ya kammala saka ƙananun kayansa, ya kalleta lokacin ta rufe jikinta da bargo a durƙushe yace "Haseeaina zanyi miki komai na rayuwa zan mayar dake ƴar gata zan fifitaki akan Lulu zan canza miki duniya ba wannan ba, inhar kin amince dani zan yi miki duka waɗannan abubuwan"
Hassana ta kalli Ala-Uddin Samir cikin kallon bakada hankali tare da fassarori daban-daban ta kawar da kanta, 4:50pm na cika Ala-Uddin Samir ya miƙe jiki na rawa har zai fice sai kuma ya dawo yace "idan kinyi shawara any time ƙofa a buɗe take"
Kana ya fice da sauri, miƙewa tayi ta faɗa toilet cikin dauriy, tayi wankan tsarki kafin tayo alwalahar la'asar, tana fitowa ta shimfiɗa sallahya ta kabbara Sallah, tana idarwa ta ɗaga hannu sama, tana kuka tana gayawa Allah halin da take ciki.
Sallamar Lulu ne ya sanyata miƙewa da sauri ta fice, ko ninke sallahyar batayi ba, ta fito parlo.
"Barka da dawowa shugabata"
Cike da izza, Lulu tace "yauwa Barka, bani labari yau Ala-Uddin yayi waya da ƴan mata ne?"
"A'a shugabata, nadaiji yana waya akan kasuwancinsa"
Juyar da ido tayi farrr tare da juya mazaunai ta isa ɗakin Ala-Uddin,
Ko jakar makarantar bata ajiye ba ta wuce ɗakinsa, yana zaune hannunsa riƙe da biro da takarda, wani irin zane yakeyi wanda ba kowane zai gane abinda yake zanawa ba, sbda sarƙaƙiyar rubutun.
Tana tsantsar sonsa, hakan yasa idan suna tare take mancewa da komai, ta rungumoshi ta baya, tana cewa "nayi missing ɗinka Hubb"
Ala-Uddin ya zagayo da ita kan cinyarsa tare da cewa "yau kinsha wahala a makaranta meyasa bazaki haƙura da karatunan ba?"
Cikin siririyar murya tace "Hubb inaso in zamo cikakkiyar ƴar jarida domin mu yaƙi masu aikata yawaitar fyaɗe da kidnap da sauran ɓarayi"
Ala-Uddin ya lumshe ido yana shafa gashin kanta, kafin yace "yanada kyau pretty sai dai Ina son rayuwarki kinsan wannan aikin salwantar da rai ne"
Lulu tayi murmishi, kana tace "ai inada kai shiyasa bana damuwa jarumina".
NIGERIA
Ƙarfe 11:am aka sallami Huda daga asibiti, idan ka kalli fuskar Mahabob ya rame sosai, hannunsa riƙe dana Huda suka shiga office, hannunshi na hagu riƙe da takardar sallama, a rubuce likitan ya rubuta musu dokokin magungunan da allurai da zasuci gaba da karɓa na kwana uku, daga nan Mahabob ya biya ragowar kuɗin kana suka fito harabar asibitin,
Kai tsaye gurin motarsa suka nufa, ya buɗe mata gaba shima ya shiga mazaunin direba, kafin ya tayar da motar suka fara tafiya.
Har sunyi nisa a titi sai kuma yace "wace anguwa?"
"Anguwar rimi"
Suna shigowa anguwar, Umman Huda tana tahowa kanta ɗauke da buhu, cikin murna Huda tace "ga Ummana.."
Da kallon tausayi ya bi Umman nata kafin yai parking a ƙofar gidan nasu, dan Umman nata har ta shige ciki.
Sai da ya fara fitowa sannan ya buɗewa Huda itama ta fito, suka shiga ciki, tana gyara mazaunin hijabinta da ya yage,
Da sallama ta shiga gidan, Umma ta fito daga ɗaki, tana salati, tare da cewa "au Huda ni na ɗauka kin fara yawon bariki ne?"
Sai kuma ragowar zancen ya maƙale mata a saman laɓɓa sbda ganin kujewar da tayi a fuskarta,
"Huda tukunna daga ina kika fito?"
"Umma wani yana yi miki magana a waje wai zai shigo"
Huda ta katse zancen.
"Ce masa ya shigo Allah yasa samuwa mukayi"
Tana fita ta sameshi a jikin mota a jingine, yana latsa waya,
"Ɗan gaye ance ka shigo"
Sai da Mahabob yayi murmishi kafin ya sanya keys a aljihu da wayarsa, kana ya shigo gidan.
Da sallama ya ƙarasa tare da tsayawa cak,
Can kwanuka nan tukwane ga tarin kayan wanke wanke marasa wanki a gefe,
Daga bakin kofar ɗakin Umma, Huda tace "wai ka shigo"
Bakinsa ɗauke da sallama ya shiga ɗakin tare da durƙusawa ya gaishe da Umman, jiki na rawa fara'a sosai ta amsa tana yi masa godiyar kulawar da yabawa Huda, murmishi kawai yayi, kana yace ta godewa Allah, bai wani jima ba ya ciro kuɗi, ya ƙirga dubu goma, dama tunda ya ciro kuɗin Umma ke zaro ido, huda kuwa haushi ya gama kamata,
"Umma ga shi a siya mata lemu"
"Ah to harda ɗawainiya ne? to mun gode Allah yaji ƙan mahaifa"
Kafin ya miƙe yana yi musu sallama, Umman kuwa sai cewa take "tashi ki bishi"
Huda tabi bayansa, har gurin mota, har ya buɗe murfin motar ya juyo ya kalleta, kafin yace "Huda ni zan wuce sai na sake zuwa dubaki"
Godiya tayi masa kana ya shiga motar ita kuma ta dawo gida.
Tun fitar Huda umma take aiyyana "inhar wannan baƙon yace yana son yarinyar nan wlhi bazan amince da auran ba, domin guduwa zatayi ta barni".
Tunda gari ya waye Hakeem yake rungume da Iffat, ita kuma sai shan yoghurt, takeyi hankalinta kwance, already Hajiya ƙarama ta riga da ta gama shiryata, dan har dady ya fito,
Lokacin ma hajiyar ta fito, hannunta riƙe da babbar jaka ta matafiya,
Hannun Iffat ta kamo kafin tace "Hakeem zaka bimu airport ne sai ku dawo tare da driver?"
Dady ya tsayar da ita tare da cewa "nayi miki transfer na kuɗin cefane ki duba ko sun shigo?"
"Oho kai ka sani kai ka damu dasu, mtsw"
Dady yayi murmishi tare da cewa "Hakeem jeka duba wayar Hajiya ko kuɗin sun shiga"
"To Dady"
Yana zuwa ya ɗauki wayar, kasancewar tana parlon Hajiyar ita kuma hajiyar ta shige bedroom, tun daga nesa wayar tayi haske, sai da ya cire key sannan ya duba gurin ganin alert sannan ya dawo da gudu yana cewa "Dady 100k"
Sannan dadyn yace "eh alhamdulilah tunda sun shiga, zomuje filin jirgi sai ku dawo tare da driver"
Acan bedroom hankalin Hajiya babba ya tashi, tunani ta fara "Anya ba bin bokaye Hajiya ƙarama takeyi ba, shiyasa Alhji yake sata a gaban goshi, komai yace ita, komai ita"
Da wannan tunanin ta miƙe ta fito parlo taga wayam babu Hakeem babu alamarsa,
"Zai dawo ya sameni"
Abinda ta faɗa kenan tana ci gaba da ruwan masifa.
Hankalin Alhji Auwal ya mugun tashi, sakamakon rashin jin ɗuriyar Mahabob da yayi, duk inda yake sa ran zai ganshi, sai ace masa bezo ba, kwatsam anyi sallahar azhar bayan ya dawo daga masallaci yaji shewa da ihu a part ɗinsu Amani, yana rungume da Batool da har yanzu basu samu damar ganawa da junansu ba, ya miƙe tare da zuwa part ɗin, yana shiga yaga Mahabob a tsaye yana yi musu dariya,
Aseela tace "wlhi na ɗauka ka ɓata ne, dama wannan shirin da nayi, nayine saboda mu tafi gidan rediyo a bada cigiyarka"
Mahabob na dariya yace "haba sai kace ke, an gaya miki ni yaro ne?"
Duk da Abban na tsaye yana jinsu, basu ganshi ba, yayi sallama, suka amsa cikin ɗokin ganin Mahabob, Abba ya zauna akan kujera tare da cewa, "yanzu Mahabob kana ganin kayi dai-dai kenan?Ai duk inda ka shiga yakamata ka buɗe wayarka tunda kira ya gagareka"
Mahabob ya risina har ƙasa kafin yace "Abba dan Allah kayi haƙuri hatsari nayi na bige wata yarinya shine aka kwantar da ita, nikuma ina gudun ɗaga muku hankali shiyasa ban sanar ba"
"To ai ba wayo bane, hankali kam ya tashi, amma ya jikin ita yarinyar?"
"Taji sauƙi Abba, sai dai ina son a taimaka musu dan wlhi talauci yayi musu yawa suna buƙatar temako"
"Mahabob duk wani taimako da kake ganin ya dace kayi musu, babu damuwa"
Mahabob ya sake yiwa Abba godiya,
Sai ga Batool nan ta shigo, tana sanye da hijabi har ƙasa, tun daga nesa Amani take watsa mata mugun kallo amma Batool ɗin bata lura ba, bayan tayi sallama ta nemi guri ta zauna, dukkansu suka gaishe ta, ta amsa cikin dakin fuska kafin ta tambayi Mahabob lafiya kuwa?"
Abinda ya faru dashi ya sanar mata, kana yace "yana son dukkansu suke su gaishe da yarinyar da ya bige"
Kafin Batool tace wani abu Amani tace "ai kuwa Abba ya kamata aje a dubota"
Abban yace "insha Allah nima zani da izinin Ubangiji, sai ku shirya zuwa gobe ko?"
Mahabob yaji daɗi sosai, yayiwa Abba godiya.
Batool ta miƙe jiki babu ƙwari, sbda inhar tana guri da kuma ƴaƴansa a guri to sai dai tayi haƙuri dan a lokacin kamar ma mancewa yakeyi da ita, kuma kafin ta faɗi magana su sun riga da sun faɗa.
Tana zuwa part ɗin ta, ta fashe da kukan nadama, tare da dana sani, itakam batasan meye ɗaɗin aure ba, komeye bashi da lokacin ta, gashi yaran gabaki ɗayansu sun dena girki, Allah yasa Inaya ana sanya mata pampas da haka zata jiƙe mata katifa, bata isa tayi magana ba,
Bayan fitar Abban, Amani ta matso kusa da Mahabob kana tace "bro wlhi wannan matar Abban ƴar raunine hankali ce, wai brakfast idan ta gama, sai dai idan mune mukaje ɗauka ko Abba ya kiramu a waya wlhi bazata kiramu ba"
Mahabob yace "kash Amani, meyasa baki da haƙuri ne?, idan tanada hali mai kyau zamu gani idan babu wlhi zamu gani"
Yana gama magana tace "uhm ana gaya maka magana baka ganewa" Aseela tace "kunna mishi videon nan"
Amani ta kunna ta miƙa masa, Mahabob yayi dariya, yayi dariya kana yace "amma ku Allah yayi munafukan yara da, bazaku bar Abbba ya huta ba, to meye amfanin yin auran idan bai kula da ita ba?"
"Taɓɓ wlhi mallake mana Abba tayi, tun kafin ta shigo gidan, badan haka ba ai da bazasu dinga wannan iskancin ba"
Amani da Aseela suka faɗa cikin haɗa baki.
"Kunga wannan shine soyayyar aure, idan kukayi kuma mazanku zasuyi muku kudena sawa Abba ido, amma kafin ku karɓomin abinci"
Amani ta fice tana cika tana batsewa ta nufi part ɗinsu Batool
Kafin tayi magana, taga Abba na rungume da ita a ƙirjinsa, ko kukan me take oho, itadai Amani taga yana share mata hawaye,
Cikin sauri tace "Aslamu alaikum"
Abba yai saurin sake Batool tare da cewa "Amani ƙalau?"
"Bro Mahabob ne yace "in kawo masa abinci"
"Batool har yanzu baki gama abincin bane?"
Alhji ya kusa, "kasan shinkafa ba kamar indomie ba"
"Please dafa masa indomie ɗin tunda shikam baya wasa da cikinsa"
Babu musu ta wuce kitchen ta ɗora indomie a gas dama tanada ruwan zafi, Amani kuwa ƙin tafiya tayi sbda batasan Abba yaci gaba da iskanci...!
Ayi haƙuri kwana biyu kunjini shiru
Insha Allah zamu ci gaba
Masu comments Nagode Allah yabar ƙauna
*💋MU RAYU A TARE💋*
Mom Islam
35-36
Har Abba ya koma ɗaki ya fito ya samu har yanzu Amani na zaune,
"Zan fita sai na dawo"
Abba yace tare da kallon Batool.
Allah ya kiyaye hanya tayi masa, dan tarasa abinda zata sake cewa bayan haka, Amani na kallon yanayin fuskarta lokaci-lokaci,
Kitchen ɗin ta koma, ta duba indomien ta tsotse, ta zubo a faranti mai kyau, kana ta miƙawa Amani,
Amani ta karɓa ta fice.
Batool ta koma kitchen sauke abinci, ta ɗora miyar da dama tariga da ta gama tun ɗazu ɗumamawa zatayi, Inaya ta shigo idanunta sunyi rau-rau zatayi kuka,
Batool tace "yarinyata keda waye?"
"Aunty Amani ce ta hanani abinci"
"Sorry na gama zo in zuba miki kici"
Inaya na murna ta zauna, a parlon kan kujera tare da ƙurawa TV ido,
Abincinta ta zuba, kana ta zuba nasu Amani a ƙatuwar kula da nama mai yawa, da miya daban sai cabeji da latas da cocumba a wata ƴar roba, kafin ta fita kai musu,
Tana shiga da sallama, bayan sun amsa ta ƙarasa ta ajiye musu abincin, sannu sukayi mata kafin ta fice duk suka yo kan abincin harda Mahabob, itako tayo waje.
Tana shigowa ta samu Inaya har tayi barci, dama tanason indan ta dawo ta kawo musu suci tare, ta zauna gefen Inaya cikin rashin jin daɗin barcin nata,
Tasa abincin iya inda zata iya cinyewa, bayan ta kammala cin abincin ta sake shiga wanka, ta shirya cikin atamfa blue anyi mata adon zanen ganye da yellow sai ratsin ɓaki, sosai atamfar tayi mata kyau, tabi ko wane lungu na jikinta da turare, kana shimfiɗa sallahya sbda tayo alwalah, jiran kiran sallah take, ta fito parlo.
Zuwa yamma liss gaf magriba Abba ya dawo, da gudu taje tayi masa oyoyo tare da rungume shi, lokacin Inaya ta farka, amma sai ta runtse idonta dan ace barci takeyi,
Sai wani shafata Abban keyi kamar mage, yana kissing ɗin ta duk a idon inaya,
"Dama ba nisa kayi ba?"
"Eh wlhi naje ganin motar Mahabob ne da na sauya masa"
"Masha Allah Ubangiji ya ƙara buɗi"
"Amin ya rabbi, saura naki dana Amani"
Batool ta zaro tana ci gaba dayi masa godiya.
SHAHAZAD FOREST.
Yau sun tashi da ni'imar ruwan sama, yawancin matan murna sukeyi, sosai kowacce tana ƙoƙarin gyaran gonakinta, hankali kwance.
Tunda mutanen Shahazad suka kwana biyu basu shigo yankin ba, wata mata wacce ta kasance itace shugabarsu ta fito hannunta riƙe da wani yaro wanda a ƙalla zeyi shekaru 10yrs a duniya, yaron fari ne tass ga dogon hanci, kowacce mace ta rufawa shugabarsu asiri, sbda suna sa ran samun ƴanci nan gaba, kuma suna saka ran yaron zai zame musu haske a rayuwarsu, shine zai yaƙi Shahazad.
A cikinsu akwai mata wanda suka kasance mace da namiji kuma duk mata ne, wato Raniya da Salha, sunyi aure ne a bisa yarjewar shugabarsu, sbda su basusan abinda ya dace da wanda ma bai dace ba, Raniya itace matar, Salha kuma miji, inda mata da miji sukeyi haka suke rayuwa, tabbas koda shugabarsu bata yarda da wannan aure ba, sai sunyi tunda kaf ƙauyen su biyunan ƙwari ne kuma hatsabiban kansu,
Zuwan bazata zuwan rashin tsammani, wani irin jiniya sukaji, yau ko sanarwar ma babu bare labari, kai tsaye cikin ƙauyen suka shigo, yau babu sauƙi hatta matan da sukayi gardama kashesu akeyi, Raniya ta fito domin tace Sahla ta gudu, wani daga cikin mota ya harbe ta da mota, jin harbin bindigar yasa Sahla guduwa dan tasan idan ta tsaya sai buzunta, tunda shugabarsu taga anata ɓarna ta kamo hannun Shukri suka ɓuya cikin ramin da mutanen basusan dashi ba, sai da sukaga sun rage yawan mutanen yankin kafin suka ɗaukesu a photo suka wuce.
Jin tsit yasa ragowar mutanen fitowa wanda suka koma tsiraru, kai tsaye Sahla na zuwa ta wuce gurin Raniya tana kuka,
Kuka takeyi wanda yake da ban tausayi, tabbas duk rashin imaninka dole zaka tausayawa Sahla, a fili tace "Raniya na rasaki har abada, ina amanar da mukayiwa junanmu ina sittin da muke yi tsakaninmu ina gwagwarmayar da muka sha kafin mu mallaki junanmu?"
Wanda suka tattara ƴan uwansu suka dawo gareta suna bata haƙuri akan tayi haƙuri ta kauce a gurin, amma ina kamar ana sake tunzurata,
Tana cikin kukan Shukri ya fito ba tare da sanin shugabarsu ba, cikin ɗaga murya yace "Sahla karki bari jinin Raniya ya tafi a banza ki shiga cikin garin Libya ki yaƙi shugaba Shahazad har sai inda ƙarfinki ya ƙare, zan taimaka miki idan shugabata ta yarda"
Cikin kuka Sahla tace "an kashe min uwata an kashemin Ubana, tunda muka taso ake kashe mutane a gabanmu, babu wanda ya taɓa yunƙurin farmakarsu ko hanasu, an mayar mana da rai tamkar na dabbobi basu ɗaukemu da amfani ba, nayi alƙawarin kawowa ƙauyenmu cigaba sannan nayi alƙawarin inhar nabar garinan bazan dawo ba, sai anyi abu biyu, ko ɗaya ya faru ko dukkansu,
Ragowar matan suka taho gurin ta kowa ya bata goyon baya tare da ƙara mata ƙwarin guwaiwa.
"Nima na goyi bayan ki sannan zan taimaka miki"
Shugabarsu ta faɗa tana yiwa Sahla murmishi.
Dole aka nemo ƙwararrun likitoci, tunda yace bai yarda da waɗancan ba, kwana uku da suka wuce babu wanda zai ce Mona zata gyaru, yanzu gashi har zama tana iya yi, bata wani cin abinci sai coffe shi kaɗai ne take iya jurar shansa,
Burinta bai wuce Allah ya bata lafiya ta hukunta Shahazad ba, bayan haka ko a ranar ta mutu tayi arziƙi,
Acan fannin Hajara, kowane motsi na lokaci baya wuce ta, sbda hankalinta gabaki ɗaya yana kan agogo, tausayin Mona takeji har cikin zuciyarta, tanaso ta ƙara shiga cikin cikin ragowar ɗakunan tana tunanin Shahazad anya bashi da wani abu wanda ake hango motsin mutum, itakam ta fara tsoro ko har numfashinta ya fara ƙirgawa ne,
Gidan ya rage ita ɗaya, sai dai daga can gurin get akwai mutane sun kai 10 kowa da aikinsa harda jami'an tsaronsa,
Parlo ta dawo ta kunna tv, domin ɗebe kewa, ina bazata iya kallon ba, ta kashe, a hankali tunanin su Inna da Goggo ya fara mata yawo a kanta, tana son kiransu tana tsoron gidan, sbda tana tunanin duk abinda ta faɗa akwai abinda yake baɗewa Shahazad na dawowa zai gaya masa, dole ta fasa kiran, amma zuciyarta nayi mata saƙa iri-iri.
Cigaba yayi da zanen yayinda Lulu take shafa masa kwantaccen gashin da yayi luff a gemunsa, "Lulu Please kiɗan matsa inaso in gyara zaman masarautar nan"
Da sauri Lulu ta zaro ido, cike da fargaba tace "haba Hubb kana nufin har yanzu baka haƙura da maganar masarautar ba? karka manta sarki ya mutu, karka manta Shakura tace ko bayan ranta bazaka..."
"Stop..!!! Haba muku a maimakon ki kwantar min da hankali kunason famomin dafin dake sakaye a cikin zuciyata?" idan kin shirya gwagwarmaya dani zamu iya rayuwa tare, kamar inda kema kikeda burin aikin Jarida kikeson cika burinki ban hanki ba, dan haka karki sake ki dakatar dani akan ƙudurina, koshi Raza bai isa ya kaucewa makirci da sharri a ba, nasha yin mafarki akan nahau kujerar sarki Mazin, dan haka kiyi shawara da zuciyarki"
Tsit Lulu tayi kamar ruwa ya cinyeta, kafin ta sake matsowa kusa dashi ta ɗora hannunta a nasa, murya a marai-raice tace "na shirya zama dakai" kana ta ɗora hannunta a nasa,
Ajiyar zuciya ya sauke tare da rungume ta ya lumshe ido. har ransa yanajin sonta amma sam ƙaunarta baya cikin zuciyarsa to meyesa?
Lokacin da aka kira sallahar magriba gari ya fara duhu, amma anan gidan nasu haske kamar rana, lokacin ta gama musu irin abincin su, ta shiga ɗaki zatayi sallah sbda tayi alwalah,
"Haseeaina.."
Cikin ɗaga murya ta amsa da "na'am"
"Kawo mana abinci ɗakin Hubb"
Cikin Umarnin Lulu ta ɗibo abincin ta jere a babban trai mai kwalliya, tana tafe ƙirjinta na dukan uku-uku, har ta ƙarasa ɗakin da sallama, babu wanda ya amsa mata, a zuciyarta kuwa cewa take sai kace arna?"
Lulu na manne da Ala-Uddin Samir, Hassana ta ajiye, Lulu ta kalli Ala-Uddin Samir kafin ta kalli Hassana sai kuma tace "lafiya kuwa Hubb?"