x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 9 - SHIMA DA NE free pages

  • 24001 words
  • 27000 words
  • Out of 65957 words

Category: Love Stories

Views 224

25 Aug 2025
Start ads
After Image Ads
gama aikin har sai ka biya kuɗin"
yace "na yadda"
yana gani suka rufe kofan bayan sun ɗaura ammi akan wani gado me na'ura, har kofan ya rufu yana kallon fuskanta da har yanzu idonta a rufe tana bacci.
ya jima a tsaye jikinshi a mace kafin yaja kafarshi da kyar ya bar asibitin, gida ya koma kamar kullum yadda ya saba aiki da yamma ya fara bayin flower yana share duk wani datti da gidan yayi, wankin motoci yayi sabida wannan ma yana cikin aikin da yake yi, sannan duk wani wanda ze shigo gidan shi yake buɗe mishi gate.
da haka har ya gama ya koma ɗakin ammi yayi shiru yana zaune ya rasa abinyi, wani abu ya faɗo mishi a rai da sauri ya cire karamin wayar ya shiga facebook yayi searching how to kidnapped someone"
hotuna ya fara gani na manyan ɓarayin duniya da manyan masu dealer ɗin kwayoyi, yaga yadda suke yin shiga su rufe fuska da bakaken kaya da safan hannu, sannan yaga suna rike karamin bindiga, kashe wayan yayi yace "to aina zan samu bindiga?"
yatsunshi yasa a kanshi yana yamutsa gashinshi, wannan ya zame mishi ɗabi'a a duk lokacin da yake tunani saiya hargitsa gashin kanshi, murmushi, rufe ido yayi sai kuma yace "zan samu a ɗakin dady naga yana dashi na kariya a lokacin da nake mishi mopping nayi mistake na taɓa drower ɗinshi na gani"
murmushi yayi yace "zanje na nemi kayan bindigan kuma sai zuwa dare"
tashi yayi ya fita bayan ya kwashe duk wasu kuɗin da yake dasu, kasuwa yaje ya siyo bakin kaya harda safan hanu da facemask ta yadda zai ɓoye kanshi, ya dawo gidan ya ɓoye a ɗaki sannan yaje part ɗin dady da niyan mishi gyara kamar kullum, yayi sa'a ya samu babu kowa hakan yasa ya ɗauke bindigan ya ɗaga riganshi ya ɓoye sannan ya tafi ya bar ɗakin yana farin cikin samun nasara.
har dare yana aiki saida dare ya fara nisa ya koma ɗakinshi dake bakin kofa wanda mallakin tsohon megadin ne sukace yana zama a ciki kamar yadda ya saba ya zauna yayi shiru bayan ya idar da sallan Isha, yana kallon time saida dare yayi nisa kafin ya canja kaya yasa bakaken sannan yasa mask ɗin ya ɓoye bindigan ya fito daga gidan, yayi mamakin da baiga motar dady ya dawo ba, fita yayi a gidan ya fara tafiya cikin duhun daren, har ya bar layin gidansu bai san ta inda zai fara ba, motar dady ya gani yana nufan gida da sauri ya ɓuya a bayan bishiya yana kallon dady, wani abu ya faɗo mishi a rai, yace "me zai hana na fara ta kanshi?"
smiling yayi sannan ya fito daga bayan bishiyan ya tsaya a tsakiyan titin ta yadda ze tare hanya wa motan dady, bindigan ya ɗaga sama yayi shirin harbi, dady daya haska yaga mutum tsaye da bindiga a hanu yayi shirin harbi ya juya da motan zai gudu sabia yau be fita da driver ba wajen sirri zaije, nawal ganin haka ya harbi tayan motan, kifewa motan yayi da dady a ciki, ko ɗas nawal baiji ba a ranshi baiji a jikinshi mahaifinshi yaji ciwo ba, baiji komai ba sai tsananin tsana da yake kara ruruwa a cikin zuciyarshi, ɓoye bindiga yayi sannan yazo ya buɗe motar, dady yana kwance yaji ciwo, ciroshi yayi a motar zai jashi a kasa ya tuna shine mahaifinshi koba komai zaici albarkacin uba a wajenshi, ɗaukanshi yayi Allah ya halicci nawal da mugun karfi amma kawai dai shi matsoraci ne kuma tsoron ya ginu ne a jikinshi tun yana yaro, tafiya ya fara dashi a kafaɗarshi har cikin tsakiyan daji ya kwatar dashi a karkashin wani bishiya ya ciro igiya a aljihu daya ɓoye ya ɗaureshi a jikin bishiyan sannan ya juya ya koma wani kango ya zauna yayi shiru, sam baya ji a ranshi cewar be aikata ba daidai ba, ji yake hakan babu kuskure hakan shine daidai.
wayan dady a hanunshi yana jiran me kira, maganin daya taɓa bawa dr shi ya bawa dady wanda zai kwana ya yini yana bacci besan inda yake ba.

momy dake salla taji hayaniya a falo batasan time ɗin da tayi sallama ba ta tashi da sauri ta fita, samha ce da nabil tauna m duka yake mata tana zaginshi, momy cikin gajiya da wannan faɗan nasu taje tana rike nabil da yake taka samha kamar namiji ɗan uwanshi yake duka, zai taka ruwan cikinta momy tace "nabil ya isheka haka nan, wai jaka ka samu ne? bakasan mace kake yiwa wannan dukan ba? me tayi maka?"
yana huci ya fizge jikinshi yace "wannan yarinyar momy a hotel na ganta tana zina da wani"
samha cikin dakuwa da ciwon da taji tace "kai me ya kaika hotel ɗin har ka ganni....?"
da karfi ya kara rufeta da duka, momy tana janshi taga zai kashe samha, ta fara kwala ihu "jama'a ku taimakeni zai kasheta wallahi zai kashe ta"
jini ne ya fara fita daga bakin samha tun tana iya zagi har bakinta yayi shiru tana jin azaban duka, momy tana janshi hankaɗata yayi ta faɗi akan centre table cikinta ya bugu da centre table ɗin, wani karan azaba tayi tace "nanil you will kill me"
bai ko kalleta ba dukan samha yake, nasir da tun daga compound yake jiyo ihun momy ya karaso da gudu ya shiga falon, ganin momy rub da ciki akan centre table ya dafa kai yace "what happened kuma?"
baibi ta kanta ba yazo yana janye nabil, yace "me tayi maka ne haka?"
yace "a hotel na ganta tana zina da wani kato..."
ai shima nasir dukan ya fara yi mata tako ina, momy ta kasa tashi ga wayarta da yake faman ringing, da kyar taja jiki taje ta ɗau wayar zata amsa call ɗin ya katse, sabon number ne shiyasa bata bi ba, ta fara kiran numbern dady sabida yazo ya raba wannan faɗan, kira biyu be ɗaga ba, ta kara kira har zai katse taji an ɗauka, tace "hello Alaji ina kake?"
cikin canja murya yace "yana wajena"
kallon wayan tayi sannan ta kara sawa a kunne tace "waye kai?"
yace "ɓarawo, na sace mijinki kuma matukar kika bari ƴan sanda suka sani zan kasheshi sabida nima ina tare da ƴan sanda da zaran kin sanar musu nima zasu sanar min daga nan suna mijinki gawa"
a kiɗime tace "dan girman Allah kada ka cutar dashi, dan Allah ka faɗamin me kake bukata wallahi zan baka ko me kake buƙata"
dariya kawai yayi ya kashe wayan, ihun da tayi yasa su nabil sukazo ganin jikinta yana rawa da waya a hanunta, nasir yace "what happened momy?"
bakinta yana rawa tace "your father is kidnapped"
tare sukace "what?"
tace "yanzu na kira an tabbatar min sunyi kidnapping ɗinshi"
tashin hankali suka shiga musamman nasir da yake shine babba, har samha dake kwance jikinta duk jini saida ta tashi tana ɗingishi tazo tace "momy anyi kidnapping na dady? muje mu faɗawa police kada a kashe mana shi"
nasir yace "tabbas mu tafi police station mu kai report"
momy tace "no please wait, yace yana tare da ƴan sanda idan muka faɗa musu zasu faɗa mishi kuma zai kashe shi"
nasir yace "Innalillahi wa inna ilaihiraji'un momy wai me yake buƙata?"
tace "bai faɗamin ba amma ya tabbatar min kada na faɗawa ƴan sanda"
jugum suka zauna kowa yana cikin tashin hankali, basuda gata sai dady idan aka kasheshi zasu rasa rayuwar jin daɗi da suke ciki.
momy ta aje waya a gabanta tayi shiru ɗakin ya zama tsit suna jiran kira, domin sunyi ta kira be ɗauka ba.
nawal a cikin kangon ya ɓoye dady sannan ya dawo gida ya canja kaya a ɗakin megadi wanda shine mallakinshi, bacci ya kwanta yana yi wayar dady a kashe yasa a kasan kayanshi.
har gari ya waye momy dasu naseer babu wanda yayi bacci sai samha ce wacce ta daku iya dakuwa.
nawal da asuba yaje masallaci ya dawo ya fara aikinshi kamar kullum, baiga kowa ya fito a cikinsu ba, murmushi kawai yayi saida ya gama aikin kafin ya shiga ciki sabida gyara ɗakin dady da nasu kamar yadda suka saba mishi tun yana karami, da sallama ya shiga falon duk suna zaune da alama ko salla basu yi ba sunyi jugum da waya a gabansu, durkusawa yayi ya gaisheta ta ɗauke kai, tashi yayi da sandan mopping ɗin zai wuce ciki tace "fita"
juyowa yayi yana kallonta nasir yace "bakaji me tace bane?"
a hankali ya fita ya rufe musu kofan, aje mopper yayi sannan ya koma asibiti domin duba Ammi duk da yasan ba zai ganta ba amma so yake yaga ko kofan ɗakin da aka kwantar da ita ne ko ranshi zaiyi sanyi, haka kuwa akayi ya tsaya a nesa yana kallon kofan yayi shiru, ya jima a wajen kafin ya koma gida yaci gaba da aiki sabida ya saba, saida dare yayi nisa ya tabbatar kowa yayi bacci kafin ya shirya cikin kayan ya koma inda ya kwantar dashi, yana bacci har yanzu, wayan ya kunna yasa tumprint nashi sannan ya kira numbern hajiya naja wato momy, kira ɗaya suka ɗauka dama jira suke ya kira, tace "dan girman Allah ka faɗa mana me kake bukata wallahi zamu baka koma menene"
har zece miliyan ɗari bakwai sai kuma ya tuna idan suka ji labarin shine kuɗin aikin zasuyi zargin shine kuma yasan da wuya su samu miliyan ɗari bakwai a daren nan kuma saura kwana biyu a nemi kuɗin, yace "miliyan ɗari shida"
momy tace "bawan Allah kayi hakuri mu baka miliyan ɗari biyar wallahi shi kaɗai zamu iya baka"
murmushi yayi a ranshi yaji sanyi ze samu kuɗin aikin yace "tsarin da zaku kawo shine yanzu a cikin darennan zaki fito da kanki ki aje a bayan gidanki ke kaɗai sannan idan na ɗauka banga ƴan police ba babu abinda ya faru zan faɗa miki inda zaku ɗauki mijinki"
da sauri tace "to na yadda"
yace "na baki 30min"
katsewa yayi, bayan minti 30 ta kira tace "na aje"
yace "okay"
tashi yayi ya wurgar da wayan a cikin dajin sannan ya tafi cikin garin daidai inda yace ta aje kuɗin, saida ya juya yaga babu kowa sannan ya sunkumi katon jakan da yake cike nak da kuɗi, buɗewa yayi ya tabbatar kuɗi ne a ciki sannan ya tafi inda yake niyan ɓoyewa ya ɓoye, komawa yayi ya ɗauko dady da kanshi ya kaishi har kofan gidan ya kwantar dashi sannan ya shiga ciki ya canja kaya ya kwanta.
sai washe gari suka ga dady kwance ɗaukanshi akayi direct sai asibiti nasir yana kula dashi domin tabbatar da babu abinda ya sameshi.
nawal kuma ya zauna yana tuna inda zai samu sauran cikon miliyan ɗari biyu daya rage, yayi iya tunani ya rasa kuma gobe shine ranan da za'a gama aiki domin ya cika kwana uku.
fita yayi daga gidan domin neman aiki ko zai samu ya harhaɗa kuɗin ba sai yayi sata ba, duk aikin karfi da yayi yau harda gini bai samu ko dubu ɗari ba bale milyan ɗari, zama yayi a karkashin bishiya yana kallon titi har dare ya fara yi, saida ya huta sosai kafin ya tashi zai tafi, covoy ɗin motoci ya gani harda jiniya suna wucewa akan kwalta, ya bisu da kallo sannan yaga na karshe an rubuta government car a jiki, yace "okay governor ne yake wuce wa kenan?"
hanu yasa aka yana wani tunani bayan sun gama wucewa yayi murmushin gefen baki yace "gidan governor shine target ɗina"
komawa gida yayi ranshi fes domin tabbas yau saiya shiga gidan governor yayi sata.

_Jiddah Ce....✍️_
08144818849
[17/08, 11:13 pm] +234 814 481 8849: 🌸🌸🌸🌸🌸
*SHIMA ƊA NE*
🌸🌸🌸🌸🌸


Na
*Jiddah S Mapi*


*Chapter 12*


~Dare nayi yayi shiri cikin kayan yasa hangloves ɗin da mask sannan ya ɗau bindigan daya ɓoye yasa a aljihun wando ya fita, tafiya yake shi kaɗai yana kara rufe kanshi da hulan rigan, yayi tafiya me nisa kafin ya isa, daga nesa yake karewa gidan kallo, so yake yasan ta inda ze fara shiga ba tareda an kama shi ba, yaga security's dayawa kuma a shirye suke daga tsayuwansu za'a gane a shirye suke a koda yaushe, kanshi ya rike yana tunani idonshi kawai za'a iya gani bayan idonshi babu abinda zaka iya gani, murmushi yayi ya fara tafiya, ta bayan gidan yaje yaga babu kowa, bindigan ya ciro yayi harbi sau biyu sannan ya ɓuya, sunji karan harbin hakan ya janyo hankalinsu wajen, duk sukayi hooking na bindigoginsu sukayo wajen, ganin haka yayi sanɗa ya shige gidan ba tareda sun ganshi ba, tafiya ya fara har ya tsinci kanshi a katon falon da yake cike da kayan alatu da duk wani abu na more rayuwa, rike waist yayi yana nazarin ɗakunan sabida sanin ta ina zai fara, idonshi ne ya kai kan hoton dake manne a jikin bango da mamaki yaga an rubuta excellency ALHAJI USMAN MAKAMA, da mamaki yace "kenan nan gidan tsohon governor ne?"
hanu yasa yana shafa gashinshi ta cikin hulan sannan yace "ai governor shine Alhaji sammani kuma ya kamata ace a government house yake wannan gidan tsohon governor nazo, amma hakan ba zai hanani abinda nayi niya ba"
cikin sanɗa yake tafiya har ya isa kofan ɗakin da yakeda tabbacin na matar tsohon governor ne, ya fahimci haka ne ta hanyan takalmin daya gani na mace, a hankali ya tura kofan ze shiga wani tunani yazo mishi, a ranshi yace "nawal bakada hankali ne zakayi sata wuta a kunne? ya zama dole ka kashe wuta"
komawa yayi ya nemi wajen da wutan gidan yake gaba ɗaya, kasa yayi da wutan take wutan gidan duk ya ɗauke, komawa yayi ya tura kofan a hankali ya shiga ciki, tocin karamar wayarshi ya kunna sannan ya fara haska ko ina na cikin ɗakin, matar tsohon governor tana kwance akan gadonta me masifan kyau tana bacci, buɗe side drower yayi nan yaga wasu sarkoki da agogo da zobuna kuma yanada tabbacin na gold ne, kwashewa yayi yasa a cikin jakan daya taho dashi na baya, cikin bacci tayi juyi taji kamar inuwan mutum ne a kanta, buɗe ido tayi a hankali, ganin wuta a kashe toci a kunne yasa ta tashi a firgice ta kwala ihu tace "taimako jama'a taimako ɓarawo ne"
nawal jin haka ya tashi da gudu yayi waje, jin ihunta yasa duk mutanen gidan suka tashi harda mijinta da personal bodyguard nasu, ya kira security jin karan harbi yace su shigo da kwai matsala, jallabiya ne a jikin Abba me taushi, ɗakin suka nufa direct, duk suka kunna tocin wayoyinsu sabida wutar a kashe take, nawal ganin ta rikeshi ya nunata da bindiga, a kunnenta yace "zan fasa kanki idan kika kara ihu"
jikinta ne ya fara rawa, tunda take bata taɓa jin tsoro irin na yau ba, idanunta a waje suke tsaban firgici, bindigan yasa a kanta yayi shirin harbi, ya kashe tocin ɗakin ya garwaye da duhu, jin muryan maza yasa ya cire bindigan daga kanta ya ɓuya a bayan kofa, a lokacin suka shigo suna haskawa, tana tsaye jikinta yana rawa tana kallon inda ya ɓuya, a hankali yaja kafarshi ya fita, bodyguard yace "MAMI ki nutsu babu abinda zai sameki zamu kamashi"
jikinta yana rawa take hawan jininta ya tashi, tana jin jiri tace "AHLAM wallahi bindiga ne a hanunshi kasheni yazo yi...."
cikin son kwantar mata da hankali yace "ba zai kashe ki ba ina tare daku"
tace "zan kwanta ahlam jiri nake ji"
taimaka mata yayi ta kwanta akan gadon, fita yayi yabi bayan Abba wanda ya jima da fita, Abba waya ya kira yace "akwai ɓarawo a gidannan a turo security's su shigo zamuyi searching ko ina a cikin gidannan domin wallahi ba zan kwana da ɓarawo ba"
kafin ya katse wayan masu tsaron gidan sun shigo dayawa suke kuma kowanne yana ɗauke da bindiga, nawal tsoro ya cika zuciyanshi ya gama sawa a ranshi lokacin rabuwanshi da Amminshi yazo, domin wannan masu tsaron idan ya shiga hanunsu yasan kwananshi ya gama karewa, hawaye ya fara yana rakuɓe a jikin bango yana jin ihun da Abba yake yiwa masu taro na meyasa suka bari ya shigo, me amfaninsu harma da cewa zai koresu su duka sun bar aiki a gidanshi, da alama yanada mugun zafi domin har stair yana girgiza da yake maganan.
cikin daka tsawa yace "aje a kunna wutan gidan domin nasan kashewa yayi, banzaye har ɓarawo ya fiku dabara harda kai Ahlam me bada tsaro na musamman"
jiki na rawa sabida sun san halinshi ko yaran cikinshi mugun tsoronshi suke, basu taɓa zama suyi magana dashi a gidan babu wanda ya isa yayi koda kwakkwaran motsi idan Abba yana nan, babu wanda ya isa ko tari yayi me kyau matukar abba yana cikin gidan, mugun mafaɗaci ne wanda har makota tsoronshi suke ji balantana ƴan cikin gida, ƴaƴanshi daga makaranta babu inda suke kara zuwa har karatun Islamiya a gida ake koya musu, yanada tsari sosai kuma baya ɗaukan raini, masu aikinshi da zaran sunga ya fito jikin kowa ya fara rawa kenan har sai ya wuce suke samun nutsuwa, matarshi batada sakat hakan yasa ma batada yawan surutu sabida bala'i da masifanshi, ƴaƴanshi kuma ba'a magana idan sun ganshi kamar sunga dodo.
kafin a kunna wutan nawal yace "gara na gudu kafin su kunna wuta koda sun kamani haka Allah ya tsara"
fitowa yayi zai gudu Abba ya rikeshi cikin duhun yace "na kamaka red handed"
ganin har yanzu da duhu ya ture hanun Abba ya fara gudu, binshi Abba ya fara buɗe kofan wani ɗaki da baisan ko nasu waye ba yayi, faɗawa yayi a ɗakin ya rufe, a lokacin aka kunna wutan gidan haske ya gauraye ko ina, ido huɗu sukayi da wata kyakkyawar budurwa wacce ta ɓuya a bayan gado ta rufe baki sabida kada tayi ihu, tunda ya shigo gidan taji ihun mami ta ɓuya, masha Allah wannan budurwa tafi kyau kyau, fara sal tanada ɗan kiɓa irin ɓul ɓul ɗinnan, rigan bacci ne a jikinta milk color yayi bala'in karɓan skin ɗinta, gashinta a barbaje da alama bacci take yi taji ihun ɓarawo, idanunta masu girma kamar madara ta zuba mishi, kyawawan yatsun hanunta a bakinta ta rufe, ganinshi ido da ido da wannan dressing ɗin ya tabbar mata shine ɓarawon daya shigo
End Ads