x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 17 - KANA NAKA ALLAH NA NASA complete document

  • 48001 words
  • 51000 words
  • Out of 66841 words

Category: Love Stories

Views 298

25 Aug 2025
Start ads
After Image Ads
kulawa ga wata mace sama da ni ba."

"Amman ka da ki manta wannan ɗin ƙanwarsa ce,kuma matar wansa."

Wani numfashi ta sauke wan da ba ma ta san ta riƙe shi har haka ba,sa bo da jin tunatarwar da Nauwwara ta yi mata,ta zauna suna hira amman duk da hakan idanuwanta suna kan ƙofar ɗakin Najjwan kai hankalinta gaba ɗaya ma ya na cikin ɗakin.

Rubf da ciki na yi na hau risgar kuka,kukan da tun da na san gurin da zuciyata ta ɗiba ta kaini muka ɗaura ƙawance da shi,ko da na ji ƙarar turo ƙofa ban tsagaita da kukan nawa ba,duk da na ji yadda na ƙara jin ƙamshinsa da na kwaso a falo ya ƙara yawa ban taɓa tunanin zai biyo ni ɗaki ba,to ya biyo ni yayi mini me?

"Ki na da damuwa ne,ko wani abu ya faru?"

Jin muryarsa yasa ni juyowa a razane ina sauke jiƙaƙƙun idanuwana a kansa.

Kallonsa na ke kamar yau na fara ganinsa.
Kallonsa nake da yadda nake jin ƙarin bugun zuciyata.
Kallonsa nake tare da karɓar dukkan feeling ɗin da ke zagawa ta jinin jikina.
Kallonsa na ke da dukkan zuciyata.
Kallonsa nake da sallamawar bazan taɓa mallakarsa yadda zuciyata take so da muradi ba.

Kallon tsakiyar idonta ya ke ya na jin yadda zuciyarsa ke wani mugun bugun da bai taɓa jin zuciyarsa na yi ba,wasu abubuwa ya ke ga ni cikin ƙwayar idanuwanta da ke shiga cikin nasa idanuwan kuma bai san da me zai kira wannan abu ba,takawa ya fara yi zuwa gabanta still dai idanuwansa na cikin nata.

Da dukkan takun da yake zuwa gare ni da dukkan yadda zuciyata ke buga tsalle a ƙirjina da kuma muradin kwanciya a faffaɗan ƙirjinsa.

"Ki na jin wani abu game da ni ne?"

Girgiza masa kai na yi ina rintse idanuwana wan da hakan ya bawa sababbun hawayen wanke fuskata.

"Wannan hawayen fa?"

Kallonsa na yi,ina ganin yadda ya matso gab da ni,shaiɗan zan ce ko kuma son zuciyata na bi ban dai sani ba nidai kawai na tsince ni a faffaɗan ƙirjinsa rungume shi na yi tsam ina sakin kukan da ke tawowa tun daga ƙasan zuciyata.

"Subhanallah Naajjjj."

Ya faɗi hakan sabo da yadda na faɗa jikinsa a bazata yayi sanadiyar sanya jikinsa rawa da karɓar saƙon da zai iya cewa bai taɓa karɓar makamancinsa ba.

Jin yadda ya ambaci sunana ya ƙara sa na kuma shigewa jikinsa sosai ina jin yadda wani abu ke tsirgawa ta marata yana fita mai ɗumi, kafin na farga da abin da na yi nayi saurin sakinsa na miƙe da sauri na fito daga ɗakin yayin da ya mara mini baya cikin bugawar zuciya da tunanin lafiya nake kuwa?
Shi kansa bazai ce ga dalilinsa da yasa yake son sanin damuwar tawa ba, ko da kwa za'a taru ana son jin dalilin nasa.

Ina fitowa cikin idon Momy nawa idon ya faɗa.
"Lafiya."
Ta jefo mini tambaya kafin fitowar Mu'azz ta sakata mayar da tambayarta kansa cike da tuhuma.

"Me ka yi mata?"

Zunkuɗa kafaɗarsa yayi kafin yace.

"Mai makon ki tambayi yaushe na dawo kin tsaya tambayar dalilin kukan 'yarki,Allah Momy ba ki damu da ni ba."

"To ai wan da ya damu da kai da shi kake damuwa."

"Momyy manaaa"

Ya faɗa yana kwaɓe fuska kamar zai yi kuka

"To ƙarya na yi?"

"Ana ta tambayarki a fanda,duk suna miƙa gaisuwa gare ki,kuma da yawansu zasu zo bikin Bro."

Ya canja maganarsu da wannan,murmushi kawai Momyn tayi ta mayar da hankalinta kaina da na nufi kicin.

"Najjwa me yake faruwa?"

"Zan haɗa masa coffee ne Momy"

"Ka matsa mata ko?"

Girgiza mata kai yayi kafin yace.

"Na yo miki tsarabar fura da nono irin wan da kike so."

"Da gaske?"

Momy ta tambaye shi murmushin ta na yawaita, gyaɗa mata kai yayi kafin ya kama hannunta yace "Muje mota mu ɗauko."

Ɗaukowa suka yi suka dawo kana suka nufi kicin yayin da Zarenah ta bi bayansu.

"Najjwa idan kin gama kiyi blending fura da nonon nan, ayi mata haɗi irin na ranar nan a zubawa kowa,ki saka mana tamu ni da Abbanki a pridge."

"To Momy in sha Allah za'ayi yadda kika ce."

Kana ta juya ta bar kicin ɗin,zama sukai shi da Zarinan a kicin ɗin har na gama haɗa masa coffee ɗin,na zuba a mug sai tiriri yake na kai mishi ba tare da na ɗaga kai na kalle shi ba,saboda matsanancin kunyar abin da na aikata ɗazu,na rasa me ya shiga kaina a lokacin.

"A kawo abincin?"

Zareena ta tambaye shi, girgiza mata kai yayi kafin yace.

"Wannan ma ya isa,idan ta gama blending ɗin furar zan sha,ya faɗi hakan duk da furar ba damunsa tayi ba,kawai dai daga jin Momy tace tayi musu irin ta ran nan ya ji ya na son sha ya ji irinta.

Barin aikin furar na yi na ɗauki plate na ɗauraye na goge da dusta me kyau kana na zuba masa haɗaɗɗiyar jalof rice ɗin da taji vegetables da hanta ta yi shar shar gwanin sha'awa na ɗora masa pape cikin a kai,na je na ajiye a gabansa, sai da na koma gurin da da nake tsaye nace.

"Zuba masa kawai zaki ki kawo masa,amman mutumin da yace miki ya na jin yunwa ta ina coffee da fura zasu wadacesa?"

Murmushi Zareena tayi kana tace.

"Irin su Bei kam,coffen ma kawai zai wadacesu,amma ke kam na ga alamun kwanan nan Doctor zai yi lukuti ya aje tumbi,don da dukkan alamu idan bai ci ba ɗura za ki masa."

Dariya na yi ina kallonsa ta ƙasan ido yadda ya janyo plate ɗin abincin ya na aikawa cikinsa ba ƙaƙƙautawa daɗi ya na kai masa ko ta ina.

Nu ni nayi mata da shi,ta kallesa muka saki dariya a tare kafin tace.
"Kin samu ladansa."
Jin dariyarmu yasa ya ɗago ya kallemu haɗe da yatsina fuska ya ture plate ɗin ya ɗauki mug na coffee ɗin ya cigaba da sipping ya na lumshe idanu.

Nauwwa ce ta leƙo kicin ɗin haɗe da cewa.

"Najj zamu huce ya ƙaraso."

"Ok Nauwwa ina zuwa."

Nace da ita ina saurin ɗauko jarka na zuba mata furar da nayi blending da kwakwa da banana da madara da suga kaɗan a ciki,na biyo bayanta a gaggauce dan kar su wuce.

Gaisawa muka yi da Najib ɗin,na miƙa mata furar muka yi sallama mu naiwa juna Allah ya huta gajiya kana suka wuce.











"Ku kallla."Fatma tace da 'yan tawagarta, gaba ɗayansu kuwa suka juya idanuwansu ya sauka akan Sajda,tana taku ɗaiɗai cike da yauƙi da yanga wan da ya zame mata jiki domin kuwa duk in da gayu yake Sajda tasan gayu ta kuma san ta kansa. Abin da ya bawa su Fatma mamaki ba komai ba ne sai yadda Sajda ta samo mayafin da ya mugun shiga da leshin da ke jikinsu gaba ɗaya,anko ne na class mate ɗinsu, sun zaga kasuwanni da dama haɗe da super market suma da dama amma basu samu mayafin da ya mugun shiga da leshin ba kamar yadda na Sajda ya shiga, abin da suke gudu ya faru (Sajda ta fisu ɗaukan wanka) Har ta gifta su ta ankara da yadda suka zuba mata ido kamar su cinyeta ɗanya, basa shiri shiyasa bata shiga shirginsu, su kullum burinsu su fita ɗaukar gayu amman hakan ya gagara saboda ta fisu sanin takan gayun.
"Lafiya dai ko na ci muku bashi?"
" Muna mamakin yadda akai kika samu mayafin da muka gama karaɗe kasuwanni da dama ba mu samu ba."
"Hmm shine matsalarku?"
"Eh"
"To matsalarku tazo ƙarshe in sha Allah zan haɗa ku da NEEHAL COLECTION daga yanzu wahalar neman mayafai ƙare muku da yardar Allah, dan nima tun da aka haɗa ni da ita na huta, duk mayafan da ake so ana samu a gurinta ko wani irin kala ne, kuma masu kyau da ɗaukar ido cikin farashi mai sauƙi."
"Au wai kina nufin mayafin na gida ne ?"

"Eh mana ɗan hannu ne."

Amma ta iya mayafai maza maza haɗa mu da ita dan baza mu shiga gurin bikin nan ba sai da irin mayafin ki muma mu ƙure gayu.

https://wa.me/message/AD4MDTQJLXIRD1

Ku bi wannan link ɗin zai kaiku in da zakui magana da NEEHAL COLECTION daga yau matsalar mayafai ta ƙare muku zaku samu duk kalar mayafan da kuke so cikin farashi mai sauƙi ina mai tabbatar muku zaku ji daɗin muamala da ita.

Ga masu bukatar a tallata musu hajarsu kofa a bude take cikin farashi mai sauki.

#Najjwa
#Sulaiman
#Mu'azz
#BR
#09037093702/08082007142
[11/18, 21:33] RASHUNA: BEBEE'ARTH



Wattpad@Rashuna



KA NA NAKA
(Allah na nasa )

29

Kamar ƙiftawar ido haka kwanaki su ka yi ta wucewa har zuwa yau lahadi ranar ɗaurin auranmu da Yaa Sulaiman kenan.
Tun ranar laraba muka fara hidimar biki, ba gidanmu ba,ba gidan su Yaa Sulaiman ba ko ina hidima ake,ba kama hannun yaro.
Ranar larabar mu ka yi kamu,alhamis kuma aka yi dinner ɗin gidan su Yaa Sulaiman,juma'a al'adar bikinmu ta sieria muka yi saboda dangin Ummata yawancinsu sunzo har da kakata tun ana ya saura sati bikin.
Asabar kuma aka yi dinner gidanmu,sai yau lahadi kuma da za'a ɗaura auran namu da misalin ƙarfe goma sha ɗaya na safe,da yamma kuma Mommy za tayi mothers day.

Ƙarfe goma sha ɗaya da kwata aka shafa fatihar ɗaurin auran Hassana Bashir Sunusi da angonta Sulaiman Aliyu Fanda.
Alƙawarin Allah ya cika anyi wannan aure, bakin Yaa Sulaiman ya ƙi rufuwa dan farin ciki waya ya zaro daga aljihunsa ya turawa Najwa saƙo kana yaci gaba da miƙa wa mutane hannu suna musabaha bakin nan ya ƙi rufuwa.

Zaune nake a bakin gado cikin farin leshi me adon golding ɗinkin riga da siket ya zauna sosai a jikina, daga kan mayafi,jaka takalmi dangin sarƙoƙi duk golding ne,daga pawder sai kwalli da lipstic ne a fuskata amman duk da hakan ba ƙaramin kyau na yi ba.
Saƙo ne ya shigo wayata wan da ya sauka tare da bugun zuciyata,ganin Yaa Sulaiman ne ya turon saƙon yasa ni saurin buɗewa na karanta.
"Alhamdlillah,finally is mine."

Ajiyar zuciya na sauke kafin siraran hawaye su biyo kuncina.

"Ta zama ta zama ta za."

Turus Nauwawa ta yi sauran maganar na maƙalewa a bakinta ta tsaya tana kallona kafin tace.
Malama yanzu dai ba lokacin kuka ba ne ki adana abin ki zai miki amfani anjima in zaki bar gida,da zaki ji shawarata ma da kin barsa sai Yaa Sulaiman zai ɓarje amarcinsa.

Harara na wurga mata kana nace.

"A surfawa zai yi ba ɓarjewa ba."

Dariya ta yi kafin tace.

"Duka dai sammakal,yanzu dai ki taso za'a yi hotunan tarihi."

"Sai kizo ki ɗaga ni"

"Girmanki ne ai amaryar Yaa Sule bara na zo na ɗaga ki."

Kifewa na yi akan gadon na hau rusar kuka,dafa kafaɗata ta yi kafin tace.

"Sau tari mukan so abu,kuma ba alkhairi ne a garemu ba,zaɓin da Allah yayi mana idan muka kwantar da hankali muka miƙa dukkan lamuranmu a gare shi a hankali zuciyarmu za ta nutsu da wannan zaɓin nasa muga alkhairinsa fiye da wancan da muke so.
Da Yaa Muhd kuka tsara rayuwar auranku Allah ya karɓe abinsa ranar da aka ɗaura auran,yanzu kuma ya zaɓa miki Yaa Sulaiman a matsayin mijinki na tabbata idan kika kwantar da hankalinki ina da yaƙinin soyayyar da Yaa sulaiman yake miki ta ishe ku rayuwa.
Yanzu ki share hawayen ki taso mu je ana jiranki za'ayi hotuna dan Mommy ma ta tsayar da Abba kuma sauri yake kinsan zasu tafi launchin yanzu."

Ina cikin gyara fuskata Aunty Faty ta shigo tana.

"Ina Najjwan ne? Ita fa ake jira lokaci yana jaa."

Nauwwa ce tace.

"Gamu nan Aunty Fati fuskarta take gyarawa an fara kukan rabuwa da gida."

"To ya za'ayi?muma ai duk da haka muka saba."

"Aikam dai."

Kamo ni tayi muka fito farfajiyar gidan namu idona akansa ya fara sauka zuciyata tayi wani irin bugawa da mugun kyawun da yayi cikin farar shadda ta sha aiki da sky blue ɗin zare dinkin babbar riga yayin da takalmi,hula,agogo suma suka kasance sky blue,cingum ɗinsa na manne da shi cikin sky blue ɗin wani tsadaddan material da yaci ubansun ɗinkin riga da siket ya zauna cif-cif a jikinta tana ta kashe su da selfie,sunyi kyau ainun duk hassadar me hassada.
Tun ranar bikin yaye mu da ga makaranta rabon da na sanya shi a idanuna,tafiya suka yi shi da ita sai jiya da daddare suka dawo.

Ɗauke idona na yi daga kansu ina ambatar "Astagfirillah cikin zuciyata."Kafin na sauke idanuwan nawa a kan Yaa Sulaiman idanuwanmu suka sarƙe guri ɗaya yana ta sakar mun tasadaddan murmushinsa,anan naga anko suka yi da MU'AZZ ɗin a she.


Bayan Gama hotunan namu suka ɗun guma Lass vigass yin launching Abbana da abokanansa da Daddyn su Yaa Sulaiman shima da nasa abokanan sai kuma me gayya me aiki Yaa Sulaiman ɗin shima da nasa mutanen.

Shi ko Baffa a nan falonsa yayi launcing ɗinsa shi da jama'arsa ya ce bazai bi su ba haka kawai tsofe tsofe da shi a ganshi a gurin shaƙatawar yara.
Tsiren mandawari kuwa yayi kuka a launchung ɗin Baffa dan na sa guda ya bashi kwangila a ka yo masa,dan ni kaina shi na samu na ci dan akwai amana a tsakaninmu.
Har Nauwwa na cewa.

"Anya bazan cewa Yaa Sulaiman tsire muke so a bakacin kazar amarcinmu ba?"
Ganin yadda na ƙi cin ko wani abinci amman ina ganin tsiren na ci,harara na wurga mata haɗe da cewa.

"Sai ki ba da himma.


Da yamma Momy da Goggo su ka yi na su yinin a nan farfajiyar gidanmu,abun ya ƙayatar sosai ba kuga jama'a ba kamar ana ƙara tututuɗo su.

Magariba na yi aka fara shirye shiryen kai amarya,dama tuni idona ya raina fata na fara gurzar kuka,ko da Aunty Hafsa ta saka ni yin wanka,haka na yi wankan ina kuka har na fito Nauwwa da Aunty Fati sai zolayata su ke na ƙi kulasu, daga ƙarshe Aunty Hafsa ce ta korasu ta cigaba da taya ni shiryawa, ta na yi tana mun nasiha me ratsa jiki,tuni jikin ya ƙarasa mutuwa murus.


Ɓaffa da Gwaggo da Inna a jimlace dai kakannina ne suka fara mun nasiha me ratsa ɓargon jiki,kafin Abbana ya ɗora tasa haɗe da sanya albarka a cikin zaman auren namu.
Kuka na ke sosai,har da kukan rashin mahaifiya a yau ɗin da zan ta fi gidan miji,zan gudanar da wata sabuwar rayuwar da ban san a yadda za ta zo mini ba.
"Allah ya gafarta miki Ummana ya kai haske kabarinki amin."

Momy kuwa ce mini ta yi.

"Ga Amanar yarona nan Najjwa na baki,duk cikin 'ya'yan da Allah ya bani na fi sonsa da ƙaunarsa domin kuwa shima ya fi kowa sona,ya fi kuma kowa ƙulafucina.
Bani da tabbacin baza ku samu saɓani a zamanku ba,domin kuwa hausawa sunce "Zo mu zauna zo mu saɓa,bare kuma zaman aure dole sai da haƙuri da kau da kai,duk kuwa ƙarfin soyayya da ƙaunar ma'auratan,amman ina da yaƙi nin za ki ji matuƙar daɗin zama da son domin kuwa mutum ne me sanyin zuciya.Ba wai don yana ɗan cikina na faɗi hakan ba sai dan na tabbata ke kanki wata rana za ki bawa wani labari,kuma shima yadda na baki amanarsa haka na ba shi amanar ki,Allah ya baku zaman lafiya ya kaɗe fitina ya kuma baku zuri'a ɗayyiba."


Ina Gursheƙan kuka haka kowa ya zame ya gudu ya barni,hatta Nauwwa ma ba ta tsaya ba,wai ai angon ba abokanai ne da shi a nan ba da zasu rakosa ta san shi ka ɗai zai shigo.
Ina wannan kukan a haka na ɓingire baccin gajiya yayi gaba da ni, ko kaɗan ban ji alamun buɗe ƙofarsa ba sai ji kawai na yi ana shafan fuska,a hankali na wara idanuwana akan fuskarsa yana sakar mun tsadaddan murmushin nan nasa,murmushin nima na sakar masa cikin yanayin rashin daɗin jikin da na farka da shi sakamakon baccin da ya fara ɗibata.

"Yi haƙuri,daure ki tashi ki ɗauro auwwala mui sallar godiya ga Ubangiji da ya nuna mana wannan ranar wacce ba kowa ya samu damar ganinta ba.

Yunƙurawa na yi zan ta shi ya taimaka mini na miƙe,sai da ya raka ni har toilet ɗin kana ya juyo,prayer mat ya shimfiɗa ya ɗauko mini sabon hijabi ya zauna zaman jiran fitowata.
Ina fitowa ya bani hijabin na saka ya jamu sallar nafila,bayan mun idar ya dafa kaina yayi addu'ar da ma'aiki (S.A.W) ya koyar da mu, ya nemi alkhairin zama tare da ni tare kawar da dukkan wata fitina daga gareni.

Bayan mun idar ya gabatar mana da gasasshiyar kaza ta madalla suya da youghurt ɗin Lnd Z.
Youghort ɗin na sha kawai,shi kuma yaci naman haɗe da youghort ɗin sosai dan yau be samu ya ci wani abincin kirki ba.


Da kansa ya ɗauko mun kayan bacci ya kawo mun na saka,kallonsa na yi da tunanin yadda zan sauya kaya a gabansa.

Rungomo ni jikinsa yayi tsaf,kana ya sake ni haɗe da sakar mini kiss a goshi.

"Bara naje ɗakina na baki space ki sauya kayan,ki yi bacci me daɗi tare da tunanin kin zama mallakin Sulaiman,ki yi kuma mafarkinsa, sai da safe."

"Allah ya tashe mu lfy."

"Amin Cwtyy,ki yi fa mafarkina da safe za ki bani labari."

Daga haka ya fice daga ɗakin,na saki guntun murmushi kafin na tashi na sauya kayana zuwa na baccin da ya ɗauko mun,na bi lafiyar gado idanuna cike da baccin gajiya.



Washe gari Nasrin ce ta kawo mana kayan Break.
Cikin kwaɓe fuska nace.
"Me yasa ba ki taho mun da twince ɗina ba?"

"Bacci suke ko tashi ba su yi ba,amman anjima tare za mu taho."

"Yauwwa kuzo da wuri dan Allah."

"In sha Allah, Bro kira mini Yaa El nayi ta nocking a gurinsu shiru ba'a buɗe ba ina jin ko ba su tashi ba."

"Ai Mu'azz suna Saudiya jiya flight ɗin dare suka bi."

Kwaɓe fuska tayi kana tace.

"Au shine bai mun sallama ba?"

"Sai ki kira shi a waya yayi miki sallamar,idan ba ta wadace ki ba sai ya dawo ya yi miki sannan ya kuma tafiya Momy."

Murmushi tayi sanin gatse yayi mata kana tayi dariya haɗe da cewa.

"Allah Bro ba haka nake
End Ads