x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 5 - MU RAYU A TARE book 1

  • 12001 words
  • 15000 words
  • Out of 62845 words

Category: Love Stories

Views 92

09 Aug 2025
Start ads
After Image Ads
nikuma kullum in dingayin typing insha Allah mai yawa

Ana wata ga wata muje zuwa...

Mom Islam
*💋MU RAYU A TARE💋*

Mom Islam

*Wanda suke nema daga farko suyi min magana*👇
http://wa.me/08141799224

21-22

A gurguje suka gama shawar-warin inda za'akai Iffat ba tare da sanin kowa ba, cike da ƙwarin guwaiwa Hajiya Fawziya tabar gidan,
Yau kam da wuri Hakeem ya dawo daga gurin aiki, duk da cewar ba wani aiki yakeyi ba, amman dai dady ya tsaya masa akan koda yaushe ya dinga zuwa yana ganin abinda sukeyi,
Yana shigowa kai tsaye ɗakin Hajiya ƙarama ya wuce, murya ƙasa-ƙasa yace "Hajiya na dawo banga Iffat ba ko tayi barci ne?"

Sai a lokacin ta dawo daga dogon tunanin da takeyi, kafin ta juyo tace "ka duba É—akin hajiyarka tana nan, idan ka ganta ka kawomin ita"

"Tom"

Yana tafe yana waƙe-waƙensa har ya iso bedroom ɗin hajiyar tasa, kalaman da yaji Hajiyar tasa tana ambata ne yasa hankalin Hakeem mugun tashi, bai yi aune ba yaji tana ci gaba da cewa "nifa tunda na ganta a hospital nasan Alhji zai bata muƙami da daraja irin wanda zai bawa Hakeem, kinga kuwa ya kamata in ɗauki mataki tun yanzu, karki damu gobe insha Allah zanzo gidanki, domin muyi shawarar inda lamuran zasu kasance"

Hankali a tashe Hakeem ya kalli ƙofar ɗakin hajiyarsa kafin ya waiga yaga babu kowa, a hankali ya juya tare da toshe bakinsa ya nufi ɗakinsa, yana shiga ya faɗa kan gado, tare da wurgar da ƴar ƙaramar leda wacce ke ɗauke da chocolate da biscuits a ciki, bai damu da zubowa kan tails da sukayi ba, ya tura hannu cikin gashin kansa wanda ya kasance baƙi wulik, irin mai kwanciya ne kamar anyi masa shampo.
Tambayar da yakeyiwa kansa, shin dawa Hajiya take yin waya?"

Bashi da mai bashi amsa, kana kuma baya fatan hajiyar tasan yaji duk wani ƙulli da take shirin yi akan Iffat, dole ya fara ƙoƙarin kawar da fushinsa, ta hanyar miƙewa ya sha banɗaki ya kulle kansa, a hankali ya ɗago hannunsa tare da kallon agogon dake ɗaure a tsintsiyar hannunsa, ƙarfe 5:20pm na yamma, kafin ya mayar da kallonsa ga mudubi yana ci gaba da tattaro sumar kansa.

"Babana.! Babana..!"

Hakeem naji hajiyar nayin nocking amma yai banza da ita kamar beji ba, sai da tayi sau uku sannan yace "ina toilet"

"Okay zan duba girki a kitchen koda zaka nemeni"

"Iffat É—in fa?"

Hakeem ya faÉ—a a hankali.

Cikin sanɗa ya buɗe ƙofa tare da wucewa ɗakin hajiyar, sai da ya tabbatar da babu mai ganinsa, kafin ya tura ƙofar, ya samu babu Iffat sai wayar Hajiyar, cikin sauri ya cire code ɗin jiki, kasancewar sunansa ne a jiki, kafin ya duba gurin da tayi kira ɗazu,  number sister Fawziya  ya gani a farko, cikin hikima da dabara yayiwa Hajiya Fawziya Text massage, kamar haka,
"Kiyi haƙuri ƙanwata yanzu Alhji ya shigo yacemin zamu fita anguwa gobe bazan samu zuwa ba"

Hakeem ya tura saƙon,

Saƙon yana tafiya sai ga kiran Hajiya Fawziya, Hakeem ya rage volume, tare da katse kiran, tabbas taji haushi sosai, saboda dama ba wani shiri suka cika yi da hajiyar ba, sai dai idan tanaso ta yagi wani abun, a jikinta, wanda ita hajiyar har yanzu ta kasa gane hakan.

Kamar Wanda ya tuna wani abu, sai ya miƙe ya dawo ɗakinsa ya kwanta, duk da cewar yasan kwanciyar yamma bata da kyau hakan ya kwanta.

Yana tsaka da tunani yaji ana nocking ɗin ƙofar ɗakinsa, cikin ɗaga murya yace "waye?"

"Nice,  Hajiya ce take kiranka tana kicin"

"Tom ina zuwa"

Hakeem ya faÉ—a yana mita..


Tunda mutumin ya yasar da ita a gurin bola, take ta wani yage-yage, ga duhu yayi, a hakan duk wanda ya santa da yarinya zai iya gano damuwa akan fuskarta, wanda hakan yasa idonta ɗaya keta fitar da hawaye,  da sauri ta miƙe tare da rugawa da gudu tana surutai, babu wanda ya kulata, bare ya tausaya mata.

Lokacin anyi sallahar magriba da isha'i duhu yayi sosai, sanyin iskar da akeyi ne, tare da gagarumin hadari kamar na ɗazu, ya sake haɗowa, ta rasa mafaka sbda idan ka lura da ita ba wani gani takeyi sosai ba, tunda babu haske a garin, sai ƙamƙame jikinta takeyi tana rawar sanyi haƙoranta na kaɗawa, a hankali ta tsagaita gudu tare da shiga irin ginin nan wanda ba'a rufa masa kwano ba, tashi ɗaya ruwa ya fara zubowa kamar da bakin ƙwarya, duk da ta rakuɓe a jikin ginin hakan bai hana ruwa dukanta ba, sosai ruwan ya jiƙata ga wani masifaffen zazzaɓi daya dirar mata tashi ɗaya, acan ƙasam zuciyarta tana kewar ƴarta Iffat, ba magana takeyi ba bare intayi a gane, koda tayi maganar ma babu mai fassara mata idan har ba Iffat ɗin ba, wani irin cakuɗin yare takeyi wanda kome tace "Allah yana sanar da Iffat, duk da ruwan ya jiƙata sosai hakan bai hana idonta na dama ci gaba da tsiyayar da ƙwalla ba, ga wani fizge-fizge da soshe-soshe da takeyi tare da rawar sanyi, har har ruwan ya ɗauke tana rakuɓe a gurin,  a hankali ta ɗaga kanta sama, taga haske ya gauraye ko ina, alamun an kawo wutar nepa, ta miƙe jikin nata na karkarwa ta fara zagaye ginin, can ta hango leda a ƙulle, da sauri ta isa gurin ledar tare da kuncewa, tsarsaman abinci ne wanda mutane suke wurgowa idan ya lalace, ta gyara bakin ledar har ji take kamar ta tura har da ledar tsabar yunwa, hannu baka hannu ƙwarya take cin abincin, tana gamawa ta suɗe hannunta tare dayin gyatsa, ta nemi  guri ta kwanta, ƙafarta ɗaure da gora.

"Aslamu alaikum.. ina mutan gidan?"

"Wa'alaikumussalam, oyoyo Inna sannu da zuwa"

Goggo ta taso daga wanke-wanken da takeyi, tare da ɗauko tabarma dake jingine a bayan ƙofar ɗakinta ta shimfiɗa wa Inna, sanin innar bata shiga ɗakinta.

Bayan sun gaisa tayiwa Goggo jajen mutuwar auren Hajara, Inna ta gyara zama, kafin tace "arziƙi yana binmu har gadon barcinmu"

Cikin rashin fahimta Goggo tace "ban gane ba Inna wani abu ne ya faru?"

"Eh to, wlhi wata yarinyar maƙotanmu ce, zata yiwa Hajara hanyar zuwa ƙasar waje aiki, shine nace bazanyi ƙasa a guwaiwa ba gurin zuwa sanar dake"

Goggo ta jinjina kai, tare da cewa "Inna ke bakya tsoron wata matsala ta ɓullo nikam ina tsoro wlhi, Hajara ko Kano bata taɓa zuwa ba, bare ƙasar waje"

Inna ta rufe Goggo da faÉ—a, harda cewa, da kinga alkairin da Hassana ke samowa wlhi bazaki kushe alkairin da na nufoki dashi ba, amma baki da hankali, mijin naki ya kori Æ´arki kika barshi, bayan yanzu ga dama tazo miki, inda zaki nuna masa ruwa ba sa'an kwando bane, amma kin tsaya ni kina tijarani"

Har ga Allah Goggo bataji daÉ—in shawarar da Inna ta kawo mata ba, "amma akwai Allah"

Goggo ta faÉ—a a zuciyarta, tare da sauke nannauyar ajiyar zuciya.

"Na'amince, amma a ina za'a samo kuÉ—in tafiyar, nikam sisi bana magani nasan koda kayan Hajara aka siyar duka kuÉ—in bazasu isa ba"

"Habawa ai Hassana Æ´ar albarka ce, tace zatayi komai, inyaso idan aka samu abinda ake nema sai ta cire a ciki"

Inna ta faɗa tana miƙewa tsaye.

"To Allah ya shige mana gaba, yaushe ne tafiyar?"

"Nan bada jimawa ba, ai hajaran ma zatazo"

Daga nan sukayi sallama Inna ta wuce.

Goggo ta dawo kan tabarma tare da jingina da bango tana tunanin tafiyar Hajara, tayi nisa a tunani sosai ta tuna da kayan miya dake ajiye a kicin, a hankali ta miƙe tare da nufar kicin ɗin tare da share hawaye, a fili tace "Akwai Allah"

Cikin tsananin buƙatuwa tsohon ya runtse ido yana cewa "yauwa ƴar albarka, shafa ta a hankali inda saƙon zai isa inda ake so, Huda taci gaba da taɓa masa idanunta na zubar da hawaye, kan kace me har ya fara shirin yaye mata mayafin jikinta, tunda har ya kai hannunsa saman ƙirjinta, a hankali murya a sanyaye tace "sai ka bani kuɗi"

Jikinsa na ɓari sbda ya gama rikicewa da abin da Huda takeyi masa, ya miƙo mata dubu ɗaya, kana yace "to ciremin mayafin, Huda tayi kamar zata cire mayafin ta miƙe ƙafa kamar me shirin yin wani abun, shikuma ya kwanta a rigingine, huda ta miƙe da sauri, tare da zubawa da gudu har tana faɗuwa, batasan ta fasa baki ba sai da takai ga gurin kayan abincinta, sannan ta shafo bakinta dake yi mata zogi, tama kasa kuka, farincikinta kuɗin da ta samu, tayi canji tasa kuɗin daya ɓata ragowar ta ƙulle a gefen zani, ta ƙarasa bakin titi ta tari mashin zuwa anguwarsu.

Washe garin safiyar Litinin an tashi da sanyi mai shiga jiki, ƙarfe 8:pm, Hakeem ya shigo ɗakin Hajiya ƙarama da sallama, tana zaune hannunta riƙe da ɗan ƙaramin cup wanda yake ɗauke da zuma, ta amsa tare da cewa "Hakeem bismillah"

Ƙarasowa yayi tare da risinawa ya gaishe da Hajiya, kafin ya leƙa fuskar Iffat dake barci cikin kwanciyar hankali, duk wanda yaga inda take barcin zai tabbatar da lafiya tana sake samuwa,

"Hajiya Iffat har yanzu bata tashi ba?"

"Ai Iffat tunda ta tashi cikin dare tasha tea ta koma barci"

Hakeem yayi murmishi tare da sake leƙata yana ci gaba da murmishi.

Hajiya ƙarama ta fice, sbda yau itace a kitchen,

A hankali yaje ya shafi gefen fuskarta tare da kamo lallausan hannayenta yayi musu kiss kafin ya tallafo kanta yana wasa da jelar kitso na kalaba, yana wasa dashi, kamar wanda ya tuna wani abu, a hankali yayi baya yana ci gaba da ƙura mata ido,
Sai kuma ya fice da sauri.

Kai tsaye bedroom É—in dady yaje, cikin sa'a ya samu dadyn a zaune da jarida a hannunsa, bakinsa É—auke da sallama ya shiga kafin dadyn ya amsa masa, yana cewa "banga ka shirya bane, ko yau kana hutu ne?"

Kawar da zancen yayi ta hanyar cewa "Dady dan Allah ina roƙon alfarma a gurinka"

Jikin dadyn a sanyaye ya kalli Hakeem, sbda Hakeem baya taɓa roƙonsa wani abun har sai dai in ya kasance mai muhimmanci sosai ba na wasa ba,

"Ina jinka Hakeem, ka faÉ—i koma meye bakada matsala"

"Dady ina ganin kamar idan aka fitar da Esha US zata iya samun lafiya"

Dadyn ya nisa, tare da ƙurawa Hakeem ido kafin yace "insha Allah zan duba inga abinda ya dace sai ayi, abinda yake yimin ciwo shine har yanzu babu labarin danginta"

Hakeem ya sunkuyar da kansa, sam ya kasa cewa komai

Bayan kwana biyar da zuwan su Inna gidan Hassana, kasancewar koda yaushe Hassana tana tare da Hajara yasa, suka dinga zirga zirgar yin su hoto da duk wasu abubuwa da ake buƙata, kasancewar itama hassanar tana da na gaba da ita a harkar,
Ana saura kwana biyu tafiyarsu, Hajara taje gidansu tun safe sai yamma ta dawo, duk zaman firar da sukayi ita da Goggo duk akan ta riƙe mutuncinta tayi abinda ya kaita, ta kiyaye cin abinda ba nata ba, kana ta kiyaye lokutan sallah kar neman abin duniya yasa ka mance da ibadarka,

Da kuka suka rabu, Goggo kam tace ta yafe wa Hajara duniya da lahira, kana kuma tace "bazata iya zuwa suyi sallama ba, Allah ya tsare".

Goggo taji daÉ—i da Baban Hajara baya nan bare yaji labari a gari, tunda shi ba waya ce dashi ba, sai yana son magana da ita, yaje gurin masu sana'ar kiran waya, ya kira su gaya masa minutes É—in da yayi ya biya su.

Washe gari, suka kammala shiri, Inna ma tayi mata faɗa sosai, jikin Hajara yayi sanyi dan har ta fara tunanin ko ta fasa ne, Inna sai ƙara mata ƙwarin guwaiwa takeyi....!

Ayi haƙuri kwana biyu an jini shiru, wanda sukayi comments ban yi musu magana ba suyi hakuri abubuwanne sunyi yawa, masu nema daga farko suyi min magana

Mom Islam

*💋MU RAYU A TARE💋*

Mom Islam

_Arewabook@momislam11_

23-24

Cikin hukuncin ubangiji jirginsu ya sauka a Libiya,

Taƙaitaccen bayani akan ƙasar Libiya.

Mutunen Libya sun kai adadin 6000,000 a sahile a arewacin kasar kabilolin Libya su ne, larabawa, barbarawa, tubawa karaglawa ( hadin turkawa da larabawa ), Buzawa da 'yan tsurarun ( hausawa da bare-bari ).

harshen larabci shi ne harshen kasar, larabcinsu yana da bambanci da sauran na kasashen larabawa kuma da akwai harsuna da yawa masu bambancin harshen ( Amazik, Buzanci tubanci da harshen Hausa ) shi ne harshen kasuwanci a birnin sabha da ke a kudancin kasar .

katafaren gida  ne, wanda idan kaga gidan zaka ɗauka ba a duniyarmu yake ba, sbda tsayawa misalta kyawun gidan zai iya zamowa ɓata lokaci, gidan babba ne, kai kace gidan mutane da yawa, a cikin gidan ko muce parlon wanda anan Nigeria, muke kiransa da mu haɗu a parlo,
Cikin isa da ƙasaita yake saukowa daga steps, daga yanayin fuskarsa idan ka kalla zaka tabbatar da koshi waye, shahazad kenan, da sauri ya ƙarasa saukowa kamar wanda ya tuna wani abu, kafin ya tako cikin taƙama ya zauna kusa da Mona, yana zama ta fashe da matsanancin kuka mai tsuma zuciya, kafin ya tallafo haɓarta, cikin cold voice ɗinsa wace ko yaushe yake using ɗinta a gurin Mona, yana ci gaba da  shafa haɓar tata yace "ƴan mata barka meyasa kika dawo parlo bayan kinsan ina tsananin buƙatarki a kusa dani?"

Jikin Mona yana karkarwa, takai lallausar hannunta ta share hawaye tare da, É—ago kanta fararen idanuwanta suka sauka a nasa kyawawan idanun, bakinta ne ke motsi amma sam ta kasa furta koda É—aya, "faÉ—i abinda ke bakinki"
Murya na rawa tace "Please ka mayar dani gurin iyayena basu da kowa sai ni, a halin yanzu suna da buƙatata"

Ta ƙarashe maganar tana tura yatsunta cikin sumar kanta, wacce ta kwanta har gadon bayanta,

"Mona, kona mayar dake bazaki taɓa canzawa a matsayin mata ta ba, ko kin mance munyi aure kuma da yardarki da yardar iyayenki, kece zaɓina don haka ki kwantar da hankalinki"

"Ni bazan iya zaman aure dakai ba, karatu zan koma"

"Zan mayar dake makaranta tunda kinaso amma ki yarda keÉ—in mata ta ce"

"Ya isaaaa.."

"Karka sake kirana da matarka, mugu azzalumi"

Da sauri shahazad ya dunkule hannu zai kai mata naushi, ko me ya tuna sai ya fasa ya dafe kansa, tare da miƙewa,

Har ya yi taku biyu, wayarsa tayi ring, a hankali ya zaro wayar daga aljihu tare da karawa a kunnensa,
"A zubasu a gidan hutawa ta"

Mona ta runtse idanunta, tashi ɗaya hawayen da take ƙoƙarin ɓoyewa suka sake sulalowa, a hankali ta miƙe tare da juyowa ta kallashi, cike da nuna yanayi na sha'awarta yai saurin miƙewa ya kamo hannunta, a hankali ta faɗo jikinsa, cikin nuna masa ƙarfinta ta fara fizgewa tana tureshi, kai kace mai neman wani abu ya fara lalubarta yana kashe mata ido.

LIBYA ANGUWAR (Sabha)

Wata hamshaƙiyar mota mai numfashi ce tai parking a wani haɗaɗden gida, ga mamakina na tsaya ganin suwaye a cikinta, Hassana da Hajara na gani ko wanne hancinsa sanye da takum kumi, har shima balaraben dake driving ɗinsu,
Duk da jar fatarsa hakan bai hanashi jin Hausa ba, kai kace bahaushe, "bismillah ku shiga gidan a buÉ—e yake"

Hassana tayi gaba Hajara na Bin ta a baya suka ƙarasa cikin gidan, subhanallah kuzo kuga tsaruwar gidan, ni kaina tsayawa kallo nayi, ga mamakina sai naga an shigo dasu gidan su Shahazad, tambayar anan shine ƙofar guda biyu ce?"

Dan ta baya aka shigo dasu, fentin kuma ba irin na gaban bane,

Da farko driver ne ya shiga ya nema musu umarnin iso kafin ya dawo ya sanar musu zasu iya shiga.

Shima Shahazad É—in yaji Hausa sosai,

Suka shigo bakunansu ɗauke da sallama, Mona tai ƙoƙarin kawar da fushinta ta hanyar amsa musu sallama, kafin ta dawo da baya ta nemi guri ta zauna, "barkanku da zuwa"

Hajara ta ƙurawa Mona kallo a zuciyarta kuwa cewa take "ina mutanen gidan ko sunyi tafiya ne? dalilin tambayarta shine, taga Shahazad babban mutum sai dai kuɗi ya ɓoye duk wani girma da wani abu na ganin muni a tare dashi, sai dai ma kaga kyawunsa, ita kuma Mona a ƙalla batafi shekaru 12yrs ba, a duniya, Hassana ta taɓo Hajara tare da ƙifta mata ido alamar ta rage kallo, zasu iya samun Matsala,

Shahazad ya ƙaraso cikin izza ya zauna kusa da Mona yana mai riƙe hannunta, kafin yace "masha Allah na gane ki, kece Haseena ko?"
Shahazad ya nuna Hassana, cikin rawar jiki Hassana tace "ga sister na sunanta Hajara"

"Masha Allah Hajar Barka da shugowa rayuwar Shahazad, ke Haseena mun riga da munyi magana da Abdul Alee akan can zakiyi masa aiki, ita kuma sabuwar zuwa zatayi mana aiki anan gidan"

Hassana tace "Nagode sosai oga, alkairinka a gareni bani da bakin yi maka godiya"

Mona kuwa tana zaune ta zuba musu idanu.

Sun kai wajen ƙarfe 5:pm, kafin wata mota ta dinga horn a ƙofar gidan, bayan masu gadi sun buɗe mata motar ta shigo, mamalakin motar ya aika ɗaya daga cikin securityn gidan domin ya kira Hassana, cikin sa'a sai gasu sun fito har da hajara, kafin su ƙarasa can gurin motar, Hassana tace "Hajara wlhi idan kika kiyaye dokokin mutumin nan ba ƙaramin hutawa zakiyi ba, keda talauci sai dai kiga anayi, amma fa kiyi ƙoƙarin riƙe sirrukansa saboda mutum ne mai haɗarin gaske, wlhi tallahi ya kashe mutum ba wani abu bane a gurinsa, duk ƴan ta'addan da kikaji ana labarinsu a ƙasar Libya to da sa hannunsa a ciki, ɗan cocaine ne na bugawa a jarida, sai dai duk iskancin da yakeyi baya Wasa da sallah, wannan yarinyar da kika ganta matarsa ce, Kuma sirrinsa"

Hajara ta dafe ƙirji, duba da inda taga Hassana tana maganar tana waiwayen bayanta.

Sukayi sallama, yayin da suka iso gurin motar, dama sunyi musayar number waya,

Hajara ta dawo jiki a sanyaye, sosai tsoron Shahazad ya fara shigarta, a zuciyarta tace "ashe suma suna yin auren wuri kenan, banda rashin tausayi ace ƙaramar yarinya ta auri wanda yake rikiɗewa saurayi da tsoho, wlhi wannan mutumin zaiyi shekaru 50yrs"

Kafin ta ƙarasa ciki bakinta ɗauke da sallama.

Har yanzu yana zaune a parlon banda Mona da ta gudu ta ƙulle ƙofarta,
Yana ganin shigowar Hajara yace "zaki iya zama sbda in gabatar miki da dokoki da tsarukan gidan, sannan ki bani hankalinki duk abinda na faÉ—a yanzu bazan sake mai-maitawa ba, sai dai muje ga abubuwa na gaba, cox bani da isasshen time da zan tsaya surutu".

Cikin ladabi da girmamawa Hajara tace "Nagode insha Allah zan kiyaye koma meye"

Kafin ya fara magana ya cillo mata bandir-bandir na kuɗinsu nacan, sannan yace na farko bana son munafurci, idan har kika sake koda kuskure kika munafurceni komai yana iya faruwa, Mona matata ce, inaso ki zamo uwa a gareta bana son a dinga takura mata ko ɓata mata
End Ads