bai yanke kiran ba, ɗagota nayi scring ɗin yayi raga-raga.
"Cwtyyy me ya faru,shirun yayi yawa."
Kara wayar nayi a kunne kafin nace.
"Bani mintina ashirin zan kira ka."
"Na baki hamsin ma ranki ya da ɗe."
"Tom godiya nake." Daga haka na katse kiran duk da ban yi tunanin wayar zata dannu ba.
Kallonsa na yi,yana nan tsaye ƙiƙam kamar an dasa shi fuskar nan a tamke,na ce.
"Ka je sa shen Momy ka jira ni,yanzu zan kawo maka."
Dan na tabbata Baffa yana gab da shigowa kuma bani da amsar da zan ba shi idan ya tarar da mu a haka,ba ma ni da ita bare na ba shin."
"Zan jira ki a nan."
Ya faɗa yana ƙarasawa kan cussion ya zauna.
Kicin kawai na nufa,dan idan na tsaya magiyar yaje ya jira nin ba lallai ya tafin ba kuma na ƙara ɓatawa kaina lokaci.
Sai da na fara buɗe fridge na ɗauki ruwa me sanyi na sha, ina jin yadda wani abu me ɗumi da ke tsirgawa ta marata,wani irin filing nake ji akan Mu'azz da ban san ina da shi ba, wannan wata iriyar masifa ce? Dole na gujewa haɗuwata da shi idan ina son kaina da lafiya amman ta ya ya?.......
"Ku kallla."Fatma tace da 'yan tawagarta, gaba ɗayansu kuwa suka juya idanuwansu ya sauka akan Sajda,tana taku ɗaiɗai cike da yauƙi da yanga wan da ya zame mata jiki domin kuwa duk in da gayu yake Sajda tasan gayu ta kuma san ta kansa. Abin da ya bawa su Fatma mamaki ba komai ba ne sai yadda Sajda ta samo mayafin da ya mugun shiga da leshin da ke jikinsu gaba ɗaya,anko ne na class mate ɗinsu, sun zaga kasuwanni da dama haɗe da super market suma da dama amma basu samu mayafin da ya mugun shiga da leshin ba kamar yadda na Sajda ya shiga, abin da suke gudu ya faru (Sajda ta fisu ɗaukan wanka) Har ta gifta su ta ankara da yadda suka zuba mata ido kamar su cinyeta ɗanya, basa shiri shiyasa bata shiga shirginsu, su kullum burinsu su fita ɗaukar gayu amman hakan ya gagara saboda ta fisu sanin takan gayun.
"Lafiya dai ko na ci muku bashi?"
" Muna mamakin yadda akai kika samu mayafin da muka gama karaɗe kasuwanni da dama ba mu samu ba."
"Hmm shine matsalarku?"
"Eh"
"To matsalarku tazo ƙarshe in sha Allah zan haɗa ku da NEEHAL COLECTION daga yanzu wahalar neman mayafai ƙare muku da yardar Allah, dan nima tun da aka haɗa ni da ita na huta, duk mayafan da ake so ana samu a gurinta ko wani irin kala ne, kuma masu kyau da ɗaukar ido cikin farashi mai sauƙi."
"Au wai kina nufin mayafin na gida ne ?"
"Eh mana ɗan hannu ne."
Amma ta iya mayafai maza maza haɗa mu da ita dan baza mu shiga gurin bikin nan ba sai da irin mayafin ki muma mu ƙure gayu.
https://wa.me/message/AD4MDTQJLXIRD1
Ku bi wannan link ɗin zai kaiku in da zakui magana da NEEHAL COLECTION daga yau matsalar mayafai ta ƙare muku zaku samu duk kalar mayafan da kuke so cikin farashi mai sauƙi ina mai tabbatar muku zaku ji daɗin muamala da ita.
Ga masu bukatar a tallata musu hajarsu kofa a bude take cikin farashi mai sauki.
Tun da dai ga shinan in da nake ganin na samu mafaka ya biyo ni har nan,dama ban fito shan ruwan ba ƙarƙari in ya gaji da tsaiwar ya juya ya fita,ƙishirwar nan dai ba ta kyauta mini ba da ta addabe ni ta saka ni fitowa.
To ko dai Momy ko Yaa Sulaiman zan gayawa? To kuma nace musu me? Tun da dai ba wani abu yayi mini wan da bai dace ba,ko ya gaya mini maganar da ba ta kamata ba,ƙarƙari yasa ni nayi masa girki,kuma wannan ma Momy na saka ni nayi masa.
Magana a taƙaice yake mini ita,ban taɓa kama shi yana kallona ba sai dai ni na saci kallonsa ni kaɗai kenan nake karɓar sabon yanayi a kansa,zuciyata kawai ke doka masa? To idan hakane me zan ce da Momyn ko Yaa Sulaiman ɗin?
Hakan yana nufin,haka zan ci gaba da jure abin da nake ji game da shi har zuwa lokacin bikinmu,tun da bikinma 'yan satittika ya rage na samu su koma in da suka fito,na huta da wannan jarabar,koma ba su koma ba duk tsaurin idonsa yana ganina a matsayin matar wansa bazai cigaba da takura mini kamar yanzu ba.
Ina ta wannan tuna ninnikan har na samu na gama haɗa masa coffee ɗin na ɗauko sabon tea flask mai matuƙar kyau na zuba masa a ciki,ina tunkaro in da yake zaune ƙirjina na mun bugu, yau ɗin yayi masifar kyau cikin wata arniyar blue ɗin jallabiya ta karɓi fatarsa fiye da yadda kuke zato,kwantacciyar sumar kansa da sajensa sai ƙyalli suke gwanin sha'awa, ya saya idanuwansa da siririn glass shima blue da ya ƙara ƙawata fuskarsa, ga ƙamshin turaransa da ya kama falon gaba ɗaya.
Ina gab da ƙarasawa in da yake zaune naga ya miƙe, ashe kenan yana ankare da ni yayi kamar bai ga fitowata ba,miƙa masa flask ɗin nayi yasa hannu ya ansa haɗe da sanya mini wata kyakkyawar waya a hannu kana ya taka ya huce,wayar na ɗago ina kallo haɗe da bin bayansa da kallo,kana na taka da 'yar sassarfa na bi bayansa lokacin har ya kai gab da ƙofa nace.
"Ka ga."
Juyowa yayi idanuwansa ba su sauka a ko ina ba sai cikin nawa wan da hakan yasa zuciyata dokawa tayi tsalle kamar zata rabu da ƙirjina,cikin rawar murya saboda yadda nake jin idanuwansa a ko wata gaɓa ta jikina nace.
"Me za'a yi da wayar?"
"Wullarwa za'ayi."
Amsar da ya bani kenan ya buɗe ƙofar ya fice,tsintar kaina nayi da sakin murmushi sabo da yadda ya daƙuna fuska da zai bani amsa ba ƙaramin ƙarawa fuskarsa kyau yayi ba.
Kan kujera na zube na tafi tunanin da bazan ce ga na meye ne ba, kawai dai jin jikina nake a mugun mace,nayi nisa cikin tunanin na ji muryar Baffa yana.
"Ke Najjwaa wani irin bacci kike ido biyu haka?"
Tashi nayi ina miƙa cikin macewar jiki nace.
"Nima ban sani ba Baffa."
"To Allah ya kyauta, maza je ki ki kwanta."
"To Baffa sai da safe." Na faɗa ina rufe bakina sabo da hammar da ta kubfce mini.
"Allah ya tashe mu lafiya,ki tabbatar kin yi addu'a kafin ki kwanta."
"In sha Allah Baffa."
Sai da yaga shigewata ɗaki kana ya kashe fitilun falon ya nufi ɗan kwaridon da zai Sada shi da nasa ɗakin.
Ina shiga ɗakin zubewa nayi akan gado na ja bargo na rufe har kaina,na rasa wani irin yanayi nake ji a jikina, wannan masifa da me ta yi kama? Ko yaa Sulaiman ɗin ji nayi bana son jin muryarsa duk da nace zan kirasa, so samu dai Mu'azz ya kira ni mu raba dare muna waya ina ji a jikina kamar bazan gaji da hakan ba,wayar da ya bani na ɗago ina dubata naga ba sim a ciki, amman tayi kyau sosai, hancina na kaita na shaƙi ƙamshin jikinsa da ya shafa mata.
Washe gari da safe haka na tashi sukuku da ni, dan ko karyawa ban yi ba na baro gidan, dan son samu na zuciyata na ganshi,ina jin kamar hakan zai rage raɗaɗin
ƙuncin da na shiga jiya cikin dare.
Driver na saka ya sauke ni a makaranta dan tuƙin ma ji nayi sam bazan iya shi ba,Allah yasa ma na iya rubuta abin kirki a jarabawar.
Da yake paper ɗaya ranar zamu zana ba mu wani jima ba muka fito na bi Nauwwa gidanta a can na samu na ci abinci, ai ina jin Najib ba ya nan yayi tafiya nace bazan koma gida ba,ba sai na ganshi shegiyar zuciyar ke zillo kamar zata fito ba, to na guje masa sai inga yadda za tayi.
Ba musu ko jaa in ja kamar yad da muka saba idan Najib ba ya nan tace na taya ta kwana wannan karan na amince, sabo da ni kaina so nake na bawa gidan space ko na samu sauƙin abin da nake ji, waya na yiwa Momy dan gidan ma sam ji nayi ban son komawa nace Nasrin ta haɗo mini kayana driver ya kawota gidan Nauwa ta kawo min, wayar Momy ta bawa Nasrin ɗin na gaggaya mata abubuwan da za ta ɗauko mini kana ta bawa Momy wayar nace.
"To Momy alhakin gayawa Baffa da Gwaggo yana wuyanki, dan kashe wayata zan yi wallahi."
Ban jira cewarta ba na kashe wayar ina dariya dan na jiyo sautin dariyarta itama, kashe wayar tawa nayi da gaske dan nasan halin Baffa yana iya kirana yace na dawo, ni bansan ya zaiyi idan nayi aure ba, ba ya ƙaunar yaga naje wani guri na kwana,ko ɓangaren Momy idan na kwana acan to ba da saninsa ba ne da bazai barni ba,dan akwai ranar da har bacci na fara yasa aka taso ni.
'Yan kwanakin da nayi gidan Nauwwa na samu sakewa sosai tun da ba ganinsa nake ba, wayar da ya bani ma a can gida na baro ta saboda kar ta dinga tuna mini da shi,na bada tawa aka gyara mini naci gaba da amfani da aba ta tun da ina son kayata.
Ranar friday Yaa Sulaiman yace mini zai zo da yamma ranar Sunday da yamma sai ya koma,dama tuni na sanar masa ina gidan Nauwwa duk da ya so na koma gida yadda zamu fi jin daɗin sakewa nace bazai yuhu ba, dan Baffa ma da ya matsan na dawo gida plane muka haɗa da Nauwwa na bata wayar ta roƙe shi akan ya barni ba ta da lafiya ne anman tana jin sauƙi in sha Allah zan taho shine muka samu lafiya.
Yau ta kama Friday ɗin kuma aka ci sa'a ranar bamu da paiper,ranar monday zamu zana paiper mu ta karshe,dan haka da wuri na gama yi masa komai na tarɓarsa.
SULAIMAN
Jirginsu na gab da tashi ya kira Mu'azz ya gaya masa.
Kamar ko da yaushe kuwa jirgin nasu na sauka a filin jirgi ya samu Mu'azz ɗin.
"Idan na tafi naga wan da zai zama driver
ɗinka."
"Matata mana,yau dinma kawai dan ban son wahalar da ita ne tun da kana nan."
Kasan ransa kuwa ba wannan dalilin ne ya hana shi cewa tazo daukarsa ba illa yad da yake jin tsananin kewarta zai iya rungumeta abin da sam ba dabi'arsa ba ce shiyasa yake kaucewa hakan,ji yake kamar ya janyo satika biyun da suka rage na bikinsu ayi kowa ya huta.
Matata ɗin da ya faɗa ya tuna masa da ita, yau kusan kwana biyar bai ganta ba,dan ya jajje nemanta ba ya ganinta,coffee ɗin da tayi masa ranar nan ya matuƙar jin daɗinsa abin da yasa kenan yake so tayi masa dan yana masa ɗanɗano da ƙamshi ɗaya da wan da ya saba sha a saudiyya,amman yayi zarya a gidan kusan sau nawa ba ya ganinta,kuma bai tambayi kowa ba haka ya dinga maleji da na Nasrin dan ya zamar masa jiki shan coffee zai iya yini yana sha ba tare da ya nemi wani abinci ba,kunun madara kuwa tun da yasa Nasrin tayi masa sau ɗaya ya kusa amai daga kurɓa sau ɗaya ya haƙura da sha,amman da zai samu irin natan zai so hakan.
Sulaiman ɗin ne ya an shi tuƙin ya cewa Mu'azz.
"Na ajiyeka gida ko mu wuce tare?"
Sauke masa idanuwansa yayi alamun tambayar ina yake nufin zasu je ɗin.
"Zan fara tsayawa gurin Najjwa ne."
Jinjina masa kai yayi alamun su je ɗin.
Ya na karyo kwanar layin gidan Nauwwa ya kira ni a waya akan ga shinan ƙarasowa dan haka na tashi na ƙara gyaggyarawa,ya na daidaita parking ya kuma kirana na fito, bai kai ga fitowa daga cikin motar ba na fito haɗe da ƙwanƙwasa glass ɗin motar,sai kwa gashi zuu yayi ƙasa ya zuge,zuciyata ce tayi wani irin dokawa na jaa baya da sauri ina danne saitin zuciyata.
Ban tsammaci ganinsa ba wallahi, ban da naci kuma irin na idanuwana basu sauka a ko ina ba sai a kansa, rigar da ke jikinsa ta kama shi ta fitar da ainiyin surarsa ta ƙarfafan maza, yayin da wuyan rigar ya bayyana saman faffaɗan ƙirjinsa me cike da gargasa.
"Ka gani ka tsorata mini mata da fuskar nan taka ta shanu,ina ga Zareena ce kawai ba ka tsoratar ba sabo da kasan matarka ce."
Murmushi kawai yayi idonsa akan wayar da ke hannunsa yayin da Sulaiman ya ɓalle murfin motar ya fito, ina tsaye ina daidaita nutsuwata da son lallashin zuciyata ta daina mini zillon da take mini.
Murmushi muka sakarwa juna yayin da na yi gaba ya biyo bayana dan ban jin zan iya furta ko da kalma ɗaya ce alhalin ina tsaye a nan gurin,dan zuciyata ta ƙi saurarata bare ta bani haɗin kai.
A siti room na sauke shi muka gaisa,kana Nauwwa tazo itama suka gaisa,na kawo masa abin motsa baki,yana ci muna taɓa hira jefi jefi.
Can aka kirasa a waya sai naji yace.
"Nima yau ban samu kunun madarar ba."
Can kuma naji ya kuma cewa.
"Ba fa zaka mayar mini da mata kuku ba, kai wa yace ka auro rainon madara?"
Sai kuma ya kuma cewa.
"Ok ba don halinka ba." Kafin ya ajiye way ar ya kalle ni yace.
"EL ne, wai ki daure ki haɗa masa coffee."
Ana gab da kiran sallar magariba mu kai sallama, har lokacin yana lalllashina nazo mu koma gida ni kuma na ƙiya,daga bakin gate na cage dan naƙi ƙarasawa bakin motar ɗin tun da Nauwwa tayi gaba da kwandon abincin da na haɗa masa,da tea flask ɗin coffee ɗin Mu'azz ɗin zata je su gaisa.
Daga nan gurin muka ƙara yin sallama ya shige ya tafi mu kuma muka koma ciki ni da Nauwwa.
"Hali dai yana nan bai sauya ba ashe? Na zata da yayi auran ya sauya tun da naga Yaa Muhd tun da kuka fara soyayya ya fara sauyawa daga ɗaure fuskar da yake mun,ke kinga da yadda aka amsan gaisuwa kamar wani basarake."
"To ai ke kinci sa'a ma tun da ya amsa gaisuwarki, ni ranar da na fara gaishe shi yi yayi kamar baisan ina yi ba,ni kwa na ƙudiri aniyar ba za'a ƙara na biyu da ni ba, sai kuma ga shi da kansa ya zo ya na buƙatar gaisuwar nace ai shi zai gaishe ni tun da a matsayin yayarsa nake."
"Cabf har kika iya kallonsa kika gaya masa haka? Ni fa mugun shakkarsa na ji ina yi, gaskiya ya fi Yaa Sulaiman buɗewar jiki da mazantaka."
"Hmmm nima naga ƙarfin halina a lokacin,kawai dai dan bana son disgi ne, amman mutumin da tun ranar da na fara ganinsa zuciyata ta doka ta fara zillo ina jin kamar har yau ba ta koma matsugunin da take a da ba,yanzu haka har yau tsalle take a ƙirjina tun da na gan shi ɗazu,abin da nake ta gujewa kenan shiyasa na ƙi komawa gida.
"Ban gane karatun naki ba Najj yi mini fashin baƙi."
"Sabo da kar na ganshi zuciyata tayi ta zillo na ƙi komawa gida,bazan ɓoye miki ba Nauwwa tun ranar da kika bani labarinsu zuciyata ta fara dokawa sunansa,na ji ina mararin son ganinsa,san da Yaa Sulaiman yazo sai da nayi suɓutar bakin tambayar Momy ina MU'AZZ,tun ranar kwa da idona ya sauka a kansa na kasa samun nutsuwar zuciyata na rasa wannan masifa."
"Idan na fahimci maganarki Najj MU'AZZ ki ke so ba SULAIMAN BA."
Cikin matuƙar tashin hankali da ruɗa ni na kalleta nace........
"Ku kallla."Fatma tace da 'yan tawagarta, gaba ɗayansu kuwa suka juya idanuwansu ya sauka akan Sajda,tana taku ɗaiɗai cike da yauƙi da yanga wan da ya zame mata jiki domin kuwa duk in da gayu yake Sajda tasan gayu ta kuma san ta kansa. Abin da ya bawa su Fatma mamaki ba komai ba ne sai yadda Sajda ta samo mayafin da ya mugun shiga da leshin da ke jikinsu gaba ɗaya,anko ne na class mate ɗinsu, sun zaga kasuwanni da dama haɗe da super market suma da dama amma basu samu mayafin da ya mugun shiga da leshin ba kamar yadda na Sajda ya shiga, abin da suke gudu ya faru (Sajda ta fisu ɗaukan wanka) Har ta gifta su ta ankara da yadda suka zuba mata ido kamar su cinyeta ɗanya, basa shiri shiyasa bata shiga shirginsu, su kullum burinsu su fita ɗaukar gayu amman hakan ya gagara saboda ta fisu sanin takan gayun.
"Lafiya dai ko na ci muku bashi?"
" Muna mamakin yadda akai kika samu mayafin da muka gama karaɗe kasuwanni da dama ba mu samu ba."
"Hmm shine matsalarku?"
"Eh"
"To matsalarku tazo ƙarshe in sha Allah zan haɗa ku da NEEHAL COLECTION daga yanzu wahalar neman mayafai ƙare muku da yardar Allah, dan nima tun da aka haɗa ni da ita na huta, duk mayafan da ake so ana samu a gurinta ko wani irin kala ne, kuma masu kyau da ɗaukar ido cikin farashi mai sauƙi."
"Au wai kina nufin mayafin na gida ne ?"
"Eh mana ɗan hannu ne."
Amma ta iya mayafai maza maza haɗa mu da ita dan baza mu shiga gurin bikin nan ba sai da irin mayafin ki muma mu ƙure gayu.
https://wa.me/message/AD4MDTQJLXIRD1
Ku bi wannan link ɗin zai kaiku in da zakui magana da NEEHAL COLECTION daga yau matsalar mayafai ta ƙare muku zaku samu duk kalar mayafan da kuke so cikin farashi mai sauƙi ina mai tabbatar muku zaku ji daɗin muamala da ita.
Ga masu bukatar a tallata musu hajarsu kofa a bude take cikin farashi mai sauki.