karatu amma batada lokaci kuma babu kuɗi, nana tasan me a ranta hakan yasa tace "unty rahama karki damu akwai Allah zakiyi karatu insha Allah"
murmushi tayi tace "Allah yasa rahama"
sallama akayi yaro ya shigo yace ana neman rahama tace "kace bana nan"
mama dake wanke yakuwa tace "kace tana zuwa"
ɓata rai rahama tayi tace "gaskiya mama banson fita"
tace "dafaki zamuyi mu cinye? ba zakiyi aure ba kike nufi? kafin na buɗe ido tashi kije"
tashi tayi tasa hijabi ta fita, yana tsaye a jikin mota tun daga nesa ta fara aika mishi harara, tazo gabanshi tace "malam meyasa kake kirana?"
yace "rahma inaso ki gane sonki nake kuma da aure"
tace "gaskiya ni dai ba yanzu zanyi aure ba"
kafin ya kara magana ta wuce ta tafi, mama ta kalleta kawai tace "Allah ya shiryeki"
ana haka kullum saiya aika gidansu tun bata kulashi har ta fara kulashi sabida naci, da shike maganan aure yake mata yasa ta yadda dashi harma yake zuwa kullum, duk kuɗin da yake bata, bata taɓa karɓa, tana yawan ganin ana kiranshi a waya amma baya ɗauka, sannan baya bata labarin rayuwarshi musamman abinda ya shafi iyalanshi, ganin haka ta faɗawa kanwarta nana komai, nana tace kiyi kokari ki ɗau numbern mutum ɗaya da kika gani ko biyu a wayarshi sabida tsaro, ta ɗau shawaran kanwarta ta ɗau numbern harma biyu ta ɓoye, haka har aka fara maganan aure ya kawo kudin aure da komai da ake buƙata harma ansa rana wata ɗaya, an fara shirye-shiryen biki mutanen gari se gulma suke wai zata aureshi ne sabida kuɗi amma ya girmeta nesa ba kusa ba ya mata girma, bata kula kowa ba domin bata jin maganan mutane harkan gabanta kawai take yi.
tana zaune shiru a gefe tayi tagumi, wayar daya siya mata ɗan karami yana kan cinyarta, kiran wayar akayi ta amsa cikin sanyin murya tace "tom ina zuwa"
tashi tayi tasa hijabi sannan ta fita ta sameshi yana tsaye a jikin mota yana murmushi, zuwa tayi cikin girmamawa data saba ta gaisheshi, ya amsa sannan ya buɗe mata motan yace "shigo"
bata saba shiga ba amma ta daure ta shiga ta zauna shima shiga yayi yace "kin san zan tafi gobe ko?"
a hankali tace "eh"
yace "to dama siyayya nakeso nayi miki muje idan nayi miki saina dawo dake"
tace "to bara na kira Nana ta rakamu"
da sauri yace "a,a bari mana yanzu fa zamu dawo"
tace "gaskiya baba zeyi faɗa gara muje da ita"
yace "baki yadda dani ba kenan?"
shiru tayi ganin ranshi ya ɓaci tace "to muje"
kunna motan yayi yaja suka tafi, sai kallon hanya take tana jin gabanta yana faɗuwa, kallonta yayi yace "ki saki jikinki Rahma babu abinda zanyi miki na cutarwa na sanki da kamun kai ba zan yadda nayi abinda ze damu rayuwarki ba"
murmushinta data saba kawai tayi sannan ta ɗan saki jiki kaɗan amma har yanzu a tsorace take.
hanyan wani gida taga ya nufa tace "ba siyayya kace zamu je ba?"
yace "eh ai akwai wata mata me siyarda kayan gyaran jiki a gidan da zamuje matar abokina ne kuma munyi magana da mijinta zamuzo ta haɗa miki kayan gyaran jiki"
tace "to amma sun san zamu zo yanzu?"
yace "bari ma na kira wayarshi kiji"
kiran wayar yayi yace "gata taki yadda gidanka zanzo Alhaji sammani"
bata wayan yayi yace "ku gaisa kafin mu karasa"
karba tayi suka gaisa yace ta kwantar da hankalinta gidanshi zasu zo kuma yanada mata, ta mika mishi wayan yace "hankalinki ya kwanta?"
gyaɗa kai tayi, yace "to yimin murmushi"
murmushinta me kyau tayi mishi, yace "ko kefa"
gidane madaidai yayi hon megadi ya buɗe suka shiga, buɗe mata marfin motan yayi yace "fito sarauniya ta"
a hankali ta fito tana karewa gidan kallo, yace "muje ko?"
tafiya ta fara har suka shiga ciki, a falon suka zauna tana nesa dashi akan kujeran tayi shiru tana bin ɗakin da kallo, bata saki jiki ba duk a takure take, wani namiji ne ya fito da plate na lemu a hanunshi ya kawo gabansu ya aje, binshi tayi da kallo beyi kama da mutumin da ze zauna a wannan gidan ba, shiru tayi ya ɗauka ya buɗe a gabanta yasa a cup, zubawa yayi a cup ya rike ɗaya ya aje mata ɗaya, kallonta yayi batada niyan ɗauka tasha, yace "kisha mana"
ta girgiza kai, ɓata rai yayi yace "kina ganin zan cutar dake ne?"
ganin ranshi ya ɓaci ta ɗauka tasha kaɗan ta aje, tace "har yanzu basu fito ba? ko zaka kirasu?"
shiru yayi mata yana kallonta tana rurrufe ido, ganin beyi magana ba ta tashi zata tafi sabida ta kasa nutsuwa ji tayi jiri yana ɗibanta, rike kai tayi tace "Innalillahi wa inna ilaihiraji'un ina jin jiri, kaina"
ta rike kanta gam tana rufe ido, tace "na shiga uku me nakeji haka...."
kafin ta karasa ta zube kasa idonta ya rufe bata kara sanin inda kanta yake ba.
*Shima ɗa ne complete is ₦400 via 8144818849 Hauwa shuaibu mapi monie point, send your evidence of payment via 08144818849*
~Tace "gani baba"
hawaye ta gani a idonshi yace "rahama shine abinda zaki min? rahama shine abinda zaki saka min dashi? rahama yadda na baki tarbiyya na yadda dake shine abinda zaki sakamin dashi? kinsa a hanani jan mutane salla a masallaci, kinsa ina tafiya ana nuna ni?"
tace "baba dan Allah...."
hanu ya ɗaga mata yace "tashi ki bar gidannan na yafe ki duniya da lahira sannan ko ƴaƴana banaso ki kara zuwa inda suke"
zatayi magana taji saukan marin da yasa ta zauna kasa daram, cikin rashin hankali tace "baba wallahi..."
a fusace ya juya ze tafi sukaga ya faɗi kasa, ihu sukayi sukayo kanshi harda nana da yaseer, ɗagashi sukayi mama ta kira me mashin suka fita dashi, asibiti aka kaisu amma tun kafin su isa ma rai yayi halinshi, bayan sun isa dr yace musu ai baya raye, mama da nana da rahama ihun da sukeyi saida ya karaɗe asibitin, yaseer ne yayi dauriya yana basu hakuri, gida suka koma dashi, mutane sai magana ake wai rahama ce tayi sanadin mutuwan baba, mama tace "rahama karki kuskura ki taɓa babanki kece sanadin wannan mutuwan ki tashi kije rahama nima na yafeki duniya da lahira"
tana kuka zatayi magana sabida bakin ciki mama ta fara dukanta kamar ranta ze fita ga bakin cikin mutuwan baba ga dukan da ake mata, da kyar nana ta janyeta ta rungumeta tace "unty rahama ba zan iya jure ganin ana wulaƙanta ki ba"
tana haƙi cikin wahala tace "nana anya mama ce ta haifeni?"
nana tana kuka tace "tabbas itace ta haifeki kawai ɓacin rai ne"
tashi tayi tace "babu komai..."
kayanta da aka watsa mata a kanta yasa ta ɗago kai ta kalli mama data nuna mata hanya tace "ki kwashe kayanki ki bar gidannan rahama koda wasa kika kara taka kofan gidannan ban yafe ba, rahama idan na kara ganinki zan tsine miki kuma na rantse"
rahama ta kalli nana ta kalli mama cikin ruɗewa ta zube kan gwiwanta ta rike kafafun mama tace "mama ki gafarceni wallahi bada sona hakan ya faru ba"
mama tana hawaye ta juya baya tace "kinja min magana a wajen mutane kinsa babanki ya mutu me zan kara yi dake? kinyi cikin shege a kauye? kinsa ina tafiya ana nuna ni, kinsa babu me zuwa ya auri kanwarki nana sabida kin aje mana tabo rahama, na yafeki wa duniya na tsani wannan cikin naki, na tsani wannan cikin na jikinki, cikinshi masifa ne a garemu idan kika haifeshi ze zame mana bala'i, ze kawo mana matsala sabida kinada cikin ma mun samu matsala bale ki haifeshi rahama kije duk lokacin da kika haihu kika rabu da wannan yaron na cikin naki kika wurgar dashi na yadda ki dawo inda nake, amma matukar kika dawomin dashi gidannan a ciki ko a waje ban yafe ba"
bata kara magana ba ta durkusa ta kwashe kayan sannan ta kalli nana tace "nana, yaseer zan tafi sabida ba zan jure ganin mama tana kuka dalilina ba"
rungume yaseer tayi tace "ka kulamin da nana kasan ina sonku sosai"
ta sakeshi yana kuka ta juya ta rungume nana tace "Nana kiyi karatu kada ki yadda ki bar karatun da kike inada tabbacin zaki samu rayuwa me kyau, Nana kada ki aikata kuskuren dana aikata a rayuwa ki kula da kanki"
sakinta tayi Nana tana kuka ta kwashe kayan ta fita, kuka take yi, mutane suna nunata suna mata tofin Allah ya tsine, yara ta gani sun fara harbinta da duwatsu suna mata ihun wai babanta ya mutu saboda ita, tana nuna ustazanci na munafurci, gudu ta fara sabida zasu illatata, da kyar ta samu ta fita daga kauyen, dare ya fara yi gashi daji take riska, haka dai ta daure tana tafiya ga yunwa ga ishin ruwa, har dare yayi nisa tana cikin dajin, rasa yadda zatayi yasa ta kwanta a kasa tana sadaukar da rayuwa, cikinta ta rike wanda take ji yana motsi, babu abinda ta tsana kamar wannan cikin dake jikinta, ko kallon cikinta batason tayi, har garin Allah ya waye tana wajen, tashi tayi taci gaba da tafiya, tayi kwana uku tana tafiya saide taci mangoro da ruwa har ta samu ta ganta a cikin gari, zama tayi a gefen titi tana kallon masu tafiya, me shayin dake ankare da ita yazo inda take yace "baiwar Allah tun ɗazu nake ganinki anan lafiya?"
ta kalleshi tayi baƙi ta rame tace "lafiya ƙalau amma ina cikin wani hali, dan Allah ka taimakamin koda shayi ne"
yace "to ina zuwa"
shayi yaje ya kawo mata ta karɓa har jikinta yana rawa ta kafa a baki tana yagan biredi kamar zata cinye da hanunta, har ta shanye tace "na gode bawan Allah"
yace "amma daga ina kike?"
tace "babu amfanin sanin hakan bawan Allah wajen kwana nake nema"
ya kalleta sannan yace "taimakon da zan iya miki shine na baki kudi kije ki kama ɗaki, sannan ki nemi aikin yi"
ta durkusa kasa tace "na gode bawan Allah"
kuɗi ya bata ta karɓa tana godiya ta tafi domin neman wajen zama, tafiya kawai take batasan ina zataje ba, wasu ƴammata biyu ta gani sunyi wanka sunci ado suna kallonta sukace "baiwar Allah me kike nema?"
tace "ni baƙuwa ce ban san inda zanje ba ɗakin haya nake nema"
kallon juna sukayi sannan suka ce "to gaskiya zaki jima baki samu ɗakin haya ba amma idan zaki iya zama damu kuɗin gidan da muke biya babu yawa"
cikin jiri da zazzaɓin da take ji burinta kawai ta ganta a daki ta kwanta tace "na yadda zan zauna"
sukace "muje"
binsu ta fara har zuwa wani gida ta bada kuɗin wa mutumin data gani kamar baida mutunci bayan ta biya kuɗin suka tafi, wani gidan da tun a bakin kofa ta fara ganin masu shaye shaye da masu caca taga sun shiga da ita, bin ko ina take da kallo ƴammatan gidan duk karuwai ne domin kowacce da samarinta ga kuma caca da sukeyi da kalangu da ake bugawa, shiru tayi tana kallonsu suka nuna mata ɗakin da zata zauna, daga nan basu kara bi ta kanta ba, ɗakin ta shiga a tsorace take bin ko ina da kallo, babu ko katifa ga sanyin kasa na siminti, shiru ta zauna kasa tayi tagumi, turo kofan akayi taga ɗayar ce ta bata wani ƙaramin katifa da tabarma marar kyau da abinci a kwano, tace "gashi sai kici ki fita ki nemi ruwa, sannan zan faɗa miki wani abu, gidannan idan baki buɗe ido ba zakisha wahala"
tace "na gode ya sunanki?"
tace "sunana Abida"
tace "to na gode"
tafiya tayi ta kalli abincin sannan ta janyo ta fara ci, badan ta koshi ba ta kwanta ta fara rama bacci, har ta tashi tayi salla babu wanda ya kara shigo mata, sai dare kafin ta leƙo da sauri ta koma ganin tulin mazan dake gidan kowa da mace suna baɗala, dafa kirji tayi tace "Innalillahi ya Allah kasan bada sona nazo nan ba"
zama ta fara a gidan duk da rayuwarta tana cikin tsoro amma tana daurewa, rashin kuɗi ke mata barazana yanzu batada kudi batada abinci kuma babu me kulata.
kama kanta tayi sosai a gidan bata bari ta saba da kowa domin babu abin kirki da akeyi a gidan banda caca da zinace zinace, Allah yasa ta samu aiki gidan wata mata tana biyanta kuɗi anan take samun kudin siyan abinci, cikinta ya fara girma tana kula dashi, yauma kamar kullum ta dawo daga aikin ta zauna a bakin kofa tayi tagumi tana kallon mutanen dake harkokinsu, idan da sabo ta saba dasu, kowa ya shaida fuskanta a gidan kamar yadda ta shaida fuskan kowa, wata dake jin kanta a gidan taja tsaki bayan ta kalleta tace "sai sunkuyar da kai na munafurci da nuna bata bin maza gashi ita har ciki ta kwaso, tanada tsaraban bariki, gara mu ba muyi cikin shege ba"
wannan maganan ya taɓa mata zuciya taji zafi sosai, idan akace cikin shege sai taji komai na duniya ya fita mata a rai, tashi tayi ta shiga cikin ɗakin ta zauna tayi shiru tana tuna rayuwar da wannan ɗan cikin nata zaiyi, tana jiye mishi zafi tun kafin ta haifeshi, tana jin ciwon kalman da za'a kirashi dashi na shege, mutane musamman na wannan zamanin basu san ƙaddara ba, ɗan da zata haifa koda shege ne to ai SHIMA ƊA NE haka Allah ya ƙaddara mishi.
hanu ta ɗaga sama tana kallon sama tace "ya Allah ni kaskantacciyar baiwa ce, ya Allah banida komai sai abinda ka bani, ya rabbi kace mu roka zaka bamu, ya Allah a cikin hadisi kace koda mutanen duniya zasu taru su so mutum idan kai baka soshi ba to duk son banza ne, sannan kace da mutanen duniya zasu taru suki wani daga cikinmu idan ka soshi to ya tsira kuma zaka kareshi"
dafa cikinta tayi cikin tsananin kuka da tausayin kanta da abinda zata haifa tace "Allah wannan abinda yake cikin cikina ina roka mishi soyayyanka, ya Allah ka soshi koda mutanen duniya baki ɗaya zasu kishi, Allah wannan addu'an uwa ce akan ɗanta ɗan da zan haifeshi a gidan karuwai, ɗan da zan haifeshi babu uba, ɗan da aka kyamaceni sabida shi, Allah ka zama gatanshi"
kuka take yi sosai tana rokon Allah kuma tasan addu'an uwa karɓaɓɓe ne a wajen Ubangiji.
Tana cigaba da rainon ciminta badan taso ba saidan karɓan ƙaddara a duk yadda yazo maka, zaune take cikin dare ita kaɗai a ɗakin tana jin bayanta yana sarawa, kirjinta kwankwasonta duk suna mata azababben ciwo, addu'a take yi a cikin ruwan dake kofi tana tofawa, bayan ta gama ta shanye ruwan, ciwon ya kara karuwa ihu ta fara tana juyi a kasa, tana kuka tana neman taimako amma babu wanda yasan da zamanta babu wanda ya ko leƙo ta, tana birgima jin azaban naƙuda tana zufa duk sanyin da akeyi tana cewa "ya rabbi ka ɗauki rayuwata a wannan halin"
da haka har taji kan yaro ya fito, nan ta fara sabon ihu har ta haihu a ɗakin bata san inda kanta yake ba, abinda take iya ji shine kukan jariri janyoshi tayi jikinta ta rikeshi gam, sai yanzu taga an turo kofan an shigo, idonta dake rufuwa ta zubawa kofan, wani ta gani sanye da bakin kaya ya rufe fuska, yana shiga ya amsa wayarshi, sama sama taji yana cewa "eh an haifi jariri yanzu a gidan kuma zamu kawoshi"
gani tayi yazo ze kwace yaron, cikin wahala da gajiya ta rike yaron gam, kwace shi ya fara nan take ta fara kokawa dashi tana kare jaririnta da iya karfin da Allah ya bata, cizo ta gantsara mishi a hanu taki sakin fatar duk ihun da yake yi bata damu ba burinta yaji zafi ya bar mata jaririn, ruwan sama ne ya sauko me karfi da iska me tsoratar wa, ganin haka ya zame ya gudu, da rarrafe taje ta kulle kofan sannan ta dawo, kasa rufe ido tayi sabida gani take kamar zai dawo ya ɗauke mata yaron da har yanzu be daina kuka ba, da kanta ta yankewa yaron cibi, sannan ta goge duk wani jini ta kintsa ɗakin a daren, kwanciya tayi akan katifan sannan ta janyoshi jikinta ta kanƙameshi gam tasa mishi nono a baki, rufe ido tayi tana hawaye, ganin yana jin sanyi ta ɗauko zani ta sashi a ciki, rufe ido tayi bacci ya ɗauketa da jaririnta a jikinta.
washe gari ta tashi cikin azaban ciwon ciki ta kalli jaririn dake bacci, murmushi tayi ganin haske ya haska mata fuskanshi, shafa suman kanshi me tsantsi tayi, gashinshi kamar bana jariri ba, fari ne sol kamar ɗan larabawa, a hankali ta tashi ta zauna ta ɗagashi tana kallonshi, buɗe ido yayi, murmushi tayi ganin wasu kyawawan idanu da Allah ya bashi, mannashi tayi da kirjinta tace "barka da zuwa duniya jaririna"
hawaye ta fara, da kyar ta lallashi kanta ta kwantar dashi ta fita daga ɗakin ta nemo ruwan zafi tayi mishi wanka sannan itama tayi wanka, ragowan abincin taci sannan ta dawo ta kwanta, ji take soyayyan yaron yana cika mata zuciya musamman idan ya buɗe idanunshi suka haɗa ido sai taji jikinta yana sanyi.
haka ta fara rainon jaririnta wanda ko suna bata sa mishi ba, saida ta samu sauki sannan ta fara zuwa aiki, yauma kamar koda yaushe gidan da take aiki ta shiga, matar tana ganinta tace "sai yanzu kika zo?"
tace "ayi hakuri ɗana ne babu lafiya"
tsaki taja tace "ɗan da ko suna baki sa mishi ba sabida rashin gaskiya, da ɗan halak ne ai da kin jima dasa mishi suna har rawan jiki zakiyi"
shiru tayi amma fa ranta ya sosu, matar tace "koda shike wacce ta zauna gidan karuwai me ba zatayi ba? je kimin aiki nikam ban san amfanin surutuna ba"
shiru tayi taje ta fara wanke wanken, badan anan take samun kuɗi ta siya abinci ta kula da ɗanta ba da bazata kara aiki anan gidan ba tunda ta faɗi waɗannan maganganun, har ta gama aikin sannan ta karɓi kuɗinta ta tafi, tana komawa gida ta saukeshi ta kwantar dashi sannan ta fito tana haɗa abinci, abida ce ta shigo tace "idan akwai abinda bani mana yunwa nake ji"
abincin data dafa wanda