ya barshi a wajen zaune daram, kukan da yaran suke ba me tsayawa bane ɗaukansu yayi ya rungume suna kukan shima ya fashe da kuka suka haɗu su duka suna kuka harda Ammi dake bin bakinsu.
wasa wasa har kwana uku babu Ibtee babu dalilinta, tun yana tsoron faɗawa Abba har ya fito fili ya faɗa mishi, aka baza a gari ko ina nemanta ake da police da civilian, hotonta aka baza ko ina ana nemanta, kamal wanda suke tare da nawal yanzu daga wajen police aka kira wayanshi, ya ɗauka yace "hello wrong number"
katsewa yayi ya kalli nawal daya rame ya zama wani kala, yace "karka damu na tabbata babu wani abu mummuna da zai sameta insha Allah"
shiru yayi idonshi yana cika da hawaye, saida ya ajeshi a gida kafin ya juya motan ya tafi, wayan ya kira yace "hello ka kirani ina tare da mutum mu haɗu a wajen da muka saba haɗuwa"
juya kan motan yayi ya kama wani hanya daban, wani farm house ya nufa, har ciki ya shiga yayi parking motar sannan ya fito da makullin a hanu, jingina yayi yana kallon wanda yake zuwa da mask a fuska, yana zuwa yace "ina fatan baka mata komai ba bayan sace ta da kayi? kuma baka ajeta a inda za'a gane akwai mutum ba?"
girgiza kai yayi yace "gaskiya ban samu daman sace ta ba, nabi hanyan da kace nabi ban ganta ba amma naga ta shiga wata jan taxi"
a razane ya kalleshi, cikin faɗa yace "kamar ya zakace min ba kai ka saceta ba? zaka rainamin hankali ne auwal? gashi nemanta ake lungu da saƙo babu ita kuma kai kaɗai na bawa wannan aikin bayan kai bansan kowa da zai iya saceta ba ka faɗamin idan kuɗin dana baka ne yayi maka kaɗan"
yace "wallahi na rantse ban saceta ba"
shaƙe wuyanshi yayi yace "ni zaka ci amanata auwal? ka faɗamin ina ka kaita kafin na tona maka asiri"
fizge wuyanshi yayi yace "ka tonawa kanka asiri dai, ni ina na santa? ba kai ka nunamin hotonta kace kanaso na sace ta ba? kana ganin za'a kamani a kyaleka ne?"
idanun kamal take suka koma jajur ɓacin rai ƙarara ya bayyana akan fuskanshi huci yake yana kallon auwal jikinshi har yana rawa.
mami ganin yadda Abba ya shiga tashin hankali yana neman ƴarshi tayi murmushi sabida tasan aikin rezo ne shiya sace ibtee domin shi ta bawa wannan aikin, bata damu ba amma ta nuna ta damu sabida kada ta zama suspect, tasan Ibtee tana kwance watakila ma bacci take cikin kwanciyan hankali, Abba yana fita ta kalli jaad da janna da suke aikin kuka har janna ta faɗa shima jaad ya rame sabida rashin bacci da damuwa, tashin hankalin janna shine bata san inda ibtee take ba ko tana cikin kwanciyan hankali ko akasin haka oho, mami ta zame a hankali ta koma ɗakinta saida ta rufe da makulli kafin ta shiga toilet, layin reza ta kira, bai ɗauka ba taci gaba da kira bai ɗauka ba, daga karshe ya ɗauka a fusace yace "wai menene kiketa kirana kamar kece kika haifeni?"
murmushi tayi tace "aikinka yayi kyau reza banyi zaton zaka iya sace ibtee cikin sauki ba, gashi ka rabata da wannan shegen mara asali, yanzu inaso ka kula da ita dan Allah ko kuɗa banaso ya taɓata, sannan inaso ka faɗamin ko nawa zan baka kasa a bata kulawa me kyau ka tabbata ka rufe gidan ta yadda ba zata iya fita ba"
yace "wani magana kikeyi? wa na sace? ba nace miki ni ba zanyi wannan aikin ba? yaushe ma na saceta?"
tace "me kake faɗa ne reza? yau kwana uku kenan da sace ibtee da kayi gashi ana nemanta lungu da saƙo babu ita, nasan kai kaɗai ne zaka iya sabida kai na bawa wannan aikin bayan kai waya san inaso na saceta?"
yace "gaskiya ki nemi wanda ya sace ƴarki domin tun ranan da nayi waya dake nake gidan hajiya rabi kwalawa suna nemana nazo ta ɓoyeni a gidanta tun kafin ranan babu inda na kara fita"
tace "what? rainamin hankali zakayi? wallahi idan wani abu ya samu ƴata zan iya yi maka illa reza"
katse wayan yayi, a ruɗe ta kira layin hajiya rabi, tace "ki faɗawa reza idan wani abu ya samu ƴata zan iya yin komai"
hajiya rabi tace "ina jin wayan da kukeyi A'isha, tun ranan da kika kirashi yana gidana ina jin lokacin da kuke waya, zan iya rantsuwa da Alkur'ani me girma reza bai kara fita ko nan da kofar gida ba har yau, taya zai sace Ibtee?"
zufa ne ya fara wanke fuskan mami, cikin rawan murya tace "kin gane idan ma wasa kuke min dan Allah ku daina, kun san inason yarana sabida sune gatana meyasa zakumin irin wannan wasan?"
hajiya rabi tace "ba wasa muke miki ba tsakanina dake ai babu wannan gaskiya nake faɗa miki"
cikin ihun da batasan tayi bama tace "wallahi saina ɗaureku idan kuka cutar da Ibtee na rantse saina faɗawa ƴan sanda"
hajiya rabi tace "kanki zaki tonawa asiri a idon duniya kuma daga karshe za'a gane bamuda hanu a ɓatan ƴarki ki binciki bayan mu dawa kikayi wannan magana amma babu ruwan mu a ɓatan ibtisam ƴarki"
katse wayan tayi, wayan ne ya silale a hanun mami ya faɗi kasa, itama bin wayan tayi ta faɗi kasa, tace "Innalillahi wa inna ilaihiraji'un me yake faruwa? wallahi su suka saceta bayan su babu wanda yasan wannan plan ɗin kuma ibtisam bata gaba da kowa bale nace abokan gabanta ne suka saceta, na shiga uku nayi abinda zai dameni"
janna wacce taji mami tayi shiru a ɗaki ta tashi a hankali cikin jirin da take ji, idonta sun kumbura sunyi jajur, a hankali take tafiya batada karfi, knocking na ɗakin mami tayi, da sauri mami ta tashi ta goge numbobin data kira, ta fito daga toilet ɗin ta buɗe kofan, kallonta janna tayi na lokaci me tsawo kafin tace "mami Are you okay?"
murya a dishe tace "how can I be okay? bayan ƴata ta ɓata?"
a hankali ta rungumeta tana patting bayanta tace "insha Allah unty ibtee zata dawo ba zata barmu ba tana tare damu kuma har abada zamu zauna tare"
shiru mami tayi, janna hawayenta ya kasa tsayawa, tun ranan da taji ɓatan Ibtee har yau bataci ko abincin kirki ba banda kuka babu abinda take yi, bata zuwa school ta zama lazy babu class babu sa kaya babu fesa turare ta zama kamar me takaba.
~Momy tana tsaye tana kallon nawal dake rungume da yara suna kuka, dariya tayi sosai tace "nawal Alhasan medara shine sunan da mahaifiyarka takeso kayi amfani dashi ko? to wallahi matukar ina raye ba zaka taɓa amfani da suna kamar yadda ƴaƴan sunna suke amfani da sunan mahaifinsu ba, dole ka gane akwai banbanci tsakanin ɗan halak da shege, matarka kuma ina fatan kayi sallama da ita na har abada kafin ta tafi, domin ba zaka kara ganinta ba saide a lahira idan kanada rabon kallonta"
waya ta kira tace "bello kayi kokari kayi aiki kamar yadda na buƙata, kada ka barta da rai ka kasheta bello sannan inaso ka kirani naga gawanta da idona na binneta da kaina domin ta hanani rawan gaban hantsi, ta hanani sakat a gidannan ta zama kariya a wajen wannan matar da take claiming ita matar mijina ce, yanzu nasan dole nawal zai rinka tafiya ya barta tareda wannan yaran, ni kuma zanyi amfani da wannan daman na kashe yaran sannan na kwanceta ta fita ta bar gidan daga nan gida zai koma nawa da yarana shi kuma nawal dama zaman mahaifiyarshi yake ranan da babu ita inada tabbacin zai bar gidannan"
Bello saida ya gama ji yace "wai hajiya me kike magana akai ne? waye na sace? waye kuma zan kashe?"
tayi dariya kafin tace "bello yanzu zakaga alart inaso ka kasheta a yau ɗinnan"
yace "wai hajiya ki dakata mana da Allah, ban san abinda kike magana akai ba, ban sace kowa ba, nifa kinga bana ma abuja ina adamawa tun wancan week ɗin"
tace "bello me kake faɗa ne? bayan ni da kai waya san wannan maganan? akwai wanda ka gayawa ne?"
yace "wa zan faɗawa maganan da har na manta ne hajiya? nace miki ba zanyi aikin ba ina adamawa me zai dawo dani Abuja? ki kira abokina nuhu mana ki tambayeshi inanan ko bana nan sannan ki tambaya yaushe na tafi, kinga dan Allah banida alaka da wannan maganar taki ni ban sace kowa ba"
tace "baka isa ba bello bayan kai babu wanda yasan da wannan maganan kaine ka saceta kuma wallahi kasa na fika...."
kit taji ya gimtse, bin wayan tayi da kallo, tace "ya kashe, wallahi ya kashe"
hanu tasa aka tace "meyasa yaki yadda shi yayi aikin? bayanshi waya san da wannan maganan? dole ne na tabbata an kasheta kafin ta samu sake ta tonamin asiri a idon duniya.
Ibtisam tana kwance kamar mara rai, ba zaka gane tanada rai ba saita hanyan numfashin da takeyi a hankali, bayan numfashin ko hanunta bata iya ɗagawa, yanzu jirgi ya sauka da ita, tana kwance lat wasu mutane fararen fata suna kewaye da ita su uku kowanne ya ɗaura kanshi da alebo ya rufe fuska da mask da jallabiya a jikinsu, bindiga ne a hanunsu sun fito sak manyan ƴan ta'addan fararen fata, wani zazzafan mota ne yazo dab jirgin yayi parking, akan gadon da take kwance suke turata har zuwa cikin motan, shigar da ita sukayi tana kwance ko motsi batayi ba, tafiya motan yayi suna rike da bindiga sunyi ready, har zuwa wani babban gida wanda aka gina kamar aljannar duniya, ma'aikatan duk larabawa ne suna sanye da fararen jallabiya sunsa rawani a kansu, ba wanda sukazo da ita bane suka ɗauketa wasu ne daban suka ɗauketa suka shiga da ita wani ɗaki wanda mata sunfi dubu goma a kwance kowacce akan gado ansa mata injina a saman kanta ɗakin haskenshi blue ne, akan gado suka kwantar da ita sannan aka kawo wani sabon inji wanda yake ɗauke da na'urori dayawa, a kanta aka sauke injin ya danna cikinta, buɗe ido tayi cikin azaba tana kallonsu, kara dannawa sukayi a cikinta saida katifan ya ɗagu da ita ta kara kwantawa tsaban azaban zafi, bakinta ya rufe bata iya cewa komai sai binsu da take da ido, suna rufe da rigan leda duk jikinsu baka ganin komai, sun rufe fuska, sun danna mata yafi sau biyar ana shida ta suma, kallon juna sukayi sannan suka cire kayan jikinta suka barta tsirara a kwance, fita sukayi bayan sun rufeta da wani ƙaramin kyalle.
bata farfaɗo ba kuma basu damu ba.
saida tayi kwana uku batasan inda kanta yake ba, a kwana na huɗu sukazo da wani gado me kyau suka ɗagata suka ɗaurata akai, bata iya ko ɗaga hanunta sai kallo, akan gadon suka kwantar da ita suka fara turata har suka fita, ɗakuna ke a jere kowanne ɗauke da mutane biyu biyu, a ɗaki me number 50 suka shiga da ita, wata mata kwance akan gado me kyau dake gefe suka kwantar da ita a ɗayan gadon, dama gado biyu ne a kowane ɗaki, bayan sun kwantar da ita taga an kara yi mata wani allura kamar alluran wuta zafi ne sosai takeji a jikinta alluran yana ƙonata babu daman ihu, ido kawai ta rufe tana jin azaba sosai, barinta sukuyi taga sun yiwa matar alluran itama amma itakam ta iya buɗe baki tayi ihu sosai sabida zafi, ga ciki a jikinta, uniform ne light green a jikinta riga ne kawai daidai gwiwa sai hulan kamar leda shima kalan rigan, itama sa mata uniform ɗin sukayi green tana kallonsu suka fita, saida sukayi nisa matar ta tashi daga kwancen da take tana hawaye ta kalli ibtee tace "very sorry I know your body is hurting like mine, but we can't do anything"
kuka ta fara da alama tana cikin wahala domin kalamanta sun nuna, da kallo ibtee take binta kana ganinta kaga asalin balarabiya, tana kallonta har wani azababben bacci ya kwasheta, itace bata farka ba saida tayi kwana uku kullum kuma sai sunyi mata alluran, hawayen dake zuba a idonta ne kawai zai tabbatar tana raye.
matar kam ba kullum suke mata alluran ba wai jifa jifa.
a hankali ta buɗe ido cikin dauriya da son yin magana tace "ruwa"
sam muryanta be fito ba amma matar gefenta tana iya ganin motsin bakinta, sauka tayi a gadonta tazo tasa kunnenta kusa da bakinta tace "what do you say?"
a hankali tace "I want to drink water"
tace "okay"
saida ta leka ta ɓulin kofar kafin ta dawo ta ɗau ruwa a karkashin gadonta tazo ta buɗe ta fara bata a baki, ya isheta ta kawar da kai, matar tace "sorry you will soon be okay insha Allah"
jin tace Insha Allah ya tabbatar mata matar musulma ce, gyaɗa kai kawai tayi, sai dare kowa yana bacci banda matar da tayi tagumi tana hawaye, a hankali Ibtee ta buɗe ido zuwa yanzu raɗaɗin da takeji ya ragu tana iya buɗe baki, a hankali tace "why are you crying?"
cikin kuka tace "i have to"
girgiza kai tayi tace "please stop crying"
share hawaye tayi tace "okay"
Ibtee ta kara kallon ɗakin bata iya motsa koda hanunta tace "ya Allah ina nake haka?"
da sauri tace "kin iya hausa?"
da mamaki jin hausa a bakinta ibtee tace "eh na iya"
matar tace "wow I never expect this"
Ibtee tace "ke balarabiya ya akayi kika iya hausa?"
tace "my mother is fulani she's from nigeria and my father is Arab he's from dubai"
tace "okay, meya kawoki nan?"
tace "duk wanda kika gani anan kawoshi akayi kuma basa taɓa ɗaukan mutum bada sanin wani naka ba dole akwai wanda ya siyar musu da kai domin basa kama mutum haka kawai suzo dashi, ni babana ne ya basu ni ban sani ba saida suka faɗamin da kansu, shine abinda yake sani kuka, suna iya faɗa maka wanda ya siyar musu da kai sabida sun san babu kai babu fita anan"
ibtee tace "meyasa suke kama mutane su kawosu nan? wani allura suke mana?"
tace "duk wanda kika gani da green na uniform irin namu to tanada ciki, duk wacce kika gani da uniform red to cikin ya zube ko kuma ta kasa ɗaukan ciki, duk wacce kika gani da blue ɗin uniform to ta haife ɗan cikinta za'a bari ta huta kafin a kara sa mata wani cikin ta hanyan dashe, ni na haifi yara uku anan yanzu inada cikin na huɗu"
ibtee ga tsinkewan zuciya gashi ba zata iya tashi ba, tace "ina yaran suke?"
tace "idan sunsa miki ciki kina haihuwa zasu ɗauke yaron, idan mace kika haifa zasu yanke mata hanu ko kafa suje su girmar da ita a wani sashi na gidannan, idan ta girma zasu fara bara da ita a cikin gari suna samun manyan kuɗaɗe daga hanun larabawa, idan kuma namiji kika haifa sunada contract da manyan ƴan luwaɗi na duniya zasu kaishi sashin maza su bashi kulawa har ya girma kafin ma ya girma a cikinsu akwai waɗanda suke yin luwaɗi dashi, bayan ya girma zasu mikashi wa manyan ƴan luwaɗi na duniya, idan kin gama haihuwa sunga bakida wani amfani zasu kasheki su jefa gawanki a wani babban ruwa da yake kusa da wannan gidan wanda ake kira da gidan na shiga ba zan fito ba, ko kuma gidan ihunka banza domin ko zaki kwana kina ihu babu me taimaka miki har sai kin gaji kinyi shiru"
hawaye masu zafi suna wanke fuskan ibtee tace "amma dole sai an basu mutum suke ɗauka? kina nufin duk mutanen gidannan basu akayi?"
tace "wallahi babu wanda yake gidannan ba tareda sun biya kuɗi suka kawoshi ba, idan ma ba kuɗi suka biya ba to akwai wanda ya badake wasu"
ibtee rufe ido tayi tana tunanin waye zai bada ita?
buɗe idon tayi tace "kina nufin inada ciki?"
tace "tabbas kinada ciki domin tun ranan da aka kawoka tun a ranan suke dashen ciki domin suna zama da kwayoyin halittan a tare dasu a koda yaushe har sai kinyi mamaki aina suke samu"
shiru Ibtee tayi hawaye basu daina zuba ba, wani makiyi take dashi da har zai badata wa wannan mutanen?
turo kofan akayi da sauri matar ta kwanta, wasu ne daban sanye da uniform amma fari suka shigo suna dubata ta rufe ido kamar tana bacci, ɗaya ya kalli ɗaya yace "she's now okay"
jijjiga kai babban yayi ya gyara mask nashi kana yace "da alama namiji zata haifa domin alluran yana saurin sata bacci"
yace "yes I understand"
duba matar sukayi kana suka fita, buɗe ido Ibtee tayi tace "naji suna cewa namiji zan haifa ya akayi suka sani?"
tace "suna sane sabida sunada na'urorin da bakya zato tunda sukace namiji ne da wuya ki haifi mace.
tace "what's ur name?"
"my name is malika"
a hankali tace "ni kuma ibtisam"
tace "wow nice name ibtsam"
shiru kawai tayi, kullum sai sun shigo sun dubasu har cikin ya fara girma kafin suka daina musu allura suka fara kawo musu abinci masu kyau wanda zasuci ya gina jikinsu suyi kyau sannan su haifo yara lafiyayyu kyawawan da zasu ɗau hankali da wuri.
Abba yana kwance ya rufe ido kamar me bacci yau wata biyar kenan da ɓatan ibtisam kuma har yau babu labarinta, nawal kullum cikin kuka yake baya zuwa ma aiki yana gida tareda Ammi wacce jikinta yayi worse, babu irin maganin da baya nema mata amma har yanzu, twins sun fara wayo amma basa samun kulawa komai ya lalace, wayanshi ne yayi sauti alaman text ya shigo, ɗaukan wayan yayi ya duba ko Allah zaisa a dace, tashi yayi ganin ibtsam ce ta turo mishi sako (Abba na gudu ne sabida na gaji da zama a waje ɗaya gaskiya nima inaso naje naga duniya sabida ka takura mana tun lokacin da muke yara baka bari mu sake kullum cikin faɗa kake da duka to nima yanzu na girma kuma na san ƴancina, kada kuyi gajiyan nemana sabida ba zaku ganni ba ni kuma duk abinda kukeyi ina sane harma da masu binciken sirri da kasa suna bincikoni sannan kasa nawal ya sakeni banason auren idan kuma