x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 6 - KANA NAKA ALLAH NA NASA complete document

  • 15001 words
  • 18000 words
  • Out of 66841 words

Category: Love Stories

Views 308

25 Aug 2025
Start ads
After Image Ads
naki ba wani iya tuwon shinkafa tayi ba."
"Au haka kace? Najwan zatai aure ne ta barni da kai ne ?"
Cewar Gwaggo da ba mu san sanda ta fito ba,dariya mukai daga ni har Baffan kafin nace.
"Idanma na yi auren na dinga kawo masa daga gidana."

"Yawwa gaya mata shalelen Baffa, tukuicinki yau dole na biya mandawari."
Yakai ƙarshen maganar yana hayewa kan kekensa.
"Yauwwa Baffa a haɗo da Rufaida."

"In sha Allah shalele,ki kula mini da tuwona ina dawowa ta kansa zan fara, ko gutsire kar ki bari Gwaggonki ta taɓa."
"Ni kam me zan yi da tuwon zamani ga tun na iyaye da kakanni?"

Bai jiyo ta ba da sai ya bata amsa ya riga da ya miƙa a dawo lafiyar ma da nake masa hannu ya ɗago mini, muka shige ciki ni da Gwaggo ina murnar yau zan ci tsiren mandawari.....
[9/25, 10:49] RASHUNA: BEBEE'ARTH



Wattpad@Rashuna



KANA NAKA
(Allah na nasa )



13

"Ku kallla."Fatma tace da 'yan tawagarta, gaba ɗayansu kuwa suka juya idanuwansu ya sauka akan Sajda,tana taku ɗaiɗai cike da yauƙi da yanga wan da ya zame mata jiki domin kuwa duk in da gayu yake Sajda tasan gayu ta kuma san ta kansa. Abin da ya bawa su Fatma mamaki ba komai ba ne sai yadda Sajda ta samo mayafin da ya mugun shiga da leshin da ke jikinsu gaba ɗaya,anko ne na class mate ɗinsu, sun zaga kasuwanni da dama haɗe da super market suma da dama amma basu samu mayafin da ya mugun shiga da leshin ba kamar yadda na Sajda ya shiga, abin da suke gudu ya faru (Sajda ta fisu ɗaukan wanka) Har ta gifta su ta ankara da yadda suka zuba mata ido kamar su cinyeta ɗanya, basa shiri shiyasa bata shiga shirginsu, su kullum burinsu su fita ɗaukar gayu amman hakan ya gagara saboda ta fisu sanin takan gayun.
"Lafiya dai ko na ci muku bashi?"
" Muna mamakin yadda akai kika samu mayafin da muka gama karaɗe kasuwanni da dama ba mu samu ba."
"Hmmm! shine matsalarku?"
"Eh"
"To matsalarku tazo ƙarshe in sha Allah zan haɗa ku da NEEHAL SPARKLES VEILS daga yanzu wahalar neman mayafai ta ƙare muku da yardar Allah, dan nima tun da aka haɗa ni da ita na huta, duk mayafan da ake so ana samu a gurinta ko wani irin kala ne, kuma masu kyau da ɗaukar ido cikin farashi mai sauƙi."
"Au wai kina nufin mayafin na gida ne ?"

"Eh mana ɗan hannu ne."

Amma ta iya mayafai maza-maza haɗa mu da ita dan baza mu shiga gurin bikin nan ba sai da irin mayafin ki muma mu ƙure gayu.

https://wa.me/message/AD4MDTQJLXIRD1

Ku bi wannan link ɗin zai kaiku in da zakui magana da NEEHAL SPARKLES VEILS daga yau matsalar mayafai ta ƙare muku zaku samu duk kalar mayafan da kuke so cikin farashi mai sauƙi ina mai tabbatar muku zaku ji daɗin muamala da ita.


****"""""

Naj na fita Isah driver ya sauke SULAIMAN ALI FANDA Farin bafulatanin da ya juye ya koma tamkar balaraben da ya samu hutu da kwanciyar hankalin rayuwa, cike da zumuɗi ya buɗe murfin motar ya fito ganin Momy ta nufo gurin da akai parking motar tasu, rungumeta yayi cike da shaƙi kafin yace "I miss you Momy." Cikin harshen da ya saba yaruka kala-kala wan da ya juye yake bada wani sauti na da ban.
Murmushi kawai Momy tayi tana ɗan kaucewa daga rungumar da yayi mata, saboda kasancewarsa ɗan fari tana ɗan kawaici a kansa shiyasa ko sunansa bata kira sai dai tace. "Son" Amman itama tayi missed ɗin yaron nata yadda bakwa zato musamman da yake akwai shi da ƙulafuci shiyasa duk a yaranta ta fi ƙaunarsa duk da tana kawaici a kansa.

Hannunsa ta ruƙo suka nufi cikin gidan tana tambayarsa ya hanya yana bata amsa, har suka shiga ciki, direct dining area ta nufa da shi saboda tasan halin son ɗin nata baya wasa da cikinsa, komai zai biyo daga baya to bayan ya cika tumbinsa ne, kuma tasan ba mamaki tea ne kawai a cikinsa tun daga wayewar garin yau saboda yasan girkinta na nan na jiransa.
Flass ɗin farko da Momy ta fara buɗewa zata yi serving nasa idonsa ya sauka akan mutuniyar tasa tayi nashar nashar da ƙwai hannu na rawa yakai ya ɗauki guda ɗaya yakai baki yana lumshe kyawawan idanuwansa.
"Allah ya tsunduma ki a aljanna Momy."

"Gaba ki ɗayanmu Amin."

Sai da yaci awarar sosai kana ya saka mulmulallen tuwon shinkafa fari sol da shi malmala biyu a plate suka haɗa ido da Momy yayi murmushin da ya fito da zallar kyawunsa.
"Wallahi yau mom babu abin da naci sai tea ne kawai a cikina."
Murmushi Momy tayi kafin tace ai nasan za'a rina. Zareenah har yau ba ta gama bokon bane bare su fara tunanin aje iyali?"

"Hmmm! Momy ki rabu da sabgar wa'yannan yahudawan mutanen, kuma babban mai laifinma EL ne saboda yasan wa ya auro kuma kafin su bashi aurenta sai da sukai yarje jeniya saboda shima yaran ba damunsa sukai ba."
"To Allah ya kyauta musu wannan lamarin, ni ita nafi ji,shi namiji duk sanda ya tashi buƙatar yara aurensa zai ƙara."
"Wai nan yayi mata alƙawarin bazai mata kishiya ba."
"To ai zamu gani tun da shi ke da ikon tsarawa kansa rayuwa, gaba ɗaya shima ya koma kamar baturen da aka haifa a turai."
"To ai Mom zama da maɗaukin kanwa....kuma zani ce ta tadda muje ni."

"To Allah ya rufa asiri, zan yi maganinsu gaba ɗaya duk randa MU'AZZ yazo bazai koma ba sai da mata in basa son yaran ni ina son jikoki, kaima dai da fatan da shirin aure ka iso."

"Ban dai zo da shiri ba,saboda har yau ban samu macen da ta kwantan a rai ba,amman a jikina nake jin lokacin aurena ya matso kinsan komai kana naka ne Allah kuma na nasa shirin kuma nasa ne gaskiya namu duk shirme ne."

"Gaskiya ne,Allah ya shige mana gaba Amin."

Wayar Momy aka kira, tana ganin number ta gane waye ya kira dan haka ta miƙawa Sulaiman dan ta san shine maƙasudin kiran,shima da ta miƙo masan Dad ɗin nasu ya kawo a ransa dan yasan shine kawai zai kira ta miƙo masa yana ɗagawa Dad ya hau faɗa kamar zai ari baki.
"Wani irin wulaƙanci ne wannan?na aiko driver tun huɗu da rabi tararka yanzu ya dawo mun da wani zance, to wallahi sam ban yadda ba yanzu ka dawo gidanku tun kafin ranka ya ɓaci don ban yadda da raina da lafiyata 'ya'yana sui zaman agolanci ba ko Nasrin dan bana nan ne akai bikin shiyasa amman yanzu na dawo ka gaya mata ta dawo mun da 'yata tun kafin rayuka su ɓaci."

"Ayi haƙuri Allah ya huci zuciya, a turo mini drivern in sha Allah zan biyo shi mu taho."

"Ok ba komai Allah ya yi maka albarka, a turo address yanzu zan turo shi."

"Amin, tom in sha Allah."

Kana suka ajiye wayar,fuskar Momy ya Kala tana nan a yadda take bai ga alamun ɓacin rai a kanta ba ko kaɗan a fuskarta duk da yana da tabbacin taji duk abin da Daddyn ya faɗa.

"Na haɗe maka abincin ka tafi da su can?"

Ai kwa Momy da kin kyauta abincin yamun daɗi sosai." Ya kai ƙarshen maganar idonsa na sauka akan hoton Najwa window siz tayi masifar kyau a jikin hoton, kamar wan da aka kafe idonsa a kai haka ya dinga kallon hoton, Momy ta nufi kicthen dama ɗauko kwandon da zata jere masa abincin shiyasa ba ta lura da Son ɗin nata ba, sai da ta dawo yace.
"Momy wace wannan?". Ya faɗa yana nuna hoton."

"Najwa ce 'yar me gidan ce,itace ma tayi maka girkin nan."

Wani murmushi ya saki cikin ransa ya furta.
"Alhmdlillah na samu matar aure."

Nasrin ce ta shigo da gudunta tana ƙwalla kiran "Yaaya" shiyasa ta katse musu maganar da suke da murnarta ta ɗane jikinsa shima kwa cike da ɗoki ya rungume 'yar ƙanwar tasa."
"Ina Yaa El,yace mini tare zaku zo?"

"Ki rabu da ni da zancen baturen yayan nan naki kamar ba a ƙasar larabawa yake zaune ba, ga tsarabar ki can jeki ki ɗauka." Ya nuna mata jerin akwatunan da aka shigo da su, ai kwa da gudu ta nufi gurin akwatinan dan hakan kawai zai mata ta rabu da shi da zancen EL mutumin da tun da ya kuma jin momy tayi aure ya kuma ɗaura gaba da nigeria, tun da da har ya fara saukowa daga fushin rabuwar Momy da Dad shiyasa ya fara zancen zuwan nasu tare.

Har drivern da Daddy ya turu ɗaukar Sulaiman yazo Abba bai dawo ba,dan haka yace in sha Allah da safe zaizo su gaisa anan ma zai yi break fast, tsokanar Nasrin ya yi akan tazo su tafi tare ta maƙale kafaɗa sai kawai yaji tausayinta ya kama shi da ya tuna Daddyn yace zai karɓe ta sai yaji yana addu'a cikin ransa Allah kar ya bawa Daddyn ikon karɓar nasrin ɗin,ba don komai ba sai don ba'asan wata irin kalar rayuwa zatai a cikin gidan ba, babu Momy babu su tunda su dama ba mazauna bane.

Motarsu na shiga harabar gidan nasu Daddy ya fito tare da Safiyya a gefen shi ta ɗau wanka tana taku ɗaiɗai ita ga wacce duniya ke garawa yadda take so, cike da so da ƙauna Daddy ya tari babban ɗan nasa suka rungume juna, bayan sun saki juna da Daddyn Safiya ta taho zata rungume shi yayi saurin jaa baya haɗe da jifanta da wani kallon baki da hankali?

Murmushin yaƙe Dad ya yi kana yace.
"Ga sabuwar momynku " yana nuna in da Safiyya ke tsaye tana rarraba ido.
"Oh sannu Aunty mun yini lafiya?"
Ya faɗa yana murmushin da bai kai zuci ba. itama yaƙe tayi kafin tace.
"Lafiya lau, ya hanya."
"Alhamdlillah" ya faɗa a taƙai ce kafin ya kalli Dad yace.
"Daddy zan huta, an jima zan shigo muyi hira." Daga haka ya nufi phart ɗinsa kai tsaye.

"Abinci fa?"

yaji muryar Safiya ta faɗa.
"A'a kar ki damu naci abinci." Yaci gaba da tafiyarsa ba tare da ya juyo ba.

Taɓe baki tayi, to ita wata damuwa za tayi dan bai ci abinci ba? Dama tayi ne don ta burge mijinta dan ta fuskanci son 'ya'yansa a ƙahon zuciyarsa yake abin da ya gagara zarewa daga cikin zuciyarsa kenan dan haka sai ta tayasa sonsu ko na ganin ido ne tunda ta samu ta fitar da mahaifiyarsu daga cikin gidan.







NAJWA

Goma saura shiyasa muke a tsure gaba ɗaya daga ni har Gwaggon dan ganin Baffa har lokacin bai dawo ba,tuni zumuɗin cin tsire ya sake ni dan ganin Baffan shiru dan kuwa da wuya yakai bayan isha a waje, ganin goma ta gota yasa ni ɗaukan waya na kira Abba na gaya masa, yace bari to yaje can mandawarin da yace zai je ya duba ya gani.

Wasa-wasa ƙaramar magana na nema ta zama babba, har ɗayan dare babu Baffa babu labarinshi duk mun ɗaga hankulanmu
ranar kwa bacci tsakaninmu sai ɓarawo da ƙyar muka ga wayewar washe gari aka ɗora nemansa daga in da aka tsaya amman babu wani labari, duk an bada sanarwar cigiyarsa ko ina, amman har akai kwana uku shiru kike ji babu wani labari, duk na fita hayyacina nayi zuru zuru ba ƙaramin tashin hankali nake ciki ba na ɓatan Baffa kuka kuwa na yishi ba iyaka."Ni kenan kullum daga wannan sai wannan, na buɗi ido ba tare da ko sanin fuskar mahaifiyata nayi ba,nazo na rasa kakata a lokacin ina tsaka da jin dadinta na kuma sha azabar matar uba, ranar da aka ɗaura mini aure ranar mijina ya rasu gashi yanzu Baffa ba'a san inda yake ba har gara ace mini mutuwa yayi hankalina zai fi kwanciya." Na cewa Momy da take ta bani bakin naci abinci amman yaƙi tafiyuwa." Ba kuka da cin abinci ne zai tabbatar da soyayyar da kike musu ba addu'arki suka fi buƙata sama da komai,shi kuma Baffa in sha Allah Allah zai bayyana shi.". Haka ta dinga lallaɓa ni har sai da na ɗan ci abincin.


Kwanan Baffa biyar da ɓata ulcer ta rafke ni aka ɗauke ni ranga ranga aka nufi asibiti da ni ba tare da nasan in da kaina yake ba.




#Rashuna
#Bebe'arth
#090 37093702

Free novel ne.masu bukatar paid novel dina su same ni a layina.

Katanga
Cin amana
Cikin Duniyarmu
Halittar Zuciya
[9/25, 10:49] RASHUNA: BEBEE'ARTH



Wattpad@Rashuna



KANA NAKA
(Allah na nasa )

14



"Ku kallla."Fatma tace da 'yan tawagarta, gaba ɗayansu kuwa suka juya idanuwansu ya sauka akan Sajda,tana taku ɗaiɗai cike da yauƙi da yanga wan da ya zame mata jiki domin kuwa duk in da gayu yake Sajda tasan gayu ta kuma san ta kansa. Abin da ya bawa su Fatma mamaki ba komai ba ne sai yadda Sajda ta samo mayafin da ya mugun shiga da leshin da ke jikinsu gaba ɗaya,anko ne na class mate ɗinsu, sun zaga kasuwanni da dama haɗe da super market suma da dama amma basu samu mayafin da ya mugun shiga da leshin ba kamar yadda na Sajda ya shiga, abin da suke gudu ya faru (Sajda ta fisu ɗaukan wanka) Har ta gifta su ta ankara da yadda suka zuba mata ido kamar su cinyeta ɗanya, basa shiri shiyasa bata shiga shirginsu, su kullum burinsu su fita ɗaukar gayu amman hakan ya gagara saboda ta fisu sanin takan gayun.
"Lafiya dai ko na ci muku bashi?"
" Muna mamakin yadda akai kika samu mayafin da muka gama karaɗe kasuwanni da dama ba mu samu ba."
"Hmm shine matsalarku?"
"Eh"
"To matsalarku tazo ƙarshe in sha Allah zan haɗa ku da NEEHAL COLECTION daga yanzu wahalar neman mayafai ƙare muku da yardar Allah, dan nima tun da aka haɗa ni da ita na huta, duk mayafan da ake so ana samu a gurinta ko wani irin kala ne, kuma masu kyau da ɗaukar ido cikin farashi mai sauƙi."
"Au wai kina nufin mayafin na gida ne ?"

"Eh mana ɗan hannu ne."

Amma ta iya mayafai maza maza haɗa mu da ita dan baza mu shiga gurin bikin nan ba sai da irin mayafin ki muma mu ƙure gayu.

https://wa.me/message/AD4MDTQJLXIRD1

Ku bi wannan link ɗin zai kaiku in da zakui magana da NEEHAL COLECTION daga yau matsalar mayafai ta ƙare muku zaku samu duk kalar mayafan da kuke so cikin farashi mai sauƙi ina mai tabbatar muku zaku ji daɗin muamala da ita.


****"""""
Sai da na kwana biyu ba tare da nasan in da kaina yake ba kana na farka da daddaɗan labarin cewa an gano in da Baffa yake,ashe mota ce ta bigeshi sai da ya kwana shida ba tare da yasan in da kansa yake ba,kafin ya farfaɗo shine ya gayawa mutumin in da zai samu Abbana yazo ya gaya masa dan yasan duk in da muke muna nan hankulanmu a tashe,to shine Abbana yaje asibitin da aka kwantar da shi a take ya nemi terensfer ya dawo da shi asibitin da aka kwantar da ni.
Ina farkawa Momy ke bani wannan daddaɗan labarin, ai kuwa na tashi da kuzarina tare da cewar ta rakani ɗakin da Baffan yake na ganshi, ta son samunta ne sai nayi wanka na samu ƙarfin jiki na sha ko tea ne sai muje naga Baffan,amman tasan idan ta hanani zuwa yanzun ba lallai na hanu ba,dan haka ta kamo hannuna muka fito zuwa ɗakin da Baffan yake.

Ba wani ciwo yaji ba,kansa ne ya bugu sosai shiyasa ya wahala sosai,amman yanzu an shawo kan matsalar dan gashi har magana yana samu ya yi.Ina ganinsa na faɗa jikinsa sai kuka yasa hannusa yana shafa kaina haɗe da cewa.

"Haba Amaryata ke da na sanki jaruma meye kuma na kukan?Ko so kike na janye Gwaggonki ta samu abun yi?"

Ɗagowa na yi ina share hawayena kafin nace. "Baffa kukan murnane, ya jikin naka?"
"Da sauƙi ya naki jikin?"
"Alhmdlillah."
"To masha Allah,ciwo dai ya ƙare tun da ga Baffa ya dawo da ransa ko."
Dariya nayi kafin nace."Sosai ma,daman ciwon na rashin ganinka ne,ni dama zasu taimaka su sallame ni yanzu wallahi naje gida na ɗumamo maka tuwonka dan yana nan a fridge na saka maka dan dama jikina ya bani zaka dawo gare mu."

"Ai idan suka bincika komai naki lafiya lau zasu iya sallamarki a yau ɗin.amman tuwo Gwaggonki ta rigaki kawo mini,tun da aka bada umarnin na fara cin abinci nace tuwo nake so shine tace aikuwa akwai wan da kika ajiye min dan haka saura nawa biyan bashin na tsire da Rufaidah."
Da saurina nace. "A'a Baffa na yafe wannan tsiren."
"Kwantar da hankalinki ba ni zanje ba har nan asibitin za'a kawo mana shi da daddare."

Murmushi nayi tare da tsallaen murna Kafin naji muryar Gwaggo na cewa.
"Daina murna babu wani tsire da zaki ci ke da ke fama da ulcer."Kwakkwaɓe fuska nayi kamar zan kuka Baffa yace."Kada ki ɓata hawayenki a banza tsire dai kam sai kin ci shi, haka kawai a dunga lanƙayawa mutane ciwo ace kar su ci abu, me ya koro ɗan ƙauye birni?ina to ba zaƙi da maiƙo bane haka kawai wani likita ba Allah ba ya hana amaryata ci."

Murmushi nayi jin furucin Baffa, Gwaggo kuwa bakinta ta ja tayi shiru dan wannan rigimamman tsohon ba ta da ƙarfin jaa da shi in dai akan Najwa ne,domin kuwa ko ta jaa dole ta saki amman idan ciwon Najwan ya tashi yafi kowa tayar da hankalinsa.

Momy kuwa cewa tayi na taso naje nai wanka na samu na ci wani abun,kafin likita yazo ya duba ni, muna shirin fita Abba ya shigo dan haka sai da na tsaya muka gaisa kafin mu tafi zuwa nawa ɗakin da aka kwantar da ni.


""""""
Da daddare muna ɗakin da Baffa yake gaba ɗayanmu har Abbana, tsiren da aka kawo da zafinsa muke ci ni da Baffa muna korawa da Rufaidah,nikam gurin kitse kitsen nake zaƙulowa na ci,idan ma ban gani ba Baffa sai ya sako mini a gabana,shiyasa dama na gudo nan dan muci tare,dan nasan a can wa'yannan nurses ɗin baza su barni naci ba.

Ƙofar ɗakin aka buɗe aka shigo ɗauke da sallama wacce ta saka ni ɗaga ido naga me wannan sallamar caraf kuwa sai idona cikin nasa, ganin ban
End Ads