yi ba, ajewa tayi sannan taje tana ɗagata tace "tashi mana janna"
tace "dan Allah unty Ibtee ki kyaleni dan Allah"
tace "haba janna me nayi miki kuma?"
tace "kenan bakiji haushi ba Abba yana jan wannan talakan cikinmu wai har abinci zamuci tare? wani irin kaskanci ne wannan?"
tace "dan Allah janna ki daina kaskanta ɗan adam koba komai shima kamar kowa yake me matsalanshi?"
tashi tayi tace "au bayada matsala ma kenan? kinaji fa Abba yana cewa wai ya fini a wajenshi..."
cup ɗin tasa mata abaki, tace "shiru nikam kiyi breakfast"
karɓa tayi tana sha, indomie ta bata shima taci kaɗan tace ta koshi, mami ce ta shigo da waya a hanu tace "Ibtee ga yusra ta kira tace na haɗaku"
karɓa tayi da fara'a tace "yusra ya kike?"
mami tana tsaye ta harɗe hanu a kirji tana kallon yadda Ibtee take dariya suna waya da kawarta, ibtee tana son yusra sosai, tace "ga janna nan"
bata wayan tayi suka fara gaisawa da yusra tace "unty yusra ki gaida su mama"
tace "zasuji jannarmu"
murmushi tayi, Ibtee ta kara karɓa sukaci gaba da wayan, mami kallon kayan dake zube akan gadonsu wanda babu guga tayi, ta karaso ta zauna a bakin gadon ta ɗaura ɗayan kafanta akai ɗayan kuma a kasa, ta fara ninke kayan, janna cikin sanyin murya tace "dan Allah mami kiyi hakuri ki daina fushi dani dan Allah"
tace "koda nayi hakuri janna zaki kuma, bakya jin maganana janna kin maidani sa'arki"
tace "wallahi mami na tuba Allah ba zan kara ba"
tace "shikenan na yafe miki"
rungumeta tayi tace "yawwa mami na nagode"
tare suka fara ninke kayan janna tana zuba musu a wardrobe.
har dare tana tare da mami kamar ba zatayi wani abin ba amma a ranta tasa yau zata je ta haɗu da sabon saurayinta da suka haɗu a wajen birthday party ɗin saarah, ta kashe jiki har Ibtee bata fahimci komai ba, kayan da zatasa ta aje a sama sama sabida kada tayi wahalan nema, riga da wando ne sai after dress da jessy veil, takalminta me tsayi ta ɓoye da jakan da zata tafi dashi, cikin dare kowa yana bacci harda Ibtee itama janna kamar me bacci haka ta kwanta harda rungume Ibtee, a hankali ta zame jikinta ta kalli agogo karfe 12 na dare, sauka tayi a gadon already tayi wanka, silky sleeping dress ɗin ta cire sannan ta ciro rigan shimi da tsinannen jinx ɗinta, sawa tayi ta ɗauko belt na wandon ta ɗaure, after dress tasa sannan ta fashe jikinta da wani arnen turare, rolling kanta tayi sannan ta rike takalmin a hanu sabida kada aji karan takunta, jaka ta rataya a wuya tasa glasses ta jefa cingum a baki, karamin wayan data ɓoye ta ciro ta tura text kamar haka (hello love gani nan zanzo yanzu a jirani a kofan muradhotel idan nazo saimu shiga muyi magana acan)
cikin sanɗa ta fara tafiya ta rufe kofan ta bar Ibtee a ɗaki.
tafiya take da takalmi a hanu har ta bar main parlour na kasa, hamdala tayi ganin ba'a kamata ba.
saida ta shiga tasa takalminta, gate ɗin taje zata buɗe nawal dake zaune a bakin kofanshi ya kasa bacci sabida tunani yaga mutum tana ƙoƙarin fita, ganin gate ɗin bai buɗu mata ba ta fara kokarin haurawa katanga, saida ya bari ta haura kafin yazo inda yace "sauka ki koma ciki"
kallon banza tayi mishi tace "waye kai da zaka hanani fita?"
yace "bodyguard"
tace "to baka isa ka hanani fita ba wallahi kayi kaɗan, who the hell think you are?"
yace "kafin na irga goma ki sauka ki koma gida"
yace "1..2..3...4...5..6..7..8..9.."
ganin tana shirin dira a waje yace "10"
bindiga ya ciro ya fara harbi, dafa kirji tayi ta waro ido ganin yana neman harbe mata kafa, ta fara tsalle a saman tana cewa "ka dakata zan sauka wallahi zan koma"
harbi yake yi kuma dab kafarta yake harba, tsallen da takeyi ya hana bullet samun kafafunta, faɗuwa kasa tayi ta kwala ihun azaba kwankwasonta kamar ya karye data faɗin domin kamar baya jikinta take ji, har yanzu bai daina harbi ba kuma kusa da ita yake harbin, birgima ta fara a kasa tana kaucewa harbin, yana binta tana kaucewa tace "kayi hakuri ka daina harbin zan koma"
saida ya rakata da harbi har bakin kofan falo kafin ta tashi tana jan kafa ta shiga ciki ta rufe kofan gau tana haƙi, hanunta a kirji ta dafa idonta rufe, ganin babu wanda ya fito ta lallaɓa ta shige ɗakinsu, a bakin ta zauna tace "wayyo Allah dama mahaukaci ne?"
Ibtisam cikin bacci taji haki yayi yawa, a hankali ta buɗe ido ta kunna wuta, ganin janna zaune a kasa tana rike da waist tace "janna?"
sauƙa tayi a gadon tazo tana dubata tace "daga ina kike? meya faru?"
tana haƙi tace "ki kaini gado unty Ibtee bayana kwankwaso na yana ciwo"
tace "to"
riketa tayi ta kaita kan gadon ta kwanta, tace "wayyo Allah kwankwasona yana ciwo na shiga uku na lalace"
tace "wai meya sameki ne? ina kikaje?"
tace "wannan mugun sabon bodyguard ɗin ne ya komar dani gida da harbi"
murmushi Ibtee tayi tasan ya hanata fita ne.
tace "sannu kiyi bacci zai warke"
kuka take yi har bacci ya ɗauketa, Ibtee tace "idan yana gidannan nasan zai koya miki hankali zaki daina satan fitan dare"
kwanciya tayi ta koma baccinta.
washe gari kamar kullum sunyi taron yin breakfast Abba ya kira nawal wanda har ya saba breakfast dasu, zama yayi kujeran dake facing na janna, bata yadda ta ɗago kai ba sai yayyanka kwai take da karamin wuka, shima bai kara kallonta ba, Ibtee ce ta zuba mishi cowslow data haɗa ta tura gabanshi, a hankali ya motsa jajayen lips nashi yace "na gode"
murmushi tayi karaf a idon mami, Abba yace "nawal jiya da dare naji karan harbi meya faru ne?"
janna tace "Abba yanada bindiga"
wani kallo Abba yayi mata tayi tsit ta sunkuyar da kai, Abba yace "nina bashi lasisin rike bindiga nina bashi bindiga, nawal meya faru jiya?"
yace "kare ne ya shigo layin kuma kamar aikenshi akayi shiyasa na mayar dashi inda ya fito"
janna kasa karasa yanka kwan tayi jin sunan daya kirata dashi "kare?"
bai kalleta ba, Abba yace "okay na san da wani abin ne zaka kirani a waya kamar yadda na faɗa maka duk abinda ka gani baka yadda dashi ba zai cutar da kai ka kirani a waya ina tare da kai"
yace "zan iya Abba shiyasa ban kira ba"
abba yace "Allah ya taimaka"
daga nan bai kara magana ba, janna idonta yayi jajur bakinta yana rawa amma ta kasa ɗago kai ta kalleshi sabida kada abba ya ganta, har suka gama breakfast suka tashi suka barta a wajen bata daina huci ba, tana ganin ya fita ta tashi a fusace kamar zata tashi sama, binshi tayi zai shiga ɗaki taja bayan riganshi ta dawo dashi baya, yace "me haka?"
ta nuna kanta tace "nice kare?"
taɓe baki yayi sabida bai son hayaniya zai shige ciki ta kara janshi tace "nice kare?"
shiru yayi mata, sakinshi tayi ruwan dake cikin roba me sanyi na dattin daya gama wanke mota sauran ya rage ta ɗauka, juyewa tayi a kanshi sannan taje ta ɗau roban sharan gidan gaba ɗaya tazo ta kife a kanshi, cikin bala'i da wutan tsanarshi dake ruruwa a ranta tace "kai zaka kirani kare? ina fatan yanzu ka tuna matsayinka a gidannan? kuma wallahi idan baka cire idonka a kaina ba saina wulakanta rayuwarka ta yadda ko cikin mutane baka isa ka shiga ba, ka fita a harkata sabida na tsaneka"
Ibtee dake kallonsu ta saman upstair da gudu ta sauko, tana zuwa tace "janna me kikayi haka? meya miki zaki zuba mishi shara da ruwa?"
juyowa tayi a fusace zatayi magana ibtisam ta ɗauketa da marin da tunda aka haifeta Ibtee bata taɓa marinta ba, dafa kunci tayi tana kallon Ibtee da mugun mamaki, tana huci ta ɗaga hanu kamar zata rama sai kuma ta dunkule hanun tana kallon Ibtee kamar zuciyanta zai fito, tace "zaki rama ne janna? zaki rama? to ki rama"
matsowa tayi gab da ita tace "ki rama mana tunda naga bakida kunya, bakida tarbiyya janna"
tana hawaye tsaban zafin rai tace "ni kike cewa banada tarbiyya?"
tace "kina dashi ne? da kinada tarbiyya zaki mishi abinda kikayi? janna meyasa kike wulaƙanta ɗan Adam? meyasa bakya girmama mutum?"
tace "Ibtisam akan wannan baren da ko danginshi ba'a sani ba kika mareni?"
tace "koda baida kowa ne a duniya janna to inaso ki sani SHIMA ƊA NE kamar kowa, talauci Allah ne yake ɗaurawa mutum ba shine yake ɗaurawa kanshi ba"
Ibtee rai a ɓace ta juya zata tafi janna ta rike hanunta, tace "sakarmin hannu jannah"
itama tana huci tace "ba zan sakeki ba har sai kin gayamin matsayin wannan ƙazamin a wajenki"
tace "ki sakarmin hanu nace"
tace "sai kin faɗamin idan ba haka ba ko zamu kwana anan saide mu kwana waye shi a wajenki?"
juyowa tayi hawaye akan fuskanta tace "masoyi"
ido a waje janna take kallonta, tace "kin san me kike faɗa?"
tace "masoyi nace ina sanshi a yadda yake koda a bola yake kwana"
fizge hanunta tayi zata tafi janna tasa mata kafa tanaso ta dawo da ita, waro ido tayi zata faɗi nawal yayi saurin riketa ta faɗo jikinshi idonta a rufe.
janna cikin shock take kallonsu, Ibtee a hankali ta zame jikinta tace "kayi hakuri nawal"
a hankali ya girgiza kai alaman babu komai, dattin jikinshi ta fara kaɗewa sannan ta cire boturan jikin riganshi rigan ya jiƙe sosai ga datti, a hankali ta zame rigan, yana tsaye a wajen kamar yadda janna take tsaye tana dafe da kunci har yanzu, Ibtee ta dawo da bargo me taushi da kauri tazo ta tsaya a gabanshi, rufeshi tayi da bargon sannan tasa karamin towel tana goge mishi ruwan daya jiƙa tulin suman kanshi, sajenshi wanda yake kara rura wutan kyawunshi ta goge mishi ruwan daya jiƙa, sajen ya kwana luf, pink lips nashi ta kalla wanda baya yawan magana saide yayi sucking lips ɗin a hankali, lumshe kyawawan idanunshi da lashes ɗin da suka jiƙe yayi, jikewan lashes ɗin ya karawa idon zama kamar na turawa, cikin sanyi taga ya motsa lips nashi alaman na gode, murmushi tayi ta sunkuyar da kanta.
Abba dake tsaye a upstair duk abinda yake faruwa a downstairs ɗin yana kallo, da farko yayi niyan ɗaukan mataki akan janna amma tunda yaga action na Ibtisam saiya fasa sabida ta gama komai.
~Mami a gajiye ta dawo gidan, hanunta rike dana jaad tana kallon cikin gidan da mamakin babu ƴan aiki ko ɗaya harta gate wani daban ne ya buɗe mata, da kallo tabi nawal daya durkusa har kasa ya gaisheta, ta amsa sannan tace "waye kai?"
yace "nine sabon p.b ɗin me gidan, kuma nine zan rinƙa gadi da kula da fulawoyi da komai daya shafi aikin gidan sannan me bawa yaran tsaro na musamman"
tace "wani me gidan? shida yayi kwana huɗu baya gidannan"
yace "mun dawo tare dashi"
waro ido tayi tace "what? kana nufin ya dawo?"
yace "eh"
hanun jaad taja suka shiga ciki, ibtisam tana zaune a falo tayi tagumi mami tana shiga tace "wai da gaske Abbanku ya dawo?"
ta gyaɗa kai jiki a mace tace "eh"
mami da mamaki tace "to meyasa jikinki a mace? bakiyi farin cikin dawowansa bane?"
tace "no ba haka bane"
tace "ina janna? ba dai ta karya dokana ta fita ba"
tace "mami Abba ya kira police sunzo sun tafi da janna da kawayenta"
dafa kirji tayi tace "what? me suka mishi?"
ta faɗa mata duk abinda ya faru, mami faɗawa tayi kan sofa tana salati, dafa kanta tayi tace "me janna take nema dani ne a garinnan? meyasa janna bataji ne? saida naja kunnenta kada tayi wannan abin janna ta nunamin ba zatayi ba ashe fitana keda wuya janna tayi, yanzu ya take so nayi dan Allah?"
ibtisam tace "gaskiya kije ki roki kan Abba yasa a sakesu ba daidai bane ace ta kwana a police station sabida Abba yanada matsayin da sunanshi zai iya lalacewa ace ma ko wani gagarumin abu tayi"
tace "Ibtee kinfi kowa sanin halin Abbanku yanzu haka zuwa wajenshi ma tsoro nakeji ibtee"
jaad yace "kenan mami za'a barta a wajen ta kwana?"
tace "jaad ai ita ta yiwa kanta ni ban san abinda zanyi ba amma bari naje na gwada bashi hakuri ko zai sauko"
tare kamar jira suke sukace "yawwa mami"
hijabin jikinta army green ta cire sannan ta haura saman da ɗan gudu gudu sabida batason stair sosai yana ɓata mata lokaci a cewanta, yayi wanka yana kwance cikin a.c ya rufe ido kamar me bacci, ba bacci yake ba tunanin ta yadda zai ɓullowa Alhaji Alhasan ya cishi da yaƙi yake yi, wannan abinda Alhaji Alhasan yayi mishi ya zama tabo a zuciyarshi ba zai warke ba sai ranan da yaga gawan Alhasan a kwance dana Ahlam a gefe kafin zai samu sauƙin wannan ciwon, da sallama ta shigo, bai buɗe ido ba tasan ba bacci yake ba, a hankali ta zauna kusa dashi ganin bai buɗe ido ba ta rungumeshi tsam, cikin sanyin murya tace "nayi farin cikin dawowanka mijina"
hanunshi kawai taji ya shafa bayanta kaɗan, tayi murmushi tace "daga station nake"
a hankali yace "na sani"
tace "da fatan ba wani mummunan abu bane ya sameka?"
a takaice ya faɗa mata yadda abin ya faru harma ya haɗa da gabatar mata da nawal matsayin sabon p.b ɗinsu, tace "Allah ya kara tsare gaba bari na kawo maka abinci"
yace "ameen I'm okay bana jin yunwa"
tace "to"
shiru tayi shima yayi shiru har yanzu idonshi q rufe, tana so tayi maganan janna tana tsoro, ta jima a haka tana kallonshi, cikin ɗar ɗar tace "dama dama nace"
yace "what?"
tace "dama maganan janna...."
cikin tsawan da har ibtisam da jaad da suke falon kasa saida sukaji yace "get out, dama shine abinda ya kawoki"
zatayi magana yace "out!!!"
tashi tayi sum sum ta fita daga ɗakin, ibtisam da jaad suka zuba mata ido tun daga saman har ta sauko, kai ta girgiza musu kamar zatayi kuka alaman yaki yadda, zubewa ibtee tayi akan lallausan sofan tace "wayyo Allah mun shiga uku"
Janna da kawayenta aka tisa keyansu har cell, janna ce suke rigima da polisawan tana cewa ba zata cire agogo da ɗan kunnenta ba, taki cire komai har aka shiga da ita haka, zama tayi tana basu hakuri tareda kwantar musu da rai, harda masu kuka domin idan iyayensu sunji ba zasuji daɗi ba, sun san me zai faru, janna tayi shiru kawai tana kallonsu, wani irin haushin maganan Abba ne yake tsaya mata a rai, wai wannan talakan bakon zaice ya fita a wajenshi, wannan maganan idan ta tuna yana mata ciwo sosai, wasa wasa saida suka kwana a cell sauro ya cijesu har jikin janna saida yayi jajur, sanyi kuma ba'a magana ga yunwa da yake azazalan cikinta, gaba ɗaya ta zama kalan tausayi, kawayenta duk suna baccin wahala.
nawal ganin Abba bai fito ba ya fara gyara fulawa kamar yadda ya saba a gidansu naseer, yayi bayin fulawan ya wanke duk motan da yake da kura, ya share gidan duk girman gidan saida ya wanke, yana kan gyaran fulawa ibtisam ta fito da katon basket a hanunta da kulan abinci a ciki ga kuma flask na shayi a ciki, tana sanye da abaya coffee color tayi bala'in kyau, a bayanshi ta tsaya tana kallon yadda yake aikin babu abinda ya dameshi, da tiyo ɗin ruwa ya juyo domin zubawa sauran ruwa bai saniba ruwan tiyo ya watsu mata a jiki, rufe fuska tayi jin ruwan har fuskanta, waro manyan idanunshi yayi yace "kiyi hakuri dan Allah ban san kina nan ba"
goge fuskanta tayi da hanunta da babu komai, kana tayi murmushi tace "ba komai zan kaiwa janna abinci a station"
yace "okay"
taɓa aljihunshi yayi yaji makullin mota, zai juya tace "gashi"
kallon ledan yayi sai kuma ya kalleta kallon me aciki?
tace "karɓa mana"
ya karɓa, tace "wannan shine uniform naka kamar yadda kowane bodyguard yake sa bakaken suit idan yana aiki a gidannan kaima wannan zaka rinƙa sawa dokan Abba ne wannan sannan duk wanda ya tsallake dokan Abba akwai hukunci me tsanani"
a hankali yace "to"
tace "jeka sa ina jiranka'
yace "to"
tafiya yayi tana tsaye tana kallon agogo, ɗakin megadi a ciki yake zama ya shiga ya sauya kayan, suit black sunyi bala'in karɓanshi, ya fito yana maida gashinshi da suka harɗe baya, ido ta zuba mishi tana kallon yadda yayi wani kyau da kwarjini, batasan ma murmushi ya suɓuce mata ba, har ya karaso ya buɗe mata mota, yace "shiga"
shiga baya tayi shi kuma ya shiga gaba zai tada motan jaad wanda dama aikinshi shine zuwa waje late ya fito da gudu tana ɗaga mishi hanu, tsayawa yayi bai tada motan ba saida jaad yazo ya buɗe gaba ya zauna, yace "good morning ya p.b"
yace "ya kake?"
yace "lafiya ƙalau"
ya kalli Ibtee yace "good morning unty ibtee"
tace "morning jaad how are you?"
yace "am fine"
fita sukayi yana driving a hankali, jaad ne yake janshi da hira amma amsa kawai yake iya badawa, daga nan sai yayi shiru yana kallon hanya, har suka isa station ya zauna a cikin motan yana jiransu.
ibtisam ta gama ciro abincin tace "fito mana"
ya kalleta tace "eh fito, idan munje waje da bodyguard namu har ciki Abba yake cewa ya shiga, a hankali ya buɗe ya fito, karɓan abincin yayi daga hanun jaad suka shiga gaba yana baya har zuwa ciki, janna tana kwance a galabaice yunwa takeji kamar tayi kuka, ganinsu yasa ta tashi tana kuka ta rungume ibtee tace "dan Allah ki cewa mami tazo su fitar dani anan ba zan iya ba"
nuna mata cizon da sauro suka mata tayi, tace "kinga nan sauro ne ya cijeni, kinga nan ma sauro ne"
ɗaga riganta tayi da sauri nawal ya rufe ido ganin abinda take shirin yi, ibtee tayi saurin sauke mata rigan tace "na gani amma ki daina ɗaga riga a cikin mutane"
tana kuka tace "dole na nuna miki tunda ke yayata ce kiga abinda sauro suka min dan Allah ko ni kaɗai ce Abba ya cireni anan"
kawarta tace "amma janna bakida kunya kina nufin mu a barmu anan? kin manta wajenki mukaje"
tace "ni nace kuzo? ni nace kuzo birthday ɗina?"
ibtisam tace "dan Allah janna ki bar wannan maganan Abba zai