masu bukatar a tallata musu hajarsu kofa a bude take cikin farashi mai sauki.
#09037093702/08082007142
#BR
[10/9, 17:16] RASHUNA: BEBEE'ARTH
Wattpad@Rashuna
KANA NAKA
(Allah na nasa )
23
Kwanan Yaa Sulaiman huɗu da dawowa ya kama ranar Sunday kenan,na kai shi filin jirgi ya wuce Abuja dan washe gari Monday ya fara ziyartar asibitin da aka tura shi, yana ta mitar dama anyi bikinmu kawai ɗaukata zai yi mu tafi tare a haka dai na lallaɓa shi ya wuce yana kuma jadda dan ranar friday zai dawo dan anan zai dinga weak end kafin kuma ayi bikinmu mu tattara mu koma can da zama.
Ina dawowa na nufi sashin Momy dan nace mata na dawo, ina murɗa handle ɗin ƙofar na ji ƙirjina ya bada wani irin bugu,ji nayi kamar na juya bayan na hango bayansa amman mun riga da mun haɗa ido da Mommy dan haka na maze na shigo da sallama.
"Yauwa Najjwa zo ki haɗawa Mu'azz abinci wannan takwarar taki ta ishe ni da rigima ga Nimra can sarkin haƙuri tana ta bacci abinta."
Kallon gefen da yake a zaune nayi kansa a ƙasa yana danna waya kamar baisan da wanzuwata a gurin ba,na ƙara jin haushinsa ya mamaye zuciyata, dan dama tun ranar farko da ya ƙi amsa gaisuwata ban ƙara kallon in da yake ba.
A raina nace.
"To wai shi matarsa ba ta mishi girki ne?kullum safe rana dare tare da su nake girki gashi tun ranar da suka dawo ya sha kunun madarar nan kullum da safe sai nayi mishi banda coffe ɗinsa na ƙa'ida kullum da daddare sai na dafa mishi,ko yazo ya ɗauka ko driver da Nasrin su kai musu."
Murmushi nayi nace.
"Kai Momy,ai duk wani mai haƙuri ya biyo bayan takwara, ni take nema yanzu ina goye ta itama zata hau bacci."
"Ba wani nan,wannan rigimammiyar har goyata nayi ɗin amman fir ta ƙi bacci."
Ta kai ƙarshen maganar ta na dungurewa Neehal kai.
"Nawa goyen take so,bara na haɗa abincin na goyata ki gani."
Ina kawowa nan na juya zan nufi kichen sai jin muryarsa nayi yace.
"Ke ba ki iya gaisuwa ba ne?"
Yi nayi kamar ban ji me yace ba,na ci gaba da tafiyata sai da Momy tace.
"Najjwa ba ki gaishe da yayan naki ba."
Juyowa nayi na kalli Momyn kafin nace.
"To ai Momy shine idan an gaishe shi ba ya amsawa, ina fa ganin yadda yakewa su Zuwaire,kuma nima ranar da suka zo da nai musu sannu da zuwa ko kallon in da nake bai yi ba shiyasa na kama kaina dan bana son yarfi, abin da ma ni ya kamata ya dinga gaisarwa tun da naga Yayansa zan aura."
Wata shegiyar tsawa ya daka mini, yana zare mini idanuwansa masu cike da ilhama yace.
"Uban waye zai gaishe ki?"
"Kai mana."
Na bashi amsa kai tsaye ina turo baki gaba.
"Ki mayar da bakin nan,in ba haka ba wallahi yanzu zan gurje shi,dan ni ba na ɗaukar raini."
"Aikam da anyi 'yar gurje gurje wallahi, kuma dai dole ace da mijin Iya Baba a to."
Ina kawo nan na juya na ci gaba da tafiyata zuwa kichen yayin da ya tashi a matuƙar harzuƙe ya biyo bayana, Momy na kiransa ko waigowa bai yi ba.
Jin takun tafiyarsa a bayana yasa ni juyowa a matuƙar tsorace,ina ja da baya yana biyo ni har na jingina da durowar kitchen idona cikin nasa wan da ke cike da tsoron abin da zai mini,ƙafarsa yasa akan tawa ya murje mini kafin yace.
"Bari na murje miki bakin in yaso sai ayi 'yar murje murjen."
Yana kawowa nan ya saka hannu ya kama leɓena na ƙasa ya matse shi,sai da ya tabbatar ya matsu kafin ya murje shi da hannunsa ya saki, ni kam rintse idanuwana nayi cike da azaba ina hana su zubar da hawaye.
Fuskarsa ya kawo saitin tawa yayin da zuciyata ta hau buga tsalle a ƙirjina,jikina ya hau kyarma sai ji nayi ya tsotsi leɓen nawa kafin kuma ya gartsa mini cizon da azabarsa ta ratsa ƙwaƙwal wata.
"A'a Mu'azz meye haka,wannan wani irin iskanci ne kuma?"
Jaa da baya yayi,ya juya ya bar kichen ɗin yayin da na durƙu she a gurin cike da takaici na hau kuka da faɗin.
"Wallah bazan yafe ba, mugu kawai, kuma abincin ma baza' a haɗa ba, kaje koɗaɗɗiyar matarka ta girka maka."
Daga haka na hau gunjin kuka, Momy ta ƙaraso gurin da nake ta ɗago ni haɗe da faɗin.
"Me ya yi miki?"
"Momy kinga fa leɓena sai raɗaɗi yake mini."
Kallon leɓen nawa tayi da yayi jajir ya ɗan tasa kana tace.
"Ayya sannu,bai kyauta ba,zai dawo ya sameni ne,taso ki bar ɓata hawayen ki a kansa."
Daga haka ta kamo ni muka fito daga kichen ɗin.
EL MU'AZZ
Da sassarfa ya fito daga cikin gidan ya faɗa mota ya ja ta da gudun gaske ya nufi gidansa, a falo ya samu Zareenah na aiki a laptop ɗinta, kallonsa tayi ba tare da gane yanayin da yake ciki ba tace.
"Ina Abincinn Bei,yunwa nake ji sosai fa?."
"Zainaba ta dafa miki."
Ya faɗa yana nufar ɗan coridon da zai sada shi da ɗakinsa.
"Wallahi Bei a kwana huɗun nan na saba da cin dishes ɗin gidan Momy,ko Zainaba ta dafa ba lallai na ji daɗinsa ba."
"Ok, kuje driver ya ajiyeku,da daddare nazo mu tafi."
"Ok"
Tace kafin ta hau kiran Zainaba da 'yar siririyar muryarta, sai ga Zainaban ta fito da 'yar sassarfa,kayan da ke gabanta ta nuna mata.
Yana shiga ɗaki jikin mirro ya tsaya yana kallon fuskarsa ta ciki, hannu yasa ya wargaza kyakkyawar baƙa wuluk ɗin sumarsa yana rintse kyawawan idanuwansa.
Idanuwanta kawai yake gani da suka cika da tsoro suka bada wani kalar kyau suna shaiki cikin nasa idanuwan,kuma rintse idanuwansa yayi yana tuno sulɓi da laushin leɓanta, da kuma ƙamshin bakinta da na jikinta da suka dunga zirarawa cikin hancinsa suna fitinar jikinsa.
"To ma me ya kai shi?"
Bai sani ba itace amsar ko da za'a taru ana yankan naman jikinsa,kawai dai ya san itace ta jaho duk abin da ya faru.
Cikin toilet ya faɗa yana buga ƙofar toilet ɗin da mugun ƙarfi kamar ita tai masa laifin, bayan ba ita ta kar zomon ba rataya aka bata.
Yana fitowa daga wankan Daddy ya kira shi a waya.
Yana ɗagawa Daddy ya isar da saƙonsa kai tsaye.
"Kazo gida ina nemanka."
"Daddyyyy"
"Umarnina ne,idan ka isa ka ƙetaresa IBRAHIM ka ji."
Daga haka ya kashe wayar.
Rintse idanuwansa yayi yana jin yadda Daddyn ya ƙara masa wata damuwar.
Sai da ya tsaya a masallacin jikin gidansa yayi sallar magariba, kana ya nufi gidan Daddyn fuskarsa a matuƙar ɗaure, a harabar gidan ya tsaya ya kira wayar Daddyn ya sanar masa gashi yazo yace ya shigo suna falo suna jiransa.
Da takun nan nasa na ƙasaita ya kutsa kai cikin gidan.
A falo ɗin kuwa ya samu Daddyn shi da Safiyya, Daddyn kawai ya kalla bayan ya nemi guri ya zauna yace.
"Daddy mun yini lafiya?"
"Lafiya lau Mu'azz, dama Auntynka ce tace na gayyato ka yau kai dinner da mu, tun da kazo ba ta ganka ba sai iyalinka da tazo mana kawai."
Daddy yakai ƙarshen maganar yana nuna Safiya da ke gefensa tana sakin murmushi, tun da ta lura Daddyn duk cikin 'ya'yansa yafi ƙaunar Mu'azz ɗin itama take nuna fake ɗin ƙaunarsa.
Wani mugun kallo Mu'azz ya wurga mata da yasa nan take ta sha jinin jikinta, bakinta ya hau motsi ba tare da tasan abin da zata ce ba.
Mayar da kallonsa yayi kan Daddy kafin yace.
"Shi kenan dama kiran?"
"Ehh"
Daddy ya bashi amsa."
"Ok, sai ince Allah ya tashe mu lafiya."
Ya faɗi hakan yana miƙewa tsaye.
"A'a me kake nufi,baza ka ci abincin ba kenan."
"Ai daga ranar da Mommy ta bar gidan nan,daga ranar abincin gidan nan ya haramta a gare ni."
Yakai ƙarshen maganar yana jin ɗacin rabuwar Mommy da Daddyn a maƙo gwaronsa kamar yanzu hakan ya faru.
Shi kwa Daddy takaici ne ya hana shi magana har Mu'azz ɗin ya ɓacewa ganinsa yayin da Safiya ta saka kukan kissar Mu'azz ɗin bai kyauta mata ba duk wahalar da ta sha gurin ƙawata masa girki amman ya baɗa mata ƙasa a ido.
Cikin sanyin jiki Daddy yace mata.
"Ni ma fa yanzu na fara jin kamar ban kyautawa yaran nan ba da na rabu da mahaifiyarsu,kamar kuma hakan ƙara nesanta ni da su yayi musamman yanzu da dukkaninsu suka waiwayi gida.
Da ace ina tare da mahaifiyarsu dukkaninsu suna tare da ni a kewaye,amman yanzu fa?"
Numfasawa Safiyya tayi kana tace.
"Gaskiya kam."
A ranta kuwa tunanin matakin da zata ɗauka take dan yanzu yaran Hasiyya ne suka shigo fagen yaƙin suna ƙoƙarin rabata da kwanciyar hankalinta dan haka dole ta san matakin ɗauka."
Sai da yayi sallar isha kana ya nufi gidan Mommy fuskar nan a mugun ɗaure.
Duk muna zaune a falon Momy,ni ina kurɓar kunun madarar da nayi a hankula dan komai ya taɓa leɓena azabar zafi yake mun, dan da gurin Gwaggo nayi guduwata ina ta zuba musu taɓara ita da Baffa dan ce musu nayi faɗuwa nayi, zuwan su Zarrena ne taje ta tattago ni muka dawo sashen Momy, da dukkan alamu Allah ya haɗa jininta da nawa.
Sallama yayi ciki ciki, tun da naji bugun zuciyata ya sauya na kuma ji ƙamshin turaransa nayi ƙasa da kaina.
Da gudu Zareena ta miƙe ta nufe shi da sassarfa babu ruwanta da idon Momy tun da mu dama ba lallai ta ji nauyinmu ba ta shige jikinsa,shima kuma ya karɓe kayarsa babu kunya, Mommy kam ina gani ta tashi ta bar falon nima na miƙe na nufi ɗakina na kira Yaa Sulaiman a waya.
Idonsa akan mug ɗin da ta ajiye ta bar gurin har suka ƙarasa gurin yasa hannu ya ɗauka,sai da ya zauna kan kujerar ya kai mug ɗin bakinsa haɗe da lumshe idanuwansa.
"Yunwa kake ji ne Bei? "
Gyaɗa mata kai yayi, yayin da ta kalli Zainaba tace.
"Ke zubo masa abinci, ko mu ƙarasa dining ɗin?"
"No abu me ruwa kawai."
Nasrin ce tace "Bara na duba kamar akwai kunun a flask dan naji kamar Abba yace zai sha."
Jinjina mata kai yayi, ita kuma ta nufi kichen ɗin, sai gashi kwa ta zubo mishi shi yana ta tiriri."
"Thanks" Yace mata bayan ya karɓa, kafin kuma yace.
"Ki haɗa mini coffee ki zuban a flask."
"Toh tace ta juya ta nufi kichen ɗin."
Momy ce ta kira shi a waya tace ya shigo ciki tana son magana da shi, dan in ta fito kuma ba ta san me idonta zai gane mata ba.
Faɗa Momy ta haushi da shi ta in da ta shiga ba ta nan take fita ba akan abin da ya yiwa Najjwa.
"Ki yi haƙuri Momy dama horata nayi."
"Haka ake horo a garinku ka kumbura mata leɓe, an gaya maka ko wace mace ce zata ɗauki jin kanka da isar ka? Wallahi ban da Sulaiman ya rigaka Najjwan zan aura maka naga ƙarshen jin kai dan itace daidai da kai.
Yauwwa kuma abin da na gani kar na sake ganin makamancinsa."
"In sha Allah, amman ba da wani nufi nayi ba."
"Ko ma dai meye nidai na gaya maka kar na ƙara gani, sannan kuma ita matarka ba ta iya girki ba ne?" Mun muku na baƙunta kuma ai abun ya isa haka 'yata ba jaka ba ce ai."
"Kiyi haƙuri Momy dududu kwana nawa zamui mu koma in da muka fito, ban da auran Bro da tuni mun juya."
"Ai ba sai ka gayan haka zan san a matse kuke a nan ba, ba kuma ka bani amsata ba."
"Ba nufina haka ba kenan Momy kiyi haƙuri, Zareenah kuma ba ta taɓa yin girki ba, muna da cheef cooks, ko kuma muje gidan cin abinci wani zubin."
"Hakan yana da kyau,tun da hakan kaga ya fi maka."
"Toh Momy rayuwarta ce,ni bana son taga kamar na takura mata."
"Gaskiya kam."
Ko da ya gama shirinsa na kwanciya ya zuba coffee ɗin da Nasrin ta dafa mishi kasa sha yayi ta ganbaɗa masa uwar suga, shi ba haka wan da ake kawo masa yake jinsa ba, tsaki ya ja ya fita falo ya ɗauki ruwan sanyi ya sha kana ya nufi ɗakin Zareena da tayi kwanciyarta a can dan yau ba ta son takura ta san in ba taje ba bazai nemeta ba,ba ta san yau a sama yake ba saman da bazai iya ƙyaleta ba, tana tsaka da baccinta mai daɗi ta ji anyi sama da ita, yayin da ya fice da ita ya nufi ɗakinsa.....
"Ku kallla."Fatma tace da 'yan tawagarta, gaba ɗayansu kuwa suka juya idanuwansu ya sauka akan Sajda,tana taku ɗaiɗai cike da yauƙi da yanga wan da ya zame mata jiki domin kuwa duk in da gayu yake Sajda tasan gayu ta kuma san ta kansa. Abin da ya bawa su Fatma mamaki ba komai ba ne sai yadda Sajda ta samo mayafin da ya mugun shiga da leshin da ke jikinsu gaba ɗaya,anko ne na class mate ɗinsu, sun zaga kasuwanni da dama haɗe da super market suma da dama amma basu samu mayafin da ya mugun shiga da leshin ba kamar yadda na Sajda ya shiga, abin da suke gudu ya faru (Sajda ta fisu ɗaukan wanka) Har ta gifta su ta ankara da yadda suka zuba mata ido kamar su cinyeta ɗanya, basa shiri shiyasa bata shiga shirginsu, su kullum burinsu su fita ɗaukar gayu amman hakan ya gagara saboda ta fisu sanin takan gayun.
"Lafiya dai ko na ci muku bashi?"
" Muna mamakin yadda akai kika samu mayafin da muka gama karaɗe kasuwanni da dama ba mu samu ba."
"Hmm shine matsalarku?"
"Eh"
"To matsalarku tazo ƙarshe in sha Allah zan haɗa ku da NEEHAL COLECTION daga yanzu wahalar neman mayafai ƙare muku da yardar Allah, dan nima tun da aka haɗa ni da ita na huta, duk mayafan da ake so ana samu a gurinta ko wani irin kala ne, kuma masu kyau da ɗaukar ido cikin farashi mai sauƙi."
"Au wai kina nufin mayafin na gida ne ?"
"Eh mana ɗan hannu ne."
Amma ta iya mayafai maza maza haɗa mu da ita dan baza mu shiga gurin bikin nan ba sai da irin mayafin ki muma mu ƙure gayu.
https://wa.me/message/AD4MDTQJLXIRD1
Ku bi wannan link ɗin zai kaiku in da zakui magana da NEEHAL COLECTION daga yau matsalar mayafai ta ƙare muku zaku samu duk kalar mayafan da kuke so cikin farashi mai sauƙi ina mai tabbatar muku zaku ji daɗin muamala da ita.
Ga masu bukatar a tallata musu hajarsu kofa a bude take cikin farashi mai sauki.
#09037093702/08082007142
#BR
[10/13, 08:52] RASHUNA: BEBEE'ARTH
Wattpad@Rashuna
KANA NAKA
(Allah na nasa )
24
Washe gari Zareena na tambayarsa Break fast, yace Zainaba kawai ta yi musu, a lokacin shiryawa yake zai fita, suna fitowa falon shi da Zareenah aka yi knocking Zainaba tazo ta buɗe sai ga Nasreen da kwandon abinci.
Mutmushi yayi a ransa yace.
"A jinjinawa mahaifiya, ita ɗin ta daban ce a ko ina."
Jikinsa har rawa yake gurin zuba coffee ɗin a mug, fatansa Allah yasa dai ba Nassrin ɗin ce ta haɗa ba, in ma itace Allah yasa ba ta gambaɗa masa suga irin na jiya ba.
Bai ji shi dai yadda yake jinsa ba, amman ya samu ya sha saboda bai yi sugan na jiya ba, iya shi kawai ya sha ya nufo gidan Momyn dan har ga Allah kunun madarar nan kawai yake son sha,idan ya sha shi da safe bai cika neman abinci ba sai yamma, idan yaci da yamman kuma sai dare ya sha coffee shi kenan ya wadatar da shi.
Falon tsit sai ƙamshin turaran wuta da air freshner da ya karaɗe ko ina, da kuma fankoki da Acn dake bada wani sanyayyan sanyi.
Tsayawa yayi cak a tsakiyar falon ba tare da ya nemi guri ya zauna ba, bai kuma kalli Zuwaire da ke durƙushe tana miƙa mishi gaisuwa ba har sai da aka yi knocking kana ta miƙe taje ta buɗe.
"Uwar ɗakina an tashi lafiya."
"Lafiya lau Zuwaire ya aiki?"
Na kai ƙarshen maganar ina jin sauyin bugun zuciyata kafin idona ya sauka a bayansa yana tsaye ƙiƙam.
"Alhdlillah Uwar ɗaki."
"Yau me kuka yi na break? Wa'yancan tsofaffin ɗan ƙa'idar nasu zasui break da shi (Ɗumaman tuwo) nikam ban son cinsa, kuma ban jin daɗin jikina bare nayi girkin."
"Ayya sannu,doya ce muka soya sai kunun gyaɗa da tea, kasancewar Abba yayi tafiya, Momyn ma har yanzu ba ta fito ba."
"Ok ba matsala, ungo wannan yi mini warming ɗinsa, amman kiyi sauri kada na makara."
Na kai ƙarshen maganar bayan na miƙa mata ledar takaddar tsiren mandawari da zan tafarwa da Nauwwa shi ina sauke idona kan agogon da ke tsintsiyar hannuna lokaci ya nuna mini bakwai da rabi, har ta kusa kaiwa kichen nace da ita.
"Nasrin fa?"
" Driver ya tafi kaita makaranta bayan sun sauke abinci gidan yallaɓai."
"Ok"
Kawai nace ina shigowa cikin falon sosai, dan masifa zuciyata azalzalata take na sauke idona a kansa amman na ƙi bata haɗin kai har na isa in da fridge ke ajiye na buɗe haɗe da ɗauko youghot ɗin L nd Z kana na nufi kichen na ɗauki glass cup na ɗauraye na tsiyaya youghot ɗin a ciki kana na zauna kan kujera ina sping ɗin youghort ɗin a hankali haɗe da lumshe idanuwana, jin ƙamshin turaransa na ƙara kusanto in da nake yasa ni wara idanuwana ban sauke shi a ko ina ba sai a kansa,sanye yake da italian suit baƙaƙe wuluk ya sassautawa wuyansa aish ɗin tie da ke jikinsa,kwarjini da zallar kyahunsa yasa gabana yankewa ya faɗi kallo ɗaya yayi mini ya ɗauke kansa haɗe da