x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 18 - KANA NAKA ALLAH NA NASA complete document

  • 51001 words
  • 54000 words
  • Out of 66841 words

Category: Love Stories

Views 295

25 Aug 2025
Start ads
After Image Ads
nufi ba, yayi mini alƙawari ne."

"Ok na ji,shige maza kije kin bar driver yana jiranki."

"Bro ka daina korata anjima zamu zo gayyarmu guda anan zamu yini."

Ta kai karshen maganar tana fita da sassarfa.



Nasrin na tafiya ya matso in da nake tsaye ya na jifa na da sanyayyen kallo kafin ya rungume ni jikinsa cikin sanyayyar muryar nan tasa yace.

"Barka da wayar gari a ranar ki ta farko cikin gidan Sulaimannn...."






"Ku kallla."Fatma tace da 'yan tawagarta, gaba ɗayansu kuwa suka juya idanuwansu ya sauka akan Sajda,tana taku ɗaiɗai cike da yauƙi da yanga wan da ya zame mata jiki domin kuwa duk in da gayu yake Sajda tasan gayu ta kuma san ta kansa. Abin da ya bawa su Fatma mamaki ba komai ba ne sai yadda Sajda ta samo mayafin da ya mugun shiga da leshin da ke jikinsu gaba ɗaya,anko ne na class mate ɗinsu, sun zaga kasuwanni da dama haɗe da super market suma da dama amma basu samu mayafin da ya mugun shiga da leshin ba kamar yadda na Sajda ya shiga, abin da suke gudu ya faru (Sajda ta fisu ɗaukan wanka) Har ta gifta su ta ankara da yadda suka zuba mata ido kamar su cinyeta ɗanya, basa shiri shiyasa bata shiga shirginsu, su kullum burinsu su fita ɗaukar gayu amman hakan ya gagara saboda ta fisu sanin takan gayun.
"Lafiya dai ko na ci muku bashi?"
" Muna mamakin yadda akai kika samu mayafin da muka gama karaɗe kasuwanni da dama ba mu samu ba."
"Hmm shine matsalarku?"
"Eh"
"To matsalarku tazo ƙarshe in sha Allah zan haɗa ku da NEEHAL COLECTION daga yanzu wahalar neman mayafai ƙare muku da yardar Allah, dan nima tun da aka haɗa ni da ita na huta, duk mayafan da ake so ana samu a gurinta ko wani irin kala ne, kuma masu kyau da ɗaukar ido cikin farashi mai sauƙi."
"Au wai kina nufin mayafin na gida ne ?"

"Eh mana ɗan hannu ne."

Amma ta iya mayafai maza maza haɗa mu da ita dan baza mu shiga gurin bikin nan ba sai da irin mayafin ki muma mu ƙure gayu.

https://wa.me/message/AD4MDTQJLXIRD1

Ku bi wannan link ɗin zai kaiku in da zakui magana da NEEHAL COLECTION daga yau matsalar mayafai ta ƙare muku zaku samu duk kalar mayafan da kuke so cikin farashi mai sauƙi ina mai tabbatar muku zaku ji daɗin muamala da ita.

Ga masu bukatar a tallata musu hajarsu kofa a bude take cikin farashi mai sauki.

#Najjwa
#Sulaiman
#Mu'azz
#BR
#09037093702/08082007142
[11/22, 08:48] RASHUNA: BEBEE'ARTH



Wattpad@Rashuna



KA NA NAKA
(Allah na nasa )
30


Kamar yadda kwa Nasrin tace gayyarsu guda suka zo,dangina da danginsu,kowa yazo ganin ɗaki kafin ya tafi,daɗinta guda daga gidan Momy aka dunga yo girkuna ana kawowa,saboda bayan zuwan su Nasrin sai ga danginsu na Fanda suma zugarsu guda sun bayyana.

Sai gab da magariba kowa ya watse sai Nauwwa kaɗai da ke jiran Najib yazo su tafi.

Bayan sallar magariba,kana muka zaga ko ina na cikin gidan naga irin tarin dukiyar da Abbana ya jibge mini. A da tun bayan da aka gama ginin gidan aka zuba musu tsadaddun furniturse da aka tashi bikin namu akace ba'a bukatar komai daga gurinmu Abbana yace bazai yuhu ba,a kwashe na ciki shi zai zuba mini komai kamar yadda ko wani uba ke wa 'ya'yansa, ni kadai Allah ya ba shi sai yanzu da twince suka zo,to su kuma ba shi da tabbacin ganin nasu auran,tun da tafiyar rayuwar ba'a tafukan hannuwanmu take ba.

Muna zama sai ga Yaa Sulaiman ya dawo, sai da suka gaisa da Nauwwa kana ya shige ciki na bi bayansa.
Ɗakin da nake tunanin nan ne na shi naga ya buɗe ya shiga nima na mara masa baya,har zai shiga toilet ya ji ƙarar buɗe ƙofa ya waigo idanuwanmu suka sarƙe guri guda,murmushin nan dai da ba ya rabo da shi ya sakar mini,kafin nawa ya biyo baya ya wara mini hannuwansa alamun na tawo gare shi,a hankali nake tafiya har ya ƙosa ya gaza haƙurin na ƙaraso ya cimmani a tsakiyar ɗakin tare da rungomo ni jikinsa tsam -tsam.

"Kin yini lafiya?"

"Lafiya lau,ftan kaima haka?"

"Alhamdlillah.Bara na yi wanka, ki koma gurin Nauwwaran kar ki barta ita kaɗai."

Ya kai ƙarshen maganar yana sassauta riƙon da yayi mini,yayin da na zare jikina na fita ba tare da na waigo ba duk da yadda nake jin idanuwansa a jikina.

****
Har nayi kwana uku gidan Yaa Sulaiman be nemi wani abu daga gare ni ba,tsakaninmu runguma ce kawai,asali ma ba tare muke kwana ba,kowa yana nasa ɗakin,bansan dai me yake nufi da ni ba na dai kawo idanuwa na zuba masa duk da ba wai na ƙagu ya nemi wani abu a gareni ba ne anman da mamaki ace lafiyayyen namiji a kawo mishi mata har tsayin kwana uku ba tare da komai ya wakana ba,ko ɗaki guda ma ba su haɗa ba. Ni da nake son yin bacci a jikin namiji dalilin da yasa nake son namiji me faɗin ƙirji kenan,ina son na shige jikinsa nayi bacci sosai a ko da yaushe sai gashi na samu namijin da ko ɗaki guda har yau ba mu haɗa ba,ƙarƙari da nayi shirin bacci na kwanta zai mini kiss a goshi ko a dukkan wani sassa na fuskata kana yamun sai da safe ya tafi ɗakinsa ya barni cikin tunani.

A yau da nake da kwana biyar a cikin gidansa yazo mini da daddaɗan labarin cewa jibi zamu tafi umara in sha Allah,duk da ina da plane ɗin zuwa amman sai azumi mukayi da Abbana zamu je gaba ɗaya hakan ba ƙaramin farin ciki ya saka ni ba,na dinga yi masa godiya da fatan gamawa da duniya lafiya.

A Ranar Lahadi jirgin da ya kwaso mu ya Lula sararin samaniya,har da Nauwwa a masu rakiyarmu nace mata.

"In sha Allah zan roƙo mana twince."

Dariya tayi saboda sanin manufata kana tace.
"Nifa ina jin alamun kamar an gamu,sai dai ki roƙo mana a samo twince ɗin 'yan maka."

Harara na galla Mata Kafin nace.

"KO an gamun zan roƙa Allah ya inganta mana ya kuma saka twince ne."

"To idan kin tashi ki roƙa mana duka."

Ban tsaya bata amsa ba sakamakon Yaa Sulaiman da ya jaa hannuna ashe ana ta kiran sunan passingers, sai hannu kawai na ɗago musu muka nufi in da jirgin yake.

Takwas na dare daidai jirginmu ya sauka a filin hawa da sauka na jiragen Madinah.

Mota muka hau ta sauke mu a Hotel mafi kusa da masallacin Annabi Muhammad (S.A.W).

Rashin sa'ar da aka samu ɗaki ɗaya ya rage kuma falle ɗaya ba kamar yadda yaso samun falle ɗaiɗai ko ciki da falo ba.

Abinci ya fara zama ci,nikam toilet na shiga nayo shirin baccina na gabatar da sallar isha'i a ciki,har Yau dai ban fara gabatar da sallar shafa'i da wutiri ba, da na fara sai na daina nazo nace kuma sai nayi aure zan fara, amman in sha Allah ina nan zan tsayar da ita domin dacewa da gwaggaban lada, na dai samu na tsayar da yin walaha,
Ina idar da sallar nazo na haye gado idanuwana cike da bacci.

"Babu abin da zaki ci ne?"

"Uhmmm ban jin yunwa."
Na faɗi hakan idanuwana a lumshe.

"A'a ki dai daure kisa wa cikin naki wani abun."

"Allah da gaske nake ba na jin yunwa."
"OK"
Yace,ya na tashi ya shiga toilet, wanka ya yo ya shirya a ciki shima kana ya fito Cikin tunani da taraddadin ta yadda yau zai iya bacci a ɗaki ɗaya da wani.
Sallaya ya shimfiɗa ya tayar da sallar isha'i kafin ya ɗora da shafa'i da wutiri.

Cikin dare sau kusan biyu ina farkawa Ina ganinshi a zaune,a farkawa na u kun ne na tambaye shi me yasa bai yi bacci ba yace da ni ya kasa nace.
"To saboda me?"
Yace.
"Tun ina yaro ba na iya bacci idan da wani a ɗakin da nake,da baccin ya ɗauke ni nake farkawa."
"Allah buwayi, bara na ɗauro auwala muyi sallah nima baccin ya sake ni."

DA na ganni a tsakiyar Rauda kuka na fashe da shi,ina shafa kabarin Manzo (S.A.W)(Madinah garin manzo Allah kA kiramu wannan gari Naka dan darajar manzon Allah SAW dan kaunar DA ke tsakaninku Amin ya Rabbi. )

Mun zaga garin madinah sosai,mun kuma yi ibada yadda ya kamata,tun washe garin da muka kwana a garin ya sama mana wani ɗakin ciki da falo ya bar mini cikin shi yake kwana a falon,zamu yini mukai dare tare idan anzo bacci kuma kowa ya kama tasharsa.
Satinmu guda a madina muka nufi mikati domin ɗaukar haramar yin Umara,kowa ya fito cikin haraminsa kana muka nufi garin makkah adduo'i dauke a bakunanmu.

Yaa Sulaiman dama ya riga ya kama mana ɗaki ta online,a hotel mafi kusa da masjidul Haram,falo ne ƙaton gaske da two bed rooms a ciki,kayanmu kawai muka a jiye muka juya masjidul haram.
Da addu'a a bakunanmu muka shiga gurin da yake da matuƙar haske da ni'ima,gurin da yake sanyaya rai da zuciya.
Sai da na zubar da ƙwalla tsabar farin cikin yau gani ga ka'aba.Muka hau ɗawafi kowa yana kai kukansa gurin da za'a share masa a biya masa bukataun da ya roƙa har da ƙari.Bayan mun gama muka gabatar da nafila raka'a biyu a bayan muƙamu Ibrahim Sannan muka wuce yin sa'ayi,bayan an gama mazanmu da matanmu muka cike ibadarmu da yanke gwargwadon abin da shari'a ta lamunce mana.

Washe gari ya Kira Mu'azz yazo ya ɗauke mu zuwa gidan da suke zaune,kallo ɗaya nayi masa ban ƙara kallonsa ba sabo da yadda zuciyata ta dinga bugawa saboda tsananin kyaun da naga ya ƙara fatarsa ta ƙAra gogewaa,zuciyata ta dinga buga tsalle a kirjina saboda kasancewarmu guri guda nidai ina ta ta'awwizu har muka ƙarasa gidan.

Plart ne guda biyu,kowa da nasa,ya anshi key a hannun Mu'azz din ya bude nasa plart din muka shiga,ina ji yana tambayarsa Zareenah yace tana india yin wani course.

Falo ne ƙato sai two bed rooms a ciki,ko ina fes fes da shi da alamu a kwai masu gyaransa a ko da yaushe. Ina ganin ya buɗe ɗaya ɗakin ya shiga ciki nima na buɗe ɗayan na shiga idanuwana cike da bacci,da ƙyar na samu na sauya kaya zuwa sasasauƙar doguwar riga ta bacci na kwanta.

Baccina yayi nisa na ji kwanciyar mutum a jikina a ɗan razane na wara idanuwana suka sauka akan Yaa Sulaiman,gira ya ɗage mini haɗe da sakin murmushi Kafin yace.

"Ai kin gama cin bashin naki yarinya,biya kawai ya rage miki."

Gabana ne ya faɗi cikin in inar da ta same ni a yanzu nace.

"Ban ga ne ba."

"Zaki gane ne."

Ya faɗa yana shinshinar wuyana,kafin ya cirani cak ya nufi ɗakinsa da ni,sai da ya sauke ni kan tattausan faffaɗan gadonsa kana yace.

"Na ci burin karɓar budurcin matata a wannan gadon,na kuma roƙi Allah yasa zuwan farko na zira ƙwallona a raga."

Sunkui da kaina nayi cike da kunya,har lokacin ƙirjina na dakan lugude cike da tsoro da taraddadin yadda wannan al'amari zai kasance.

"Ki fa daina tsoro dan yau babu abin da zai tsayar da ni,dan hakurina ya riga ya kare."
Ya faɗa yana shinshinar wuyana tare da shafa dukkan wani sassa na jikina,nikam ban da kyarma babu abin da jikina yake.

Bakinsa ya tsayar akan nawa kamar zai yi kissing ɗina sai kuma ya dakata ya ɗago ya kalle ni idanuwanmu suka gauraya guri guda,ban da tsoro babu abin da ya gano cikin nawa idon,shikam fitina ce kala kala na hanga cikin nasa idanuwan.

"Kema kina son wannan abun ne?"

Da sauri na girgiza masa kaina saboda tsabar yadda nake a tsorace ina jinsa ya sauke ajiyar zuciya da alamu bai ma san yana riƙe da ita ba kafin yace.

"Na jima ina roƙon Allah ya bani matar da wannan abin bai dame ta ba, dan nikam a ƙazanta na ɗauke shi,da kuma al'adun turawa da muka ɗauka muka aza bisa kawunanmu, dan nidai in kika cire wannan kiss ɗin."
Ya manna min kiss akan laɓɓana da kumatuna da goshina kafin yaci gaba.
"Babu wani kiss da zan yi bayan shi,wai naga ashe kiss ɗinma kala kala ne ko wanne da sunansa ko?"

Ƙasa na kuma yi da kaina ba tare da na ba shi amsa ba,to nace masa me? Ya barni ma da tsoron da ke ƙara shigata a ko wani second.

A hankula ya bi da ni cikin lallashi da lallamawa kafin akai in da notinan kansa suka kwance gaba ɗaya,ya manta kansa bare ma ya tuna da cewa farin shiga ce ni a yau yau ɗin nan zan san wannan al'amari me girma.

Na jigatu babu ƙarya bayan ya gama sauke mini buƙatunsa na shekaru da dama tun daga ranar da ya fara balaga,ƙirjina,cinyoyina da gurin gaba ɗaya raɗaɗi suke mini,yadda Nauwwa ta bani labari ba haka na ji ba,tace wlh ita duk yadda ake zuzuta azabar daren farko ba haka ta ji ba, kawai ya danganta da yadda namiji ya jewa mace,wasu mazan sukan yiwa mace zuwa ɗaya ne,wasu kuma sukan yi kwanaki ana buɗa gurin a hankula wananna kam sune baza su ɗorar da wahalarsa ba tun da an raba musu zafin ba na lokaci guda aka musu ba amman fa wannan sai maza masu haƙuri irin Najib ɗin Nauwwa,Amman yadda ake faɗarsa a novel ban taɓa ji ko ganin haka a gaske ba,dan nikam har yau ban taɓa ganin wacce ta suma ba a daren farkonta sai a novel.

Shi ya haɗa mini ruwa me zafi ya taimaka mini na tsarkake jikina,na gasa shi sosai yadda ya kamata,bayan na gama tsane jikina na saka wata sassauƙar rigar baccin ina ƙoƙarin kwanciya ya shi go riƙe da mug sai tiriri yake. Shayi ne haɗin kauri,ya san ni da son murtuk ɗin shayi shiyasa yamin irin haɗin ba musu na ansa na fara sha a hankula,yana zaune yana ta kallona har na gama sha,ya bani magani na sha wan da zan ji sauƙin jikina kana na kwanta ya sauke mini pick a kumatu.

"Allah yayi miki albarka, Allah kuma yasa na yi babban dashe me albarka a mahaifarki, tabbas da ace mata da yawa sun san kima da mutumcin da martabar da suke in sun kawo wa mazansu budurcinsu da da yawansu ba su wasarere da shi ba,ba su bayar da shi a banza ba,gurin da ba'a san daraja da mutumcinsa ba.Ke dai kam babu abin da zance da ke,sai dai Allah ya jiƙan Ummanmu ya kai lada kabarinta,ya ƙarawa Abbanmu da Baffanmu lafiya da tsayin rai me amfani yayi musu sakamako da gidan aljanna."

"Amin."

Nace ina matuƙar jin daɗin addu'arsa har cikin raina.

To ban da abin wasu matan ma, ni banga abin daɗi a wannan abun ba ban da wahala da har zan bayar da kaina a banza ba,Allah na gode maka da ka tsare mini mutumcina ka nufe ni da kawowa mijina shi har na samu tukuicin add u'a wa iyayena.


Sati biyu muka ƙara ya na gwangwaje amarcinsa kafin mu nufi sieria can dangin Mamana.
A sati biyun da muka yi tun ranar da Mu'azz ya sauke mu ban ƙara sanya shi a idanuwana ba,ba ya shigowa idan ma magana zasu yi sai dai su haɗu a waje,lokacin kuma da zamu fita baya nan yana asibiti har mu dawo,wani zubin ma a can asibitin yake kwana,sai a ranar da jirginmu zai tashi zuwa sieria ya kaimu airport.

Ya na tsaye jikin motarsa muka fito,idanuwanmu suka sarƙe guri guda,yayin da ya lumshe nasa idanuwan ya kuma warasu cikin nawa idon,nikam kamar wani magnent na kasa cire nawa idon daga cikin nasa duk da yadda zuciyata ke buga tsalle a ƙirjina,sai da ƙyar na yakice su daga kansa saboda yadda muke ƙara kusanto gaban motar.
Yayin da nake ta faɗin.
"Astagfirillah Allah ka yafe mini,ba laifina ba ne laifin zuciyata ne,Allah kar ka bata ikon sarrafa ni a ko da yaushe,ka ɗorani a kanta kasa kuma na fi ƙarfinta Amin."

Sai da muka ɗauki hanya muna tafiya ya dubi Yaa Sulaiman yace.

"Na rasa me na yiwa matarka Bro ba ta kula ni."

Kallona Yaa Sulaiman yayi cike da tuhuma,na numfasa nace.

"Allah Man." Sunan da nake kiransa kenan yanzu da ya titsiyeni da sai na daina kiransa da Yaa Sulaiman, nace zan dinga kiransa da MAN yayi masa? yace "Eh to ba laifi." Nace."Be yi ba kenan a sauya?"
"A'a yayi mana matar Man" Ya faɗa haɗe da jan karan hancina.

"Idan aka gaishe shi ba ya amsawa."

Na ƙarasa maganata,kallonsa Yaa Sulaiman yayi kana yace.

"To ka ji laifinka."

"To shikenan mutum idan yayi abu sau ɗaya ko da yaushe hakann ne zata kasance?"

Saboda kawai na tsagaita maganar nace da shi.
"Ina yini?"
Saboda ni kaɗai nasan yadda Accenrt din muryarsa ke ragargaza zuciyata,bacin haka sau nawa zanga su Zuwaire na gaishe shi sai dai ya ɗauke kai kawai idan ni yayi mini sau ɗaya?

"Ki bar gaisuwar ki yanzu saboda ni na roƙa ki barta sai haɗuwarmu ta gaba."

Daga haka babu wan ya sake cewa komai har muka isa airport ɗin,sai muryar Man da ke ta shi a cikin motar yana amsa wayar Miqdad abokin aikinsa.


Su Inna da Kawu sun yi matuƙar farin cikin ganinmu,har suka rasa in da zasu sakamu tsabar murna da farin ciki,kwananmu uku,duk gurin da ya kamata muje munje Man yayi musu alkhairi me girma.A ranar da muka sauka hotel ya so kama mana,Inna tace sam ba wannan zancan ga wadataccen muhalli babu wani hotel da zamu tafi.
Ɗaki ne guda me kyau da tsari aka bawa Man,duk da Inna ta so korani gurinsa a ranar nace mata ai ba ya iya bacci da wani a kusa da shi,tace.
"Ikon Allah,Allah buwayi kenan, me halittar bayinsa kala-kala."
Tun daga ranar muke kwana tare da ita,mu raba dare muna hira tana bani labarin mahaifiyata,ƙuruciyarta da komai nata da yadda take matuƙar son iyayanta da 'yan uwanta,har zuwa yau da muka yi sallama da su zamu tafi cike da kewa.
Man yayi musu alkhairi sosai,haka nima na basu
End Ads