ruwa, a takaice yake magana baya da surutu, mutumin ya mikawa police waya, jim kaɗan yace "a saki maman wannan yaron"
ganin ruwan sama ya sauka sosai jaririya da mamanta sun jiƙe ya shiga mota sabida gudun mura, atake police ya kira yace a saki ammi, nawal be san zancen da suke yi ba, yana zaune a inda ya mayar gidanshi yaga sunja motar sun bar wajen, ruwan ne yake karuwa sosai akeyi, kanshi ya ɗaura a gwiwa yayi shiru yana jin karan ruwan da har yana taɓashi, ji yayi an ɗaura hanu a kanshi, ɗago kai yayi suka haɗa ido da ammi, ta jike jigib a cikin ruwan, waro ido yayi yace "Ammi? kece?"
gyaɗa kai tayi tana hawaye tace "tabbas nice nawal"
tashi yayi ya faɗa jikinta suka kanƙame juna, be damu da ruwan dake dukansu ba murna kawai suke yi, tace "nawal muje kada ruwan ya janyo mana zazzaɓi"
yace "ammi kince ruwa alkhairi ne a rayuwata gashi ana ruwa aka sakeki ammi mu bari ruwan ya dake mu"
murmushi tayi ta tsaya ruwan yana dukansu saida aka ɗauke ruwa cat kafin ta rike hanunshi tace "muje nawal"
yace "ammi ina zamuje? gidanmu na da zamu koma?"
girgiza kai tayi cikin sanyin da takeji tace "a,a nawal camp na ƴan gudun hijira zamu je"
yace "to ammi"
baya son koda wasa yayi mata musu shiyasa duk abinda ya faɗa yana amsa mata da eh.
Rumfan ƴan gudun hijabi sukaje suka saje cikinsu suka nuna suma gudun hijira sukayi, saide tun daga yau sun gane ba zasu iya zama ba sabida babu me taimakawa ga kuma rashin lafiya da akeyi sosai a wajen ga mutanen sunyi yawa cuta zaiyi saurin yaɗuwa, nawal da ammi baransu suke yi sabida su samu abinda zasu ci su kuma nemi gidan haya, ammi ce take rike musu kuɗin idan sunje bara, bata saba da kowa a camp ɗin ba hakan yasa suka haɗa ƴan kuɗaɗe suka koma wani ƙaramin gida suna cigaba da yin bara suna samun kuɗin kashewa.
wajen da suke bara a gefen titi ne nesa da gidansu tun safe idan sun fita se yamma suke dawowa.
ammi cikin zazzaɓi take baran yau nawal ganin haka yace "mu tafi gida ammi"
tace "karka damu jikin be damuna sosai"
yace "ammi bana miki musu amma mu tafi dan Allah"
tace "to shikenan mu tafi"
tafiya sukayi shi yayi musu girki ya haɗa mata ruwan wanka tayi wanka taci abincin, jikin yaki sauki sai zafi yake yi, cikin damuwa yace "ammi muje ayi miki allura"
cike da tausayinshi tace "a,a ka bari zanyi sauki"
zama yayi a kusa da ita yayi tagumi yana jin tausayinta kamar ya maida ciwon jikinshi haka yake ji.
cikin dare jikin ya kara tashi washe gari da sassafe ta yanke shawaran zuwa chemist domin yin allura ko zata samu sauki, tafe suke tana rike da hanunshi a hankali take tafiyan sabida jikinta babu daɗi, cikin sanyin murya tace "nawal zan saka a makaranta"
cikin jin daɗi yace "nima zan fara zuwa karatu Ammi?"
ta gyaɗa kai tace "eh"
har sukaje tayi allura suka dawo yana mata maganan makaranta, saida jikinta yayi sauki kafin ta kaishi makarantar gomnati tayi mishi register da uniform da sauran kayan zuwa school ɗin, a nufinta idan taje tayi bara ta samu kuɗi saita biya mishi kudin karatu, Allah yasa tana neman aiki a duk inda ta gani, kuma ta samu yin wanke wanke awani hotel dake kusa dasu, bata damu da hotel ɗin ba abinda ya kaita kawai take yi, da kanta take kaishi makaranta kuma da kanta take ɗaukoshi, yana gane karatu Alhmdllh babu laifi kanshi yana ja, yauma kamar kullum ta ɗaukoshi daga school tana rike da hanunshi suna tafiya, ta kula tunda suka fara tafiya bece komai ba, duk da dama baya magana sosai iyaka ya kalli mutum ya sunkuyar da kai ne kawai, ta ɗan murza hanunshi a nata tace "nawal ɗin ammi meya faru yau kayi shiru? ko yunwa kake ji?"
girgiza kai yayi kamar zeyi kuka yace "ammi waye babana?"
gabanta ne yayi mummunan faɗuwa jin tambayan da nawal yayi mata, ɗauke kai tayi tana kallon titi tace "laaa nawal ɗina kaga wata mata me siyar da baby ɗin yara"
kallo yayi sannan ya daka tsalle yace "yee ammi zaki siyamin baby mace?"
dariya tayi na yaƙe sannan tace "meyasa kakeson mace?"
yace "sabida na aureta"
yarantarshi yasa tayi dariya kawai sukaje ta siya mishi karamin baby me kyau, tafiya sukayi bayan ta biya kuɗin, wasa yake da gashin baby ɗin me tsayi yace "ammi matata zata zama da gashi?"
tace "eh mana zata zama da gashi kamar kai, kuma zaka samu kyakkyawa me hankali wacce zata kula da kai koda bayan na mutu"
yace "Ammi ba zaki mutu ba saide mu mutu tare"
murmushi kawai tayi, duk da ya manta maganan ita bata manta ba yana ranta, wani amsa zata bashi idan ya girma yayi mata wannan tambayan?
ranta ya kara tsinkewa batasan amsan da zata bawa nawal ɗanta ba.
be kara mata tambayan ba hakan yasa tayi addu'a Allah ya mantar dashi kada Allah ya bashi ikon tambayanta, tsaye yake a gaban black boat yana karanta abinda malama ta sashi karantawa, wani kalma ɗaya ya hanashi furta kalman me kyau, da kyar ya harhaɗa ya faɗa, malama tace a tafa mishi, tafi akayi mishi aka kira malama ta fita ze koma ya zauna yaran aji suka kira sunanshi NAWAL RAHMA shine sunan da yake amfani dashi, juyowa yayi domin yaji dalilin kiran, yaron yace "yaron mace"
dariya suka kwashe dashi, duk da yara ne sosai kanana amma abin yaci ranshi, baya magana hakan yasa yaje ya zauna yayi shiru, wata yaji tace "ai shi bayada baba macece ta haifeshi shiyasa yake amfani da sunanta, mamana tace akwai wanda ake haifansu cikin shege basuda asali"
dariya suka kuma yi, zuwa yanzu idonshi ya cika da hawaye, yaran ajin suna jin haushin shi sabida yanada ilimi kullum malamai sunanshi suke kira, gashi duk ajin babu wanda ya kaishi kyau, kai duk school ɗinma babu me kyawun nawal, jin dariyan da suke mishi suna cewa baida baba shi cikin shege ne yasa ya kifa kanshi jikin table ya fara kuka, a hankali yake kukan sai shesheƙa yake.
har aka tashi ya share hawaye ya ɗau jakanshi ya fita, ammi ya gani tana jiranshi a kofa kamar kullum, yazo ya rike hanunta tace "nawal ɗina ya kake?"
a takaice yace "lafiya"
shiru tayi sabida yanayinshi ya canja, har suka isa gida baiyi magana ba bata wani damu ba sabida haka nature ɗinshi yake baya yawan magana, washe gari yaci abinci tace "nawal baka shirya ba, ba zaka makaranta bane?"
girgiza kai yayi yace "yau ba zanje ba ammi kaina ciwo"
tace "sannu nawal"
rikeshi tayi ta ruɗe tana mishi sannu, a ranshi kuma lafiya ƙalau yake bayason zuwa ne sabida takuran yaran school ɗin da suke mishi na cewar baida baba sai mama kaɗai.
yayi kwana uku a haka idan tace yaje school sai yace baida lafiya, har ta gane beson zuwa ne, ta sashi dole ya shirya ta kaishi, yana zuwa ya zauna a gefe ya takure yana kallon karatun kan boat, har aka tashi be wani sake ba, baida aboki, har ya fita ya tuna ya manta jakanshi da takaddunshi a ciki, da gudu ya koma domin ɗaukan jakan, turus ya tsaya ganin babu hakan, kallon yaran dake zaune kusa da bencin yayi, cikin yanayinshi na tsoro da rashin son hayaniya yace "ina jaka na?"
duk suka mishi shiru, kuka ya fara yana cewa "ku bani jakana Ammi na zata min duka"
dariya sukayi ɗayan yace "ba zamu bayar ba ko zaka kira mana babanka ne?"
shiru yayi yana kallonsu, sai kuma yace "zanje na faɗawa headmaster"
sukace "kaje ka faɗa ɗan mace kawai"
fita yayi yaje office na headmaster ya gaisheshi cikin ladabi kamar yadda ammi tace ya rinƙa gaida manya, daga nan yace "kaga wasu sun ɗauke min jakana ko? kuma suna cewa wai banida baba ni shege ne"
ya gyara farin glasses nashi daya karkace yace "jeka kiramin su"
fita yayi yaje ya kirasu, tare sukazo suka durkusa a gabanshi, ashe ɗayan yaron ɗan headmaster ne kuma yana jin haushin nawal da yafi ɗanshi karatu kullum shi yake zuwa na ɗaya zuwan nawal yasa ɗanshi ya fara zuwa na biyu, yace "meyasa kuka ɗauke jakanshi?"
duk sukace basu ɗauka ba, headmaster yace "muje idan har anga jakan a wajen to shi zaisha duka guda goma, idan kuma ba'a gani ba ku zaku sha duka goma goma"
duk sukace sun amince, aka taru da headmaster da bulala suka nufi class ɗin, ganin jakan akan bencin yasa nawal waro ido yana kallon su, headmaster yace "yawwa kaine da laifi kai zamu yiwa duka"
yana kuka yana cewa bashi bane aka rikeshi yayi mishi bulala goma masu zafi, take jikinshi ya farfashe ya fara jini farin fatarshi ya koma jajur, headmaster yace "ai ba karya suka maka ba dama ance duk wanda ba'a haifa da uba ba yana yiwa masu uba sharri yana so ace sune da laifi, idan kanada uba ba zakayi sharri ba, ko ba'a gidan karuwai aka samu cikinka aka haifeka ba?"
kanshi kasa be ɗago ba saide hawayenshi yana sauka har kan kafar headmaster, yaran suna mishi dariya, headmaster yace "idan kanada uba me sunanshi?"
yayi shiru, ya kara daka mishi tsawa yace "me sunanshi nace? meyasa kake amfani da sunan mace ina ubanka?"
yayi shiru beyi magana ba, suna mishi dariya suka barshi a wajen, ya kasa tashi yafi minti ishrin a durkushe beda niyan tashi.
*Shima ɗa ne complete is ₦400 via 8144818849 Hauwa shuaibu mapi moniepoint, your evidence via 08144818849*
~Yana durkushe babu me lallashinshi, har yayi kukan yayi kukan ya gaji, rahama tana sanye da atamfar data koɗe sosai daga green harta koma fari, da farin guntun hijabi a jikinta, tayi kyau sosai sai tare hasken ranan daya fuskantota take yi, abinka da farin fata batason rana sosai sai tarewa take da dogayen yatsan hanunta masu kyau, ganin be fito ba har ɗalibai sun gama fitowa tace "yau nawal lafiya ne fito ba? ko dai rubutu ne be gama ba?"
tsaki kaɗan taja ganin be fito ba har yanzu, shiga ciki zatayi ya fito, da mamaki taga ya ɗauke kai be kalleta ba, murmushi tayi tace "ɗana har nayi zaton baka gama rubutu bane"
shiru yayi, ganin haka taji gabanta yana faɗuwa, murmushi tayi ta durkusa kasa a gabanshi ta riko hannayenshi tana kallon fuskanshi, a hankali ta manna karamin bakinta a goshinshi tayi mishi kiss me kara tace "yau ɗana fushi yake yi shiyasa be yiwa amminshi magana ba, na dafa maka indomie nasan idan ka gani zakayi farin ciki"
shiru yayi ya kauda kai yana hawaye, juyo da face nashi tayi ta share mishi hawayen sannan ta rungume shi tace "ka daina kuka karka karyamin zuciya"
tashi tayi ta rike hanunshi suka fara tafiya, har sunyi nisa yace "ammi"
tace "na'am nawal"
yace "me ake nufi da shege?"
jiri ta fara ji yana kamata, da kyar ta harhaɗa magana tace "me kace?"
yace "menene shege?"
murmushi tayi ta durkusa a gabanshi ta rike hanunshi tace "nawal shege yana nufin yaro me hankali, yaro me nutsuwa wanda ze samu mata kyakkyawa da zata kula dashi idan mamanshi bata raye"
fizge hanunshi yayi ya juya baya yace "ba haka ba ne, kullum haka kike cewa amma nasan karya kake min"
tana kallon bayanshi tace "nawal nice nake karya?"
kama hanunshi tayi ya fizge da karfi yace "karya ne, ance banida uba, yau sunce babu aure kika haifeni"
jikinta yana rawa zata rikeshi yayi wurgi da jakanshi ya juyo yana kallonta idanunshi sunyi jajur, da mugun mamaki take kallon yadda jijiyoyin kanshi suka tashi, kamar ba yaro karami ba, yana hawaye yace "kullum sai ance min shege, sai abokaika sunce ni banada baba"
cikin ruɗewa tazo ta rike hanunshi muryanta a sanyaye tace "nawal akan titi fa muke mutane suna kallonmu"
da ihun da yasa ta toshe kunnenta yace "to meyasa nake amfani da sunanki? me sunan babana? ina yake? ina ƴan uwanshi? meyasa kowa da sunan babanshi ni kuma da sunanki meyasa?"
hannunta toshe da kunnenta idanunta ta rufe saboda bata taɓa ganin nawal cikin wannan halin ba, yana magana yana kallonta babu ko shakka, juyawa yayi ya fara tafiya ranshi yana ƙuna, har yayi nisa be juyo ba, a zatonshi tana bayanshi sabida idan yana fushi yayi gaba tana binshi a baya har su isa gida kafin su shirya, ihu yaji a baya, da sauri ya juyo, amminshi ya gani a kasa a sume, bayan tafiyanshi ta cire hanu a kunnen tana kiran sunanshi amma muryanta yaki fita, bin bayanshi zatayi kirjinta ya bada sauti marar daɗi, faɗuwa tayi kasa take mutane suka yo kanta, da gudu yaje yana ture mutanen da suke kanta yana cewa "ammi ki tashi, ammi ki tashi dan Allah banaso ki mutu dan Allah ki tashi Ammi na"
wani mutum daya tsaya da mota yazo wajen ya kallesu sannan yace a sata a mota ya kaita asibiti, a mota suka sata sannan mutum ɗaya ya shiga motan shima nawal ya shiga suka kaita asibiti, emergency aka karɓeta, mutumin ne ya janyo nawal dake kuka yana shafa kanshi yace "kayi hakuri ka daina kuka babu abinda ze sameta"
shiru yayi a ranshi yace "ba zan kara yiwa ammi wannan tambayan ba"
har ta farfaɗo yaje da gudu ya rike hanunta yace "ammi ba zan kara miki wannan tambayan ba wallahi ba zan kara ba Ammi kinji?"
shiru tayi tana kallonshi, a ranta tace "ya rabbi kada kasa ya tashi da wannan ɓacin ran irin wanda ya nuna min yau"
mutumin ne ya shigo ya zauna yana mata sannu, murmushi kawai tayi mishi sai kallon nawal yake, da kanshi yaje yayi musu siyayya da ganin mutumin ka san me kuɗi ne sosai domin yanayinshi ya nuna, har kwana uku shi yake kula da ita da nawal ɗin abinci da komai yana kawo musu sannan duk abinda aka bukata yana badawa na kudi da sauran bukatu, godiya take mishi, yau aka sallamesu suka shiga motarshi domin kaisu gida, nawal ne a gaba kusa dashi yace "nawal yau ba zamu zauna tare ba idan na kaiku gida shikenan mun rabu"
nawal yace "zaka rinƙa zuwa dubamu?"
yace "zan zauna daku ma na har abada"
yace "ta yaya?"
kallon rahama yayi ta cikin madubi yace "idan amminka ta yadda ta aureni zaka zama ɗana zan kaika school zan nuna maka gata kamar yadda kowane ɗa yake samu, a zaman da nayi daku a asibiti na fahimci komai da yake gudana a rayuwarku zanso ta amince ta aureni"
sunkuyar da kanta tayi, nawal yayi dariyan yara na jin daɗi yace "ammi nima yanzu zan samu baba, yace zai aureki ya kaini school kinga nima za'a daina cewa banada baba"
shiru tayi amma tayi murmushi kawai, ran Alhaji Umar yayi sanyi ganin yadda tayi murmushi ya tabbatar zata amince da aurenshi.
koda ya kaisu gida kayan abinci ya zuba musu da kudi masu yawa ya bata da waya ƴar karama wanda zasu rinƙa gaisawa.
nawal yaki zuwa school hakan yasa ma ta amince da auren Alhaji Umar yau aka ɗaura aure aka kaita gidanshi wanda yake da mata ɗaya da yara biyar, tareda nawal suke zaune a ɗakin tayi shiru tana tuna maganganun da matarshi ta faɗa mata a lokacin da za'a shigo da ita gidan "sabida kinada kyau bashi ze nuna Alhaji ze soki ba, alhaji nawa ne ni kaɗai da ƴaƴana, sannan ki sani agola ba zai taɓa zama na tsawon lokaci a wannan gidan ba, gara tun wuri ki nemi inda zaki aje ɗanki"
maganan ya tsaya mata a rai amma tayi addu'a a ranta kawai ta barwa Allah komai.
zamanta da nawal a gidan ya fara gagara domin Alhaji yana son nawal sosai koda yaushe so yake ya zauna kusa dashi, bayason nawal yayi nisa dashi abinda yake tsaya mata a rai shine babu abinda ya shiga tsakaninta da Alhaji koda ranan girkinta idan ya shigo zece sai an ɗauko nawal ya kwana tare dasu, haka ze kwana rungume da nawal, nawal yayi kyau sosai ya kara zama kamar ɗan larabawa gashinshi ya kara tsayi da tsantsi, a koda yaushe addu'a take mishi bata bari ana yabonshi sabida tana tsoron bakin mutane, bata bari ya fita idan ba makaranta ba sai islamiya sabida kyawunshi yayi yawa, sam hankalinta baya kwanciya, saide idan Alhaji ya fita to yaranshi sun sa nawal a gaba kenan daga me duka sai me zagi, sam yaron baya samun kwanciyar hankali, koda yaushe a tsorace yake da anyi magana ze firgita, kullum saide ya ɓuya a ɗaki yaki yadda ya fito duk yadda zatayi dashi zece ba zai fito ba, gashi shiru shiru baya son magana zakayi magana ɗari idan yaga dama ze amsa sau ɗaya, wani kuma ya zuba maka ido kana magana sai ka gama ya tashi ya tafi bama ze amsa ba, abin yana damunta da farko halinshi ne haka amma yanzu ya haɗu da takura da wahala, kwance suke akan gado suna bacci, yau weekend ne shiyasa yake gida saida rana ze tafi islamiyya, sallama akayi Alhaji Umar ne ya shigo ɗakin ya tsaya a kansu ya kurawa nawal ido yana kallonshi babu kyaftawa, ammi dake bacci a hankali ta buɗe ido jin inuwan mutum a kansu, kallonshi tayi da sauri ta tashi tace "laa yaushe ka shigo?"
abin mamaki bema san tana magana ba idonshi akan nawal yana yiwa yaron wani irin kallon da bata gane kona menene ba, saide taga yana lasan lips nashi na kasa, gabanta yayi mummunan faɗuwa, da sauri ta rungume nawal tana kallon Alhaji, firgigit yayi ganin ta rungume yaron, yace "rahama nazo ne fa na duba ki da yarona naga ya kuke kuma naga kuna bacci"
murmushin karfin hali tayi sannan tace "Allah sarki ai nasan yau baka zama a gida shiyasa nayi mamaki"
yace "eh wlh dama nazo ne na ɗauki nawal mu tafi shopping"
ras ras taji zuciyanta yana tsinkewa, haka kawai taji bataso ta barsu su biyu, ta kalli nawal dake bacci da innocent baby face nashi, tace "Allah sarki Alhaji gaskiya kana matukar son ɗanka sosai, na gode da kulawan da kake bashi, yau jikinshi yayi zafi tun ɗazu yake kukan zazzaɓi har nace zan kiraka amma na bari sabida banaso