x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 11 - SHIMA DA NE free pages

  • 30001 words
  • 33000 words
  • Out of 65957 words

Category: Love Stories

Views 226

25 Aug 2025
Start ads
After Image Ads
a gaba sukaga tana shirin faɗuwa, ibtisam ce ta riketa tace "mami what happened to you?"
tace "ibtee babu sarƙana na gold ko ɗaya kuma sune kaɗai abinda na mallaka a a duniya na dukiya ibtee ɓarawon jiya ya kwashe"
ibtee tayi shiru, kwantar da ita tayi akan gadon sannan tace "insha Allah zaki samu wanda ya fisu mami"
tace "ya zanyi Ibtee? yanzu dame za'a kai janna asibiti?"
tayi shiru, mami tace "ki ɗau gold naku ki kaita dashi"
tsayawa tayi sabida babu ko ɗaya ta tattara ta baiwa ɓarawon da a yanzu gani take yayi mata asirine yasa ta bashi komai sannan ta rufa mishi asiri, mami tace "lafiya? meyasa kikayi shiru?"
tace "ba komai bara naje na duba"
tafiya tayi zuwa ɗakinsu, tana shiga ta jingina bayanta da kofan tayi shiru, a ranta tace "anya ba aikin asiri bane yasa na tattara komai na bashi?"
shiru tayi, tunawa tayi da akwai kuɗi a jakan janna domin bata rabo da manyan kuɗi, buɗe jakan da janna take ajiya tayi sannan, waro ido tayi ganin daloli ne kwance dal a cikin jakan masu yawan gaske, da mamaki tace "aina janna ta samu daloli haka? Abba baya bamu kuɗi hasalima cewa yayi kuɗi yana lalata yara janna ina ta samu kuɗi haka?"
ɗaukan uku tayi sannan ta rufe sauran ta aje a inda ta gani, fita tayi ta samu mami tace "mami wallahi har namu an sace banga komai ba"
mami tace "ya Allah ka tsinewa ɓarawon daya shigo ya rabani da gold ɗina, Allah ka tona asirinshi ko a wani wajene wallahi idan na ganshi saina wulaƙanta rayuwarshi, saina sa anyi mishi hukunci daidai da abinda ya aikata"
shiru ibtisam tayi, saida mami ta gama sannan tace "zamu tafi da ita Ahlam yace akwai kuɗi a wajenshi"
tace "to ibtee ba sai na faɗa ba nasan zaki kula da ita"
fita ibtee tayi ta samu janna ta gama galabaita har ta gaji da kukan tayi shiru, taimaka mata tayi ta tashi sannan tasa mata guntun hijabin itama tasa nata, jaad ne ya riketa shima suka fita ahlam yana gaba, mota ya buɗe musu janna sai ɗingishi take har suka shiga motar Ahlam yaja suka fita a gidan, asibiti aka kaita Dr yana gani yace ta samu karaya a hanu, fara ɗaure karayan akayi banda ihu babu abinda janna take yi, Ibtee sai sannu take mata tana jin kamar tayi kuka itama, da haka har aka gama aka bata magani tasha sannan ya wanke ciwon da taji a baki, duk inda taji ciwo saida yasa spirit ya wanke sannan ta fara jin sauki banda kanta dake ciwo, a hankali suka sata a motan duk suka shiga Ahlam ya fara tada motan amma yaki tashi, ya fito domin duba meya samu motan baiga komai ba ya koma yana tadawa bai tashi ba, tsaki yaja yace "me matsalan motar nan?"
Ibtisam tace "yaki tashi ko zamu kira me gyara?"
dafa kai yayi yace "wallahi bansan meyasa motar nan taki tashi ba lafiya ƙalau kuma take"
fitowa zaiyi domin kara dubawa yaji an fara turasu, ta cikin madubi ya kalli wanda yake turawan, nawal ne sanye da kananan kaya riga fari da wando blue jinx, yasa picap a kanshi fuska babu walwala kamar kullum, motan ya tashi sakamakon turasu da yayi, murmushi ibtisam tayi tace "kaga wani ɗan albarka ya tura motar kuma ta tashi"
Ahlam yace "gaskiya mutumin kirki ne bamu rokeshi ba yayi abinda ya dace"
sauke glass tayi sannan tasa kanta tana lekawa domin zataso taga wannan me taimakon da ba'a rokeshi ba, ido huɗu sukayi da nawal da sauri ya kauda kanshi, da gudu yaja motar zai fita tace "wait Ahlam wait"
yace "saide kiyi hakuri idan na tsaya motan zaiki tashi"
duk yadda taso ya tsaya bai tsaya ba tafiya sukayi, nawal ajiyan zuciya ya sauke sannan ya tafi, Ammi an kwantar da ita a ɗakin da ake kwantar da wanda aka yiwa surgery, office na dr ya shiga bayan anyi mishi iso, ya samu dr zaune akan kujera ya zauna sannan yace "dr ina Ammina?"
dr yace "tana nan lafiya aiki ya kammala saide har yanzu ba zata iya tafiya kamar yadda mutane suke yi normal ba, dole saita rinƙa rike sanda komai yayi yadda akeso, amma ba zamu baka ita ba hasalima ba zakasan inda take ba har sai ka biya kuɗin aiki"
jakan bayanshi ya sauke ya aje a gaban dr yace "ga kuɗin aiki"
da mamaki ya kalleshi sai kuma ya kalli jakan, buɗewa yayi yaga kuɗi ne cike nak da jakan, ya kara kallon nawal kallon ina ya samu kuɗi haka?
nawal yace "ina Ammi na?"
dr ya kira waya, babu jimawa wata nurse ta shigo, yace "kaishi ɗakin new patient ɗinmu da akayi surgery"
tace "okay sir"
tashi nawal yayi tana gaba yana baya.

_Jiddah Ce...✍️_
08144818849
[17/08, 11:13 pm] +234 814 481 8849: 🌸🌸🌸🌸🌸
*SHIMA ƊA NE*
🌸🌸🌸🌸🌸


Na
*Jiddah S Mapi*


*Chapter 14*


~Ɗakin da ammi take kwance suka shiga, da mamaki yaga wani saurayi a kusa da ita yana kula da ita tamkar mahaifiyarshi, jikinshi a sanyaye ya karasa tana zaune yana bata ayaba da kanshi, murmushi tayi ganin nawal yazo, tace "nawal kazo?"
idonshi ya cika da hawaye a hankali ya sunkuyar da kai yace "eh"
tace "kada kayi kuka nawal gashi na samu lafiya, wannan shine yake kula dani tun safe yazo duba ƴan uwanshi ne anan asibitin amma an sallamesu a lokacin ake fita dani daga ɗakin tiyata yace ba zai iya tafiya ba ganin babu kowa a kaina"
kallonshi yayi kyakkyawa ne kuma yanada kwarjini jikinshi me kyau, ya karaso ya mika mishi hanu suka gaisa, cikin sanyin muryanshi da rashin hayaniya yace "na gode"
Ammi tace "sunanshi KAMAL"
a hankali yace "na gode kamal"
murmushi yayi yace "ba komai nawal tunda kazo bari na tafi dama ana kirana insha Allah gobe da safe kafin a sallameku zanzo na kara dubata"
a hankali yace "to na gode"
sallama kamal ya yiwa ammi sannan ya tafi, zama nawal yayi a inda ya tashi yace "ammi ya jikin?"
tace "jikina da sauki nawal, na tashi na ganni da kafafun roba nawal dr yace kaine ka kawoni kuma kace zaka je ka nemo kuɗin aiki shiyasa baka zo lokacin da aka gama aikin ba"
yace "eh naje neman kuɗin ne kuma na samu harma na biya"
tace "nawane kuɗin nawal?"
yace "dubu hamsin ne na basu dubu arba'in saura goma"
tace "Allah sarki nawal aina ka sami kuɗi har dubu arba'in?"

"aikin karfi nayi Ammi kuma Allah ya rufamin asiri na samu"
tace "nawal duk halin da zaka shiga kada ka saci abin mutum, nawal kada ka ɗauki hakƙin wani ka zama mutumin kirki me neman halak"
jinjina kai yayi alaman to, murmushi tayi tace "ga ayaban da kamal ya siya kaci ga ruwan gora da lemu nasan bakaci komai ba"
be musa ba dan rabonshi da abinci tun ranan daya kawota asibitin, a hankali yake ci tana kallonshi kamar tayi kuka sabida tausayin da yake bata, a wajen ya kwana yana zaune akan kujera ita kuma akan gadon tayi bacci, washe gari yayi salla ya taimaka mata tayi salla itama, dr yazo ya dubata yace anjima ze sallamesu, da mamaki saiga kamal kamar yadda yace zai zo ya dubasu ya shigo da abinci a kula da flask na shayi, nawal ne ya karɓa mishi suka karasa suka zauna akan tabarma, gaishe da ammi yayi ta amsa cikin fara'a sannan suka gaisa da nawal, shiru nawal yayi a gefe domin bai saba sakewa a wajen mutum ba, sai wajen ammi kawai yake iya sakewa, kamal tun jiya ya lura da hakan shiyasa ma bai damu ba shi da Ammi kawai suke hira nawal saide ya bisu da ido kawai baya cewa komai.
har zuwa lokacin da dr yazo ya basu takaddan sallama, kamal yanada karamin mota a ciki suka shiga yace zai kaisu gida, sun hau titi yace "saide ammi baki faɗamin ina unguwan ku ba wani gida kuma zan kaiku"
kallon nawal tayi shima ya kalleta, murmushi tayi tace "low-cost"
yace "okay"
nawal yana gefenshi yayi shiru yana tunanin duniya, har suka isa unguwan nawal be sani ba, kamal ne yace "mun shigo unguwan Ammi wani gida ne?"
tace "gidan Alhaji Alhasan medara"
da mamaki yace "Alhaji Alhasan daya nemi takaran gomna?"
cikin sanyi tace "eh"
kara kallon Ammi yayi sannan ya kalli nawal yace "kai ɗanshi ne?"
ammi zatayi magana nawal ya girgiza kai yace "A,a ni megadinsu ne aiki nake a gidan"
yace "okay okay na gane"
shiru Ammi tayi jikinta yayi sanyi, har kofan gidan ya tsaya dasu, fitowa sukayi Ammi bata saba tafiya da kafan ba tana ɗingishi sosai har suka shiga kamal yana rike da kayan, a kofan megadi suka tsaya inda nawal yake zama ya karɓi kayan yace "mun gode Allah ya saka da alheri"
yace "ameen zan koma amma zamu iya zama abokai? sabida ɗabi'unka sun birgeni"
shiru yayi sabida bayason aboki sam gashi kamal ɗin ya mika mishi hanu alaman su gaisa, sai kallon hanun yake ya kasa gaisawa dashi a matsayin aboki, Ammi ta katse shirun tace "me aciki? kun ma zama abokai"
kallon Ammi yayi ta mishi alama da eh, a hankali yasa hanu ana kamal ɗin suka gaisa, kamal yace "na gode"
murmushi kawai yayi, numbernshi ya karɓa sannan ya musu sallama ya tafi, Ammi tace "muje ka kaini ciki nawal tsoron shiga ciki nake"
hanunta ya rike a hankali take tafiya shima yana janta a hankali sabida ɗingishin da takeyi, har suka isa main parlour na gidan, ganin dady a falon saida jikin nawal ya fara rawa tsaban tsoro, ga momy dasu naseer zaune suna kallo, samha ce ta kallesu tace "dady dama waɗannan basu bar gidannan ba?"
shiru yayi, momy kuma ta zabga musu wani mugun kallon da yasa nawal damƙe hanun Ammi, naseer dake rike da remote yace "what the hell think you are doing here?"
cikin tsawa yayi maganan, Ammi tace "ka kaini ɗaki nawal"
jan hanunta yayi zasu wuce dady ya daka musu tsawa yace "wait"
tsayawa sukayi, Ammi ta ɓuya a bayan nawal sabida wallahi tsoro take ji, yace "ina kuke tunanin zaku shiga min da wannan dattin jikin naku? tukunna aina ta samu kafa?"
momy cikin mugun kishin ganin Ammi da kafafu tana tafiya hakan yasa diri da kyawunta ya kara bayyana sosai dama ashe dan a zaune take baduga wutan kyau da take dashi ba, saida ta tashi taga asalin diri da kyau, idonta rufe dan kishi tace "Alhaji ya zama dole ka saki wannan miskinyar matar"
girgiza kai yayi yace "no naja ba zan iya sakinta ba sabida zai taɓamin takaran da zanyi zuwa gaba sannan idan na saketa na tabbata akwai abokin gabana da zai iya lallaɓawa ya aureta sabida su ɓatamin rayuwata na gaba, zan zauna da ita amma saita gwammace bata sanni ba"
juya baya tayi batason ko ganin Ammi domin wani harbawa zuciyanta yake yi, ji take zata iya kashe Ammi, dady ya nuna musu hanyan waje yace "ku koma bakin kofa ɗakin megadi acan zaku rinƙa zama da kai da ita, ba zan saketa ba idan kunga zata iya yawo da aurena ku tafi idan ba zata iya ba ku zauna a ɗakin megadi"
nawal zaiyi magana Ammi ta damƙe hanunshi tace "A,a nawal shi ɗin mahaifinka ne, ba zan bari yana faɗa kana faɗa ba, nan shine asalinka kuma ba zan cuceka na rabaka da asalinka ba koba komai a gaba zai maka amfani"
shiru yayi sabida ko karen hauka ya cijeshi ba zai iya musu da Ammi ba, hanunshi taja suka fita, ɗakin megadin ya share sannan ya shimfiɗa bargo a kasa ya bar mata katifan, ya raba musu tsakani da zanin gado sabida ita macece shi kuma namiji duk da itace ta haifeshi akwai privacy da dole zata nema watarana, kallonshi take yana aikin, a hankali ya ɗago suka haɗa ido murmushin karfin hali daya saba yayi mata sannan yaci gaba da gyaran har ya gama ya kwanta a kasa ya ɗaura kanshi akan kafarta ya rufe ido babu irin tunanin da baya yi, itama Ammi tunanin take.

Janna bacci take yi na wahala ibtisam tana gefenta tayi tagumi, sam zuciyanta ya kasa walwala tunanin wannan ɓarawon data ganshi take yi, tunawa take da lokacin daya ɗaga mask na fuskanshi sabida ta ganshi, sai gashi yau ma ta ganshi amma bata samu daman magana dashi ba, a hankali janna take buɗe idonta da yayi nauyi ta kalli ibtisam da tayi tagumi a kwana biyunnan ta kula tana yawan tunani, duk da dama asali tana yawan tagumi idan Abba yayi faɗa ko duka amma na wannan lokacin tunanin yayi yawa, tace "unty ibtee? unty Ibtee?"
bata jita ba tayi nisa cikin tunani, taɓata tayi tace "unty ibtisam magana fa nake miki"
firgigit tayi tace "na'am"
"tunanin me kike?"
tsaki taja kaɗan sannan tace "ya jikin naki? da fatan babu inda yake miki ciwo"
tace "kaina naji ya ɗanyi nauyi amma babu inda yake min ciwo sai wannan ɗaurin da akamin"
tace "dama wannan dole ne yayi ciwo sannu, tashi kiyi wanka bara na kawo miki abinci kici sai kisha magani ko?"
tace "to amma unty tunanin me kike yi? nasan kin saba tunani amma na wannan lokacin yayi yawa"
tace "ba komai tashi kiyi wanka"

sauka tayi a gadon ita kuma ibtisam ta kama hanyan fita, jaad ne ya ɗaga murya yace "unty ki buɗemin kofa da abu a hanuna"
saurin buɗewa tayi tace "jaad kanina kaine?"
yace "eh abinci na kawo muku Abba baya gida ya fita kuma da alama kwana zaiyi a waje yau"
wani tsalle data daka shiya nuna tayi farin cikin jin wannan maganan, shima cikin murna yace "nima daɗi nakeji bakiga har magana nake yi da karfi ba? na kira p-b Ahlam yace da wuya su dawo yau"
cikin jin daɗi ta rungumeshi suka fara tsalle, janna da sauri sauri ta gama wankan ta fito ɗaure da towel a kirji, tace "tsallen me kuke?"
jaad yace "yau Abba ba zai kwana a gida ba...."
kafin ya karasa ta fara tsallen da yafi nasu, cikin jin daɗi tace "thank god yau zan tafi inda naga dama kuma ba zai sani ba"
ibtisam ta tsaya da tsallen tace "what? ina zakije?"
tana zuwa wajen mirror tace "ina ruwanki? dama birthday ɗin saara za'ayi kuma sun ɗaga party ɗin sabida banje ba jiya yau za'ayi bari ma ki gani"
jaad yace "dan girman Allah unty janna ki rufa mana asiri kar kije ko ina idan kuma akayi rashin sa'a ya dawo fa?"
tace "bama za'ayi ba domin janna me sa'a ce"
wayarta ta ɗauka ta kira tace "ku shirya yau za'ayi"
katse wayan tayi duk da hanu ɗaya take aiki bata ɗaga ɗayan, mai ta shafa sannan ta buɗe wardrobe Ibtee tana tsaye tana kallonta, cikin kwarewa take dressing, wani dogon riga baƙi me stones a jiki tasa, bayan yana jan kasa shape nata ya fito sosai, tasa siririn mayafi kawai a kanta sabida ba zata iya ɗauri ba, ko powder bata shafa ba lips kawai ta shafa sannan tasa dogon takalmi baki ta rike karamin pos ta fesa turare tareda sa katon bakin glasses a idonta, tazo zata fita ibtisam ta tare kofan tace "babu inda zakije janna"
tace "unty ibtee kin san ba zaki iya hanani zuwa inda naga dama ba ko ta window idan nayi niyan fita kin san zan fita, kinfi kowa sanin halina"
tace "ko mai zaki faɗa ki faɗa amma ba zan barki ki fita ba"
tsaki taja tace "wallahi baki isa ki hanani fita ba, ki matsamin na wuce"
kin matsawa tayi, jaad yace "wallahi saina faɗawa mami"
ture ibtisam tayi ta fita da gudu, ibtee suka bita da jaad suna kiran sunanta da gudu take tsallake stair har ta fita ta rufe kidan falon, compound nasu ta nufa da gudu ta shiga motar data saba tafiya yawonta idan babu Abba, hon tayi aka buɗe gate ta fita da mugun speed, jaad da ibtisam da mami wacce suka faɗa mata abinda yake faruwa suka fito da gudu sukabi bayanta, mami dafa goshi tayi tace "Innalillahi wa inna ilaihiraji'un janna saina mutu zata huta, janna bata tausayina"
ibtisam ta dafa kai tana hango tashin hankali da bala'in da za'ayi idan Abba ya dawo yau be kwana a inda yaje ba, jikinta a mugun sanyaye tace "jaad mami duk muyi addu'a Allah yasa Abba ya kwana a inda yaje koma inane Allah kada ya dawo dashi yau"
mami tace "ya zanyi Ibtee? ya zanyi da janna ne?"
jaad yace "sorry mami muyi addu'a Allah yasa kada Abba ya dawo kawai yau"

janna tana fita ta hau titi da bala'in gudu take driving, glass na motan tinted ne, saida tayi nisa da gidansu kafin ta ciro cingum a pos nata ta jefa a baki, kuɗin data ɓoye a cikin motan ta ciro sabbi dal dashi zatayi spray, waka ta kunna tana ji tana bin bakin wakan hanunta yana ciwo amma dole taje wannan party, babban hall ɗin data bada shawaran a kama ta shiga, motocin alfarma ne akayi parking sabida party ɗin yaran manya ne, tana fita ta fara taku kamar hawainiya, tun daga bakin gate ake mata tafi ana ihun zuwanta, fara'a ne akan face nata tana shiga waje ya ɗauka, dj yace "munji daɗi munyi farin cikin zuwan babban baƙuwa babbar kawar birthday girl JANNAH USMAN MAKAMA ɗiyar tsohon governor na garinnan"
tafi aka fara, aka saki waka janna suka shigo fili da manyan abokanta maza suna tikan rawa, hanunta rike da party cup tana sipping tana rawa cikin kwarewa, bata cire glasses na idonta ba vibe take kashewa a wajen.

nawal kallon time yayi a yadda yasa a ranshi ba zai daina sata ba saiya addabi kowa, tunda babu me taimakonshi kowa gani yake mugu ne a wannan rayuwan, sannan ya yiwa kanshi alƙawari duk abinda ya sata ba zaiyi amfani dashi ba, tunda Ammi tace kada yaci kuɗin haram ba zai taɓa ci ba koda zai mutu ne da yunwa amma yayi rantsuwa da ubangijin daya halicceshi saiya dami garin da sata, saiya sace duk wani abinda ake alfahari dashi a garin, sannan duk gidan daya ga sunada kuɗi babu su babu kwanciyan hankali, kuma duk tarin dukiyan daya samu ya yiwa Allah alkawarin ba zaiyi amfani dashi wa karan kanshi ba saide ko may be idan abu ya sameshi na dolen dole, kallon Ammi dake bacci akan katifanshi yayi, a hankali ya ɗan durkusa ya dafa kanta yace "ki yafeni Ammi zuciyata tana tafasa ba
End Ads