gida,
Iffat kam lafiya ta samu, sbda babu abinda bata ganewa na game da rayuwa, sai dai yawan surutunta ya ragu sosai.
NIGERIA
Tun ana saura kwana bakwai su dawo, dady ya sanarwa Hakeem da Hajiya babba, wani lokacin ma Iffat tana gaisawa da Hakeem idan dady ya kirashi, abinda Hajiya babba bata taɓa tsammani ba kenan, wato samun lafiyar Iffat, abin ya dagula mata lissafi,
A ranar da suka sanar mata da lokacin dawowarsu, ta shirya zuwa gidansu, cike da mamaki mahaifiyar Hajiya babba take kallonta, kafin ta amsa sallamar tana cewa "yaushe rabon da inji muryarki ko a waya?"
Hajiya babba ta fashe da kuka mai cike da makirci, kana tace "umma ina Fawziya?"
"Fawziya tana ciki auren ma ya mutu"
Hajiya babba ta dafe ƙirji kana tace "innalilahi wa inna ilaihir raji'un, wannan wane irin mummunan labari ne?"
Umma tayi shiru tana kallon yanayin Hajiya babba.
Koda ta shiga ɗakin tagumi tayi, Umma ta shigo kana ta zauna gefenta, cikin sigar lallashi tace "wai meke faruwa ne naga duk kin rame kin lalace tashi ɗaya Hajiya babba ta sake fashewa da kuka, a cikin kukan take cewa "yanzu alhaji baya Sona yafi son waccar shegiyar, ga wata y'ar tsintuwa da Hakeem ya samo aka kaita gidanmu, anyi cigiyar iyayenta har an gaji, dayake ciwon juyewar k'wakwalwa ne ya sameta, shine ya fitar da ita waje, har yanzu basu dawo ba".
Hajiya babba ta k'arasa maganar tana sake fashewa da kuka,
Umma ta matso kusa da ita kana tace "haba y'ata ki kwantar da hankalinki, wato yana nufin, har yar kwararo ta fiye masa na cikinsa, to wlh inaga akwai ayar tambaya akansa, kodai yarsa ce?"
"A'a Umma wlhi ba yarsa bace, nidai so nakeyi a kaini gurin wani malamin yayimin temako dan waccar shegiyar ta lashe masa zuciya sai abinda tace shi yakeyi"
"To ki kawantar da hankalinki idan har Ina raye saina share Miki kukanki, akwai dubu goma a gurina, Babanku baya gari, barin k'arasa aiki inzomuje gurin malam Mai turakar yasin wlhi idan kika amayar masa da duk matsalolin da suke damunki anyi an gama"
Hajiya babba ta share hawaye, tare da rungumo Ummanta kafin tace "Umma wlhi Ina alfahari dake".
Bayan Umma ta kammala aiyukanta ta d'auki hijabi da key motarta, Hajiya babba ta zauna mazaunin driver Umma ta zaro ido, tare da cewa "ni wlhi ban isa ba, kice lahira salamu alaikum, ace duk kudin mijinki har yanzu baki mallaki mota ba, ki duba ki gani motata ta uku kenan, ke ko d'aya baki ajiye ba"
Hajiya babba ta fito tana cewa "umma ai yanzu nasan abinda yafi mota ma zan samu insha Allah...
Ina mai bawa ma masoyana hak'uri, musamman akan rashin ganin posting kuyi hak'uri dan Allah insha Allah yanzu zamuci gaba.
Mom Islam 08141799224
*💋MU RAYU A TARE💋*
Mom Islam
57-58
Kai tsaye suka wuce gurin boka, wani ƙasurgumin jeji suka dinga tafiya, bakajin kukan komai sai na, tsuntsaye, riƙe da hannun juna suke tafiya har Allah ya kawosu gindin wata ɗirkekeyiyar bishiyar kuka, cikin ƙaraji da murya marar daɗin sauraro sukaji ance "ku koma da baya, sannan kuma bama son sallama"
Jikin Hajiya babba ya ɗauki kyarma, ta riƙe hannun umma gam tana cewa "Umma wlhi mu koma nikam bazan iya jure wari da tsawar nan ba"
Shiru Umman tayi bata kulata ba, har suka iso gurin bokan suna tafiya da baya, kana Umma taja hannunta suka zube a ƙasa.
"An gaisheka boka an gaishe da madugu an gaishe da hatsabibi"
Cikin jin daɗin kirarin yayi murmishi jajayen haƙoransa suka baiyyana, sai kuma ya turɓune fuska kafin yace "baku da matsala da maganina, duk wanda muka bawa sai ya dawo yayi mana godiya, dan haka ku kwantar da hankalinku, meke tafe daku?"
Umma tace "wlhi kishiyar yarinyata ce ta mallake mijin bayajin maganar kowa sai Tata, sannan akwai wata maiyyar yarinya da aka tsinto, yana mugun sonta"
A gaggauce boka yace "yanzu me kukeson ayi mata?"
Hajiya babba da sai yanzu ta samu bakin magana tace "inaso ya zamo maganata kawai yakeji, sannan ya zamo danginsa suna sona sosai, ita kuma yarinyar inason a sanya ya mance da labarin ta, sannan ya dinga ji dani kamar tsoka ɗaya a miya"
"Duk wannan zancen da kikayi, anyi an gama, ɗan gajere na jinki shine zeyi komai, amma kafin nan munason gashin kan ita kishiyar taki, sai kuma farcen Alhaji shima muna buƙata, sannan munason rigar yarinyar guda ɗaya"
Jikin Hajiya babba na rawa tace "ni yanzu ina zan samu waɗannan abubuwan daka ambata?"
Cikin daka tsawa yace "idan har kinason aiki dole kibi hanyoyin dana faɗa idan kuma bakyaso ku ɓacemin anan"
Umma tayi murmishin yaƙe cikin sigar bada haƙuri da kwantar da muryar,
"Dan Allah boka kayi mana rai, saboda inganci aiki irin naka shiyasa muka taho gurinka domin ka taimakemu"
Boka ya sheƙe da dariya, kana yace "na gama magana idan an samu abubuwan dana ambata ko yanzu kuka kawo, yanzu aiki zai wakana"
Umma ta riƙe hannun Hajiya babba kana ta fiddo kuɗaɗe dubu ashirin ta ajiye a gabansa, kana suka miƙe, suna tafiya da baya-da baya har suka iso gurin mota.
Koda suka shiga mota, Hajiya babba ta rafka uban tagumi kana tace "Umma a ina zan samo waɗannan abubuwan da boka ya ambata?"
Umma tace "haba kekuwa sai kace ba mace ba, idan har ke jinina ce wlhi zaki iya, kidena bani kunya"
Hajiya babba tace "to shikenan Umma zan jaraba in gani"
Sai bayan isha'i sannan ta koma gida,lokacin Hakeem ya daɗe dayin barci, sai da ta leƙashi sannan ta wuce ta kwanta babu batun Sallah, sai ma tunanin "ta yaya zata samo abinda boka ya umarceta?"
Da wannan tunanin barci mai nauyi yayi awon gaba da ita.
Tun bayan tafiyar Huda daga gidan Ummanta, ta koma sarin kayan sawa takalmi da kayan koli hoda janbak da sauransu, sannan ana kawo mata kayan ɗaki irin kamar idan auren mutum ya mutu ta siya, sannan tana siyarda maganin mata sosai, dan yafi ƙarfi ma a sana'ar ta,
Safiyar Asabar, bayan ta kammala gyara gida tayi abin karyawa, ta ɗaga waya ta kirawo ƙawarta, abin mamaki kuɗin da Alhji Auwal ya bata ba ƙaramin bunƙasa sukayi ba,
Bayan ta ɗaga Umma tace "Maryamah ya zakiyi min haka, kawai jiya wani mutumi yazo hira gurina?"
Wacce Umma ta kira da Maryamah ta tuntsure da dariya kana tace "wlhi gani nayi Kun dace shiyasa nayi masa hanya"
Umma tace "to duk ma ba wannan ba, kinsan kuwa yace da wuri yakeson auren, nida nafi shekara goma ban waiwayi dangina ba, to yanzu me zance musu?"
"Hhh Gaskiya ƙawata akwai ki da tsoro, a tunanina zaki fara nemo mana hanyar jin daɗi da huta kawai sai ki dinga wani tunani can, ko ance miki masu ɗaura miki aure babu su ne a garinnan? "
"Gaskiya ne Maryamah Allah yasa mu dace, ya kamata kizo gobe ki rakani siyo kayan ɗaki tunda ya fara maganar bikin bayason ya wuce sati ɗaya"
Maryam tace "ai komai zai tafi dai-dai insha Allah kedai kici gaba da tsuma kanki da magungunan nan naki masu rikita kwanyar mazaje"
Umma tayi dariya kana tace "sai kinzo"
Ta katse kiran.
Jiga-jigan magunguna ta dinga ci gaba dasha, sbda ta gigita sabon ango.
Washe gari, suka shiga kasuwa suka siyo gado da katifa da drowa da madubi, duk da na hannu ne, amma basu wani ji jiki ba, a ranar aka jera komai, da yamma sai ga Mahabob da Huda sun shigo da sallama, baki washe Umma take amsa wa, kana ta shigar dasu ɗakinta, bayan sun gaisa, Huda ta ajiye wa umma sabulai da omo tace Mahabob ne ya siya mata,
Godiya Umman tayi masa kana ta sanya musu albarka, ta tambaye su ya iyayen nasu,
Sukace l"afiya lau"
Mahabob ya miƙe tare da cewa "Huda zan jira ki a waje"
"To" tace masa kana ta mayar da hankali kan kayan ɗakin da taga an sauya"
"Umma masha Allah ɗaki yayi kyau"
Umma ta washe baki kana tace "wlhi Huda aure zanyi nan da kwana shida, shiyasa naketa gyara gida"
Huda tace "kai Umma shine ko ki gayamin?"
"Huda ba gashi kin sani ba"
Daga nan suka ɗan taɓa hira, huda tayiwa Umma sallama suka wuce, da niyar sai ana biki saura kwana biyu zata zo ta kwana.
Alhaji Lukman ɗan tijara, sunan wanda Umma zata aura kenan,
Mutum ne mai arziƙin gaske, sai dai yanada wasu ɓoyayyun ɗabi'u, wanda ba kowa zai san da haka ba sai wanda ya zauna dashi,
Zuwa dare har Umma ta kwanta rurin wayarta ya tasheta, murya irin ta mai barci tace "ranka shi daɗe Barka da dare"
"Barka amaryar Lukman ina fatan kina cikin ƙoshin lafiya"
Umma ta amsa da "lafiya lau Alhmdulilah"
"Dama inaso gobe idan Allah ya kaimu muje ki zaɓi irin gidan da kikeso ki zauna"
Da sauri ta tashi zaune, tare da cewa "ni harna gyara gidana wlhi"
"No ai bazai yiwu ba, dole a low cost zaki zauna G.R.A,"
Cikin farinciki tace "Allah ya kaimu goben"
Ya amsa da "Amin"
Alhaji Lukman ɗan tijara ya kalli abokansa dake zaune kusa dashi, kafin yace "mutuniyar ta faɗa"
Suka sheƙe da dariya mai sauti, ɗaya daga cikin abokansa yace "ya kamata ka sanar mata da larurar dake tare da kai, kar sai Kunyi aure a dinga kai ruwa rana"...!
Ayi haƙuri da rashin posting da yawa Please
Mom Islam
*💋MU RAYU A TARE💋*
Mom Islam
59-60
Sam baiji daɗin maganganun nasu ba, sannan ya alƙawartawa zuciyarsa bazai baiyyana mata ɓoyayyen sirrin dake lulluɓe a zuciyarsa ba.
Washe gari, breakfast kawai tayi sai ga kiransa ya shigo wayarta, ring ɗaya ta ɗaga cikin salon bariki tace "amincin Allah ya tabbata a gare ka Alhajin Allah"
Sai da ya lumshe ido, kana ya shafa tumbinsa, kasancewar daga shi sai gajeren wando yake zaune, kafin yace "tare dake, idan kin gama shiryawa zanzo mu tafi, kiga gidan da yayi miki"
"Eh na gama"
Ta faɗa tana miƙewa tare da ajiye wayar.
Cikin sauri ta gyara ko'ina kana ta shirya cikin atamfa ɗinkin riga da zani sai mayafi data yafa, kalar adon atamfar wato pink color, kana ta maƙala ɗan kunne ta fito hannunta riƙe da key na gidan, kana ta fito waje, lokacin da take kulle gidan Alhji Lukman ɗan tijara ya iso, horn ya danna kana yayi murmishi, kallon Umma yakeyi kamar ƙaramar yarinya, sbda tashi ɗaya tayi haske tayi kyau, musamman ma da ta shiga shafe-shafe.
Kai tsaye suka wuce G.R.A dake ɓukur park, a bakin milk color ɗin get yayi parking kana suka fito, key ya ciro a aljihunsa sannan ya buɗe ƙofar suka kutsa kai ciki,
"Masha Allah gida yayi kyau"
Umma ta faɗa daga shigarsu,
"Sai ma kin shiga ciki"
Koda suka shiga cikin gidan, a kan ɗirkekiyar kujera mai numfashi Umma ta zube, tare da sauke ajiyar zuciya kana tace "Alhji bani da bakin yi maka godiya, sai dai ince Ubangiji ya ƙara arziki da wadatacciyar lafiya"
"Amin ai kin wuce hakan, a gurina"
Sai da ya zagaya da ita lungu da saƙo na gidan, kana ya tambaye ta idan akwai abinda beyi mata ba ta faɗa,
"Yayi komai gunin sha'awa"
Umma ta faɗa jiki na rawa.
Daga nan suka wuce kasuwa, ya kashe mata kuɗi sosai musamman gurin siyan zannuwa da turaruka.
Daga nan suka wuce Shan Rufaida yoghurt, koda sukaje Umma bata wani yi kauyanci ba, saima burgeshi da take dad'ayi,
Daga nan ya dawo da ita gida, kaf kayan da suka siyo harda akwatunan yace ta wuce dasu gida.
Bayan ya ajiyeta ya wuce.
Tana shiga gida ta nemi guri ta zauna tare da ƙarewa kayan kallo.
Jiki na kyarma ta ɗauki waya ta danna number Maryamah, kamar jira take, ring ɗaya ta ɗaga tare da cewa "sai kuma na jiki shiru"
Umma ta kwashe da shewa kana tace "hamm Alhji ya kashemin kuɗi, da kinada halin zuwa da kinzo kin kashe ƙwarƙwatar ido"
Maryamah ta gigice tare da cewa "wlhi ganinan zuwa ko zan sami wani abu"
Lokacin da Maryamah tazo ana kiran sallahar azhar, ta samu umma na sallah, bayan ta idar ta shafa adu'a kana ta kalli Maryamah tayi murmishi kafin tace."ƙawata kwaso kayan a kan gado"
Jikin Maryamah na rawa ta kwaso kayan, tare da cewa "kai-kai ƙawata Allah ya yanke miki wahala, gaskiya irin waɗannan alhazan abin riritawa ne, gaskiya ki riƙe shi gam ƙawata"
Maryamah tace "haka akeso amma a shawarce ya kamata ki je garinku saboda kinsan aure ba abin wasa bane, dalilin...."
Cikin daka tsawa, Umma tace "bakisan komai a kaina ba bakisan kowa nawa ba, dan haka bana buƙatar kowa ya sani"
"Haba Umman Huda, ya ina baki muhimmiyar shawara kina kaucewa, bakya tunanin ta dalilin ƙaryar waliyai da zakiyi masa idan ya gano gaskiya abin bazaiyi kyau ba?"
KANO•• Ƙauyen ƴan yakuba
Garine wanda ya kasance ƙauye sosai, yawancin abinda sukeyi shine noma da kiwo, kowanne magidanci taƙamarsa noma da kiwo,
Gidan malam Ado, gidane mai ɗauke da mata biyu, koda yaushe basu da aiki sai masifa, duk da dukkansu babu wacce ta taɓa aihuwa, amma masifa taƙi ƙarewa a cikin gidan,
Hansa'u itace babba sai Saratu ita kuma itace amarya, hansa'u ta kasance mace mai haƙuri da kawaici, yayinda Saratu ta zamo gagararriya a cikin gidan, shekararsu biyar da auren Saratu, ya shawarcesu akan zai koma zuwa Jos cirani, dukkan su sunyi na'am, Wase Gari kuwa Saratu taje gidansu ta sanarwa mamanta maganar da malam Ado yayi, cikin rashin amincewa da tafiya da Saratu, tace "wlhi da ke zai tafi, ƙarya ne, tashi muje gurin baba insha a anyi an gama"
Saratu ta miƙe tare da yafa zanin da ta luluɓa kana suka wuce gurin malam wato baban mamanta, suna zuwa maman nata ta isar masa da duk abubuwan da suke so, kana suka kwashe ƙarya da gaskiya suka gaya masa,
Yayi musu alƙawarin kawar da hankalin jama'a akan tafiyarsu, sannan aka sanya masa tsanarta a zuciyarsa. "ammafa tanada juna biyu harna wata uku"
Malam ya faɗa yana kallon Saratu, Saratu ta zaro ido tare da dafe ƙirji kana tace "wlhi sai na kashe abinda ke cikinta ko ta haisheshi"
Daganan suka dawo da ƙulle-ƙullen magunguna, Saratu ta dawo gida, bayan sati ɗaya, abubuwa suka fara faruwa, kama daga kaf danginsa abokan arziƙinta da ƴan uwanta duka suka tsaneta, ko ina Hansa'u ta shiga sai dai a dinga kyararata tare da hantara, hakan yasa ta dena fita ko ina, sai alwalah da wanka ne yafe fito da ita, abinci kuwa sai dai idan almajiri ya shigo ne saratu zata zuba abincin ya miƙa mata,
Sosai Saratu ta zamo tauraruwa mai haska ko ina, duk wannan gwagwarmayar da akeyi, mahaifiyar Hansa'u tayi tafiya garinsu sati Uku kenan bata gida, bayan ta dawo ta samu mummunan labari game da ƴarta Hansa'u, itakam asirin beyi tasiri a kanta ba, sbda tayi kuka kamar me,
Kwanan mahaifiyarta biyu da dawowa su Saratu suka tafi Jos,
Koda ta kawowa Hansa'u ziyara ta sameta tana kuka, ta tambaye ta lafiya ta sanar mata su malam Ado sun tafi sun barta, tana kuka take maganar,
Maman ta dinga rarrashinta tare da sanar mata, inhar Allah ya sauke ta lafiya, bayan ta yaye zata bashi yaronsa, idan namiji ne, idan kuma mace ce Tom"
Da wannan shawarar suka koma gida, mamanta taci gaba da taimaka mata.
Sun sauka lafiya a Anguwar Dogon agogo, dama ya riga da ya kama gida, kai tsaye shiga sukayi tunda mukulin gidan yana hannunsa, sukaci gaba da rayuwa cikin so da ƙauna, baya ganin lefinta sam ko me tayi masa, sannan ko aiki yaje ya dawo zai zazzage mata aljihu su raba kuɗin dai-dai...!
Dan Allah ayi haƙuri zafa mu shiga typing da yawa🤣insha Allah amman yau anguwa naje, sannan ina jiran shar'i..
Ayi haƙuri da typing error
Mom Islam
*💋MU RAYU A TARE💋*
Mom Islam
Book1
61-62
Acan ƙauye Hansa'u na aihuwa aka raɗawa yarinya suna Huda, wato sunan mahaifiyar malam Ado, shekarar Huda ɗaya a duniya Hansa'u ta rasu, sakamakon ciwon nono wanda ya zame mata cutar ajali,
Sai da akayi kwana bakwai sannan malam Ado yazo gaisuwar rasuwa, mahaifiyar Hansa'u ta damƙa masa huda a hannunsa, yayi magiya akan su barta zai dinga aiko da kuɗi, ai mahaifiyar Hansa'u taƙi yarda, washe gari dole ya dawo da Huda Jos.
Saratu na murna mijinta ya dawo, kawai ta hango yarinya a jikinsa, cikin yamutsa fuska tace "mezan gani ƴar wa ka kwaso mana?"
A tunaninsa murna zatayi tunda bata taɓa aihuwa ba, sai yaga akasin hakan, ta murtuke fuska tana tuhumarsa,
"Yarinyar Hansa'u ce da ta mutu ta bari"
"Toni ina ruwana da mutuwarta wannan kai ta shafa, nidai kasan ba ƴar raino bace ko?"
Cikin lallashi ya siye zuciyarta tare dayi mata alƙawarin siya mata kayan ɗaki,
Haka huda ta taso cikin rayuwa marar daɗi ga tsangwama da kyara da duka, har Allah yasa ta girm, tun tana da shekaru goma Saratu take ɗora mata tallah, Huda nada shekara goma sha daya malam Ado ya rasu, yafuta gurin aiki sai dawowa akayi da gawarsa,
Saratu tayi kuka sosai, duk da bawai yana nunawa Huda kulawa bane, amma hakan bai hanata yin kuka ba.
Bayan rasuwarsa, Saratu taci gaba da ɗorawa huda tallar shinkafa da miya, a haka har ta ƙara shekaru biyu, shine har kawo yanzu da Allah ya haɗata da Mahabob.
Back to story
Bayan kwana uku da yin maganar sistern Batool, Abba ya kira Mahabob a waya, kasancewar lokacin 12:pm yana barci bai ga kiran Abba, wayar sai ringing take, kasancewar a silent take.
Sai 12:20pm ya farka, ya kunna haske wayarsa, ganin miss call ɗin Abba hankalinsa ya tashi, ɗaurayo baki kawai yayi ya fito zuwa part ɗin Batool.
Da sallama ya shiga, suna parlo Abban na breakfast, Batool ta amsa fuska a sake, kana ya nemi guri ya zauna, cikin girmamawa yace "Abba kayi haƙuri lokacin da ka kirani ina barci"
Sannan ya gaishe da Batool ya gaishe da Abban,
"Babu damuwa, dama inason in sanar maka nayi maka mata ne, duba da yabawa da hankalinta da nayi sbda yarinyar nitsatsiyace, kuma nasan bazaka bani kunya ba"
Sam zancen beyiwa Mahabob daɗi ba, kasancewarsa mai biyayya yasa ya kawar da damuwar da takeson lulluɓe masa fuska, yai ƙoƙarin aro murmishi kana yace "Abba godiya nake"
Abba yace "wato Mahabob nidai babu abinda zance dakai sai godiya, sbda biyayya kam kanayi min, hakan yasa na baka kyautar Company ɗina na cikin gari"
Batool ta zaro ido ba tare da kowa ya sani ba, sannan tace "godiya yake Alhaji"
Abba ya ƙara da cewa "yarinyar ƙanwar Batool ce, sannan yau zatazo gidannan sai ku gana"