x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 19 - MU RAYU A TARE book 1

  • 54001 words
  • 57000 words
  • Out of 62845 words

Category: Love Stories

Views 105

09 Aug 2025
Start ads
After Image Ads
ya karɓa, ya ɗaga ƙoƙo yana surkullensa a ciki, kana ya ajiye ƙoƙon da a halin yanzu yazo cike da magunguna da laya a ciki,

Ƙullin magani ya ɗauko kana yace "wannan ki tabbatar kin sanya mata a cikin abinci"

"Wannan laya ce, ya zamo koda yaushe tana kanki, kokuma kiyi kitso da ita, ma'ana ki binne ta a cikin gashinki, ga wannan maganin kin ganshi, ba a ko'ina zaki sameshi ba, shi wannan ko fesawa yarinyar kikayi ko kuma kisa mata abinci taci, shikenan kamar inda naji kunyi shawara zata zamo biri rayuwarta a jeji zata koma yi"

Rai fess suka dinga yi masa godiya, Umma ta miƙa masa bandir ɗin ƴan dubu ɗaya guda huɗu kana ta sake yi masa godiya,
Yasan Umma ko wacece a gurinsa baya ƙayyade mata kuɗi, sbda tana biyansa fiye da inda zai ambbata, kafin ya kalli Fawziya yace "kema ƴarinyar Hajiya ce?"

Jikin Fawziya na rawa tace "eh"

Boka ya miƙa mata wani icce dogo, kana yace "ki jiƙashi a kofi kidinga wanka dashi, kafin kiyi wankan ki ɗibi ruwan da hannuwanki biyu ki kira sunan mijinki, na baki mako guda zaki dawo kibawa Aljani ɗan gata labari"

Fawziya ta dinga godiya kamar bazata dena ba, Hajiya ma taji daɗi sosai,

Haka suka shigo mota ko wanne zuciyarsa wasai.

Sam Hajiya babba taƙi amincewa Fawziya ta wuce da ita gidansu, sbda zumuɗin aiwatar da abinda boka ya bata, a bakin hanya suka sauketa ta tari mai mashin zuwa anguwarsu,

Suna isowa ta bashi kuɗinsa kana ta ƙwanƙwasa get, mai gadi na buɗewa ta miƙa masa dubu ɗaya ta shige ciki,

Yanta yi mata Godiya itakam tayi gaba.

Idan kaga fuskar Hajiya babba kai kace ance mata gobe aljanna zaki shiga,

Da sallama ta shiga babban parlonsu, tana shiga ta samu, Hakeem da Iffat da Hajiya ƙarama har da Dady suna kallo,

Har zata balbalesu da masifa sai ta tuna kwana nawa ne ya rage?"


Ta nemi guri ta zauna tayi musu sannu da gida,

Dukkansu suka amsa da yauwa, Iffat tana ta kallonta tana murmishi,

Dady yace "daga yanzu zan dawo shikenan har ƙarfe uku na rana"

Hajiya ƙarama tace "Alhaji yace Umma babu lafiya, wllhi Ni ban san zaki tafi ba ai da na biki"

Hajiya babba tace "ai taji sauƙi hawan jininta ne ya tashi yanzu alhmdulilah tana gida"

A zuciyarta kuwa cewa take "idan da kin biyo NI ai da kin taƙai tani"

Hakeem ya miƙe tare da wucewa ɗakinsa ya ɗauko key ɗin mota ya dawo zai wuce, Dady yace "Hakeem ina zuwa?"

"Zanje duba Umma ne"

Ko Uffan batace ba ya wuce.

Hajiya ƙarama tace "a gaishe ta nima gobe zaka ka kaini"

Hajiya babba ta miƙe tana cewa "washh"

Ta shige ciki.

A kan gado ta zauna tana tunanin yaushe ya kamata ta aiwatar da komai,
A fili ta furta "insha Allah zuwa dare zan gama komai"

UMMA House°°

Kiran sallahar Azhar ne ya tashe ta a gurin, sbda jikinta yayi matuƙar sanyi har tunani takeyi da wane ido zata dinga kallon mijinta?

Bata bar kan sallahya ba har sai da aka kira sallahar la'asr,
Tana zaune jingine da jikin gado, taji sallamar Alhaji Lukman, jiki a sanyaye ta amsa, tare da kai dubanta gareshi,

"Sannu da dawowa"

Fuskarsa ɗauke da murmishi yace "yauwa Hajiyar Alhaji da fatan kin wuni lafiya ya baƙonmu"

Sai da ƙirjinta ya bada rass!! Kafin tace "ai ya tafi"


"Masha Allah ai ya kirani a waya yake sanar min da kayan tarba da aka shirya masa, wllhi har kyautar dubu ɗari biyar yamin, yace in baki dubu ɗari, ya ƙara da cewa wllhi Alhaji Abdussalam mutumin kirki ne ba ƙaramin kyauta ne dashi ba, yana yimin alkairi da yawa"

Umma tace "Masha Allah mun gode"

Kana ta miƙe dan kar ya gano tana cikin damuwa, hannunsa ta kamo suka dawo parlo, ta zubo masa ragowar abincin da ta dafa, dan a halin yanzu ƙarfin hali takeyi kawai,


Yana ta zuba mata sumbatu yana cewa "abincin yayi daɗi kamar zai tsinke kunne"

Bayan ya kammala cin abinci, ya miƙe ƙafarsa a kujerar da yake zaune, kafin ya kalli Umma yace "kuyi haƙuri wataran sai labari, nasan akan rashin lafiyata ne abun yake damunki insha Allah komai zezo ƙarshe, tunda yau munyi magana da Alhaji Abdussalam akan rashin lafiyata kwanannan zan tafi asibitin Egypt domin a sake dubani, kinsan sunada Islamic hospital acan"

Umma ta kawar da kanta tare da runtse ido sai kuma ta buɗesu a hankali tana ambaton sunan Allah,

Ya lura da yanayin ta, cikin kwantar da hankali yace "haba wannan aikin da za ayi domin mu ne gaba ɗaya, a tunanina farin ciki zakiyi ba ɓacin rai ba"

"Ta wan gefen ina farin ciki ta wani gefen ina baƙincikin rabuwar da zamuyi na wasu lokutan da bansan yaushe zaka dawo ba"

Ba jimawa zanyi ba, bai wuce wata ɗaya ba, sai dai kuma daga nan idan maganar transfer da za'ayi min ta taso zan wuce ko one week ne inyi"

Tabbas duk wannan shirin yana daga cikin makircin Alhaji Abdussalam ya gaya mata komai game da hakan, ita kam ta kasa gano mafita, daga ƙarshe ta miƙawa Allah lamuranta,


Haka suka dinga hira jifa-jifa sbda yana lura da yanayin ta, shiyasa yake janta hira.

Har aka kira sallahar magriba suna zaune, daga ƙarshe ta miƙe zuwa sallah, shima alhajin ya miƙe ya wuce masallaci,

Akan sallahya bayan ta idar da sallah adu'oi ta dinga kwararowa tana kuka....


Aslamu alaikum masoya makaranta littafin MURAYU A TARE,
Book2&3 zai zo muku a paid Normal 300 vip 700

Munkusa gama book1 abinda nakeson cewa shine, inason ya zamo wanda sukeson littafin sun biya kudin su, domin muna gama book1 zamu shiga two ba tare da ɓata lokaci ba, da izinin Ubangiji, idan na gama book1 mutane basu gama biya ba, zamu dakata da posting sbda bana son na haɗa abubuwa biyu, ga typing ga adding.

Wanda suka shirya biyan kuɗi su tura ta nan. 3175689751 Zainab Habibu first Bank. Shedar biya ta wannan number 08141799224

Dan Allah kar ayi min Vtu Please idan kuma kati ne, hoton katin zaki ɗauka ki turomin

Ƴan Niger zasu tura da katin Airtel


Mom Islam

*💋MU RAYU A TARE💋*

Mom Islam


Book1

89-90

Da kallon mamaki Bappa Dattijo yabi Prince, kana ya nemi guri ya zauna yana kallon ƙwaryar furar da Prince besha ba,

"Abdullahi meyasa bakasha fura ba, ko baƙunta kakeyi mana?"

Prince ya sunkuyar da kansa ƙasa kafin yace "zansha Bappa wayata ce a hannun yarinyar da tazo dama wannan nonon har yanzu bata shigo ba"

Bappa ya miƙe da sauri ya fice yana cewa "Ashsha Boɗɗo lamarinta sai ita"

Koda ya fita waje bai ganta ba, ya tsaya a ƙofar gida tare da tunanin inda zai gano inda take.

Ta ɗayar ƙofar Boɗɗo ta shigo da uban gudu, tare da sunkuyawa gaban akuyarta dake ɗauke da tsohon ciki, kurma ihu tayi tare da rungume akuyar tace "unguwar joma ta shusheni"

Prince ya fito da gudun dan ganin me take yiwa ihu, ga mamakinsa sai ya ganta gaban akuya ta rungumeta idanun ta shaɓe-shaɓe da hawaye,

"Dan Allah ki bani wayata, Noɗɗo kike ko Joɗɗo? nikam ki taimakeni Please"

Boɗɗo ta zaro masa manyan idanun ta tare da cewa "kai mara taushayin ina ne, akuya ta jata aifu kana min jancen wani abun banja da wofi"

Prince ya zaro ido, sbda yana maganar hankalinsa na gurin akuyar, ta wahala sosai, cikin sauri yace "kawo leda"

Boɗɗo tace "bamu da leda me jakayi?"

"Zan taimaka wa wannan akuyar ne"

Da gudu ta miƙe ta kawo masa leda guda biyu, yasa ya ɗaure hannuwansa, cikin ikon Allah shi ya taimakawa akuyar har komai ya dai-daita,

Tashi ɗaya ƙyanƙyami ya kama Prince, sai zubar da miyau yakeyi, ta kawo masa omo da ruwa ya wanke hannu, yana miƙewa sai ga Bappa ya shigo,

"Ah Abdullahi me kakeyi anan?"

Kafin yayi magana Boɗɗo tace "anguwar joma tayi mana"

Bappa yace "Masha Allah ashe ka karanshi aikin anguwar joma?"

Dariya ta kama Prince ya gimtse ya shige ɗakin yana cewa "eh"

Bappa kam ya mance da maganar waya, tunda yaga akuyar Boɗɗo ta haifi yara uku, ya fice waje yana farin ciki,

Bayan boɗɗo ta bawa akuyar abinci da ruwan sha, ta fice da gudu, ta tari ƙawayenta ta fara gaya musu akuyarta ta aihu sannan kuma anguwar joma tazo gidansu,

Suka ɗunguma kan yashi, ashe anan ta binne wayar Prince ta zuba ƙasa akai,

Wayar ta fara ring, ai dukkansu suka watse a gurin, tsabar tsoro, sai da akayi kira kusan goma suna nesa da wayar, daga ƙarshe wata a cikinsu tace "waƙa ce Kuzo muyi rawa,

Idan wayar tayi ringing sai suyi ta rawa, idan kiran ya katse sai su tsaya,

A haka har Prince ya zo gurin da suke, cikin sa'a yaji ringing ɗin wayarsa, sam ya rasa a ta ina take, cikin lallashi yace "dan Allah ku bani wayata"

Boɗɗo ta matsar da yashi kana ta ciro masa tana cewa "kinshi darajar anguwar joma"

Gaba ɗaya burin Prince bai wuce yaga wayar tasa batayi komai ba, amma fa ta cika da yashi, ya koma ciki yana gogewa.

Sai da ya gama, ne ya samu damar shan nonon, sannan ya fara shawarar asubar fari zeyi sammako yabar garinnan sbda wannan yarinyar zata iya hallaka shi,
****. ***

Tunda Tasneem ta dawo kullum sai Zahraddin ya zo, safe yamma, har abun ya fara damun Hajiya, ta kira Uncle a waya tace "itafa mijin Tasneem ya dameta da zarya dan Allah yazo ayi maganar mayar da ita, Uncle yace "insha Allah nan da kwana biyar zata koma"

Amma Allah yayi wa yaron ƙanwar matarsa Rashida rasuwa,

Tasneem na daga nesa da Hajiya tace "Allah ya gafarta masa"

Hajiya ta amsa da Amen tare da cewa "kinga Allah ba azzalumin kowa bane, Tasneem marainiya zaki koma gidanki lafiyar Allah, dama ina ta tunanin wannan yaron wllhi"

A ranar Hajiya ta kira wata ƙawarta ƴar mai duguri kasancewar ta zo gyaran amare wani gida anan cikin garin Kano,

Sukayi alƙawarin gobe da wuri zatazo,

Washe gari kafin matar tazo, Hajiya ta aika Tasneem kasuwa sbda idan an fara gyaran bazata dinga fita ba.

Dawowar Tasneem kenan taga mai gyaran amarya tazo, bayan sun gaisa, sukayi sallah lokacin an kira Azhar aka fara.


Yau kwana ɗaya da Zahraddin ya bata waya, ya kira yafi sau biyar kuma ko wanne sai sunyi magana,

Kasancewar a keɓe suke da ita mai gyaran jikin, ta dinga gaya mata sirruka na zama da miji da inda zata zamo tauraruwa a gurin mijinta da sauransu.


Yau kwanan Alhaji Al'amin biyu da tafiya, sam Juwairiya taƙi buɗe takarda, gashi ya kirata ya sanar mata da cewar sun kusa shigowa gari,

Sosai ta shirya masa haɗaɗen girki mai rai da lafiya, tare da drinks na abarba da su kankana da madara, sai kunun zaƙi da tayi masa, ta shirya cikin leshi mai ruwan shuɗi, ɗinkin doguwar riga, tayi kyau sosai saboda a halin yanzu harda kumatu tayi.


Ƙarfe 5:pm na yamma sai ga horn ɗin motar Alhaji Al'amin, kamar ta ruga da gudu ta tarboshi haka ta dinga,

Tana zaune a parlo taji sallamarsa, kana ya tura ƙofar ya ƙaraso ciki, da gudu taje tayi hugging ɗinsa tana murnar dawowarsa, fuskarsa yalwace da murmishi yace "i miss You my Juwairiya da fatan kema kinyi kewata?"

Tana kashe masa ido tace "eh man sosai ma"

Suna rungume da juna suka zube akan kujera,

Yaja kunnenta sai da tayi ƴar ƙara kafin yace "kin buɗe saƙon takardar nan baki cemin komai ba"

Juwairiya ta waro ido kafin tace "wllhi na mance ne, ban ma karanta ba"

"Oya jeki ɗauko"

Taje ta ɗauko a sanyaye ta dawo ta zauna akan cinyarsa, ta buɗe ga abinda ta gani a rubuce"

"Matata farincikina, haƙiƙa zanyi kewarki, kafin in dawo ki shirya zamuje ƙauyen iyayena domin su sanya mana albarka, ya zamo already ina dawowa tafiya zamuyi"

Juwairiya ta sauke ajiyar zuciya, ya sake rungumeta tsam, kana yace "yaushe kike ganin ya kamata mu tafi?"

Juwairiya tayi sama da ido tare da cewa "ko jibi"

Sosai yake shafa ta yana cewa "gaskiya ina tunanin bazan sake tafiya ba tare dake ba, wllhi har mafarki nakeyi, i miss You so much my wife"

Hannunta tasa ta ratayo ƙugunsa kana tace "uhm ni da ka tafi ka barni na dinga kuka?"

Dariya yasa yana lakace mata hanci.

Tace "ka tashi muje kaci abinci"

"Gaskiya na gaji, sosai inason ki rakani in watsa ruwa sannan sai inzo inci abincin"

Ya miƙe tare da ɗagota,

Rungume da juna suka wuce bedroom ɗinsa, sai da ta tayashi cire kaya kafin suka shiga toilet, aca n ɗin ma wasanni suka dinga yi daga ƙarshe akayi wankan suka fito, sam ya kasa haƙuri da ita, dole ya nuna buƙatarsa a fili, ko be gaya mata ba idanunsa sun nuna mata....


Aslamu alaikum masoya makaranta littafin MURAYU A TARE,
Book2&3 zai zo muku a paid Normal 300 vip 700

Munkusa gama book1 abinda nakeson cewa shine, inason ya zamo wanda sukeson littafin sun biya kudin su, domin muna gama book1 zamu shiga two ba tare da ɓata lokaci ba, da izinin Ubangiji, idan na gama book1 mutane basu gama biya ba, zamu dakata da posting sbda bana son na haɗa abubuwa biyu, ga typing ga adding.

Wanda suka shirya biyan kuɗi su tura ta nan. 3175689751 Zainab Habibu first Bank. Shedar biya ta wannan number 08141799224

Dan Allah kar ayi min Vtu Please idan kuma kati ne, hoton katin zaki ɗauka ki turomin

Ƴan Niger zasu tura da katin Airtel


Mom Islam

*💋MU RAYU A TARE💋*

Mom Islam


Book1

91-92


Sosai ya nuna mata kewarta da yayi na wasu lokuta, daga ƙarshe ya dinga fito mata da tsaraba iri-iri,

Washe gari, bayan anyi sallahar asbha, tare suka shiga kitchen suka ɗora breakfast, Juwairiya tana ta yi masa dariya harda riƙe kwankwaso kai kace mace, bayan sun kammala suka shiga wanka a tare, suna fitowa suka shafa mai, tare da sanya ankon bikinsu shadda mai ruwan sararin samaniya, sunyi kyau matuƙa, duk da simple makeup tayi,

Bayan sunyi breakfast yace mata zasu fita yanzu, bata tambaye shi ina zasuje ba, bayan sun gama kintsawa ya kamo hannunta suka fito, tana sanye da ƙaton hijabi, suka shiga mota, da kansa yayi wa motar key suka fice, bayan an buɗe musu get,

Kai tsaye kasuwa ya wuce, sukayi siyayya sosai mai yawa, har ta siyawa babanta shadda yadi goma da takalmi, siyayya sukayi na tafiya ƙauye, kaya na gani na faɗa.

Daga nan suka dawo gida, a gajiye, ranar ko girki batayi ba sai tea suka sha suka kwanta, bayan sun rama sallolin da basuyi ba,
Suka kwanta da niyar gobe in Allah ya kaimu da wuri zasu fita,

Ikon Allah barci yayi daɗi har da makara, ko kiran sallahar asbha basuji ba, sai ƙarfe shida da rabi Al'amin ya fara farkawa,

Kafin ya shiga toilet da sauri ya ɗauro alwalah yana mamakin barcin da sukayi mai yawa haka,

Kana ya tashi Juwairiya, ganin gari ya fara haske yasa ta farka da sauri, tare da durowa ta wuce toilet, alwalar ta ɗauro kana ta shimfiɗa sallahya ta kabbara sallah,

Bayan sun idar aka fara haramar wanka kasancewar da ruwa a flaks,

Da safen ma tea suka sha kana ta janyo kayanta da ta riga ta shirya su, haɗe da nashi, duk wasu abubuwa wanda tasan zata buƙata sai da ta sanyasu, ƙarfe 10:am dai-dai suka kulle ko ina kana suka wuce parking space, drivern gidan na ganinsu ya je da gudu ya karɓi akwatin hannun Juwairiya kana yasa a Booth yana yi musu Allah ya kiyaye hanya, yau ma Al'amin ɗinne ya shiga mazaunin driver suka fice, ma'aikatan gidan sunayi musu adu'ar isa lafiya.

Suna tafe tana ƙare masa kallo, duk da shiɗin ba yaro bane, amma tana jin sonsa a cikin jikinta, koda yaushe tunaninta bai wuce shi ba, jifa-jifa yakan kalleta su sakarwa junansu murmishi, sunyi nisa da inda suka baro, yace mata ƙauyen Kano zamuje Jibga, Juwairiya tace "ikon Allah wllhi ban taɓa jin sunan garin ba, Allah ya saukemu lafiya"

Ya "furta Amen"

Sannu a hankali Allah ya kawo su cikin garin Kano, ta ɗauka har sun iso ne, sai taga ina abin dai za'ace wasa farin girki, wasu ƙyauyaku ya dinga kutsawa, itadai Juwairiya shiru tayi, sbda tafiyar ta shallake tunaninta, sunyi tafiya mai nisan gaske, gashi ƙauyen da suke tunkara ko alamun pol waya na wuta babu,

ƘAUYEN JIBGA
Ƙarar shigowar mota da ilahirin yaran suka ji ne yasa ko wanne ya rugo da gudu, bayan Al'amin yayi parking, suka zo jikin motar suna shafawa, shiko sai washe baki yakeyi, sam ƙyanƙyamin garin takeyi bare ta zauna tare da mutanen cikinsa, ta tsani ƙuye ko ƴan ƙauye, musamman yanzu da ta sake komawa ƴar gayu,


Ganin ta tsaya kallonsu yasa Al'amin kamo hannunta suka ƙarasa cikin gidan nasu,

Wata mata da ta taho taga riƙe hannun da Al'amin yayi da Juwairiya, ta ruga da gudu har tana bigewa da bango, kai tsaye cikin gidansu ta shiga tare da faɗawa ɗakin Mari, cikin ƙasa da murya tace "wllhi tallahi yau idona idon Aminu ya dawo shida wata ƴar iska wllhi Karki ganta sai kace baturiya"

Wacce aka kira da Mari ta miƙe tsaye cikin masifa tana sanye da rigar atamfa koɗaɗiya sai zani daban ko zanen jiki babu shima ya fita hayyacinsa, ga nono raɓeɓe har ciki, tana girgiza tace "wato da akayi masa asirin rabani da shi, aka kaɗashi binni shine yaje yayi kuɗi har ya mance dani da ƴa'ƴansa ko?"

Wacce ta kawo gulmar tace "wllhi Karki sake a koma babu ke, ki tattara yaransa ku koma, sannan ki gayawa malam kinsan mahaifinsa da tausayi ki gaya masa a haɗaku kici uban shegiya, ubanme zata nuna miki a kula da miji....


😔Wllhi rashin wuta yasa banyi muku typing ɗin da wuri ba, gashi babu yawa, akwai bidiri a ƙauye🤸 barci kuma nakeji..

A page 100 zamu ƙarƙare insha Allah, idan an gama biya da wuri muna gama book1 zamuci gaba da book2 idan ba'a biya da wuri ba, aradun Allah sai mun fi sati ɗaya ba'aci gaba da posting ba

Nagode masoyana masu comments da shar'hi.


Normal 300
Vip 700

08141799224
*💋MU RAYU A TARE💋*

Mom Islam


Book1

93-94


"Ki ƙyaleni da su ai indai makirci ne irin na ƴan bariki babu abinda za'a nuna mana"

Tun daga babban zauren gidan Al'amin ya fara cewa Juwairiya "dan Allah ki saki jikinki kwana uku zamuyi ki koma"

A shagwaɓe tace "kai fa?"

"Tare zamu koma ai ban isa in barki ki tafi ke kaɗai ba"

Suka ƙarasa ciki bakunansu ɗauke da sallama, babban gida ne gidan a ƙalla mutanen ciki zasukai talatin, gidan ya haɗa da
End Ads