x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 3 - MU RAYU A TARE book 1

  • 6001 words
  • 9000 words
  • Out of 62845 words

Category: Love Stories

Views 93

09 Aug 2025
Start ads
After Image Ads
yin duka bata raga mata, musamman ma akan dukiyarta, kamar wacce aka tsikara tace "na amince"

Me shagon ya ce "bismillah"

Yayi mata alamar ta shigo da hannunsa, ba musu tashigo, ya shiga da takalmanta ciki, kana ya rufe ƙofar shagon, kafin ya rufe sai da ya duba yaga babu kowa sannan ya rufe, kana ya ƙarasa ciki, ya samu huda tana tsaye a raɓe tana kuka, a hankali me shagon ya ƙarasa ya rungumota, tare da miƙa mata ragowar taliya wacce yaci,
ya rage,
Tana karɓa ta fara ci, kamar wacce ta kwana da yunwa, tana gamawa, ta ajiye robar, ya miƙa mata ruwan wanke hannu ta wanke, kana ya fara matsota tana matsawa baya, har ya ƙureta a jikin bango,
Cikin ƙaramar murya yace "idan baki yarda na taɓa nonuwanki ba wlhi bazan baki kuɗin ba"

Da sauri Huda ta yaye hijabinta, mai shago ya ɗorata akan cinyarsa ya dinga lugui guice mata nonuwa, yana sauke wani fitinannen nishi, jin bugun ƙofar da akeyi ne ya sanya shi sakinta da sauri, yana cewa "gaskiya idan ina taɓawa  kamar kar in dena, idan kuɗinki ya sake ɓata kullum ki dawo wlhi zan dinga baki,

Huda tace "to" jikinta na ci gaba da rawa,

Tana kuka ta sanya hijabi tare da riƙe takalmanta a hannu...

Shin me zakucewa Huda itada mahaifiyarta???
Nace ba?  idan akayi shar'hi read more 6 zan dinga yi kuma kullum insha Allah
Mom Islam
*💋MU RAYU A TARE💋*
             

Mom Islam

11-12

Sai da ya leƙa ta window  yaga me buga ƙofar, kana ya dawo ya zauna, wanda idan ya buɗe masa komai zai iya faruwa,

Gurin Huda ya dawo, ya miƙa mata kuɗin kana yace "bari wancan munafikin ya wuce sai ki fita"

Huda tace "to" jikinta na ci gaba da rawa.

Can anjima da ya tabbatar wanda yazo ya wuce, ya buɗe mata ƙofa ta fita, tare da ƙara jaddada mata idan tana neman cikon kuɗi ta dinga zuwa.

Kayan abincin nata ta kwashe ta haɗasu a cikin kular, kasancewarta babba, kana ta tsare me mashin ta gaya masa anguwarsu ta hau, suka tafi.

Suna isowa ta nuna masa ƙofar gidansu, ya ajiye, ta sauka ta miƙa masa kudin ya wuce, ita kuma ta shige gida, kanta ɗauke da kular abincin,

Da sallama ta shiga, ta samu Umman nata tana kwashe shanya, sakamakon hadari daya haɗo, "sannu da gida Umma"
Huda tace, lokacin da ta ƙarasa ciki, cikin dakin fuska Umman tace "yauwa Huda ƴar albarka sannu, da fatan dai anyi ciniki?"

"Eh Umma, na dawo miki da bashin da kikebi"

Umman na murmishi tace "jeki ɗauki abincinki kici ƴar albarka"

Huda zuciyarta a sake ta ƙarasa bakin murhu ta buɗe kwanon abincin nata, ta washe baki, kafin tace "Umma kice mutumina kikayi

Umma na washe baki, tace "ai kuwa idan ma zaki ƙara akwai"

Huda ta ɗauka ta wuce ɗaki,

Tunda ta shiga ta ajiye ɗan waken a gefe, ta fara tuno abubuwan da wannan mai shagon ya dinga yi mata, a zahiri tace "inhar zai dinga bani kuɗi in dawo in samu Ummana cikin farinciki zan dinga zuwa"

Kafin ta ɗauki abincin ta fara ci hankali kwance.

IFFAT

Yau kwananta Uku a asibiti, Hajiya babba ce ta koma kula da ita, Hakeem kuwa ya jingine zuwa aiki, saboda koda wane lokaci ka gansa baya cikin nutsuwa, yau ake saka ran sallamarsu, tunda jikin Iffat ɗin ya sauka, an samu ƙwararrun likitoci wanda sukazo daga waje, duk da taimakon Dady da shugaban asibitin, kasancewarsu abokan juna tun suna makarantar sakandare, idan mutum yaga Iffat komai rashin tausayinka dole ka tausaya mata, duk da uwarta mahaukaciya ce, bai hana jikinta yin kyau ba, ga yalwar gashi, amma yanzu ta koma kamar tsinke tsabar sirantaka, gashin kanta kuwa yayi wani iri, duk da dama ba gyara yake samu ba tun asali.

Iffat ɗin na zaune akan cinyar Hakeem wani baturen likita ya shigo, cikin nutsuwa ya kalli Iffat kana yace "insha Allah akwai alamar nasara, a binciken da mukayi mun gano ciwon beyi mata yawa sosai ba"

Niko sai kallonsa nake, saboda inda yake magana kai kace wanda yayi rayuwa cikin hausawa.

Kafin yaci gaba da cewa, akwai buƙatar ta dinga samun walwalah koda wane lokaci, a guji ɓata mata rai, sauran bayanan zamu rubutasu"

Ya nuna Hakeem yace, ya biyoshi office,

Kafin ya miƙe ya kamo hannun Iffat yace "tare dake zamu tafi"

Iffat kawai kallonsa takeyi amma sam ta kasa magana, sosai takejin bakinta yana yi mata nauyi sosai, haka suka tafi tana ɗan ɗingishi, suka ƙarasa office, aka basu magunguna da sauran abubuwan da ya kamata a kiyaye kana ya miƙawa Iffat hannu, har yanzu kallonsa takeyi, Hakeem ya kamo hannunta yasa ana doctor, kana yace "Kyakkyawar yarinya inayi miki fatan samun lafiya"

Hakeem yace "insha Allah"

Lokacin da suka dawo ɗakin da aka kwantar da Iffat, dady yazo suka tattara kayan su suka wuce gida.

ALHJ AUWAL

Bayan ya gama binciken cigaban da aka samu da naƙasun da ya shigo, ya dawo gida da wuri kafin sallamar magriba, sbda lokacin ma ƙarfe biyar ne, tun da su Mahabob da Amani sukaji ƙarar tsayuwar motarsa suka fito da sauri, Amani ta buɗewa Alhaji murfin mota, bayan ya fito Mahabob ya ƙarɓi takardun hannunsa sukayi masa sannu da dawowa,

Cike da farinciki Alhaji Auwal yake kallonsu, kafin yace "Aseela da  Inaya ?"

Amani tace "Abba suna ciki"

Suna tafe suna hira suka ƙarasa cikin gidan, a parlo dukkansu suka yada zango, su Aseela suka fito, ko wanne yana ƙoƙarin tambayar Abban "ya gajiyar aiki"

Cike da nuna kulawa yace "Alhmdulilah albishirinku"

Dukkansu suka amsa da "goro" suna son a gaya,   musu.

"To yau dai burinku ya cika nayi budurwa, yanzu ma zan kirata, amma me kuke ganin zance mata?"

Amani tace "Abba Gaskiya ayi bikin da wuri, Mahabob yace "Abba nidai inason kafin bikin dukkanmu har da antyn muje Makkah"

Inaya tace "kai bro iyayen ita antyn basu da hankali ne, ba'a ɗaura aure ba zasu bayar da ita?"

Aseela tace "nidai Abba kayi mana kaya iri ɗaya da antyn harda kai"

Inaya tace "eyeeee Abba zai kawo mana anty"

Abban ya ƙyalƙyale da dariya kana yace "Mahabob sai anyi aure, wannan alƙawari ne, harda sabuwar mota zan siya muku kai da Amani da Aseela, ita kuma Inaya zan siya mata kayan wasa"

Dukkansu suka fara yi masa godiya, kana gurin yayi shiru, Abba yace "yau anje makaranta kuwa?"

Dukkansu sukayi shiru, sbda basu da gaskiya.

Mahabob yace "Abba ka kirata mu gaisa"

Dukkansu suka matso kusa da Abban,

Alh Auwal ya danna number Batool, ring ɗaya zuwa biyu ta ɗaga, cikin zazzaƙar muryarta, kafin tace "Aslamu alaikum Barka da yamma Alhji"

Mahabob da Amani da Aseela da Inaya suka zaro ido.

Alhji Auwal yace "Barka da fatan kin koma gida lafiya?"

Batool tace "lafiya lau"

Alhji Auwal yace "ga yarana zaku gaisa",

Bata damu ba, tace "to"

Cikin nuna ko ɗarr ya bawa Mahabob, ga mamakinta sai taji Muryar ƙato, bayan sun gaisa, aka bawa Amani itama bayan sun gaisa aka miƙawa Aseela, Aseela ta miƙawa Inaya, cikin shagwaɓa Inaya tace "anty ai zaki zamo Mamyn mu ko?"

Batool tayi murmishi kafin tace "eh insha Allah, ya sunanki?"

Inaya tace "sunana Inaya"

Batool tace "masha Allah suna mai daɗi"

Kafin Inaya ta miƙawa Abba,

Yana dariya yace "kinji Inaya da rigima ko?"

Batool tace "uhm"

Kana ya sake cewa "ki sanarwa da iyayenki zan aiko magabata na"

Nan da nan cikinta ya bada Ƙuuuuu,

Sai kuma tace "toh"

Sukayi sallama ya ajiye wayar.

Acan ɓangaren Batool, suna gama waya da Alhji Auwal, ta fashe da matsanancin kuka, cike da nuna kulawa mahaifiyarta dake zaune akan carpet ta kalleta kafin tace "Batool lafiya naga kina kuka?"

Cikin kuka Batool tace "Ummy wlhi wani Alhaji Auwal wanda yake da ma'aikatar sarrafa kayayyaki ne yace yana sona, dalilin haɗuwata dashi, naje Company ɗinsu gurin Sadeƙa, anan ya ganni, yanzu fa muka gaisa da yaransa, harda wani mai babbar murya, duk inda akayi ɗansa ma ya haifeni"

Ummy tayi murmishi kafin tace "lallai Batool sai yanzu na tabbatar da ƙuruciya na damunki, kin dangwalo mana arziƙi kina neman yi mana haramiyarsa? kin kuwa san alkairin dake cikin auran wannan mutumin?"

Batool tace "Ummy wataran zasu iya dukana fa"

Ummy tace "wlhi basu isa ba, jefa baki da wayo, bakisan irinsu masu shekarunan sunfi nunawa yara kulawa ba, bazai taɓa bari a rainaki ba, duk da mahaifinki yanada ɗumbin dukiya amma ai kema kinsan be kamo ƙafar Auwalu ba, inhar na isa dake ki sanarwa da Alhaji kokuma ni in sanar masa"

Cikin gamsuwa da maganar Ummynta tace "to Ummy ki sanar masa, nadena tsoro"

Kiraye-kirayen sallahar magriba yasa suka bar parlo Ummy ta wuce ɗaki domin tayi alwalah, Batool ma ta wuce ɗakinta.

Bayan anyi magriba, har lokacin sallah isha'i yayi, sannan Baban Batool ya dawo,

Da sallama ya shigo, Ummy tayi masa sannu da dawowa, haka ma Batool ɗin kafin suka hallara a dining, tuwon shinkafa Ummyn tayi miyar kuɓewa ɗanya wace taji  soyayyen kifi, kana suka fara ci, sam Batool ta kasa zagewa taci abincin sakamakon tunani da yayiwa zuciyarta ƙawanya,

Baba yace "Mamana lafiya kuwa?"

Kamar wacce ta razana tace "baba babu komai"

"A'a ban yarda ba"

Ummy ta ajiye cokali kafin tace "Alhji wai dan Alhaji Auwal yace yana sonta shine tabi ta damu mutane"

Baba yace "wane Alhji Auwal?"

Ummy tace "wanda dai ka sani to shi, ɗan kasuwa"

Baba yace "Mamana ke kinyi arziƙi ai ke abin alfaharinki ne ma, ace sunanki ya kewaye duniya"

Sunata ƙarfafa mata guwaiwa, har Ummy take gayawa baba cewar gobe zai turo da magabatansa,

Baba yayi murna sosai,

Acan ɓan garen Alhji Auwal bayan sunyi salloli harda isha'i, kafin suci abinci, Mahabob da Amani, sukace "Abba mu zamu siyo kayan lefe"

Alhji Auwal yace "kamar nawa kuke ganin zai isa?"

Sukace "sai dai munje gobe amma harda kai ko Abba?"

Yana dariya yace "a'a kune zakuje, ai kunsan duk abinda ya dace"

MALAM YUSUF.

Da ƙyar Juwairiyya ta taimaka masa ya miƙe tsaye, ta ɗauko tabarma wacce take ɗakinta ta shimfiɗa masa,  tasa masa pillow kana ta kwantar dashi, sai wash-wash yakeyi, tanayi masa sannu.

A wahalce yace "na rabu da Hajara na huta da ƙaya, Juwairiyya tace "ai kuwa wlhi Baba idan ka samu lafiya ka auro budurwa"

Malam Yusuf yace "ina ni ina auran budurwa, ƴan mata yanzu idanuwansu sun buɗe kowacce budurwa zakaji tana cewa sai mai mota.

Juwairiyya tace "nima baba ina fatan Allah ya bani mai mota"

Tana cikin magana wani yaro ya shigo tare da sallama,

Bayan ta amsa, akace wani mutumi yazo yace ayi masa sallama da Juwairiyya,

Juwairiyya tace "kace ina zuwa"

Ta miƙe tana cewa Allah yasa me mota ne.

Ɗakinta ta koma ta feshe jikinta da turare, kana ta lulluɓa mayafi ta fito,

A hankali ta kalli saurayin dake tsaye, kyakkyawa dashi son kowa ƙin wanda ya rasa, sai dai jikinsa wata koɗaɗɗiyar rigace wacce ta gaji da duniya, ƙafarsa kuwa tsohon silifas ne shima ba'a magana, a tsanake ta ƙare masa kallo kafin tace "a'uzubillahi wlhi nafi ƙarfin talaucinka, insha Allah sai me mota, ni zaka shafawa farar ƙafa, ma za wuce ka bani guri da jikinka kamar tsohon almajiri"

Saurayin yayi murmishi kafin yace "haba ƴan mata, baki tsaya kinji abinda zan..."

Kafin yakai ga idda maganar Juwairiyya ta shige ciki,

Abokinsa Mubashir ya ƙaraso yana dariya ya taɓa kafaɗarsa kana yace "Prince Abdul ya kamata ka dena wannan basajar da ka ɗauko wa kanka, ka fitowa ƴan mata a kamanninka, nan ne zakaga rububi, mahaifinka sananne ne, kai kuwa kwanan nan ka dawo daga, Bangkok"

Prince Abdul yayi murmishi, kana yace "nayi alƙawarin bazan taɓa auran matar da burinta ajiyemin yara da kuma burin mutuwata domin taci gado na, nafison matar da zataji tausayina kana ta soni tsakani da Allah, sannan kuma ta kula dani sannan ta haifamin yara masu tarbiyya, kasan kuwa zansha wahala, kuma yanzu na fara wannan shigar...!

Waye shi ?

Ya Rayuwar Iffat zata kasance?

Ina mahaukaciya

Juwairiyya fa?

Hajara?

Matar tsoho Batool?

Idan akayi comments na gobe sai yafi nayau

*💋MU RAYU A TARE💋*
             

Mom Islam

13-14

Kai tsaye su Prince Abdul suka wuce mota.
Mubashir ne a mazaunin driver, shikuma Prince Abdul yana kusa dashi, Mubashir ya harari Prince Abdul lokacin da yake tuƙi sun kusa fita a anguwar, dariya kawai Prince Abdul ɗin keyi, sbda haɗe fuska da Mubashir yayi, yasan faɗa zasuyi dole.

IFFAT
Yau kwanansu biyu da komowa gida, hankulan mutanen gidan duk ya tattara ga Iffat, saboda ta shiga ransu sosai, abin mamaki ko ruwa Iffat batasan ta inda zatasha ba, sai dai Allah bai mantar da ita sunansa ruwa ba, Hakeem kam koda wane lokaci yana ƙoƙari akanta da kuma abinda yake ganin zai gina mata jiki, washe gari, ta kama Lahadi, Dady yana gida, sbda tun asabar suke hutu, ya sanya Hakeem suzo shi da Iffat, yana riƙe da hannunta suka ƙaraso ɗakin dadyn yana zaune da tulin jaridu a gabansa, Hakeem yace "dady barka da rana"

Dady yace "my son anyi la'asar sai dai muce Barka da yamma"

Hakeem yayi murmishi kafin yace "hakane Dady, gamu"

Iffat kuwa tana ta wasa da jaridun kasancewar komai ta gani abun wasa ne, sbda ta zamo mai juyaiyyar ƙwaƙwalwa, batasan abinda zai amfaneta ba, bata kuma san abinda zai zamo illa ga rayuwarta ba.

Hakeem, wace shawara kake gani ya kamata mu yanke akan wannan ƙanwar taka?, ya kamata mu nemi iyayenta, Susan halin da take ciki, in yaso sai mu roƙi alfarma akan su bar mana ita muci gaba da kula da ita"

Tunda Dady ya fara magana Hakeem ya fara sharar ƙwallah, gani yake za'a rabashi da farincikinshi, yanayi mata so na ƴan uwan taka, sbda ada Hajiya ƙarama ta haifi wata yarinya mai kama da Iffat, sai dai waccar da tana duniya da tuni ta kusa shekaru goma, ita kuma Iffat bata wuce huɗu ba,

Dady yace "Hakeem bakace komai ba"

Duk da dadyn ya lura da yanayinsa, bayason goyon bayansa akan abinda basu da ƙwaƙwarar hujja akai.

Hakeem yaja numfashi "uhhhm"

Kafin yace "dady nikam da zakaji shawarata da kaci gaba da riƙeta har abada"

Dadyn ya girgiza kai, tare da faɗin "yaro-yaro ne tabbas bakasan komai akan duniya ba, dole daga yau zuwa ƙarshen satinnan mu fara bincikar iyayenta"

Hakeem dai bai gamsu da shawarar dady ba, babu inda ya iya, ita kuma Iffat ɗin wasanta ma takeyi, sai dai taji suna kiranta da Eshat, wato sunan yarinyar Hajiya ƙarama wacce ta rasu.

Dady yace "kuje"

Hakeem ya kama hannun Iffat suka wuce.

Suna komawa part ɗinsu, Hakeem ya kirayo Hajiya ƙarama da Hajiya babba, kana ya zaiyyana musu kaf abinda dady ya faɗa, ga mamakinsa sai yaji dukkansu sunce,"shawarar Alhji tayi dai-dai"
Cikin fushi ya miƙe yabar gurin.

ALHJI AUWAL
Dukkansu ya sa a mota suka wuce kasuwa domin siyayyar kayan Abban nasu,  sai yamma liss sannan suka dawo, ko wanne yana kukan ya gaji, bayan anyi sallahar magriba da isha'i, basu samu damar ɗora komai ba, sai haɗa tea, kasancewar akawai ruwan zafi a flaks, sai da kowa ya ƙoshi, sannan nutsuwa tazo musu, ita kam Inaya har tayi barci tsabar gajiya, Alhji Auwal ya kirasu duka, kafin ya fara tambsyarsu meye babu?

Amani da Mahabob sukace Abba saura kayan kwalliya, Aseela tace "Abba akwatuna har goma sha biyu?"

Amani ta buge bakinta,

Abban dai kallonsu ya koma yi, shima a gajiyen yake, ya miƙe yana ce musu sai da safe, sai a cigaba da lissafi.

Anan ya barsu suna ƙirga tsadaddun zannuwan da suka siyo, kaf ciki babu ta 6k ko sama da haka, daga na 10k sai sama, shadoji kuwa ba'a magana, haka ma leshi da sauran mayafai da kayan barci,suma suja kuɗi.

Aseela dama ta wuce ɗakinsu, Mahabob da Amani suka dinga jidar kayan suna kaiwa ɗaki suna dawowa, har sai da suka gama, tayiwa Mahabob sallama ta wuce ɗakinsu.

BATOOL
Kamar inda Alhji Auwal yayi mata alƙawarin washe garin ranar da suka haɗu zai turo magaba tansa, haka kuwa akayi, bai saɓa alƙawari ba sai gasu sun zo, da taimakon Batool ɗin.

Baban Batool shi da yayunsa uku suka zauna da dangin Alhji Auwal suma su Uku, bayan tattaunawa da sanar da iyayen Batool ɗin da sukayi Alhajin yanada yara, kana suka ƙara da cewar tun Inaya na jaririya mahaifiyarsu ta rasu, wato gurin aihuwa,

Iyayen Batool sukace Allah yayi mata rahama, ai duk ɗa na kowa ne, sunyi shedar Batool bata da matsala game da hakan,
Daga nan suka buƙaci a yanke musu dukiyar aure, iyayen Batool sukace 200k, su kuma iyayen Alhji Auwal suka miƙa 500k, a matsayin sadakin Batool harda kuɗin gaisuwa a haɗe.

Masha Allah kowa yakeyi, abu yayi Alhji Auwal ya haɗu da gidan karamci, dan an karrama su, daganan aka sanya rana sati biyu masu zuwa, sukayi sallama, koda suka bar gidan, suna hanya lokacin ƙarfe tara na dare 9:pm suka kira Alhji Auwal suka sanar masa da duk inda lamuran ya wakana, tare da sanar masa da cewar ansa biki kamar inda ya buƙaci a sanya masa, wato sati biyu"

Yayi musu godiya sosai.

HAJARA
Tun da aka kwaso kayanta a gidan malam Yusuf, Goggo take cikin fargaba, da tsoron hukuncin da mahaifin Hajara zai yanke idan ya dawo, yau kwananta biyu da zuwa, yau ne kuma malam ɗin ya kira waya, a wayar mai shago dake ƙofar gidansu, dama idan yayi tafiya shi yake kira sai a bawa Goggo, bayan sun gaisa ya sanarwa da Goggo yana hanya,

Hankalin Goggo a tashe tace "Allah ya kawoka lafiya, ta ajiye wayar saboda tunani wanda ta riga tayi nisa a kansa.

Zuwa yamma sosai an kusa kiran sallah sai ga malam ya rangaɗo sallama, fuskarsa cike da murmishi, Goggo taje itama da fara'arta ta karɓi jakar hannunsa tanayi masa sannu da dawowa, yauwa yace tare da zama kan tabarmar da aka shimfiɗa a tskar gidan, sai ga Hajara nan ta fito daga nakewayi, a faɗace yace "ke kuma wane irin iskanci ne nan da nan sai kinzo kwana?"

Hajara ta sunkuyar da kai, kafin tace "baba ya sakeni ne"

"Ya me??"

Wannan ƙarya ne, wlhi sai dai ki nemi gidan wani uban badai ni ba, bazan iya zama dake goɗai-goɗai da girmanki a gida ba, tamm abinda Goggo take gudu ya afku, Goggo ta share hawayen dake sintiri a fuskarta kafin tace "malam kayi haƙuri mu rungumi ƙaddara, kowane bawa da tasa ƙaddarar yake zuwa, kasan dai haƙurin da Hajara takeyi da Yusuf ba kowacce mace ce zata iya zama dashi da fitsararriyar yarinyarsa ba"

"O' hoo kice harda sa hannunki ta nemi saki a gurin mijinta, nidai nace ta nemi wani gidan wallahi kinji na rantse ba gidana ba"

Hajara na kuka, ta shiga ɗaki lokacin ana kiran sallahar magriba, ta ɗauko jakar kayanta, Goggo ta miƙe ta bi bayanta, kafin ta kamo hannun Hajara tace
End Ads