gashi nan ta tafi ta bar mana duniyar tana k'ok'arin raba tsakaninmu ita sai Allah ya rabata da nata numfashin kuma babu yadda za ta yi babu yadda zata iya komai sai da amincewarsa sai da yardarsa yake faruwa baka isa ka canja faruwar komai ba.
(Me yafi wannan asara cikin rayuwa Ka mutu kana aikata shirka, bayan baro warka gurin mushirikin?Allah da kansa yace ba ya yafe laifin shirka idan har baka tuba ba,idan kaje gurin boka sai kayi kwana arbain sallar ka ba ta karb'u ba,kana da tabbacin zaka mayar da asarar wannan sallar da kayi?ko kwa kana da tabbacin zaka wuce kwanaki arbain din ba tare da ka amsa kiran mahaliccinka ba? Wannan tambayoyin ya kamata ka fara yiwa kanka yayin da shaid'aniyar zuciyarka ta kwadaita maka zuwa gurin boka,ka kuma nemo amsoshinsu wanda bai wuce baka da tabbacin domin kuwa ba ka san me gobe ta tanadar maka ba,Allah ne kawai ya barwa kansa sani to sai ka sakawa ranka babu wani k'ato ko gardi da zai iya yi maka abin da Allah bai maka ba domin kuwa shima yadda aka baka aron numfashi da rayuwa haka aka bashi,yadda ake sarrafa taka rayuwar shima haka ake sarrafa tasa,duk wani abu da zai faru to dama can haka yake a rubuce "An d'auke alk'aluma kuma takaddun sun bushe." Allah ka kiyashemu kasa mu dace Amin. )
Abba sai fasa tafiyar da yayi niya ya yi ya dawo a ranar akaiwa Mama sutura aka kaita aka barota daga ita sai halinta domin kuwa shine kad'ai zai kunceta ya bata salamar kwanciya cikin aminci idan ta aikata daidai(Innalillahi wa inna ilaihir raji'un wallahi ina tunanin wannan ranar.Abun damuwar kuwa baka san ranar da zata riskeka ba sai dai ka bud'i ido ka ganka cikin kabari,halinka na gari shine zai ceceka,Allah ka bamu ikon aikata daidai Amin.)
Sai da daddare da muka yi waya da Abbana yake gayan mutuwar nace."Allah ya jik'anta.
Satinmu d'aya a sierea mun gama zaga dangi gaba d'aya duk in da muka yi Aunty Fati na tare da mu,ita ke fassara mana abin da wasu ke fad'a dan ba iya yaren nasu muka yi ba.Muna da sati biyu da zuwa aka fara gudanar da bikin Aunty Fati,al'adar bikinsu gwanin birgewa.Anyi biki lafiya an gama lafiya gidan Aunty Fati babu nisa da na Aunty Hafsa,kuma da alama mijin Aunty Fati yana da farcen susa.
Kwanci tashi ciki k'udirar Ubangiji har mun cinye wata uku a sierea,daga ni har Nauwa har mun fara koyan yarensu.Gobe muke saka ran tafiya sai shiri muke da yake jirgin da zai tashi da asuba zamu bi,yadda kasan kar na rabu da kakannina suma haka suke ji kamar nayi ta zamana a tare da su haka muka yi sallama da tunanin ko zamu k'ara ganin juna?Domin kuwa Allah shi ya barwa kansa sani bamu da tabbaci,ta cewar Kawu.
"Wai shi yasan rayuwarsa tazo gangara,yamma ta cimmasa daren kawai yake jira." Nace."Babu wanda yasan gawar fari sai Allah k'ila na rigasu yin gaba,k'ila muna da sauran rayuwar mai tsayi gaba d'aya wannan kuma du Allah ne ya barwa kansa sani sai dai muyi fatan Allah k'addara saduwarmu."
Cikin k'oshi lafiya muka sauka k'asarmu,cikin garinmu,mun baro su Inna da kewa.Muna sauka direban da Abba ya aiko ya d'ebemu sai gida muna shiga na d'afe Gwaggo ina murna tace.
"Najwa kar ki k'arasa ni mana dama k'ashi ba k'wari ba duk ya takwar kwashe."
"Kai Gwaggo wata uku cur ba ki kewata ba?"
"Na yi kewarki mana,anman lafiya ai tafi kewar."
Baki na turo gaba,na shige ciki ina k'walla kiran Baffa sai naji Gwaggo tana.
"Bai jima da fita ba."
"Allah sarki Habibina Allah ya dawo mun da shi lafiya amin,nasan ya yi kewata ba kad'an ba."
"Nauwara shigo ta barki tsaye sai zance take."
"Wallahi kuwa Gwaggo."
Sai da muka shiga d'aki kana muka gaisa da Gwaggo tana tambayarmu yadda muka baro su.
"Naj nifa na matsu naga Baba da Ummana."
"To muje na rakaki,anman ke zaki d'au kayanki dan na gaji bazan iya d'auka ba."
"To cewa na yi ki d'aukar mun 'yar rainin hankali."
"Oho dai,kinga ni muje."
Tafiya muke har muka je gidansu ba wanda yace da d'an uwansa uffan,muna shiga da sallama Ummansu da ke tsakar gida ta amsa mana,Nauwa ta fad'a jikinta cike da murna da kewa.
"Ummana sannu da gida,mun sameku lafiya?"
"Lafiya lau Nauwara,ya kuka baro su?"
"Lafiya lau."
Na tsuguna har k'asa na gaisar da Umma na k'ara da.
"Umma su Gwaggo sunce a muku godiya Allah ya bar zumunci."
"Ai babu komai Najwa,ke da Nauwara d'aya nake d'aukar ku saboda k'aunar dake tsakaninku kullum addu'ata kada Allah ya bawa shaid'an damar shiga tsakaninku."
Mukace"Amin"Gaba d'ayanmu.
"Baba baya nan ne?"
Cewar Nauwa,Umma tace.
"Yana ciki ku shiga ku gaisa."
BEBEE'ARTH
Watpad@Rashuna
KANA NAKA2024
[Allah kuma na yin nasa]
(7)
Mun same shi a kishin gid'e da alamun bacci ke d'an fisgarsa,sallamar da muka yi ce ta saka shi bud'e idanunsa tare da amsa mana.
Guri muka samu muka zauna,a tare muka had'a baki gurin gaishe shi ya amsa mana cike da farin-cikin ganinmu yace.
"Kun baro kakannin naku lafiya?"
Nace. "Lafiya lau,kuma,sunce a gaishe ku ai muku godiya,Bafffa da Gwaggo ma sunce a k'ara musu godiya Allah yabar zumunci."
"Amin,kice musu ai ba wani abu duk an riga an zama d'aya."
"Tom in sha Allah zan fad'a musu." Daga haka na mik'e na fito na bar Nauwa na hira da mahaifinta,na koma gurin Umma na zauna muna tab'a hira da ita kafin na mik'e na yiwa Umma sallama zan tafi,sai ga Nauwa ta fito.
"Tsaya na rakaki ba dan halinki ba."
"Ki bash shi ba na so,ai ba rok'a na yi ba bare amini ba don halin nawa ba."
Daga haka na doshi hanyar fita,tayi saurin janyo mayafina.
"Umma jiye mini wannan maganar;ita fa ta fara tsokanata shine har zata fini fushi."
"Kinga malama babu ruwan Umma a wannan maganar."
"Aikwa ita ke da ruwa,ruwan ma na maliya."
Umma ce tace."Wai me ke faruwa?yanzu na gama yi muku nasihar kar ku bawa shaid'an damar shiga tsakaninku,ku dinga hak'uri da juna."
Nauwa ce tace.
"Umma ba fa wani abu ne ya faru ba."
Ta zayyana mata abin da ke tsakaninmu,Umma tace.
"To me ye abun fushi anan?"Sai a sannan nai magana nace.
"Umma kinga fa tun da muka taho ta had'e fuska ta sha kunu shi ne nima nasha kunun da yafi nata yawa.Ai a tsakaninmu Ummq babu zancen fushi ko?"
"Eh hakane Najwa.To dai yanzu abu ya huce kar na kuma ji kar na kuma gani."
Nace. "In sha Allah Umma"
Na kalli Nauwa na sakar mata murmushi nace.
"Afuwa 'yar uwa,bazan kuma ba."
Martanin murmishina ta maida min tace.
"'Yar uwa dama ke kika d'au abin da zafi.Muje na raka ki."
"Ba ki gaji ba?"
"Kar ki damu ai mun saba rakiyar kura in ba muyi ba ba ma jin dad'i."
Dariya muka yi a tare na yiwa Umma sallama muka fito.Sai da Nauwa ta rakani har k'ofar gida kana ta juyo,ina shiga na tarar Baffa ya dawo na shige d'akinsa muka gaisa muka d'an tab'a hira kana na shiga d'akin Gwaggo.
"Idan kin yi sallah ga abincinku nan,naga Nauwara ta matsu taje gida shi yasa ban tsaida ta ba."
"Toh Gwaggo idan nayi sallar na kirata a waya tazo mu ci."
Wanka na fara yi nai sallah kana na kira Nauwa a waya tazo mu ci abincin sai cewa ta yi itama yanzu abincin zata ci,bara ta taho da shi sai mu had'u mu ci gaba d'aya.
Satinmu guda da dawowa muka soma zuwa makaranta,dama Abba ya gama mana shirin komai,nan da nan muka fara d'aukar karatu musamman da yake ajin sience muke sosai muka daga da karatu Yaa Muhd yana taimaka mana ta b'angaren lesson d'in da yake mana.Muna sss2 Abba ya tashi yin aure shima saboda matsawar Baffa,sam ba ya son ganinsa babu aure domin kuwa shine cikar mutumtakar mutum.
Ina gidansu Nauwa muna hira,sai muka shiga hirar auren da Abba zai yi,domin jiya Gwaggo ke fad'a mini 'yar uwar su Nauwa Abba zai aura.
"Nauwa ashe 'yar uwarku Abba zai aura?"
"Eh wallahi nima jiya nake ji a bakin Umma wai Mommy Hasiya zai aura."
"Mommy Hasiya dai k'anwar Baba?"
"Eh wallahi ita,kinga zumuncinmu zai k'ara k'arfi,dan nasan gidanku zaki koma nima sai na tattara na biki dama Mommy Hasiya ta gurina ce."
"Sai dai in ke zaki koma,nikam ina gaban Baffa da Gwaggo babu abi da zai saka ni matsawa."
"Kin san dai Mommy Hasiya ba irin Kubrah ba ce,tana da kirki da hak'uri ga son mutane,ba wai ina fad'a miki haka ba ne don tana k'anwar mahaifina."
"Na sani Nauwa,nima ba wai ina gudun kar ta cutar da ni ba ne, kinsan irin k'uncin da takurar da na shiga lokacin Mama,haka ta saka Abba ya kore ni har da cewa ya tsane ni kar ya k'ara ganina a gidansa shine Baffa yace ni da gidan nasa kuwa sai dai bayan ranshi.Kinga kuwa babu ni ba saka ran komawa."
"Gaskiya kam,ai Mama ba ta kyautawa kanta ba,gashi nan Zainab na girbar abin da uwarta ta shuka mata,gashin k'uma matan babanta suke mata ba kad'an ba,ko makaranta ba ta zuwa tun da muka yi juniour candy tana nan tana musu bauta."
"Hmmmm! Nauwa kayi mai kyau ma ya ka k'are bare ka shuka tsiya? Ai kad'an ma ta gani,ba itace me muni gwalo ba sun samu duniya to gashinan itama uwar tata ta tafi in da tawa taje ta barta da shan azaba."
"Wallahi kuwa,ai na rasa ina tunanin mutane ke tafiya?su dinga azabtar da 'ya'yan mijinsu ko tunanin had'uwarsu da Ubangiji ba sa yi,kowa yasan rik'on d'an wani da wani akwai wahala da wuyar sha'ani,anman idan ka kau da kai kayi hak'uri ka tafiyar da shi kamar yadda zaka tafiyar da d'an cikinka sai wannan d'an ya yi maka abin da ba lallai d'an da ka tsuguna ka haifa yai maka ba.Mu saka a ranmu ba lallai sai 'ya'yan da muka tsuguna muka haifane kawai 'ya'ya ba akwai wan da zai zame maka d'a ba tare da ko alak'ar jini kun had'a ba."
"Maganarki gaskiya ce Nauwa ,Allah ka ganar da mu baki d'aya."
"Amin ya Allah.Ai Naj yanzu Abbanmu zai san yayi aure Momy Hasiya mace ce me kirki da hak'uri lafiya suke zaune da mijinta kafin wata shegiya ta shiga tsakaninsu kai wasu matan dai a kallesu kawai zuciyarsu babu Allah a ciki."
"Wallahi kuwa Nauwwa ,to me yasa Annabi yace mata sunfi yawa a wuta? Muna da rauni da tausayi anman sai ki rasa ina na wasu matan ke tafiya?"
"Shaid'an ne ya zare shi mana,mudai fatanmu Allah yasa mu fi k'arfin zuciyarmu."
"Amin.Ina jinki ki bani labarin Mommy Hasiyan."
"Tom shikenan bud'e kunnuwanki ki sha labari.."
Kamar yadda kika sani Mommy Hasiya k'anwar Babanmu ce,uwarsu d'aya ubansu d'aya sun taso cikin kulawar mahaifansu da kuma k'aunar junansu wanda rana d'aya aka yi bikin Babanmu da Momy Hasiya a yadda muka samu labari.
Mijin da ta aura Aliyu Hassan Fanda shahararran mai kud'i wan da suka ga jiya suka ga yau cikin dukiya suke fantamawa,yana matuk'ar son Mommy itama kuma tana son kayanta.
Mommy Hasiya ta riga Ummanmu haihuwa sai a haihuwa ta biyu suka yi tare da Ummanmu,Mommy Hasiya ta haifi EL MU'AZ Ummanmu ta haifi Yaa MUHD, d'anta na fari kuma da ta haifa SULAIMAN.
Ummanmu tun daga haihuwar Yaa Muhd haihuwa ta bud'e mata ita kuma Momy Hasiya ba ta k'ara haihuwa ba sai da suka jera haihuwarmu ni da Nabila,sai dai kuma kafin suna Nabila ta koma.
Daga nan ba ta sake haihuwa ba sai akan Nasrin a lokacin su Yaa Sulaiman sun gama juniour school har da El Mu'az da yake gab'b'an girma gare shi sai suka tashi kusan tare da Yaa Sulaiman duk da tsiran shekaru kusan uku dake tsakaninsu,tun gama school nasu Daddynsu yake musu shirye shiryen tafiya Jiddah domin yin seneour school d'insu a can,bayan sun kammala su d'ora ba tare da sun waiwayi gida ba sai da shaidar kwalinsu na kammala karatu gaba d'aya,in yaso su Mommyn zasu dinga ziyartarsu akai akai.
Wata d'aya kafin tafiyarsu suka je Fanda zaga dangi,wanda nima na samu zuwa a lokacin nazo hutu gidan,Fanda akwai dad'i sosai domin kuwa mun yawata mun zaga sosai da Yaa Sulaiman dan yafi Yaa El kirki shi halinsu d'aya da Yaa Muhd na kicin kicin da rai kawa hadarin kaji.
Sati d'aya da dawo warsu jirginsu ya d'aga zuwa k'asa mai tsarki,Daddy ne yayi musu rakiya Mommy saboda jego ba ta samu damar zuwa ba anma ta musu alk'awarin zuwa da zarar ta yaye Nasrin.
Nasrin na da shekara biyar gidan Mommy Hasiya ya fara rikicewa sakamakon Safiya da ta kutso cikin rayuwarsu.
Tun da ta k'yalla ido taga fulanin Fanda jajir da shi wanda ya tashi cikin hutu da jin dad'i kai ba ka ce shine ya haifi zaratan samarin da ke Jiddah ba ,zuciyarta ta katsa nutsuwa bare risinawa har sai da tasan yadda ta yi ta mallaki wannan card'ed'an magidancin.
Safiya kyakkyawar zankad'ed'iyar budurwa ce anman kaish!ta b'ata rayuwarta da shaye-shaye saboda tashin rayuwarta da tayi a sangarce,komai idan tayi daidai ne gurin mahaifanta dake matuk'ar so da k'aunarta.
Tun da tayi tozali da Ali Fanda ta kasa sakat har sai da ta samu mahaifinta ta gaya masa domin kuwa ta in da aka hau ta nan ake sauka,tun da tare ta gansu da Abban nata.Matuk'ar farin-ciki Abban nata ya shigesa domin kuwa duk wan da ya nuna yana son Safiya kai tsaye zata nuna ba ta sonshi ba ta ra'ayi har yau da take da shekaru talatin a duniya dan haka baiyi k'asa a guiwar samun Ali Fanda ba wanda kai tsaye ya nuna ba ya ra'ayin auren mata biyu matarsa ta gida ta ishe shi ya kuma bawa Abban nata hak'uri.
Ina wuta?Safiya ta jefa kanta da jin sak'on Ali Fanda a bakin mahaifinta ta shiga k'unci da damuwa wanda ta lashi takobin mallakar Ali Fanda ita kad'ai ta gidan da yake ikirarin ta ishe sa sai ta bar mata shi.
Ta shiga bin bokaye da malamai har sai da ta siye zuciyar Daddy da kud'i mai tsada yaji duk duniya ba macen da yake so da k'auna sai ita,ana wannan halin har yakai kud'i aka saka rana ba tare da Mommy ta sani ba sai dai kuma taga canji da sauye sauyen halaye a gurinsa.
Tana zaune a falo Daddy yayi sallama ya shigo ta amsa, nan ma'aikatan gidan suka shiga jere akwatuna har sai da suka jere guda talatin da shida,ita dai Mommy mamaki ne ya daskarar da ita a zaune sai bin masu shigo da akwatunan take da kallo bayan sun gama sun fita kuma ta mayar da kallon nata kan Daddy na kai nake jira kamun bayani daga ina wannan akwatunan suka fito?
"Ba na son wani tashin hankali,aure zan k'ara,akwatuna goma sha biyu naki ne,ashirin da hud'u na amarya ne gobe su Yaya Ladi zasu zo daga Fanda za'a je a kai."
Yana kawowa nan ya tashi zai bar falon don ko ido yak'i yadda su had'a da ita yana gab da shigewa yaji muryarta tana.
"Abbansu nifa ban fahimci inda maganarka ta dosa ba"
Ko juyowa bai yi ba daga haka ya bata amsa.
"Aure nace zan k'ara Hasiya,gobe su Yaya Ladi zasu zo sukai lefe."
Daga haka yayi shigewarsa ciki.
Wani k'ululun bak'in ciki ne ya tokare a wuyan Mommy yak'i gaba yak'i baya.
Ba kishin da aka san ko wace mace da shi ba,rashin daraja da mutumcin da har aka kai kud'i aka saka rana sai ana ya gobe za'a kai lefe yake gaya mata zai k'ara aure wannan abu yafi komai yi mata ciwo,ciwon da baza ta iya misalta shi ba.
Tun daga wannan ranar komai ya kuma rikice mata,ko kad'an ta kasa gane kan Daddy har zuwa shigowar Safiya cikin gidan daga nan komai ya kuma rincab'ewa domin kuwa Safiya kissa da kisisina take zubawa a cikin gidan tana juya akalar Daddy yadda ta so.
Mommy ta shak'i bak'in cikin Daddy da Safiya yadda ba kya zato,domin kuwa Safiya ta lashi takobin sai Mommy ta bar mata gidan Ali Fanda ta yi yadda take so da shi,aikwa ba ta huta ba har sai da Mommy ta bar mata wannan gidan a wata rana da Nasrin ta dawo daga makaranta uniforme d'inta kawai ta cire ta nufi sashen Safiya gurin Daddynta dan tasan a can ne kawai zata same shi,motarsa da ta gani da direbansa a parking space ya bata tabbacin yana cikin gidan,sai dai kuma ta tarar ba ya gurin Safiyan ya fita masallaci har zata fito Safiya ta janyota ta buga mata takarar kar ta k'ara ganin k'afafuwanta sun zo gurin Daddyn in ba haka ba sai ta cire mata k'afafuwan ta zama gurguwa ba ta k'yaleta ba sai da ta rarrank'washe mata kai Nasrin taje gurin Mommy tana kuka riris ta zayyana mata abin da Safiyan ta yi mata,Mommy ba tace komai ba ta kama Nasrin d'in ta rarrasheta can sai ga Safiyan ta shigo.
"Ai na zata zuwa kika yi ki gayawa uwar taki tazo ta rama miki."
Mommy ko d'aga kai ta kalleta ba tayi ba,sai Nasrin ce cikin k'un k'uni tace.
"Ba dai uwata ba."
Ita Mommy ko lura da kunkunin Nasrin d'in ba tayi ba sai Safiyan ce ta gani aikwa ta harzuk'a ta kama Nasrin tana kila kamar an aikota sai da Mommy taga dukan ya wuce na hakali kana ta janye Nasrin d'in.
"Ba fa tsoranki nake ji ba,duk guguwar da kike ji da...."
Mommy ba ta k'arasa abin da zata ce ba taji saukar mari a kuncinta kafin hannun Safiya yakai k'asa Mommy ta sauke mata nata marukan har uku wanda yayi daidai da shigowar Daddy shine kuma yayi sanadiyar mutuwar auren Mommy nan take.
Gurinsa Safiya tana kukan munafunci ta had'a mishi k'arya da gaskiya wacce ya hau ya zauna a kai babu tambayar ba'asi ya wanke fuskar Mommy da maruka har uku.
Safiya ta tsaya kai da fata sai Daddy ya zab'a ko ita ko Mommy in ba haka ba ta bar gidan dan baza ta zauna wataran Mommy ta kasheta ba tun da aka fara da duka.
Haka Daddy ya yiwa Momy saki d'aya a take a gurin ko awa Mommy ba ta k'ara a cikin gidan ba ta barshi cikin k'unar rai da bak'in ciki....