x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 19 - SHIMA DA NE free pages

  • 54001 words
  • 57000 words
  • Out of 65957 words

Category: Love Stories

Views 230

25 Aug 2025
Start ads
After Image Ads
tace "la'ilaha illallah Ibtee ta kwace hanunta daga nawa janna, janna Ibtee ta nuna ba zata ki aurenshi ba janna"
kuka mami ta fara janna ce ta dawo tana bata hakuri, jaad yace "wai mami me aciki dan ta aureshi? shi yayi laifin..."
a fusace zata kai mishi duka ya fita da gudu.

Mami da janna duk yadda sukaso su hana auren Ibtee taki, tuggu suke yi ta yadda Abba da kanshi zai kori nawal a gidan Abu ya gagara, ramewa mami ta fara tana neman hanyan da zata raba mara zuri'a da ƴarta, amma sam Ibtee taki, duka zagi faɗa mami babu wanda batayi mata ba, harma ta dawo yi mata nasiha taki, Abba ya bata karamin waya yace su rinka waya da nawal, duk wani abu na abba ya ɗaura nawal akai yanzu nawal shine manager ɗin company ɗin Abba, shaƙuwa sosai yayi da ibtisam sabida soyayya da take nuna mishi, masha Allah yau saura kwana uku aure, tana zaune a garden tana kallon tsuntsaye tayi shiru, jiran nawal take domin anan yake zuwa suna hira idan batason damuwa, ganin bai zo ba har yanzu ta kira wayarshi a kashe, cikin damuwa tace "meyasa bai zo ba?"
numbern kamal ta kira tace meyasa yau nawal baizo ba? kamal yace Amminshi ce babu lafiya, tayi godiya ta kashe wayan, tashi tayi ta tafi, ɗakinsu ta shiga tasa dogon hijabi tasa flat shoe zata fita janna tace "ina zaki unty Ibtee?"
tana gyara fuskanta tace "gidansu nawal"
tashi tayi tazo inda take tace "unty Ibtee dole ne na hakura nabi zaɓinki sabida ina sanki ba zan iya fushi dake ba, amma ki sani wallahi ba zan taɓa son ko girmama nawal ba har duniya ta tashi"
murmushi tayi tace "soyayyan da kikemin kaɗai ya isa janna kuma na gode, saide shima soyayyan da nake mishi kaɗai ya isheshi ba sai kin kara da naki ba"
a hankali ta buɗe mata hanu tace "come here"
zuwa tayi ta rungumeta, murmushi tayi tana shafa bayanta tace "kiyi hakuri da fushin da nake dake"
tace "ba komai ya wuce janna bari naje kada dare yayi"
sakinta tayi ta fita, janna tace "ya zanyi? dole na hakura amma zaiga asalin munafurci"
Ibtee taga mami a falo, cikin respect ta gaisheta ɗauke kai tayi bata amsa ba, a hankali ta tashi ta fita.
mota ta shiga direct sai gidansu nawal, sallama tayi aka buɗe mata gata ta shiga, a hankali take tafiya tana kallon katon gidan daya girmi nasu, da tambaya ta isa main parlour, tsayawa tayi tana sallama, amsawa akayi samha tace "wasalam waye da yamma nan yake rafkawa mutane sallama kamar gidan ubanshi?"
a bige tayi maganan tana saukowa kamar zata faɗi a stair, sanye da riga guntu da wani banzan takalmi me uban gashi, ganin zata faɗi Ibtee taje da gudu ta riketa ta faɗo a jikinta, taɓe baki tayi ta yatsine fuska tace "wacece ke?"
tace "sunana ibtisam"
tsaki taja ta janye jikinta tace "meya dameni da sunanki?"
shiru Ibtee tayi tana kallonta, nasir ne ya shigo da wata budurwa suka zauna akan sofa, gaisheshi Ibtee tayi ko kallonta baiyi ba, magani ya ɓare sannan ya ɗauko ruwa yace "gashi drink it cikin zai zube yanzu, wannan medicine ɗin asalinshi anyi ne for abortion so relax and drink nothin will happen"
karɓa tayi da alama tasha kuka domin idonta a kumbure, shan maganin tayi sannan yace "sleep"
kwanciya tayi ibtisam tana tsaye tana kallon ikon Allah, a ranta tace "ko dai ba nan bane gidan da akamin kwatance? anya kamal baiyi mistake ba?"
jim kaɗan taga yarinyar ta fara birgima tana rike ciki, kuka ta fara tana cewa "cikina"
yace "sorry abortion yayi yaron zai sauka yanzu ki daure"
ihu takeyi kuma da mamakin Ibtee babu wanda ya fito, ta fara tsorata zuwa yanzu dama tanada saurin jin tsoro, wayan nawal ta kara kira yanzu ya shiga amma bai ɗauka ba, juyawa tayi zata fita nabil ya shigo yana waya tsayawa tayi ya gama ta tambayeshi ko zai bata amsa, ji tayi yace "eh koda bakada gaskiya nasan kai kayi kisan faruk amma na maka alƙawari zan kareka a kotu"
dariya ya kwashe dashi sannan yace "karka damu ka kawomin kuɗin anjima dan bana karɓan transfer, zan bawa alkali nashi cin hancin babu wanda zai kamaka bakaga case ɗin fyaɗen daka yiwa wancan yarinyar na rufe ba?"
dariya yayi yace "to faruk sai kazo"
katse wayan yayi, Ibtee tayi shiru ta kasa tambayanshi, yace "who are you?"
tace "tambaya nazo yi"
harara yayi mata yace "for what?"
tace "dan Allah nawal nake nema ance nan gidansu ne"
wani kallo yayi mata sannan yace "point of correction nan ba gidansu bane nan gidanmu ne"
shiru tayi, nuna mata hanya yayi yace "fita"
da sauri ya kama hanya zata fita taji muryan nawal muryanshi me sanyi da yake sanyaya zuciyarta yace "Ibtee"
a hankali ta juyo, wani murmushin farin ciki tayi da sauri taje ta sameshi, yace "kinzo?"
tace "kamal yace min Ammi batada lafiya shine nace zanzo na dubata"
yace "anyi mata allura tayi bacci"
tace "Allah sarki ya jikin nata?"
yace "da sauki kanta ke ciwo kuma tun jiya ne amma yanzu da sauki karki damu"
tace "to Allah ya kara mata lafiya"
yace "muje ki ganta"
ta kalli lokaci sannan tace "no tunda tana bacci idan ta tashi kawai ka faɗa mata nazo, amma yamma yayi Abba baisan na fito ba"
yace "to muje na raka ki"
tafiya sukayi har zuwa wajen motarta suna hira, sai murmushi take domin yana sakewa da ita suyi hira, yace "kiyi hakuri"
tace "dame fa?"
yace "da abinda suka miki"
tace "babu komai ai ba wajensu nazo ba kai da Ammi nazo dubawa"
yace "to na gode"
shiga mota tayi yana ɗaga mata hanu har ta tafi, a kofan masallaci ya zauna har akayi mangarib.

rana bata karya kamar yadda Abba ya faɗa hakan ya faru yau aka ɗaura auren nawal da ibtisam akan sadaki dubu ɗari biyu, Abba ne ya zama waliyin ango, mami da janna babu wanda suka gayyato, janna kam ɓoye auren ma take yi sabida bataso kowa yasan Ibtee bodyguard ɗinsu ta aura, mami sam taki yadda ta faɗawa kawayenta wannan abin kunyan wai wanda baida asali za'a bawa auren ibtisam, wannan abin yana ci mata rai, Ibtee tana zaune a bakin gado tayi kyau sosai cikin farin leshi tana waya da nawal, janna ma tayi kyau amma fuska babu walwala tunda safe rabon da tayi koda murmushi Ibtee bata gani ba, jaad ne kawai ya tayata murna yana mata congrats bayan shi babu wanda yayi mata, taji a ranta koda me zasuyi mata ba zai rage soyayyan nawal a ranta ba.


_Jiddah Ce...✍️_
08144818849
[17/08, 11:13 pm] +234 814 481 8849: 🌸🌸🌸🌸🌸
*SHIMA ƊA NE*
🌸🌸🌸🌸🌸


Na
*Jiddah S Mapi*


*Chapter 23*


~Yusra ce tazo ai ko ibtsam ta rinƙa murnan ganinta suka zauna suna hira daga nan ta daina damuwa, har lokacin da Abba ya kirata yayi mata nasiha, motan ɗaukan amarya guda biyu ne na kamal da wani abokinshi, janna kin shiga ko ɗaya a ciki tayi motar gidansu ta shiga tana sanye da bakin glasses tana taunan cingum cikin raini har suka isa gidan Alhaji medara, shiga da Ibtee akayi har zuwa ɗakinta da nawal, kanta kasa tana rufe da farin mayafi babu abinda ke sata kuka kamar mami da har yau taki mata magana, tana zaune a bakin gado janna ta shigo, rungumeta tayi sukayi kuka me isansu yusra ma tana tayasu tana basu hakuri, da kyar sukayi mata sallama suka tafi, sai kuka take ita kaɗai ce a ɗakin har yanzu bataga nawal ba kuma baya ɗaukan kiranta, kamal ta kira yace "amarya kiyi hakuri jikin ammi ne ya tashi shiyasa nawal yace muje kawai zaizo daga baya kiyi hakuri dan Allah"
tace "ba komai kamal na gode"
shiru ta zauna a wajen har dare ya fara nisa.

momy cikin tsananin damuwa tace "boka kana gani fa har an ɗaura auren wannan shegen, boka yanzu idan ta haife wannan cikin na ƴan biyun da yake jikinta ta zama daidai dani fa a gidan, gashi wannan shegen yayi aure ƴaƴana suna nan babu me hankali, daga me zubar da ciki sai me neman mata da danne hakkin mutane sai mashayiya? kenan haka zan kare a gidan Alhaji yana ruɗewa a kanta? kullum fa yana satan zuwa ɗakinta, taya hankalina zai kwanta boka?"
shiru yayi yana wasu abu a cikin kwarya, cikin tsawa yace "shiru hajiya naja, yanzu haka aiki ya kama shi wannan yaron babu abinda muka isa muyi mishi amma ita yanzu haka ta haukace ki koma gida ki gani da idonki, karki kuskura ki cutar da yaron domin yafi karfinmu yanada ibada lokacin salla baya wuceshi sannan yana yawaita karatun Kur'ani koda yaushe cikin tsarki yake da alwala ba zamu iya dashi ba, amma ita tunda ta samu wannan cikin ta fara samun rauni a ibada shiyasa mukayi galaba a kanta"
sai yanzu tayi dariya tace "na gode boka, amma dame zan biyaka?"
yace "yanzu zaki biyamin buƙatata"
tace "me kake so boka?"
dariya yayi sosai sannan yace "saina kwanta dake aikin zai tabbata"
tace "kwanciya kuma boka?"
a tsawace yace "ba zaki yadda bane? na lalata aikin yanzu?"
girgiza kai tayi tace "ranan biyan buƙata rai ba'a bakin komai yake ba"
yace "kin yi wayo yarinya"
fara cire kayan jikinta yayi boka yana zaune yana kallonta har ta kwaɓe duka kayan ta tsaya a gabanshi, wani tabarma ya nuna mata yace "kwanta anan"
kallon kasa tayi ga datti ga wasu kayan bokanci harma da allurai akai, tace "amma fa da allura..."
yace "kwanta"
rufe ido tayi ta kwanta akan alluran duk jikinta alluran ya soke, shi kanshi bokan wani irin datti ya tara me yawa ga gashin kanshi ƙura ga hakoranshi baƙi ƙirin da kasumban daya cika mishi fuska, rufe ido tayi sabida ko ganinshi batason yi.

Nawal yana kusa da Ammi sanye da babban rigan ɗaurin aurenshi, tun a wajen ɗaurin auren gabanshi yake faɗuwa hakan yasa ya dawo gida immediately bayan an gama, ya faɗawa kamal ya gaisa da mutane shi zaije ya duba Ammi, yana shiga yaga ta faɗo daga kan gado tana birgima a kasa, da gudu ya ɗagata ya maidata kan gadon tana rike kanta tace "nawal kaina"
ya rungumeta yace "Ammi zai daina kiyi hakuri"
tace "nawal kaina"
yace "ammi kiyi hakuri dan Allah zan kaiki asibiti yanzu"
fizge fizge ta fara, yana danneta ta fara tureshi tace "ka sakeni, nawal ka sakeni, zan mutu nawal kaina"
kanƙameta yayi yaki sakinta, shiru tayi kamar wacce tayi bacci, shima yayi shiru yana sauke ajiyan zuciya ganin ta daina fizge fizgen, da wani irin murya tayi maganan daya firgita nawal, tace "zan gudu dodo zai kamani"
addu'a ya fara mata yana tofa mata a kanta, tace "dodo zai kamani, dodo ka sakeni na gudu"
ihun data fara saida duk gidan sukaji, Ibtee data kwanta har bacci ya fara ɗaukanta tana jiran nawal, ihun da ammi takeyi yasa ta tashi da sauri tasa flat shoe ɗin dake kusa da gadon ta fita, ɗakin da takejin ihun ta nufa, tana tura kofan taga nawal yana danne Ammi tana bugunshi da karfi tana cewa ya barta ta gudu, garin kokawan da sukeyi yana shirin ɗaureta ta ɗaga kafarta ta buga mishi a ciki, rike ciki yayi cikin azaba yace "wayyo cikina"
dira tayi a gadon ta nufi waje zata gudu, kafarta ɗaya ya fita, ɗaura hanu aka Ibtee tayi ta kwala ihu tace "na shiga uku kafarta ya fita nawal"
Ammi kokarin buɗe kofan take ta gudu ibtee ta riketa, kokawa suka fara tana kwace kanta ibtee tana riketa, ƙafan ya ɗauka ya fara sa mata, Ibtee sai kallonshi take cikin mamakin yadda yake maida kafan, dama ƙafan roba ne?
saida ya gama ya rike ammi duk ihun da takeyi saida ya ɗaureta akan gadon, tana jujjuya kanta tana cewa "ku sakeni zan tafi wajen mamana ku sakeni zan tafi, kuna dukana kuna zagina kullum, bakwa sona zan tafi wajen mamana"
kwanciya yayi a gadon ya rungumeta ya fashe da kuka me taɓa zuciya, jingina da kofa ibtee tayi tana jin tausayin Ammi a ranta, ji take kamar ta karɓa mata katon cikin dake gabanta wanda haihuwa yau ko gobe, hawaye ta share tana jin kukan nawal har cikin ranta, tana maganan haka har tayi bacci, shiru yayi a jikinta, saida tayi bacci ya tashi jikinshi a mace yace "kiyi hakuri Ibtee muje ɗakinmu hankalinki ya tashi ki yafeni"
hawa gadon tayi tace "ina zamuje mu bar Ammi a wannan halin? ai tare da ita zamu kwana babu inda zamuje sabida zata iya tashi ta gudu"
shiru yayi yaga ta cire mayafi ta kwanta ta rungume ammi ta rufe ido, murmushi yayi sannan ya tashi ya sauya kaya yazo ya kwanta a bayanta ya rungumeta, a kunnenta yace "na gode"
hanunshi ta rike cikin nata tana murzawa tace "karka damu"
suna kwance shi ya kasa bacci ita kuma Ibtee bacci tayi, ido ya zuba musu su biyun yanzu sune rayuwarshi da Ammi da ibtee duk yana musu wani irin soyayyan da zai iya bada ranshi sabida su.

washe gari momy tana jin daɗi sabida tasan yau dole wannan matar ta gudu ta bar gidan domin ihun da takeyi jiya da dare tasan nawal yana fita itama zata gudu.
Ibtee tayi salla a ɗakin nawal yaje yayi salla a masallaci, yana shigowa gida ya fara jiyo ihun Ammi, da gudu ya shiga yaga ta rike Ibtee a wuya tana neman kasheta, zuwa yayi ya kwaceta da kyar, Ibtee gefe taje tana haƙi hanunta a wuya tsaban azaba, nawal ya kira kamal ya sanar dashi halin da ake ciki, nawal yace zaizo da likitan ƙwaƙwalwa, yana zaune a gefe ammi tana wani irin kuka ibtee kuma taji tsoro ta zauna a gefe, sun zama shiru a ɗakin.
janna wacce ta jima da shigowa gidan Abu ta kawowa ibtee wanda ta bari a gida, babu kowa a falon sai momy, ko kallonta batayi ba bale ta gaisheta, momy ganin zata wuce tace "ke babu manya ne a gidanku da zaki wuce babu gaisuwa?"
ta kalleta sannan tace "manyan gidanmu basa rokan gaisuwa shiyasa ban iya gaidasu ba"
tafiya tayi ta barta, ibtee ce ta fito domin ta dafa musu koda indomie ne domin rabonsu da abinci tun jiya, janna ta gani da gudu taje ta rungumeta tace "jannah kinzo?"
tace "eh unty ibtee me haka? ya nake ganinki haka? meya faru da wuyanki naga yayi jajur"
tace "jannah Ammin nawal ce jiya ta rinƙa ihu ashe ta samu taɓin hankali ne"
tace "dama uwarshi mahaukaciya ce ya ɓoye miki? unty Ibtee mu tafi gida kada ta kasheki ki dubi wuyanki, kiga yadda kika rame yau kaɗai duk kin fita a hayyacinki"
tace "A,ah janna tana neman me kula da ita domin tanada ciki haihuwa yau ko gobe yanzu ma mun kira likitan ƙwaƙwalwa zaizo ya dubata"
tsaki taja tace "amma unty ibtee bakida hankali idan ta kasheki fa...?"
sallaman dr da kamal yasa tayi shiru, dady yazo ya cewa kamal "idan kun tashi ku fita da ita ku kaita ɗakin bakin kofa data saba zama bazan jure wannan ihun a gidana ba yana hanamu bacci da matata"
kamal yayi shiru, shiga akayi da dr ya fara dubata, kallon nawal yayi yace "am sorry to say wannan ba lalle ta warke ba, saide a rinƙa mata allura me karfi shi zai lafar da ita amma idan alluran ya saketa ba'a kara mata wani ba zata iya gudu ma domin karfinta karuwa zaiyi ba raguwa ba"
hawaye ya fara kamal ya faɗa mishi sakon dady, tareda kamal ɗin suka riketa suka fito da ita tana fizge fizge tana son gudu suka riketa har ɗakin bakin kofa kafin kamal yaje ya siyo chain suka ɗaureta dashi Dr yayi mata alluran atake ta kwanta a wajen, yace "ga kalan alluran ko cikin dare zai iya tashi mata sai kayi mata zata lafa"
yace "to na gode"
kuɗi ya biya sannan dr ya tafi.
Janna tace "kina nufin da wannan mahaukaciyar zaki zauna? zaki iya zama da ita?"
tace "zan iya janna kamar mahaifiyata take yanzu....."
wurgar da abin tayi sannan ta fita fuuu a fusace, motar da tazo dashi ta shiga da gudu ta fita a gidan, tana zuwa gida ta samu mami a falo tace "mami asiri ya yiwa Ibtee wallahi asiri ne"
mami tace "me kuma ya faru janna?"
tace "mami ashe mamanshi mahaukaciya ce ya ɓoye mana?"
dafa kirji tayi tace "mahaukaciya kuma jannah?"
zaunar da mami tayi ta irga mata duk abinda ya faru, tace "Innalillahi na shiga uku na lalace jannah ya zanyi?"
janna tace "shi mijin nata yace a fita da ita daga ɗakin baison ihu ya dameshi da matarshi"
mami tace "ki kwantar da hankalinki auren Ibtee dashi ba zan taɓa bari yayi lasting ba wallahi saina rabasu, ba ita tace tanada taurin kai ba? sai nayi maganinta wallahi"
tashi tayi ta shiga ɗakinta waya ta kira tace "kina ina hajiya Rabi? yau zanzo da dare ki jirani sannan ki kiramin reza"
tace "babu komai kede kiyi abinda nace"
katse wayan tayi tana kai komo a ɗakin.

da dare ta sashi hanya da sunan zataje asibiti, wani unguwa taje wanda kawarta hajiya rabi take, har cikin gidan ta shiga, bayan sun gaisa hajiya rabi tace "lafiya A'isha? meya faru?"
cikin damuwa tace "akwai matsala rabi, ina cikin tashin hankali"
tace "subhanallah meya faru?"
tace "Ibtee tayi aure kin sani?"
tace "rumours nakeji a gari ban zaci da gaske bane"
tace "tabbas tayi aure kuma kinsan abin ɓacin ran?"
tace "a'ah"
"shege ta aura mara asali wanda aka haifa babu aure shiyasa na ɓoye maganan"
dafa kirji tayi tana salati tace "meyasa kika bari?"
tace "ba wannan ba yanzu neman hanyan kashe auren nake amma ibtee tana sanshi Abbansu ma yanaso, Inaso a sace Ibtee a nesanta ta dashi ta yadda zai hakura da kanshi ya saketa yayi wani auren sabida mamanshi ashe mahaukaciya ce abin ya taru yamin yawa rabi"
tace "kina ganin babu kuskure a sace ƴar cikinki a ɓoyeta wani waje sabida a nesantata da aurenta? idan abbansu ya sani kin san dani dake duk ba zai barmu ba"
tace "rabi kin san ba zan cutar da ƴata ba ko? abin ne ya zama dole nayi ki taimaka ki kiramin reza"
tace "na kira reza kuma zai zo gidannan babu jimawa kinsan shi idan zaki biyashi kuɗi duk abinda kikeso zai miki"
tace "ba komai ina jiranshi kuɗi ba matsala bane..."
kafin ta rufe baki wani gaye ya shigo kanshi kamar ɗakin tsuntsu tsaban gashi, yana zuwa yace "hajiya gani"
tace "baka iya gaisuwa bane?"
yace "ina kwananku"
tsaki
End Ads