"Ban san dokawar zuciya ba sai akan Mu'azz,akansa na san yadda take tsalle a ƙirji kamar zata fito,idan na ganshi ko na ji muryarsa. To idan hakan yana nufin shine soyayya, Yaa Muhd da Yaa Sulaiman duk ban so su ba kenan?"
"Ba haka nake nufi ba, kawai dai abin da kike ji game da Mu'azz duk ya girmi abin da kika ji game da Yaa Muhd da Yaa Sulaiman zan iya cewa akan Mu'azz zuciyarki ta fara numfasawa."
"Innalillahi wa inna ilaihir raji'un!Me yasa zuciyata zata mun hakan? Na ɗauka kawai burge ni yake ashe gurin da ta ɗauka ta kai ni da ban. Da fari tabbas da na gan shi zuciyata ta doka masa,amman na yi tunanin burge ni yake musamman da na ganshi da dimple domin kuwa ina matuƙar son dimple kema kin sani,kuma na ga ya na ɗiban kamanni da Jhon Abraham tun da kin san duk cikin Actors ɗin india tsaffi da sabbi babu wan da yake birge ni kamarsa.
Me yasa zata mun haka,me yasa take son janyo mini abin kunya?"
Na kai ƙarshen maganar cikin raunin murya yayin da Nauwwa tace.
"Ba mu sani ba,ba mu san me Allah ya shirya a nan gaba ba."
"Nikam ko soyayyarsa zata kashe ni bazan bari ta fito ba Nauwwa,zan jure komai zan kuma daure har illa ma sha Allah,kema kam dan Allah ki riƙe mini wannan sirrin."
"In sha Allah babu me ji, amman idan na ga zaki mutu bazan san lokacin da zan faɗa ba."
"In sha Allah soyayyarsa tayi kaɗan taga bayana."
*
Sai da nayi da kacen yin wannan maganar da Nauwwa,domin kuwa kamar jira zuciyata ta ke nasan son Mu'azz ta ke ta adda be ni da tunaninsa,kwana nayi ina juyi a gado maƙale da tunaninsa da mararin son ganinsa, daga ƙarshe kuka na saki sabo da baƙin cikin abin da zuciyata ke son janyo mini, ji nake kamar na janyo kwanakin da suka rage na bikinmu da Yaa Sulaiman ayi ko na samu wannan mayyar ta barni na huta.
Auwwala na ɗauro na kalli gabas na dinga kaiwa Allah kukana, sai da nayi sallar asuba kana na kwanta bacci yayi awon gaba da ni bayan na samu nutsuwa a zuciyata.
**
Ranar lahadi da Yaa Sulaiman zai koma yini muka yi tare a gidan Nauwwa,kafin lokacin tashin jirginsu ya gabato na kai shi filin jirgin muka rabu cikin kewar juna da alƙawarin ranar alhamis zai zo in sha Allah bikin yaye mu daga makaranta,daga nan kuma sai bayan bikinmu in zamu koma tare dan hutu zai ɗauko gaba ɗaya ya taho.
Monday tushen aiki.Rana ce da ta kasance mun kammala karatunmu,duk da sai ranar alhamis za'ai bikin yaye mu bai hana yin hidima yau ɗin ba,girkuna mu ka yi kala Kala da snacks da lemo,bayan mun fito daga paiper ƙarshe muka hau partynsu,kafin kuma a shiga hotuna ana shewa da raƙashewa da abubuwa iri-iri kamar yadda kuka san 'yan graduation na yi.
Sai yamma liƙis muka taho zamu bar makarantar, yau dama nake da niyar komawa gida,dan yau Najib zai dawo cikin dare, duk da Nauwwa na ta mun na cin na bari sai gobe na tafi amman ban jin zan bari sai goben gaskiya.
Nauwwa ce ta hange shi jikin motarsa a jingine ta taɓo ni haɗe da nuno mini shi,kamar jira yake na kallo in da yake tsaye ya ɗago kansa idanuwanmu suka sarƙe guri ɗaya,zuciyata ce tayi wani irin dokawa da har sai da na riƙe hannun Nauwwa ƙam kamar hakan zai sama mini relef daga tsallen da zuciyata ke a ƙirjina.
Yafito ni yayi da hannunsa alamun na je, na kalli Nauwwa itama ta kalle ni haɗe da mun nuni da naje ɗin, yayin da na nufi gurin da yake tsayen, da duk takun da nake da yadda zuciyata ke bugawa har na isa in da yake.
Buɗe murfin motar yayi haɗe da mun nu ni da na shiga.
Tabbas ina buƙa tar zaman ko zan samu sauƙin yadda zuciyata ke tsalle kamar zata tsaga ƙirjina ta fito.
Ina shiga ya rufe kana ya zaga ɗaya side ɗin ya shigo.
Maimakon na samu sauƙin abin da nake ji sai ma gaba da ya ƙara musamman bayan ya daidaita zamansa cikin acent ɗin muryarsa yace mini.
"Yunwa na ke ji."
Rintse idanuwa nayi saboda yadda muryar tasa ta ratsa ni ina jin yadda wani abu ya tsarga ta marata,cikin rawar murya nace.
"Za ka ci cake?"
Ya girgiza mini kai.
"Samosa fa?"
Nanma kan ya girgiza mini.
"Danbun nama fa?"
Da gajiya a muryarsa da tambayoyina yace.
"Abu me ɗan nauyi kawai, yunwa nake ji sosai naje gida Momy ba ta nan,ba ko wani jagwalgwalo nake ci ba, muje gida ki sama mini wani abu."
Gyaɗa mishi kai na yi.
Ya tsare ni da idanuwansa da nake jinsu a ko wata gaɓa ta jikina.
"Tom."
Nace dan nasan dalilin kallon kenan yana jiran na amsa shi da baki bayan shi yanzu ya gama bani amsa da kai ɗin.
"Bani dambun naman na ci kafin mu ƙarasa gidan."
Fitowa nayi daga motar a raina ina Allah yasa Nauwwan ba ta tafi ba, Allah ya taimaka ba ta tafin ba kuwa.
"Ai jira nake naga ya ja motar kana nima na ja tawa na tafi."
"Hmmm wai yunwa yake ji, Allah ni dai yana takura mini."
Na faɗa ina kwaɓe fuska kamar zan kuka.
"To yanzu me zaki masa?"
"Dambun nama zan ɗaukar masa da lemo ya fara ci kafin mu ƙarasa gida."
"Kice shi kenan tafiyar, sai dai na biyo ki da kayanki."
Harara na galla mata ina ɗaukar robar dambun naman da lemo, ta saki dariya kafin ta kuma cewa.
"Gaskiya Yaa Sulaiman ya ci girma ya barwa ƙaninsa dan da dukkan alamu shima ya kamu."
Wata hararar na kuma wurga mata ina barin gurin dan ban da abin ce matan,ina jiyo dariyarta har naiwa gurin da take nisa.
Sai da ya gama cin dambun naman kana ya ja motar muka bar harabar makarantar,ina gani aka kira shi a waya ya ɗaga ban jin abin da aka ce a ɗaya ɓangaran ba sai shi da yace.
"Ok gani nan in sha Allah."
Sai naga ya ɗauki hanyar da zata kaimu gidansu anan na gane Daddynsu ne ya kira shi,kuma bai ce da ni ƙala ba har muka ƙarasa gidan yayi parking cikin harabar gidan,ya fito bayan ya kashe motar ya rufe ni a ciki ya nufi cikin gidan cikin takun nan nasa na ƙasaita.
Safiyya ya samu a falo tana bawa 'yan aiki order yadda zasu jera abinci kan dining, kallo ɗaya ya yiwa gurin da take tsaye yasa kai koridon da zai sada shi da sashin Daddynsu ba tare da ya bi ta kan 'yan aikin da suka zube suna gaishe shi ba.
Kallo Safiya ta bi shi da shi ta na ƙwafa haɗe da jin muguwar tsanarsa, yaron ya mugun raina ta, har ba ta ƙaunar taga yazo gidan, dan ranar nan da yazo Daddy yace.
"Ba kaga Auntynku ba?" Ya faɗa yana nunata, sai da yayi mata kallon raini kana yace."Ban lura ba ne, sannunki fa."
Abin yayi mata ciwo fiye da tsammani shiyasa ta fita sabgarsa,har gara Sulaiman da Nasrin zasu gaisheta cikin mutumci amman suma ba ta ganin fara'arsu.
Babu dai yadda zasui da ita dukkaninsu,mahaifinsu ne dai ta riga ta ƙwace sai haƙuri.
Cike da farin ciki Daddy ya tari ɗan gaban goshin ɗan nasa,ya kwana da sanin Allah ya jarabce shi da son Mu'azz sama da kowa cikin 'ya'yansa shiyasa bashi da wani buri da ya wuce na ganin 'ya'yan Mu'azz ɗin sai dai kuma shiru har yau matar tasa ba ta haihu ba,amman yana fatan kada Allah ya ɗauki ransa ba tare da yaga jinin Mu'azz ba.
Gaisawa suka yi, yayin da Daddyn ya shiga yi masa bayanin dalilin kiran nasa, yana son bayan bikin Sulaiman idan sun koma shima ya haɗo komai nasa ya dawo gida zai buɗe musu ƙaton asibiti da gidajansu a ciki.
"Amman ban ƙi ta taka ba Daddy Zareenah fa?"
"Idan ma ba ta amince zata biyo ka ba,sai ka baro ta a can duk san da ta samu lokaci sai tazo maka, in yaso sai ka samu wata a nan kayi auranka ba shikenan ba,dama ina son ganin 'yan dagwai-dagwai ga naka ga na Sulaiman."
"To zan duba na gani."
" Yauwwa ko kai fa, Allah ya shige mana gaba, muje mui sallah naji an fara kira."
Tare suka je masallaci sukai sallar da suka dawo a nan harabar gidan suka yi sallama Daddyn ya koma ciki shi kuma ya shiga motar ya fara ƙoƙarin tayar da ita.wan da ƙarar motar ne ya tashe ni daga baccin da ya kwashe ni.
Sai da na yi wanka nayi sallah kana na shiga kichin har lokacin na rasa ma me zan dafa masa,yana ajiye ni ya juya yace zaije ya dawo, har lokacin Momy ba ta dawo ba kuma tare suka fita da Nasrin, Gwaggo ke gayan cewa taron sauka suka tafi na aminiyar Momyn.
Jalof ɗin couse-couse nayi masa ya ji vegitavles da kifi kana na haɗa masa da ɗan ƙaidar tasa coffee,ina gamawa sai gashi kamar wan da aka gayawa, a lokacin har an idar da sallar isha ina to ma sai da yayi sallar ya shigo.
Kwandon abincin na ɗauko na kawo masa ya karɓa kafin yace da ni.
"Na gode."
Murmushi kawai nayi ba tare da nace komai ba ina bin fuskarsa da kallo, yadda tayi fresh da alamu wanka ya sake kamar nace ya tsaya nayi ta kallonsa har mahadi ya bayyana.
Ina tsaye kamar statut har ya juya ya fice kana na juya kicin na ɗauko na Momy na nufi sashenta dan na kai mata dan na santa da son course-couse,ana kiran sallar isha na ji dawowarsu.
Bayan mun gaisa da Mommy tace.
"Ai da ba ki dawo ba,niyata dama gobe naje na taho da ke,ga me gyaran jiki tun tuni ta iso babu amarya,kuma gobe nake saka ran dawowar Abbanki."
Murmushi kawai nayi na sunkui da Kai ƙasa musamman da Mommy tasa Nasrin ta ɗebo mini katunan ɗaurin auran da Abba yasa aka kawo su ɗazu.
"Kai Mommy ai ba sai na gani ba."
Dariya Mommy tayi kafin tace.
"Kya ware ma,ni a 'ya na ɗauke ki ba sirika ba, ga me gyaran jiki nan ta iso dama bari nayi ku gama yawan jarabawar tukunna, tun da lokaci bazai ƙure ba,ko na sati ɗaya aka yi za'a san anyi bare ma zai fi sati,gobe in Allah ya kai mu za'a kai lefen naki sashen Gwag..."
Ta shi nayi ban bari ta ƙarasa ba nace.
"Mommy ga couse-_couse nan na kawo miki."
Kana na fice da sauri ina jiyo dariyarta,tana.
"Naga yadda za'ayi hidimar bikin 'ya na jin kunyar uwarta
"Ku kallla."Fatma tace da 'yan tawagarta, gaba ɗayansu kuwa suka juya idanuwansu ya sauka akan Sajda,tana taku ɗaiɗai cike da yauƙi da yanga wan da ya zame mata jiki domin kuwa duk in da gayu yake Sajda tasan gayu ta kuma san ta kansa. Abin da ya bawa su Fatma mamaki ba komai ba ne sai yadda Sajda ta samo mayafin da ya mugun shiga da leshin da ke jikinsu gaba ɗaya,anko ne na class mate ɗinsu, sun zaga kasuwanni da dama haɗe da super market suma da dama amma basu samu mayafin da ya mugun shiga da leshin ba kamar yadda na Sajda ya shiga, abin da suke gudu ya faru (Sajda ta fisu ɗaukan wanka) Har ta gifta su ta ankara da yadda suka zuba mata ido kamar su cinyeta ɗanya, basa shiri shiyasa bata shiga shirginsu, su kullum burinsu su fita ɗaukar gayu amman hakan ya gagara saboda ta fisu sanin takan gayun.
"Lafiya dai ko na ci muku bashi?"
" Muna mamakin yadda akai kika samu mayafin da muka gama karaɗe kasuwanni da dama ba mu samu ba."
"Hmm shine matsalarku?"
"Eh"
"To matsalarku tazo ƙarshe in sha Allah zan haɗa ku da NEEHAL COLECTION daga yanzu wahalar neman mayafai ƙare muku da yardar Allah, dan nima tun da aka haɗa ni da ita na huta, duk mayafan da ake so ana samu a gurinta ko wani irin kala ne, kuma masu kyau da ɗaukar ido cikin farashi mai sauƙi."
"Au wai kina nufin mayafin na gida ne ?"
"Eh mana ɗan hannu ne."
Amma ta iya mayafai maza maza haɗa mu da ita dan baza mu shiga gurin bikin nan ba sai da irin mayafin ki muma mu ƙure gayu.
https://wa.me/message/AD4MDTQJLXIRD1
Ku bi wannan link ɗin zai kaiku in da zakui magana da NEEHAL COLECTION daga yau matsalar mayafai ta ƙare muku zaku samu duk kalar mayafan da kuke so cikin farashi mai sauƙi ina mai tabbatar muku zaku ji daɗin muamala da ita.
Ga masu bukatar a tallata musu hajarsu kofa a bude take cikin farashi mai sauki.
Washe gari kamar yadda Mommy tace aka kar ɓi lefena a sashen Gwaggo na gani na faɗa wan da dangin Abbana ne da na Gwaggo suka kar ɓa yayin da dangin Mommy suka jagoranci kawowa ciki har da Ummansu Nauwwa,wan da hakan yasa aka tuna da Yaa Muhd aka yi masa addu'a tare da fatan dacewa.
Sati biyu masu zuwa aka tsayar lokacin bikin sa bo da Abbana ma akan hakan ya bugo kati,Yaa Sulaiman da muka yi waya ya na ta mitar ƙarin da aka samu nace.
"Kai da Allah ya taimakeka aka rage bikin a yadda aka saka tun farko ma."
"Hmmmm haka dai kika ce,amman ƙarin sati gudan nan ji nake kamar na shekara."
"Kamar fa yau ne idan mai duka ya kaimu,abu idan aka saka mishi rana an yi me wuyar,fatan kaiwa lokacin kawai ya rage."
"Wannan haka yake Cwtyy,Allah Ubangiji ya bamu aron rayuwar."
"Amin ya Rabbi alamin."
**
Ranar alhamis aka yi bikin yayemu daga makaranta,mun samu kyaututtuka da yabo sosai ni da Nauwwa,Yaa Sulaiman ya samu damar halarta amman sai dai a ranar ya juya bai ɗauki hutun ba sa bo da ganin an ƙara sati a bikin namu,kuma akwai wa'yan da zaiwa aikin ido a ranar, shiyasa daga nan makarantar kawai ya juya ko samun walimar da Abba ya haɗa mana a gida bai yi ba.
A na tashi muka ɗunguma mukai gida baki ɗaya aka yi walimar da Abba ya haɗa mana a cikin gidan namu.
Muna zaune a falon Momy muna hira da yake kowa ya huce gida daga ni sai Nauwwa da ke jiran Najib yazo ɗaukarta sai su Zareenah da zasu kwana a nan kasancewar Mu'azz ɗin ba ya nan.
"Amman dai zaku cigaba a karatun naku?"
Cewar Zarina tana kallonmu.
"Me kika gani?"
Na mayar mata da tambayar nima.
"Kawai dai."
"Burina ne zama nurse ina ganin hakan ya ishe ni rayuwa."
"Ke fa?
Ta tambayi Nauwwa.
"Nima dai kam hakan ya wadatar da ni."
"Amman so samu ku ɗora karatun na ku yadda zaku samu zurfaffan ilimi, kinga ni I'm Gynic Doctor kuma yanzu ina karatun busseness,na cika nawa burin yanzu kuma ina kan cika na mahaifina saboda sanin kan kasuwanci da harkokinsa."
"A na cewa ba'a haɗa taura biyu a baki yau na ga wacce ta haɗa kuma suka taunu cikin ruwan sanyi,gaskiya dai kam kin yi ƙoƙari."
"A'a Nauwwara ba dai cikin ruwan sanyi ba akwai wahala sai ka jajirce, nikam har wani abu daga ɓangaren jikina na sadaukarwa da karatu..."
Maganarta ce ta tsaya saboda shigowarsa cikin falon da muke zaune idonta ya sauka a kan sa,ta shi ta yi ta nufo shi da sassarfa saboda ganinsa a bazata,kwanansa uku ba ya nan sunje Fanda da Daddynsu,tayi kewarsa sosai da sosai.
Jikinsa ta faɗa haɗe da mishi kyakkyawar runguma.
"Bei kai ne? Me yasa ba ka gaya mini yau zaka dawo ba?"
"Tun da dai gani gabanki komai ya huce Zareeenah."
Ya faɗa yana zameta daga jikinsa ya zauna kan kushin yana lumshe gajiyayyun idanuwansa.
Ina ganin abin da yasa maganarta tsayawa na jaa hannun Nauwwa dan mu bar falon don zuciyata har ta fara dokawa da wani irin sauri-sauri,amman ta kafe ba in da zata je,rintse idanuwana na yi da naga shigewar Zarena jikinsa ina jin wani mugun ɗaci a maƙo gwarona, hanyar barin sashin gaba ɗaya na nufa idona har wani yaji-yaji yake ko na uwar me ye oho masa.
"Yunwa nake ji."
Ya faɗa a wahalce yana kuma lumshe idanuwansa.
Zareena ce tace
"Mu ƙarasa dining ɗin ko nasa a sauke abincin a nan?"
Bai bata amsa ba sai kiran sunana da yayi cikin accent ɗin muryarsa da naji duk faɗin duniya ba wanda ya iya kiran sunana kamar haka irinsa,a lokacin ina gab da ficewa daga falon.
"Naajjjj"
Ɗan dakatawa nayi zuciyata na ƙara bugun da take,kafin na saka hannu zan murɗa handle ɗin ƙofar na fice na ji Zarenah na cewa. "Najjwa kiran ki yake fa."
Juyowa na yi,abin da dai nake gudu idona ya sauka akan farar kyakkyawar fuskarsa,rintse idanuwana nayi ina jin yadda yau ɗin yayi mini kyau fiye da ko yaushe.
"Ki bani coffee pls na sha ko zan samu hanjina ya warware."
Ya faɗi hakan yana mayar da bakinsa ya rufe tamkar ba shi ya yi maganar ba,ba tare kuma da ya dube ni ba.
Tahowa nayi kamar zan nufi hanyar kicin sai kuma na ɗauke hanya na nufi ɗakina ina jin wani kuka na taho mini wan da ban san na me ye ba,koma dai me ye ya na da nasaba da yadda na ga Zareenah zaune akan cinyarsa ta na masa magana ƙasa-ƙasa.
Wara idanuwansa yayi yana kallon in da ta shiga, miƙewa yayi tare da cire Zareena daga jikinsa. "Bei ka bari na saka Zainaba ta haɗa maka."
Bai ce da ita komai ba ya nufi ɗakin da ya ga Najjwan ta shiga, yayin da Zarenah za ta bi bayan shi Nauwwara ta danƙo hannunta.