x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 17 - MU RAYU A TARE book 1

  • 48001 words
  • 51000 words
  • Out of 62845 words

Category: Love Stories

Views 111

09 Aug 2025
Start ads
After Image Ads
tashi ka shiga ciki, yanzunnan ta wuce"

Sum-sum ya miƙe ya shige, kai tsaye ɗakin da take, duk da besan inda ta shiga ba, cikin Sa'a ya hango ta zaune akan gado, da murmishi a fuskarsa ya ƙarasa, ita ko ta juya baya kamar mai tunanin wani abu,

Ta baya ya rungumeta, har ta buɗe baki zatayi ihu ya rufe mata baki tare da ɗagota cak, duk da tanada ɗan ƙiba ba sosai ba, amma bai ji nauyin ɗagata ba, ya ɗorata akan gado, kana ya zauna a gefen ta, cikin Cold voice yace "Wlhi da kinsan irin missing ɗinki da nayi da baki dinga jamin aji ba, ace kin dawo garinnan amma bani da labari?"

Kafin tayi magana sai da taɗau lokaci, kamar bazata ce komai ba, sai kuma tace "jiya na dawo"

Ya kwaikwayi muryarta yace "jiya na dawo"
Wannan abu nasa yana bata dariya, tana murmishi tace "har yanzu kana nan da halinka"

Shima murmishi yayi kafin yace "yaushe zaki dawo gareni?"

"Sai abinda su Hajiya sukace?"

"Ke baki da abinda zaki ce musu? kawai ki sameta kice kinason komawa gidan mijinki"

Tasneem ta zaro ido, kafin tace "ehhh, sokakeyi suce bani da kunya?"

Zahraddin ya tallafo kumatunta, murya ƙasa-ƙasa yace "nayi missing ɗinki sosai, sai dai naga kamar ta ɓangarenki ba haka bane?"

Dariya kawai tayi, cikin kuɓutar baki tace, "bazaka gane bane"

Kamar wanda aka zabura ya rungumeta yana ce mata, "da gaske kema hakanne a zuciyarki?"
Gyaɗa masa kai tayi, sbda rungumar da yayi mata, ta gamsu da kewarta da yayi, kamar Maraya ya kwantar da kansa a gadon bayanta yace "dan Allah ki dawo da wuri, my Tasneem kowacce mace na gani wlhi batayimin kyau, amma yanzu da nayi tozali da kyakkyawar fuskarki sai naji sanyi a raina, a kanki na fuskanci ƙalubale a gurin Dady, har cewa yayi zai haɗani aure da yarinyar abokinsa.."

Cikin sauri tare da kishin da ya taso mata, ta kuma kasa tareshi tace "ai da ka aureta!!"

Zahraddin na rungume da ita yace "ban riga da na amsa ba, bare aje babin aure, kinga amaryar Zahraddin mayar da wuƙar daga ke babu ƙari, na rufe ƙofa"

Ajiyar zuciya ta sauke, lokaci ɗaya taji sonsa ya sake nunkuwa a cikin ranta,

Uncle kuwa abin nasu yafi ƙarfinsa, yayiwa Hajiya sallama ya fice.

Sun shafe awa ɗaya, Zahraddin yana ta nanata mata kewarta da yayi, da Hajiya ta gaji, tace "zoka fice ka barmin ƙawata ta huta haba"

Zahraddin yayi murmishi kamar hajiyar na kallonsa, kana ya zare jikinsa ana Tasneem yayi mata kiss a goshi ya sauka daga kan gadon kana ya tsaya yana ƙare mata kallo, itama narkakkun idanuwansa take kallo, tashi ɗaya ya bata tausayi ta sauko da sauri ta rungumeshi tare da fashewa da kuka, hankali a tashe yake bubbuga bayanta, a hankali yace "Babyna lafiya?"

Cikin Muryar kuka tace "sam banji ka ambaci jininka ba, banji ka kira sunanta ba, banji ka sanarmin da yadda kayi kewarta ba, zuciyata tana zafi idan na tuna na aihu amma bana tare da ƴata"

Zahraddin ya cireta a jikinsa, tare da dafa kafaɗarta yace "tabbas ko barci nazo yi, ina tunanin ta, dan me zai sa in famo miki ciwo, nazo saki farin ciki in tafi kina kukan baƙinciki kenan?"

Tasneem ta girgiza kai, shikuma yai saurin ficewa,

Koda yazo parlo babu kowa, hakan ya bashi damar ficewa ko sallama bai yiwa hajiyar ba.

UMMA House💋

Washe gari, da asbha ta farka, lokacin ma an jima da kiran sallah, duk mugamcinta bata ƙetare lokacin kiran sallah, amman Alhaji Lukman bai tashi ba, har ta shiga kitchen ta ɗora ruwan zafi tazo ta gyara gidan, duk da ba wani datti yayi ba, lokacin da ta ajiye ruwa a flaks a kan dining lokacin ya fito, yana waya, da alamu kiran da akayi masa ne ya rage masa jin daɗin barcin.

Cikin rage murya tace "Alhaji Barka da fitowa anyi sallah tun ɗazu"

"Toh"

Kawai yace mata, kana ya wuce bedroom ɗinsa acan yayi sallahar.

Kafin ta dawo ɗaki, ta dinga tunani kona meye oho,


Ragowar ruwan ta juye ta shiga wanka, tana fitowa ta shafa mai tare da murza hoda tasa tozali kana ta buɗe drowa ta ciro, doguwar riga irin ƴar katinnan koda tasa ta matseta sosai, ana ganin shatin nonuwanta da mazaunanta, kasancewar rigar pink color ce, tasa hula pink, ta fito ta koma kitchen, acan Alhaji Lukman ya sameta, tun daga can nesa yake ƙare mata kallo, dama yazo sanar mata da cewar zai wuce gurin aiki, sai yayi ido biyu da abubuwan da sukafi burgeshi,

A hankali yaje ya rungumeta tashi ɗaya, Umma taji ta dunguri robar fitsari, a ƙasan zuciyarta haushinsa ta kama ji, ga mutum har mutum amma bashi da lafiyar yin aiki, mtsew, shiko sai jifanta da murmishi yakeyi,....


Anjima akwai new update Amma fa idan kukayi comments,


Aslamu alaikum masoya makaranta littafin MURAYU A TARE,
Book2&3 zai zo muku a paid Normal 300 vip 700

Munkusa gama book1 abinda nakeson cewa shine, inason ya zamo wanda sukeson littafin sun biya kudin su, domin muna gama book1 zamu shiga two ba tare da ɓata lokaci ba, da izinin Ubangiji, idan na gama book1 mutane basu gama biya ba, zamu dakata da posting sbda bana son na haɗa abubuwa biyu, ga typing ga adding.

Wanda suka shirya biyan kuɗi su tura ta nan. 3175689751 Zainab Habibu first Bank. Shedar biya ta wannan number 08141799224

Dan Allah kar ayi min Vtu Please idan kuma kati ne, hoton katin zaki ɗauka ki turomin

Ƴan Niger zasu tura da katin Airtel

Nagode

Karkisake ayi book2 babu ke😂 domin kuwa hmmm
*💋MU RAYU A TARE💋*

Mom Islam


Book1

79-80

Rurin da wayarsa ta yi ne, yasa ya matsa gefe tare da amsa kiran,

Bayan ya gama wayar, ya juyo gurin Umma, kafin yace "yau munada manyan baƙi ina tunanin koda sun zo bazasu sameni ba, ko shi kaɗai Alhaji Abdussalam ɗin yazo, sai ku gaisa".

"Ai Gara ka bari su zo sai ka tafi"

Alhaji Lukman ya kamo hannun umma tare da cewa "karki damu babban abokina ne, shida sauran abokanmu"

"Toh"

Umma tace, kafin ta narke ido tace "uhm ko abinci safe bakaci b"

"No karki damu, kedai ki fara hidimar yi musu girki, yanzu zan fita"

Cikin gamsuwa Umma ta juya kitchen taci gaba da hada hadar girki,

Ƙarfe 7:30am ya wuce gurin aiki,

Bayan Umma ta gama zuba sanwa a tukunya tare da sinadarin ɗanɗano, ta dawo parlo tana tunani,
Tabbas duk wanda yaga Alhaji Lukman bazai yi tunanin yanada wata matsala ba, sbda yanayinsa da walwalarsa na, kamar bai damu da sharholiyar ba,

Sosai tayi zurfi a tunani, daga ƙarshe ta tashi ta koma kitchen, cikin Sa'a ta samu ruwan ya tafasa, ta zuba shikafa da busashen kifi, bayan ta wankeshi da gishiri, kafin ta kawo hantar da dama ta riga da ta tafasata, ta yankata ƙana ƙanana, sannan ta motsa ta rufe,

Duk da cewar ba wasu kalolin abinci ta iya ba, amma tanada yaƙinin wannan ɗin zeyi daɗi.

Ɗakinta ta koma tana duba kayan da zata sauya, taji wayarta tayi ruri, rufe drowar tayi kana ta dawo kan gado ta zauna,
Sai da ta daidaita nutsuwarta kafin ta ɗaga wayar, daga cikin wayar Maryamah tace "amarya an mance damu, ko kira babu?"

Umma tayi murmishi na iya gefen baki kafin tace "haba Maryamah ni na isa in mance dake, ai da na zamo butulu"

Maryamah tace "hmm zaki iya tabbas, sbda wannan tafkeken gidan da kika mallaka komai ze iya shige miki duhu"

"Haba Maryamah ki dena wannan zancen, kinga zansa a tura miki da dubu goma yanzu, sai ki turo da lambar account"

Jikin Maryamah na rawa tace "tabbas alamomi sun nuna baki mance dani ba"

Cikin sauri ta turo mata da number account ɗin tare da sake kira tayi mata Godiya, Umma tace "kinga nikam ban iya tura kuɗin ba, zan bawa mai gadi ya kai a tura miki"

Daga nan Umma ta katse kiran.


Fasa ciro kayan tayi ta koma kitchen ta duba abinci, lokacin ta kusa tsotsewa ta dawo bedroom ta buɗe drowa ta ciro riga da zani wanda basu kamata ba, ta ciro ƙaramin hijab iya ƙirjinta tasa, kana ta dawo kitchen ta sake duba abincin ya dahu, ta sauke, ta rasa me zata sake dafa musu kawai ta kashe electric stove ɗin.

Lokacin da ta kammala komai har 11:am tayi,
Hakan yayi daidai da nocking ɗin ƙofa da taji, a tunaninta mutum biyu ne ko sama da haka, sai taga akasin hakan mutum ɗaya,
Cikin sakin fuska tayi masa sannu da zuwa, tare da nuna masa gurin zama, ta janyo table gabansa, kasancewar yana da ɗan girma yasa ta ajiye tiran abincin akai, tare da ɗauko drinks na kwalba kala uku ta ajiye da duk wasu abubuwan da tasan ana buƙata, sam ta kasa sakewa, Allah -Allah takeyi ya fita kawai.

Ringing ɗin da wayarta tayi ne ya sata miƙewa ta koma can dining ta ɗaga kiran,
Daga can Alhaji Lukman yace "wannan wanda yazo shine ogana kuma masoyina, duk wasu lamura nawa shine dan Allah karkisa muji kunya"

Umma ta leƙo ta kalli ogan nasa kafin ta koma da kanta ta katse kiran, bayan tayi masa alƙawarin baza'aji kunya ba, cikin rage sautin muryarta.

Ga mamakinta sai taga yaci abincin sosai, yasha lemun kwalba, kafin ya ajiye cup ɗin, yace "sunana Alhaji Abdussalam, da fatan mai gidan yayi miki bayanin koni waye?"

Fuskar Umma a sake tace "eh yace mai gidansa ne, muna godiya Allah ya saka da alkairi"

"Amin Alhaji Abdussalam yace, kafin ya kalli agogon Hannunsa yace "sai dai wani hanzari ba gudu ba, kinada masaniyar mijinki bashi da lafiya?"

"Eh"

Umma ta gyaɗa kai.

"Hakan baya damunki?, tabbas zai dameki, kamar ke mace mai aji mace mai kyan diri mace mai jini a jika mace mai zubin halitta irin taki, ace da auren Lukman kikayi tozali,"

Umma ta sunkuyar da kanta ƙasa, tana nazarin maganarsa,

Kafin ya sake cewa "yakai shekaru shida, yana fama da wannan cutar har ƙasar waje anje ba'a dace ba, sannan lokacin da ya fara maganin gargajiya, wani mutumi yace "Aljanu ne suka shafeshi, to gashi har yanzu beyi dacen magani ba"

"Akwai shawarar da zan baki, nasan zatayi miki amfani"

Duk da Umman batasan me yake shirin cewa ba, amma ƙirjinta ya fara lugude, sbda har zufa tafara yi.

Ya ƙara da cewa, "idan har kin amince zan aureki, in baki sadaki a hannun ki, sannan inyi miki kayan lefe, sannan in baki kyautar gida bayan haka zan biya miki Makkah a matsayin nayiwa Lukman kyauta,
Idan kikaƙi amin cewa da buƙata ta, tabbas zan kafa shedu in faɗawa kowa kin nemi nauyi lalata dake nikuma naƙi yarda, kinsan wane sakamako alhajin zai baki?, rabuwar wulaƙanci zakuyi nikuma inada ikon ajiye ki a gidana ko kinaso ko bakyaso".

"Dan Allah Alhaji kayi haƙuri wlhi wannan haramune ne, ya haramta a musulunci"

Da sauri ya dakatar da ita, tare da cewa "sati ɗaya na baki, zan aureki dole "

Umma tace "aure kan aure?"

Gyara zaman hularsa yayi, yana daga tsaye yace "nan da kwana uku zanyiwa Lukman transfern gurin aiki, zai koma ƙasar waje da aiki, zan ƙara masa matsayi ninki biyu sannan kema zai ƙara miki matsayi,

"Ki rubuta ki ajiye sai wata rana"

Yana faɗar haka ya fice.

Umma ta rafka uban tagumi, tare da fashewa da kuka, ta ɗaga hannu sama tana cewa "Allah ka kawomin mafita na shiga uku"

JUWAIRIYA House

Yau kwananta biyu a gidan Alhaji Al'amin

Soyayya yake gwada mata mai tsayawa a rai, kamar inda ya faɗa yau zeyi tafiya zuwa ƙasar da aka sauya masa a gurin aiki, London,


Hankalin Juwairiya ya tashi sosai, tunda ta shirya masa kaya take kuka, shima jikinsa yayi sanyi, cak ya ɗagata ya ɗora kan kujera tare da mannata da jikinsa, ya haɗe goshinsu guri ɗaya sannan tayi shiru, da yaga haka, hankalinsa ya kwanta, tana kwance akan doguwar kujera har ya shiga ya fito da kayan bata biyo shi ba,
Yana zuwa parlo yaga harda gyara kwanciya, tayi barci, da sauri ya ɗauki biro yayi rubutu ya ajiye mata ya fice,

Yana zuwa parking space ya ƙwalawa driver kira, cikin sauri drivern ya shiga mota shikuma Al'amin ya shiga backside suka wuce....


Aslamu alaikum masoya makaranta littafin MURAYU A TARE,
Book2&3 zai zo muku a paid Normal 300 vip 700

Munkusa gama book1 abinda nakeson cewa shine, inason ya zamo wanda sukeson littafin sun biya kudin su, domin muna gama book1 zamu shiga two ba tare da ɓata lokaci ba, da izinin Ubangiji, idan na gama book1 mutane basu gama biya ba, zamu dakata da posting sbda bana son na haɗa abubuwa biyu, ga typing ga adding.

Wanda suka shirya biyan kuɗi su tura ta nan. 3175689751 Zainab Habibu first Bank. Shedar biya ta wannan number 08141799224

Dan Allah kar ayi min Vtu Please idan kuma kati ne, hoton katin zaki ɗauka ki turomin

Ƴan Niger zasu tura da katin Airtel


Mom Islam
*💋MU RAYU A TARE💋*

Mom Islam


Book1

81-82

Duk da tashi ɗaya barci mai nauyi yayi nasarar ɗaukarta, hakan bai hanata farkawa ba, sakamakon wani mugun mafarki da tayi, da sauri ta sauko da ƙafafunta ƙasa, kafin ta miƙe tsaye tana yamutsa fuska, a tunaninta Al'amin yana bedroom ɗinsa, cikin rashin sa'a ta leƙa ko ina bata gansa ba, rai a ɓace ta ɗaga waya zata kirashi, sai ta fasa kamar wacce ta tuna wani abu,

Parlo ta dawo ta zauna akan kujerar da ta kwanta, kana ta kalli agogon dake manne a jikin bango, ƙarfe 11:am, sauke idon da zatayi idonta ya sauka akan takarda, a tsorace ta jujuya takardar sbda ya ninketa, a fili ta furta, "gaskiya idan nace na buɗe wannan takardar akwai matsala, karfa azo ya rubuta abinda zai dameni ne, barin ɓoyeta.

Jiki a sanyaye ta wuce kitchen domin samawa cikinta abinci.

Bikin Naeema da Mahbob ya rage saura sati ɗaya, abin mamaki, ko sau ɗaya Mahbob bai taɓa furta wa abokansa maganar aurensa ba, har kawo yanzu da lokacin bikin ya matso,
Da maraice Abba ya kirashi a waya, lokacin yana tare da Amani a wani gurin hutawa, suna tattauna abubuwan daya kamata su aiwatar a lokacin bikin,
Cikin lallashi Amani tace "bro abinda nakeso dakai shine, ka kwantar da hankalinka, idan da zuciya ɗaya take sonka zaka gani..."
"Please Amani ki rufe min baki, wace irin magana ne wannan, a halin da ake ciki ko maganar 5 minutes ban taɓa yarda munyi ba, sometimes wari ma take yimin, a hakan zamuyi zaman aure?"


Amani ta sunkuyar da kansa ƙasa, hawaye na bin fuskarta, cikin shesheƙar kuka tace "a tunanina da Ammy na da rai Abba bazai fara wulaƙantamu ba"

Mahbob ya kamo hannunta cikin marairaicewa yace "yanzu me kike ganin ya dace inyi?"

"Kayi haƙuri insha Allah a hakan zamu samo mafita"

Amani ta faɗa tana miƙewa tsaye,

Suna tafe a hankali suna magana, har suka kawo gurin motar Mahbob, ya jingina a jikin motar kana yace "ki sani zanbi shawararki, duk abinda ya biyo baya kece sila"

Cikin sauri ta dafe ƙirji tare da zagayawa mazaunin driver, shima ya shiga tayiwa motar key"

Sosai Abban yaji haushin ƙin ɗaga wayarsa da Mahbob yaƙi yi, har ya hassala, Batool ta matso tana bashi haƙuri, sannan ya sake kiran number Mahbob ɗin, jiki a sanyaye yakai hannu ya ɗaga tare da sallama, kalmar data fara fitowa a bakin Abba itace..

"Kanada hankali kuwa, har da zan kiraka kaƙi ɗagamin waya?"

Gaban Mahbob ya bada dumm cikin wani irin yanayi yace "Abba dan Allah kayi haƙuri"

Sannan Abban yace "nasa an gyara ko ina na gidanka ka sanarwa da yarinyar Bama buƙatar komai"

"Tom Abba"

Mahbob ya faɗa hawaye cike da idanunsa, da sauri Amani tasa hannu ta goge masa tare da cewa "karka damu wllhi wataran sai labari, abinda yafi bani mamaki da Abba bai wuce, komai ya dinga fifita wannan yarinyar a kanmu ba, sam yanzu baya ambatarmu ko kiran waya ka gani to maganar aure zeyi maka"

Har suka isa gida Amani na mita.

Yau kwanan Naeema ɗaya da komawa, Dady yayi farin ciki da auran Naeema sosai, kaf abokansa kuwa babu wanda bashi da labari, sannan suka kira ƴar tashi da mai Sa'a, mama kuwa tun yanzu take ta kiraye-kirayen waya, akan danginta suzo su tayata aiki,
Abinku da gidan da za'a huta, washe gari suka cika gida harda masu tambayo kwana goma a gurin miji.

Ana biki saura kwana biyar, safiyar talata, Huda sam taƙi cin komai, Aseela ta damu sosai, suka dinga tambayarta meya faru, sai tace musu "babu komai"

Sosai Amani ta tsorata da yanayin ta, da sauri ta ɗaga waya ta kira Mahbob, kan kace me sai gashi ya shigo, har yana mancewa da cire takalmi, cikin tausasa murya yace "Huda gayamin me akayi miki?"

Kanta a ƙasa tace "Anty Batool ce ta kwaso kayan wanki da yawa kuma tace inzo inyi mata girkin dare, wai zasuje wankin kai"

Mahbob ya riƙe ƙugu, a fusace yace "yaushe ta ganki?"

"Tun su anty Amani suna barci ta aiko wata yarinya ta kirani"

"Okay kice mata ni Mahbob nace bazakiyi ba, idan ta matsa miki kiyi mata jiƙa-jiƙa ina Worshing machine ɗin gidan?"

Huda tace "tace min kar in kuskura inyi dashi"

Amani ta dafe kumatu tana mamakin irin samun gurin da Batool tayi har takeyi musu iskanci haka.

"Aslamu alaikum wai Huda tazo inji anty Batool"

A hassale Mahbob yace "kice inji Mahbob bazata zo ba"

Amani ta kamo hannun yarinyar tace "Karki faɗi haka kinji beautiful baby zan siya miki ice-cream"

Yarinyar tayi murmishi kana tace "to me zance?"

"Kice kawai tana zuwa"

Yarinyar ta fice da gudu,

"Bro nasan nayi maka lefi na tari numfashinka, karka manta, danginta sun cika gidannan so kakeyi su tafi damu a baki?"

Shiru yayi bai ce da ita komai ba, sai ma shigewa ciki da yayi rai a ɓace,

Yarinyar na zuwa tace "wai tana zuwa"

Batool ta kalli ƙanwar mama da itace mahaifiyar yarinyar tace "wllhi Ummi kinga kisisinar da yarannan suke yi min?"

Ƙanwar mahaifiyar Tata tace "hamm ai yaran miji ruƙonsu sai me haƙuri wllhi koni nayi banji daɗi ba, ki godewa Allah matane kuma sun girma nan bada jimawa ba auransu za'ayi, lokacin ne zaki miƙe ƙafa kiyi abinda kike so"

Batool ta sauke ajiyar zuciya,

Dawowar Abba ne yasa Ƙanwar maman nata tafiya, Abba ya ƙirgo 5k ya bawa yarinyar kana suka wuce sunayi masa godiya,

A ƙofar shiga part ɗinsu Amani Batool ta haɗu da Huda zata wuce, Batool ta janyo mata wuyan hijab tare da cewa "ke har kinyi wayewar da zan aika a kiramin ke amma kiƙi zuwa?"

"Kuyi haƙuri anty wllhi aikana
End Ads