x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 7 - KANA NAKA ALLAH NA NASA complete document

  • 18001 words
  • 21000 words
  • Out of 66841 words

Category: Love Stories

Views 306

25 Aug 2025
Start ads
After Image Ads
san shi ba sai na ɗauke nawa idon daga kansa,ganin yadda kowa ke sakan masa murmushi,shi kuma yana binsu
ɗaya bayan ɗaya yana gaisarwa,haka ma suka gaisa da Baffa cike da ƙauna yana tambayarsa jikinsa, Baffan kuma ke ce masa baya gajiya ganin ledojin da wani ya shigo da su ya ajiyesu hakan sai naji yana ƙaryata tunanin da nai akan ko likitan da ke duba Baffa ne?

Baffa ne ya fitar da ni daga tunanin nawa ta hanyar cewa.
"Najwa ga Yayanki nan Sulaiman ɗan wajen Momynki Hasiya."

Kallonsa na kuma yi a gain dai idanuwanmu suka kuma gaurayewa guri ɗaya, alamu ke nan idonsa a kaina yake.Naiver shiyasa naga yana ɗibar mini kamanni da Yaa Muhd mai makon na gaishe shi sai na mayar da idanuwana kan Momy nace.
"Momy to ina EL MU'AZZ?"
Ganin yadda idanuwa suka yo kaina gaba ɗaya yasa na gane aikin da na ɗebowa kaina to me ya kaini wannan tambayar? Na rasa me yasa tun da Nauwwa ta bani labarinsu sunan ya tsaya mini a zuciyata na kuma zaƙu da son ganin mamallakin sunan.

"Dama kin san shi ne?"
Momy ta jefo mini tambayar.
"Um um Nauwwa ce dai ta bani labarinsu ta kuma ce EL MU'AZZ suna ɗiban kamanni da Yaa Muhd sosai." na faɗi hakan dan wanke zargi kawai ba wai dan hakan Nauwwan ta gaya mini ba."

"Ai kuwa Nauwra ba ta san kamanni ba, Son shi ke kama da Muhd sosai ba MU'AZZ da ko hanyar kama ba su haɗa ba."

Mayar da idanuwana nayi kan fuskarsa har lokacin idanuwansa suna kaina nima kuwa na hau ƙare masa kallo duk da yadda naji yanayin jikina na sauyawa saboda irin kallon da yake mini,ga gabana da ke ta faduwa bazai wuce nasaba da fuskar Yaa Muhd da nake gani cikin tasa ba.

Tabbas suna kama da Yaa Muhd, wani ma zai iya rantsuwar uwa ɗaya ce ta haife su."

Cikin rawar harshen da na tsinci kaina a ciki na furta masa. "Ina yini?" Ko zan samu tsagaitawar wannan kallon da yake mini.

"Lafiya lau,ya jikin naki?" Ya faɗa da wani karyayyan harshe.
"Alhmdlillah" Nace ina kautar da kaina gefe dan wannan kallon nasa kuma ya ishan. Muryarsa na tsinkaya yana cewa Momy zai huce cikin raina nace."Ai gara ka wuce ɗin ko na huta da wannan kallon naka." Sai kuma naga sun fita tare da Mom ɗin bayan yaiwa su Abba sallama da neman karin lafiya ga Baffa.



SULAIMAN

Ganin da ya yi mata a sarari sai yaga ta fi kyau akan a hoton, har cikin zuciyarsa yake jin cewa tabbas ya samu matar aure, domin kuwa sonta da ƙaunarta ba su shigesa da sauƙi ba a tun san da ya fara sauke idanuwansa akan hotonta.

"Momy nikam na samu matar aure."
"To Alhmdlillah,a ina ɗiyar tawa take?"
"Najjwa ce Mom ina sonta sosai."
Ya faɗa haɗe da danne saitin da zuciyarsa take, sororo Mom tayi tana kallonsa,tabbas tana matuƙar sha'awar Najwa ta zamo sirikarta, amman ba Sulaiman take wa sha'awarta ba MU'AZZ ne dan ta yankewa ranta duk ranar da ya sako ƙafarsa garin nan bazai koma ba sai da auran Najwa,zata roƙi Abba alfarmar ya ɗaura aurensu tasan bazai ƙi yi mata ba,Najwan ce tarkon da take ƙoƙarin jefawa MU'AZZ ko zata ƙwato shi daga hannun yahudawan mutanan can da ya jefa kansa a ciki,sai kuma gashi Sulaiman yazo da batun son Najwan wan da tasan tun da ya furta to hakanne a zuciyarsa don sam bashi da zurfin ciki ko nuƙu nuƙu irin na MU'AZZ shi ɗan kai tsaye ne baya barin abu ya cuceshi idan har yana so a cikin ransa.

Maganar Sulaiman ɗince ta katseta daga tunanin da take.
"Mom ko wani ya riga ni ne?"
"A'a sai dai kuma itace Muhd ya aura wan da ranar auran nasu ne ya rasu."
"Ayya ai jiya munje da Nasrin nai musu ta'aziya. Yauwa maganar Nasrin ɗin kwa nake so muyi Daddy ke ƙoƙarin shigar da ƙara kan sai kin bashi 'yarsa da ƙyar na samu dai ya haƙura akan nan da wata uku in sha Allah zata komo na yi hakanne don kafin lokacin in sha Allah naje haɗo komai nawa na dawo don so nake na dawo ƙasata itama na hidimta mata ina kuma saka ran kafin lokacin kema in sha Allah kin sauka."

Maganarsa ta ƙarshe ce ta rufe bakin Momy ruf dan magana take shirin yi,ashe duk ɓoyen da takewa cikin nan sai da yaron nan ya gano shi? kenan kowa ma yasan da ciki a jikinta abin da take ta ɓoyewa da tsoron a sani goɗai goɗai da ita tsakani da Allah a wani ce tana da ciki? abin da har suruka ne da ita banda sun ƙi haihuwa ta tabbata da tuni tana da jikoki, shi kuwa Abba ba ruwansa murna ya dunga yi da kyautar da Allah yayi masa bayan ya cire rai da samun wasu 'ya'yan tun daga kan su Najwa sai gashi kuma Allah zai nufe shi da samun wani ba dole yayi murna da farin ciki ba?

Juyawa Momy kawai tayi ta tafi ta barshi a gurin a tsayen yayin da ya saki murmushi dan yasan abin da yasa Momyn tafiya ta barsa,to ya zasuyi da hukuncin Ubangiji?Babu babu yadda za su yi da shi domin kuwa ya tabbata rabon wannan cikin ne ya fito da Momyn tasu daga gidansu,shiyasa har Safiya ma ta samu dama akan Daddyn nasu.....
[9/25, 10:49] RASHUNA: BEBEE'ARTH



Wattpad@Rashuna



KANA NAKA
(Allah na nasa )


15


"Ku kallla."Fatma tace da 'yan tawagarta, gaba ɗayansu kuwa suka juya idanuwansu ya sauka akan Sajda,tana taku ɗaiɗai cike da yauƙi da yanga wan da ya zame mata jiki domin kuwa duk in da gayu yake Sajda tasan gayu ta kuma san ta kansa. Abin da ya bawa su Fatma mamaki ba komai ba ne sai yadda Sajda ta samo mayafin da ya mugun shiga da leshin da ke jikinsu gaba ɗaya,anko ne na class mate ɗinsu, sun zaga kasuwanni da dama haɗe da super market suma da dama amma basu samu mayafin da ya mugun shiga da leshin ba kamar yadda na Sajda ya shiga, abin da suke gudu ya faru (Sajda ta fisu ɗaukan wanka) Har ta gifta su ta ankara da yadda suka zuba mata ido kamar su cinyeta ɗanya, basa shiri shiyasa bata shiga shirginsu, su kullum burinsu su fita ɗaukar gayu amman hakan ya gagara saboda ta fisu sanin takan gayun.
"Lafiya dai ko na ci muku bashi?"
" Muna mamakin yadda akai kika samu mayafin da muka gama karaɗe kasuwanni da dama ba mu samu ba."
"Hmm shine matsalarku?"
"Eh"
"To matsalarku tazo ƙarshe in sha Allah zan haɗa ku da NEEHAL COLECTION daga yanzu wahalar neman mayafai ƙare muku da yardar Allah, dan nima tun da aka haɗa ni da ita na huta, duk mayafan da ake so ana samu a gurinta ko wani irin kala ne, kuma masu kyau da ɗaukar ido cikin farashi mai sauƙi."
"Au wai kina nufin mayafin na gida ne ?"

"Eh mana ɗan hannu ne."

Amma ta iya mayafai maza maza haɗa mu da ita dan baza mu shiga gurin bikin nan ba sai da irin mayafin ki muma mu ƙure gayu.

https://wa.me/message/AD4MDTQJLXIRD1

Ku bi wannan link ɗin zai kaiku in da zakui magana da NEEHAL COLECTION daga yau matsalar mayafai ta ƙare muku zaku samu duk kalar mayafan da kuke so cikin farashi mai sauƙi ina mai tabbatar muku zaku ji daɗin muamala da ita.


****"""""
Ba shiri likita ya sallamemu don ganin yadda muka mayar masa da asibiti dandalin party,tun safe idan nai wanka nake gudowa ɗakin Baffa anan za'a haɗu gaba ɗaya ai ta shan shafta da dirama kala-kala da daddare kuma ayi phartyn tsire da youghurt na Rufaida ko L nd Z, ɗaki ɗaki haka zamu bi mu raba musu duk da suma ba su fi ƙarfinsu ba haka zasui ta murna da farin ciki,wan da hakan ya janyo mana shaƙuwa da wasu sukan zo ɗakin Baffan suma ai ta shan diramar da su ana kwasar dariya ganin haka yasa ya tattara mu gaba ɗaya ya sallame mu tun da dukkaninmu babu wata matsala da tai saura, har gara Baffa ma tun da yace zai cigaba da zuwa gida yana dubasa.

Ba ƙaramin kai ruwa rana akai ba kafin Baffa ya amunce mu koma gidan Abbana da zama, domin kuwa phart biyu ne a cikin gidan wan da ya gina shi da burin iyayansa su zauna a ciki amman Baffa ya kafe yaƙi yadda sai yanzu aka samu aka shawo kansa ya amunce muka koma, Momy sai murna take da farin ciki, a zaman asibitin da nayi na ƙara gasgata so da ƙaunar da matar nan ke mini, haka ta tattaro tazo tayi ta ɗawainiya da ni har aka sallame mu.
Duk ɓoyen cikin da take sai da na gano na dunga murna da farin-cikin nima zan samu 'yan uwa wan da har na kasa shiru sai da na fesawa Baffa da Gwaggo suka ce tun kan na gani suka gani sun barta ne taci gaba da ɓoyenta san da ta haife cikin ai ba ta isa ta ɓoye mana ba, duk da sun san nauyi da kunya ne yake saka Momyn ɓoyen cikin ban da abinta mutum ai bai isa ya ja da ikon Allah ba,wannan rabon shine ya kawota cikin zuri'armu.


""""""
Muna zaune a perllow ni da mommy ina dan danna mata ƙafarta data kunbura saboda cikinta da ya tsufa ina tai mata sannu sai ga Yaa Sulaiman ya shigo sai ƙamshi yake sanye yake da jus baƙi da farar riga fuskar nan tashi tai fresh ya ƙaraso ya tsugunna ya gaida mommy nima na gaidashi da murmushi a fuskarsa ya amsa yana bina da wannan kallon nasa da a yanzu na fara sabawa da shi, nace "Ina Nasrin?" Da yake bayan komowarmu gidan nan Mommy tace Yaa Sulaman ɗin ya mayar da Nasrin gidan mahaifin nata,Allah yana tare da ita addu'arta kuma za ta yi ta bibiyarta. Yace "Tana makaranta"

Waya tace tai ringing na ɗaukota sai naga nauwara ce na ɗaga haɗe da sallama tace "Ki maza ki shigo makaranta Gadanya zai yi test."
Nace "To ganinan"
" Mommy nauwara ce Gadanya ne zai mana test tace na shigo makaranta."Tace "To maza tashi ki tafi mana tunda a shiryenki kike."Na miƙe na shiga ɗakina na sashen na ɗaukko mayafi da takalmi da jaka na fesa turaruka na ɗaukko key ɗin motata na futa nace "Mommy na tafi"Tace "To Allah ya kiyaye sai kin dawo" Na amsa da "Amin"


Sai da na fara shiga gurin su Gwaggo nai musu sallama Baffa ya bani sautin rogo da gyaɗa kana na fito, har na shiga Mota zan tayar Yaa Sulaiman ya dakatar da ni ranƙwafowa yayi ta saitin da nake da murmushi a fuskarsa yana bin fuskata da wannan mayen kallon nasa yace "Za'a iya ragemin hanya?" Nai murmushi kafin nace. "Me zai hana kuwa?" Bai ce komai ba ya zaga ɗaya ɓarin ya buɗe motar ya shigo na jata muka ɗau hanya muna tafiya shiru ba wanda yayi magana na juyo na kalleshi idanunshi a lumshe nace. "Yaa ina zan saukeka?" " Nima makarantar zani" Ganin ina kallonsa da neman ƙarin bayana sai ya lumshe idanuwansa ya buɗe cikin karyayyar muryashi yace.
"Aran motar zaki bani kan ku gama test ɗin" na dawo na ɗaukeki."
Ban magana ba har muka isa nai parking a in da ɗalibai ke ajiye abin hawansu daidai Nauwara ita ma ta ƙa raso muka futo a tare ta ƙaraso gurinmu tana dariya tace "Sai gashi kuma munzo tare" Nace "Ehh ke da kika sanar dani ba, ni na zata ma kina makarantar." Tace "Ina fa a group na gani, na sanki chart ba damun ki ya yi ba shiyasa na sanar miki." Yaya Sulaiman ne ya fito daga motar yace "Su Nauwara manya." tace "Ashe tare kuke?"Yace "Ehh tare muke da gimbiya ta." tace "Ai ni fa fushi nake da kai tunda kazo bakazo gidana ba." yace "Ai ba ni zaki tuhuma ba ƙawarki zaki tuhuma tunda laifinta ne itace ba ta rakoni ba." tace "Kai ai bana fushi da sister kuma ai laifinka ne da kace ta rakoka ai bazata ƙi ba." Nace "Yawwa nauwara tare mun ya lanƙaya min laifi." Dariya yayi yace " To ku mun taran dangi nima ɗan uwana ya kusa dawowa da yananan da tuni ya shigarmin." Nauwara tace "Caf wannan miskilin ba ma sai in zai kulamu ba, ba mamaki ma yace bai sanni ba" Yace "Kai ai kwa sai na gaya masa, bara ma na kirashi a waya."Tace "Yi haƙuri da wasa nake." Nan dai suka gaisa na bashi key ɗin ya ja ya tafi.

Bayan mun fito daga test ɗin ne Naawwa ta cemin "Sister wai yaushe zaki aure ne?" Nace "Sai kin haihu." tace "Caf to wallahi sister na gaya miki ko cikin ba ni da shi."
Nace "Kai ki ji tsoran Allah kin kusa fa shekara."Tace "In ma shekaru na kusa yi ba sai Allah yayi zan samu cikin ba" Nace "Haka ne sister kar ki damu kanki wallahi ai dama akwai wayan da suke daɗewa basu haihu ba, dan ma yanzu haihuwar ta zama ta zamani wata tara cif sai kiji ance wance ta haihu,a daa kwa ance mace sai ta daɗe a ɗaki kafin ta haihu."
"Ai dama ban ɗaurawa kainaba shima mai gidan bai da mun kansa, wani zubin ma nice idan nai maganar ciki sai kiji yace to ke zaki bawa kanki, dududu ma yaushe akai bikin namu?" " To kinga sai ki kwantar da hankalinki wata ƙila a daran yau ma mu samu rabo"

Wayarta ce tai ruri ta ɗaga haɗe da sallama ya amsa mata kafin yace "Na dawo gida in kun gama test ɗin ki tawo mana." Tace "To gani nan ya kashe ta miƙe "To sister mai gidana ya dawo ni zan wuce ko na ajeki a gida? nace "A'a zai zo ya ɗaukeni ke dai kije kiran me gida may be ma rabon ne yau ya koro shi da wuri." Harara ta zabga mun kafin tace "Ko da Yaa Sulaiman za'ayine?" nace."Za'ai me." "Kin fi ni sani." "Hmmm wai soyayya ai na gama soyayya tun daga kan Yayana." "Baza ki aure ba kenan?" "Eh mana." "Da yake shi kuma Abban zuba miki idanu zai yana kallonki? Yanzu ɗan ɗaga miki ƙafa sukai ki gama zille zillen ki dole mu sha biki."
"Kinga malama ki shige ki tafi kiran mijinki ."
"To na tafi tun da korata kike."
Hannunta na riƙo da sauri kafin nace.
"Sorry ni ba korarki nake ba."
"To yaushe zaki zo?kin fa daɗe ba kizo ba."
"Sai Momy ta haihu, kinsan cikinta yanzu ya tsufa ina ɗan taimaka mata da wani abun tun da Nasrin ta koma gidansu,ga Abba Kuma ba ya nan."
"Ok to Allah ya raba lafiya, Abin Allah."
"Budurwa da jika ba."
Muka saka dariya ta buɗe motarta ta shiga kafin ta kalle ni tace.
"Tom ni zan huce."
"Ok a gai da gida a gaida mun da me gidan."
"Zai ji in sha Allah, a gaishe mun da su Baffa kice masa nayi missing ɗin tsiren mandawari."
"Zan gaya masa in sha Allah."

Hmmm kamar jira ake ta tafi hadari ya haɗo,gari ya haɗu yayi baƙiƙƙirin,gabana ya yanke ya faɗi dan wallahi na tsani ruwan sama ya taɓa ni,kai ni in ba dole ba ma in akai ruwa bana ƙaunar fita, cike da tsoro na fito bakin get ko zan samu abun hawa tun da ban san me ya riƙe Yaa Sulaiman ba sai dai kuma duk adai daitar da zata huce a cike take har abin da nake gudu ya sauka, watakan aka tsuge da ruwan sama kamar da bakin ƙwarya, tuni na fara rawar ɗari ina waige waigen gurin fakewa amman ban hango gurin fakewa ba, kawai sai na nemi guri na zauna ruwan yaci gaba da sauka a kaina ina ta tunanin ko me ya hana Yaa Sulaimam zuwa? Ina ganin masu mota da babura na tsayawa ko zasu ragen hanya amman ko in da suke bana kalla har su gaji su tafi."


SULAIMAN

Bayan fitowarsa daga makarantar su Najj Asibitin Aminu kano ya shiga gurin wani abokinsa da sukai karatu tare a Jidda, shi amma tun bayan gama warsu ya dawo yake aiki wa ƙasarsa, suna cikin hira Momy ta kira shi akan yazo maza -maza, dan haka yaiwa abokin nasa sallama ya taho, a lokacin yasan Najj ba su isa fitowa daga test ɗin ba dama da sai ya biya ya ɗauketa sai su huce."

Yau kusan kwana uku Momyn na jin ciwo amman bai tsananta ba sai yau ɗin bayan fitowarsu ciwon ya taso mata ganga ganga sai kuma haihuwar tazo da gardama musamman ga jikin girma kuma an daɗe ba'a haihu ba shi ya sa, Hadi direba Baffa ya aike shi shi ya sa Momyn ta Kira Sulaiman ɗin dan dama yace mata zai ari motar Najj ɗin tace masa ga tata motar nan ya hau amman yace ta Najj yake son hawa ko da yake dama ganin damar ɗauko motar ne bai yi ba tun da can gidan nasu ma akwai motoci na gani na faɗa.

Yana zuwa Momy suka fito tare da Gwaggo ya kwashe su sai Aminu kano, ana mata scanning aka gano baza ta iya haihuwa da kanta ba, dan haka nan da nan aka hau shirin shiga theater da ita, to abunka da kuɗi ƙare magana ga kuma abokin Sulaiman Ishaq da ya tsaya akan komai.

Sai da aka fito da Momy bayan an ciro mata twince ɗin yaranta duk mata kana Sulaiman ya tuna da Najj salati yayi ya sanar da Ubangiji kana ya fito da sassarfa har lokacin ruwa ake tsugawa, fatansa Allah yasa dai ba ta fito daga makarantar ba kar ruwa ya dake ta.....
[9/25, 10:49] RASHUNA: BEBEE'ARTH



Wattpad@Rashuna



KANA NAKA
(Allah na nasa )


16


"Ku kallla."Fatma tace da 'yan tawagarta, gaba ɗayansu kuwa suka juya idanuwansu ya sauka akan Sajda,tana taku ɗaiɗai cike da yauƙi da yanga wan da ya zame mata jiki domin
End Ads