"ki wuce gidanmu kawai, gobe da safe ina nan zuwa....
Ayimin afuwa dan Allah
*💋MU RAYU A TARE💋*
     Â
Mom Islam
15-16
Washe gari da wuri su Alhji Auwal suka koma kasuwa domin ƙarasa siyayya, Alhmdulilah yau kam sun gama, sun yiwa Batool siyayya ta gani ta faɗa,  har da ankon shaddar da Abban nasu yayi musu alƙawari duk sun siya, daga can ma suka miƙa ɗinki.
Sai bayan sallahar azhar sannan suka dawo, wannan karon sun biya gurin sha ice cream, da su shawarma da pizza, daganan suka dawo gida,
Alhji Auwal ya wuce masallaci wanda yake jikin gidansu, su kuma suka shiga yin alwalah, bayan sun idar sun fito parlo, Mahabob ya shigo, kafin ya zauna, sukaji anata rangaɗo sallama, da sauri Aseela ta nufi bakin ƙofa tana cewa "waye?"
Baba Amarya ita da Anty Saratu da Inna Binta suka ce, "kinci gidanku, zaki buɗe mana ko sai ranki ya ɓaci?"
Amani ta miƙe da sauri, tana cewa "oyoyo su Inna amarya sannunku da zuwa"
Bakinsu a washe suka shigo ciki, tare da kallon Mahabob dake ƙoƙarin zamewa ya gaishe su, sai da suka zauna sannan Mahabob ɗin ya gaishe su, suka amsa cike da nuna kulawa, kafin Inaya taje gurinsu tana dariya, da fara'arsu suka amsa, Inna Binta ta kamo hannunta,
Kafin anty Saratu tace "ashe bikin Alhji ya kusa, shikam dangi sun isheshi baya neman kowa?"
Amani tayi murmishi kafin tace "wlhi mun ɗauka su Kawu sun sanar muku ne, shiyasa kuyi haƙuri"
Dukkansu suka amsa da "babu komai, dama munzo ne muji me yakeso a siya masa, kayan sa lalle kokuma kuÉ—i"
Amani ta rufe baki, tare da cewa "bro Mahabob Please tayani mu kwaso kayan akwati kaga mun mance ashe harda wani abu ne?"
Suka kwaso akwatunan, Anty Saratu ta riƙe baki, tare da cewa "wato har kun gama komai naku ba tare da neman shawara ba?"
Ba su ce mata komai ba, sai cewa da Aseela tayi, ya kamata kayan sa lalle zaku siya, suka amsa da "toh"
Lokacin sun buɗe akwatuna ko wanne sai riƙe baki yake, inna Binta tace "waɗannan kaya ma sunyi yawa a rage su"
Amani tace "wlhi akwai wanda sukafi wannan, Ace kamar Abba zai kai kaya sai an nuna ƙaranta?"
Anty Saratu tace "ke rufewa mutane baki"
Ana cikin muhawara sai ga Abban ya shigo,
Cikin fara'a yake yi musu sannu da zuwa, bayan sun gaisa suke shawartarsa akan a rage kayan akwati, furr yace a'a idan da ƙari su kawo, suka tambaye shi kayan sa lalle, yace "eh suyi shikam besan ma anayi ba"
Da suka tashi tafiya, Amani ta kawo musu drinks, sukayi musu sallama suka tafi.
HUDA
Yau ma kamar koda yaushe, Umman ta kammala dafa shinkafa da miya, ta zub a kula, kana ta ƙwalawa Huda kira,
Da sauri ta fito, yau kam tana sanye da riga irin ta gwanjo mai dogon hannu sai skel dogo wanda ya saukar mata ƙasa, ta fito tana gyara mazaunin hijabinta, kafin tace "Umma sannu da aiki"
"Yauwa" Umman tace, tare da É—ibo cokula tana ajiyewa,
Ƙarar mashin ɗin da sukaji ne, yasa Umma da Huda suka fara jidar kayan suna kaiwa gurin mai mashin ɗin, Umman na ajiyewa a zaure, Huda kuma na ƙarasawa dashi,
Leƙowa Umman tayi ta bata kuɗin mashin kana tayi mata Allah ya kiyaye hanya,
Huda na isa gurin siyar da abinci, mai mashin ya tsaya, ta sauke kayan tare da miƙa masa kuɗi ya wuce.
Sai da ta gaishe da mutanen da suke gurin kafin ta nemi guri ta zauna, ko wanne na tsokanarta,
Yau kam gidan mai ya cika da motoci, kasancewar ana lodin garuruwa anan, lokacin fara siyan abinci nayi, mutanen gurin suka sisiya kana masu tafiya suka wuce.
Wasu mata su biyar suka taho gurin huda, dukkansu sukace a sanya musu abinci na É—ari uku, ya kama duka É—ari bakwai da hamsin kenan, Huda ta sanya musu takai musu motar da suke, da mota ta tashi tafiya matan suka ajiyewa Huda robobin suka tafi, can anjima ta taho kafin takai ga gurin ragowar motocin taci karo da robobinta, hankali a tashe ta zaro ido tare da fashewa da kuka, tace "shikenan sun tafi, na shiga uku na lalace yau Umma zata kasheni"
Tana kuka ta dawo gurin zamanta, mutanen da ta barsu a gurin suma sun tafi, sai da tayi kuka mai isarta, gashi abinci ya ƙare babu kuɗin robobi biyar,
BATOOL
Kwanci tashi asarar me rai, ikon Allah biki har ya rage saura kwana tara, Ummy kuwa sai É—irkawa Batool magungunan mata takeyi a cewarta Alhajin ya daÉ—e babu aure baze yi mata da wasa ba,
Shi kuma Baba duk abinda Ummy ta gaya masa sai ya biye mata, anyi mata haɗin turaruka da duk wasu kayayyaki na gyaran jiki, idan kaga Batool har wani walƙiya take, tsabar kyau, dama bazamu kirata da mummuna ba,
Ƙawayenta kuwa tunda sukaji Alhji Auwal zata aura ko wacce sai shishige mata takeyi, har biki ya rage saura sati ɗaya, anata shirye shirye, ango kuwa kwata-kwata zuwansa befi sau biyu ba, yace kar a siyi kayan gado, iya kayan kitchen zasu siya, duk da yana dashi.
A rana ta shida ne, Batool taje gurin dangin Ummynta, suma can ba'a barsu a baya ba, gurin ɗurka mata jiƙo na ƙarin ni'ima da neman zaman lafiya lolz,
Kwananta biyu, ta dawo gida, sai da ta kwana ɗaya a gida kana taje ɗangin babanta, sukuma tayi musu kwana uku,biki ya rage saura kwana huɗu, washe gari ta dawo gida,
A ranar da ta dawo, a ranar aka kawo kayan akwati da na sa lalle daga ɓangaren Alhji Auwal, su Inna amarya da sauran dangi ne suka kawo.
Dama sun san da zuwan kayan, suka shirya musu sha tara ta arziƙi, kafin da suka tashi tafiya aka basu 30k a matsayin tukaici, sunyi murna sosai da karamci irin na gidan baban Batool,
Washe gari akayi mata su dilka dama anayi mata, amma bai kai na wannan lokacin ba, koda yaushe anayi mata wankan turare, suma sun kashe kuÉ—aÉ—e masu yawa.
HAJARA
Bayan tayiwa su Inna wato mahaifiyar Goggo bayanin sakin ta da Yusuf yayi, Inna tace "ko wane bawa da tasa ƙaddarar, nidai kin ganni nan babu mai bani sai na fita tallar kayan koli sannan nake samun abinda zanci, idan ba damuwa, kiyi shawara da Goggonki ki siyar da kayan ga donki ki fara sarin kayan sawa ko gwajo ne, kina shiga dashi ƙauyika,
Hajara tace "to insha Allah zan gaya mata"
Washe gari, kwanan Hajara ɗaya da zuwa, basu suka karya ba sai wajen azhar babu abinci, a hakan ma sai da Inna ta aika Hajara karɓo mata bashi sannan suka samu suka siyi lifton da bredi,
Ƙarfe uku dai-dai, inna ta ɗauki tallar kayan koli ta fice, Hajara ta zauna tayi jugum tana tunani iri-iri, can zuwa la'asar sai ga Inna ta dawo, hannunta riƙe da leda babba, Hajara da ta idar ta sallah taje ta karɓa, tanayi mata sannu da dawowa, Inna tace "wlhi biyan bashi akayi min da garin rogo shine na karɓo"
Hajara tayi shiru, suna cikin magana, wata ana ce mata Hassan mai kyau ta shigo, Hajara na ganinta ta washe baki, saboda sun san juna tun ba yau ba, halin Hassana ne yasa Hajara rabuwa da ita, akwai ta da munafurci da cuta harma da cin gumin da ba nata ba, bayan hakan bata shakkar ta ciwa uban kowa mutunci, a hakan dai inda tazo kamar ta gyaru, dan akwai alamun nutsuwa a tare da ita.
Hassana tace "Hajara ashe zamu sake haÉ—uwa?"
Hajara tace "ai kuwa gashi Allah ya haÉ—amu"
Goggo tace "banda mutuwa da auranta yayi ...
Kuyi haƙuri bani da chaji Please a tayani share Banda chaji dan Allah
*💋MU RAYU A TARE💋*
     Â
Mom Islam
17-18
"Mazan yanzu sun zamo abin tsoro wlhi aure ya zamo shige da fice yanzu, nikam tunda nayi wani aure shekaru uku da suka wuce, muka rabu tsiya-tsiya dashi, Allah yasa ma ban aihu dashi ba, tun daga nan na sallami aure"
Inna tace "Uhm Hassana, babu macen da zata iya zure tozarci da wulaƙanci irin wanda Hajara ta jure a gidan auranta, nidai nace mata ta siyar da kayan ɗakinta ta kama sana'a, saboda babu inda zamuyi mu zauna babu sana'a, tunda bamu da kowa sai Allah"
Hassana tace "idan babu damuwa Inna kuzo muje gidana sai muyi wata magana acan, zaku ganewa idonku ikon Allah"
Hajara tace "to Inna zamuje ko?"
Inna ta miƙe tare da janyo mayafi a jikin igiyar shanya tacewa Hajara "tashi muje"
Hajara ta miƙe ta ɗauko hijabi a cikin ɗaki kana suka fita tare da Hassana, suna tafe suna hira, har suka iso anguwarsu Hassana, duk da ba wani nisa ne da anguwar ba, amma akwai tafiya.
A bakin wani tangamemen get Hassana ta tsaya, hakan yasa suma suka tsaya, Hassana tasa key ta buÉ—e get É—in tare da cewa "ku shigo"
Duk cikinsu ko wanne tunaninsa be wuce yaji ina Hassana ta kawosu ba.
Kamar inda ta umarcesu suka shiga ciki har parlon nata, ta nuna musu tsala-tsalan kujeru suka zauna, Hajara harda sauke gwauron numfashi,
Hassana ta zauna a kujera mai kallon ta Inna kafin tace "Inna nasan zakuyi mamaki idan har nace muku nan ne gidana, anan nake rayuwa, ina aiki a ƙasar waje,
Jikin Inna yana rawa tace "ikon Allah kice har kin leƙa waje kin barmu, to wane irin aiki kikeyi?"
Hassana tace "wlhi aikin wanke-wanke a gidan larabawa, suna biyan mutum albashi mai kaurin gaske, shiyasa na dage, a cikin shekara É—aya kinga inda na zamo"
Tunda Hassana ta fara magana Hajara ta zuba mata ido, tana son cewarsu da ee de q, ya za'ayi nima inje, tana tsoron abinda Inna zatace,
Kamar daga sama, taji Inna tace "to yanzu kamar Hajara zata iya zuwa kenan?"
Free 3 se Waqqas Waqqas q ware se 3w welcome welcome 3
"Eh sosai ma, wlhi zata samu alkairi sosai, bayan haka kaf danginta sai sunyi alfahari da zuwanta"
Inna tace "gaskiya bamu da kuɗi, koda an siyar da kayan ɗakinta bazasu isa taje can ƙasar ba"
Hassana tayi dariya, kafin tace "haba Inna me kayan koli, nima mai iya yi muku jagora ne, ba tun yanzu nasan Hajara ba, wlhi tanada kirki, insha Allah zan taimaka muku, kawai ta fara shiri, koda tafiyar ta matso ya zamo a shirye take".
Cikin amincewa tare da sanya albarka Inna tace "mungode, yanzu kuma ya rage tsakanina da iyayen ta, idan sun amince zaki ji ni".
Daga nan sukayi sallama, a dawowa mashin su Inna suka hau ita da Hajara, ragowar kuÉ—in sukayi cefane, kasancewar kuÉ—in mashin biyu ta basu, sukuma suka hau mashin É—aya.
HUDA
Tunda takawo shinkafa mutane suka fara miƙa mata kuɗi, sakamakon yau ba da wuri tazo ba, ana tsaka da siyan abinci ta ruɗe, har wani ya tafi mata da kuɗi bata sani ba, sai da tayi lissafi kafin ta zabga tagumi, gashi gurin mai shagon da ta saba zuwa baya nan, shawara ta yanke zuwa gurin masu yin lodi anan tashar, gurin babu mutane kasancewar sai an gangara duk tana kai abinci nan, idan sunada buƙata, "dan Allah malam ka taimakeni ka bani ɗari uku in cika kuɗin abinci wlhi wani yaci ya gudu"
Wani dattijo wanda a ƙalla zeyi shekaru sittin ya kirawo ta, sakamakon wanda take yiwa magana ma waya yakeyi besan tayi masa ba, "biyoni ɗaki zan baki"
Jikin Huda na rawa tace "to"
Ba tare da jin ko mai b, ta shiga ɗakin da taga ya shiga, tunda idan ma bin nasa tayi bai wuce ya taɓa mata nonuwa ba ya bata kuɗi, cikin salo na wayo dattijon ya nemi wani buhu wanda yake a shimfiɗe a ɗakin ya zauna, tare da yi mata alama da hannu wato "kizo"
Sai yanzu gabanta ya fara faÉ—uwa, duk da bayan haka batasan komai ba, ta gwammace yayi mata abinda zeyi mata ya bata kuÉ—in kodan kauce wa dukan Ummanta,
Tana ƙarasowa kusa dashi ya ɗorata akan cinyarsa, tare da kunce mazugin wandonsa yana cewa "taɓa min nan, yanzu zan baki kuɗi"
Huda ta tura hannu cikin tashin hankali, cikin rashin tsammani ta taɓo wani abu wanda ta kasa banbance meye...
BATOOL
Kwanci tashi asarar mai rai, gobe insha Allah Asabar ta kasance ranar É—aurin auran Batol da Alhji Auwal, tun kafin ranar Batol tayi kyau har ta gaji, anyi rabon invitation card da sauran su, iya walimah zasuyi yau, cikin ikon Allah akayi komai aka kammala,
Acan ɓangaren su Amani kuwa ansha party wanda shi kansa Abban nasu besan sunyi ba, tunda maza aka tara da mata aka dinga raye-raye, abinci ma basu wahalar da kansu ba ordersa akayi daga restaurants, a ranar aka sanya Mata lalle, bayan tayi na henna da ja,
Washe gari dubban al'umma suka sheda d'aurin auran Alhji Auwal da Batool, ɗaurin auran da ya samu halartar manyan mutane wanda sukazo daga ƙasashe da dama, haka ma ƴan uwan Ummy da baban Batool suma ba'a barsu a baya ba, sunyo gudun mawar kayan ƙamshi na girki da kayan yaji da su kaninfari da sauransu, hatta can ƙaramar ma'aikata anyi wadaƙa da abinci da drinks da sauran abubuwan da aka dinga rabawa,
Batool tasha faÉ—a agun dangi, musamman akan tayi biyayya ta kula da yaransa kar ta sake ta É—auki zugar mutane ta cutar dasu Allah na ganinta,
Hakan yasa ta dinga kuka, tunda taji mutane nata cewa nauyi ya hau ta ga na mijinta, ga na yara.
Sai yamma liss sannan motoci guda biyar sharoon suka zo ɗaukar amarya, mutane kam harda maƙota babu wanda bai je ganin gidan Batool ba, kodan azo a bada labari,
Alhmdulilah gida yayi kyau, ya tsaru, duk da dai anan É—in yaransa suke, É—akinta ne daban da parlonta amma duk a sashen suke kuma Babu inda zaka ce kafin kaje ka fita waje,
Kowa sai yi mata fatan alkairi yakeyi, komai yayi,
Ana kawosu zuwa magriba bayan anyi sallaha masu motoci suka aiko duk wanda zai koma gida yazo su tafi, sbda ba'a kwana, a gurguje aka sake jaddada mata nasiha tare da sake bata haƙu akan tayi zaman haƙuri tare da yi masa biyayya, kuma ta dinga jan yaran nasa a jiki.
Batool tayi kuka sosai, gashi ita kaÉ—ai a É—aki, hakan yasa tayi alwalah tazo tayi sallar magriba da isha'i, wanda batayi ba, ta zauna akan sallahya bayan ta kammala adu'ointa,
"Aslamu alaikum"
"Wa'alaikumussalam"
Batol ta amsa tare da jirin shigowar masu sallamar, Amani Alhji Auwal da Mahabob, sune suka shigo, hannun Mahabob riƙe da ledar kaji, ita kuma Amani hannunta riƙe da ledar Rufaida Yoghurt....
Kallo É—aya Batol tayi musu kafin ta, sunkuyar da kanta, cikin sanyin murya tace "sannunku da shigowa"
Amani tace "sannu Aunty Yaya Mahabob taso mu tafi"
Alhji Auwal yayi murmishi kafin yace "bye Allah ya tashemu lafiya"
Basu ƙarasa ɗakunan nasu ba, suka zube akan kujerun parlonsu, Mahabob akan 1 sitter Amani akan 3 ta miƙe ƙafa, sai ga su Inaya da Aseela sun fito suna cewa "kowa ya watse kenan?"
Inaya ta fara kuka tana shure-shure da ƙafafu, Amani ta tambaye ta "lafiya kuwa?"
"Nidai gurin dady zani"
Aseela ta ɗauke ta, tare da ficewa da ita zuwa sashen Batool, da ƙarfi tayi nocking a bakin ƙofar, kasancewar kukan Inaya ya ƙaru sosai,
Har sunyi sallar nunawa Allah godiya,
Ya kamo hannun Batol kenan yaji nocking, da sauri yace "waye?"
Aseela tace "Abba Inaya ce take kuka, tace gurinka zata zo"
Abba ya mayar da babbar riga ya miƙe ya buɗe ƙofar kafin ya ƙarɓi inaya, har ya juyo Aseela tace "aunty ina wuni"
Batool ta amsa da "lafiya lau ya karatu"
Kafin Aseela ta bawa Batool amsa, Abban yace "oya sai da safe"
Bayan ta tafi, ya rufe ƙofar, tare da dawowa gurin Batool, ya kalli Inaya dake zaune akan cinyarta kafin yace "Auta kin gaishe da Auntyn baki kuwa?"
Inaya ta kwaɓe fuska zatayi kuka,
Har ƙarfe 12:am na dare suna zaune, da zarar Inaya taji ance za'a kwanta sai ta fashe da kuka,
Batool kam sai gyangyaɗi takeyi, har Allah yasa Inaya tayi barci, Abba ya ɗorata akan gado, yazo ya ɗaga Batool itama ya kwantar, sosai yaci alwashin raya wannan dare tare da Batool amma hakan bai yiwu ba, dole ya haƙura, ya tashi ya yi alwalah, ya fara salloli tunda asbha dai tariga da tayi, sai dai a jira kiran sallah.
IFFAT
Washe gari, dady ya kira Æ´an jaridu da masu aiki a gidan TV da duk masu yaÉ—a sanarwa a kafafen sada zumunta, tare da hotunan Iffat,
Abin mamaki su Dadyn nata zuba ido suji an samu iyayen Iffat amma shiru.
Hankalin kowa ya tashi, musamman ma su Hajiya babba da Hajiya ƙarama,
Hakeem ya koma bakin aiki, a hakan ma sai da Dady yayi ta masa faÉ—a sannan, Iffat kuwa komai ta gani kallo ne, gashi bata cika magana ba, duk da suna yawan zuwa gidan Zoo ko zataga wani naman daji ko abun da zai sanya tayi magana, batayi sai dai kallo kawai.
Bayan sati Uku.
Hajiya babba da Hajiya ƙarama da Iffat suna zaune a parlo, hira sukeyi akan mugayen iyaye wanda suke jefar da ƴa'ƴansu a bola wasu tsinta suyi rainonsu, duk maganar akan Iffat ake yinta, suna tsaka da hira Hajiya Fawziya tayi sallama, cikin fara'a dukkansu suka amsa, bayan sun gaisa ta kalli Iffat kafin tace "a ina kuka samo wannan yarinyar?"
"Hajiya ƙarama tace "wlhi yarinyar sisterna ce"
Hajiya Fawziya ta taɓe baki, duk Hajiya ƙarama na kallonta, kamar meyin wani abu Hajiya ƙarama ta miƙe, a sukwane tabar gurin.
Parlon ya rage daga Hajiya babba sai Iffat da Fawziya,
"Ƴar tsintuwa ce, wlhi Hakeem ne ya bigeta shikenan ta samu juyewar ƙwaƙwalwa, kin ganta nan anyi cigiya har an gaji babu iyayenta"
Hajiya Fawziya ta zaro ido, cike da tsegumi tace "shine kike zaune da ita?"
Kinsan dai Hakeem befi shekaru 18yrs ba, bakya tunanin ya taso yace yana sonta?"
Hajiya babba tace "wlhi kuwa, nima dai na fara tunani amma ai wannan Eshat ɗin ƙarama ce"
"Mtsw aunty ina baki kina ƙin karɓa wlhi tallahi irinsu ne suke zamowa wanda ya riƙesu masifa, wata ƙil ma aljana ce baki sani ba, dubi idanuwanta, dubi gashinta har gadon baya"
Hajiya babba tace "Ƙanwata yi a hankali, dan wannan me baƙin halin ta jiki wlhi sai tayiwa Alhji famfo...
Ayi haƙuri babu yawa, insha Allah zan dinga yi da yawa, nidai burina aci gaba da comments,