Ammin ya fara cin karo a kwance tayi lamo amman kuma ba bacci take ba,tana ganinsa ta miƙe zaune haɗe da miƙo masa 'yan hannuwanta alamun ya ɗauketa tana ta wangale masa baki,ajiye cake ɗin yayi akan stool haɗe da ƙarasawa ya ɗauketa yana.
"Hey Prityy."
Yana sakar mata tasa dariyar shi ma,ɗaukarta yayi,ya zauna bakin gado haɗe da janyo stool ɗin da cake ɗin yake kai,tsadaddiyar wayarsa ya saka ya yanka cake ɗin haɗe da gutsurowa ya kai bakinta yana.
Happy seven month prityna."
Kana ya kai ragowar na hannun nasa bayan ya saka mata a baki bakinsa,daidai nan na fito daga toilet ɗaure da tawul ruwa sai zirarewa yake daga jikina saboda santsin fatata ruwa sam ba ya zama a jiki.
Yau kwata-kwata ko falo ban leƙa ba,komai nake buƙata Zuwaire ke kawo mini,saboda har lokacin yanayin be sake ni ba,yini nayi ina kuka bayan na kira Momy akan cewa nifa zanyi dawowata gida,dan wallahi na gaji da abin da ke fitinata a jikina a kan MU'AZZ tun da aka fara haka nan gaba bansan me zai faru ba,maganin kar ayi kar a soma gara na lallaɓa na koma,idan ban ganshi ba ai zan samu sauƙin abin da ya addabe ni cikin jikina.
Amman Momy sai cewa tayi "Nayi haƙuri na zauna,kamar yau ne zan dawo,tunda wata shida ne ya rage,ko wani abu Mu'azz yake miki?"
Ta jefo mini tambayar da ta zo mini tare da faɗuwar gaba cikin rawar baki nace da ita.
"A' a"
Ina jin kamar ta san abinda ya faru tsakaninmu jiya.
"To ki kwantar da hankalinki,ba zaman kowa kike ba zaman samun lafiyar Ammi kike,nan da wata shida in sha Allah komai zai wuce,nima sosai nayi missing ɗinku,Mu'azz ɗinma naji yace gobe zai tafi calcuta yin wani course sai nan da wata shida zai dawo,kinga ma daidai da gwajin Ammin kenan."

Maganarta ta ƙarshe ta kuma saka na ji kamar Mommy ta rafko abinda muka aikata jiya,amman duk da haka na ji daɗin cewa Mu'azz ɗin zaiyi tafiya,tunanin babu shi cikin gidan zai bani salamar cewar,ba wani abu da zai haɗamu bare mu aikata wani abu mara kyau.

Ƙafafuwana ne suka ɗau rawar ganinsa ba zato ba tsammani a cikin ɗakin,yayin da shi kuma ƙarar buɗe ƙofar ta saka shi waigowa idanuwanmu suka gauraya guri guda,kafin ya janye idonsa daga kallon ƙurillar da muke bin juna da shi zuwa jikina yana ƙarewa halittata kallo cikin wani fitinannan kallon da nake jinsa har cikin ɓargon jikjna,juyawa nayi zan koma toilet ɗin saboda yadda na ji duk wani ƙarfina yana narkewa duk wata gaɓa ta jikina ta na mini sanyi.

Caraf na ji tattausan hannunsa ya riƙo nawa hannun ya juyo da ni haɗe da sanya ni cikin jikinsa cikin muguwar kiɗimar da ta same shi.
Ya kanainaye ni gaba ki ɗaya ya shiga cikin jikina ta ko ina haɗe da cusa fuskarsa ta ƙasan wuyana, haɗe da goga mini sassaƙan sajensa mai taushi ta gefen wuyana wanda yayi sanadiyar miƙewar tsigar jikina.
Duk inda hannunsa ya sauka a
End Ads