x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 17 - SHIMA DA NE free pages

  • 48001 words
  • 51000 words
  • Out of 65957 words

Category: Love Stories

Views 229

25 Aug 2025
Start ads
After Image Ads
huce kuma zaisa a sakeku insha Allah ki daina kuka"
rungume jaad tayi tace "jaad kanina kana gani cizon sauro zai hallaka yayarka?"
yace "sorry unty janna you will be fine"
tace "ku bani abinci"
karɓan abincin Ibtee tayi ta sawa kowa a plate sannan ta sawa janna, fara bata tayi a baki tana ci a hankali, ɗago kai tayi zata tambayi ruwa suka haɗa ido da nawal, wani kallo ta aika mishi sannan tace "me wannan megadin yake yi anan?"
Ibtee tace "shiya kawomu"
tsaki taja tace "ki bani ruwa"
ruwa ta bata tasha, tace "unty ibtee idan dai zaki kara shigomin da wannan megadin kada ki kara kawomin abinci na yafe, gara ki barni na mutu da yunwa da wannan ya biyoki wajena, duk abinda p.b Ahlam ya yiwa Abba wallahi nafi kaunarshi sau dubu akan wannan me zubin munafu...."
marin bakinta ibtee tayi tace "bakida hankali ne? mutum yana nan kina zaginshi be girmeki bane?"
juya baya tayi alaman ba zataci abincin ba, Ibtee ganin ta kwana da yunwa tace "kiyi hakuri kici abincin ba zan kara ba"
tace "bana bukata kinsan ni na taso a cikin abinci ko kaɗan naci zan koshi ki bawa wanda ya taso a cikin yunwa yaci ina zaifi mishi amfani"
shiru Ibtee tayi ta kalli nawal daya ɗauke kai yana jin abinda take faɗa, jikinta a mace tace "shikenan zan tafi sai gobe"
karɓan sauran plate tayi taja hanun jaad suka tafi, nawal ya fara jan motan a hankali kamar yadda yake yin komai, saida suka hau titi tace "kayi hakuri ita ɗin yarinya ce karama girman jiki ne kawai da ita"
murmushi yayi ya ɗauke kai sabida shi ba bakon bakar magana bane, har suka isa gida yana ganinta ta tacikin madubi ta kasa sakin jiki da alama abin be mata daɗi ba sosai, buɗe musu yayi suka fito ya basu basket ɗin, tace "kayi hakuri dan Allah kaji?"
a hankali ya gyaɗa kai kawai, wucewa yayi ya zauna a bakin gate, saida yamma kafin yaje ya duba Ammi ya samu tana bacci shiyasa bai tasheta ba ya zauna kawai kusa da ita yana kallon fuskanta, jin Amminshi yake har cikin ranshi, ita kaɗai ce bata mishi gori sai abokinshi kamal su biyunnan kawai yake so sabida basa faɗa mishi magana me ɗaci.
har saida ta gama bacci ta buɗe ido a hankali ta kalleshi, tashi tayi tace "nawal ɗana yaushe kazo?"
ya kwanta sannan yace "na jima amma kina bacci shiyasa ban tasheki ba"
tace "daka tasheni ai"
murmushi kawai yayi, tace "da gaske ka samu aiki a gidan wani me kuɗi?"
yace "eh Ammi na samu aikin kula da gidan nine megadi kuma nine me basu tsaro na musamman sannan nine me bayin flower kinga zan samu halal na rinƙa kawo miki abu me daɗi kina ci"
dariya tayi me kyau sannan tace "Allah na gode maka da nawal ya samu aiki"
yace "Ammi meyasa...."
muryan dady yaji saida gabanshi ya faɗi ganin dady ya shigo kai tsaye da jallabiya a jikinshi, ya tsaya akansu ya kurawa Ammi dake sanye da riga roba roba ido, Ammi kare jikinta ta fara a tsorace sabida tasan meya kawoshi, nawal ɗauke kai yayi kamar bai ganta ba, a hankali yace "ina wuni"
ba yabo ba fallasa yace "lafiya"
shiru sukayi sai wani kallo da yake bin Ammin dashi, nawal tashi yayi ya fita daga ɗakin, tun kafin ya karasa fita dady ya fara taɓa jikinta, fizgewa take yi tana cewa "karka taɓani ka kyaleni nikam"
nawal da kyar ya bar part ɗin yana jin kanshi na mishi nauyi, ihun Ammi da yaji saida ya toshe kunnenshi, fita zaiyi aka turo kofa momy wacce taje unguwa ta kalleshi sama da kasa ya gaisheta ko kallo be kara isanta ba ta wuce, a falon ta zauna tana kallon tv tana shan ruwan sanyi sabida gajiyan hanya, nawal fita yayi daga gidan gaba ɗaya, gidansu kamal yaje saida ya haɗu da kamal damuwanshi suka ragu hira sukeyi hakan yasa ya saki jikinshi ya daina tunanin abinda ya faru.
dady ne ya gama abinda zaiyi ya fito daga ɗakin, ido huɗu sukayi da momy, da sauri ya fara dabarcewa yana mata sannu da dawowa, binshi kawai tayi da kallo har ya shiga ɗakinshi, tashi tayi ta goya hannayenta a baya tana jeka ka dawo tana cewa "ya kamata na ɗau mataki na san me zanyi akan wannan matar, sabida ta fini kyau shiyasa baya iya kallonta ya kyale? meyasa yake satan zuwa wajenta kullum? wannan cikin da yake jikinta ba zan taɓa bari ta haifeshi lafiya ba, sabida lawyer da suka sa a wannan maganan shiyasa har yau ban kasheta na kashe wannan shegen yaron da aka haifa kafin fatiha, yaron da yafi yarana kyau da nutsuwa ya fisu farin jini da komai wallahi da sun san zafin da nakeji a duk lokacin da naga wannan shegen wanda kamar ɗan aljanu ne sabida wutan kyau da yake dashi da sun daina yadda ina haɗa ido dasu, saina san abinyi na raba wannan matar da Alhaji wallahi ko zanyi yawo tsirara saina tabbatar na haukata wannan matar ta yadda bata isa ta gane waye ɗanta bama bale ta kai kara"
waya ta kira ana ɗauka ta fashe da kuka tace "boka kana gani ana shiga HAƘƘI NA? kana gani Alhaji yana tarayya da wata macen kuma banida daman ɗaukan mataki sabida kotu da suka sa sharuɗa? boka kasan da tuni na jima da kashe wannan matar me kama da aljanu da wannan ɗanta shegen kafin su fara haɗa zuri'a da Alhaji, gashi yanzu cikine babba da ita na rasa yadda zanyi boka, ga yaron yafi ƴaƴana nutsuwa duk cikin yarana babu na kirki daga ƴar ƙwaya sai dr me zubar da ciki da bin mata, sai lawyer me danne hakkin mutane sai wanda mahaifinshi ya koya mishi cin amana? wannan yaron na tabbata zai zo ya shiga zuciyan Alhaji sabida nutsuwanshi kuma wannan cikin jikinta kasan yanada gado a gidan idan ta haifeshi sabida shi da aure aka samu cikin? boka na shiga uku na lalace, na mutu ni naja'atu"
boka yace "ki nutsu kiji me zan faɗa miki najah"
tace "ina jinka"
yace "zamu san me zamuyi karki damu ki barta da cikin zata haife amma zan san me zanyi ki zuba ido kawai ki gani"
ta share hawayen tace "na gode boka nasan zaka sharemin kuka na"

Ammi yana fita ta tashi tana jan kafar da har yanzu basu zama mata daidai ba amma dai yafi babu domin ba kowa zai gane wannan kafar ba nata bane, ta shiga bathroom tayi wanka ta haɗa da alwala ta fito, shimfiɗa sallaya tayi ta fara salla nafila take yi babu adadi tana kai kukanta wa Ubangiji tareda addu'an Allah ya sauketa lafiya Allah ya kara mata tsawon rai domin ta kula da nawal ɗinta.
tana zaune akan sallayan hanunta rike da casbi tana tuna duk abinda ya faru a gaban ɗanta, share hawaye tayi tana kara yiwa Allah godiya akan jarabawan da yake mata.

Nawal ya koma gida Abba ya kirashi a waya, har yau abba yana kwance a ɗaki yana hutawa kafin ya fara fita, ɗaukan kiran yayi yace "kaje station ka ɗauko ƴata da take rufe"
yace "to"
motar da akace dashi zai rinka zuwa aike shi ya shiga ya tafi station, yana cikin motan har ta fito tana layi kamar tasha abu, tsayawa tayi a kusa da motan tana kallonshi, ganin ba zai fito ba kuma tana jin jiri tace "malam wa kake jira ya buɗemin mota?"
a hankali ya fito ya buɗe mata ta shiga baya ta zauna, rufewa yayi kana ya shiga shima yaja motar, da mamakinshi yaga kawayenta sun fito da kafa suka tafiya, jakanta ta buɗe ta ciro wasu abinda baisan ko me ba, tace "bani ruwa"
ruwa ta mika mata ta wufce sannan ta haɗiye abun yana kallonta ta madubi, babu jimawa ta kwanta a wajen ta fara bacci, har suka isa gida bata ko buɗe ido ba tana bacci, fita yayi ya fara knocking inda take yace "hajiya, hajiya"
ganin bata tashi ba ya buga da karfi, firgigit ta buɗe ido, ta zuba mishi idanunta masu girman da suka koma na bacci tace "me haka?"
yace "munzo gida"
buɗe mata motan yayi ta fito, jiri ne ya kwasheta zata faɗi ya rike hanunta, fizge hanun tayi ta wankeshi da mari tace "how dare you zaka taɓamin hanu?"
ya dafa inda ta mareshi yayi shiru, tace "idan ka kara wannan kuskuren saina wulaƙanta ka useless"
tafiya ta fara tana layi kamar zata faɗi, juyawa yayi yaga ibtisam tsaye tana mishi murmushi, a hankali ya kauda kai, chocolate babba ta ciro a bayanta data ɓoye ta mika mishi, kallon chocolate ɗin yayi an rubuta SORRY da manyan harufa a jiki, tace "gashi naka ne"
girgiza kai yayi zai wuce ta tare mishi hanya, ya kalleta tace "babban ɓarawo wannan naka ne kuma dole saika karɓa"
karɓa yayi yace "na gode"
smiling nata da yake kara mata kyau tayi, zai tafi tace "ka daina sata ne?"
da mamakinta taga ya girgiza mata kai alaman a,ah, tace "okay kenan wani plan na satan ya kawoka gidanmu again?"
ya girgiza kai alaman A,ah, zai tafi tace "wait"
tareda tare mishi hanya, tace "meyasa da janna ta mareka baka rama ba?"
yace "ba komai na yafe"
murmushi tayi tasan har cikin ranshi yayi maganan, jin saukan yatsunta a inda janna ta mareshi ya sashi saurin kallonta, tace "kasan me? ina matukar son mutum me hakuri a rayuwata, banason mutum mara hakuri amma inason mutumin da idan akayi mishi cin zarafi ya rama, yawan hakuri idan yayi yawa yana zama cutarwa, janna batada kunya idan baka buɗe ido ba zata baka wahala, sannan zata rinka yi maka abu da gayya sabida ta kureka matukar bata kureka ba kuma bata hakuri zataci gaba da yin haka har sai taga ka biye mata kun fara rigima zata samu kwanciyan hankali, ina me baka shawara ka...."
juyawan da zatayi taga babu shi yana can banin kofanshi yana wanki, shiru tayi da alama ya jima da tafiya ya barta a wajen, tafiya tayi rai a ɓace ta shiga ciki, eyelashes nashi masu tsawo yana kwance akan face nashi, ya ɗago idanunshi yabi bayanta da kallo, maida kanshi yayi zuwa wankin da yakeyi, marin da tayi mishi ya mishi zafi amma maganan Ammi kullum shine ya zama me hakuri zaiyi nasara a rayuwa, lips nashi ya cusa cikin bakinshi yana cigaba da wankin har ya tashi yana shanyawa akan igiyan da masu gadi suke shanya a baya, janna daga sama tana tsaye akan stair tana kallonshi a down, bowl kato na roba cike da ruwan sanyi har yana kankara shine a hanunta, murmushin rainin hankali tayi ganin yazo dab inda take so yazo, karkata bowl ɗin tayi ta fara tsiyaya ruwan daga saman zuwa kasa, zubar da ruwan tayi a kanshi sannan ta saki bowl ɗin ya faɗi a kanshi ya rufe mishi fuska, dariya ta fara ganin ya fara rawan ɗari, tace "sai kayi dana sanin cewar Abba ka fini a wajenshi saika gane baka kaini komai ba a wajenshi"
nawal baya son kankara bayason ruwa me tsananin sanyi idan bana sama bane ya taɓashi a take zai fara rawan ɗari, cire bowl ɗin yayi sannan ya ɗago kai sabida yasan daga sama abin ya zubo, smiling tayi mishi ta kewaye hanunta a baby face nata, saida ta tabbatar ya san itace kafin ta juya ta bar wajen, komawa ɗaki tayi ta faɗa kan lallausan gadonsu ta rungume teddy ɗinta tace "I miss my teddy"
Ibtee ce ta shigo fuska ba walwala, da gudu ta sauka a gadon taje ta kanƙameta tana cewa "i really miss you my ibtee"
murmushin karfin hali tayi mata kana tace "miss you more"
hanunta ta rike suka karasa ciki, a bakin gado ta zaunar da ita sannan itama ta zauna, tace "janna look at me"
kallonta tayi, tace "janna meyasa kika mari p.b nawal?"
taɓe baki tayi tace "au shi yace miki na mareshi?"
tace "bashi bane nice na gani da idona"
tace "laifi yamin shiyasa na mareshi"
tace "haba janna a girme fa ya girmeki bakiji kunyan marin innocent soul haka ba?"
tashi tayi tace "nifa gaskiya unty Ibtee wanka zanyi"
bata bari ta kara wani magana ba ta faɗa bathroom, tagumi Ibtee tayi sabida kwata kwata abin bai mata daɗi ba.


_Jiddah Ce...✍️_
08144818849
[17/08, 11:13 pm] +234 814 481 8849: 🌸🌸🌸🌸🌸
*SHIMA ƊA NE*
🌸🌸🌸🌸🌸


Na
*Jiddah S Mapi*


*Chapter 21*


~Tafiya Ibtee tayi ta barta a wajen shima ya shiga ɗaki yana kanƙame bargon sabida sanyi, janna tafi minti ashirin a tsaye hanunta a kunci, da kyar taja kafarta ta koma ciki, a falo ta zube akan sofa tayi shiru, tunda take da ibtee bata taɓa marinta ba tsawa ma bata yi mata bale mari yau akan wannan ta mareta?
har dare basu yiwa juna magana, mami ta kula da hakan, ta kirasu su duka tana tambayan meya faru basa yiwa juna magana?
duk sukayi shiru, tace "idan ma ba zaku faɗa ba ya kamata kusan ciki ɗaya kuka fito kada ku bari wani abu ya shiga tsakaninku ya ɓata"
ibtisam tace "insha Allah"
tace "ku tashi kuje"
fita sukayi har aka gama weekend basa magana, yau monday kowa ya shirya cikin uniform nashi janna na goye da jakanta na baya suka fito, Ibtee da kanta ta buɗe marfin mota ta shiga, shima jaad haka janna kuma tsayawa tayi tana jira nawal ya buɗe, da sauri ya karaso yana kallon agogo sun kusa late, buɗe mata yayi ta shiga ta zauna, shiga yayi jaad ya gsisheshi ya amsa sannan Ibtee ma haka, fita yayi ya dawo ya rufe gate sannan yaja motar suka tafi, a hanya sun zama shiru babu me magana sannan baida ɗabi'an kunna waƙa a mota, har kofan school ya kaisu, Ibtee ta fito rike da hanun jaad suka shiga sabida sunyi late yau, janna ta bar jakanta a cikin motan ta fito tana takunta data saba, kallon nawal tayi a wulaƙance tace "ka biyoni da jakana"
tafiya tayi ya ɗau jakan yabi bayanta, tana gaba yana baya har suka shiga ciki, ana assembly kowa yana tsaye harda malaman suna yiwa ɗalibai jawabi, a baya ta tsaya ya bata jakan ta karɓa, juyawa yayi zai fita tace "kai bodyguard ka ɗaukomin goran ruwana"
yace "to"
tace "dakata"
tsayawa yayi tace "meyasa kake magana babu respect kamar kai ba ɗan aiki bane?"
a hankali yace "to hajiya za'a kawo miki"
fita yayi, jikin ibtisam ya mutu sosai, taji babu daɗi ganin kawayen janna duk suna binshi da kallon raini da kaskanci kuma tasan janna tayi hakan ne sabida ta kaskanta shi"
goran ruwan ya kawo mata ya mika mata ta harɗe hanu a kirji tana kallonshi, tace "babu respect kake mikamin?"
ɗan durkusawa yayi ya mika mata, karɓa tayi tana murmushin rainin wayo tace "yawwa yanzu ka zama good bodyguard"
tashi yayi kawai ya tafi, ibtisam kallonta tayi taji zafi sosai batajin daɗin abin ba, batasan yadda zaiji a ranshi ba, zaiji kamar shi ɗin ba kowa bane face kaskantaccen bawa wanda bashida komai a rayuwa, har aka tashi hankalinta baya jikinta, yana jiransu a kofan school baya late na zuwa ɗaukansu, da mamakin janna taga Ibtee ta zauna a gaba ba kamar yadda suka saba zama a baya ba, gaishe da nawal tayi a nitse ya amsa, jan motan yayi tana kallonshi bini bini tana murmushi, juyowa yayi suka haɗa ido da sauri ya ɗauke kai ganin murmushin da take mishi, har suka isa gida janna da jaad suka fita Ibtee tana zaune, yasa hanu zai buɗe shima ya fita tace "nawal"
tsayawa yayi bai fita ba, tace "dan Allah ka kalleni"
a hankali ya kalleta ya kara ɗauke kai, da alama yana jin nauyin kallon cikin idon mutum, ji yayi ta rike hanunshi, tace "nawal kayi hakuri da abinda janna take maka, kada hakan yasa ka karaya kaji kai ɗin ba kowa bane, nawal kowane ɗan adam Allah ya bashi baiwa kuma kana cikin wanda Allah ya bawa baiwa, dan Allah kayi hakuri kada ka rike komai a ranka kaima ɗa ne kamar kowa"
a hankali ya sunkuyar da kanshi, maganan ya mishi daɗi ta gane hakan ne ta hanyar murmushi da taga yana yi, ta saki hanunshi yace "na gode"
fita tayi daga motan ranta fes, Abba yana kallon duk abinda ya faru dama jira yake su dawo nawal ya fita dashi, shiru yayi yana nazari har Ibtee ta gaisheshi ta wuce, a hankali yaje ya buɗe motan ya shiga, nawal kanshi kasa har yanzu yana smiling ganin baima san ya shigo ba yace "muje to idan ka gama"
da sauri ya ɗago kai yace "ina wuni Abba"
yace "lafiya"
fita sukayi a gidan.
janna abinda Ibtee tayi ya tsaya mata a rai duk hanyan da tasan zata wulakanta nawal sai tabi, wulaƙanci take mishi iri iri sabida yayi zuciya ya bar gidan.

cikin riga da skirt na kanti ta fito da hula me malafa a kanta, tana mika da alama bacci be isheta ba, tayi kyau da sleeping face nata, kallonsu tayi har sun fara breakfast da wannan da ta tsani ganinshi kamar ta kasheshi, ga Ibtee tana facing nashi sai satan kallonshi take, wani abu ya tsaya mata a wuya, a hankali ta koma ɗaki ta fito tana ɓoye abu a bayanta, saida ta tabbatar basa ganinta tayi kamar wucewa take ta zuba mai a daidai bakin kofa inda tasan nawal dole saiya taka kafin ya wuce, a gefen mami ta zauna tana murmushi kasa kasa dan tasan yau saiya gane kuskurenshi, gaishe dasu tayi sannan ta fara breakfast itama, Abba ne ya fara tashi ya wuce sama, nawal ma ya tashi yana cewa "na gode"
ta kasan ido ta kalleshi kananan kaya ne a jikinshi bakin polo da bakin wando, yayi bala'in kyau bakin kaya yana fito da asalin kalanshi, tafiya ya fara cikin nutsuwa, daidai bakin kofa yaji kamar ya taka abu me sulɓi juyawa zaiyi sulɓi ya jashi ya zube kasa tim, janna aje cokalin tayi ta kwashe da wani irin dariya har tana faɗuwa akan kujeran, nawal runtse ido yayi sabida zafi, ya kasa tashi domin ƙafarshi yaji ciwo, Ibtee ta waro ido da abinci a bakinta ta kasa haɗiyewa, mami rufe ido tayi tace "subhanallah"
da kyar Ibtee ta haɗiye abincin bakinta itada jaad da gudu sukaje suna ɗagashi, rufe ido yayi lokacin daya tashi ƙafarshi kamar ba'a
End Ads