kan kujerar mudubi tana haɗiyar magani a daidai lokacin kuma Mu'azz ya turo ƙofar ya shigo babu damar ɓoyewa domin kuwa idonsa akan serchet ɗin msganin ya sauka.
Direct gurinta ya nufa yana ƙanƙance idanuwansa a kanta yayin da ƙirjinta ya bada wani irin bugu na tsoro da taraddadin yadda zai karɓi al'amarin.
Wata iriyar wawuyar runguma yayi mata yana shinshinar dokin wuyanta,lumshe idanuwanta tayi haɗe da sauke wata wawiyar ajiyar zuciya.
Bakinsa ya kai saitin nata yana son haɗe bakinsu guri ɗaya ta kautar da kanta,abin da ta kasa sabawa da shi,sam ba ta son shi yayin da ta fuskanci shi kuma abin da yafi ƙauna kenan zai iya ɗaukar lokuta masu yawa yana kissing ɗin bakita ba tare da ya gaji ba.
"Plsssss."
Yace da ita yana lumshe buƙatattun idanuwansa, haka ta miƙa masa bakin nata amman Allah na gani ita ba so take ba, yayi ta wani tsotse mata baki,dan ba da abin da take taya shi, shi kaɗai yake bidirinsa.
Bayan ya samu nutsuwa ta kira sunansa.
"Beii"
"Uhmmm"
Ya faɗa yana kuma shigewa jikinta tasan kaɗan daga aikinsa ya kuma takalo wani zancen ita kam har ga Allah ta gaji wallahi.
"Ba kace komai ba"
"Game da me fa?"
"Maganin da ka ganni ina sha, ina tsoron haihuwa Bei,in fact ma nayi ƙanƙanta da haihuwa,kuma ina son bawa karatuna muhimmanci."
"Shike nan tun da haka kika zaɓa."
Ya faɗa tun da shima yaran ba damunsa suka yi ba, shima kuma a ganinsa yayi ƙanƙanta da fara tara iyali.
"Mi kike son karanta ne?"
"Ina son zama likitar mata, Abei kuma bussenes yake so na karanta, so sai nace masa zan fara nawa karatun idan na gama shi ma harkar bussenes ɗin zan karanta kaga na cika mana burukanmu gaba ɗaya."
Jinjina mata kai yayi yana kuma shigewa jikinta.
Washe gari jirginsu ya ɗaga sai Saudiyya in da ta fara karatunta na ghynic dama kafin su koma Abei ya gama mata komai, ta fara karatunta cike da nasara a gefe guda kuma suna zuba soyayyarsu da Mu'azz babu ruwansu da wata aba kunya a gaban kowa zasu iya rungume juna ba wani abu ne a gurinsu ba,rayuwarsu suke cikin sakewa in da shekaru suka miƙa suna lulawa har zuwa san da ta gama karatunta cike da nasara,kana kuma ta juya tana karantar bussiness wanda shekaru uku kaɗai zasu ɗauketa ta kammala shi sai kwasa kwasai da zata je yowa a kuma tsukun ne planning ɗin da take ko wanne ya ƙi karɓarta shine kawai tayi shawarar cire mahaifar gaba ɗaya,dan sam ba ta sha'awar haihuwa, ga wahala ga kuma rainon yara shima wahala, kuma duk su wani bi su tsotse maka nono ya taɓile musamman ita da ƙirjinta ba a cike yake ba.
Kuma ta ga shima El ɗin yaran ba damunsa suka yi ba shiyasa tace masa kawai zata cire mahaifarta amman kafin nan yayi mata alƙawarin bazai mata kishiya ba, to shi kam ta ya ma za'a yi yayi wasu mata biyu?ba da shi ba ɗayar ma yayi ne saboda sauke buƙatar sa to kuma akan me zai nemi ƙari?
Dan haka kansa tsaye yayi mata alƙawarin bazai mata kishiya ba,amman fa shi bai ce ta cire mahaifa ba bai kuma ce kar ta cire ba duk abin da ta zabawa kanta shike nan .
Yayin da tayi shawara da Abei in da ya nuna mata goyan bayansa dan shima a ganinsa rashin haihuwar zai taimaka gurin zurfafa iliminta, ta ƙi gayawa Ammi dan ta san baza ta taɓa goya mata baya ba, ita kam har ga Allah tsoron haihuwa take musamman da ta gani ƙuru ƙuru yadda mata ke shan wahala da azaba iri iri ita kam ba da ita ba,daga nesa dai yaran na bata sha'awa amman ba ta taɓa jin sha"awar ta haifa da kanta ba....
Ku kallla."Fatma tace da 'yan tawagarta, gaba ɗayansu kuwa suka juya idanuwansu ya sauka akan Sajda,tana taku ɗaiɗai cike da yauƙi da yanga wan da ya zame mata jiki domin kuwa duk in da gayu yake Sajda tasan gayu ta kuma san ta kansa. Abin da ya bawa su Fatma mamaki ba komai ba ne sai yadda Sajda ta samo mayafin da ya mugun shiga da leshin da ke jikinsu gaba ɗaya,anko ne na class mate ɗinsu, sun zaga kasuwanni da dama haɗe da super market suma da dama amma basu samu mayafin da ya mugun shiga da leshin ba kamar yadda na Sajda ya shiga, abin da suke gudu ya faru (Sajda ta fisu ɗaukan wanka) Har ta gifta su ta ankara da yadda suka zuba mata ido kamar su cinyeta ɗanya, basa shiri shiyasa bata shiga shirginsu, su kullum burinsu su fita ɗaukar gayu amman hakan ya gagara saboda ta fisu sanin takan gayun.
"Lafiya dai ko na ci muku bashi?"
" Muna mamakin yadda akai kika samu mayafin da muka gama karaɗe kasuwanni da dama ba mu samu ba."
"Hmm shine matsalarku?"
"Eh"
"To matsalarku tazo ƙarshe in sha Allah zan haɗa ku da NEEHAL COLECTION daga yanzu wahalar neman mayafai ƙare muku da yardar Allah, dan nima tun da aka haɗa ni da ita na huta, duk mayafan da ake so ana samu a gurinta ko wani irin kala ne, kuma masu kyau da ɗaukar ido cikin farashi mai sauƙi."
"Au wai kina nufin mayafin na gida ne ?"
"Eh mana ɗan hannu ne."
Amma ta iya mayafai maza maza haɗa mu da ita dan baza mu shiga gurin bikin nan ba sai da irin mayafin ki muma mu ƙure gayu.
https://wa.me/message/AD4MDTQJLXIRD1
Ku bi wannan link ɗin zai kaiku in da zakui magana da NEEHAL COLECTION daga yau matsalar mayafai ta ƙare muku zaku samu duk kalar mayafan da kuke so cikin farashi mai sauƙi ina mai tabbatar muku zaku ji daɗin muamala da ita.
Ga masu bukatar a tallata musu hajarsu kofa a bude take cikin farashi mai sauki.
#09037093702/08082007142
#BR
[10/7, 12:24] RASHUNA: BEBEE'ARTH
Wattpad@Rashuna
KANA NAKA
(Allah na nasa )
22
NAJJWA
Shiryawa nake a gaggauce zamu je ɗauko su Yaa Sulaiman a filin jirgi ni da Nassrin da Daddynsu ya haƙura ta dawo hannun Mommy da zama,dan ba ta kwana biyar ba ta zo gurin Mommy ba,kuma bazai iya hana ta ba,shiyasa da yahon da take yace gara ta komo gurin Mommyn tun da mace da yahon gida biyu akwai illar tarbiya a ciki,duk da dai har da zigar Safiya ma a barin nata,dan Nassrin ɗin na gab da ɓaro mata aiki a ɗan zaman da suka yi tare.
Maimakon wata gudan da yace zai yi sai da
ya ƙara sati biyu a kai,bayan transfer tasa tuni ta iso,amman mai makon kano Abuja suka tura shi.
Sai daga baya taji a bakin Momy ya tsaya ne su taho tare da Mu'azz,matar Mu'azz ɗin ake jira ta ƙara warwarewa saboda tayi fama da rashin lafiya.
Tu ni dama na gama yi musu abun tarɓarsu yanzu sauri muke mu isa filin jirgin kafin jirginsu ya sauka.
Kamar haɗin baki ni da Nasrin dogayen riguna muka saka,tata black ce tawa kuma blue black da tayi masifar yi mini kyau ta ƙara fito da hasken fatata.
Na ɗauki Neehal ta ɗauki Nimra da na shirya su cikin wata arniyar doguwar riga me siririn hannu pink iri ɗaya sak babu abin da ya bam bamta su, amman sai da na saka musu over roll fara ƙal a ciki kafin na saka musu rigar a kai.
Sun yi kyau gwanin sha'awa kamar ka ƙwace su ka zura da gudu, mu kaiwa Momy sallama itama tana ta murna yau zata ga zaratan samarin nata su biyu a gabanta.
Ba mu daɗe da zuwa ba jirginsu kuwa ya sauka, bayan daidaitar komai suka nufo gurin da muke a tsaye, Yaa Sulaiman ne a gaba muna sakarwa juna murmushi, daga bayansa kuma wasu couples ne da sukai matuƙar dacewa da juna, kayan jikinsu ma shigen iri ɗaya blue da ya ƙara fito da hasken fatarsu tana ta shaiƙi da ɗaukar ido,daga bayansu kuma wata matashiyar budurwa ce janye da trolynsu.
Yaa Sulaiman na ƙarasowa gabana ya miƙa hannu ya karɓi Neehal yana cillata sama yana dariya kafin yace.
"Masha Allah, sun ƙara wayo."
"Aikam dai,wayo a cikinsu har da na siyarwa, barka da isowa,fatan kun sauka lafiya."
Ɗage mini gira ɗaya yayi kana yace.
"Idonki bai gane miki ba, kewarki ce kawai so samu na rungume ki amman babu dama."
Murmushi nayi ina juyar da kaina gefe.
Nasrin kwa da gudu ta nufi El Mu'azz ta rungume shi cike da kewarsa, shima rungume ƙanwar tasa yayi yana sauke idonsa kan yarinyar da ke hannunta, bayan ta sake shi ta rungume Zarina itama, kana Zareenan ta amshi Nimra da ke hannun Nasrin cike da sha'awa suka tako zuwa in da muke tsaye a jikin mota.
"Najj ga Bro da matarsa Zareenah. ku kuma ga Najjwa wife to be in sha Allah."
Ɗago kaina nayi idona ya sauka a kansa bansan dalili ba na ji gabana ya yanke ya faɗi, wallahi ban da nasan ƙanin Yaa Sulaiman ne ba ta yadda za'a yi na yadda wai wannan Yaa Sulaiman ya girme shi, dan ya fi ya Sulaiman komai da komai, da dukkan alamu yana ɗaga ƙarfe dan a buɗe yake ko ta ina buɗewa irin ta cikakkun maza ni a fisge ma da Actor ɗin film ɗin india yake mun kama Jhon Abraham.
Murmushi na sakar musu haɗe da faɗin. "Barka da isowa,fatan kun iso lafiya?"
Matar tasa ce Zareena kawai ta amsa mini tana sakar mini murmushi shi kuwa kau da kai yayi gefe,sai naji raina bai mini daɗi ba ni fa a rayuwata ba na son yarfi,shi yasa nake jan mutuncina a ko ina,ƙwafa nayi a raina nace.
"Kayi da 'yar halak."
Ko gefen da yake ban ƙara kalla ba na dubi Yaa Sulaiman nace.
"Zaka ja motar ne ko na jaa?"
Wani kallo ya jefe ni da shi kafin ya zaga ɗaya site ɗin yana.
" Ki ja mu kawai,a gajiye nake."
Cike da tausayawa na dube shi nace.
Sannu kana na buɗe motar na shiga,su ma Nasrin ta buɗe musu bayan motar suka shiga da yake motar da girmanta ko kaɗan ba su takura ba,na tayar da motar a hankula na yi revers na fice daga filin airport ɗin,ina jinsa yayi ƙasa da murya yace.
"So samu ina zuwa ki haɗa mini ruwan wanka ki taya ni muyi tare kana na kwanta ki tayi mini tausa. "
Kautar da kaina nayi, nayi kamar ban ji abin da yace ba,ina kallonsa ta gefen ido yana sakin murmushi mai sauti.
Ko gama daidaita parking ban yi ba El ya buɗe murfin motar ya fice ya hau ƙwallawa Momy kira kamar wani makaho, ko da yake makahon ne tun da baisan ina zai nufa da zai tadda Momyn a ciki ba.
Sai ga Momyn sun fito ita da Gwaggo daga sashen Gwaggon, jin yadda ake raftakawa Momyn kira,duk da ita ta gane muryar ɗan nata.
Idonsa na sauka akan Momyn ya nufo gurinta da sassarfa ya rungumeta.
Bai san yayi mugun kewar mahaifiyar tasa ba sai yanzu, bai san girman kewar ta kai haka ba, shekaru ɗaiɗai har biyar rabon da ya sanyata a idanuwansa a zahiri,sai yau, shekaru biyar kuwa ba wasa ba ce.
"Nayi kewar ki Momy, shine ko ki fito tara ta?"
Ya faɗa yana turo baki gaba.
"Nann tafi can,ni matsa na taryi ɗiyata, ranar da ka fara damuwa da ni na fara fitowa tararka."
"Kai Momy."
Ya faɗa yana turo baki gaba da dira ƙafa a ƙasa kamar wani ƙaramin yaro.
Ita ko Mommy Zareena ta janyo jikinta ta nai mata barka da isowa Nigeria katonta na farko a rayuwa, kafin mu ɗunguma mu shiga sashen su Gwaggo dan su gaisa da Baffa.
Bayan sun gaisa a can muka baro su muka fara yo gaba ni da Yaa Sulaiman zuwa sashen Momy.
Direct dining area muka nufa, na buɗe masa warmer ɗin da na zuba masoyiyarsa a ciki,hannunsa har rawa yake gurin kaiwa ya
ɗauka ya kai ta baki, yana kaiwa baki ya lumshe ido yana taunawa kafin yace.
"Allah ya yi miki albarka." Nace "Amin."
Kana na zuba masa awarar a plate da Ku nun madara sai tiriri yake, yana cikin ci su Mommy suka shigo.
"Najjwa ɗauko kwandon abincin su Mu'azz driver zai ajiye su gida su samu su huta."
Cewar Mommy.
"Tom.". Nace,kafin Yaa Sulaiman yace.
"Ya bari na ƙarasa mu huce tare, Najjwa zata ajiyemu,tun da drivern ba sanin gidan da zai ajiye su El ɗin yayi ba."
Ba tare da ta dubi Ell ɗin ba tace.
"To ka jira ya gama ɗin sai ku wuce. Zarina zo ga guri ki zauna, ya sunan yarinyar taki ne?."
"Zainaba."
"Ok Zainaba kema shigo ki samu guri ki zauna ."
Shi kwa gogan dining ya nufo cikin takunsa na ƙasaita yayin da takun nasa ke tafiya da bugun ƙirjina ban kuma san dalilin hakan ba.
Ta tsakiyarmu ya tsaya haɗe da duƙowa ya sanyo farin kyakkyawan hannunsa mai cike da baƙa wuluk ɗin gargasa da tai kwance luff abunta ya ɗauki awara guda ɗaya ya kai bakinsa haɗe da cewa.
"Duk dai ba'ai mana tayi ba bari mu ci mu ji."
Zagawa yayi ta gefen Yaa Sulaiman ya ja kujera ya zauna kana ya janyo plate ɗin awarar gabansa ya hau ci, tishu Yaa Sulaiman ya zara ya hau goge hannunsa kana ya turawa El mug ɗin kunun madarar.
"A'a ya da haka? Najwa maza zubowa Zareena da Zainaba awarar da kunun, tun da shi ya zame yana ci ya rabu da su."
Momy ce tayi maganar sanin dama ban saka musu awara da kunun madarar cikin kwandon abincinsu ba, yayin da Zareena tace.
"A'a Momy nikam bani ci."
"A'a ki dai ci ki ji,ba kiga mutuminki ya zage yana kwasar daɗi ba."
Ta nuno mata El da ya ɗaga mug ɗin kunun madarar yana sha daɗi yana kai masa ko ta ina.
"Bara naje can mu ci to."
Ta faɗa kanta tsaye ta nufo gurin dining ɗin, ganin haka ni kuma yasa ni zubowa Zainaba na taso na baro gurin dining yayin da Yaa Sulaiman ya biyo bayana.
"Mu fara biyawa ku gaisa da Dad ne?"
Yaa Sulaiman ya jefowa El tambayar, yanzu shi ke jan motar El a gefensa, ni da Nasrin,Zareena,Zainaba muna baya.
"No, zanje na same shi a office dan babu abin da zai kai ni wannan gidan."
"Ok"
Kawai Yaa Sulaiman yace yaci gaba da tafiya.
A daidai wani ƙaton gida naga yayi kwana yayin da garƙameman baƙin gate ɗin ya fara zugewa da kansa kana ya kutsa hancin motar ciki, Innalillahi muna shiga naga wasu haɗaɗɗun mension guda biyu ɗaya daga hagu ɗaya daga dama, na hagun naga ya ɗauki hanya ya bi,shima kafin mu ƙarasa haɗaɗɗen farin gate ɗin ya wangale kansa, ya kutsa hancin motar ciki, a daidai bakin ƙofar da zata sadaka da cikin gidan yayi parkin muka firfito, shi dai Yaa Sulaiman bai fito ba daga nan yacewa El.
"Ba dai ka manta securityn ƙofofin ba?"
Jinjina masa kai yayi ya fara takun nan nasa na ƙasaita su Zareenah suka take masa baya, kallon Nasrin Yaa Sulaiman yayi da ta bi bayansu yace.
"Ke kuma ina zaki bi su?"
"Au Yaa baza mu shiga ciki ba?."
"Uban me zaki shiga ki yi a ciki,ko kwa yau kika fara zuwa gidan?"
Sai kuma ya juyo ya kalle ni yace.
"Ko zaki shiga ciki ki gani ne?"
Girgiza masa kai nayi,fuska ba wasa ya kalli Nasrin yace.
"Zo ki shige mota mu wuce."
Sai da muka fito yace.
"Ko mu shiga naki site ɗin da za'a kawo ki ki gani?"
Nan ma na girgiza masa kai .
"To wai rowar muryar kike mini ne?"
Dariya nayi kafin nace.
"Ana rowar murya ne dama?"
"Ana yi mana,gashinan kuwa kina mini."
A bakin gate ɗin gidansu muka tsaya yayi parking ya fito nima na fito na zaga ɗaya site ɗin, Nasrin ta miƙo masa kwandon abincinsa mukai sallama ya shige cike na ja motar muka nufo gida bayan Nasrin ta dawo kujerar gefen me zaman banza....
"Ku kallla."Fatma tace da 'yan tawagarta, gaba ɗayansu kuwa suka juya idanuwansu ya sauka akan Sajda,tana taku ɗaiɗai cike da yauƙi da yanga wan da ya zame mata jiki domin kuwa duk in da gayu yake Sajda tasan gayu ta kuma san ta kansa. Abin da ya bawa su Fatma mamaki ba komai ba ne sai yadda Sajda ta samo mayafin da ya mugun shiga da leshin da ke jikinsu gaba ɗaya,anko ne na class mate ɗinsu, sun zaga kasuwanni da dama haɗe da super market suma da dama amma basu samu mayafin da ya mugun shiga da leshin ba kamar yadda na Sajda ya shiga, abin da suke gudu ya faru (Sajda ta fisu ɗaukan wanka) Har ta gifta su ta ankara da yadda suka zuba mata ido kamar su cinyeta ɗanya, basa shiri shiyasa bata shiga shirginsu, su kullum burinsu su fita ɗaukar gayu amman hakan ya gagara saboda ta fisu sanin takan gayun.
"Lafiya dai ko na ci muku bashi?"
" Muna mamakin yadda akai kika samu mayafin da muka gama karaɗe kasuwanni da dama ba mu samu ba."
"Hmm shine matsalarku?"
"Eh"
"To matsalarku tazo ƙarshe in sha Allah zan haɗa ku da NEEHAL COLECTION daga yanzu wahalar neman mayafai ƙare muku da yardar Allah, dan nima tun da aka haɗa ni da ita na huta, duk mayafan da ake so ana samu a gurinta ko wani irin kala ne, kuma masu kyau da ɗaukar ido cikin farashi mai sauƙi."
"Au wai kina nufin mayafin na gida ne ?"
"Eh mana ɗan hannu ne."
Amma ta iya mayafai maza maza haɗa mu da ita dan baza mu shiga gurin bikin nan ba sai da irin mayafin ki muma mu ƙure gayu.
https://wa.me/message/AD4MDTQJLXIRD1
Ku bi wannan link ɗin zai kaiku in da zakui magana da NEEHAL COLECTION daga yau matsalar mayafai ta ƙare muku zaku samu duk kalar mayafan da kuke so cikin farashi mai sauƙi ina mai tabbatar muku zaku ji daɗin muamala da ita.