zata barni ba ammi"
Already yayi dressing ɗinshi yadda ya saba a duk lokacin da zaije sata, yasa mask ɗin sannan ya ɓoye karamin bindigan da dady yake nema a haukace ya rasa inda yake, fita yayi ya rufewa Ammi kofa sannan cikin sanɗa ya haura katanga ya dira, tafiya ya fara cikin tsakiyan dare babu kowa a hanya.
~Hall ɗin da ake tsaka da party ɗin birthday tun daga kan motocin dake fake yasan ba yaran kananan mutane bane a wajen, bindiganshi ya ɓoye sannan ya cire mask ɗin, yi yayi kamar ba ɓarawo suka barshi ya shiga sabida yanayinshi ba irin na wanda ya taso cikin tsantsan wahala bane, saida ya shiga kafin yasa mask ɗin yana bin ko ina da kallo, disco light ne a wajen wuta kala kala yake kawowa blue, red, yellow, white wajen ya zama busy kowa sai rawa yake janna ce gaba gaba wajen yin rawa har yanzu bata gaji ba, ga birthday girl da abokai maza da mata suna ɓarin kuɗi a wajen, ji yayi ranshi yana tafasa ganin yadda suke wasa da kuɗi da abinci da drinks bayan mutane dayawa suna kwana da yunwa, iyayensu sun sace kuɗi sun basu tsaban rasa abinyi da sukeyi da kuɗi shine suke wannan party party da taron da babu amfani, rufe ido yayi ya gyara mask nashi, babu wanda ya kula dashi sabida hankalinsu baya kanshi, kutsawa ya fara cikinsu, taka mutum yayi ba tareda ya kula ba, ƙafan jannah ya taka, dago kai tayi cikin hasala taja riganshi baya ganin zai wuce ko sanin ya takata baiyi ba, juyo dashi tayi bata kula da mask ɗin fuskanshi ba ta ɗaukeshi da mari, dafa kunci yayi da hangloves a hanunshi baki, kallonta yayi itama ta kalleshi tace "kai makaho ne? ka wani sa bakin abu a fuska a ganinka kai wani jan wuya ne me ji da kanshi? waye ubanka a garinnan da zaka taka janna kuma ka wuce ba tareda ka bata hakuri ba?"
kallonta yake yi tana maganan, tunda Ammi ta haifeshi bai taɓa ɗaura ido akan mutum yaji tsanan meshi kamar wannan ba, marin da tayi mishi ya taɓa zuciyarshi ga wani masifa da take yi tana nunashi da yatsa, ɗaga glasses na idonta tayi ganin baiyi magana ba saima kallonta da yake kamar ma kallon rainin wayo yake mata, shi kuma nature ɗinshi ne haka kamar me kallon raini, champagne ɗin dake hanunta ta watsa mishi sannan tace "useless ka wani kuramin ido ko zaka rama ne?"
shiru kawai yana jin sanyin drink ɗin a jikinshi, juyawa yayi yana kara tsanan masu kuɗi a ranshi, su suke wulakanta mutane a cewarshi, ido ya zuba akan wajen kashe wutan, murmushi yayi ganin babu hankalin kowa a kanshi, zuwa yayi yaga wayoyinsu duka sun adana a wani waje mutum yana gadin wayan sabida tsaro, saida ya haddace ko ina kafin yaje yaga babu me kallonshi ya kashe wutan, wajen ya koma duhu, baka iya ganin komai tsaban duhu, kowa ya fara cewa "ya akayi aka ɗauke wuta bacin solar suke amfani dashi?"
wajen ya kaure da surutu kowa yana neman inda wayarshi yake domin haska toci, wayoyin ya kwashe ya zuba a jakan, harbi yayi, ihu sukayi jin harbi a inda suke, yace "shiru kowa yayi shiru"
tsit sukayi yana tsaye a sama yace "duk wanda yayi magana saina fasa kanshi da bindiga"
shiru sukayi, yace "duk zan amsa kiran da iyayenku suke yi babu me fita anan"
janna cikinta ne ya ɗuri ruwa kenan ɓarawo ne ya shigo? kenan shi ta mara?
a tsorace take kalle kalle ta fara ta cikin duhun ko zata ganshi amma bataga komai ba.
rufe wajen yayi ta yadda babu me iya fita ya rike makullin a hanunshi sannan yace "duk wanda yayi niyan kiran police ya kira amma ku sani idan police suka zo nan ba'a biyamin bukatata ba zansa wuta anan duk mu mutu sabida kunga wannan"
ya kunna tocin waya ya haska laita da galan da fetur daya ɓoye a jakanshi, ya ciro wani abu dake kawo red na wuta yace "wannan bomb ne zai iya tashi a duk lokacin dana taɓa wannan jan sabida haka kowa ya nutsu banason ko tari ayi anan, akwai wasu da nake tare dasu sun kewaye nan wajen ba kowa bane zai gansu duk wanda yayi yunkurin illatani suna ganin kowa a yanzu haka, duk abinda nakeyi akan idonsu"
har yanzu babu wanda ya iya koda yunkurin yin tari ne, kowa yana tsaye jikinshi yana rawa, daga mazan har matan, duk suka fara salati ya daka musu tsawa tareda harba bindiga a sama yace "shiru kowa ya zauna"
shiru sukayi kowa ya zauna, babu karan komai saina takun nawal wanda yayi ready da bindiga yana kai kawo sabida su san yana kusa dasu.
jannah fitsari take ji tsaban yadda hantar cikinta ya kaɗa saida numfashinta ya ɗauke na wasu lokaci, babu abinda take gani sai Abba, tasan watan barin gidansu ya kama matukar Abba yasan ta fita a gida kuma harma bata kwana ba zai koreta a gidanshi.
ibtisam tsaye a kan mami tana bata hakuri ta daina kuka ta nutsu janna zata dawo kuma insha Allah Abba ba zai dawo yau ba, mami cikin kuka tace "ibtisam idan Abbanku ya dawo fa zan rasa inda zanje matukar yasan janna ta kai wannan lokacin karfe ɗaya na dare bata dawo ba wallahi zai koreni ibtisam ina kuma zanje? banida kowa banida uwa banida uba babu kowa da zanje gidanshi na zauna, ibtisam meyasa janna take min haka?"
zama tayi ta rike ta tace "mami calm down jannah zata dawo kafin Abba bari na kira Ahlam kiji shi yace da alama kwana zasuyi"
wayan mamin ta karɓa ta kira layin ahlam tace "p.b ina Abba?"
cikin kasa da murya yace "yanzu zamu dawo gida"
dafa kirji tayi tace "innalillahi wa inna ilaihiraji'un dan girman Allah p.b kasan yadda zakayi ka lalata motan kada ku zo gida yau ka lalata motan a hanya dan Allah p.b"
yace "ibtisam kin san Abbanku da naci..."
katse wayan yayi taji muryan Abba yana cewa "muje p.b na gama"
aje wayan tayi tace "innalillahi wa inna ilaihiraji'un Abba zasu dawo yau mami"
shiru mami tayi, jaad yace "saida muka faɗawa unty janna kada ta fita ba lalle su kwana ba amma taki jin magana saida ta fita"
ibtee cikin tsawa tace "ba kai ka faɗa mata ba? dama wa yace ka faɗa?"
yace "unty ibtee Abba yanada takura yara ranan da baya kusa damu murna muke yi sabida zamu samu freedom shiyasa naje faɗa miki ba ita bama"
tsaki taja tace "ya zanyi? janna ina kike?"
safa da marwa ta fara ta kasa tsayuwa waje ɗaya, mami jingina kai kawai tayi da gadon tayi shiru, saita mutu janna zata huta.
suna wajen har sukaji karan buɗe gate alaman su abba sun dawo, da gudu taje ta ɗaga labulen window tana leka downstair, gani tayi an shigo da g-wagon motar da Abba yake fita dashi black, har personal bodyguard nashi wato p.b Ahlam ya buɗe mishi marfin motan ya fito sanye da babban riga da jaka baki a hanunshi, da gudu ta saki labulen ganin zai ɗago kai, a ruɗe tace "mami wallahi ya dawo, Abba ya dawo gidannan janna bata dawo ba mami mun shiga uku"
mami tace "jaad tashi kaje ɗakinka ka kwanta kema ibtee kije ki kwanta idan ya tambaya zance kunyi bacci"
tare sukace "to mami"
fita sukayi kowa ya nufi ɗakinshi, jaad ya kwanta itama ta shiga ɗakinsu ta jera pillow akan gadon ta rufa da bargo ya zama kamar mutum ne a kwance, itama ta kwanta ta kashe wutan sannan ta rufe ido kamar me bacci.
da sallama ya shigo fuska babu walwala ya kalli mami data karɓi jakanshi yace "ina yaran?"
tace "duk sunyi bacci"
yace "okay"
gabanta ne ya faɗi ganin ya nufi kofan ɗakinsu janna, ji tayi fitsari yana shirin zubo mata, buɗe knocking yayi sannan ya tura kofan ya kunna wutan ɗakin yana kallon gadon, ibtisam dukan tara tara kirjinta yake yi, ta rufe ido tana cewa "ya Allah kada ka tona mana asiri Allah Allah Allah"
saida ya gama kalle ɗakin kafin ya kashe wutan yaja musu kofan, ajiyan zuciya mami ta sauke ganin dabaran da ibtee tayi, ɗakin jaad ya duba sannan ya wuce ɗakinshi, mami tace "me za'a kawo maka?"
a takaice yace "ruwa"
fita tayi domin kawo mishi ruwa, ɗakinsu janna ta shiga tace "ibtisam ya zama dole musa ido muga shigowan janna kada abbanku ya gane"
tace "insha Allah mami"
tashi tayi ta koma falon kasa domin ganin zuwan janna, sai kallon agogo take amma har yanzu shiru, mami ta koma wajen Abba sabida kada hankalinshi ya koma waje saide hankalinta duk yana waje, Allah Allah take janna ta dawo bai sani ba.
Ibtisam tun tana jiranta har bacci ya ɗauketa a falon, mami ma bacci tayi Abba ma bacci yayi, janna suna can har yanzu babu wanda ya runtsa, kiran wayoyinsu da akeyi yake amsawa, waya ɗaya ne ba'a kira ba shine wayan janna, kallon wayan yake yi har yanzu babu wanda ya kira, duk sauran gidansu sun san anyi kidnapping nasu amma me wannan wayar ba'a sani ba, yace "waye me wannan wayar?"
janna dake zaune duk tayi la'asar ga bacci ga yunwa ga tsoro duk sun mata yawa tace "nawa ne"
kasancewar ya haska da toci shiyasa ta gani, wajenta yazo yasa bindiga a kanta yace "meyasa babu wanda ya kiraki? ko dai ba'a gidanku kike da zama ba? dan kinfi kama da masu zaman bariki"
tayi shiru amma maganan yaci ranta, cikin tsawa yace "ba magana nake miki ba"
tace "nafi karfin zaman bariki babana shine tsohon governor na garinnan ina fatan baka mantashi ba tunda babu jimawa kayi sata a gidannan"
murmushi yayi yace "okay kece ƴarshi da kika ɓuya a bathroom ranan dana shiga gidanku?"
a razane ta kalleshi ta cikin duhun sabida tayi mamakin yadda yasan ta ɓuya harma da inda ta ɓuya, yace "babanki shine yake nemana ido rufe duk inda yaje yana bada sanarwan duk wanda ya kawo mishi ni zai bashi makudan kuɗaɗe to idan kin samu na sakeki ki faɗa mishi nafi karfin kamu kuma zanci gaba da addaban rayuwarku"
ya lura tanada tsaurin ido shiyasa ya kara danna bindigan a kanta yace "kinji ko bakiji ba?"
tace "naji"
number ya gani tayi saving da sweet mom, kiran numbern yayi yafi sau biyar ba'a ɗauka ba, sai daga baya yaga an kira, yana ɗauka yaji muryan namiji ne da alama Abba ne ya ɗau wayan, murmushi yayi sabida haka yafi so, yace "ƴarka tana hanuna nida kake nema ido rufe sabida nayi sata a gidanka, ba ita kaɗai ba itada sauran mutanen da suke party sannan duk sai an biyani kuɗin dana faɗa kafin na sakesu.
har yanzu be cire bindigan a kanta ba yace "kiyi magana"
a tsorace tace "Abba zai kasheni bindiga ne a goshina..."
jin muryan janna wayar ta faɗi a hanun abba ya zauna a bakin gadon yana cewa "Innalillahi wa inna ilaihiraji'un"
mami dake bacci taji anata salati da sauri ta tashi tace "lafiya?"
yace "ina janna?"
bakinta yana rawa tace "ta..ta..tana ɗakinsu"
yace "tashi muje na ganta"
jikin mami ya fara rawa, yace "tashi mana!!!"
a tsorace ta sauka a gadon suka fita, ɗakinsu janna ya buɗe yace "tasheta"
kallon gadon tayi sannan tace "bacci take fa...."
yace "tasheta nace"
zuwa tayi ta yaye zanin gadon gani yayi pillow aka jera, yace "ina ibtisam?"
a lokacin ibtisam ta shigo tace "Abba gani"
yace "ina janna?"
tace "may be tana toilet.."
wani tsawan daya daka musu saida suka rike juna, yace "kofan toilet ɗin ba gashi a buɗe yake ba? kun san bata gida kukace min tana nan harda yin plan ku jera pillow kamar itace akan gadon?"
shiru sukayi yace "ku amsa min"
mami tace "dan Allah kayi hakuri abban ibtee wallahi tallahi saida ibtisam ta hanata fita amma taki ji"
yace "okay an hanata fita ta fita? to shikenan bari na barta a wajen ɗan kidnapping ɗin da yayi attacking nasu a inda suke party suke aikata ba daidai ba suna saɓawa Allah idan ta zauna acan ya kasheta gobe zata kuma karya doka na"
mami tace "kidnapping?"
itama ibtee tace "kidnapping?"
juyawa yayi a fusace yace "kidnapping ɗinsu akayi kuma babu ruwan makama a wannan maganan kada wanda yazo min da wannan maganan koda wasa a barta a hanunsu"
mami jingina tayi da bango tace "Innalillahi ibtisam anyi kidnapping ɗin janna, ibtisam na shiga uku na lalace"
ibtisam sabida tashin hankali ta kasa cewa komai.
~A zaune janna suka kwana duk ta sauya kamanni ta zama kalan tausayi, nawal yana kansu har gari ya waye, be buɗe wajen ba kira ya fara samu daga gomnati suna tambaya menene abinda yake bukata sabida akwai yaran manya sosai a wajen da yayi attacking, murmushi yayi yana kallon kiran da suke mishi, saida kiran ya isheshi kafin ya kashe wayan yana cigaba da tsaresu, saida sukayi kwana biyu a wajen nawal yaki amsa kiran da gomnati take mishi, a kwana na uku ya amsa ya zauna akan kujeran da suka aje domin dj, tambaya aka kara mishi me yake bukata, yace "asibitin general hospital babban asibitin dake garinnan mutane sun kai dubu biyar kwance babu lafiya, saide babu maganin da za'a kula dasu inaso yau idan kuna son yaranku ku kai magani ishashe wannan asibitin yau, malaman makaranta sunyi wata biyar ba'a biyasu albashi ba sannan babu wani alama daya nuna za'a biyasu inaso yau a basu albashinsu na wata biyar da aka rike, unguwannin da suke tsananin buƙatan ruwa sunfi ɗari amma babu ko ɗaya da akasa himma za'a gyara inaso yau naji an damƙa kuɗin gyaran ruwa a kowane unguwa, sannan kuɗin fansan yaranku miliyan ɗari tara ne idan an biyamin bukatana ko yanzu zan saki yaranku idan kuma baku biya ba zanso ku kirani video call domin na nuna muku bomb ɗin da nake ɗauke dashi ban damu ba dan na mutu tare dasu akwai dayawa da zasuci gaba da yin irin wannan aikin na kidnapping, sannan zasuyi attacking na manyan wurare da yaddan Allah.
amsa mishi sukayi da "dan Allah kada ka illata kowa wallahi mun karɓa zamu baka duk abinda ka tambaya"
yace "dako kun tsiratar da yaranku"
janna ta kasa gane wani murya ne ɗaya nashi domin ya canja murya yafi sau goma sannan kowane murya ya iya sosai kamar ba shine yayi magana ba ɗazu idan yayi yanzu.
"mami tashi dan Allah kisha koda tea ne kinga har jaad baije makaranta ba sabida damuwan da muke ciki yau kwana uku kenan bakici komai ba mami"
tana kwance akan gado ta juya musu baya, muryanta ya dishe da kuka tace "me na yiwa wannan ɓarawon? meyasa yake shiga rayuwarmu? me mukayi mishi? yazo ya kwashe duk wani gold da yake mallakinmu yanzu kuma yayi kidnapping na janna me mukayi mishi?"
ibtisam tayi shiru da cup na shayi a hanunta, mami tashi tayi ta zauna tace "ibtisam wani irin mara imani ne zai rike mata har kwana uku watakila yana can yana cutar dasu, meyasa mutane suka lalace suke cutar da mata bayan addini ya hana a cutar damu?"
ibtisam tace "mami ki taimaka kisha shayin sabida sabida ba zamu iya jure ganinki babu lafiya ba, mami dan Allah ko kaɗan ne kisha"
tace "ban san me yake musu ba acan suna zaune da yunwa sabida son abin duniya Allah ya isa tsakanina da wannan ɓarawon na tsaneshi wallahi na tsaneshi ibtee"
da kyar ta lallasheta tasha tea, bata maganinta tayi sannan ta zauna a gefenta tayi tagumi, Allah kaɗai yasan halin da janna take ciki gashi Abba yaki yadda yaji komai daga bakin kowa yace babu ruwanshi da wannan maganan, shigowa yayi da sallama, jaad da ibtisam suka tashi da sauri suka fita sabida sun san wajen mami yazo, gyaran murya yayi sannan yace "munyi magana da gomna akwai ɗanshi a cikin attack ɗin, sannan kidnapper ɗin ya faɗi duk abinda yakeso kuma za'a biya mishi bukatanshi, na sauko ne sabida wannan satan yana nema yayi yawa yanzu ko ina sace mutane ake ana neman kuɗin fansa kuma na tabbata wannan tsinannen shi yake wannan laifukan, Allah ya nunamin ranan da zanga wannan yaron ido da ido wallahi babu wanda ya isa ya hanani kashe shi, saina wulakantashi ta yadda ba zai taɓa jin daɗi ba koda ance ya kara rayuwa"
shiru tayi sabida itama tana jin zafin abin, juyawa yayi ya fita daga ɗakin, hamdala tayi tace "Allah na gode maka daya sa baki a wannan abin koba komai janna zata dawo garemu"
sai yanzu taji sauki yana zuwa mata.
saida aka biyashi duk abinda ya tambaya sannan ya bare har zuwa dare ya silale daga ɗakin ba tareda sun ganshi ba, cire kayan yayi ya zubar a wajen, ya cire mask da safan hanu ya zama kamar shima party yazo, fita yayi saida safe sukaga kofa a buɗe, kowa a galabaice yake sabida yunwa da wahala, da kyar suka tashi suna fitowa, harda janna wacce take jan kafarta daya sha jini sosai, idonta ya faɗa sabida yunwa da gajiya, ga bacci da tsinkewan zuciyan haɗuwanta da Abba, kowa iyayenshi suna jiranshi a bakin kofan wajen, duk suka rungume juna suna kuka banda janna wanda bataga kowa nata ba, tasan haka zai faru tasan abba zai hana, badan mami da jaad da unty ibtee ba babu abinda zaisa ta koma gidan dan tasan saina lahira ya fita jin daɗi yau, motar da tazo dashi ta shiga tana jin bama zata iya driving ba sabida babu karfi a jikinta ko kaɗan, da kyar take jan motar ta hau titi, jiri yasa ta fara ganin hanya bibbiyu da kyar ta isa gida lafiya, shiga ciki ya gagareta ta zauna a cikin motan tayi shiru, ta ɗau lokaci me tsayi a wajen kafin ta fito a hankali take tafiya tana layi kamar ƴar kwaya, masu aiki suna gaishe ta bata ko kallonsu dama tana lafiya ma bata amsa ba bale batada lafiya, falon kasa ta tsinci kanta a ciki, Abba yana zaune ya ɗaura