zataci shi ta bawa Abida, karɓa tayi batasan shine iyaka ba tace "na gode"
har ta fita sai kuma ga dawo, tace "ki kula da ɗanki sosai saboda wannan gidan ana sace yara, matar data buɗe wannan gidan zata iya ɗaukanshi a yadda yake jariri taje ta girmar dashi ta fara lalata dashi, bama wannan ba koda yana yaro karami zata iya koya mishi yadda zaiyi lalata da ita hakan ya faru akan idona idan so samu ne a ki ɓoye ɗanki kada ki bari tasan kinada yaro, sabida zata lalata rayuwarshi sannan tana zuwa kowane karshen wata, abinda yasa baki ganta ba shine taje kasar waje jiya ta dawo"
a firgice ta kalleta, taɓe baki abida tayi tace "kwarai abinda yasa na faɗa miki sabida naga kinada hankali abincin da zakici kika ɗauka kika bani shiyasa na faɗa miki ki kare ɗanki"
tafiya tayi, ido ta zubawa yaron tana kara juya maganganun a ranta, yaron da take jinshi kamar rayuwarta ba zata yadda wani mugun abu ya sameshi ba, tun yana karami yake da wannan masifaffen kyawun ya zama dole ta kareshi ba daga matar gidan ba har mutanen waje, buɗe ido yayi ya kalleta, dariya taga yayi mata, hawaye ya cika mata ido itama ta mishi dariya tace "yau zansa maka suna ɗana, karka damu da rashin uba da kuma haifanka da nayi bata hanyan aure ba, Inaso ka sani kaima ɗa ne kamar kowa"
share hawaye tayi tace "kai kyauta ne Allah ya bani hakan yasa zansa maka suna NAWAL ma'ana KYAUTA"
kafin ta karasa rufe baki ruwan sama ya sauko da karfi, kallon sama tayi ta fito dashi zuwa waje cikin farin ciki ta tsaya a tsakar gidan ruwan sama yana wankeshi, murmushi tayi tace "Allah ya amsa wannan sunan naka na kyauta shiyasa ya kara saukar da ruwan sama na kyauta a lokacin dana raɗa maka suna"
ɗagashi tayi sama ruwan yana wankeshi tace "Allah ka wankemin ɗana, kasa ya zamo kyauta a cikin al'umma, kasa ya kare rayuwa daga sharri, kasa ya zamo garkuwa a rayuwar bayinka"
saukeshi tayi taga yana dariya, murmushi tayi tace "yara idan ruwan sama ya dukesu kuka suke amma shi nawal dariya yake ina fatan ruwan sama ya zame mishi kariya a rayuwarshi, ina fatan ya samu duk abinda yake so a rayuwa a cikin ruwan sama"
*Shima ɗa ne is 400 via 8144818849 Hauwa shuaibu mapi moniepoint, evidence via 08144818849*
~Tun daga ranan bata kara fita dashi ba duk inda zataje a ɗaki take barinshi sabida so take ta kareshi daga kowane sharri, yau tun safe take bacci sabida gajiya yau babu zuwa aiki shiyasa take hutawa, hayaniya taji a gidan da sauri ta buɗe ido ta tashi, lekawa tayi taga faɗa ake akan mace harda wuka, rufe ido tayi ganin yanke yanke da suke ta koma ta kwanta shiru tayi kamar bata ɗakin.
haka take rayuwa da ɗanta wanda har ya fara girma sannan yana kara kyau fiyeda yadda ta haifeshi, hakan yana daga cikin dalilin da yasa bata fita dashi sabida bakin mutane ita kanta tasan kyau shine dalilin shiganta wannan halin, a ɗaki take barinshi duk inda zataje, tasan da batada kyau da yanzu tana tare da iyayenta da kannenta, share hawayen tayi tace "tabbas KYAWUNA JARABTA TA bana fatan kyawun ɗana ya zama mishi jarabtarshi"
haka har yaron ya fara wayo a gidan, matsalanta dashi yawan tambaya duk inda taje ta dawo sai ya sata a gaba yana tambaya ina taje, idan ta faɗa kuma ya fara mata tambayoyi, shiru tayi mishi tana cin abinci, yace "Ammi?"
tace "na'am nawal"
yace "meyasa kullum ina ɗaki?"
tace "sabida banaso ka mutu"
ze kara wani tambayan tace "shiru"
shiru yayi har ta gama cin abincin sannan tayi salla ta kwanta yana gefe yana wasa tunani ta rinƙa yi har bacci ya ɗauketa.
washe gari zata fita aiki tace "na tafi nawal"
yace "ammi yau zan biki"
girgiza kai tayi tace "a,a nawal sai wani lokaci"
zaiyi magana kawai ta fita,
yana zaune a ɗakin tun safe har yamma, ji yayi muryan mutane dayawa a waje, buɗe kofan yayi yadda yaga tana buɗewa idan zata fita, ya leka sabida ta hanashi fita, caraf idonshi ya haɗu dana hajiya bilkisu wacce take sanye da bakin glasses, sauke glasses ɗin tayi tana kallonshi, tace "wow wannan ɗan waye?"
duk sukayi shiru sabida sun san ana ɓoyeshi hakan yasa bata sanshi ba batama taɓa ganinshi ba duk zuwanta gidan, da hanu tayi mishi alaman yazo, make kafaɗa yayi yana kallonta da idanunshi farare masu hasken blue a ciki, tamkar ɗan turawa musamman gashinshi data gani a harɗe, ze rufe kofan tasa hanu ta rike, yace "ammi ta hanani zuwa"
hanunshi zata rike ya fizge, murmushi tayi tace "tunda nake da wannan gidan ban taɓa ganin kyakkyawan halitta irin wannan ba, zanso ganin wacece mahaifiyarshi"
kuka ya fara ganin taki sakin hanunshi, kira tayi wasu maza suka shigo suka ɗaukeshi tana biye dasu suka fita, a wani jeep baki suka sashi sannan itama ta shiga suka bar wajen, ihu yake mata a motan yana kiran Amminshi, maida glasses nata tayi tana kallonshi.
saida ta biya kasuwa kafin ta dawo gida a gajiye, ganin kofan a bude yasa tace "ya akayi nawal ya buɗe kofan?"
shiga tayi, ledan hanunta ne ya faɗi ganin babu shi a ɗakin, dudduba ko ina ta fara a haukace take tambayan ina nawal?
duk cikinsu babu wanda ya amsa mata, kuka ta fara tana neman nawal tana bi kowane ɗaki tana ɗaga musu labule tana kiran nawal nata, zama tayi daram a cikin gidan ta ɗaura hanu aka tace "na shiga uku nawal ina ka shiga? nawal meyasa zaka tafi ka bar Amminka?"
Abida ce ta shigo gidan tana sanye da riga da wando, kallonta tayi tace "meya sameki?"
tana kuka tace "banga nawal ba na tambaya kowa babu wanda ya amsa min banga nawal ba abida"
fashewa tayi da kuka, abida tace "hajiya bilkisu tazo ne?"
da shike suna tsoronta suka amsa mata da eh, kallon rahama tayi tace "dama na faɗa miki ki kare ɗanki daga sharrin wannan matan amma baki jini ba, Allah ya bawa ɗanki kyau da hajiya bilkisu ba zata iya kyafta ido a kanshi bataji tana sanshi ba gashi tazo ta tafi dashi, taimako ɗaya da zan baki shine kada kije inda take ki hakura domin zata iya sa a ɓatar dake"
shiru rahama tayi tana kallonta har ta gama maganan, zata tafi tace "abida"
tsayawa tayi, tace "ki taimaka min koda shine karshen taimakon da zakimin dan Allah ki faɗamin ina gidan hajiya bilkisu yake"
shiru tayi tana kallonta, sai kuma ta kalli gefe da gefenta taga babu me kallonsu, cikin kasa da murya ta faɗa mata inda gidan yake, godiya tayi ta tashi, duk kiran da take mata bata juyo ba tafiya kawai tayi, bata cikin hayyacinta har ta shiga mashin domin zuwa gidan.
garin gombe yanada girma ba lalle ta gane inda zataje ba sabida bata fita.
Nawal yayi kuka har ya gaji, babban gida ne me matukar kyau suka nufa aka buɗe musu gate suka shiga, buɗe mishi mota tayi ya fito yaki fita, hanunshi ta damko ta fito dashi, yana tirjewa har ta shiga dashi ɗakin dake da bala'in kyau, shiga ciki tayi bayan ta rufe kofan ta shiga bathroom tayi wanka ta fito da towel ɗaure a kirjinta, yana zaune a kasa ya takura kanshi ya ɗaura kanshi akan gwiwanshi yana kuka, a gefenshi ta zauna ta zuba mishi ido, yanada bala'in kyau ga wani kwantaccen gashinshi dake tafiya da imaninta, hanu tasa a kanshi zata shafa yayi baya yace "nikam karki taɓani"
dariya tayi sannan tace "kyakkyawan yaro tunda aka haifeka a bariki a barikin ma a gidan karuwai ba zaka iya gujewa asalinka ba, ko bakayi yanzu ba zakayi a gaba, gara ka hakura na koya maka kaga zaka tashi da kwarewa"
mannewa yayi da bango yana girgiza kai, duk da be fahimci me take cewa ba amma yasan abinda amminshi kullum take cewa ne babu kyau kada ya kuskura ayi mishi, ganin ta fara rabashi da kayanshi ya fara ihu, rufe bakinshi tayi saida ta rabashi da kayan sannan ta tashi cikin tafiyan da take girgiza jiki taje ta kashe wutan ɗakin, ganin duhu a ɗakin ya kara ihu yana birgima a kasa.
rahama cikin tashin hankali ta fito daga mashin ɗin ko kuɗin bata bashi ba, yana tambayanta ma ko kallonshi batayi ba, gate ɗin da abida tace mata shine gate ɗin gidan hajiya bilkisu ta fara bubbugawa ganin baya buguwa mata da kyau ta ɗau dutse ta fara buga kofan da karfin da Allah ya bata, megadi ne ya buɗe yana mata kallon sama da kasa yace "me kike bukata?"
tureshi tayi ta shiga a guje sabida tasan zasu hanata shiga, yana binta yana cewa "ki tsaya ki gaya mana wacece ke?"
ganin ya rike mata gefen hijabi ta bangajeshi ta shiga ciki, kofan ɗakin ta tura ta shiga, jikinta ne yayi sanyi jin ihun da nawal yake yi har muryanshi yana dishewa, kasa karasawa tayi jikinta ya fara rawa, a hankali take takawa zuwa ciki, hajiya bilki taji tana wani irin nishin data kasa gane na menene, a hankali ta buɗe kofan bedroom ɗin ta rufe ido sabida batason ganin nawal a wani halin da zaisa ta samu bugun zuciya, juyowa hajiya bilki tayi domin ganin wani me karfin halin ne ya shigo mata ɗaki babu excuse, nawal ganin amminshi ya gantsara mata cizo ya tashi da gudu yazo inda Ammi take ya rungumeta, jikinta yana rawa tace "nawal me tayi maka?"
yana kuka yace "ammi ki kaini gida tana min wani abu kuma ina jin zafi"
jiri ta fara ji, ta rike hanunshi ta kasa magana kawai take janshi zuwa waje.
hajiya bilki ta tashi da bargo a jikinta tazo ta rike hanunshi, rahama ranta yana tafasa tace "sakeshi"
"bazan sakeshi ba, ubanwa ya baki daman shigowa gidannan har cikin ɗakina?"
tace "ki sakeshi nace"
tace "ba zan sakeshi ba saina gama abinda zanyi dashi"
sakin hanun nawal tayi ta juya baya kamar zata tafi, nawal yace "ammi ki rikeni zata kasheni"
flower ves dake kusa da bakin kofa ta ɗauka, cikin zafin nama ta juyo ta kwala mata akai, rike kanta tayi tana kallonsu ta fara silalewa kasa, faɗuwa tayi tim daga nan bata kara motsi ba, nawal yace "ammi ta mutu?"
tace "mu gudu nawal nima ban sani ba"
hanunshi ta rike suka fita a guje, saide abinda ta gani yasa ta tsaya turus, police ta gani sun kewaye gidan, jikinta yana rawa take kallon nawal, ta saki hanunshi ganin police ɗaya ya shiga ciki, tace "nawal ka gudu duk yadda za'ayi kada ka tsaya sai inda Allah ya tsayar da kai"
shiru yayi domin ko zai mutu ba zai iya tafiya ya bar amminshi ba, koma meya sameta zasu zauna tare.
police ya fito yace "tabbas ta kasheta domin bata raye ta mutu"
jikin rahama ya fara rawa ganin sun sa mata ankwa sun fara janta, kuka ta fara tana cewa "wallahi cutar da ɗana tayi dan Allah kada ku tafi dani"
nawal yana cewa "ku saketa karku tafi da ammi na"
a mota suka sata, tace "nawal ka tafi karka bini ka gudu nawal"
har suka fara tafiya da ita be tsaya ba binsu, ɗaukan hotonta aka fara da video aka fara yaɗawa a duniya tayi kisa, nawal binsu yake yana gudu motan yana gudu har suka isa prison, kayanta aka sata canjawa tasa uniform aka shiga da ita ciki nawal duk yadda yayi ya shiga sun hanashi, waje suka fitar dashi yana kallo ana dukan amminshi ana gana mata azaba na cewar tayi kisa, tana ihu yana jin ihun har cikin ranshi, a bakin kofa suka wurgar dashi, ya kwanta a kasa bai yadda ya tafi ba yasa a ranshi anan ze rinƙa kwana har sai amminshi ta fito.
bacci yayi a wajen be tashi ba saida safe yunwa yana damunshi ya tashi ya zauna yana kallon masu shige da fice, hankalinshi akan ammi amma sunki bari ya shiga, a hankali ya tashi jin yunwa na damun cikinshi, bakin titi yaje ya tsaya kawai ya rasa abinda zeyi, wani mutum ya gani yana zuwa inda motoci suke gowslow yana roko kuma ana bashi abu, hakan yasa shima ya cire riganshi ya fara bara, murmushi yake yi ganin anasa mishi kuɗi, saida motocin suka wuce kafin ya maida riganshi ya zauna yana irga kuɗin bai ankara ba yaji an wufce kuɗin duka, saurayi ya gani daya kwace kuɗin ya fara gudu, tashi yayi ya fara binshi, cikin kafiya yake binshi har yayi nasaran rike riganshi ta baya, ganin haka ya ciro reza a aljihu ya yanka hanunshi, jin zafi yasa ya sakeshi yana kuka, jini ya fara zuba ya ɗaure da tsumma sannan ya koma wajen poison ɗin ya haɗa kai da gwiwa yana kuka, yunwa yake ji kuma ya samu kuɗi an kwace, haka yake zaune da yunwan har washe gari ya cire riganshi ya fara bara a inda yaga mutane ya samu kuɗi sosai yau ma, ze ɓoye sabida kada a kwace yaji an kwace kuɗin, yau kam kuka ya fara, ganin haka yasa a ranshi babu wanda ze kara kwace mishi abu, washe gari daya tara kuɗi reza ya siya yana tsaye yana irga kuɗin akazo za'a kwace yaga hanun meshi yayi da reza cikin rashin tsoron da suka koya mishi na kwace haƙƙin mutum, ganin haka meshi ya fara gudu, murmushi yayi ya haɗa kuɗin ya tafi shago, abinci ya siya nashi dana ammi.
*Shima ɗa ne complete is 400 via 8144818849 Hauwa shuaibu mapi moniepoint, evidence via 08144818849*
~Cikin murna ya shiga cikin prison sabida yaba ammi abinci, sun hanashi shiga har kasa ya durkusa da kayan jikinshi me datti tamkar almajiri ya rinƙa rokonsu da kyar suka yadda ya shiga, ammi tana kwance ta fita hayyacinta faɗawa jikinta yayi yace "yeee yau naga Ammi"
wani farin ciki taji a ranta jin muryan nawal nata, a hankali take shafa kanshi, ta kalleshi yadda yake murnan ganinta ya isa ya nuna mata soyayyan da yake mata, cikin sanyin murya tace "ɗana ya kake?"
kanƙameta yayi cikin sanyin muryanshi na rashin sabo da magana yace "ina lafiya ammi na kawo miki abinci"
murmushi tayi ya saketa ya buɗe abincin ya ɗiba a hanunshi ya kai bakinta, karɓa tayi tana hawaye, share mata hawayen yayi yace "ammi banaso kina kuka nayi alkwari zan hanaki yin kuka a rayuwarki"
tausayinshi take ji yaro ne karami amma yana shiga wannan halin, tace "to nawal amma aina ka sami abinci?"
turo karamin bakinshi yayi yace "ammi kince kada nayi karya shine zan faɗa mikii gaskiya bara nayi na samu kuɗi shine na siya miki ga sauran kuɗin ma kin gani?"
ajiyan zuciya ta sauke tunda ba sata yayi ba ta kalli kuɗin daya nuna mata sannan taja kumatunshi kaɗan tayi mishi kiss a goshi tace "nawal ko wani irin hali zaka shiga kada kayi sata"
yace "to Ammi"
daga waje akace "fito lokacinka ya kare"
tashi yayi da rashin fara'anshi yace "Ammi sai gobe zan kara kawo miki abinci"
tayi dariya tace "tom na gode nawal kada kayi nisa dani kaji?"
yace "a bakin kofa nake kwana"
murmushi kawai tayi ya fita yana farin cikin yaga Ammi itama tana farin cikin da Allah yasa be ɓata ba.
haka yake rayuwa a wajen kullum yana zuwa yayi bara yana samun kuɗin abinci, yauma ya dawo kenan daga bara yana irga kuɗaɗenshi yaga hadari sosai kamar ruwa ze sauko yanzu, ze nemi maɓuya wani zazzafan mota ya tsaya a kofa police suna biye dasu, fitowa me motan yayi yana masifa suma police ɗin masifa sukeyi, yace "wallahi babu wanda ya isa ya raba ƴata da mahaifiyarta itace ta haifeta na faɗa muku sabida tana kuka shine zakuce ba itace ta haufeta ba?"
police yace "sai mun tabbatar domin har yanzu yarinya taki karɓan nono kuma barayi shiru ba"
ihun jaririya yaji tana kuka kamar zata tada motan, ga kuma hayaniya da suke yi, buɗe mota matar tayi ta fito da alama jego ce ita bata jima da haihuwa ba wannan fitinan ya ɓullo, nawal daga inda yake tsaye yana hango jaririyar da take tsala kuka tana rufe cikin towel na yara, matar cikin ɓacin rai tace "kuna nufin ba nice na haifeta ba? bakwa ganina ne?"
police yace "hakan ba zaisa mu baki gaskiya ba tunda yarinya tana kuka taki yadda da kowa sai mun tabbatar babu wani abin"
cikin takaici matar ta fara kuka, ɗaukan yarinyar tayi tana jijjigata tace "dan Allah kiyi shiru kinji? kinga mahaifinki tunda aka haifeki be samu natsuwa ba yana cikin tashin hankali sabida rashin yin shirunki yasa ake zargin ko ke ɗin ba ƴarmu bace kiyi shiru dan Allah kinji?"
kara ihun yarinyar tayi, police yace "ka gani?"
karɓanta mutumin yayi yana jijjigata taki shiru, nawal dake tsaye a gefe yana kallonsu har ta kara kwantar da yarinyar ganin mijinta ze kwashi dambe da police taje tana janshi tana bashi hakuri, hankalin kowa ya koma kansu jaririya tana ihu ita kaɗai, a hankali yaje wajen motan ya ɗauketa, ruwan sama ne ya sauko a lokacin daya rungume yarinyar a kirjinshi yana jijjigata kamar yadda ammi take mishi idan yana kuka, ruwa ne ya fara jiƙasu daga shi har jaririyar, tsit tayi kamar bata taɓa kuka ba, duk suka juyo suna kallonsu, yana girgiza ta a kirjinshi yana goge ruwan dake sauka a fuskanta, mamanta ta kalli mutumin tace "tayi shiru wallahi tayi shiru"
tsallen murna ta fara a cikin ruwan, shima mutumin cikin farin ciki yake kallon yaron, yarinyar bata kara kuka ba, karɓanta matar tayi cike da mamaki suke kallon juna ganin bata kara kuka ba, suka kalli nawal daya juya zai tafi, mutumin yace "me kayi mata?"
yace "Allah ne yasa tayi shiru sabida Ammina tace idan ana ruwa komai zai zama daidai a rayuwata"
murmushi yayi yace "wacece amminka?"
nuna prison yayi yace "yau shekara ɗaya da kulleta anan tana ciki"
ya kira waya kawai, nawal cikin rashin son magana ya koma gefe ya zauna inda babu