x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 14 - SHIMA DA NE free pages

  • 39001 words
  • 42000 words
  • Out of 65957 words

Category: Love Stories

Views 231

25 Aug 2025
Start ads
After Image Ads
tabbacin mugunta yake yi dan jiya naji yace a sawa wani guba a gidan, wai kasan me?"
yace "A,ah"
tace "wai mutumin shine tsohon gomna shine yake neman senator basa shiri da dady tsofin abokan gaba ne, dady ya tsaneshi shima ya tsani dady so suke ma kowanne su kashe junansu, shi yana harin dady shima dady yana harinshi, har dady ya aika wani gidan yaje a matsayin p.b ɗinshi wato personal bodyguard Ahlam, shi mutumin be san dady bane ya turashi kullum yana waya da dady yana faɗa mishi sirrin gidan, yanzu shirin kasheshi suke gadan-gadan wai shine yasa aka tuge dady a party ɗin da yake ciki ya bawa Alhaji sammani gomna"
shiru yayi yana jinta, a fili yace "kisa kuma?"
ashe taji, tace "wallahi dady yace ya bashi kwana uku idan be kashe mutumin ba zai tona mishi asiri"
akan gadonta ya kwantar da ita, rufata yayi da blanket sabida sanyi, zai tafi ta rike hanunshi, yace "me kuma?"
tace "yaya kayi hakuri nasan momy batada imani zata iya yin komai domin kada ka raɓi jikin dady ka dage da addu'a domin momy tana bin boka batada aiki sai hayake hayake da bin bokaye suna bata magani shiyasa ko dady be isa ya kara aure ba kuma be isa ya tsallake magananta ba, kaji?"
a hankali ya gyaɗa kai sannan ya zame hanunshi ya fita daga ɗakin, zai fita naseer ya shigo rike da hanun mata santaleliyar budurwa tana sanye da kayan da suka matse ta, harara naseer ya aika mishi, yarinyar tace "wannan shine shegen gidanku?"
yace "shine"
tace "wow amma wallahi he's handsome yanada bala'in kyau"
hararanta yayi yaja hanunta suka wuce tana juya baya tana kallon nawal daya buɗe kofa ya fita, maganganun samha suna yawo a kanshi, kenan dady yanada mummunan gaba tsakaninshi da Alhaji usman makama? har yana nema ya kashe shi?
Ahlam wanda yake gidan harma yayi zaton yayan yarinyar da ranan yaje sata gidansu ce shine maci amana? shine yake can sabida yayi kisa?"
da wannan maganan ya wuni, yana gidansu kamal bai dawo gida da wuri ba yau saida dare ya fara nisa kamal ya kawoshi har kofa ya saukeshi, sallama sukayi ya shiga gida, saiya duba Ammi kafin yayi bacci hakan yasa ya fara tafiya zuwa ɗakinta, har zai wuce ɗakin dady yaji yana waya, tsayawa yayi yana jin maganan da yake faɗa, yace "Ahlam na yadda da kai ka tabbatar kamin wannan aikin sabida kai ɗana ne, Ahlam daga ni sai momynka da kuma kannenka muka san kaine babban ɗana Ahlam bayanmu babu wanda ya sani sabida a kasar waje kayi karatu tun kana yaro karami, inaso ka cikamin wannan burin nawa ka kashe Alhaji Usman makama a gobe, sunada meeting a gidan gomna na tabbata zai faɗa maka yau zaku fita gobe kusa da gidan gomna akwai wani kwalta daya rabu gida biyu, ɗaya idan kabi senta shine zai kaika gidan gomna ɗayan kuma ɓarawon hanya ne, Inaso kabi ɓarawon hanya Ahlam zanje wajen a lokacin zai san kai ɗana ne na cikina sannan zaka kasheshi da hanunka"
yace "gobe idan zaku fita ka faɗamin domin na zauna a shirye"
dariya yayi sosai sannan yace "zasu san sunyi da ɗan halak"
katse wayan yayi, nawal rufe baki yayi yana kallon kofan, jin ya yanke kiran ya taka cikin sanɗa ya shige ɗakin Ammi bai bari kowa yasan yaji ba, tunda ya shiga Ammi tace "nawal me yake damunka kake tunani?"
yace "ba komai ammi"
kwanciya yayi ya ɗaura kanshi a kafarta yayi shiru, hanu tasa a sumanshi me yawa tace "gashinka ya kara taruwa kamata ka rage ai duk da yanada kyau"
murmushi yayi ya gyara kwanciyan yace "Ammi na ina sanki"
tace "nima ina sanka nawal amma kasan me?"
girgiza kai yayi tace "inaso kayi aure"
shiru yayi, tace "nawal dan Allah ka nemi mata kayi aure wannan shine burina"
ya rike hanunta yace "tunda shine burinki ammi zan cika miki"
tace "yawwa nawal wacece zaka aura to?"
yace "ina zuwa"
waya ya ciro a aljihu ya kira layin kamal, yana ɗauka yace "ya akayi?"
yace "kamal wannan yarinyar da kace tana sona inaso ka faɗa mata ammina tanaso nayi aure gobe da safe zamu zo gidansu neman aurenta"
kamal da mamaki yace "nawal da gaske ka yadda zaka aureta? ai ɗazu ma ta kiraka a waya take fadamin maganan aure kawai take jira kayi"
yace "ba komai gobe da safe zamu zo da Ammi na gidansu"
yarinyar makociyar su kamal ce batada matsala ko kaɗan, da fari nawal ne ya fara ganinta amma baiyi magana ba saida yarinyar tace tana sanshi kamal ya mishi magana, sunanta fatima tanada hakuri sannan kullum tana kiran nawal a waya shine baya damuwa da ita, kamal cikin murna ya faɗa mata ta sanar da gida gobe da safe nawal zasu zo domin maganan aure, ai kuwa tayi farin ciki kuma ta faɗawa babanta da mamanta duk sunyi farin ciki, sun san nawal yana zuwa unguwan wajen kamal kuma kamal mutumin kirki ne.

Ammi tace "nawal na gode sosai kana matukar girmama duk abinda nake so, na gode nawal"
yace "Ammi idan ban miki biyayya ba wa zanwa? ke kaɗai fa nake dashi sai kanina ko kanwata da zaki haifa"
murmushi tayi ta sunkuyar da kanta, tashi yayi yace "zanje na kwanta saida safe"
tace "Allah ya tashemu"
tace "Ameen"
fita yayi, samha wacce ta shigo cikin sanɗa takalminta a hanu bataso kowa yasan sai yanzu ta shigo, ta juyo daga rufe kofan sukayi ido huɗu, ajiyan zuciya ta sauke tace "ya nawal kaine? na zaci wannan mugun nabil ɗinne ashe kaine"
yace "eh nine"
tafiya ta fara tace "ya nawal saida safe"
ganin ta haura sama da gudu yace "Allah ka shiryeta"
ɗakinshi ya tafi ya kwanta yana tunani har bacci ya ɗaukeshi.
Asuba ta gari, bayan sunyi salla ya haɗawa ammi dashi karyawa suka shirya domin zuwa gidansu fatima wacce yayi waya da ita akan zuwansu, kamal ne yazo ya ɗaukesu har kofa, suna tafe suna hira harda Ammi kamar ƴan uwa, har suka isa kofan gidan, kamal ne ya buɗewa Ammi ta fito sukayi sallama kafin aka musu iso suka shiga, akan babban tabarma suka zauna tareda iyayen fatima suka gaisa harda kanin babanta, Ammi ce ta faɗa musu kudirinsu na son auran fatima, babanta ne yace "to tunda yarinya tana so shima yaro yanaso ba zamu hana ba, to amma kin san maganan aure dole sai munga dangin mahaifinshi ina nufin koda mahaifinshi bai zo ba mu samu ko kaninshi ko yayanshi da zamuyi magana"
shiru sukayi, gaban nawal ya fara faɗiwa, Ammi kuma wani abu ne ya tsaya mata a wuya, ta kasa haɗiye miyau, babanta yace "shin ina mahaifinshi ya rasu ne? ko yana raye? idan baya raye ina kaninshi ko ɗan uwanshi na jini?"
shiru Ammi tayi ta kasa amsawa, kanin baban fatima yace "ya zama dole ku amsa mana wannan tambayan domin neman aure ba wasa bane, ina mahaifinshi?"
ammi ta nuna kanta tace "nice mahaifiyarshi kuma nice mahaifinshi"
da mamaki sukace "kamar yaya kina mace ki jagoranci aure?"
tace "nawal ba..."
nawal yace "banada uba"
kallonshi sukayi "bakada uba kuma?"
jijjiga kai yayi yace "eh babu aure aka haifeni"
babanta yace "ana wata ga wata ɗin kenan, kana nufin bata hanyan aure aka haifeka ba? kai ba ɗan sunna bane?"
Ammi ranta yana tafasa tace "kada ku kara ce mishi shiba ɗan sunna bane kawai dai tsautsayi ne yasa aka haifeshi bata hanyan aure ba"

"babu wani tsautsayi kina nema dai kawai ki kare kanki, ta yaya zamu ɗauki ƴa mu bawa wanda bayada asali? ta yaya zamu bawa wanda akayi zina aka haifeshi ƴarmu? so kuke a rama akan ƴaƴanta suma su haifi shegu? zuri'a ya taɓarɓare? ai bamu san kai mutumin banza bane...."
cikin tsawa Ammi tace "ya isheku haka, nawal ba shege bane nice shegiya domin baida laifin komai, baisan komai ba shi haifansa akayi babu wanda zan kyale matukar ya rinƙa faɗa mishi munanan maganganu, nawal ba shege bane rahama ce shegiya tunda ita tayi zina ta haifeshi...."
ganin har jikinta yana rawa nawal yazo ya riketa yace "Ammi please kiyi shiru"
fatima wacce ta ɓuya a bayan kofa tace "baba na yadda wallahi na yadda zan aureshi ko baida uba"
mamanta ne ta tashi tace "fatima kinyi hauka ne zaki haɗa zuri'a da shege? to wallahi matukar kikace zaki zaɓeshi saide ni ki rabu dani zan yafeki duniya da lahira fatima"
kuka ta fara, baba yace "barta yarinya ce ba zata gane matsalan yanzu ba saita haifi yara zata gane inda matsalan yake, kaida samun aure a gidan tarbiya waɗanda suka san darajan kansu zaiyi wuya, saide ka nemo daidai kai wacce itama ta hanyan zina aka haifeta kaga babu me yiwa wani gori cikinku amma ni gaskiya ku tashi ku fita ku barmin gida"
Ammi tace "ko baka faɗa ba zamu bar gidanka kuma insha Allah ɗana ba zai rasa mata ƴar gidan tarbiya ba aniyanka ya bika"
hanun nawal ta rike suka fita, kamal yana tsaye a gefe yayi shiru abin bai mishi daɗi ba sam, har suka tafi jikinshi a mace, Ammi banda kuka babu abinda take yi, tana ganin ta gama cutan rayuwan nawal domin tabbas zai samu matsala wajen neman aure, kamal har kofa ya ajesu sannan yace "kuyi hakuri Ammi bansan haka zai faru ba da bazan fara ba tun farko kuyi hakuri abokina"
yace "karka damu kamal duk a cikin rayuwa ne"
hanunshi rike dana Ammi suka shiga gidan, momy tana zaune a falo tana kallo suka shigo, da ido tabi Ammi sannan a ranta tace "wannan cikin ba dai ki haifeshi ba in shegen ne zan bari ya zauna amma banda ɗan halak ƴaƴana ne kaɗai ƴaƴan halak"
tagumi tayi a bakin gadon, ya durkusa a gabanta yace "ammi kada ki damu kinji? amma nasan za'a samu matsala a neman aurena me zai hana mu koma kauyenku nayi aure acan?"
tace "nawal babu abinda zai kara kaini kauyenmu, nawal mutanen kauyenmu sunfi kowa sanin kamun kan dana tashi dashi, a lokacin da ƙaddara bata hau kaina ba kowa yanason ƴarshi tayi ƙawance dani, nawal saida ƙaddara ya hau kaina suka manta duk kyawawan halina, suka ɗauki sharri ɗaya daya afku min suka rinƙa ƙyarata da hantara ta, ciki harda mahaifiyata wacce ta kasa karɓan ƙaddara wacce ta manta da wacece rahama a baya, nawal ko kallon mamana banason nayi sabida itace silan faɗawata cikin wannan bala'in, data jani a jiki da zan haifeka a kauyenmu duk zagin a zasumin zan daure na girmar da kai, zanyi sana'a kamar yadda na saba na ciyar da kai, amma ta koreni sabida maganan mutane wai batason abin kunya, batasan idan na tafi yunwa yana iya sa mace yin zina ba, batasan a gidan karuwai na haifi cikin data koreni sabida shi ba, batasan zan iya komawa ruwa ba idan wahala yamin yawa, a halin yanzu ko sunan kauyenmu tufan banason ji, mutane biyu nake tunawa sune kanwata nana da kanina yaseer su biyu ne kaɗai nake tuna ko wane hali suke ciki, ko tayi aure? ko tayi karatu kamar yadda nake faɗa mata kuma nake dagiya a kullum? ko ta samu miji me hankali kamar yadda nake mata addu'a, ko ta samu miji marar hankali, ko yasir yayi aure Allah ne kaɗai masani"
tace "nawal zaka samu mata me sonka wacce zata soka a kowane hali kake ciki, ba kuma zata iya gudunka ba ko wani hali ka shiga, nawal a lokacin dana haifeka nayi addu'a Allah ya baka matar da zata tsaya maka wacce batada tsoro zata iya fuskantar duk matsalanka, kuma zaka samu"
yace "na gode Ammi"
tashi yayi tunawa da wayan dady na jiya, da sauri yace "Ammi zan fita"
tace "ina zakaje?"
yace "zan dawo bada jimawa ba"
fita yayi da sauri, ɗakinshi ya shiga yasa bakaken kayanshi amma baisa mask ba, ya ɓoye bindiga sannan ya fita daga gidan.


_Jiddah Ce....✍️_
08144818849
[17/08, 11:13 pm] +234 814 481 8849: 🌸🌸🌸🌸🌸
*SHIMA ƊA NE*
🌸🌸🌸🌸🌸


Na
*Jiddah S Mapi*


*Chapter 18*


~Mashin ya hau me kafa biyu sannan ya tafi inda yaji dady yana faɗa jiya, babu kowa da alama basu fito ba, ya samu gefe ya zauna a bayan bishiya ta yadda ba zasu ganshi ba, har ya gaji da zaman ya tashi zai tafi yaga zazzafan mota yazo wajen, ɓuya yayi yana kallo yaga motan ya tsaya a daidai tsakiyan titi inda dady yace Ahlam ya tsaya, fitowa yayi kamar wanda zai duba mota, nawal ya kare mishi kallo sai yanzu yaga tsananin kama da sukeyi dasu naseer, yace "koda na girmi Ahlam ba lalle ya zama sosai ba, sabida zamuyi sa'a dashi, meyasa dady yake koya mishi cin amana da zamba cikin aminci? meyasa ya koya mishi yadda zai cuci wanda ya yadda dashi ya bashi amanan gidanshi da komai nashi, ya zama me bashi tsaro na musamman duk inda zaije koda wajen sirri ne tare suke tafiya"
gani yayi Ahlam ya juya baya ya ciro bindiga, waro ido yayi ganin ya ɓoye bindigan a baya yana knocking na glass ɗin motar alaman Abba ya fito, can saiga motar dady ta tsaya a gaban nasu, gani yayi dady ya fito Abba ya fito shima, da mamaki sosai akan fuskan Abba yace "Ahlam meyasa ka tsaya da mota?"
dariya yayi sosai sannan yace "mahaifina ne yasa"
yace "mahaifi kuma? Ahlam kai maraya ne iyayenka sun mutu tun kana yaro taya akayi ka samu mahaifinka?"
nuna dady yayi da bindigan sannan yaje ya rungume dady yace "kai wani irin wawa ne Alhaji usman makama? shin ka manta tsohon gaban dake tsakaninka da mahaifina Alhaji Alhasan medara? meyasa bakada kula baka kula da kamannin da nakeyi dashi ba? to ai mun jima muna shirya wannan ranan dama ta kan ƴaƴanka zamu fara wato ibtisam da janna amma munfi so mu gama da kai kafin mu koma kan ƴaƴanka sannan dady na ya aure matarka idan naga dama na auri ƴaƴanka"
Abba ranshi yana tafasa yace "Ahlam dama kai macuci ne? Ahlam dama..."
bindiga ya nunashi dashi yace "kwarai kuma yanzu zan kasheka domin na cika burin mahaifina nasan zai mutu yana alfahari dani"
nawal ganin sunyo kan Abba sun fara duka yaji ba zai iya tsayuwa yana kallon hakan ba, kallon wani da yake wucewa akan keke yayi tsoho ne ya tsayar dashi, ya durkusa kasa yace "dan girman Allah baba ka bani kayanka na sauya da nawa wancan mutumin zan taimaka"
kallon Abba da ake daka ga kuma bindiga dake hanunsu yayi, ya kalli nawal da babu alaman karya ko cutarwa a tare dashi, sauka yayi a keken yace "zan baka yaro Allah ya maka albarka Allah ya haɗaka da alheri duniya da lahira yasa kafi karfin makiyanka"
yace "ameen baba"
tsoffin kayanshi ya cire ya bashi shima nawal ya cire bakin kayan ya bashi sannan yace ya tafi sabida kada su ganshi suyi harbi, ya tafi shi kuma nawal ya ɗauko alebo (harami) da tsohon ya bashi ya ɗaure fuskanshi ta yadda babu wanda zai ganeshi, bindigan ya ciro sannan yabi ta bayansu, a lokacin Abba yana kwance a kasa suna mishi dukan mutuwa, bindigan ya harba kafan dady bullet ya sauka, waro ido yayi ganin ya harbi dady, Ahlam a razane yake kallon dady, ya kalli nawal daya zubawa bindigan ido shima da alama baisan harbin zai taɓa dady ba, Ahlam shima bindiga ya ciro zai harbi nawal ruwan sama ya sauko kamar da bakin kwarya ga wani iska me karfi, da gudu nawal yazo zai janye Abba daga wajen domin ya tseratar dashi Ahlam ya daga bindiga a cikin ruwan zai harbeshi, kwacewa yayi suka fara kokawa, Ahlam kokarin cire alebo yake shi kuma nawal kokarin ɓoye fuskanshi yake bayaso ko da wasa su ganshi, ruwan sama kara sauka yayi da karfi, yayi nasaran ture Ahlam sannan ya ɗaga Abba dake kwance rai a hanun Allah, ƙafan Abba yana jini ya sashi a mota, Ahlam jin ciwo da dady yake kira ga jinin dake zuba sabida hujin bullet yayi saurin komawa wajen dady yana duba ƙafan, a mota nawal yasa Abba, kamal ya koya mishi mota amma be kware ba.
sa Abba yayi ya shiga motan da gudu ya bar wajen Ahlam sai harbi yake amma iskan ruwan saman ya hana bullet samun su nawal.

har ya shiga cikin gari dashi yana lekawa yana cewa "sannu"
sai ɗaga kai Abba yake yi, asibiti ya wuce dashi na cikin gari, aka karɓeshi emergency sabida sun san matsayinshi, nawal yace "gara na tafi idan ya tashi kada ya sanni"
zai tafi dr yace "ga magungunan da za'a siyo"
ya karɓi takaddan sannan ya fita, da kafa ya tafi ruwa na dukanshi yaje ya siyo magani da ruwa sannan ya dawo, ɗaurawa Abba ruwa akayi sannan aka mishi allura duk ciwon da yaji sukayi dressing, yana kwance har yanzu be buɗe ido ba, fuskanshi ya kumbura sosai, nawal yace "ya rabbi kasa yanada rai bai mutu ba ameen"
kasa tafiya yayi ya zauna kusa dashi a bakin gadon, shiru yayi yana tuna harbin dady da yayi da hanunshi, ya tsani dady da family ɗinshi amma baiso ya harbi mahaifinshi ba, godiyan da yake yiwa Allah shine basuga fuskanshi ba kuma da wuya su ganeshi, yana wajen Abba har dare yayi bai farka ba, ya kira kamal yace yaje ya faɗawa Ammi ba zai samu dawowa ba akwai aikin da yaje, zama yayi a wajen Abba sabida bayada tabbacin Abba zai farka.
a wajen ya kwana akan kujera yayi bacci, Abba motsi ya fara da hanu a hankali yake buɗe baki yana cewa "ruwa..ku bani ruwa"
buɗe ido yayi yaga nawal kwance a kusa dashi ya rufe jikinshi da alebo yana bacci kamar zai faɗi akan kujeran kuma da alama a wajen ya kwana, yace "ruwa..ka bani ruwa"
firgigit nawal yayi ya yaye alebon sannan ya kalli Abba, wani murmushin da yayi na jin daɗin tashin Abba yace "ka tashi? na gode Allah"
muryanshi harya dashe sabida sanyin ruwan daya dakeshi kuma ya kwana da kayan a jikinshi ba tareda ya sauya ba, ruwa ya bashi, ya komar dashi ya kwanta, Abba yace "na gode"
shiru nawal yayi, rufe ido yayi ya kara komawa bacci, nawal yana wajen har yayi sallan azahar, koda ya shigo yaga Abba ya tashi ya zauna jikin da sauki, juyawa yayi zai koma Abba yace "zo mana"
a hankali ya koma, Abba ya nuna mishi wajen zama yace "zauna"
a gefenshi ya zauna, yayi shiru shima
End Ads