x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 20 - MU RAYU A TARE book 1

  • 57001 words
  • 60000 words
  • Out of 62845 words

Category: Love Stories

Views 110

09 Aug 2025
Start ads
After Image Ads
yara da jikoki harda surukai,
Tunda mutan gidan suka hangosu aka fara gulmace-gulmace, shiko fuskarsa wasai sai gaishe su yakeyi, Juwairiya kam gaisuwar take amma sam bakajin abinda take cewa sai dai idan ka lura da bakinta na motsawa, kai tsaye suka wuce sashin su Al'amin, sashin ya kasance yana kewaye da ginin ƙasa amma da karar dawa suke girki ko kashin shanu, Baaba na ganin Al'amin ta washe baki, a fili tace "Aminu ashe rai kanga rai, zamu haɗu, dama kana raye?"

Al'amin yayi murmishi kafin yace "Baaba ina raye, wllhi haka kawai naji hankalina ya tashi inason inga gida"

Baaba ta kalli Juwairiya da ta sunkuyar da kanta ƙasa, kana tace "wannan kuma fa?"

Sai da ya ɗan yi jimm kafin yace "Baaba mata ta ce, ko wata uku bamuyi ba"

Cikin farin ciki tace "Masha Allah ga mari can ma ashe lokacin da ka tafi tanada ciki, yanzu shekarar yarinyar goma"

Juwairiya ta zaro ido, tabbas taji kamar sunason cewa yanada mata, amma bazata yarda da tatsuniyar da kunnuwanta sukeyi mata ba, har sai ta ji daga bakinsa,

Baaba na washe baki tace "ka shigar da ita can rumfa yanzunnan na kwashe dambu yaji zogale bari a siyo muku mangyaɗan ƙuli yanzu"

Juwairiya ta yamutsa fuska, sai kuma ta yi murmishi sbda ganin yanayi mata murmishin,

Hannunta ya kamo kana yace "muje can"

Ga mamakinta ko tabarmar kirki babu, sannan gashi ɗakin duk warin daddawa, badan kar ta tashe hanci ya ganota ba, ai da ta toshe, kafin Baaba ta shigo, aka shigo masu da kayan dake cikin booth dukkansu,
Nan fa mutane suka fara rubibin shigowa wasu su shigo wasu su fita, abinci kuwa sai da aka kawo kusan kala goma ko wanne da kwanonsa, Baaba ta shigo hannunta riƙe da dambu a kwanon Silva, sai mangyaɗa shima aɗan ƙaramin kwano da cokula biyu sai farantan Silva suma guda biyu, sannan ruwa a kofin Silva, tana cigaba dayi musu sannu, Al'amin ya kamo hannun baaba kana ya zaunar da ita, ya ce "Baaba duk waɗannan kayan naku ne keda malam"

Baaba ta washe baki kana fara firfito dasu madarar gwangwanin da sauran kayan shayin, sannan sai kayan abinci buhun shinkafa buhun taliya irin ƴar buhunnan sai mangyaɗa da manja da sauransu,

Baaba ta fashe da kuka tare da cewa "wllhi Aminu na ɗauka koda kaje binni ba a kintse kake ba"

Al'amin ya miƙe tare da cewa "malam ya fita ne?"

"Eh yana gona anjima nan zaka ganshi"

Juwairiya dai sai kallonsu takeyi, gabaki ɗaya ƙauyen ya ishe ta ta gaji da zaman nan duk da yau sukazo, rabon ta da shan ruwan randa ko na leda tun kafin tayi aure ƙila ma yanzu ruwan rafi zatasha,

Al'amin yace "Juwairiya kici abinci"

Baaba tace "ashe ma uwata ce, Allah ya sanya muku albarka, idan bazata ci ba tunda ga kayan shayi sai a haɗa mata"

Juwairiya tai saurin cewa "zanci mama"

Shima yaji daɗi sosai sbda yaga alamun bata ƙyamaci ƙauyensu ba.

Al'amin ya kamo hannun Baaba suka fice, can ɗakin awakai ko me suke tattaunawa oho,

Juwairiya ta ciro wayarta taga network ya ɗauke, tayi tsakin da iya karsa laɓɓa kafin ta sanya cokali a cikin kwanon dambun bayan ta buɗe ta ɗibo takai baki, har zata kurma ihu sai kuma ta tuno da inda take, sannan ta haɗiye abincin daƙyar kamar zatayi amai, ta mayar da murfin ta rufe.

Al'amin bai dawo ba har akayi sallahar la'asr, lokacin Baaba ta shigo, tare da cewa "Zuwaira kinci abincin kuwa?"

"Juwairiya tace "eh naci mama"

"To taso kiyi sallah yanzu malam ze shigo sai ku gaisa"

Ta miƙe tare da ɗaukar butar tace "inane bayi?"

Baaba ta nuna mata, daƙyar ta iya tsugunawa tayi fitsari, sbda dole nema yasa ta yi, dan ya matseta sosai,

Ta fito tayi alwalah ta shigo ɗakin, ta samu Baaba ta shimfiɗa mata wata yaloluwar darduma, Juwairiya ta kawar da dardumar kana ta shimfiɗa ɗankwalinta, tayi sallahar akai, Allah yasa ma raka'a biyu zatayi.

Bayan ta idar tai saurin naɗe ɗankwalin nata ta ninke dardumar ta koma ta zauna,

Gyaran Muryar Malam da taji ne yasa ta gyara zama, har zata fito sai taji yayi sallama ya shigo,

Cikin ladabi ta gaishe shi, bayan ya amsa yake tambayarta iyayenta, tace "suna lafiya"

Kana ya sanya musu alkairi yace "Aminu ya sanar dashi kwana uku zasuyi su koma"

Juwairiya sam bataji daɗin hakan ba, sbda a tunaninta gobe zasu koma, malam ɗin ya fara yi mata magana cikin sigar fahimta tare da sanar mata da yanada mata da yara guda biyar, anyi masa asiri ne yabar garin, har yakai shekaru goma bai dawo ba, sannan ya ƙara da cewa "matar ba ƙaramin dauriya da haƙuri tayi ba, idan sun cika kwanakin da zasu koma zai tafi dasu duka, kana ya ƙara da bata haƙuri akan cewa tayi haƙuri su zauna lafiya"

Godiya Juwairiya tayiwa malam, a ƙasan zuciyarta kuwa gani take kamar an caka mata mashi, sbda har tafarfasa takeyi, malam ya fice yana farin cikin samun suruka ta gari.

Sai da akayi magriba da isha'i, duk Juwairiya batayi alwalah ba, sbda batayi hutu ba, sannan tayi sallah, bayan ta idar ta ninke ɗankwalinta sai ga Al'amin nan ya shigo,

Bata nunar masa da komai ba, ta ƙirƙiro murmishi ta maye gurbinsa da baƙincikin da take ciki, kafin tace "ina ka shiga na jika shiru har baba ya shigo?"

Al'amin yayi murmishi kafin yace naje gaishe da ƴan uwa da abokan arziki,

A zuciyarta tace "wllhi gobe bazanyi wunin ƙauyennan ba, bare ace zamu tafi wani gurin"

Suna zaune Baaba ta kawo musu tuwo miyar kuɓewa bushashiya, Al'amin ya gyara zama kana ya ce a kawo masa cokali, bayan an kawo ya fara ci, sai da yayi mata magana kafin tasa hannu ta fara ci kamar mai tsoron abincin, shine ma yaci sosai, ya ƙudurtawa zuciyarsa baƙunta ne yake damunta,

Zuwa dare ya wuce gurin kwana ita kuma Baaba tace "hau babban gado ki kwanta"

Ta haye tare da kunna kallo a wayarta,

Shiko ya samu yayi cajin wayarsa da power bank, asubha ta gari...

Washe gari, kiran sallahar farko a kunnen Juwairiya, ta miƙe zaune tana ƙarewa ɗakin kallo, daga ƙarshe ta duro ƙasa tana kuka tana yarfe hannaye, daga ƙarshe ta dafe cikinta da kanta, Baaba ta sauko da sauri tana ce mata "maiya faru?"

A wahalce take cewa "cikina kaina hannuwa na....

*💋MU RAYU A TARE💋*

Mom Islam


Book1

95-96

Hankali a tashe ta fito tana bubuga ƙofar ɗakin malam, a firgice ya miƙe, kasancewar yana zaune kan darduma kana yace "lafiya?"

"Babu lafiya matar Aminu ce take ciwon ciki"

Malam yace "subahanallah ina zuwa"

Bai jima ba ya fito hannunsa riƙe da allo yayi rubutu, ya miƙawa Baaba ta wanke ta bata tasha, tun daga nesa Juwairiya take jifan Baban da mugun kallo har ta iso, Allah sarki hankalin tsohuwa duk yabi ya tashi, Juwairiya kuwa sai ci gaba da juyi take, Baaba ta wanke ta miƙa mata tare da cewa "kiyi Bismillah Kisha"
"To" baaban na ficewa ta buɗe zip ɗin jakarta ta ciro gorar fanta da tasha ɗazu, ta juye rubutun a ciki kana ta zuge zip ɗin, har taci gaba da ihun Baaba na waje tana haɗa wuta, bayan wutar ta kama tayi alwalah ta dawo ɗaki tana jerawa Juwairiya sannu,


Irin ta jigatan nan har wani gyaɗa kai takeyi, alamar bakin ma yayi nauyi.

Da ƙyar ta miƙe taje ta ɗauro alwalah ta dawo, burinta be wuce gari ya ƙara yin haske Al'amin ya shigo ya Kaita asibiti, daga ƙarshe ma su wuce gida.

Tana zaune akan sallahya malam ya shigo lokacin an fito daga sallah, yayi mata ya jiki yace da sauƙi,

A inda yaga yanayinta ya tsorata sosai, sbda sai juyi take tana riƙe da ciki, malam yace "bari mijinta yazo, ko asibitin bebeji su tafi"

Kwatsam sai ga sallamar Al'amin, ya durƙusa ya gaishe da malam kana ya gaishe da Baaba ya kalli Juwairiya dake ta juye-juye, hankali a tashe yace "maiya sameta?"

Baaba tace "wllhi tun asbha take haka, malam ma yayi rubutu an bata tasha Allah be kawo lafiyar ba tukuna"

Al'amin yace "tashi muje asibiti"

Tana kwance kamar wata wacce ta shekara tana ciwo, idan kaga inda take wani lanƙwashewa sai ka rantse ciwon gaske ne, gabaki ɗaya ta tashi hankulan mutane,

Dole Baaba ta riƙeta suka shiga motar Al'amin aka wuce da ita asibitin bebeji,

Bayan an shigar da ita ɗakin da ake kwantar da marar lafiya, da farko test akayi mata suka tabbatarwa Al'amin da tanada cikin sati biyu, sai maleria da typod dake damunta, suka sanya mata drip yana zuba kaɗan-kaɗan,

Baaba ta koma gida domin ya dafo musu abinci, Al'amin ya zauna kusa da ita tare da gyara mata zaman hannu, sai sannan wayarsa tayi ringing alamun ana kiransa, da sauri ya ɗaga, harda ɗan ranƙwafawa alamar yana magana da wani mai muhimmanci, ji nayi yace "insha Allah megida gobe muna hanya"

Kana ya ajiye wayar, sosai Juwairiya taji daɗi tare da fara ɗokin komawa gida.

Zuwa yamma, dole aka sallame ta, suka koma gida, bayan Baaba ma ta dawo, ta kawo abinci sai komawa dashi sukayi,

Bayan sun koma gida, Al'amin suka keɓe da malam,

Acan bayan gari suka zauna, malam yace "Aminu bayan barin ka ƙauyennan wace irin rayuwa ka shiga?"

Al'amin ya sunkuyar da kansa ƙasa kafin yace...

Da farko daga nan na wuce garin Gombe, da sana'ar tura baro na fara, ina siyarda leda, kasancewar na tafi da dubu biyu ragowa bayan kuɗin mota, nakai shekara a haka, Allah ya haɗani da wani mutumi ya ɗaukeni gadi a gidansa, kwanci tashi ya dinga yabona akan wai inada gaskiya da riƙon amana, yasa aka koya min dreba, daga nan kuma ya buɗe min babban shago na siyar da turaruka, arziƙinsa nata hau hawa, har ya zamo na samu jari nawa na kaina, ya fara turani ƙasar waje sarin turaruka, nima ya zamo ya buɗemin babban shago, a halin yanzu shagunansa bakwai, nikuma inada shaguna uku a cikin garin Gombe ina da babban shago a ƙasar waje, a halin yanzu shikuma ya ƙara bunƙasa kasuwancinsa ta hanyar cigaba da sarin motoci yana siyarwa, wllhi har yanzu muna zaman arziƙi dashi, dama da muka zo inada niyar in siya muku gida acan sai ku koma kai da Baaba"

Malam yace "Masha Allah haƙiƙa adu'ata bata faɗi ƙasa banza ba, sbda babu dare babu rana adu'oi nakeyi maka"

"Sai dai bazan iya tashi in koma wani gari ba, idan ma haka kakeji ko fili ka siya sai kayi mana ginin zamani, amma inaso ka tafi da Mari da yaranka, kodan samun nutsuwa da kwanciyar hankali"

Al'amin yace "eh nima inada niyar hakan, sbda jiya naje mun gaisa, na yi musu siyayya na sanar mata da ta shirya gobe zamu wuce insha Allah, sbda mai gidana ya kirani ɗazu akan zamuyi tafiya tare"

Malam yace "to Masha Allah inayi muku fatan alkairi sai dai ka kula da matanka, karka dinga nuna musu bambanci a fili, duk da zuciya takan karkata ga ɓangaren da akafi yi mata biyayya"

Al'amin yace "to"

Daga nan ya dawo gida ya sanarwa da Baaba gobe zasu wuce, tare da alƙawarta mata zai turo da kuɗi su tashi anan su koma ginin da zeyi musu,

Tun da yamma Juwairiya take shiri, bayan ta gama, taɗan kwanta, kasancewar Baaba ta haɗa mata tea da bredi, da tasha ta ɗanji dama dama, sbda iskancin nata harda yunwa a ciki,

Can dare da dare kusan ƙarfe 9:pm sai ga Mari ita da yaran su uku, da wacce takai shekara goma sha biyar da mai shekaru goma sha uku, sai mai shekara goma, biyu mata ɗaya mai shekaru sha ɗayan shine namiji,
Babbar Suwaiba, namijin Abubakar suna kiransa da Ɗan Bala, ƙaramar kuma Salma suna kiranta da Salamatu,

Bayan sun gaishe da mama da Juwairiya, Mari ma ta gaishe su, daga nan take gayawa Baaba Aminu yace ta shirya gobe su wuce,

Baaba tace "eh munyi maganar dashi, ga ƴar uwarki nan, ku zauna lafiya, kece babba dan Allah karku ɗauki zugar mutane"

Cikin sanyin murya Juwairiya tace "insha Allah"

Mari ma tace "in Allah ya yarda zamu zauna lafiya"

Baaba tasa musu albarka, suka ɗan taɓa hira Juwairiya na jinsu, can anjima sukayi mata sallamar sai da safe, lokacin har Juwairiya tayi barci.

Tun daga ranar da Alhaji Abdussalam yazo har washe gari, umma bata da walwalah, duk da Alhaji Lukman ya lura da hakan, sai ya bari, akan tafiyar da ya gaya mata ne,

Bayan kwana uku da faruwar hakan.

Alhaji Lukman ya fita aiki da wuri, sai ga wani saurayi yayi sallama, ƙarar bubuga ƙofar da Umma taji ne yasa ta ɗauko hijabi tasa, kana ta fito, bayan sun gaisa yace "saƙo ne daga Alhaji Abdussalam yace sunada taron saukar alƙur'ani na yaransu jibi insha Allah sanan yace a baki wannan"

Karɓa tayi ta shige ciki ko uffan batace masa ba, hankali a tashe ta zube akan kujera tana tunanin mafita,

Koda aka kira sallahar Azhar, ta miƙe taje tayo alwala tazo ta kabbara sallaha, kuka ta kamayi tana gayawa Allah damuwoyinta domin kuwa sunfi gaban tunaninta sheɗani ya shigo cikin rayuwarta yana neman ruguza mata farincikinta, duk da cewar Alhaji Lukman bashi da lafiya, amma bata taɓa tunanin rabuwa dashi ba, koda yaushe tayi masa adu'ar samun lafiya da nasara akan aikin da za'ayi mas

*💋MU RAYU A TARE💋*

Mom Islam


Book1

97-98

Jiki babu ƙwari ta janyo ledar da Alhaji Abdussalam ya bayar a kawo mata, kamar kar ta buɗe ledar, haka kawai ta tsinci kanta da buɗe ledar, kana ta ciro kayan ciki, doguwar riga ce abaya pink color sai mayafinta ɗan siriri gunin sha'awa, har zata mayar da rigar sai ta hango envelope, ta ɗauko ta buɗe taga kuɗaɗe masu yawa, bata da lokacin ƙirgasu ta mayar ta ajiye, tare da miƙewa da sauri ta haye saman drowa ta ɓoye kayan.

Kana ta sakko tana tunanin idan har Lukman ya gano abinda ke shirin faruwa, tabbas bazai taɓa fahimtar ta ba, tanason ta sanar dashi tana tunanin gargaɗin da Alhaji Abdussalam yayi mata, akan cewar idan har ta sanarwa wani sai ya tozartata kuma sai yasa mijinta ya tsaneta, hawayen baƙinciki suka zubo mata,

Ta rasa wa zata gayawa matsalarta, tana tunanin sanarwa da Maryamah tana shayin kar maryaman ta tona mata asiri, dole dai tabar abin a zuciyarta duk da zai zame mata dafi!


Zuwa dare Alhaji Lukman ya dawo a gajiye, sai da yayi wanka ya sanya sleeping dress sannan dawo gurin Umma da sam taƙi zuwa ɗakinsa alhalin ba haka ta saba masa ba, koda ya shigo bedroom ɗinta ya samu tana kwance ta ƙudundune, da sauri ya ƙarasa inda take yakai hannu ya shafi fuskarta, hankali a tashe ya cire tare da ƙare mata kallo, ya fara kiranta a hankali, shanyayyun idanuwanta ta zuba masa haƙoranta suna karkarwa tace "sannu da dawowa"

Cikin tausaya wa yace "haba uwar gida baki da lafiya shine kika kasa kirana, ai da duk abinda nakeyi zan bari inzo gareki, yanzu dai tashi muje asibiti"

Duk da ciwon yaci ƙarfinta, amma gara ciwon da takeyi da ace taje walimar sauka tayi ido biyu da maƙiyinta gara ta wuni a asibiti,

Ƙarfe 8:30pm tayi musu a asibitin Dr shugaba, bayan an bata gado anyi mata ƴan gwaje-gwaje, suka tabbatar masa da akwai abinda yake shirin faruwa musamman ciwon zuciya dan tana shikin firgici da tashin hankali,

Kwananta ɗaya a asibitin, sai dai dinga yi musu take away na abinci, alhamduliy jikinta yayi sauƙi har ta samu tayi sallahar asbha, bayan ya dawo daga masallaci kiran Alhaji Abdussalam ya shigo wayarsa, jiki na rawa, gaishe shi yayi kana yace "ranka shi daɗe dafatan an wayi gari cikin ƙoshin lafiya?"

"Lafiya lau dama inaso in gaya maka jiya har muka rabu ban sanar maka ba, akwai saukar alƙur'ani da yarana guda biyu zasuyi, idan matarka ta samu zuwa sai ka kawota"

Alhaji Lukman yace "wllhi gamu a asibiti zazzaɓi anan muka kwana amma ina tunanin zasu sallamemu zuwa anjima"

Alhaji Abdussalam yace "toh shikenan insha Allah zamuzo dubaku nida Hajiya Abida"

Daganan sunayi sallama,

Nidai nace Allah ya taimaka bataji zasu zo ɗinba, da ta sake firgita.


Koda ya leƙo ya ganta akan sallahya tana zaune ya koma siyo mata tea da kayan shayi, cikin sauri ya dawo ya haɗa mata tasha shikam ya kasa sanya komai a bakinsa,

Ƙarfe 10:am aka rubuta musu sallama tare da bashi takardar magani yaje pharmacy yasiya, ta biya kuɗi suka wuce a motarsa.

Koda suka koma gida, a parlo ta kwanta sbda ji takeyi duniyar ta ishe ta, shikuma yanason ta samu sauƙi ya tambaye ta wace matsala ce take damunta?

Ƙarfe 12:dai-dai wayar Alhaji Lukman tayi ringing, ya ɗaga yana cewa "Allah ya taimaki oga"

Alhaji Abdussalam yace "gamunan mun kusa isowa"

Jikin Alhaji Lukman na rawa yace "Allah ya kawo ku lafiya"

Kafin ya matso kusa da Umma yace "oga fa suna hanya shi da matarsa"

Aɗan firgice ta buɗe ido, tare da runtsesu kafin tace "Allah ya kawo su lafiya"

Ya lura da ita kamar batayi murna da zuwan da zasuyi ba, amma sai yayi shiru tunda yaga ba isashiyar lafiya ne da ita ba.

Har barci ya fara ɗaukarta suka ji nocking ɗin ƙofa, Alhaji Lukman yaje ya buɗe yanayi musu sannu da zuwa cikin fara'a, tare da yi musu umarnin su ƙaraso.

Akan kujera mai zaman mutum uku suka zauna,

Umma ta gaishesu ɗaya bayan ɗaya, sukayi mata ya jiki, tace da sauƙi, duk da ta ɗan rufe idanuwanta amma tana ƙarewa Hajiya Ubaidah kallo, farace tass babu abinda Umman zata nuna mata, duk da tafi Umman shekaru amma jin daɗi ya ɓoye hakan, ƴar gayu ce ajin farko, dan sai a ɗauki wata budurwar ma ba'a ɗauketa ba, kafin suka miƙe suna cewa zasu wuce gurin walimah, sai da suka fita masu gadi da driver suka fara shigo da kayan abinci harda na ƙwalama kamar bazai ƙare ba, sam kayan babu abinda ya burgeta a ciki, sannan ta lura da irin kallon da yake bin ta dashi, duk da Hajiya Abidah bata lura ba, da Alhajin.

Suna can parking space Alhaji Abdussalam yake ce masa idan jikin yaƙi ya sauyawa Umma asibiti, Hajiya Ubaidah tace "kodai laulayi takeyi kake ɓoye mana?"

Dariya yayi yanayi musu Allah ya kiyaye hanya tare da rufe musu murfin mota.

Ita ko ta zurfafa cikin tunanin ga matarsa kyakkyawa me zeyi da ita mugu kawai.

Alhaji Lukman ya dawo cikin fara'a yana cewa "Masha Allah Alhaji akwai halin kirki"

"Mun gode" kawai Umma tace, kamar mai jin barci, hakan yasa shi wucewa ɗakinsa ya barta ta
End Ads