yace "shine yaron da muke baku labari"
tare sukace "shegen?"
nabil yace "yes shine"
dariya suka fara mishi kowa yana cewa "shege baida baba"
tafiya yayi ya barsu a wajen ranshi yana zafi.
da kafa ya koma gida, yana shiga falon sukayi karo da mutum, da sauri yace "sannu...."
marin da aka mishi yasa kunnenshi ya fara zafi, ɗago kai yayi ya kalli yarinyar dake tsaye tace "waye kai da zaka bigeni?"
yayi shiru, momy ce ta fito tace "na'eema dama na faɗa miki shege baisan mutuncin mutum ba, shiyasa ya bigeki"
ta kalleshi tace "wannan ƴar yayana ne respect zaka bata kamar ta girmeka"
a hankali yace "to"
tace "oya cire kaya ka fara aiki"
cire uniform yayi ya fara aikin da yafi karfinshi, bai huta ba sai dare kafin ya samu yaje bayan kofa ya ɓuya yana kuka sabida bayaso Ammi ta ganshi, ya gaji gashi baida lafiya kuma dukan da akayi mishi yasa jikinshi ya tattashi, saida yaci kuka sosai kafin ya fito yaje wajen Ammi ya zauna yayi shiru sabida baya hira.
*Shima ɗa ne complete is ₦400 via 8144818849 hauwa shuaibu mapi moniepoint, your evidence via 08144818849*
~Ammi ta kalleshi ta tabbatar yayi kuka domin idanunshi sun nuna, zama yayi kusa da ita ta rike hanunshi tace "nawal ɗin Ammi meyasa kake kuka?"
yace "ammi suna cemin shege"
shafa kanshi tayi tace "to kasan menene ma'anan shege? shege yana nufin yaro me hankali, yaro me nutsuwa wanda ze zo ya samu mata kyakkyawa wacce zata rinƙa kula dashi a koda yaushe koda amminshi bata raye, shege yana nufin yaro nitsatse kamar nawal ɗina"
murmushi kawai yayi a duk lokacin da akace mishi shege wannan fassaran take mishi kuma yana jin daɗi a ranshi.
haka rayuwa take tafiya cikin ɗaci da wahala kullum nawal yake rayuwa, saide ya ɓuya a bayan kofa yaci kuka har ya koshi, daga nan ze share hawaye ya dawo ya zauna kusa da Ammi, ya zama kamar bawa a gidan baya zama na hutu koda na minti ɗaya ne shine bayin fulawa shine buɗe gate sabida dady ya kori megadi yasa shine zai rinka kula da gate, sannan duk wani aike da akeyi a gidan nawal ne yake zuwa, kama daga kasuwa zuwa siyan komai da komai shi yake yi, sannan babu soyayya tsakaninshi da kannenshi basu ɗaukeshi yaya ba sun tsaneshi duk zagi duk yana sha a kansu, dady yafi bashi wahala sabida shine sanadin ɓacin kujeranshi, shine ya lalata mishi komai ya bawa abokin gabanshi Alhaji sammani daman hawa kujeran gomna wanda a yanzu baida abokin gaba kamar Alhaji sammani.
***
rayuwa tana tafiya nawal ya girma domin a yanzu yana da shekaru 28 a duniya ya zama cikakken matashi me kwarjini, duk da wahalan da yake ciki wutan kyawunshi kara ruruwa yayi, ya zama kamar a sace a gudu, duk da wanda ya kalli nawal saiya kara kallonshi, Ammi bataso haka ba a rayuwa babu abinda ta tsana kamar kyau domin shine sanadin shiganta wannan mummunan halin da take ciki na rashin kwanciyar hankali da kyakkyawan rayuwa kamar yadda kowa yake yi, a kullum idan ta kalli nawal gabanta faɗuwa yake gani take kyawun da take dashi a lokacin da take budurwa babu abinda nawal ya bari, harma ya ninkata kyau da komai, ya gama secondary da kyar har yanzu kuma babu maganan karin karatu, nasir da nabil sun girma suma sannan da kanwarsu samha wacce itama a yanzu ta kai 18year itama kyakkyawa ce sosai da sosai, nasir ya zama dr shi kuma nabil ya zama lawyer kowanne a cikinsu ana damawa dashi.
nawal shine me kula da komai da komai na gidan duk abinda ya shafi wahala shi yake yi, babu kyakkyawan maganan daya taɓa shiga tsakaninshi da dady domin a duniya babu abinda dady ya tsana kamar nawal.
cikin sauri yake tafiya hanunshi rike da leda kuma sai kiran karamar wayar hanunshi ake, yasan momy ce idan bai isa gida da wuri ba zata haɗashi da dady sannan dady kalaman bakinshi babu daɗi a kanshi, shiyasa yake iya kokarinshi dan ganin yayi duk abinda ta sashi, yana tafe yana tunani halin da Ammi take ciki a gidan yafi komai tsaya mishi a rai, tana matukar shan wahala domin idan baya gidan duk aikin gidan itace take yi, duk da kafarta baya tafiya akan wheelchair take tafiya tana aikin har ta gama, wani ma saide yazo ya tarar ta faɗi ƙasa daga kan keken tana jan jikinta babu me taimaka mata kamar sunga kashi haka suke yi idan sun ganta, dady kuma ko kallo bata isheshi ba domin ya tsaneta har yau yana rike da ita akan abinda tayi mishi na tona mishi asiri ta zubar mishi da kima, nawal baida aboki kowa yana cewa ba zaiyi aboki da shage ba.
yana isa gidan ya fara kalle kalle ko zai hango Ammi, bai ganta ba kamar kullum da take zama a waje tana aiki, ya kaiwa momy sakon cikin masifa ta karba tana zaginshi, tashi yayi ya fita, sauka yake a stair yaji ihun samha shigowa tayi tana ashar kamar zata tada ɗakin, sanye take da riga da wando na pakistan ya mata kyau tayi rolling kanta da jessy veil maroon sannan tasa takalminta me tsayi da tsini shima maroon wayarta iPhone 16, nabil ne ya shigo ɗakin da belt a hanunshi yana sanye da farin riga ya nunata da belt ɗin yace "shaye shaye kike yi ba samha? samha you are drug abuser? samha me kikaje yi a club?"
jin tayi shiru ya watsa mata belt ɗin, ihu ta kuma yi tace "Allah ya isa ban yafe maka ba, kullum ka rinƙa duka na banyi maka komai ba, ina ruwanka dan nayi shaye shaye? kuma ina ruwanka dan ka ganni a club ko s*x kaga inayi jikinka ne?"
rufe ido nawal yayi yana jin zafin kalman data faɗa babu ko kunya a gaban yayanta, nabil tsayawa yayi yana kallonta yadda take mishi ihu kamar ta girmeshi, kafanshi yasa ta bayanta ya kifar da ita a kasa, wani irin dukan mutuwa ya fara mata yana taka cikinta, yace "to bari na kasheki sai kisan na girmeki"
tana ihu tace "kaima ai bakada gaskiya ko an gaya maka ban san duk wani me laifi kana kareshi bane a kotu? idan ana neman barrister mara tsoron Allah me cin hakkin mutane me maida karya ya zamo gaskiya a sameka ya nabil, kaima maci amana ne ina sane da umman khadijah wacce ka kareta a kotu bayan kasan itace batada gaskiya itace ta kashe ɗan kishiyarta tasa mishi guba a abinci yaci ita da bakinta ta faɗa maka a gidannan da kunnena naji amma sabida ta baka kuɗi ka kareta kasa aka wanketa a kotu, sanadin haka maman yaron da aka kashe ta faɗi ta mutu an gaya maka ban san danne hakkin mutane da kake yi bane?"
yace "ni dake ɗaya muke? ni namiji ne ke kuma mace"
nawal ganin abin yayi yawa ya daure ya karaso yana rike nabil, ran nabil ya ɓaci dukan mutuwa yake yiwa samha, janye samha yayi ta rikeshi tana kuka, a hankali yace "ya isa haka ku bari"
cikin masifa nabil yace "meya saka a ciki? kai har kanada bakin magana? kaida aka haifa babu aure uwarka fa zina tayi ta haifeka ba gara mu ba uwarmu batayi zina ba"
toshe kunne yayi sabida wannan maganan yana dakan mishi zuciya, saida ya gama kafin yace "kada ka kara cemin ɗan zina"
samha tace "karya yayi kai ba ɗan zina bane? karya yayi ba zina amminka tayi da dady suka samu cikinka ba? Ada aure suka haifeka?"
jikinshi ya fara rawa, ya ɗaga hanu zai mari samha nabil ya rike hanun yace "karka sake ka taɓa mana kanwa wallahi kana taɓata sai mun kasheka a gidannan"
shiru yayi bayason ɗaga hankalin Ammi idan taji suna rigima hankalinta tashi zeyi, yace "sakarmin hannu"
"Idan yaki saki fa?"
nasir wanda yake sanye da labcoat da glasses fari siriri a idonshi yayi maganan, aje briefcase ɗinshi yayi sannan yace "meya saka cikin faɗan ƴan uwan juna? meya saka cikin faɗan waɗanda aka haifesu ta hanyar sunna? meya sa bakinka? ai ko kashe kansu zasuyi ka kyalesu tunda faɗan masu uba ake"
fizge hanunshi kawai yayi ya juya zai tafi yaji nabil yace "idan na kara ganinki a club kina shan abu saina kashe ki"
tace "babu abinda ya shafeka da rayuwa ta...."
mari nasir ya wanketa dashi yace "ke yayanki yana magana kina magana who are you?"
ta dafa kunci tace "yaya nas ina ganin mutuncinka duk da kaima ba me mutunci bane sabida duk garinnan babu likitan da yake zubar da ciki kamar kai, kaine dr da yake iya markaɗa yaro a cikin uwarshi ko wata nawa yake dashi babu tausayi babu tsoron Allah sabida haka nasan halin kowa a gidannan babu wanda....."
duka ya rufeta dashi, nabil yana tayashi, momy da gudu ta fito tana cewa "nabil? nasir zaku kasheta ne? kun fara kuma yau ko? Allah ya wayi gari kun samu daman faɗa da juna kamar karnuka ɗin ko? wai sai yaushe zaku nutsu ne ku zama mutanen kirki kamar kowane ɗa? meyasa kuka zama mutanen banza ne? meyasa bakuda aiki sai faɗa da juna da bakar magana a tsakaninku? kunaso sai na mutu zaku shirya? sai kun kasheni zakuji daɗi?"
nabil yace "momy a club fa na ganta, tana shan giya momy giya fa"
sallama dady yayi, yace "to gari ya waye kun fara kuma ko?"
shiru sukayi babu wanda ya kara magana, yace "kowa ya koma ɗakinshi banason rigima"
nasir yace "dady dama akwai maganan da nakeso muyi"
yace "ina jinka"
sosa kai yayi yace "dady dama kuɗi nakeso 20million naira zan siyi wani abu"
dady ya zauna akan sofa yace "okay zansa maka a account anjima amma banason wannan faɗan"
yace "thank you dady"
samha tace "dady nima inason 8million za'ayi birthday ɗin kawata"
yace "okay kema zansa miki anjima amma kada na kara ji kuna faɗa da junanku"
tace "to dady"
momy zama tayi kusa dashi duk suka tafi kowa ya nufi ɗakinshi, samha ɗakinta me masifan kyau ta shiga ta faɗa gado ta fara bacci bata cire ko takalmi ba, da jakan a gefenta.
nabil yana shiga ɗaki ya kwanta a sofa ya cire takalmin yace "bro yau fa kotu babu daɗi saura kiris nayi loosing yau"
nasir yana rage kayan jikinshi yace "kaji tsoron Allah fa nabil akwai mutuwa"
wani harara ya aika mishi sannan yace "kai har kanada bakin da zakace aji tsoron Allah? akwai ma wanda ya kaika rashin tsoron Allah? kaida kake markaɗa yara a cikin ciki, duk wata karuwar garinnan ai kaine ka bata lasisi domin kai kake zubar da ciki idan ta samu"
tsaki yaja yace "to ni nace suyi?"
nabil yace "nasan kuɗinnan da kace dady ya baka ma mata zaka ɗauko ɗan iska kaida baka ɗaukan mace ɗaya ma sai biyu ko uku tsaban iskanci shine zakace aji tsoron Allah? ba gara ni da bana neman mata ba iyakana danne hakkin mutane a kotu mara gaskiya na bashi gaskiya"
ɗaura towel yayi a waist sannan ya ɗau brush yace "kaika sani"
shiga wanka yayi shi kuma nabil ya fara chatting.
Nawal ɗakin ammi yaje yana shiga yaji wari ya bugashi, be toshe hanci ba sabida ammi tafi ƙarfin toshe hanci a wajenshi ko wani irin wari yaji daga gareta koda zai cutar dashi ba zai taɓa toshe hanci ba, tana kwance akan gado kamar batada rai, da gudu yazo yana kiranta "Ammi? Ammi?"
a hankali ta buɗe idanunta da suka kankance suka koma jajur murya kasa kasa tace "nawal kafafuna sun ruɓe nawal inda aka yanke sun ruɓe suna tsutsa nawal ka fita kada wari ya illataka nawal kaje kayi rayuwa ka barni anan nawal kada warin yasa maka cuta"
wasu zafafan hawayen tausayin ammi ne suka cika kyawawan idanunshi, yaji duk duniya babu abinda ya tsana kamar ciwon ammi, a hankali yasa hanu ya ɗaga rigan dake jininta wanda ya rufe kafafun, rufe ido yayi ganin kafarta yana tsutsa ga wani wari da yake yi, baisan time ɗin daya saki rigan ya silale a wajen ya rushe da wani irin kuka me cin rai ba, cikin jin ciwo tace "nawal kasan babu abinda banaso kamar naga kana kuka ko? nawal kullum sai kayi kuka banaso ka kare rayuwarka cikin kuka nawal dan Allah kada kayi kuka koda na mutu ban yadda kamin kuka ba nawal"
tashi yayi yace "dole mu tafi asibiti ba zan jure ganinki haka ba Ammi"
fita yayi daga ɗakin yanaji tana kiranshi, ɗakinsu dady yaje, a kasa ya durkusa ya rike kafafun dady yace "dan Allah dan darajan ma'aiki s.a.w ka taimaki rayuwar ammi na ka kaita asibiti kada ta mutu"
janye ƙafarshi yayi sannan ya tashi yace "tashi mana"
tashi nawal yayi, ya kalleshi sannan yayi murmushi yace "nawal ko?"
gyaɗa kai yayi alaman eh, ya kara murmushi sannan yace "kasan wani rana ne nake jiran zuwanshi a rayuwata?"
ya girgiza kai, yace "ranan mutuwan wannan tsinanniyar Ammin taka, da inada dama dana jima da kaita lahira, kasan meyasa ban kasheta ba? sabida nasan zan zama suspect shiyasa ba barta amma kowane rana wutan tsananta kara ruruwa yake a cikin zuciyata, zanyi farin ciki idan numfashinta ya ɗauke yanzu"
zubewa kasa yayi ya rike kafafunshi duka biyu yana rokonshi yace "dan girman Allah ba dan halina ba ka taimaka"
janye ƙafarshi yayi ya juya ya bar wajen, rike kafafun momy yayi yana kuka yace "ki taimaka ki ceci rayuwar ammi na rokeki"
dariya kaɗan tayi sannan tace "kasan yadda nake jin tsananta kamar yadda nakejin tsanarka ne a duk lokacin dana tuna dadyn yarana yanada wani ɗa guda ɗaya a gefe, mutuwa ne kawai banayi sannan ni bazan taimaki kishiya ba"
janye kafarta tayi ta barshi a wajen, gashinshi ya haɗa da kasa yayi shiru hawaye yana sauka har kan tiles, yafi minti talatin a wajen baida niyan ɗago kanshi, samha wacce ta tashi daga bacci tasa wani ɗan iskan karamin riga wanda ya kama jikinta sosai babu ɗankwali ta bazo gashin baya tana tafiya a ɗan bige sabida har yanzu giyan be saketa ba, murza ido tayi cikin muryanta da bai gama warwarewa ba tace "waye a kwance a kasa haka?"
shiru yayi mata bai ɗago kai ba kuma har yanzu hawaye basu daina zuba ba, tace "ya Allah may be matsalan kuɗi ke damunka, ga hanyoyin samun kuɗi dayawa yanzu wa zai tsaya yana kukan kuɗi?"
tafiya take tana magana da alama batama san me take cewa ba, har taje bakin kitchen tace "ga kidnapping ga sata zasu kawo maka kuɗi ga kuma saida kwaya"
kitchen ɗin ta shiga taci abinci a wajen ta kara kwanciya a bige ta fara bacci.
nawal sai yanzu ya ɗago kanshi a hankali ya tashi ya tsaya gaban mirror dake korido ya kalli kanshi sannan yace "kidnapping? sata? saida ƙwaya?"
ya rufe ido sabida yasan shi wannan da yake kallon kashi a madubi ba zai iya wannan aikin ba, sai kuma ya fara tuna ranan da ammi batada lafiya ranan da yaje neman magani a asibiti dr yayi mishi wulaƙanci, a ranan ya sace dr kuma ya samu biyan buƙata, a hankali ya buɗe manyan idanunshi da suka koma red, ya ciza pink lip nashi na kasa ya cusa cikin bakinshi hanu yasa akan tulin gashin kanshi da yake a kwance luf luf yasa yatsu biyu ya tada gashin, rigan jikinshi ya kalla sannan ya kara kallon kanshi a madubi, wani irin murmushin gefen baki yayi wanda ya bala'in kara mishi kyau.
*Shima ɗa ne complete is ₦400 via 8144818849 Hauwa shuaibu mapi, moniepoint, evidence via 08144818849*
~Ya jima yana kallon kanshi a haka kafin ya bar wajen, ɗakin ammi yaje ya tarar tana baccin wahala, cak ya ɗagata be damu da komai ba ya rungumeta, fita yayi da ita a ɗakin, yana rungume da ita tana bacci batama san ya ɗauketa ba, gidan ya bari ya tari taxi yace a kaishi babban asibitin da yafi kowane asibiti tsada da kyau a garin, me taxi ya amsa mishi da to, har yanzu tana kwance a jikinshi tana bacci, yadda take baccin ya tabbatar mishi ta jima bata samu bacci ba, murmushi yayi ya shafa kyakkyawan fuskanta da tsaban wahala saida ta koma baƙa, hawaye masu zafi ya share, a kofan wani tsadadden asibiti suka tsaya me bala'in kyau, yace "wannan shine asibiti mafi tsada likitoci daga India suka zo aiki anan"
yace "na gode"
biyanshi kuɗi yayi sannan ya ɗauketa ya shiga ciki da ita, akwai layi hakan yasa ya zauna a kasa sabida taji daɗin kwanciya, bin mutane yake da ido, ya girma haka yake sabida takura baya magana baya shiga harkan kowa koda anyi mishi magana be fiye amsawa ba, saide ya gyaɗa kai ko kuma ya zubawa mutum ido, ammi ce kaɗai ta fahimceshi sabida ta zauna dashi ga wanda be zauna dashi ba zai ce yanada masifan girman kai, har layi yazo kansu kafin suka shiga dan ganin likita, babban likitan yana duba ciwon yace sai anyi aiki sannan asa mata kafafun roba ta yadda zata iya takawa amma ba kamar yadda kowane ɗan adam yake takawa ba, likita ya kara da cewa dole sai an kashe manyan kuɗaɗe domin yin wannan aikin sabida ƙafan ya riga ya cinye duka sai an cire inda akayi aiki aka rage a baya, aikin beyi kyau ba shiyas ya kara ruɓewa, ya kara da cewa zaka iya tafiya da ita idan kun shirya sai ka kawota ayi mata aikin"
yace "ayi aikin na shirya"
dr ya kalleshi sannan ya kara kallonta yace "kasan nawa ake bukata a cikin kwana uku da ake aikin?"
yace "a faɗamin koma nawa ne zan biya"
dr yace "miliyan ɗari bakwai ake nema fa"
saida gabanshi ya faɗi, cikin dauriya yace "ayi aikin zan biya a cikin kwana uku"
takadda ya bashi yace "okay kayi sign to"
sign yayi dr ya kira aka kaita ɗakin tiyata, yace "nan da kwana uku zata fito daga ɗakin lafiya lau da kafafun roba amma fa ba zaka ganta bama koda mun