x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 11 - MU RAYU A TARE book 1

  • 30001 words
  • 33000 words
  • Out of 62845 words

Category: Love Stories

Views 108

09 Aug 2025
Start ads
After Image Ads
ta amsa da "na'am"

Makirin murmishi yayi, kafin yace "kin amince da buƙata ta?"

Jikinta na karkarwa tace "nidai kayi haƙuri ka barni in koma garinmu dan Allah na yafe maka duk abinda kayimin"

"Never!!!"

Yana saurin ajiye coffe ɗin,

"Wlhi bazaki koma ƙasarku ba har sai kin amince da ƙudurina, nima inaso burina ya cika akan masarautar mu"

Sam ta gaza fahimtar abinda yake nufi, dole ta zube a gurin tana roƙonsa, ganin yaƙi saurararta yasata cewa "shugabata tanada zafin kishi zata iya kasheni idan ta ganmu tare"

"Sai me? ƙarya ne, ni bazan bari ta gano komai ba, sosai nake samun nutsuwa dake, tun kafin a bani umarnin kusantarki, dan haka ko kinaso ko bakyaso sai na dinga sex dake koda wane lokaci"

A firgice Hassana ta miƙe tare da juyawa zata fice, da sauri ya fincikota ta faɗo jikinsa, cikin sauri ta kauce tare da sunkuyar dakai, hawaye na ambaliya a fuskarta, sam ta gaza haɗa ido dashi, sbda iya idanuwansa faɗar mata da gaba yakeyi,

Yayi kisa a gaya mata zai sauya mata gida wanda yafi wannan, sai ga Lulu nan, ashe tanata sallama basuji ba, ganin Hassana a durƙushe gaban Ala-Uddin Samir yasata wurga jakar kan gado, tana gyara sumar kanta da ta rufe mata ido, tare da riƙe ƙugu tace "Hub lafiya?"

"Mu Lulu wai dole sai ta tafi gida, naga kina buƙatar zamanta yasa nace "babu inda zata shine taketa kuka"

"Kai Haseeaina, wannan karon bakizo da niyar yin aiki ba, wancan karon ai kinkai shekara ɗaya da rabi, meyafaru kikeson zuwa gida, idan kuɗi ne baki dashi ki bani number account zansa miki"

Har Lulu tayi maganganunta ta gama Hassana ta kasa magana,

Sai ma miƙewa da tayi ta fice da gudu, tayi kuka sosai da ta koma ɗakinta, sbda ta kasa ɗaukar coffe ɗinma ta sha.

Hajara na kammala abincin tasa a faranti mai faɗi fari na tangaras, tare da saka cokula biyu, sbda haka Shahazad ya umarceta  tun farkon zuwanta,
Tana haurawa steps gabanta na tsananta faɗuwa,
Batasan takamaiman ɗakin da suke ba, dole ta fara nocking na Mona, cikin sa'a, yace "Yes"

"Na kawo abinci ne"

Hajara ta faɗa tana jiran abinda zece mata,

"Okay"
Ta shigo bakinta ɗauke da sallama, karfa idanunsu ya sarƙe ana juna,

Hajara tai saurin sauke idanuwanta ƙasa, ashe Shahazad yana kallonsu,

Bata jira an bata umarni ba, ta fice.

Shahazad yayi wani irin makirin murmishi,

Jikin Hajara na karkarwa ta ƙarasa ɗakinta, itakam gida take buƙatar zuwa, amma bataga fuskar magana ba, "gashi sai ya dinga yi mata mugun kallo ko meye dalili oho?"

Mona na kwance, duk irin kallon da Shahazad yake yiwa Hajara tana kallonsa,  murya wata iri tace "shin Hajar tayi maka wani abunne?"

"Ehhh, tana shiga gonar da ba Tata ba"

Shahazad ya faɗa cikin kakkausar murya.

"Dan Allah ka sassauta mata, tabani labarin batada iyaye, shiyasa ta zaɓi tayi aiki anan"

Shahazad ya shafi gashin kanta, kafin yace "ki kwantar da hankalinki ki ci abinci zamuyi magana zuwa anjima"

Mona ta fashe da kuka tana shure-shure tace "nidai kayi min alƙawari zaka riƙeta cikin aminci?"

A gurinsa Alƙawari ba ƙaramin abu bane mai muhimmanci, idan yayi zaiyi wuya ya saɓa,

Sam yaƙi cewa komai,

Taci gaba da kuka tana ihu,

Tunowa da dokokin asibiti da suka sanya masa, ya sashi saurin kamota ya ɗorata jikinsa kana yace "nayi miki alƙawari inhar kema kikayi min alƙawari"

Batasan Alƙawarin meye yakeda buƙata ba, cikin sauri tace "nayi maka"

Yana shafa gashin jikinta tare da mammatsa mata hannaye yace "Yakamata kisan ni masoyinki ne, inada burin baki farinciki sama da Ni kaina Amma kin kasa fahimtata"

Sosai tayiwa Allah godiyar wannan tambayar da yayi mata, dan ta samu damar tuhumarta iyayenta.

"Ka kawomin iyayena in gansu, nayi maka alƙawarin zan zauna dakai"

Shahazad yai saurin ture ƙafafunta, kana yace "me kikeso ince miki?"

"Dama kinsan zaki jawomin tashin hankali, su suka bani auranki, mahaifinki ne ya damƙamin ke a matsayin mata, nikuma na karɓa"

Da sauri ta tare bakinta, a fili tace "ka kashesu"

A nitse kamar ba kuka takeyi ba, yace "suna raye"

"Yaushe zaka haɗani dasu"

"Ranar Litinin saura kwana uku tunda yau muna Asabar"

Sosai farinciki ya kamata, shiko a halin yanzu yana jin babu daɗi a zuciyarsa.

Da sauri ya miƙe ya koma wani ɗaki can nesa da nata ya ɗaga wayar tafi da gidanka, wanda ya kira yana ɗagawa yace "kasan iyayen Mona?"

"Eh na sansu sun jima da mutuwa"

"Eh nasan da haka, inaso a samomin mutane biyu wanda suke da murya irin tasu, ka gaya musu ko nawa sukeda buƙata zan biya"

Wanda ya kira yace "to angama me gida"

Mona kuwa tanata farincikin zatayi magana da iyayenta.

NIGERIA
Yau kwanan Huda ɗaya a gidan Abba, bayan sun kammala cin abincin safe ta tattara kwanuka takai kitchen ta wanke, tana zama Inaya ta taho da gudu tana cewa "anty Huda wai kizo ki yiwa momy wanke-wanke"

Amani ta taɓe baki, kana tace "zauna ki huta, ai ba ke aka kawowa ita ba"

Huda tace "ai ba hutu nazoyi ba aiki aka ɗaukeni"

Karaf a kunnen Mahabob, ya kamo hannunta ya zauna akan kujera ita ta zauna a ƙasa kan carpet kafin yace "ke ba ƴar aiki bace, dole a tausaya miki, shima Abban ba a ƴar aiki ya ɗaukoki ba, dan haka ki kwantar da hankalinki"

Sam ta kasa kwantar da hankalin kamar inda suka faɗa, dan gani take kamar zata iya fuskantar hukunci a gurin momyn nasu,

Yana fita Amani itama ta shige ciki, Huda ta fice da sauri.

Lokacin Abba ya fita,

Batool na ganinta tace "wato har kin fara samun gurin da zaki miƙe ƙafa a kirawoki kiyi burus kamar ba ke aka kirawo ba"

Cikin tausasa murya, Huda tace "kiyi haƙuri Hajiya, na tsaya wanke nasu anty Amani ne"

"Aikinsu yafi nawa kike nufi?"

Kan Huda a ƙasa sam ta kasa ɗagowa, saboda cikowa da hawaye da sukayi,

Kicin ta wuce, kasancewar Batool ɗin ta nuna mata tana ci gaba da masifa.

Cikin sauri ta wanke kwanukan tunda ba yawa ne dasu ba, ta fito tasa hijabi ta koma part ɗinsu Amani, Batool ta bita da mugun kallo,

Tana zuwa ta samu Aseela a zaune ta share hawaye, kana tace "ina anty Amani?"

Aseela ta ƙwalawa Amani kira,

Sai gata ta fito tana gyara dogon wandonta.

"Ehee fita kikayi, sannan naga kamar kuka ma kikayi keda waye?"

Sam huda bataso sanar musu da komai ba, amma ta kasa daurewa sai da ta gaya musu abinda Batool ta faɗa mata,

Aseela tace "Anty Amani kira Abba kice matarsa tayiwa Huda duka"....!

Kunsanni da barci da wuri😫 wato yau comments ɗin da nagani, wlhi naji daɗi sosai sbda kuna ƙaramin ƙarin guwaiwa sosai.

Mom Islam

*💋MU RAYU A TARE💋*

Mom Islam

47-48

Sa'arsu ɗaya wayar Abban yaƙi shiga, dole suka haƙura.

Bayan Tasneem da Ummi sun gama haɗa girki, tasa taliyar bayan ruwan ya tafasa, kana ta kalli agogo  1:pm, sukayi sallah sbda gudun katsewar labarin, lokacin da suka idar abincin ya dahu, babu maganar ci, aka juyeshi a kula, kana Ummi tace "Tasneem nikam ina jiran ci gaban labari"

Murmishi Tasneem tayi, kafin taci gaba..

"Duk da na koma gidan Hajiya, Haseem bai dena bibiyata ba"

Zuwansa biyu, Hajiya ta tareni tana tambayata meyasa nake kulashi tunda ba shi zan aura ba, sam na kasa gaya mata komai, sbda bata sanshi ba, bata ma san yanada dangantaka da Uncle ba, da ta matsamin nace, Hajiya sbda nace bana sonsa shine anty Karima ta fara tsangwamata shine Uncle ya dawo dani gidanki"

"Ana auran dole ne yanzu?, har guda nawa kike da zasu aurar dake, nifa har yanzu hankalina bai kwanta da auranan da za'ayi miki ba, shiɗin yaron waye?"

Hajiya ta tambayeni cikin fushi.

"Yaron ƙanwar anty Karima ne, ya daɗe a gurinta dan haka take kiranshi yaronta kuma ɗan uwanta, dalilin da Uncle yace in dena kulashi, yana shaye-shaye"

"Innalilahi wa inna ilaihir raji'un, wato ke kuma taƙi ƙaddarar kenan, shi wanda ya turo iyayensa me sunansa?"

Kaina a ƙasa nace "Zahradden"

"To Allah yasa idan anyi auran ya riƙeki tsakani da Allah"

Nidai bance komai ba, na tashi na tattara kwanukan da nazo na samu, wanda hajiyar bata wanke ba, tass na wankesu na kife, na dawo ɗaki,

Zuwa yamma, wayar Hajiya tayi ring, ina daga tsakar gida, naji Hajiya ta ƙwalamin kira, da sauri na shigo ɗakin na sameta ina cewa "Hajiya gani"

Ta miƙo min wayar, tana cemin "Uncle ɗinki ne ya kira"
Ƙara wayar nayi a kunne kana nace "Uncle ina yini"

"Lafiya Tasneem ki shirya Zahradden zai zo yau Please ki nutsu karkiyi masa shirme"

"To" nace cikin jin kunya.

Sai da akayi sallahar magriba nayi, sannan na shiga wanka, ina fitowa na goge jikina da towel, na ɗauki mai na shafa, dama kwalliya bawai ta dameni bane, sai dai powder da na shafa, kana na buɗe akwatin kayana na ciro doguwar riga ta material, sai da na fesheta da turare, sannan nasa, kana na kalli kaina a mudubi,  na ɗauki hijabi nayi sallahar isha'i kasancewar ana kiran sallahar, na zauna adu'a dama tunda nayi wanka nayi alwalar sallar isha'i.

Inajin ring ɗin wayar Hajiya gabana ya bada rass, sbda nikam ban taɓa hira da saurayi ba, wannan shine karon farko,

"Tasneem zoki karɓi waya"

Na fito da sauri,

"Yazo ki fito"

Bakina yayi nauyi, a zuciyata kuwa cewa nake "lallai ma ya raina Uncle shine ɗan aikensa"
Cikin sauri na dawo ɗaki na ɗauki hijab wanda ya tsaya min iya guwaiwa fari nasa, kana na fita jikina na kyarma sbda fargabar inda zan sameshi.

A hankali nake tafiya kamar wacce ƙwai ya fashewa, har na iso gurin da Hajiya tasa a ajiye fararen kujeru banga kowa ba, cikin sanyin murya naji ance "ji inda kike zaro ido kamar matsoraciya"

Da sauri na waiga idanuwanmu suka sarƙe dana juna,

Kunyarsa ta lulluɓeni, bansan lokacin dana durƙusa har ƙasa nace "ina wuni ba"

"Lafiya" ya amsa yana dariya,

"Wow na samu yarinya  har da durƙusamin"

Da sauri na ɗago, tare da sanya tafin hannuna na rufe fuskata,

Kafin ya sake wata magana nace "dan Allah kayi haƙuri zan koma gida cikina na ciwo"

Lura da yayi na riƙe cikin ina yamutsa fuska yasashi, cewa "tom sai gobe, ga wannan zamudinga waya"

Da sauri nace "a'a"
Harna fara tafiya, naji yace "sai na gayawa Uncle"

A zuciyata nace "yasan sunan da nake gayawa Uncle ɗin kenan?"

Dole na karbi wayar, yacemin "harda sim card a ciki" nayi masa godiya na wuce.

Ina shiga na miƙawa Hajiya wayar, na wuce toilet na dinga kashi, ƙarshe gudawa ne ya biyo baya, duk na tsure saboda tsoro, banyi zaton haka hirar take ba,

Ina fitowa, na zube a gaban Hajiya.

Kafin nayi magana, tacemin "masha Allah wayar tayi kyau"

Wlhi na ɗauka zata yimin faɗa ne,

Hajiya tayi-tayi dani inci abinci na kasa, na shige ɗakin da nake da wayar, na buɗe kwalin, infinix ce hot 10, ina kunnata kira na shigowa,

Ikon Allah har yayi saving sunansa wai My life,

Haka rayuwa ta dinga tafiya, koda yaushe muna waya, amma bana son inji yace zezo, shima da ya gane nafi sakewa a waya bai cika zuwa ba,

Kwanci tashi asarar mai rai har bikinmu ya rage saura kwana biyar, zuwansa huɗu, duka bana wani sakewa dashi, an sanarwa dangi na kusa dana nesa, tunda bikin ya rage kwana uku, mutane suka fara zuwa,  irin gyaranan na fata da ake yiwa amare nikam babu wanda yayi min, ko meye dalili oho, amma fa naga gata sosai, ta fannin dangin mahaifina da mahaifiyata kuɗi da kaya har sai da aka nemi wani ɗakin,
Uncle yayi ƙoƙari shima, ta fannin furnitures daga ƙasar waje aka kawosu,
Ana biki saura kwana biyu, yayan Abbana yasa aka yankamin zabi manya aka soyesu akayi min miya, ranar da aka samin lalle nayi kuka sosai, sbda tunowa da mahaifiyata da nayi, duk da an nunamin gata amma wlh nayi kukan rashinta, ana gobe biki, Uncle ya kawomin ɗinkuna kala goma sha biyar, duk ciki babu na ƙaramin kuɗi, dama Ni ba ƙawaye ne dani ba, haka akayi taro ina ɗaki, anyita soya cincin da nakiya da dubulan, ranar da aka ɗaura aure, sabuwar gudawa ta dawo min, gani nakeyi  kamar a mafarki, ban gama tabbatarwa gaske bane sai da naji ance wai motocin tafiya da amarya sunzo"

Lokacin anata yimin nasiha inata kuka, Hajiya ta riƙe hannuna muka shiga mota nida ita,

Motarmu ce ta fara tafiya kafin ta sauran iyaye ta biyo baya.

Gaskiya dangane da kyan gidan babu abinda zance, sbda ko gidan Abbana da ake labarin haɗuwarsa bekai na Zahradden ba, an narka nera, anan muka wuni da mutane, tunda gidan ya cika naji daɗi gani nake kamar baza'a watse ba, kasancewar lokacin ƙarfe 3:pm ne, sai da suka jira akayi la'asar sannan kowa ya fara haramar tafiya ciki harda Hajiya, har Hajiya tayimin sallama tayi gaba, ta dawo da baya tana cewa "kiyi haƙuri Tasneem antynki Karima batazo ba, bansan meye nufin ta ba"

Duk da nasan ni take kwantarwa da hankali, nima nace "Hajiya yanzu haka tanayin nata taron ne acan"

Sannan naga fuskar hajiyan taɗan sake, da kuka muka rabu, ashe haka aure yake.

Zuwa dare, lokacin inata rama salolin da ake bina Zahradden ya shigo, na gaishe shi, kasancewar nayi sallama kuma na shafa adu'ar, amsa wa yayi cike da fara'a kafin ya kamo hannuna muka dawo parlo ya buɗe ledar dake ɗauke da gasassun kaji har uku da fresh milk kana ya cemin "bismillah"

Shi ya dinga bani, duk da banci da yawa ba, nace barci nakeji,

Sam yaƙi yarda, sai da yasa nayo alwalah dukkanmu mukayi sallah raka'a biyu, yayimin adu'a bayan ya dafa kaina, kana yazo fannin karɓar hakkinsa,
Duk da nayi kuka sosai, amma ban wani yi masa gardama ba, sbda gargaɗin da Hajiya ta dingayi min.
Tunda nayi wanka na dawo na kwanta, da asbha ya fice, aiki bayan ya dawo daga masallaci, lokacin da gari yayi haske wlhi na rasa nutsuwata, sam na kasa ban-bance halin da nake ciki, wani azababben ciwon kai ya ziyarceni,

Nidai kawai naga Zahradden ya dawo, na cukumeshi ina cewa ka sakeni...!

Please and Please nasan yayi kaɗan kuyi manage dan Allah idan na samu time zuwa dare zanyi muku wani.

Mom Islam

https://arewabooks.com/chapter?id=648b370d0b7269564606cc70


*💋MU RAYU A TARE💋*

Mom Islam

49-50

Sam nakasa gane abinda yasa nakeyi masa rashin mutunci, washe gari, ya riko hannuna ya dawo dani gidan Hajiya, lokacin da muka shiga ɗakin Hajiya naji tana cewa "dama Uncle ɗinta yace yau zaku zo, da naji shiru wlhi har na fara tunanin ko ta gudu ne?"

Zahradden ya fashe da matsanancin kuka ina kallonsa, Hajiya ta fara rarrashinsa tana ce masa "magani za ayi min idan na warke zan dawo ɗakina"

Cikin kukan yake cewa "dan Allah karku rabani da matata wlhi ina sonta"

Duk wani kalami da zai kwantar masa da hankali tayi amma ya kasa fahimtarta, dole Hajiya ta kirawo Uncle shima yazo ya dinga yiwa Zahradden nasiha, nidai naga Zahradden ɗin yayi waje, idanunsa shaɓe-shaɓe da hawaye, tun daga ranar naji soyayyarsa ta ficemin arai, idan yazo guduwa nake, idan naji muryarsa toshe kunne nakeyi.

Na koma shiru-shiru bana fita ko'ina, hatta aiki Hajiya ta Dena bani, sbda na koma marar kunya tashi d'aya, Allah sarki duk da ciwon daya riskeni da rashin kunyar  da nakeyi musu da rashin magana, basu taɓa tsangwamata ko zagi ba, koda yaushe mutum biyu suna hanyar nema min magani,

Ashe dukkansu biyu Uncle da Hajiya sun san inada ciki, kwanci tashi ina wannan hali cikina yakai wata bakwai, ciwo yanata gaba, lokacin cikina ya fito, Hajiya zata riƙemin hannu muje asibiti awo ko scanning, lokacin da cikina yakai wata tara da kwana tara, wlhi bansan inda kaina yake ba, washe gari nadai ganni a kwance riƙe da yarinya Hajiya ta sanya mata nono a baki, ina yawan ji ana cewa bada nono ga jariri akwai zafi, nikam banji ba, wlhi bansan ciwon komai ba, ranar suna yarinyar aka sanya mata Iffat.

Ranar da Hajiya tace "idan mukayi arba'in, zamu koma gidan magani"

Aiko ana i gobe zamu koma, naji kamar ana kiran sunana a waje, riƙe da Iffat na tashi, tun daga ranar bansan inda nake ba, sai yau..

Ummi ta dafa kafaɗar Tasneem kana tace "ki kwantar da hankalinki, idan zaki gane gida insha Allah zamu kaiki gidanku"

Tasneem tace "nan wane gari ne?"

Ummi tace "nan Kaduna ne"

Tasneem ta zaro ido cike da mamaki amma ba tace komai ba.

A ranar da yamma 4:pm Aliyu yazo gidan Ummi, sai da yabi kowane ɗaki ya gaishe su kafin ya dawo ɗakin Ummi, cike da murna Ummi tace "oyoyo ɗan albarka ga baƙuwarka ta warke"

Aliyu yace "masha Allah godiya ta tabbata ga Allah tunda har akayi nasara, baiwar Allah sannu"

Tasneem tace "Nagode Allah ya saka da alkairi Ummi ki tayani yi masa godiya"

Kasancewar Ummi ta sanar mata da taimakon da Aliyun yayi mata.

"Ummi malam yayi nisa ne?"

"A'a yaje gaishe da abokinsa Hudu ne a can katsina road, na mance ban tambayeka Hadiya ba?"

"Ummi tace in gaishi ki, gobe insha Allah tana nan zuwa"

Cike da jin daɗi Ummin tace "Allah ya kaimu".

Bayan an dawo da Hakeem gida, yana shigowa ya fashe da kuka, Hajiya babba ta dangware masa kai, tare da cewa "wlhi Hakeem dama inaso inyi maka magana tare da gargaɗi na ƙarshe, muddin kace bazaka fita a harkar waccar matacciyar yarinyar ba, wlhi sai nayi maganinka, har yaushe kayi girman dazan gaya maka kaƙi jin maganata, ko kana so kai da mahaifinka ku kasheni ne?"

Cikin tausayawa Hajiya yace "Hajiya wlhi bazan sake ba, amma Eshat tana bani tausayi sosai"

"Kai dalla can, wlhi idan da kasan asalin yarinyar nan, ko ance ka bibiyiyeta wlhi bazaka kulata ba"

"Hajiya kinada labarin iyayenta ne?"

"Eh mana tsintacciya ce a bola, anyi cikin shege ne aka yarda ita, shiyasa ka tsintota babu wanda yace ƴarsa ce, inaso ka cireta a cikin rayuwarka ka mance da ita, mahaifinka yana son haɗa matsayinku a guri ɗaya"

Cikin sauri Hakeem yace "Hajiya kenan ƙazama ce na dena kulata wlhi"

Tsabar murna da hajiyar ke ciki, ta janyosa ta rungume tana sanya masa albarka.

ALGERIA
Abin farinciki abin jin daɗi Iffat a zaune a ƙafar Hajiya ƙarama, Dady ya shigo, fuskarsa ɗauke da fara'a, naji yace "Hajiya gobe ne za'ayi sallamar nan, ya kamata in samu in cika musu kuɗinsu, Alhmdulilah"

Cike da jin daɗi Hajiya ƙarama tace "wlhi na ɗauka zamuyi wata a asibitin nan sai naga kwananmu biyar, har an kammala komai, ragowar magungunan Islamic ɗin duk ta shanye"

Dady yace "Eshat zo"

Ta sauko daga jikin Hajiya ƙarama ta je gurin dady tana murmishi,

Washe gari ya cika kuɗin asibitin aka sallamesu suka dawo gida.

Kwanan Iffat shida da fitowa, suka tafi shopping, Iffat tayi kyau sosai, sbda duk kayan da Dady ya gani siyo Mata yakeyi komai tsadarsa,
End Ads