bari kowa ya lura da hakan ba, amma kash Hajiya ta gane kallon da Tasneem take yiwa yaron, kawar da kai Tasneem tayi, tare da zuba musu abincin, Uncle ya fito waje tare da kiran Hajiya,
Bayan Hajiya ta fito yace "Hajiya mutanen nan sunada kirkin da suka can canci ayi musu babbar kyauta, a ganinki meya kamata ayi musu dan nuna godiya?"
Hajiya tace "sosai ma kuwa, kaga inda Tasneem tayi kyau kamar ba itace ta fita cikin wani yanayi ba, munyi cigiya har mun gaji, nidai a nawa ganin ka biya musu kuɗin Hajji dukkansu"
Uncle yace "nima nayi tunanin hakan, amma sai nake ganin kamar zasufi buƙatar kuɗi"
"A'a kayi hakan, zan basu dubu ɗari bayan sun dawo duk da nasan ba komai zatayi musu ba"
"Allah ya shige mana gaba"
Uncle ya faɗa cikin amincewa da shawarar Hajiya.
"Malam dan Allah ka rage wannan masifar da kake yi, ita kanta Inna da tasan haka ne zai faru, Hajara ta tafi taƙi dawowa Wlhi bazata soma ba"
Kamar ana ƙara masa faɗan, yace "shikenan ai talauci ba hauka bane, kinfi son a dinga nunani a layi kenan, babu wanda bashi da labarin inda Hajara taje, tsakanina daku Wlhi ba zan yafe ba"
Ran goggo a ɓace ta gyara ɗaurin zaninta, a tunzure ta fara magana,
"Karka yafe ɗin, yarinyar da auranta ya mutu ka tozartata, ai a tunanina abin ka jata a jikinka ne, shine zaka dinga wani surfewa mutane masifa, ni nan mahaifiyarta Wlhi na fika shiga damuwa, dan haka karka sake yimin maganar Hajara"
"Anyi ɗin kiyi abinda zakiyi, ita mahaifiyar taki ai abin duniya tabi, shiyasa ta turata garin larabawa nemo kuɗi, dan haka ki ficemin a gida"
Goggo ta taɓe baki, kafin tace "au ka mance gida ya zamo nawa, harda takardar sheda, kuɗina nasa na siya dan haka sai ka barmin gida"
Jikin malam a sanyaye ya janyo kujera ƴar tsugunno ya zauna.
Hausawa sukace rana bata ƙarya..
Yau kam mutuniyarku ta shiga daga ciki, a wani katafaren gida ilahirin motocin kawo amarya sukayi Horn, mai gadi ya buɗe, nan fa kallo ya koma sama, duk da kunsan garin Kano akawai tsararrun gidaje, to ga wani ma, wanda sai ka rantse a ƙasar Turai akayi ginin, yawancin murafen ƙofofin kai kace na zinare tsabar walwalin da yakeyi,
Abin mamaki babu dangin Alhaji Al'amin sai iya dangin Juwairiya ta fannin babanta da mamanta, sai abokan arziƙi, ba wasu aiyuka sukayi ba, sbda gidan a gyare yake, anayin sallahar la'asr motocin komawa da mutane suka fara ɗibarsu,
Gida ya rage iya Juwairiya, sosai take jin tsoron gidan, musamman ma da ya kasance tafkeke, a fili ta fara shawarar idan har sun zauna sun fahimci juna zata ce ya nemo mata ƴar aiki ta dinga ɗebe mata kewa.
Har akayi sallahar magriba bai shigo ba, har akayi isha'i shiru, hankalin Juwairiya ya tashi sosai, ta ɗaga waya ta kira shi, ring ɗaya ya ɗaga tare da cewa "amarya bakya lefi, Wlhi tafiya ce ta kamani zuwa Dubai, bani da inda zanyi idan ba can na tafi ba"
Jikin Juwairiya na ɓari tace "har ka tafinne?"
A'a ban riga da na tafi ba, akwai wasu muhimman takardu da nake cikewa insha Allah ganinan zuwa"
"Allah ya kawo ka lafiya"
Juwairiya tace hankali a tashe.
Har barci ya fara ɗaukarta taji alamun shigowarsa, da sauri ta murza idonta tare da tashi zaune, kana tace "baby Wlhi kasa na firgita"
Al'amin yayi murmishi kafin ya ƙaraso gurinta, yace "matsoraciya"
Tare da lakutar hancinta,
Murmishi tayi kafin ta zauna kusa dashi a bakin gado, a shagwaɓe tace "uhm nikam Wlhi tafiyar nan bada son raina za'ayi ta ba, dan Allah karka tafi ka barni"
Cikin kwantar da hankali yace "insha Allah, babu abinda zai sameki, nidai fatana koda yaushe mu kasance cikin so da ƙaunar junanmu,
Kafin ya kamo hannunta suka wuce kitchen, nidai cewa nayi ko pillow aka miƙo min wallahi zanyi barcina a kitchen, yayi kyau sosai, ya buɗe gurin gasa cake ya ɗauko kaji a faranti mai kyau, kana ya miƙa mata ya rufe,
Karɓa tayi tanayi masa murmishi tare da kallon farantin dake cike da gasashen naman kaji an yankasu,
Riƙe da hannun juna suka taho parlo, da kansa ya buɗe fridge yace "wane irin lemo zakisha?"
"Fanta"
Juwairiya ta faɗa.
Kawo mata yayi, ya ajiye akan table kana ya dawo ya zauna,
Kamar wata jaririya ya ɗauko tare da miƙa mata baki, ta ƙarɓa tana yi masa murmishi.
Bayan sun gama ci ta tattare kayan ta mayar dasu suka koma bedroom ɗinta, umartar ta yayi da tayi alwalah, already shima yayi, suka kabbara sallah raka'a biyu, kana ya dafa kanta yayi mata addu'a sannan ya riƙe mata hannu suka haye gado, sun raya daren cike da soyayya mai tsayawa a rai, musamman ma inda yake lallaɓata kamar wani ƙwai, a daren sai da ya mayar da ita cikakkiyar mace, tare da yi mata alƙawarin zasu tafi honeymoon ta zaɓi ƙasar da takeso, bayan ya dawo daga tafiya zasu wuce.
Washe gari tun asbha Iffat ta tashi da zazzaɓi, wanda ya tayar wa da mutanen gidan hankali, banda Hajiya babba da take shirin ƙaɗata a gidan,
Jikin Dady na rawa yace wa Hajiya ƙarama ya kamata mukai Eshat hospital sbda jikin nata ya tsananta"
Ya ƙara da cewa "ba zanyiwa Hajiya babba magana sai ta kaita"
Sam Hajiya ƙarama bataji daɗin abinda Dady yace ba, amma batasan ya fahimci akwai wasu matsaloli sai taja baki tayi shiru, dama ta riga da ta shirya Iffat ɗin, bayan gari yayi haske Dady ya tafi da Hajiya babba da Iffat Asibiti...
Aslamu alaikum masoya makaranta littafin MURAYU A TARE,
Book2&3 zai zo muku a paid Normal 300 vip 700
Munkusa gama book1 abinda nakeson cewa shine, inason ya zamo wanda sukeson littafin sun biya kudin su, domin muna gama book1 zamu shiga two ba tare da ɓata lokaci ba, da izinin Ubangiji, idan na gama book1 mutane basu gama biya ba, zamu dakata da posting sbda bana son na haɗa abubuwa biyu, ga typing ga adding.
Wanda suka shirya biyan kuɗi su tura ta nan. 3175689751 Zainab Habibu first Bank. Shedar biya ta wannan number 08141799224
Dan Allah kar ayi min Vtu Please idan kuma kati ne, hoton katin zaki ɗauka ki turomin Nagode
*💋MURAYU A TARE 💋*
Book2 coming soon 💃
Takensa *Wasa⛹️♀️farin girki🍵🔥*
Mom Islam
*💋MU RAYU A TARE💋*
Mom Islam
Book1
Page 73-74
Cikin ƙungurmin jejin garin Shahaza forest Sahla take ci gaba da tafiya, a gajiye ta yada zango a gindin wata bishiya,
Sai fitar da numfashi takeyi mai cike da alamomin gajiya,
Ƙugin da cikinta yayi ne yasa ta buɗe jakarta ta ciro gurasa guda ɗaya ta dinga ci kamar wacce bata taɓa ido biyu da abinci ba,
Acan saman bishiyar kuma wani ƙaton maciji ne yake saukowa yana harin gurin Sahla, kamar ance ta waiga, cikin sauri ta wurgar da ragowar gurasar hannunta kana ta ɗauki jakarta zata ruga da gudu,
Cikin rashin tsammani ta zame a kan ganyayyakin dake shimfiɗe a ƙasa, ta kurma ihu tare da cewa "abar bauta ki taimakeni"
Kafin takai ƙasa macijin ya shimfiɗe a ƙasa, ganin a kansa zata faɗo dole, yasa ta runtse idanun ta tare da gama saddaƙarwa ta mutu an gama,
Duk da yanayin fatar jikin macijin ta ban banta da sauran majizai, hakan yasa ta sake razana, gata uwar tsoro,
Shiko yabi ƙasa ya daɗa gyara mata kwanciya tayi luff a gadon bayansa, ashe sumewa tayi tsabar fargaba,
Abin mamaki da al'ajabi macijin ya rikiɗe zuwa fatar larabawa harda yanayin fuskar ma, ya ɗauketa ya tsallake ruwa kai kace iska, sbda ni kaina bazance ga lokacin da suka tsallake katafaren kogin dake gabansu ba, cikin wasu lokuta ya kawo ta gidansu, ikon Allah kenan, gidan dai zamu iya cewa kamar gidan tarihi, sau da yawan turawan yankuna da dama, wannan gida ya mugun tsole musu ido, ansha kawo masa hari ta fannin tsafi, adu'ar musulmai akan galaba, duk Allah besa sun shiga ba, a taƙaice dai ginin kai kace bada ƙasa aka yi shi ba, sannan tambari da adon dake jikin ginin shine zai matuƙar firgita mai karatu, gini ne wanda ya amsa sunansa gini, sannan tambarin yawancin masu faɗa aji wanda suke da tarihin wannan guri sunada hoton tambarin, ada kenan zamu ce da kowa yake iya ganinsa, duk wanda kuka gansa a gurin zamu iya cewa yakai ƙwaro sosai, ma'ana Jarumi, yana ɗaya daga cikin dalilin da yasa shahazad Junaid Khan ya ƙirƙiri wannan jejin kenan, sukuma mazauna jejin tun kafin shahazad ya shirya wani tuggunsa suke zaune a ciki"
A hankali ta buɗe ido, tare da kallon inda take, da sauri ta waiga taga babu kowa a ɗakin, hankali a tashe ta miƙe zaune tare da sake gyara zaman jakarta, kallon abubuwan da aka kewaye ɗakin, jikinta na karkarwa ta zuro ƙafafunta ƙasa, kana ta kalli fitillun da aka kunna sunkai guda goma,
Shi kansa gadon da take kwance kyawunsa yafi gaban kwatance,
Wata kyakkyawar mata ta fito daga cikin ɗakin dake kallon inda Sahla take, cikin zazzaƙar murya budurwar tace "sannu dame zan iya taimaka miki?"
Sahla tace "inaso a mayar dani hanya, ni matafiya ce"
Budurwar ta yi murmishi kafin tace "karki damu kafin nan ki bari Ludtfi yazo"
Sahla ta ware ido, kana tace "waye shi?"
Zaki gansa amma kafin ga wannan yace "ki tafi dashi, yanada labarin gurin shahazad zakije, sannan yace ki riƙe shi a matsayin kariya kuma dukiya, idan kinason dawowa nan ki ajiye diamond ɗin a gurin da rana take fitowa, sannan ki rufe idonki"
Sahla tace "Nagode"
Nocking ɗin ƙofar da akayi ne yasa Karan Khan firgita, murya ƙasa-ƙasa yace "ƴan sanda ne"
Ya kamo hannun mona da na Hajara, a sukwane ya fice dasu ta ƙofar da jami'an Basu san da ita ba,
Suna tsaye suna shirya inda zasu yi su kama karan Khan ashe ya tsere musu,
Kowanne da waya a hannunsa, suna magana a hankali tare da tafiya cikin sanɗa,
A hankali suka faɗa cikin gidan, suka hau bankaɗe ko ina amma sukaga wayam, sawun takalmin Karan Khan da suka gani a hanyar da suka fice ne yasa suka fara shiga ta hanyar, amma sai dai kash sun tsere.
Acan ɓangaren Shahazad kuwa, ya daɗa baza jami'an tsaro ta hanyar mota da jeji da jiragen ƙasa, lokaci guda ko ina suka ji labarin an sace mona ita da ƴar aikinta, ƴan jaridu suma ba'a barsu a baya ba gurin bincike da yaɗa sanarwa,
Shi kansa yana binciken duk wani motsi na mutanen garin a na'ura.
💋
Wani irin juyi yayi akan kujerar da yake zaune, a fusace ya miƙe ya wankawa sojan dake tsaye a gabansa mari,
"Get out of my office"
Cikin ladabi sojan ya fice,
Zancen banza zancen wofi, abin mamaki duk yawan mutanen garinnan ace sun kasa gano min inda mata take, Wlhi nan da kwana uku idan ba'a gano inda take ba, sai na sa an buɗewa ƴan garinnan wuta dukkansu,
Da sauri Ministan harkokin kayayyakinsa da suke shige da fice, ya miƙe na kusa dashi ma suka miƙe cikin haɗin baki sukace "ayi mana sassauci mai girma shahazad, a fusace ya miƙe tare da cewa...
Aslamu alaikum masoya makaranta littafin MURAYU A TARE,
Book2&3 zai zo muku a paid Normal 300 vip 700
Munkusa gama book1 abinda nakeson cewa shine, inason ya zamo wanda sukeson littafin sun biya kudin su, domin muna gama book1 zamu shiga two ba tare da ɓata lokaci ba, da izinin Ubangiji, idan na gama book1 mutane basu gama biya ba, zamu dakata da posting sbda bana son na haɗa abubuwa biyu, ga typing ga adding.
Wanda suka shirya biyan kuɗi su tura ta nan. 3175689751 Zainab Habibu first Bank. Shedar biya ta wannan number 08141799224
Dan Allah kar ayi min Vtu Please👏 banda Vtu
idan kuma kati ne, hoton katin zaki ɗauka ki turomin Nagode
*💋MURAYU A TARE 💋*
Book2 coming soon 💃
Takensa *Wasa⛹️♀️farin girki🍵🔥*
Mom Islam
*💋 MURAYU A TARE 💋*
Mom Islam
_Ina taya masoya barka da sallah, Allah Ubangiji ya biya mana buƙatunmu na alkairi, Allah yasa munada rabon ganin ta baɗi da rai da lafiya_
💋 75-76
Sharce zufar dake sintiri a fuskarsa kana yace "na baku nan da kwana uku, bayan nan idan Mona bata dawo ba duk hukuncin da na yanke shine dai-dai da tsarina.."
Dukkansu suka amsa da cewa "mai girma shahazad da yardar Ubangiji hakan ma bazai faru ba"
Ko kallonsu beyi ba ya fice.
Kai tsaye ya nufi gidansu, a nutse ya zauna akan kujera 3 sitter, kana ya shafin gashin da ya kewaye masa baki, a fili ya furta "never..!!"
Rai a ɓace ya miƙe ya nufi upstairs, da sauri yake haye benen har yakai ƙofar ɗakinsa, hannu yakai kan handle ɗin ƙofar zai buɗe, kamar wanda ya
tuna wani abu, sai ya fasa, ya koma ƙofar ɗakin Mona, jiki a sanyaye ya buɗe ƙofar tare wucewa bedroom ɗinta, kallonsa yakai kan kayan ɗakin tare da kallon madaidaiciyar hand bag ɗin dake ajiye akan gado yayi, kana ya buɗe jakar yaga babu komai, wurgi yayi da ita gefe tare da miƙewa ya kunna computer ɗin Mona, a farkon gurin searching yaga sunan Kharan, a tsorace ya shiga profile ɗinsa, kana ya hau binciken asalinsa duk da shiɗin ba ɓoyayye bane a gurinsa,
Har chatting ɗinda sukayi da Mona duk ya gani, sbda har Whatsapp ɗinta ya duba,
Cikin yanayin jarumta mai cike da tsantsar tunanin irin hukuncin daya dace ya miƙe, kana ya hau kewaye ɗakin yana bubuga hannu.
Cikin sauri ya ɗauki number Kharan yayi saving a wayarsa, kana ya rufe computer ya koma ɗakinsa.
"Hello Samir ga number wanda ya sace mona nan na turo maka"
Samir yace "ai munada numbersa, a halin yanzu bata shiga, sannan mun bibiyi layin an dena amfani dashi"
Shahazad ya cilla wayar kan gado tare da ture table ɗin dake kusa dashi, glass cup ɗin dake kai ya fashe, be bi ta kansa ba, ya dafe kansa.
Sahla na tsaye ita da budurwar nan, sai ga wani kyakkyawan saurayi ya shigo, fari dogo kayan da yasa ba irin nasu wanda suke sawa bane, sbda ya banbanta da shigarsu, doguwar riga ce a jikinsa mai tambarin zanen dake jikin ƙofar shigowa, rigarsa har ƙasa baka iya ganin ƙafafunsa, sai da budurwar ta rusuna da kanta kafin tace "ya shugaba, baƙuwarmu tana son wucewa"
Kansa a sama yace "an gama"
Kana ya shige ɗakin da wannan budurwar ta fito,
Shin Ludtfi mutum ne ko aljan?
A hankali suka fito tare da budurwar ta nuna mata hanya kana ta koma cikin gidan,
Sahla ta juyo ta kalli ginin, ya matuƙar bata tsoro da mamaki, sai dai wannan tambari da ta gani, bazai taɓa wuce mata ba, kamar ƙiftawar ido, ta tsallake kogin, kana taci gaba da tafiya,
Tafiya takeyi kanta tsaye, tunda tasan wannan hanyar zata sadata da babban titin da zata je garin SABHA, wato garinsu Shahazad.
Idan kaga inda take tafiyar kai kace bata sauri, sbda ƙafarta ko takalmi babu,
Tashi ɗaya taga yamma tayi sosai, hankali a tashe ta fara tunanin inda zata yada zango, batayi yunƙurin tsayawa ba taci gaba da tafiya har Allah ya kawo ta kusa da bakin titi,
Sahla tayi murmishi tanaci gaba da rungume jakarta, a gefen hanya ta zauna, tare da gyara zaman jakarta a kan cinyarta, cikin Sa'a wata mota ta hasko fitila, cikin sauri Sahla ta miƙe kana ta taho da gudu tana cewa "temako -temako"
Drivern ya yi murmishi tare da kallon abokinsa dake kusa dashi a fili yace "sabuwar kamu"
Dukkansu sukayi murmishi,
Har ta cire rai zasu taimaka mata, sai gashi sun buɗe mata ƙofar baya, ta shiga tare da sake rungume jakarta.
NIGERIA( Kano
Sai washe gari Uncle ya kai su umma tasha, bayan albishir da yayi musu na zuwa Makkah dukkansu, tare da kyautar dubu ɗari uku, sosai Tasneem taji daɗin kyautar, sbda harda ita aka yi musu rakiyar, basu dawo gida ba sai da motar su ta tashi, a hanyarsu ta dawowa gidan Hajiya, Uncle ya hango Zahraddin yana cikin mota yana waya, duk da ance fuskar masoyi ko Muryar masoyi bata ɓacewa masoyin gaskiya, tabbas Tasneem ta mance da kamaninsa, amma tunda ta samu lafiya soyayyarsa take yawo a ko ina na jinin jikinta,
Cikin ɗaga murya uncle yace "yarona..."
Kunsan meye?"
Wannan taɓa ka lashe ne, aiyuka ne sukayi min yawa shiyasa banyi muku typing da yawa ba, amma insha Allah komai yanzu yayi sauƙi alhmdulilah.
Sannan albishir ɗin da zanyi muku shine,
Kawo kunnenki kiji👂
Idan har kinason gano bakin zaren labarin, ki bibiyi book2&3 dake shirin zuwa nan bada jimawa ba,
Shin kun shirya jin zazzafar cakwakiya🤷♀️
Mom islam💋08141799224
*💋MU RAYU A TARE💋*
Mom Islam
Book1
77-78
Zahraddin ya kawar da wayar daga kunnensa, kafin ya ware ido,
Da sauri ya fito daga mota, yana cewa "Uncle a ina kaga Tasneem?"
Uncle yayi murmishi, su kuma idanun su suka sarƙe ana juna, a nutse yake ƙare mata kallo a zuciyarsa yana jin zafin nesa da juna da sukayi na wasu shekaru, tabbas soyayya abin so ce, musamman idan ka gamu da masoyin gaskiya, Uncle ya tsaya yana kallon irin yanayin da suke ciki, a fili ya furta "yaran zamani babu kunya, to zakizo mu tafi ne ko zaki bi mijinki?"
Tasneem ta sunkiyar da kanta ƙasa, sosai kunya ta lulluɓeta, tarasa yanayin da takeji game da Zahraddin ɗin.
A kunyace ta rufe murfin motar da bata san lokacin da ta buɗe ba, Zahraddin na tsaye Uncle yayiwa motar key suka wuce.
"Ikon Allah ashe ina da rabon ganin mata, ashe zamu sake rayuwa cikin farin ciki kamar inda mukayi a gidana".
Kana ya shiga mota ya wuce gidan Hajiya.
A mota Tasneem sai sunkuyar da kanta ƙasa tayi, saboda kunyar Uncle da ta lulluɓeta, har suka iso gidan Hajiya kanta na ƙasa, shiko da ya lura da yanayin ta sai yayi murmishi, bayan yayi horn mai gadi ya buɗe masa ya shige, tare da parking motar, kafin ya fito ta riga shi fita da sauri ta shige ciki gurin Hajiya.
Hajiya na ganinta ta washe baki, tana cewa "ikon Allah keda waye kiketa sauri har zaki murjemin ƙafa?"
Tasneem tasa dariya tana cewa "Uncle ne Wlhi"
Kafin Hajiya ta sake magana taji muryoyi biyu sunyi sallama, Hajiya da amsa da "wa'alaikumussalamu"
Uncle ya shigo shi da Zahraddin, kasancewar Uncle ɗin na tsaye motar Zahraddin ta shigo shine suka shigo tare.
Hajiya na washe baki tace "lale marhabun, angona sannu da zuwa"
Zahraddin yayi murmishi kafin yace "ƴar tsohuwa mai ran ƙarfe, shine ko ki kirani a waya kicemin Tasneem ta dawo ko?"
Uncle yayi gyaran murya, wacce tasa Zahraddin gimtse dariyar da ta kufce masa,