x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 7 - SHIMA DA NE free pages

  • 18001 words
  • 21000 words
  • Out of 65957 words

Category: Love Stories

Views 222

25 Aug 2025
Start ads
After Image Ads
matata ce? ka aje magani kafita kafin na kira maka police"
ajewa yayi yace "zata iya mutuwa Dr"
yace "ta mutu, ba zaka samu magani ba sai ka kawo dubu goma"
duk rokon da yayi mishi yaki yadda daga karshe ya ɗaga waya ya kira police, nan ne ya fita sabida beson a kamashi.
ya koma wajen ammi ya zauna yana kallonta har tayi rawan sanyin ta gaji, be samu kuɗin magani ba har washe gari, ya tashi da sassafe domin neman abinda zasuci, cikin rashin sa'a aka biyo ɓarawo mutane ne dayawa da sanduna, suna ganin nawal wani yace "shine wallahi shine ɓarawon"
nawal cikin rashin sanin me suke nufi yace "wallahi ni ba ɓarawo bane, banyi sata ba kuma ban taɓa sata ba...."
sanduna bulala duk suka fara dukanshi dashi, duka suke mishi na rashin imani, yace "bani bane"
wani yace "dama taya zaka yadda kaine? idan ba kai bane meya fito da kai da sassafe haka? mutane suna gidan ubansu kai kana layi? ko dai shege ne kai bakada uba mun san sune suke addaban mutane"
jikinshi yayi lankwas sabida ba karamin duka sukayi mishi ba, ɗayan yace "ku kawo fetur mu kona shi gobe ba zai kara sata ba"
fetur suka kawo suka zuba a kanshi tayoyi suka sa mishi sannan suka kara fetur ɗin, ashana zasu kyafta wani babban mutum yana wucewa yace "haba bayin Allah meyasa zaku kashe shi?"
wanda ya kyasta ashana yace "sata yayi kuma dole sai mun kashe shi"
wutan yasa, take jikin nawal ya fara ci da wuta, da gudu mutumin yazo yana kashe wutan daya fara ci a jikin nawal, yace "Allah be ce a kashe wanda yayi sata ba, yace a yanke hanunshi ɗaya idan ya kara a yanke ɗayan hanun idan kuma ya kara a yanke kafarshi idan ya kara a yanke ɗayan kafar, me yasa zaku ɗau hukuncin kisa aka ɓarawo?"
shiru sukayi, yace "bawan Allah tashi ka tafi"
tashi yayi zasu kara rufeshi da duka mutumin ya tareshi da kyar ya samu ya kuɓuce, jikinshi kamar babu jini haka yake tafiya ya gaji sosai kuma be samu komai ba.

ya koma wajen ammi wacce jikinta yayi zafi, yayi tagumi kawai yana kallonta, motan dr ya gani yana wucewa, a ranshi yaji babu wanda ya tsana kamar wannan dr ɗin, binshi yayi a baya be san me zaiyi ba amma ji yayi a ranshi yanaso ya hukunta wannan daya hana amminshi magani, har yayi nisa kafin ya tsaya siyan nama, saida yaga babu kowa ya buɗe boot na motar ya shiga rufewa yayi har dr yazo ya shiga motar yaja, a fili yace "ya naji yanzu motar ta ɗanyi nauyi?"
cigaba yayi da driving har zuwa gidanshi aka buɗe mishi gate nashi na alfarma ya shiga, fita yayi ya ɗauki manya manyan ledojin daya zo dashi, nawal saida yaga ya fita kafin shima ya fita, dare yayi hakan yasa babu wanda ya kula, yana ganinshi matarshi tazo ta karɓi ledojin, fakewa yayi har dare yayi nisa, wani kyalle daya gani a motar ya ɗauka ya ɗaure fuskanshi ta yadda babu me iya ganeshi, shiga ciki yayi cikin sanɗa yake bi ta jikin bango har ya shiga ciki, duk sunyi bacci harda Dr, wani irin zafi nawal yake ji a ranshi idan ya tuna duk abinda dr yayi mishi daga shekarun baya har zuwa yau, durkusawa yayi ya ɗaure bakin dr da ɗankwalin matarshi, janshi ya fara akan tile ya fita dashi, a motar ya sashi sannan ya shiga baisan yadda ake driving ba amma yana gani, hakan yasa yayi hon dr ya buɗe ya fita dashi a gidan, gudu yake bai san inda ze taɓa ya tsaya ba, da haka har dr ya tashi ya fara fizgewa, nawal cikin rashin magananshi yace "kayi shiru ko kuma na kifar damu a motar nan, iyalanka su zama marayu"
tsit yayi, nawal yayi yayi ya tsayar da motar taki tsayawa saida suka shiga wani daji suka bugu da bishiya kafin motar ta tsaya, ganin motar zata fara ci da wuta yayi gaggawan cire dr ya wurgar dashi a gefe, take motar ta kama da wuta, dr yana kallonshi ya rufe fuska ba zaka gane shi ba, wayan aljihun dr ya ciro sannan ya ɗaureshi a jikin bishiya bayan ya buga mishi itacen bishiya a kanshi ya suma, ya zauna a gefe yana jin kukan tsuntsaye, a wajen yayi bacci, washe gari da ruwan sama aka tashi, buɗe ido yayi a hankali yana bin dajin da kallo, sauke idonshi yayi akan dr wanda har yanzu a sume yake, wayan ya ɗaga ya amsa call ɗin daya shigo, cikin tashin hankali matarshi tace "mun nemeka na kiraka na kiraka baka ɗauka ba, nasan babu lafiya ina kake dr?"
murmushi yayi yace "yana nan yana raye amma dab yake da mutuwa a hanuna"
cikin tashin hankali tace "waye kai? me yayi maka? me kake so?"
yace "amsan karshe kawai zan iya baki shine me nake so"
tace "dan Allah kada ku cutar dashi ka fadi duk abinda kake so wallahi zamu baka"
murmushi ya kuma yi sannan yace "idan kika sake kika sa hukuma a wannan maganan zan kashe shi"
tace "wallahi na rantse maka da Allah babu wanda zan faɗawa ka faɗi duk abinda kake so"
yace "magani nake so"
da mamaki tace "magani kuma?"
yace "eh maganin zazzaɓi nake so"
shiru tayi, sai kuma tace "shikenan ka faɗi inda zan aje zan kai maka harma da naira miliyan ɗaya"
yace "magani kawai nake so ki aje a kofan asibiti sannan idan na ɗauka zan faɗa miki inda yake kije ki ɗaukeshi"
tace "yanzu zan aje"
da gudu ta fita ta kai, ta kirashi ta tabbatar ta kai sannan yaje ya ɗauka, ganin ba'a kamashi ba ya faɗa mata inda zata ɗaukeshi.
maganin ya kaiwa Ammi ya bata tasha kuma Allah yasa zazzaɓin ya fara sauka, hamdala yayi ya kara godewa Allah da bata mutu ba.

matsalan abinci da wajen zama ya fara damunshi duk hanyan da zebi ya samu kuɗi yabi be samu ba, Allah ya haɗashi da wani me gyaran gado yana zuwa suna gyara tare saide naira 500 yake bashi, duk gajiyan da zeyi ɗari biyar yake bashi, yana kallon irin makudan kuɗaɗen da mutumin yake samu kuma tare dashi suke aikin, yau yazo mishi da zancen baida lafiya ya bashi kuɗi ya siya magani, mutumin ya fara masifa da bala'i meyasa ze tambayeshi kuɗin magani kenan be gode da 500 ɗin da yake bashi ba?
shiru yayi kanshi a kasa har ya gama, cikin rashin magananshi da tsananin hakurinshi ya fara aiki.
har zazzaɓi yaci jikinshi babu magani babu kuɗin magani, shawara ya yanke ze sace uban gidanshi har sai ya samu kuɗin magani zai sakeshi, hakan kuwa akayi saida aka kusa tashi yasa mishi magani a ruwa, yana sha ya fara bacci a wajen har dare nawal yayi kamar be ganshi ba yana cigaba da aikinshi, saida dare yayi nisa kafin ya janyeshi a wajen ya kaishi inda babu wanda ze san yana wajen, kara haɗa maganin yayi yasa mishi a baki saida ya shanye ya kwantar dashi ya rufe bakinshi, nemanshi aka fara ciki da waje, iyalanshi sunfi kowa shiga tashin hankali, murmushi nawal yayi kuma tare dashi suke nemanshi, waya ya samu karami yasa sim ya kirasu kudi ya yanka musu miliyan ɗaya domin ko kaɗan baya jin tausayinshi.
sun aje kuɗin ya dauka kafin ya faɗa musu inda yake, bayan komai ya wuce tare suka kara cigaba da aiki.
hankalin nawal ya fara rabuwa kashi biyu, kuɗin daya samu beso ya rabu dashi, murmushi yayi shi kaɗai yana kallon ammi da take cin abinci me kyau daya siya mata, sauran kuɗin ya sadakar wa yara, sabida kullum nasihan ammi shine nawal kaji tsoron Allah.

*Shima ɗa ne complete is ₦400 via 8144818849 Hauwa shuaibu mapi moniepoint, evidence via 08144818849*


_Jiddah Ce...✍️_
[17/08, 11:03 pm] +234 814 481 8849: 🌸🌸🌸🌸🌸
*SHIMA ƊA NE*
🌸🌸🌸🌸🌸


Na
*Jiddah S Mapi*


*Chapter 9*


~Cikin tashin hankali hajiya naja ta kira layin Dr, nabil ne ya shigo shima yaro ne kyakkyawa yana kama da yayanshi nasir, saide yafi nasir kiba domin jikinshi irin na girman falo ne, ya kalli nasir da yake kuka yace "bro nas meya samu dady? kar dai sabida wannan useless ɗin ya faɗi?"
nasir yace "eh sabida su ne nabil banaso dady ya mutu ya barmu"
nabil yace "that's why I hate them, I don't even want to see there faces daga shi har wannan kazamar gurguwan matar, dama momy tace talakawa suna son yiwa me kuɗi sharri they want to have connection with us sabida kuɗin dady"
nasir ya janyoshi jiki ya rungumeshi yace "stop crying dady will not die insha Allah"
momy kam ta goya hannaye a baya banda safa da marwa babu abinda take yi, ta rasa me zata fara yi, dr ɗinsu wanda yake kula dasu ya shigo domin security tasa suka shigo dashi, fara dubashi yayi ya kalli momy dake kallonshi tana jiran amsa yace "yana bukatan gado emergency"
a ruɗe tace "to ka taimaka mana mu kaishi"
hijabi tasa suka rike dady harda su nasir suka fita dashi.

nawal dake zaune yayi tagumi sabida yadda yaga gidan yasan da wuya suji daɗin zama anan, Ammi tace "nawal"
a hankali yace "na'am"
gefenta ta nuna mishi tace "zauna anan"
zama yayi ya ɗaura kanshi akan keken guragu sannan tace "nawal ka saki jiki ka zauna a gidannan domin nan shine asalinka, wannan shine mahaifinka nawal banaso na mutu na barka bakada kowa, ka daure duk wani abinda za'ayi maka kamin alƙawari ba zakayi fushi ka bar asalinka ba"
a hankali yace "na miki alkwari"
tace "nawal ka ɗago ka kalleni kace nayi alkwari duk wahalan da zansha ba zan tafi na bar asalina ba"
da kyawawan idanunshi masu ɗaukan hankali ya kalleta, a hankali cikin nutsuwanshi ya motsa lips nashi wanda suke pink sosai har sun koma red kaɗan, yace "nayi alkwari duk wahalan da zansha ba zan bar asalina ba"
murmushi tayi tace "Allah ya maka albarka"
ya ɗaura kanshi a cinyarta a hankali yace "ameen"
hawaye ta share na tausayinshi, tasan akwai kalubale me yawa da zai fuskanta a gidannan sabida taga alamu tun a kotu, amma dole ya hakura sabida shine mahaifinsa, fitowa sukayi da dady wanda baya motsi, momy ihu ta fara tana cewa "na shiga uku ku taimakeni kar ya mutu"
nasir da nabil babu takalmi a kafarsu suke binsu a baya dr yana rike dashi, nawal da sauri ya tashi yana kallonsu, ganin dady a haka ya kalli ammi, lumshe ido tayi ta mishi alaman yaje, da sauri ya fita, babban compound na gidan wanda yake ɗauke da manyan motoci masu tsada da kyau suka nufa, wani katon jeep baƙi ƙirin suka buɗe, ɗaga dady yayi amma ya kasa sashi a motan, nawal ne yazo yasa hanu zai taimaka musu a sashi a mota, wani marin da momy ta bashi saida ya dafa kunci, ta rike hanunshi da karfi tayi wurgi dashi, faɗuwa kasa yayi ta nunashi da yatsa cikin masifa da tsananin tsanan da take mishi tace "don't dare touch my husband"
jikinta har yana rawa tace "idan ka kara taɓashi da wannan ƙazamin hanun naka sai na lahira ya fika jin daɗi, kaje ka samu wannan kazamar matar da kuka taho tare ka faɗa mata ni nafi karfin kishiya, sannan ka gaya mata babban goro sai magogin karfe, bamuda alaka da matsiyata daga zuriyar mahaifina har na mahaifiyata harma da zuri'ar mijina kaje ka nemi ubanka wannan uban ƴaƴana ne kuma ba zasu haɗa uba da kowa ba"
dr yace "hajiya muje kada wani abin ya samu Alhaji"
tana huci ta tufawa nawal yawun bakinta tace "kazami"
nasir da nabil kallon tsana suke mishi har suka shiga mota suka barshi a wajen, tashi yayi bayan sun fita ya koma ɗakin Ammi, duk abinda ya faru ta gani, suna haɗa ido taji hawaye a idanunta, murmushi yayi mata sannan yace "ammi banji ciwo ba fa kinga murmushi ma nake yi"
sunkuyar da kai tayi tace "ka yafemin nawal..."
da sauri yazo ya rufe mata baki yace "shii Ammi kada kice haka baki min komai ba kuma banji komai ba"
rungumeshi tayi yayi shiru yana tuna maganganun da hajiya naja ta faɗa mishi.
kwana biyu sukayi a asibiti aka sanar mata kada su rinƙa yin abinda ze ɓata mishi rai domin gab yake da kamuwa da mummunan ciwon hawan jini, a mota suke driver yana tukasu tareda yaran suke tace "dan Allah kayi hakuri wallahi ba zan iya jure rasaka ba"
girgiza kai yayi yace "na miki laifi kiyi hakuri dole kimin hukunci sannan na yiwa yarana laifi ki rokamin su yafiya kuma insha Allah ba zan taɓa haɗasu da kowa ba"
tace "sun jima da yafe maka"
sukayi shiru a motan, gate ɗin aka buɗe suka shiga, a compound akayi parking, buɗe musu marfin motan akayi nasir ne ya fara fitowa ya rike babban basket yana mika sabida ya gaji, duk suka fito, nabil ya rike wuyanshi suka jera suna tafiya su ammi suna bayansu, nawal da yake gyaran flower yana basu ruwa ya hangosu daga nesa, da shike gidan yanada girma, hanunshi rike da tiyo yana bayin dogayen fulawoyin gidan yana tabbatar sun samu ruwa da kyau, tunda ya lura ba'a basu kulawa yadda ya kamata ya karɓi bayin a matsayin aikin da zai rinƙa yi kullum, aje tiyo yayi cikin jin daɗin ganinsu yaje yana cewa "kun dawo?"
ko kallonshi basu yi ba, duk da ya girmesu bai hanashi karɓan basket na hanun nasir ba, wurga mishi basket ɗin nasir yayi sannan ya taɓe baki ya tufar da yawu ya kalli nabil yace "wari nakeji"
nabil ya toshe hanci ya nuna nawal yace "shi yake wari"
jikin nawal yayi sanyi ya tsaya da basket ɗin a hanu, kallon jikinshi yayi yaga babu datti tsaf yake sabida yana wanka kullum, a lokacin momy suka karaso, durkusawa yayi ya gaishe da dady tareda momyn sannan yace "ya jiki?"
momy a harzuƙe tace "ina ruwanka da jikinshi? me haɗinka dashi da zaka mishi wannan tambayan?"
dady yaja tsaki yace "please kyaleshi muje ciki"
tafiya sukayi suka barshi a wajen rike da basket ɗin, jikinshi a mace ya kai basket ciki ya dawo yana cigaba da bayin fulawa.

washe gari tsadadden school ɗin da suke ciki momy ta shiryasu cikin uniform nasu maroon na wando da riga white, sunyi kyau sosai kowa yana rike da lunchbox wanda akasa musu egg da Irish da drinks nasu a ciki, kowa ya rataya katon jaka suka fito tareda dady yana rike da hanunsu sun sashi a tsakiya, mota suka shiga da kanshi ya shiga buɗe mishi gate akayi harya kunna mota zai tafi yaga nawal tsaye a jikin kofa, ɓata rai yayi ya tuna da maganan alkali na cewar dole ya sashi a school ɗin da yaranshi suke karatu, rai ɓace ya buɗe motan yayi mishi alaman yazo da hanu, zuwa yayi yace "shiga"
shiga yayi ya tada motan be kara dariya ba har suka isa school ɗin, da kanshi ya kai sauran yaran class nasu sannan ya kalli nawal yace "duk wanda ya tambayeka kai ɗana ne karka kuskura kace kai ɗana ne kace tsintarka nayi"
kanshi kasa yace "to"
shiga ciki sukayi ya fara mishi registration, sukace "ya sunanka?"
a hankali yace "nawal Alhasan medara"
wani kallon da dady yayi mishi shi yasa jikinshi fara rawa, da sauri yace "da wasa nake sunana nawal rahama"
ɗauke kai dady yayi, suka sa mishi nawal rahama, bayan ya biya kuɗi ya fita ba tareda yasan ko wani class zasu kaishi ba.
sun nuna mishi class nashi sannan suka nashi uniform akan gobe yasa idan zai zo, shiru yayi ya zauna a class ɗin, sam bayason magana shiru yafi mishi daɗi.

washe gari ya shirya cikin uniform ɗin kamar yadda suma suka shirya, yana tsaye a compound yana murmushi sabida ze je school, dady tareda yaran suka fito sai hira suke yana basu labari suna dariya, ganin nawal ya ɗaure fuska yaki dariya, yaran yasa a mota sannan ya shiga bai ko kalli inda nawal yake ba, ammi dake kallonsu idonta ya cika da hawaye ganin nawal tsaye yana murmushin yaƙe.
zai fita momy tace "kai tsaya"
tsayawa yayi yana kallonta har ta karaso, cikin respect ya durkusa yace "ina kwana momy"
wani bakin ciki taji a ranta, tace "na maka kama da momynka?"
shiru yayi, tace "tashi muje ciki aiki zakayi yaran yayana suna hanya yau"
yace "zanje makaranta...."
cup na ruwan dake hanunta ta kwala mishi a goshi, rikewa yayi yace "wayyo"
duka ta fara mishi a baya tace "zaka je makaranta kake gayamin ni sa'arka ce da zansa ka aiki kaki?"
cikin tsawa tace "ka biyoni nace"
jikinshi yana rawa ya bita, har zuwa falonta me girma ta bashi mopper tace "gashi so nake naga komai yayi tsaf, sannan wancan ɗakin zasu sauka a ciki ka tabbatar ka gyara"
karɓa yayi ta fita daga ɗakin ta barshi, aikin ya fara da sauri sabida ya samu ya gama ya tafi makaranta, aikin ba kaɗan bane hakan kuwa ya gama ze tafi ta buɗe kofan ta shigo, ruwan da ya manta be goge ba ta taka, faɗuwa tayi cikin azaba tace "wayyo Allah"
da gudu yazo yana ɗagata yana ce mata sannu, rikeshi tayi bayan ta tashi, katon roban mopping ɗin ta ɗauka ta fara kwala mishi aka kamar zata kashe shi, tun yana ihu har yayi lakwas yayi shiru yana jinta kawai tana kwala mishi saida ta gaji dan kanta kafin ta kyaleshi kwance a wajen yana rike da kanshi.
cikin wahala yaja jikinshi da jakan da takaddun suke ciki ya fita, be yadda ammi ta ganshi ba ya fara tafiya har zuwa waje, kanshi na jini amma be damu ba so yake yaje school ɗin yayi karatu, kallon hanya yake yi yana tuna inda sukabi jiya a mota, Allah ya bawa nawal basira yana gane abu da wuri, shi kaɗai yake tafiya be tambayi kowa ba Allah yasa ya hango school ɗin daga nesa, murmushi yayi har ya karasa da kafa, yayi late hakan yasa akayi mishi bulalan late jikinshi yayi tsami ya daure yaje class ya zauna yana sauraran karatu.

bayan an tashi ya fito yana ganin nabil da nasir a wajen abokansu yana smiling yaje yace "nabil zamu tafi daku tare?"
nasir yace "no kayi tafiyarka dan babu haɗinmu da kai"
abokin nabil yace "nabil where do you get this handsome boy? ka ganshi kyakkyawa kamar ɗan India?"
nabil ya ɓata rai
End Ads