x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 2 - MU RAYU A TARE book 1

  • 3001 words
  • 6000 words
  • Out of 62845 words

Category: Love Stories

Views 94

09 Aug 2025
Start ads
After Image Ads
ko a tv bai taɓa ganin inda akayi hatsari ƙwa-ƙwalwa ta bugu tashi ɗaya ba, har ya fara zargin kodai likitan ƙarya yayi masa,
Kamar wanda aka tsikara ya matsa jikin tagar asibitin, ya kafa idanunsa a gilashin tagar yana hango Iffat an naɗe mata kanta, sai wani irin numfashi take,
A razane ya sake kai kallonsa gareta ya kuma fashewa da kuka, kafin daga baya ya fara tunanin ya za'ayi taci abinci?,
Yanke shawarar komawa gurin likita yayi, cikin azama ya nufi ofishin likitan, yana zuwa kai tsaye ba tare da neman izinin shiga ba, ya shige,
"Likita nace marar lafiyar zata iya cin abinci kuwa?"

Hakeem ya faɗa yana tsaye a bakin ƙofa,
"Babu buƙatar cin abinci sai zuwa gobe insha Allah"

Jikin Hakeem a sanyaye ya koma ya zauna, a haka har gari ya waye ko runtsawa beyi ba, kafin a shiga sallar asuba yaje yayi alwala ya fara nafila har aka shiga sallah, bayan an idar ya ɗaga hannuwansa sama yana roƙawa Iffat lafiya a gurin Allah, har kowa ya fice aka barshi shi kaɗai, daga ƙarshe ya fito, tare da kallon harabar asibitin, duk da bawai gari yayi haske sosai bane.

Sai yanzu ya tuna tun dare da ya kashe wayarsa be kunna ba, ya cirota kana ya kunna, kafin ya cire a security kiran dady ya shigo, Dady yace "suna mota Hakeem ya gaya musu sunan asibitin, bayan Hakeem ɗin ya sanar dasu suka kamo hanya,

Shikuma Hakeem ɗin ya ƙarasa cikin asibitin, yana shiga ya doshi ɗakin Iffat, wani likita ya dakatar da Hakeem yana cewa "kaine ka kawo wata yarinya?"

Jikin Hakeem na rawa yace "eh nine lafiya?"

Likitan yace "akwai buƙatar a samo mata ruwan kunu ko shayi tasha"

Hakeem yace "insha Allah"

Jin Muryar su Hajiya babba yasa Hakeem juyawa yana yi musu sannu da zuwa, kafin ya nuna musu ɗakin da Iffat ke kwance har yanzu da oxygen a hancinta, jikin Hajiya ƙarama yayi sanyi matuƙa, sai kallon Iffat takeyi, wacce take ta rarraba idanu tana kallonsu kamar yau tazo duniya,
"Dady yace "iyayenta fa?"

Hakeem yace "dady kowa na tambaya cewa yakeyi be taɓa ganinta ba"

Dadyn yace "amma ya yanayin jikin nata?"

Hakeem yace "dady har yanzu dai banji tayi magana ba, duk da akwai abun numfashi a tare da ita, amma ance ƙwa-ƙwalwarta ta taɓu"

Dukkansu suka kama salati Hajiya babba tace "yanzu aiki kenan zasuyi mata ?"

Hakeem yace "wlhi nidai ban sani ba, gadai shi nan mun zuba musu ido"

Dady yayi shiru, tausayin yarinyar ya kamashi, yana son gano inda yasan yarinyar amma ya kasa ganowa, haka dai ya haƙura, ya kawar da tunanin ta, suna zaune likita ya shigo da kayan aiki, ya cire mata abin numfashin kana ya sake yi mata wasu gwaje-gwaje, kana yace "sannunku, zaku iya bata abinci amma marar tauri, suka amsa da "to"

BAUCHI
Cikin shirin tafiya aiki Alhaji Auwal ya fito, hannunsa riƙe da ja ka irin wacce ma'aikata suke riƙewa,

Amani ta fito riƙe da hular Alhaji Auwal a hannunta, ita kuma Aseela hannunta na riƙe da turare, Amani ta sanya wa Abba hula, Aseela ta fesa masa turare, Mahabob kuma yana riƙe da mukulin motar Abban, Inaya ta fito a shagwaɓe, kasancewar itace autarsu, Abba na ganinta yace "ƴar albarka lafiya?"

"Abba aunty Aseela ce ta hanani wayarta, inyi Game"

Abba yayi dariya, shi yama ɗauka wani babban abu ne, cikin sigar lallashi yace "karki damu zan siya miki sabuwa, Aseela ayi haƙuri a bata kafin in siyo mata nata"

Aseela ta shagwaɓe fuska tace "Abba wlhi ta fiye shige-shige ne"

Kana Aseela ta miƙa mata wayar, ta koma ciki da gudu su kuma suka fita raka Abba parking space,

Suna tsaye ya shiga mota, Mahabob ya miƙawa driver key, suka yiwa Abba adu'ar Allah ya tsare, kana suka koma ciki.

Tunda suka dawo, suka kafa meeting, akan auran da suke son Abban nasu yayi, sunata adu'ar Allah ya haɗashi da mata ta gari mai tausayinsa,

A hankali drivern yayi tuƙi har suka iso ma'aikatar Alhaji Auwal ɗin ta ƙera kayayyaki, musamman atamfofi da rigunan sanyi, bayan drivern yayi parking an buɗewa Alhaji Auwal ya fito, idanunsa yai tozali da wata budurwa ta fito daga wani office, cikin nutsu yake kallonta har ta ƙaraso ta wucesu, ya ɗan tafi da sasarfa, kana ya tsaya ƙyam, yace "Ahmadu driver kiramin waccar yarinyar, cikin mamaki Ahmadu yace "to" har ta kusa fita daga get ɗin ya isar da saƙon Alhajin, jin ance mata Alhaji Auwal ne yake kiranta, sai ta fara rawar kai da rawar jiki, tunda ta sanshi tasan labarinsa, labarin gidansa ne bata sani ba, cikin nutsuwa ta iso gareshi, driver ya wuce, kana ta durƙusa ta gaishe shi, cikin farinciki da yabawa da hankalinta da yayi ya gyara tsayuwa, kana yace "sunana Alhaji Auwal"
A hankali budurwar tace "masha Allah" kana yace ko zan iya sanin sunanki?"

A kunyace budurwar tace "sunana Batool"

Allhji Auwal yace "masha Allah, idan bazaki damu ba ina sonki, so bana wasa ba so na aure, kinsan dai ni ba yaro bane"

Batool tace "to Alhaji yanzu zanje gida babana yanata kirana"

Alhajin ya karɓi number wayarta tare da ciro kuɗi har kimanin 20k ya bata kana sukayi sallama,

Tana tafe gabanta na ci gaba da faɗuwa, a zahiri bawai kiran nata akeyi ba, ƙafafuwan ta ne suka gaza ɗaukarta dan haka ta samo mafitar faɗan haka, Alhaji Auwal yayi murmishi, bai bar gurin ba har sai da Batool ta ɓace, kana ya shiga ciki,

*💋MU RAYU A TARE💋*


Mom Islam

7-8

Da sallama Huda ta shigo ita da wasu yara guda biyu, ɗaya yana riƙe da kular abincin siyarwarta, ɗaya yana riƙe da bokitin miya, ita kuma tana riƙe da robar soso da omo,
Daga inda Umma take zaune ta amsa tare da cewa "oyoyo Huda ƴar albarka, an siyar da abincin duka ko?"

Huda na murmishi tana kallon yaran da suka ajiye mata kaya tace "na gode" suka wuce.

Kafin tace "Umma an siyar amma naga kuɗin bekai kamar na jiya ba"

Cike da ruwan bala'i Umma tace "ni zaki mayar ƴar iska wacce batasan abinda takeyi ba, in tashi tun asuba in hana idona runtsawa kuma in hana jikina hutu, amma kicemin kuɗin be kai ba?"

Kafin Umman ta kamo Huda ta cakumi wuyan rigarta tana cewa "gayamin wa kika bawa abinci bai baki kuɗi ba?"

Huda ta zazzaro idanu waje cike da tsoro tace "wlhi Umma babu wanda na bawa daga zubin abincin ne haka"

"Dan ubanki ce miki akayi nima a shago irin zubin abincin da sukeyi min kenan?"

Huda ta girgiza kai cike da tsoro,

Umma tace "gobe in Allah ya kaimu wlhi tallahi kinji na rantse idan baki dawo min da kuɗina cass ba sai na illataki tunda kin fara nunamin rashin gaskiya"

Jikin Huda na rawa tace "nayi miki alƙawari Umma ki sakeni wlhi zan kawo miki gobe"

Sannan Umman ta saketa tana mayar da numfashi kamar wacce tayi gudu,

Tsabar tsoro da ya kama Huda, tunda ta miƙawa Umma kuɗin ta ɗauki buta ta yi alwalah, ta dawo ɗan ɗakinta ta shimfiɗa wani ɗan ƙyalle ta kabbara sallah, tare da rama sallolin azhar da la'asar, kana ta zauna jiran magriba.

Har akayi isha'i bata fito ba, Umman ma bata nemeta ba,

IFFAT
A hankali Hajiya ƙarama ta dinga bata tea tana sha cikin nutsuwa, sai dai har yanzu babu wanda yaji sautin muryarta, ko kallon da take yiwa mutane ma wani iri, marar kyau, duk wanda yaga ƙwayar idanuwanta inda suke juyawa yasan Iffat na cikin wani hali.

Haka suka wuni jiki a sanyaye babu wani kuzari, zuwa yamma Dady ya ɗauki Hajiya babba suka koma gida, ya rage saura Hakeem da Iffat ɗin da kuma Hajiya ƙarama,

Hakeem ne ya fara fita yin sallahar magriba, bayan ya dawo Hajiya ƙarama taje tayi alwalah itama ta kabbara sallah, Hakeem na zaune yaga Iffat nata jijiga, alamun jikin ya tashi, cikin hanzarin da gudu yai ofishin likitan, ko sallama babu bare neman izini yace "doctor kazo yarinta zata mutu"

A inda Hakeem ɗin yayi magana, doctor ya bawa wanda yake sallama haƙuri kana ya fice da gudu, abin al'ajabi, likitoci uku ne suka haɗu a kanta, amma sam har yanzu Iffat bata numfashi, a zahiri dai an fara kyautata zaton ko mutuwa tayi?, hankalin Hakeem yayi mummunan tashi, zufa babu ta inda bata karyo masa, rai a ɓace yace "aikin banza aikin wofi, likitoci kunkai ku huɗu amma kun kasa ceto rayuwar yarinyata kun kasa dawo mata da numfashinta?"

Ɗaya daga cikin likitocin yayi murmishi ya girgiza kai,

Ana fita da Hakeem yana ci gaba da gaggaya musu maganar da duk ta fito daga bakinsa.

GIDAN MALAM YUSUF
Har akayi kiran sallahar magriba Hajara na zaune akan kujera ƴar tsugunno ta rafka uban tagumi, tashin hankalinta baya wuce idan malam Yusuf ya shigo gidan ya fara surfa mata ruwan masifa, shine babbar damuwarta, jin an shiga sallah ya sanyata miƙewa ta ɗauki buta ta nufi banɗaki, tsaki tayi, sakamakon ganin tiƙeƙen kashi a bakin masai, kana ta samu tsinke ta tura tana Allah wadai da hali irin na Juwairiyya, kama ruwa tayi ta fito, kana ta tsugunna ta ɗaura alwalah ta nufi ɗakinta, tana shiga tasa ƙafa ɗaya ta faɗi tiimm, sakamakon santsi da ya kwashe ta wanda batasan ta ina yazo ba, cikin ɗaga murya tace "Juwairiyya bakya jina ne ?inata ihu dan Allah kizo ki taimaka min in tashi ƙafata ta gurɗe"

Juwairiyya na daga ɗaki tace "kinga bani da lokacinki, kuma wlhi girki ne dole kiyi, idan baba ya kawo"

Hajara tace "wlhi banga wanda ya isa ya sanyani girki a gidan an ba, musamman ma a wannan halin da nake ciki"

Juwairiyya na daga ɗaki tace "idan baba ya dawo zaki mai-maita masa"

Hajara ta fashe da kuka, mai ban tausayi, cikin ƙarfin hali ta kama bango da ƙofa ta miƙe, kana ta nemi guri akan kujera ta zauna, cikin ikon Allah aka kawo wutar nepa, Hajara ta kalli gurin da ta faɗi, ga zahiri nan sosai mangyaɗa aka zubar domin ta, tasan aikin na Juwairiyya ne, ba sai an gaya mata ba, Hajara ta girgiza kai, ta fara tunanin itakam me ta tarewa Juwairiyya a gidannan ne?

Tana tsaka da tunani sai jin mutum tayi ya faɗi timmm..., cikin firgici tace "malam lafiya?"

Ashe tun daga ɗakin Juwairiyya yake surfa masifa, yazo yiwa Hajara ya faɗi a bakin ƙofa, santsin man gyaɗan ya yar dashi, hajara ta rufe bakinta sakamakon dariya dake zuwar mata, malam Yusuf ya tattaro dukkan ƙarfinsa, yana cewa "ƴar baba zo kiyi temako babanki ya faɗi"

Juwairiyya ta fito da gudu, ta bankaɗo labulen ɗakin Hajara, tana cewa "wlhi baba ina kallonta ta zuba maka miyar yauƙi a gurin kawai zata kashe mana kai ne"

Tana maganar tana kamo hannun mahaifin nata, cikin ikon Allah ya miƙe amma har yanzu yana riƙe da Juwairiyya, Hajara ko ta zuba musu ido ba Um, ba um-um.

Har zasu fice "Hajara tace "baba kasan dai ni marainiya ce, mahaifiyata ta rasu dan Allah baba ka rabu da Hajara, domin inada yaƙinin zuwa gaba zata iya kashemin kai"

Cikin bin umarnin Juwairiyya yace "Hajara kije gida har sai na nemeki"

A hassale Hajara ta miƙe, tama mance da zugin da ƙafarta keyi, cikin masifa tace "wlhi tallahi idan har baka sakeni yau ba, baka cika lusari me jin maganar fitsararriyar ƴarsa mai gurɓatacciyar tarbiyya"

Sosai maganar tayiwa malam Yusuf zafi, zuciyarsa na raɗaɗi jikinsa na ɓari yace "Hajara yaushe kikayi baki da har kike jifana da munanan kalamai?"

Kafin Hajara tayi magana, Juwairiyya ta saki baba ya faɗi ragwab, ta taho da sauri tare da ɗaga hannu zata mari Hajara, cikin azama Hajara ta riƙe hannun ta yar da Juwairiyya a ƙasa ta dinga duka kamar an aikota, malam Yusuf dake ƙoƙarin miƙewa ya kasa, gashi yaji Juwairiyya tana nishin mutuwa, cikin ɗaga murya yace "Hajara ki tattara duk abinda kika sani naki ki barmin gida, na sakeki saki uku na sake ƙara uku, kai idan anayin goma sha biyu yau nayi miki fice, karki kashemin yarinya ita kaɗai Allah ya bani, dan kinga ke bakya aihuwa shine zaki kashe ta, munafuka muguwa,

Hajara tayi tafi tare da cewa "ayirii- yirrii, wlhi tafi nono fari, dama zaman gidanka ya zamemin dabaibayi ne, babu inda zanyi, yanzu kam Alhmdulilah"

Ta fara tattara kaya, Juwairiyya ta miƙe jiki babu ƙwari, ta kamo baba suka fice, ita kuma Hajara ta fara tattara kayanta, takai kusan azhar sannan ta gama, ta fita ƙofar gida neman mota, cikin sa'a kuwa ta hango motar wani saurayi, wanda suke mutunci dashi, wato akori kura, ta ƙarasa tayi masa magana, ya amince zai kwashe mata kayan, amma zata nemi kuɗin fetur ta bashi, kan kace me, har sun kusa kwashe kayan, hatta tukwananta duk ta kwashe, babu abinda ta bari wanda ya kasance mallakinta.

Bayan sun gama ta shiga gaban mota suka wuce anguwar su dake Rugan Julli, bayan drivern yayi parking a ƙofar gidansu, kasancewar ta nuna masa tun suna nesa, ta buɗe motar ta fito, shima haka, ta shige ciki, shi kuma ya fara firfito mata da kaya, tana shiga ta fashe da kuka, Goggo Dije na ganinta ta taso da sauri tana cewa "Hajara lafiya?"
Hajara ta share hawaye, kana tace "mama baba yana ciki ne?"
Goggo tace "ai ya tafi Kaduna neman kuɗi, ki sanar dani meke faruwa?".
Kafin Hajara tayi magana, samarin anguwar sun fara shigowa da kayan gado, Goggo tayi shiru, domin ta fara zargin aikin gama ya gama,

"Hajara kaso auran naki kikayi?"

Hajara tace "wlhi Goggo duk hakurin da nakeyi bai gani ba, ya sakeni saki uku, Goggo tace "me kikayi masa?" sai ga wani saurayi nan ya shigo da takarda a hannunsa ya miƙawa Hajara, Hajara tayi masa godiya kana ta kalli takardar, kasancewar taɗan taɓa hausar boko tace "Goggo takardar saki ce"
Goggo kam ta kasa furta koda kalma ɗaya, tunanin ta bai wuce baban Hajara idan yazo ya surfa musu masifa itada Hajara ba, dama sau tari yakan ce itace take hana Hajara zaman aure, tunda auran Hajara na biyu kenan, duk da ƙarancin shekarunta.

HUDA
Yau ma kamar kullum, taci kwalliyarta ta sanya riga da zani na atamfa, ɗinkin yayi mata kyau, kayan ma sababbi ne, kasancewar ɗinkin ƙaramar sallah ne da Umma tayi mata, rataye da jaka da hijab ta fito tsakar gida, Umman ta miƙa mata abinci a kwano tare da cewa "lokaci dai ba tsayawa jiranki zeyi ba"

Cikin sauri-sauri, Huda take cin abincin, bata kai ga cinyewa ba ta miƙe tana cewa "Umma na ƙoshi"

"Ai ke haka kike, daga ance miki kiyi sauri sai ki ajiye kwanon abinci, to wlhi kanki kika yiwa ba niba"

Umman ta faɗa tana shiga ɗaki ta ɗauko mata takalmin sallahar ta,

Huda na gani, ta zaro ido, kafin tace "umma wannan ai takalmin sallah ta ne"

"Eh sai me, inace ni na siya miki?"

Huda bata sake magana ba, tasa tare da ɗaukar bokiti tayi waje, Umman kuma ta ɗouko babbar kula, sukayo waje, cikin sava sai ga mai mashin ɗin da Umma ta samar mata, wanda sukayi dashi zai dinga zuwa yana ɗaukarta kullum,

Cikin ikon Allah suka iso gurin sana'arta, bayan ta sauka ya sauke mata kayan abincin, tayi masa Allah ya tsare ta wuce,

Yau kam anfi koda wane lokaci cika a gurin, dan harda baƙin ido wanda bata sansu ba, lokacin zuba abinci nayi ta fara zuzzuba musu, suna bata kuɗi, wasu sai sun gama ci sannan zasu miƙa mata kuɗi, wanda yake tare mata faɗa, ya miƙe tare da cewa "Huda dama ke nake jira kizo inyi miki sallama, babana yace in koma gida saboda aurena ya kusa"

Idanun Huda sun ciko da hawaye, tace "Allah ya kiyaye hanya, shike nan bazaka sake dawowa ba?"

Saurayin yace "gaskiya da kamar wuya, inayi miki fatan alkairi"

Ya wuce shima zuciyarsa babu daɗi,

An kammala cin abinci mutane biyu basu bata kuɗi ba, Huda ta miƙe tace "dan girman Allah ku bani kuɗi zan tafi gida", ɗayan ya ciro ɗari biyu ya miƙa mata, Huda tace "hamsin ɗin fa?"

Saurayin yace "ki yafemin"

Shiru tayi batace komai ba, shiko wanda bai bata kuɗin ba, ashe ya faki idonta ya gudu, gashi kowa ya tafi,

Hankalin huda a tashe ta ɗora hannu a kai, kana ta fara hararo masu shagunan gurin, tare da shawarar "gurin wa zataje ya taimaka ya bata kuɗin abincin, gashi jiya tayiwa Umma alƙawarin yau zata ciko mata kuɗin daya ɓata"


Ayi min afuwa kwana biyu banyi posting ba,

Please a tayani share fisabilillah

*💋MU RAYU A TARE💋*
             

Mom Islam


Page 9-10

Jiki a sanyaye ta nufi shagon wani saurayi, yana siyarda manja da man gyaɗa da kuma kayan hatsi, cikin ladabin dole ta durƙusa a gabansa, kafin tace "ina wuni"

"Lafiya lau ya kasuwa?"

Me shagon yace mata, lokacin da yake fitowa daga cikin shagon sbda ya ganeta, yana yawan ganin an wuce da ita a mashin da kular abinci,

"Malam dan Allah ka taimaka ka bani ɗari biyar, Ummana ce tace yau idan ban koma mata da kuɗi sun cika ba, sai tayimin duka"

Mai shagon ya girgiza kai, tare da jin takaicin iyaye masu irin wannan halin, kafin ya ciro ɗari biyu, yace mata "nima ban daɗe da dawowa daga kasuwa ba, duk na kashe kuɗina"

Da sauri ta karɓi kuɗin jikinta na karkarwa, ta miƙe tanayi masa godiya,

A cikin zuciyarta kuwa bayan ta miƙe cewa takeyi "an kashe miciji ba'a sare kansa ba"

Tana tafe tana kuka, ta ƙarasa shagon dake can bayan gidan mai, tana shiga shagon mai siyarda su drinks ɗin ta ƙarasa ciki, kasancewar bataga kowa ba, ido shaɓe-shaɓe da hawaye ta durƙusa a gaban mutumin da a ƙalla zeyi shekaru arba'in, kana tace "malam ka taimakeni ka bani ɗari uku, zan cikawa Ummana kuɗin abinci idan na koma gida duka zatayi min"

Mutumin ya ce "meyasa zata dukeki?"

Huda tayi shiru, sakamakon kukan da ya kuɓce mata,

"Zan baki amma nima zaki bani wani abu"

Jikin Huda na rawa tace "wlhi zan baka, saboda sam bata ma san abinda yake nufi ba, sbda kwata-kwata shekarunta basu wuce sha huɗu ba, amma Allah ya azurtata da cikar halitta, sbda ƙirjinta a cike yake, idan ka kalleta sai kace mai shekaru sha takwas ko ashirin.

Mutumin ya ciro ɗari huɗu, kana ajiye su can kan dogon bencin dake shagonshi, kana yace "idan kika amince dani kinga harda nera ɗari na ƙara miki, yanzu Huda ta fara gano abinda mutumin yake nufi,

Tunda ta tuna da dukan da Umman tace zatayi mata, sai taji zuciyarta ta tsinke, sbda idan Umman ta tashi
End Ads