x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 9 - MU RAYU A TARE book 1

  • 24001 words
  • 27000 words
  • Out of 62845 words

Category: Love Stories

Views 100

09 Aug 2025
Start ads
After Image Ads


Nan da nan kishi ya rufe Lulu cikin masifa tace "badai kallonta kakeyi ba?"

"No kayan jikinta ne tadena sawa sunyi datta da yawa"

Sannan Lulu tayi ajiyar zuciya, har zata miƙe Ala-Uddin ya riƙeta tare da cewa "ina buƙatarki a kusa dani a halin yanzu"

Cikin jin dadi ta sake matseshi wanda a zahiri ba haka bane a zuciyarsa,

Sai da sukaci abincin kafin sukayi sallah.

NIGERIA
Daƙyar saurayin ya shawo kan mahaukaciya tare da cafko kayan jikinta, wanda yana riƙe ta suka sake yagewa, dama a yage suke,

Tunda yaga zatayi masa gardama ya ɗagata cak ya goyata, tare da yin tafiya da ita, sunyi tafiya sosai tanata fizge-fizge,
A jikin wani gida suka tsaya, ya sauketa tare da kallon masallacin, yaga babu kowa, shiga da ita gidan yayi.
Gidane babba, irin gidan yawannan matan gidan sunkai biyar, zamu iya kiran gidan da gidan gado, kowa yana gadara da gidan, akwai mama Lantana mahaifiyar saurayin wato Aliyu, sai mama Hajara bata da yara, sai mama Uwani sai Inna Hasiya, sai Ladi me tuwo,

Ilahirin matan gidan suna zaune a tsakar gida,
Suna ganin Aliyu da mahaukaciya suka riƙe baki, Mama Lantana tana ɗaki, Ladi me tuwo tace "ahayye faɗan da babu ruwan ka daɗin kallo gareshi"
Mama Hajara ta zaro ido tanaso taga inda Aliyu zai shigar da mahaukaciya,
Tunda sukaga ya shigar da ita ɗakin mamansa, suke jira suji malam yaro ya rufe shi da masifa, amma sukaji shiru,
Bayan ya gaishe da mahaifinsa, ya kalli mahaifiyarsa kana yace "Ummi ki taimaka mata, Malam yaro yace "tabbas baiwar Allahan nan tana buƙatar taimako, amma Lantana sai kinsa baki"

Mama Lantana tace "insha Allah, idan mune silar warkewarta zan tayata da adu'a, kaima sai kaci gaba dayi mata temako"

"Da yardar Ubangiji a daren nan zamu gayawa Allah, insha Allah akwai alamun samun lafiya a tare da ita, yarinya ƙarama da ciwon HAUKA, kwata-kwata batafi shekaru21 ba amma jibeta"

Aliyu ya sunkuyar da kansa, ƙasa, sbda tausayinta yana yawan kariyar masa da zuciya.

Nan fa su Mama Hajara aka shiga gulma iri-iri.

"Mama zan tafi gida, ko akwai abinda kuke buƙata?"

Malam yaro yace "eh ka siyo mana ruwan zam-zam da dabino dan Allah kayi sauri"

Cike da ladabi ya amsa ya fice.

Bai jima ba sai gashi ya dawo hannunsa riƙe da ƙatuwar leda, abinda ya bashi mamaki shine, ganin mahaukaciyar ta nutsu sosai sai kallon malam takeyi,

Aliyu ya ajiye ledar tare da yi musu sallama,

Mama na buɗe ledar taga madarar gari da milo da lifton harda ƙaton bredi da suga zam-zam ɗin da dabino, kamar inda malam ya buƙata....!

Gobema akwai posting da yawa, amma fa idan naga comments ɗinku nayau

Mom Islam

*💋MU RAYU A TARE💋*

Mom Islam

37-38

Zaku samu littafin tun daga farko har inda aka tsaya a gurare kamar haka👇

Arewabooks@ Momislam11

Wattpad@momislam2021



"Allah yayi maka albarka"

Ummi ta faɗa lokacin da Aliyu yake yi musu sallama.

Yana  fita ya tari mashin zuwa anguwar da yake,  duk da ba wani nisa ne dasu ba, amma yakan hau mashin wani sa'in,

Suna tafe yana yiwa mai mashin ɗin kwatancen inda zai saukeshi, suna zuwa ya sauka kana yaba mai mashin kuɗinsa ya shiga gida.

Gidane madai-daici, bashi da wani girma, amma koda yaushe suna cikin rufin asiri, sana'arsa shine, siyarda kayan abinci, tun yana da ƙaramin shago, yanzu Allah ya sake ɗaukakashi ya buɗe shago a kasuwa, Alhmdulilah anan yake samun duk wani abinda zeyiwa iyayensa hidima da gidansa, matarsa ɗaya Heedaya, bata taɓa aihuwa ba, a hakan suke cikin so da ƙauna.

Da sallama ya shiga gidan yana ƙwala mata kira, "Hadeey.. Hadeey"
Murmishi yayi sakamakon ganinta akan sallahya da yayi, ta ɗaga hannayenta sama tana roƙon Allah, shima ya ɗaga hannunsa, lokacin da tazo shafa adu'ar a tare suka shafa, tace "sannu da dawowa"

"Yauwa sannu, ya kamata kiyimin oyoyo yau sai naji babu ɗaɗi"

"Yi haƙuri yayah ka bini bashin na gobe idan Allah ya kaimu, ya ka baro su Ummi da malam?"

"Sunan lafiya,  Hadeey na haɗu da wata mahaukaciya"

Da sauri Heedaya ta miƙe tare da ninke sallahyar ta matso kusa dashi tare da cewa "Yayah a ina ka ganta?"

"A can hanyar anguwarmu, wlhi daƙyar da nakamota, na kaita gidanmu gurin malam, kafin in kaita har na fara tunanin ko malam ɗin zai koremu ne, sai naga ya ƙyalemu ya amshets hannu biyu"

Cikin tausayawa Heedaya tace "Yayah duk wanda ya taimaki wani Allah zai taimake shi, kaga idan ta sanadin ka Allah ze kawo mata lafiya, kaima kanada kaso mai tsoka a gurin Ubangiji"

"Hakane Hadeey amma ina neman shawara a gurinki, nasan bazaki bani shawara marar kyau ba"

"Tom Yayah ina jinka"

"Inaso sati mai zuwa mu koma gidanmu tunda an gama saka tayis da winduna, kinga wannan gidan sai a barwa su Ummi"

"Cikin farinciki Heedaya tace "wlhi da nafi kowa farinciki, nidai badan karkaji haushina ba sai ince, dama wannan gidan na tsaneshi, sbda babu inda zanyi ne yasa nake zuwa"

Aliyu bai ce komai ba, sai ma rungumota da yayi yana mammatsa mata hannu a hankali,

"Ga abinci can akan tabarma"

"Me kika dafa mana?"

"Shinkafa da miya ne sai kifi busashe"

Aliyu ya shagwaɓa fuska kamar wani jariri, kafin yace "nikam ba yanzu zan ci ba, banfa yi sallah ba, sbda kamo matarnan wlhi yau ban samu sallah ba"

"Yayah jekayi sallah idan ka dawo sai muci abinci"

"Uhm kinsan alƙawarin mu na jiya, kince yau zakiyi tsarki ya kamata ki gyara wlhi ina dawowa sallah hamm"

"Gimtse dariyar dake ƙoƙarin suɓuce mata tayi tare da ruƙo hannunsa, suka nufi inda butoci suke, butarsa ta miƙa masa kana koma ciki tana cewa "nifa nasan halin kayana"

Yana daga tsakar gida shima dariyar yakeyi.

Yana fita, ta ɗauko kwaɓaɓɓen haɗinta wanda yaji zuma ta lakata tayi matsi dashi, kafin ta ɗibo garin kaninfari ta zuba cokali biyu tare da madarar ruwa ta juye a ciki, ta nemi guri ta zauna tare da ɗaga kai ta shanye,
Sai da akayi sallahar isha'i sannan ya dawo, lokacin haɗin ya fara bin jikinta, tanajin sallamarsa ta ɓoye a cikin labule, tasani tsabar zumuɗi abincin ma bazai ci ba,

"Aslamu alaiku, Hadeey.."
Jin shiru yasashi ƙarasawa cikin ɗakin yana cewa "wlhi ki fito kokuma idan na kamoki zaki gane shayi ruwa ne"

Da sauri ta fito, sbda ya taɓa yi mata haka, bataji da daɗi ba.

Daga bayansa ta tsaya, ta rungume shi ya goyata yanata zagaye ɗakin da ita, ciro soyayyar doya daƙawai sbda yasan tanaso, ya miƙa mata, godiya tayi masa kana ta kamo hannunsa suka wuce dakinta, sbda ɗakuna biyu ne a gidan, nata ciki da parlo sai kicin sai bayi,
A kan gado suka zube, ya ƙura mata ido, ga mamakinta sai taga hawaye na zarya a idonsa, ko me ya tuna oho.

Hankali a tashe take kallonsa, cikin tausasa murya tace "yayana ko nayi maka wani abunne?"

"Babu abinda kikayi min sai ma wanda kikeyi min gurin kyautata min, ina ganin kaf duniya babu matar da zata ji tausayina ta kyautata min ta somin iyaye sannan kuma ta jure buƙatata sama dake"

Sam tama kasa magana, cikin salo na kissa ta fara shafa masa baya kamar inda yake sanar mata yanaso,
Lumshe ido yayi tare da sake rungumota yana sinsinar kanta dake fitar da ƙamshin man kitso,
Sun daɗe suna wasa, daga ƙarshe suka faɗa duniyar luv.

Daga airport aka dawo da Hakeem gida, lokacin duk sun shiga jirgi sai dai muyi musu fatan isa lafiya.

ALGERIA
Lokacin da jirginsu ya sauka Iffat tana barci, Kai tsaye masaukin da aka shiryawa dady suka wuce, Hajiya ƙarama tana rungume da Iffat,
Gidane rantsatse mai kyau, tsayawa misalta kyau da tsarin gidan, ɓata lokaci ne, gidane da idan mai karatu ya gansa zai ga kamar duk gilashi akayi, sbda walwali da gidan keyi.
Masu gadin gidan ma sunkai mutane biyar, sbda gidan babba ne, haɗe da jami'an tsaro,
A parlo suka zube, Hajiya ƙarama har ta zauna ta miƙe domin kwantar da Iffat, tsarin gidan sai yayi mata wani iri, ɗakunan gado wanda ta leƙa sunkai huɗu, ɗakin da Allah ya bata iko ta shiga, ta kwantar da Iffat tare da yi mata adu'a, gurin dady ta dawo ta samu yanata waya, har ta daɗe a zaune bai gama wayar ba,
Miƙewa tayi ta shiga neman bayangida sbda tayi alwalah, wayarta ta mutu batasan ko ƙarfe nawa bane yanzu.

Cikin sa'a ta hango bayangida, ta shiga ta kunna pampo dan bataga buta ba, kallon numbobin dake jere tayi, kafin ta ɗaga kanta sama duk iya bokonta da sanin kayan zamani takasa kunnawa, sai da ta dawo ta kira dady, lokacin ya gama waya, ya danna wasu numbers sannan ruwan ya zubo Mai kyau ga daɗi.

Kafin tayi alwalah ta buɗe jakar tafiyarsu ta ciro sallahya, ta dawo ɗakin da ta kwantar da Iffat ta fara Sallah.
Kamar kullum da koyaushe, tana yawan saka Iffat a adu'a, bayan ta gama ta shafa.

Jingina tayi da jikin gadon, kafin Hajiya babba ta faɗo mata, Hajiya ƙarama ta girgiza kai tare da miƙewa ta ninke sallahyar,

Parlo ta dawo, ta samu dady baya nan ya fita,
Ta koma gurin Iffat lokacin harta tashi,
Little Eshat kin tashi?"

Iffat ta zubawa Hajiya ƙarama ido kamar meson cewa wani abu.

Dady ya shigo hannunsa riƙe da cajar Hajiya ƙarama yace "kisa wayarki sannan kuzo dining room abinci na can"

"To" tace masa, tare da jona wayar Tata, sannan ta kamo hannun Iffat suka fito zuwa gurin cin abinci.

Suna zuwa, Hajiya ƙarama ta zaunar da Iffat akan cinya tare da buɗe warmers ɗin dake ɗauke da abinci,
Hannu Iffat takai kan farfesun kaji, Dady yace "masha Allah Iffat tanaso zataci"

Saukowa ƙasa sukayi kan grass carpet mai taushi, Hajiya ƙarama ta fara bata a baki, dama ba ƙashi ne dashi ba.

A daren yayi magana da babban likitan ƙwaƙwalwa,

Washe gari, da sassafe aka shigar da Iffat ɗakin aiki.

NIGERIA
Zaune yake gaban malam mai Almajirai hannunsa riƙe da ɗari uku, bayan sun gaisa, malam Yusuf yace "nikam na warware, nazo ne akan yarinyata Juwairiyya"

Malam mai Almajirai yace "masha Allah ai tunda na ganka nasan lafiya ta samu, to menene matsalar ita ƴar wajen naka?"

Malam Yusuf yace "wlhi babu manena ne, babu wanda yake zuwa gurin ta, ni nafison samari su dinga yi mata layi, koma basuyi mata layi ba, inaso ta samu hamshaƙin mai kuɗi, wanda zata huta"

Malam mai Almajirai yace "to yanzu dai wani hanzari ba gudu ba, akwai abubuwan da zamu siyawa aljanun kanta, sbda sune suke Kore mata samari, bayan haka zan bata wani kwalli da hoda, idan zata fita ta shafa, amma fa ta tabbatar anguwar masu hannu da shuni zataje, ko ba aikanta akayi ba ta dinga zagayawa"

Malam Yusuf yace "to kamar nawa ne kuɗin turarukan?"

"Dubu goma, nayi maka alƙawarin inhar kwalliya ta biya kuɗin sabulu sai kun ninka dubu goma sau miliyan kuma zakace munyi wannan zancen"

Cike da jin daɗin alƙawarin da malamin yayi masa, yace "ina komawa gida zan taho maka dashi, ya miƙa masa ɗari uku yace "gashi asiyi goro"

Godiya malam mai Almajirai yayi kana yace "yana tsumayinsa"

Bayan tafiyar malam Yusuf malam mai Almajirai ya fara haɗo magunguna hardasu hayaƙi da turare na jiki da hoda da kwalli,

Sai yamma liss lokacin ankusa shiga sallah, sannan malam Yusuf yazo,

Bayan sun sake gaisawa ya miƙawa malam mai Almajirai kuɗin, shikuma ya miƙa masa magani, yayi masa godiya ya wuce.

Washe gari, da wuri su Amani suka shirya, bayan sun gama karin kumallo sukayi wanka, suka haɗe cikin shadda mai ruwan sararin samaniya ita da Aseela, ita kuma Inaya doguwar riga ƴar kanti Batool ta sanya mata, Batool tasa Abaya milk color mai ratsin yellow ba sosai ba, sai adon duwatsu da rigar tasha, sam Abba ya hanata sanya mayafin dole sai dai tasa dogon hijabi, ta ɗauko handbag ɗinta ta fito part ɗinsu Amani, suma sun gama shiryawa, har suka gaisheta suka fito, sbda Mahabob yana parking space yana jiransu, Abba ma ya fito dukkansu suka wuce,

Kasancewar sabuwar motar Mahabob ɗin mai ɗiban mutane kamar 8 ne yasa suka tafi a sake, kai tsaye anguwarsu huda suke shirin zuwa, a hanya Abba yace a siya musu kayan marmari, koda mai kayan ya zuba a leda ya miƙo Abba ya miƙa kuɗin sukaci gaba da tafiya.

"Wlhi kinji sauƙi duk wani lamɓo da kikeyi saboda karkije tallah na rantse gobe sai kinje, ni zaki mayar shegiya marar galihu, in girka in baki kina daga zaune, gobe nayi zaki wuce tallah kinji na gaya miki karma kice bakisan da maganar ba"

Sosai Umman take faɗa kamar zata ari baki, dama bawai taji sauƙi irin sosai ɗinnanne ba, jikin dai ya warware mata, tashi ɗaya ta fara rawar sanyi daga inda take zaune, Umman ta leƙo tana cewa "jibi abinda kikeyi sai kace bugun aljanu, wlhi abokin sharrinki yayi nisa, ni zaki gayawa ciwo, tun kafin kizo duniya nasan ana rashin lafiya, ke ciwon ma da yazo miki da gata harda asibiti sai kace ƴar gwamna, kina ganin idan zan kwanta ciwon mutuwa babu mai temakamin dole dai haka zan warke tunda jikin talaka ne"

Idon Huda ta gefe na zubar hawaye tace "Umma sanyi nakeji Umma ki ɗagani anan Umma zan mutu"

"Au..au ashe me mutuwa ma yanada kama? da ciwon gaskiya kikeyi zan ɗagaki amma tunda ciwon ƙarya kika rakitowa kanki nabar ɗagaki"

Tun daga zauren gidan su Mahabob sukejin magana kamar ana faɗa, da gudu Mahabob yaje ya ɗago Huda, tare da kallon Umman da idanunta ya rufe, sbda har ta shiga ɗaki tana ci gaba da surfawa huda masifa,
"Aslamu alaikum" Abba yayi sallama muryarsa wata iri, duk da sunyi ɗazu tun kafin su shigo Umman bataji ba,

Da sauri ta fito tana amsa sallamar baki kamar gonar auduga, tace "ku shigo"

Tunda suka shiga Mahabob ya fara shawarar inda zai nesanta Huda da gidan, a zuciyarsa yace "ta zamo ƴar aikinmu shine mafita....


Mom Islam ce...

*💋MU RAYU A TARE💋*

Mom Islam

39-40

Da kallon tausayi Amani ta bi Huda dashi, sakamakon kwanciyar da taga tayi.

Cikin zumuɗi ta gaishe su, bayan sun gama gaisawa Abba yace "dama munzo duba jikin marar lafiya ne"

"Lahh ai taji sauƙi iskanci takeji shiyasa kuka ganta haka"

Abba yace "Ash shaa.. Allah ya shirya mana zuri'a"

Bayan shiru da gurin yayi, Mahabob yayi gyaran murya kana yace "Abba ya kamata mu ɗauke ta aiki kodan su dinga rage zafin wani abun"

Sai da Abban yayi nazari, kafin ya kalli Huda dake kwance har yanzu tana rawar sanyi, yace "eh hakane, idan ta samu lafiya muna neman alfarmar a bamu ita ta dinga yi mana wanke-wanke sai ki faɗi albashin da ya kamata a biyata"

Abba ya faɗa yana kallon Umman Huda, tare da jiran amsar da zata bayar.

"Toh Alhaji nidai bazance muku "eh ko a'a ba, sbda tana zuwarmin tallah, kuma dashi muke ci muke sha harma mu ɗinka tufafi"

"Amani tace duk ba wannan ba, kuɗin kawai zaki gayawa Abba koma nawa ne zai baki"

"Uhm gaskiya riba tsugugu nake samu a sana'ar shinkafa"

Cikin ƙosawa da ƙaguwa Mahabob yace "am sorry kuɗin kawai zaki gaya mana"

"Kullum idan na dafa shinkafa ina samun ribar dubu biyar"

Huda ta ɗago jajayen idanuwa da suka rine tsabar zazzaɓi, tare kallon Umma, murya ƙasa-ƙasa, Huda tace "dubu ɗaya ne da ɗari uku"

Umma tace "ke...ke kee gidanku, maƙaryaciya zaki mayar dani? cewa fa kikayi baki da lafiya, shiyasa nace ƙarya kikeyi"

Abba yace "zan dinga biyanta dubu ɗari biyu da hamsin duk wata"

Cikin sauri "Umma tace "to aiko mun gode amma tafiya da ita zakuyi ko anan zata zauna ta dinga sintirin tafiya kullum?, nikam bani da kuɗin mota"

Mahabob yayi murmishi sbda umma dariya take bashi, kafin Abba yace wani abu, Mahabob ya riga shi yace "zamu tafi da ita Asabar da Lahadi zata dinga zuwa islamiyya duk ranar Lahadi sai ta dinga zuwa gaisheki.

"Ah ai babu komai, koni in dinga zuwa gaisheta ba?"

Babu wanda ya sake cewa da ita komai, sbda a maganganun nata sai kace na mai taɓuwar hankali,

"Mahabob jeka mota ka duba gurin da nake ajiya akwai kuɗaɗe a ɗaure, kowanne dubu hamsin ne sai ka kwaso guda biyar"

Cikin ladabi Mahabob yace "toh Abba"

Umma kam hankalinta ya tashi, ashe Amani tanata yi mata magana bataji ba, sai da "Huda ta matso tace "umma anayi miki magana"

Sannan tai firgit kamar me mafarki ta wayance da cewa "rikicin duniya, meye?"

"Yaushe zamu tafi da ita?"

Amani ta faɗa fuska a tamke.

"Ko yanzu wlhi zaku iya tafiya"

Batool ta girgiza kai.

Mahabob na kawo kuɗin ya miƙawa Abba, tun kafin a miƙowa Umma take leƙe, duk suna kallonta.

Sannan Abba ya miƙa mata kana yace "a shiryawa  yarinyar kayanta"

"To..to Alhaji mungode dama munajin labarinka a gidajen talabijin ashe Allah zai haɗamu da irinku masu mutumci da sanin darajar ɗan adam"

"Ke huda tashi ki shirya kayanki"

Umma ta faɗa tana danne kuɗin da guwaiwar ƙafarta.

Cikin dakiya, Abba yace "ayi mata uzuri a shirya mata"

Duk wani kaya da Umma ta sani nata duk ta haɗa mata dashi harda takalmanta, da kayan kwaliyarta, ta ajiye musu gana masgo ɗin a gabansu, duk ta yage babu mamora, ta wani gefen duk kuɗin cizo"

Abba yace "Batool ki juye kayan a mota, mu wuce"

Kafin Abban ya miƙe dukkansu suka tashi, tare dayi mata sallama suka wuce,

Tayi godiya kamar zata ari baki,

Amani ce ta riƙe huda suka tafi gurin mota, sbda jikinta babu ƙwari.

            __________
Tunda malam Yusuf ya kawowa Juwairiyya magani da turare taje tayi wanka, ta daɗe a wankan kamar zata sauya fata, ta fito hankali kwance, ƙasan zuciyarta fara'a ne a lulluɓe, ta nufi ɗakinta ta shafa mai, tayi kwalliya kai kace gurin ƙwararru taje, tasa shaddarta pink color tasha aikin wuta, har ƙasa, tayi kyau sosai, nima dai cewa nayi kumafa ba matar yara bace.

Turaruka kala biyu ta fesa masu sauƙin kuɗi, kafin ta yafo farin mayafinta, ta ɗauko farin takalmi, kafin tazo ɗakin babanta ta ɗauki kwallin tasa,ta fesa turare, ragowar ƙullin maganin sai dare, ta fice bayan tayiwa baban sallama yace da ita "Allah ya bada sa'a"

Amin tace masa ta fice tana karairaya,

Can ƙasan anguwarsu ta nufa, tana tafe tana karairaya, cikin yauƙi ta ke kallon wata haɗaɗiyar mota dake tahowa, yana zuwa daf da ita ya rage gilashin motar, tare da cewa "ƴan mata idan bazaki damu ba, zan iya sanin sunanki, cikin sauri tace "sunana Juwairiyya"

"Wow nice name suna mai daɗi, ko zan iya samun soyayyarki"

Cikin zumuɗi tace "mezai hana?"

"Okay Tom shiga mota in rage miki hanya"

Motar ta shiga tare da nuna masa wani danƙareren gida tace "nan ne gidansu"

Saurayin yace "sweety ni baki tambayi sunana ba?"

Juwairiyya ta rufe fuska tare da cewa "yi haƙuri mantuwa nayi"

Sunana
End Ads