yace "waye?"
nawal yace "nan ne gidan Alhaji alhasan me
medara?"
fuska ba walwala yace "eh nan ne"
ammi tace "dan Allah ka mana magana dashi mana wajenshi mukazo"
yace "ku su waye?"
tace "kayi mishi magana shi ya sanni"
yace "a,a gaskiya Alhaji yana cikin uzuri bayaso a dameshi may be ma ku maroka ne kunga ƴan siyasa sai kunbi kun samu kuɗi a wajensu ku bar kofar gidannan"
zuciyan ammi yana tafasa tace "malam kayi mana magana dashi ko na tara maka mutane"
yace "idan kin fasa tarawa keba ƴar halak bace"
duwatsu ta ɗiba ta fara harbin gate ɗin dashi, nawal yana hanata tana fizgewa tareda yin ihu, take mutane suka fara fitowa daga gidajensu dan ganin meke faruwa a unguwarsu da babu hayaniya, Alhaji alhasan yana ɗaki yana bacci matarshi taji harbin da ihun tazo da sauri tana tashinshi, yace "lafiya?"
tace "akwai matsala ihu da harbi nakeji a waje kuma kamar muryan mace ne ya kamata ka leka"
sauka yayi a gadon suka fita a tare har mutane sun gama taruwa buɗe kofan yayi yana jin bacci sosai yace "musa wai me yake faruwa...?"
waro ido yayi ganin mace zaune akan kujeran guragu ga kuma wani saurayi yana hanata harbi, yace "baiwar Allah me nayi miki kike harbin kofan gidana?"
zubar da sauran duwatsun tayi sannan tace "sunana rahama Abubukar sadik"
waro ido yayi yana kallonta, tabbas yasan wannan fuskan amma ya manta aina ya sani, murmushi tayi na takaici sannan tace "baka gane ni ba ko? ka manta rahama ta kauyen tufan wacce akasa muku ranan aure da ita?"
kallonta yake da mugun mamaki ganinta akan keken guragu, yace "rahama? gaskiya ban ganeki ba saide idan abokan adawa na ne na siyasa suka turoki domin ki ɓatamin neman kujeran gomna da nake yi"
wani abu ne ya tsaya mata a rai taji kirjinta yana suya, taji wani irin tsananshi da haushi ya cika mata zuciya, batasan time ɗin data janyo wani katon dutse ta wurga mishi ba, kaucewa yayi dutsen ya samu gate ya fasa glass ɗin dake jikin gate ɗin, cikin zafin rai tace "kana nufin baka gane ni ba? kana nufin ka manta yarinyar da tafi kowace mace kyau a kauyensu kuma tafi kowace mace nutsuwa da kamun kai? kana nufin ka manta wacce kazo da niyan aurenta ka lalata mata rayuwa? ka manta rahama wacce take tallan alale a titi kace zaka aureta ka yaudareta kayi mata fyaɗe? ka manta wacce kasa mahaifinta ya mutu dalilin fyaɗen da kayi mata har ta samu ciki? ka manta wacce mahaifiyarta tace zata tsine mata idan ta kara ganinta a gidansu sabida cikin daya shiga jikinta a lokacin da kayi mata fyaɗe? to idan ka manta yau zan tuna maka Alhaji Alhasan yau nazo gareka domin na tuna maka abinda kayi a baya, yau nazo domin na nuna maka sakamakon cutarwan da kamin"
janyo hanun nawal tayi tace "wannan shine sakamakon wannan shine ɗan dana haifa maka da cikin da kamin"
zufa ya fara ganin har mutane sun fara mishi video yasan yanzu ma haka wasu live suke yi, tace "wannan shine ɗanka daka ajemin a cikina ta hanyar cutar dani kuma na kawoshi ya zauna tare da kai sabida SHIMA ƊA NE kamar kowa"
yace "karya kike sharri kikemin sabida kinga zanci zaɓen bana, kinga inada tarin masoya abokan adawata suka turoki ban sanki ba bansan wannan yaron da kike magana a kanshi ba, kije can ki nemi ubanshi amma bani ba"
dariya tayi amma dariyan tareda hawaye suke sauka, tace "eh baka sanshi ba amma ni kayi rantsuwa baka sanni ba?"
yace "na rantse ban sanki ba"
nawal ne yaje inda yake ya durkusa kasa akan gwiwoyinshi ya haɗa hannu biyu yace "dan Allah Abba kada kace baka sanni ba, na jima inason sanin wanene mahaifina kuma tunda na ganka naji a jikina kaine dan Allah kada ka musa...."
da sauri yayi baya cikin ɗaga murya yace "karka sake wannan ƙazamin hanun naka ya taɓani ban sanka ba bansan me take magana akai ba, kaje ka nemi ubanka amma ni ban haifi shege ba, watakila a yawon bariki ta samu cikinka saiku kara gaba ku lankayawa wani ba niba"
Ammi dutse ta fara harbi dashi tana jin ciwon rashin takawa da batayi da yau saita nuna mishi itace rahama daya cutar, kafin kace kwabo ƴan sanda sun shigo maganan domin kiransu akayi, ganin rigima ya ɓarke matar Alhaji tace bata yadda ba sharri ake yiwa mijinta kuma uban ƴaƴanta police suka kwashesu suka tafi dasu duka, acan aka kara ɗago sabon fitina, daga karshe d.p.o ya bada shawaran ayi d.n.a text, nan take Alhaji ya fara zufa, matarshi kuwa tace "idan har aka gane ba shine baban wannan yaron ba wallahi sai na kai kara an kulleku da laifin sharrin da kuka yiwa baban ƴaƴana"
d.n.a text aka fara duk suka tsaya rahama sai kuka sabida taga nawal ya zauna a gefe yayi tagumi hakan yasa zuciyanta ya karye a yadda taga matar Alhaji Alhasan kawai taji tana tausayin kanta da ɗanta domin tabbas zasu fuskanci gagarumin matsala ji take dama ta hakura sun zauna kawai a inda suke basu zo nemanshi ba, sakamako ne yazo jikinshi yana rawa yace "ya akayi dr?"
bashi result yayi yace "kaine mahaifin wannan yaron ko ina zakuje haka za'a tabbatar maka sabida jininka ne"
musawa zaiyi matarshi tace "shin da gaske ɗanka ne?"
yayi shiru, cikin ihu tace "tambayanka nake ɗanka ne?"
ya kalleta sannan yace "a,a ba ɗana bane"
tashi tayi tace "zan kai kotu acan zamu kare wannan shari'ar sabida ban yadda da wannan gwajin ba"
fita tayi, Alhaji ya share zufa ya kasa tashi a wajen.
wasa wasa case ya tafi kotu, nan take aka fara shari'ar alkali da kanshi yasa akayi gwaji aka kawo mishi result, tsit kotu yayi kowa yana sauraron alkali wanda yake shirin yin magana yanzu, yace "tabbas nawal ɗanka ne Alhaji Alhasan kuma zai fara amsa sunan NAWAL ALHASAN MEDARA sakamakon kunci da damuwa da tashin hankalin daka sa rahama a ciki kuma kotu tana umartanka da aurenta kuma yanzu kotu zata ɗaura aurenku saboda ta samu daman zama da ɗanta a cikin gidanka kamar yadda sauran ƴaƴanka da matarka suke zama sabida SHIMA ƊA NE kamar sauran yara, sannan wannan auren babu saki saida kwakkwaran dalili saɓanin haka kotu zata ɗau mataki a kanka"
silalewa matarshi tayi kasa ta faɗi a sume jin an fara ɗaura auren, alkali be tsaya ba saida ya tabbatar aure ya ɗauru kafin ya bada umarnin a dubata, Alhaji sai zufa yake mutane kowa yana tofa albarkacin bakinshi, nawal shiru yayi yana kallon yadda Alhaji ya ruɗe akan matarshi yana tashinta tareda kiran sunanta NAJA'ATU sai zufa yake sharewa, taimakon gaggawa aka bata akan gadon asibiti aka kwantar da ita, Alkali yace a kai nawal da amminshi gidan Alhaji alhasan sannan a basu masauki kamar yadda matarshi da ƴaƴanshi suke zama, jikin nawal a mace yake bin tafkeken makeken tsararren gidan da aka kawosu wanda cikinshi kamar aljannan duniya, wannan gidan ya wuce tunanin me tunani, wani ɗaki da aka kaisu kamar ɗakin gomna acan aka musu masauki, banda kallon gidan babu abinda suke yi, daga shi har ammi a tsorace suke domin basu saba zama a irin wajennan ba sunfi zama a bola da datti.
dan kyar hajiya naja ta dawo hayyacinta, Alhaji banda hakuri babu abinda yake bata daga karshe ya fashe mata da kuka, a duniya babu wanda yake jin magananta kamar matarshi bayaso ko kaɗan ranta ya ɓaci tamkar aikin asiri, yaransu biyu maza nawal ya girmesu ɗaya sunanshi naseer ɗaya kuma nabil tanada karamin ciki kuma yanzu suma sun girma kuma sunada wayo nasir shine babba nabil kuma karami, suna tsadadden makarantan da yaran wane da wane ne a nigeria suke ciki, basajin hausa sosai sunfi gane turanci amma suna fahimtan hausa, duk duniya babu abinda Alhaji Alhasan yake so kamar matarshi da wannan ƴaƴan nashi da cikin dake jikinta bayason ko kuda ya taɓasu, koda yaushe suna cikin shaƙatawa, yana neman gomna kuma ya ɗau hanyan samu saide wannan abin daya faru yasa jikinshi yayi sanyi, yaji babu abinda ya tsana a duniya kamar wannan yaron da aka kawoshi rana tsaka akace wai ɗanshi ne, wannan yaron ze taɓa kujeran da yake nema idan beyi sa'a bama ba zai samu ba, har suka koma gida taki mishi magana yaran ma sunki mishi magana sabida sunga komai a social media sannan hoton da Alkali yasa aka ɗauka na nawal da Abbansu sun gani.
kwance Abba yake akan makeken gadonshi na alfarma ya ɗaga kai sama yana kallon saman ɗakin, ya kasa amsa kiran kowa duk yawan kiran da yake shigo mishi ya kasa ɗauka, sakonni sunata shigowa ya kasa ko kallon wayan, nasir ne ya shigo, kyakkyawa ne sosai sabida Abba yanada kyau ya tsaya a bakin kofa sanye yake da armless fari da gajeren wando, jikinshi na ƴan hutu ne sosai yake glowing, yace "dady wai da gaske ne bamu kaɗai bane yaranka an haɗamu da wani?"
shiru yayi yana kallon yaron, hawaye yaron ya fara yace "dady i can't wallahi i can't share you, nida nabil kawai nakeso ka zama dadynmu banda wancan kazamin da yazo yau, Abba i hate him I hate him so much Abba, please I want him to leave this house banason ko ganin fuskanshi dashi da wannan kazamar gurguwan matar, dady nasan sharri sukayi maka sabida sunga zaka samu kujeran gomna, they want to ruined you, dady kasa security su koresu please, kaga momy ma tun ɗazu sai kuka take yi she's not feeling good"
a hankali ya sauka akan gadon, zuwa yayi ya janyo yaron jikinshi sannan ya fara shafa bayanshi cikin lallashi yace "calm down my boy wannan umarnin alkali ne amma ni ɗan siyasa ne nasan duk wani hanyan da zanbi na samu duk abinda nakeso, i will never compare you with anyone, ku kaɗai ne yarana he will just be with us for some times amma shi ba ɗana bane bazan taɓa karɓanshi a matsayin ɗana ba"
yace "dady i hate him ka koreshi kawai momy ma batason ganinsu she hate them with all her heart"
shiru yayi, turo kofan akayi momy ce ta shigo ɗakin babu ko sallama, hanun nasir ta rike ta fizgeshi daga jikin dady sannan tace "bance kada ka kara zuwa wajenshi ba har sai ya fitar da waɗannan dattin daya kawo mana gida? why are you stubborn ne nasir? can't you see your brother ya kama kansa baizo wajen wanda ya haɗaku da wani a matsayin ɗa ba? your father cheat you, he cheat"
dady ya rike hanun nasir sannan yazo gabanta ya durkusa ya haɗa hanu biyu yace "please and please my love kada kimin haka, da wanne zanji? da wannan bala'in daya sameni ko da wannan abinda kuke min, an tabbatar ɗana ne amma ai kuskure ne, kuma nima banji ina sanshi ba ko kaɗan a cikin raina, kinfi kowa sanin ni ɗan siyasa ne yanzu takaran gomna nake yi kuma zan samu, abu kaɗan ne zai iya sa na rasa wannan kujeran kuma kinsan zan iya yin komai domin na samu wannan kujeran sannan zan iya yin komai idan na rasa wannan kujeran...."
wayarshi ce ta fara ringing da sauri ya saki hanun nasir ya tashi yaje ya ɗauka sabida wannan ringtone ɗin na kiran majalisa ne, ɗauka yayi yace "your highness barka da warhaka"
cikin tsawa da masifa yace "abinda nake ji da gani a social media gaskiya ne?"
shiru yayi, ya kara cewa "gaskiya ne?"
jikinshi yana rawa yace "eh"
cikin ɓacin rai yace "yanzu haka munyi meeting na gaggawa kuma mun zartar da hukunci mun saukeka daga neman kujeran gomna mun ɗaura abokinka Alhaji sammani, an koreka a party daga yau kai ba ɗan DCD bane"
wayan ne ya faɗi a hanunshi ya rike kirji yana ciza baki, yace "Innalillahi wa inna ilaihiraji'un..."
kafin ya karasa ya faɗi kasa, da gudu momy da nasir sukazo suna jijigashi idonshi ya rufe.
*Shima ɗa ne complete is ₦400 via 8144818849 hauwa shuaibu mapi moniepoint, evidence via 08144818849*
~Jikinta ya fara ci da wuta, nawal ya shiga tashin hankali fiyeda ɗazu, janta yake yana cewa "ammi mu gudu, ammi banaso ki mutu"
sai yanzu ta saki hanunshi da gudu ya fita yana kiran mutane su taimakeshi, hajiya da gudu ta hauro jin ihun nawal, yanzu yaran suka dawo daga shopping, ganin wutan da yake ci suka fara neman hanyan tseratar da mutanen ciki, ammi tana kwace a cikin wutan itace kaɗai suka ceta shi kuma Alhaji umar already ya kone harma ba zaka iya ganeshi ba, asibiti aka tafi da ammi domin akwai rai a jikinta, saide idonta a rufe domin kafafunta sun kone fatan ƙafan ya ɗaye sosai yayi jajur, nawal a tsirara ya bisu asibitin, da kyar aka kashe wutan, ammi kuma aka bata taimakon gaggawa, likitoci sun dubata amma sun tabbatar kafafunta ba zasu kara tafiya ba domin dole sai an yanke sabida wutan yaci har kashin kafarta, yaran Alhaji umar sun tafi sun barshi shi kaɗai a asibitin sabida suma ta babansu suke ba tashi ba, yana zaune tsirara babu kaya ya haɗa kai da gwiwa yayi shiru a bakin kofan ɗakin da ammi take kwance suna aikin yanke mata kafafu sabida ƙafan ba zai kara aiki ba"
duk masu wucewa sai sun kalleshi be damu ba burinshi ya tabbatar ammi tana raye, take aka fara yaɗawa a gari Alhaji Umar ya mutu sakamakon gobaran daya faru a gidanshi, sai dare kafin suka bari ya shiga, ammi tana kwance ansa mata oxygen kafafunta kuma duk biyu aka yanke, gata dai a kwance kamar mara rai, kanshi ya ɗaura a cikinta yayi shiru ya kasa kuka, yadda yaga rana haka yaga dare, da kyar bacci ya saceshi baima san yayi ba, har washe gari yana bacci saida dr ya tasheshi, a firgice ya buɗe ido yana kallon dr, yace "tashi mana nan wajen bacci ne?"
yace "a,a kayi hakuri"
cikin sanyin muryanshi yayi maganan, dr yace "ina ƴan uwanka?"
yace "banada ƴan uwa daga ni sai Ammi"
cikin tsawa yace "me kake nufi da bakada ƴan uwa? du waɗanda suka kawota su waye?"
yace "yaran mijinta ne"
yace "to kaje ka kirasu suzo su biya kuɗin aiki"
shiru yayi, dr yace "baka ji bane?"
a firgice yace "naji"
yace "me kake jira?"
tashi yayi ya fita jikinshi har yana rawa tsaban tsoro da yunwa, a tsirara yaje gidansu ya samu hajiya da yaran yace suje asibiti su biya kuɗin aiki koranshi sukayi sukace basu da komai a gidan kada ya kara taka kofan daga shi har Ammi ko kuma su sa police su kullesu, jin haka yaji tsoro da yaji police ya koma asibiti, Dr yace "ina suke?"
jikinshi yana rawa yace "sunce bamuda komai a gidan..."
wani tsawan daya daka mishi saida ya ɓuya a bayan kofa, ya kwala kira nurse suka shigo yace su ɗaurata akan keken marasa lafiya su fitar da ita daga asibitin, duk inda sukaga ya dace su wurgar da ita.
nawal ya durkusa ya fara bashi hakuri ball yayi dashi ya fita a ɗakin, suka ɗaurata saman keken suka fitar da ita, a kofan asibitin sukayi wurgar da ita, rasa yanda zeyi yasa ya tashi yana bin mutane yana neman taimako, kowa ya gani sai yace "ku taimaka ku ɗaukemin ammina daga can batada lafiya"
babu wanda ya kulashi kowa kallon mahaukaci yake mishi musamman da suka ganshi tsirara.
har dare babu wanda ya kulashi, a bakin kofan asibitin yaje ya sameta ya kwanta, bacci ya fara ga sauro ga sanyi, rungume da ita yake har yanzu bata buɗe ido ba, washe gari ya tashi yana kara neman taimako, da kyar ya samu wani riga me datti daya gani a kasa yasa a jikinshi, babu wando amma rigan ya sauka ya rufe gabanshi, kamar yadda suka saba bara shida ammi yauma haka yake bin titi yana bara, kwano ya samu yana zuwa neman abinci, Allah yasa ya samu abinda zeci ga kuma kudi ya samu kaɗan, komawa yayi ya janye ammi ya kaita bayan asibitin kan wani bola ya kwantar da ita sannan shima ya zauna a kusa da ita ya buɗe abincin ya fara bata, kallonshi take bata iya magana sabida zafin wutan ya bugata sosai shiyasa har yau bakinta be buɗe ba, datti yayi sosai gashinshi ya taru yayi kura yayi datti, duk da shi fari ne amma ya dishe yayi baki saide har yanzu da haskenshi, hawaye yana wanke mishi fuska, share mata hawayen ya fara sannan yace "ammi kici abinci karki zauna da yunwa"
kasa buɗe baki tayi, ya buɗe bakin a hankali yake sa mata, ci tayi sannan shima yaci yana farin ciki yau tashi abinci.
haka yake kula da ita idan yaje yayi bara ya kawo abinci suci, babu me kula dasu har ya fara girma ya fara zama saurayi a bola suke kuma bara yake yana samun na rufin asiri, yanzu ya kai 15year kuma a kullum rayuwa darasi take kara koya mishi, be taso cikin daɗi ba amminshi tana cikin wahala gashi babu kafafu, hadari aka haɗa sosai yau da alama ruwan ba mai sauki bane, ga iska da yake tashi sosai, yayi shiru yana kallon ammi yayi tagumi ya rasa ina ze kaita kada ruwan ya taɓata, ammi murmushi tayi mishi tace "nawal meyasa kayi shiru?"
bai amsa ba kawai ya rike hanunta yana murzawa idanunshi sunyi jajur har ruwan sama ya fara dukansu da ita, duk yawan ruwan a kansu ya kare daga karshe aka sauko da wani sanyi me ratsa jiki, ammi ta fara rashin lafiya ta fara rawan sanyi, yana rike da ita yana kallonta tana kakkare jikinta, tashi yayi domin zuwa siya mata magani, cikin asibitin ya shiga yana kare jikinshi sabida sanyi, ya samu dr wanda shine ya yiwa ammi aiki shekaru dayawa da suka wuce, yace "maganin zazzaɓi nake so"
Dr be ganeshi ba ya fara haɗa mishi magani saida ya gama sannan yace "gashi"
karɓa yayi ya ciro ɗari biyar shine iya kuɗinshi daya rage ya bashi yace "gashi"
wani kallon da yayi mishi kallon bakada hankali ne?
cikin tausayin ammi yace "ka taimaka min wallahi ammina ce babu lafiya"
cikin tsawa yace "ta mutu mana ina ruwana?