koda yaushe yanayi Mata kallon Eshat ɗinsa ne, suna zuwa ShopRite dady ya haɗu da abokansa turawa, sai ɗaukar Iffat sukeyi suna cewa yarinyar tanada kyau, dady yana yi musu godiya, sbda Iffat yarinyace Mai shiga ran Wanda ya raɓu da ita.
LIBYA
Sosai Mona taji sauƙin jikinta, duk wani motsi nata yana tafin hannun Shahazad,
Washe gari ta kama monday da misalin ƙarfe 5:am Shahazad ya fito cikin shirinsa na fita aiki, bata saba ganin ya fito cikin wannan lokacin ba, tana cikin barci, taji kamar a mafarki an turo ƙofarta,
Firgit ta farka tare da miƙewa zaune, kallonsa kawai take ba tare da tace dashi komai ba, tako cikin isa tare da zama kan bed ya miƙo wuya kamar me neman wani abu, hannu ya tura cikin aljihun suit ɗinsa ya ciro biro kana ya buɗe tafin hannunta ya rubuta mata, idan har kika kwashe sirrin komai nawa kika bawa mutane sai na kasheki"
Da sauri ta fara ja da baya, alamar tsoro,
Yana wata makirar dariya yace "ai ban kashekin ba, gargaɗi dai nayi miki akan ki riƙe bakinki"
Yana faɗar haka ya gyara gashin bakinsa, yayi Mata kiss a goshi ya fice,
Da sauri ya ke sauka daga kan steps yana waya, har hajara ta fito, tana hangoshi ta koma da gudu,
Cikin wayartasa ne yake cewa "banason wasa, hannu na da naka gobe zamu shiga India, jirgin safe zanbi, ku zamo cikin shiri, duk Wanda yayi gardama ku harbeshi"
Kafin yace "Hajarr.."
Da sauri ta fito daga d'akinta tare da zubewa a ƙasa tace "Barka da fitowa me gida"
"Yauwa ki kulamin da matata kar in ji mummunan labari a kanta idan har naji hakan' hhhh, ki ƙaddara kin mutu"
Jikin Hajara na rawa tace "hakan ma bazata faru ba da yardar Ubangiji"
Har yayi gaba, ya juyo yace "nasa 1 million a account ɗin da sisternki ta bani lokacin da kukazo"
Hajara tace "godiya nake Allah ya saka da alkairi"
"Amin yace kana yayi gaba"
Jikin Mona a sanyaye ta miƙe tsaye, dan ita ba sallah takeyi ba, amman shi Shahazad yanayi shima ɗin dai sai a hankali,
Cikin sauri ta sauko ta nufi ɗakin Hajara, ta samu tana sallah,
Bayan Hajara ta idar da sallahar tace "Barka da safiya Madam"
Barka "Hajar inason in baki labarina Please ki taimakeni, ina ganin kamar kece zaki iya miƙani ga iyayena"
Gaban Hajara ya bada rass tare da tsoro, tace "idan inada halin hakan zan taimaka miki, amma karki manta muna cikin hatsari ni dake"
Mona tace "karki damu Bama cikin hatsari, amma kin iya aiki da computer?"
Mona ta tambayi Hajara.
"Gaskiya ban taɓa amfani da ita ba, amma ina ganin abubuwa in karanta"
"Akwai wata wacce Shahazad ya siyamin, sbda harkar kasuwancinsa da yakeso in temaka masa, nikuma bani da ra'ayin hakan"
"Uhm nifa tsoro nakeji dan Allah karki ɗauko"
Hajara ta faɗa tana runtse idanu.
Cikin rashin tsoro Mona ta miƙe, tare da, ficewa da gudu.
Computer ta ɗauko ta fito hankalinta kwance, bazaka gane tsoro ya gushe a zuciyarta ba, har sai kunga inda ta zauna a parlo tana sarrafa computer hankali kwance,
"Hajarr"
Mona ta ƙwala mata kira.
Cikin rawar ɗari ta fito, kamar me jin sanyi, ta zauna daga nesa.
Kai tsaye Mona ta shiga searching ta rubuta Shahazad forest,
Da sauri Hajara ta matso kusa da Mona tana cewa "mijinki yanada wani gari ne mallakinsa Kuma me sunansa?"
"Eh yanada anan muke rayuwa"
Gaban Hajara ya sake faɗuwa, ta fara jajantawa kanta mutuwarta, sbda har ta hango inda Shahazad zai kashesu babu tausayi,
"Hajar kalla ki gani ga wani video"
A tsorace Hajara ta sake matsowa, videon kashe-kashen da akeyi a yankin ta gani, tare da mutanen ƙauyen da suketa guduwa, gudun ceton rai.
"Inaso inje jejin nan domin inga iyayena dangina da sauran ƙawaye na, zamana a ƙauye nan yafi min zaman ƙuncin da nakeyi a wannan gidan"
Hajara tace "tabbas garinku-garinku ne, amma ni sai nake gani kamar zaman gidannan yafi karɓarki"
Hajara tayi maganar domin kaucewa Maganar Mona.
Gaskiya "Hajar kin yi kuskure sbda wannan gidan da kike gani kamar lahira yake, ina tsoron Shahazad, haka kawai yake zuwa ya kashe mutane ba tare da sunyi masa komai ba, shiɗin mugu ne"
Hajara dai, idan ta tuno da gargaɗin Shahazad gareta sai cikinta yayi ƙugi, tsabar tsoro.
Daga ƙarshe Hajara ta zame ta durƙusa gaban Mona kafin tace "dan Allah kiyi haƙuri ki gafarceni ki mayar da wannan abun, saboda wlhi tallahi zai iya haɗawa dake ya kashemu, ina ganinsa kamar me wankin idanu"
Mona ta rufe computer tare da murmishi tace "komi daran, daɗewa wlhi sai na koma garinmu"
Hajara tace "wlhi ni zaki shafawa dan bazai taɓa amincewa da abinda zance masa ba, nima kasheni zeyi, ki gafarceni"
Mona ta miƙe tare da hayewa steps tana sheƙewa da dariya.
Tunda Hassana ta koma ɗakinta tunanin Ala-Uddin Samir ya addabi rayuwarta, duk zuwanta gidansa da takeyi bata taɓa tsammanin haka yake ba,
Acan ɓangarensa yanason Lulu tayi barci yaje ya dubo Hassana ya gani, shin maganin ya fara aiki.
Sai shafata yakeyi yana cewa "my Lulu ya kamata ki kwanta ki huta, bakya samun enough time da zaki dinga barci da rana"
"Hub idan ina tare dakai sam barci ƙauracemin yakeyi sbda tunaninka, amma yaushe ne zamu je masarautar ku"
Ta faɗi maganar tana kashe masa idanu,
"Ya kamata muje a cikin watannan sbda wasu shirye-shirye da nakeson gabatarwa a gidan, duk da bani da uwa uba duk sun mutu nine zan zamo mahaifin kaina, inaso in kawar da Nara a doron ƙasa, inaso Raza ya zamo maƙasƙanci a ƙarƙashina, inaso in tura ahalinsu wata duniyar, a halin yanzu na gama zana irin kujerar da zan sauya zanen taswirarta bayan nahau, ko bakyaso a kiraki da Princess Lulu?"
Cikin farinciki tace "tabbas Nima na gano wani haske a tafiyar, sai dai kasan mutanen garinnan matsafa ne, meyasa bazamu shirya ba kafin muje"
Ala-Uddin ya bubuga kafaɗarta a hankali, kafin yace "kamar kin mance waye Ala-Uddin Samir?"
Ta tallafo haɓarsa tare da sanya harshenta a cikin bakinsa, ta fara karkaɗawa...
Mom Islam
*💋MU RAYU A TARE💋*
Mom Islam
51-52
Sun daɗe cikin wanan yanayin.
Duk da haka zuciyarsa bata tare da ita, gangar jikinsa ne a tare da ita, hankalinsa ya tattara ga Hassana, itace burinsa da buƙatarsa, har waswasi yakeyi anya boka Namraj bai sanya masa soyayyar Haseeaina a zuciyarsa ba.
Kamo joyst ɗinsa da tayi tana mulmulawa ne yasa ya firgit, lokaci ɗaya yanayinsa ya sauya, sha'awar da yake yiwa Hajara ta rikiɗe i zuwa gurin Lulu,
Ganin ya zuba mata narkakkun idanuwansa, ya sanyata rungumeshi murya ƙasa-ƙasa tace "my Hub meyasa bakason saukemin haƙƙina alhalin kasan l love sexy Hub musamman da ƙirar jikinka take gwada jarumtarka"
"Uhm Lulu nima inaso, sai dai some times tunanin kujerar da zan hau, take janyowa inji bana marmarin wata mace a kusa dani"
"Haba my hub yakamata ka nutsu ka San Lulu zata taimakeka, kadena sanya damuwar da ta zamo ƙarshe a tarihin rayuwarmu, zanyi komai dominka, amma yanzu lokacin Hub da Lulu ne"
Baya da zaɓi daya wuce ya biye mata, tunda bai samu ta ɓangaren Hassana ba,
Da kanta ta cire masa komai tana wani shafeshi kamar mage, ko wane sashi na jikinsa da lungu lashewa takeyi, cikin salo na jan hankali,
Acan ɓangaren Hassana, ta kammala haɗa kayanta a jaka, burinta taji muryarsu a parlo ta tambaye su zata koma gida mahaifiyarta babu lafiya, tayi kuka har ta gaji, idanunta sun kumbura, wannan zuwan bata zo a sa'a ba, ko tun da ɗin ma dai batasan yana amfani da ita bane oho?.
Daga ƙarshe ta fito parlo ta zauna sanye da hijabi, da jakar kayanta a gabanta, takai kusan awa a zaune, sai da ƙarfe 1:20pm tayi, sannan suka fito rungume da juna,
"Hassienna akwai matsala ne, na ganki da jakar kaya a gabanki?"
"Babu inda zaki ai ba haka mukayi dake ba"
Ala-Uddin ya faɗa yana juyar da kansa gefe.
Cikin tausasa murya ta sauko kan carpet ta durƙusa kafin tace "dan Allah, kuyi haƙuri ku barni in tafi mahaifiyata babu lafiya"
"Mahaifiyarki zata samu lafiya nawa kike da buƙata a tura mata?"
Lulu ta tambayi Hassana cikin tausayawa.
Dai-dai lokacin da zata buɗe bakinta tayi magana, hawaye suka zubo a tare tace "ina buƙatar ganinta dan Allah kuyimin rai"
Lulu ta ciro wayarta a aljihu kana tace samin number,
Sai da tayi jimm bata motsa ba, Ala-Uddin Samir yace "muna jiranki"
Jikin Hassana na karkarwa tace "ba sai kun kirata ba, duk da kunajin Hausa amma ita bataji"
"Okay okay shi kenan ai ke kinajin Yaren da takeji ungo saka number ki kirata muyi magana"
Bata da zaɓin daya wuce ta kirawo Inna, cikin rashin sa'a koda aka gwada number bata tafiya,
Ala-Uddin Samir yace "bazakije ko ina ba, ance miki zuwa Nigeria kamar zuwa nan da cikin garinan ne?"
Da sauri ta ɗauki jakar kayanta ta koma tana kuka,
"Da girmanta amma bata da ikon yin komai, mtsw"
Bayan tafiyarta, Lulu tace "Hub na rasa abinda ke damun Haseeaina"
"Mance da maganar sakarci ne kawai"
Washe gari, bayan sunyi brakfast, cikin sauri Lulu suka shirya fita, Ala-Uddin Samir zai ajiyeta a makaranta daga nan ya wuce gurin aiki,
Hakan yasa Hassana ta samu damar sake fito da jakar kayanta ta fito da gudu, kamar haɗin baki duka masu tsaron gidan basa nan.
Da gudu ta fice, anguwar shiru babu mutane, hakan yasa ta dinga gudu kamar bazata tsaya ba.
Cikin sa'a wata mota ta fito tana tafiya a hankali, ganin Hassana yasa mai motar tsayawa yace "can I help you?"
Jiki babu ƙwari ta juya ta kalli wanda ya kawo mata wayar, kana tace "ina ne cikin gidan?"
Ga ba ya shige, tana binsa a baya har suka isa, cikin gidan. Kawai zan iya ce muku gidan ya haɗu, ba ƙaramin kuɗi ya kashewa gidan ba, sbda muhimmancin masu zaman gidan.
Sai da ya nuna mata ko ina sannan ya miƙa mata keys na gurin da kuɗaɗe suke ya fice.
Takasa cewa saurayin komai, duk da tanayi masa kallon kamar mai sauƙin kai.
Abin mamaki, gabaki ɗaya wayarta babu network ya ɗauke.
Tunda Mona ta koma ɗakinta, mai makon ta ajiye computer kamar inda Hajara ta gaya mata, sai ta sake buɗewa tana searching manya-manyan ƴan ta'addan ƙasar Libya.
Farko Shahazad ta gani a farko, sannan Ala-Uddin Samir, sai Karan Khan, su Uku a jerin wanda akayi cancel da jan biro.
Hoton wani saurayi ta gani a gefe Mai suna Karan, kyakkyawan matashi mai ji da ƙarfi, da sauri ta bibiyi profile ɗinsa, kana ta shiga gurin chart tayi masa magana, da farko ta rubuta please I need your help don't forget to call me kana ta rubuta masa numberta, ta ajiye ta fita tare da kashe computer.
Kafin ta zauna tana ci gaba da tsarawa zuciyarta da rayuwarta mafita,
Hajara na zaune a parlo har yanzu ta kasa motsawa nan da can, ring ɗin wayar tafi da gidanka yasata saurin miƙewa ta ɗaga, "gobe ku shirya kuzo gurin bikin ƙanwata anan Ghat, nayiwa driver magana, sannan nasa a shirya komai, ki kularmin da Mona, na damƙa amanar Mona a hannunki, tabbas idan wani abu ya sameta sai na sheƙe ki....
Kuyi haƙuri wlhi ciwon kai tun jiya nake fama dashi
Mom Islam
*💋MU RAYU A TARE💋*
Mom Islam
53-54
Bayan ta ajiye ta haura sama tayiwa Mona nocking, bayan ta buɗe ta gaya mata saƙon da Shahazad ya sanar mata.
Daga haka ta juya ba tare da Mona tace komai ba.
Kai tsaye computer ta ƙara janyowa kana ta kuma serching sunan Kharan, duk da shi wancan wanda aka haɗa hotonsu sunsa karan Khan, shikuma wannan karan sunansa,
Cikin sa'a taga yasa mata, "a ina zamu haɗu insha Allah zan taimaka miki"
Cikin sauri ta fara typing tace "gobe zamuje Ghat nida auntyna Please ka kawar dani daga gidan Shahazad, mugu ne"
Da sauri ya turo mata, "idan da wannan number kikeyin whatsapp ki yimin magana, karki sake magana a system"
Nan da nan tasa number tayi saving sai gashi ta ganshi a online.
"Me ya kaiki gidan Shahazad?"
Bata da amsar da ta wuce tace "ƙaddara" hakan ko ta rubuta masa.
Yayi mata voice da cewar "a halin yanzu Shahazad ya fita a garin Libya jirginsu ya sauka a Bangkok, inaso kiyi taka tsantsan wajen kare kanki da duk wata hanya da zatasa ya gano inda kike"
"Eh zanyi ƙoƙari amma a ina zamu haɗu?"
"Bani adreshin gidan bikin zanzo da kaina ba tare da kowa ya sani ba"
"Mona tasa masa emoji na murmishi tare da yi masa godiya, ta tura masa bayanan komai akan anguwar da zasuje"
Hajara nacan kitchen tana ɗora abinci, ga mamakinta sai taga Mona ta fito yau fuskarta wasai da farinciki, tace "Hajarr yau inason cin Kaji kabsa da Zabibi"
Cike da kulawa Hajara tace "Madam yau kina cikin farinciki kodai oga yana hanya ne?"
Hajara ta faɗa da alamar zolaya.
"Haba Hajar, dan zai dawo yau kawai sai inyita farinciki nikam haka kawai nakejin shauƙi"
Hajara ta cigaba da haɗa abubuwan da zata buƙata, ita kuma Mona ta koma ɗakinta tare da lodar kaya masu yawa.
*********
Duk da kyawun gidan, bai hana Hassana jin tsanar gidan a ranta ba, sam gidan ya isheta, Abin takaici network ɗin wayarta bayayi, meke shirin faruwa da ita?, gashi ɗazu yaron da Ala-Uddin ya kira, kiran ya shigo wayarsa amma ita kira baya tafiya, cikin fushi ta miƙe tsaye tana zagaye ɗakin, a ƙasan zuciyarta tana nadamar zuwa Libya
aiki
Mom Islam
*💋MU RAYU A TARE💋*
Mom Islam
55-56
Washe gari da wuri suka shirya domin halartar taron bikin sistern Shahazad, sai da Mona ta tabbatar da ta gama shiryawa barin garin.
Abin mamaki wanda Hajara ta daɗe bai wuce mata ba shine, fitowar da Mona tayi ko jinkiri babu, a parlo ta zauna tana jiran Hajara, har Hajara tayi wanka ta shirya cikin doguwar riga irin ta larabawa ta fito rataye da jaka a kafaɗarta, Mona batace mata
komai ba, duk da hankalinta ya raja'a akan waya,
"Madam tun ɗazu shugaba ya kira yana tambayar mun tafi?"
Zuciyar Mona wasai tace "mun gama komai ni dama ke nake jira, sai kaya da zan sauya"
Hajara tayi murmishi sbda Sam ta kasa gane inda Mona ta dosa.
Sanye da riga da wando Mona ta fito tare da ɗaura siririn mayafi a kanta kana suka wuce gurin mota, driver na ganinsu ya buɗe suka shiga, kana ya rufe, motoci biyi na biye dasu.
Har sukayi nisa Mona bata ɗago kai ta kalli titi ba, har sai da taji alamun mota ta daina tafiya sannan ta ɗago kai ta kalli Hajara, Hajara ko hankalinta na gurin masu wasa da ta hango a filin gurin.
Driver ya buɗe musu mota tare da ɗaukar kayan Mona da jakar Hajara aka shigar ciki, tashi ɗaya hankulan mutanen gurin sukayo kan su Mona, dama bawai ta taɓa zuwa gidan bane, sbda Bama kowa ta sani ba, tunda wannan shine karo na farko daya barta ta shiga cikin taron mutane.
Suna tsaye wata budurwa tazo gurinsu, cikin farinciki da ɗaga murya take cewa " matar yaya tazo"
Hankulan mutanen gurin sukayo kansu, wata farar mata Balarabiya kamar su ɗaya da Shahazad ta rungume Mona tana cewa "Hindu zoki shigar dasu ciki"
Hajara sai murmishi takeyi, Sakamakon tattali da kula da taga mahaifiyar Shahazad take gwadawa Mona, riƙe da hannun Hajara aka shigar da Mona ciki,
Bayan sun huta lokacin da aka kira sallahar azhar Hajara ta tashi ta shiga toilet ɗin ɗakin da suke ta ɗauro alwalah kana ta shimfiɗa ɗankwalinta ta kabbara sallah, ga dukkan alamu ba sallah mutanen gidan sukeyi ba, abin ya bawa Hajara mamaki sbda wasu lokutan tana ganin Shahazad yana Sallah, duk da hakan shima bai mayar da ita farilla ba.
Hajara na idarwa Mona tace "idan kin shirya gujewa wannan mugun zan tafi dake idan kuma zakici gaba da zama shikenan"
Murya ƙasa-ƙasa Hajara tace "ban fahimci me kike nufi ba?"
"Ina nufin zamana ya ƙare tare tare dashi, dama na daɗe ina neman mafita da muhimmiyar yanya yanzu ko na samu komai"
Hajara tayi murmishi mai cike da tarin tambayoyi kana tace "bakya tsoron idan ya gano komai yasa a kashemu?"
"Haba Hajar wanda zai tafi damu nan da mintuna talatin zai ƙaraso"
Hajara tace "shikenan amma nayi farinciki"
Suna zaune aka dinga jere abinci kala-kala a dining kana aka umarcesu da suje suci.
Koda sukaje cin abincin kaɗan sukaji, a zahiri jikin kowacce daga cikinsu ya tsinke,
Sannan ko wacce da tunanin da takeyi a cikin ranta.
Wayar Mona tanayin ringing suka miƙe a tare, Mona ta kalli agogon dake manne a bango 6:30pm ga haske ta ko ina, tashi ɗaya duhu ya gauraye ko'ina na gidan, hakan yabawa Kharan damar ce mata ta fito ta ƙofar baya, yana jiransu,
Cikin sanɗa suka fita riƙe da hannun juna, kana suka isa gurin motar, motarsu na tafiya haske ya baiyyana a gidan, kasancewar mutan gidan a gajiye suke, maman Shahazad tasa Hindu ta je ta nuna musu gurin kwana, cikin rashin sa'a Hindu na shiga taga wayam, babu su babu kayan su, ta duba toilet nan ma shiru kana ta zaune tana dogon nazari, sannan kuma ta fara tunanin me zataje ta cewa mama?.
ALGERIYA
Ikon Allah kenan yafi gaban wasa, yayinda lokuta suke tafiya kwanaki suke shuɗewa, yau kwanansu Hajiya ƙarama goma sha huɗu, 2weeks a Algeriya, inda sukayi nasarorin samun lafiyar Iffat tare da nasara akan aikinsa, gobe suke sa ran zasu koma