x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 15 - MU RAYU A TARE book 1

  • 42001 words
  • 45000 words
  • Out of 62845 words

Category: Love Stories

Views 107

09 Aug 2025
Start ads
After Image Ads
ciki, cikin Sa'a yaci karo da Kharan yana shan coffee, hankali kwance ya toshe masa baki ya fita dashi ta baya, shima aka sanya shi a mota suka wuce dasu.

Hannunsa riƙe da Basmati ya shigo tare da cewa "wacece a cikinku takeson Basmati?"

Mona tace "nice" tare dayi masa godiya,

Hajara tace "kanata ɗawainiya damu mungode" Kharan Khan yayi murmishi kafin yace "ai yiwa kaine, taimakawa mutane ya zamomin abokin rayuwa....

Kuyi hakuri wayata babu chaji, dan karkuyita zuba ido ne yasa nayi muku kaɗan anjima zamu ɗora

Mom Islam

*💋MU RAYU A TARE💋*

Mom Islam

                     Book1
67-68 

Inda Mona take cin Basmati ɗin sai yayi matuƙar burgeshi har wani murmishi yayi, kafin ya miƙe tsaye yace "amma ke ƴar Nigeria ce ko?"

Ya kalli Hajara.

"Eh amma ina fatan komawa nan bada jimawa ba"

Murmishi ya sake yi a karo na biyu kafin yace "Mona matar shahazad Junaid Khan, ki ayyana a ranki kin tsere masa, abinda nakeso dake shine, ki rage tunani ni nan zan zamo muku gata ko wacce zata koma inda takeso"

Ya faɗi maganar yana shafa sajen da yayi luff a gefen kumatunsa.

"Bamu da isasshen lokaci, yanzu zamu bar nan zamu tafi India, sbda tserewa Shahazad, ya baza jam'i ta ko ina, mafitarmu shine mubar garin an, nariga na gama komai zamubi jirgin ƙasa"

Inda yake maganar sai ka rantse da Allah har cikin zuciyarsa yakeyi, hankalin Mona a kwance tace "nifa ƙauyenmu nakeso ka mayar dani, ita kuma taimako take nema zuwa Nigeria"

Kharan Khan yace "na fahimceku, Abinda nake nufi, duk wata hanya da zamubi za'a iya gano inda muke matsawar ba India muka tafi ba"

Gabaki ɗaya kan Mona ya kulle a fili tace "idan har sai mun koma India a bar mu anan ai lokacin dana nemi taimakon ka bakace min haka ba"

"Keee!!"

Kharan Khan ya daka mata tsawa, tare da cewa "bawai sai abinda kikace zanyi ba, ko kubini India kokuma in barku anan"

Tashi ɗaya suka fara kuka, Hajara kam sai ambaton sunayen Allah takeyi, gabanta na cigaba da faɗuwa.

Kharan Khan zeyi magana kenan, sukaji jiniyar motar sojoji.

Nigeria
Abubuwa sun faru, haɗuwar Juwairiyya da Alhaji Al'amin, sati guda da haɗuwarsu Amma ya sauya musu gida, ya siyawa Malam Yusuf Mashin ita kuma ya mayar da ita ƴar gayu, a take malam Yusuf ya tara shedu aka sanya ranar auren Juwairiyya akan sadaki dubu ɗari bakwai, kuɗin gaisuwa dubu ɗari.

Yanzu kam Alhaji Al'amin ya zamo ɗan gida, saboda daga yazo da mota zeyi sallama ya shigo,
Kamar koda yaushe idan yana gari baya rabuwa da gidan nasu, yauma hakan take hannunsa riƙe da babbar leda ya shigo da sallama, kasancewar malam Yusuf ya fita sai Juwairiyya yasa taje ta karɓi ledar tana gaishe shi, amsa wa yayi kana yace "nama ne na kaji ki juye, jiki na rawa taje ta juye, ta dawo tsakar gida inda ta shimfiɗa masa tabarma,
"Uhm kin kusa zamo wa mallakina ina jiran wannan ranar har mafarkinta nakeyi"

Juwairiyya ta rufe ido tare da cewa "me kakeci na baka na zuba?"

Yace "dambu"

Ta kwashe da dariya, tare da cewa "uhm saura kwana shida ai"

Murmishi yayi, kana ya miƙe tare da ajiye mata maƙudan kuɗaɗe ya fice ta miƙe ta rakashi, a hanya yake nuna mata photon gidan daya siya mata, kana yace kar su malam su siyi komai har kayan sawa.

Kamar zata rungume shi tsabar Godiya.

Malam Yusuf na dawowa ta sanar masa, yayi farin ciki harda ma ganin naman daya kawo musu.

Abinda kowa bai sani ba, Alhaji Al'amin bai sanarwa da danginsa auren da zeyi ba, ko meye dalili oho.

Acan ɓangarensu Dady yau suka sauka a garin su Bauchi, cikin kwanciyar hankali, tare da Iffat da Hajiya ƙarama, bayan sun gaisa a parlo, suka zube, Hakeem kam bakinsa yaƙi rufuwa, Hajiya babba kuwa ta shirya musu abincin tarba mai rai da lafiya, bata nuna musu komai ba, saboda cikar ƙudurinta,
Har ɗaukar Iffat tayi ta ɗora a cinya, kana tace mata "ya jiki"

"Da sauƙi" Iffat tace tana kallon Hakeem,

Hakeem yace "wato kowa kinje gurinsa amma ni kinƙi kulani ko?"

Iffat tayi dariya kana tace "yi haƙuri yaya gani nazo"

Ta taho tanayi masa dariya,

Washe gari, Dady ya koma ɗakin Hajiya babba, Iffat ta saba dashi, abinka da yaro ta bishi can, bayan sun gama breakfast ta hanyare cinyarsa tana cewa "Dady jiya da dare yaya yace zai sani a school idan ka yarda"

Hajiya babba ta galla mata harara tare da kawar da kanta gefe,
Dady yayi murmishi kafin yace "eh ni da kaina zan kaiki amma sai first an dawo hutu"

Iffat ta hau  tsalle tana murna, Dady ya miƙe tare da cewa "nikam barin je in duba abubuwan da suka wakana bayan tafiyarmu kuyi hira ga Eshat nan"

"Toh Alhaji a dawo lafiya"

Yana fita ta kamo kunnen Iffat tace "wlhi idan kina shigo min sashe na sai na yankaki, kuma idan naji kin gayawa wani sai na ƙona bakinki"

Iffat ta toshe baki, tare da miƙewa zata fice, Hajiya babba ta fincikota ta faɗi ƙasa, kana tace "munafuka ƴar zina"

Iffat ta sunkiyar da kai, tare da fakar idon Hajiya babba ta ruga part ɗin Hajiya ƙarama da gudu.

Cikin tuhuma Hajiya ƙarama tace "my Eshat lafiya?"

"Babu kowa"

Iffat ta faɗa tana zaro idanu.

Har rana tayi Dady bai fita aiki ba, da yazo cin abinci yace "a kira masa Iffat"

Sai da Hajiya babba tayi jimm kana ta miƙe taje sashen Hajiya ƙarama ta tsaya a bakin ƙofa kafin ta dawo,

"Alhaji tayi barci"

Dady yace "ikon Allah barcinta babu wuya, nazo wucewa naji firarsu ita da hajiya"

Aran Hajiya babba kuwa, baƙinciki ne yayi kwance sam bata son taji Dady ya ambaci sunan iffat ko kaɗan.

Hakeem ya mayar da hankalinsa ga jarabawar ƙarshe da suke yi na s.s.c.e, shi yasa bai cika zama a gida ba, sai dai idan ya dawo, yana cin abinci zai wuce gurin aiki, hakan yayiwa Hajiya babba daɗi, sbda batason taraiyyarsa da Iffat.

Horn driver yayi a bakin get ɗin gidansu Amani, mai gadi ya taso da gudu ya buɗe get ɗin tare da yi musu sannu da zuwa, cike da isa da iko ta zuro ƙafafunta waje, kana ta fito da jikinta duka tana gyara mazaunin gilashinta, gyara zaman mayafinta tayi tare da fara takawa i zuwa cikin gidan, kamar mai tsoron taka ƙasa, cikin rashin sanin inda ta dosa ta murɗa handle ɗin ƙofar part ɗinsu Mona, Mahbob dake tsaye yana gyara zaman hular kansa suna magana da Amani, ta Kunno kai, a hankali ta jawo gilashinta tare da ƙaremusu kallo tace "Please nan ne gidan Alhaji Auwal?"

Amani ta ture Mahbob ta ƙarasa fitowa gurinta kana tace "dallah banziya marar tarbiyya ki koma idan aka koya miki sallama da tarbiyya sai ki zo ki tambaya, nan gidan ya samu ingantaccen yabo kinji"

Shikam Mahbob har ya riga ya fice, sbda baya son hayaniya,

Naeema ta zaro ido kana tace "kee!!!, kinsan dawa kike magana kuwa?"

"Ahh to dawa nake magana idan banda marar tarbiyya?"

Naeema ta danna number Batool tana ɗauka, Naeema ta fashe da kukan ƙarya kana tace "tayi mistake ɗin shigowa yaran mijinta sunyi mata duka"....!

Uhm nace kuyi haƙuri har yanzu banyi muku mai yawa ba.

More comments more eheem

Mom Islam
*💋MURAYU A TARE 💋*

Mom islam

            Book1


page 69-70




Tuntsirewa da dariya Amani tayi, kana tace "shagali, sharri ga mai yinka"

Ta shige ciki tare da bugo ƙofa.

Naeema tayi ƙwafa tare da gyara zaman gilashinta, taci gaba da tafiya zuwa part ɗin su Batool,  cikin zafin rai, take bubuga ƙofar, Batool ta buɗe mata tare da rungumeta,

Suna shiga ciki, kai tsaye suka wuce bedroom ɗin Batool, Naeema tace "wlhi anty Batool yaran mijinki basu da kunya harni zasu gaggayawa magana?"

Batool ta tashe bakin Naeema da tafin hannunta, cikin rage murya tace "haba Naeema so kike yi mahaifinsu yaji kinsan fa yana gida?"

"Mtsew ai yaran ne basu da tarbiyya wlhi"

Naeema ta faɗa tana cire mayafin jikinta,

"Yauwa ƙanwata, abinda nakeso dake, ki yi iya yinki gurin farauto zuciyar Mahbob, wlhi ba ƙaramin ji dake zai yi ba, kinga inda kika sake fresh ne ga kumatu kin ajiye"

"Highe anty Batool duk ma ba wannan ba, shine kika zuga su Dady da mama dole sai na auri wannan yaron?, Bayan kinsan a tsarina babu batun aure har sai na cika muradi na?"

Batool ta taɓo kafaɗar Naeema kafin tace "nasani amma dole ki kawar da ƙudirinki, tunda ga aljannar duniya zaki samu, ki wataya inda kike so ki taka wanda kikaga dama, duk da ke ba matar gwamna bace, amma dole da yawan mutane zasu biki, girkifa sai kinga damar yi har wanki wanke-wanke da guga, kinga kuwa rayuwar jin daɗi zakiyi"

Duk da haka dai Naeema batace komai ba,

Wayar Batool ta fara ruri, kallon screen ɗin wayar tayi, kana ta miƙe da sauri, tace "ki shirya zuwa gaishe da sirikinki"

Naeema ta waro ido kafin tace "uhm nifa banason takura"

Batool tace "nidai karki bani kunya"

Batool na fita Naeema ta cire rigar ta ya rage daga ita sai bra da dogon wando,

A hankali ta murɗa handle ɗin ƙofar ɗakin Abba, tare kutsa kai ciki, ga mamakinta taga har ya shirya cikin shadda fara, tasha aikin wuta,
Zama tayi a gefensa tare da kamo hannunsa tace "wlhi na ɗauka kana barci har yanzu shi yasa ban shigo ba"

Cike da so da ƙauna ya janyota jikinsa, yana cewa "inason fita da wuri shi yasa"

"Naeema tazo"

Batool ta faɗa, tana rungume a jikinsa.

"Masha Allah tazo lafiya?"

"Lafiya lau"

"Am na mance ban gaya miki ba, jiya yayana yakai dukiyar auren Mahbob gidanku"

Batool tayi kamar zata shige jikinsa, a fili tace "Masha Allah, Ubangiji ya sanya alkairi"

Abba ya amsa "da Amin".

Ta ɗauko agogon hannu ta ɗaura masa,

Kana ya miƙe tsaye, itama miƙewar tayi hannunta riƙe da hula, suka fito parlo.

"Barin yiwa Naeema magana"

Tana tura ƙofar ta ganta daga ita sai bra da dogon wando, murya ƙasa-ƙasa tace "dan Allah ki sanya kaya da hijabi ki fito ku gaisa"

Naeema ta turo baki, tare da cewa "uhm ni wlhi kina takuramin da yawa"

Hijabi ta saka kafin ta wuce parlo, zubewa tayi ta gaishe shi, ya tambaye ta yasu mama, tace masa "lafiya lau"
Kana ta koma ɗaki,
Batool tazo ta zauna kusa dashi, dama ta riga da tasa masa hular, Abba yace "gaskiya Naeema akwai hankali ga tarbiyya"

Batool tace "kai Alhaji"

Yace "da gaske gidanku ai babu wanda zai samu mata yayi buruss iri mai albarka"

Batool ta kalli agogon dake manne a jikin bango, ƙarfe 12:30pm, Batool tace "Alhaji breakfast fa?"

"Zanyi yanzu"

Taje kitchen ta ɗauko flaks na ruwan zafi da gwangwanin madara da bonbita ta kawo, da cup kana da bredi, bayan ta haɗa masa shayin ta miƙa masa, ta kunce ledar bredi ta miƙa masa,
Suna hada ido sukayi murmishi a tare.

Yana kammala breakfast ɗin ya miƙe tare da cewa "sai na dawo"

"Allah ya kiyaye hanya Allah ya tsare"

Batool tayi masa kana ya fice.

Kai tsaye part ɗinsu ya wuce, dukkansu suna zaune a parlo yai sallama ya shiga, "walaikumusalam" suka amsa, kowanensu ya gaishe shi, lokacin suma suke karyawa,

Bayan ya amsa yace "ankai kuɗin auren Mahbob"

Inaya ta taho da gudu ta rungumeshi,

Cikin tsokana yace "auta maiyasa kwana biyu bakya zuwa part ɗin momynki?"

"Babu komai"

Inaya tace.

Daga Batool har Aseela babu wanda yace komai, bare Huda, da bakowa ba.

Da kallon mamaki yabi Amani, sbda ya santa farin sani, baya taɓa magana tayi masa banza, sannan duk abinda yake so shi takeso "

"Amani lafiyarki kuwa?"

Amani ta ƙirƙiro murmishin yaƙe kana tace "lafiya Abba"

Abba yace "ba haka kike ba maiyasa kika sauya"

Cikin ƙosawa da tambayoyin Abban tace "Allah ya sanya alkairi "

Amin yace, jiki a sanyaye ya miƙe, tabbas gabaki ɗaya yaran sun sauya masa, har Inaya da batasan komai ba,

"Ku shiga ku gaishe da budurwar Mahbob tazo ɗazu"

"Toh" sukace cikin haɗin baki.

Yana fita sukace babu inda zasu,

Amani ta kalli Huda tace "wlhi idan kika sake zuwa sashen Batool sai na ɓata miki rai"

Huda tace "Anty Amani, wlhi itace takeyi min masifa"

"Ai ƙarewar masifa ta dukeki shine zata tabbatar da ita ba kowa bace fashe muguwa"

Aseela tace "Abin mamaki aure daɗi, Abba baya shigowa ya duba tafiyarmu, ko yaga mun ci abinci ko bamuci ba, sannan ko fira ya dena yi damu"

Amani tace "mtsew ke kika damu dasu ma"

Huda tace "za'ayi bikin Ummana yau nakeson tafiya"

Aseela tace "bari bro Mahbob yazo sai ya kaiki"

Acan ɓangaren Umma kuwa, tayi sharr da ita, saboda harda shafe-shafen zamani akayi, tayi kyau, abokan malam Ado, wato mahaifin Huda, sunyi rawar gani, dan har karɓar auren sukayi, sai ranar ɗaurin auren Mahbob ya kawo Huda, a hakan ma yace "da yamma zai zo ya ɗauketa.

Umma tayi kyau sosai, ta haɗe cikin atamfa ɗinkin riga da skirt, dama ba jiki ne da ita ba, sannan kuma bata da wasu yawaitar shekaru, sbda bata wuce 35yrs ba.

Huda ƴar amarya, tare Umma tayi musu ɗinkin, yanzu kam ta rage yi mata kyara ko hantara,

Zuwa la'asar motocin ɗaukar amarya suka zo guda uku, sharoon, yawancin mutanen anguwar sai da suka tafi, wasu sunje ganin ƙwaƙwaf, wasu sunje Allah ya sanya alkairi.

Kasancewar Mahbob yazo lokacin da motocin zasu tafi, yace Huda ta shiga ya Kaita, bayan sun ga gida, suka yiwa Umma sallama ya koma da ita gida.

Wannan gida shi ake kira da aljannar duniya, saboda gidan ya haɗɗu ya gaji da haɗuwa, mai kushe kyansa da tsaruwarsa sai maƙiyi.

Wasu ma cewa suke yi ko sana'ar yankan kai mijin nata yakeyi,

Lokacin da motocin suka dawo domin komawa da mutane, Maryamah na gurin Umma, sai gaya mata sirruka ake yi, daga ƙarshe suka yiwa Umma sallama suka tafi,

Ita kuma ta buɗe toilet ta shiga, tsayawa kallonsa tayi, wasu abubuwan ma batasan inda ake amfani dasu ba, ta kunna famfo tayi alwalah, ta fito ta kabbara sallah.

Bayan ta idar gami da yin addu'a, ta ninke sallahya ta hanye gado,

Kiran sallahar isha'i ne da akayi, yasa ta sakko tayi sallah, lokacin Alhaji Lukman ya shigo, ita kuma tana ninke sallahya, Barka da shigowa tayi masa, kana ta zauna a bakin gado,

Hannunsa riƙe da ledoji guda biyu, ya ajiye tare da cewa "kawo mana faranti"

Da lalube taje kitchen ta ɗauko da cokali da cups ta dawo, umartar ta yayi da ta buɗe kajin da gasashen naman, ta zuba ko wanne kaɗan-kaɗan, ya zauna suka fara ci, ta tsiyaya musu 5alive mai sanyi,
Ita ta fara cire hannu kana ta miƙe taje tayi brush ta sauya kaya zuwa na barci,

Shima a nasa ɓangaren fridge yakai, kana ya koma ɗakinsa ya sauya kaya zuwa na barci.

Ɗakinta ya dawo, lokacin ta kwanta, abin tambaya anan banga sunyi alwalar masu first night bane HHH, ya bi bayanta ya rungume,

Kun sanfa Umma an tsumu sosai, sai wani turo masa ƙirjinta da yaci kuɗi tsabar gyara takeyi, shiko yanajin tudun nonuwan yayi burus ko meye dalili oho, shafo gashin kanta yayi, wanda yasha gyara, yace "maiyasa ba'ayi min kitso ba?"

Murya ƙasa-ƙasa tace "uhm babu komai"

Burinta bai wuce taji ya zura hannu a ƙasanta ba, sbda a halin yanzu duk ta fara tsiyaya, sai wani mammatse ƙafafu takeyi, harda dabara duk dan kar ya gane ta,

Bakinsa yakai kan nipple ɗinta, hannunsa ɗaya yana murza ɗayan,

Daga ƙarshe ta kai hannunta gabansa, taji wani babban Abu,

Murya ƙasa-ƙasa tace "meye wannan?"

"Robar fitsari ce"

Umma ta zaro ido.

Acan Garin Bauchi, Ummi da Aliyu sunata shirye-shiryen komawar Tasneem garin Kano, yau kwanan Haneefa biyu da zuwa, tazo ta gaishe da Tasneem da jiki,

Jiya suka koma sabon gidansu, ita kuma Ummi gobe zasu koma,

Washe gari, dama mota ta gama kwashe kayan, su Tasneem da matar Aliyu sunje sun gaya kayan, zuwa yamma Umma tayiwa mutan gidan sallama ita da malam suka tafi.

Nanfa tsegumi ya tashi, kowanensu na tofa albarkacin bakinsa,

Kwanansu biyu da komawa, Aliyu yace Tasneem ta shirya gobe zasu tafi Kano harda Malam.

Washe gari, kuwa ta shirya, cikin baƙar abaya tasha ado, kasancewar Aliyu ya siyo mata kaya da ɗan yawa, da safe suka wuce tasha suka hau mota zuwa Kano,
                     *****
Cikin hukuncin Allah sai gashi sun shigo Kano, bayan an saukesu a tasha, suka tari napepe zuwa anguwar Kurna,

Ikon Allah duk haukar da Tasneem tayi bata mance da gidan Hajiya ba, suka ƙwanƙwasa ƙofa, wani ɗan ƙaramin yaro ya buɗe yana ta kallonsu, suka shiga, bayan sunyi sallama a ƙofar ɗakin hajiyan, bata ɗauki Muryar Tasneem ɗin ba, sai ganinsu tayi sun shigo, Hajiya ta mutsike idonta ta buɗe kana tace "Tasneem ashe kina raye?"

Sai kuma ta fashe da kuka mai ban tausayi.

Ummi da Aliyu sukace "Hajiya farin ciki zakiyi ba kuka ba"

Tasneem tace "Hajiya ina uncle"

Hajiya tace "ya lafiya ko jiya sai da yayi maganar ki, ina Iffat jaririyark?"

Wasu zafafan hawaye suka kwaranyo a idanun Tasneem, zata yi magana kuka ya sarƙeta,

Hajiya ta ɗaga waya, ta kira Uncle, yana ɗagawa tace "ga marainiyar Allah ta dawo gida, Tasneem"

Jikin Uncle na karkarwa yace "gani nan zuwa Hajiya"

Ba'a ɗau tsawon lokaci ba, sai gashi nan ya shigo, tsabar gigicewa a ƙasa ya zauna yana ƙarewa Tasneem kallo,

"Ikon Allah ashe zamu sake haɗuwa, adu'armu bata faɗi ƙasa banza ba"

Kana yace "Tasneem su waye waɗannan"

"Sune suka taimakeni, Uncle wannan shine ya tsintoni, ta nuna Aliyu, kana tace "malam kuma mahaifin Aliyu ne shine yayimin magani, ga mahaifiyarsa itace ta kula dani....

Idan har naga comments sosai, zanyi wani, idan babu comment an jima  bazaku samu ba🤩

*💋MURAYU A TARE💋*

Mom Islam

        Book1

Page 71-72

Cikin jin daɗi Uncle yace "Masha Allah" tare da kallon Ummi da malam kana yace "muna godiya Ubangiji ya saka muku da mafificin alkairi"

Hajiya tace "Aliyu haƙiƙa kayi namijin ƙoƙari, Ubangiji yasa a gama da duniya lafiya"

Aliyu ya amsa da "Amen"

Hajiya tace "Tasneem jeki kitchen ki ɗibo musu abinci"

Tasneem ta miƙe tana murmishi kana ta wuce kitchen,

Babbar foodflaks ta ɗauko taci ka musu shi da shinkafa, sannan ta ɗauko na miya tasa miya, ta zuba soyayyun nama kamar inda ta gani a ajiye,
Sai da ta ɗauki cokula da farantai masu kyau, kana ta fito ta kawo parlon Hajiya.

Har yanzu Uncle bai gaji da kallon Tasneem ba, shi a tunaninsa ma tariga da ta mutu,

Ƙaramin yaron da suka samu a bakin get ne ya fito yana cewa "Hajiya na bige wayo Allah"

Hajiya taje da sauri tana duba masa goshin da ya bige,

"Babu abinda ya sameka kai dai raki irin naka"

Tasneem kam kallon yaron takeyi babu ko ƙiftawa, sbda yayi mata kama da wani sashi na rayuwarta, sam bata
End Ads