jikinshi ba, Ibtee a ruɗe ta fara jera mishi sannu, idonta ya cika da hawaye tace "sannu kaji?"
gyaɗa kai yayi cikin dauriya, tana rike dashi shima jaad haka tace "mu kaika asibiti?"
girgiza kai yayi, tace "jaad jeka ɗauko makullin mota zamu tafi asibiti"
mami tace "Ibtee a faɗawa Abbanku"
girgiza kai tayi tana kallon ƙafarshi jaad yana fitowa ta karɓi makullin tace "rikeshi mu tafi"
nawal yace "karki damu...."
tace "shiru!!!"
shirun yayi tace "muje"
cikin ɗingishi yake takawa suna rike dashi sannu kawai take iya faɗa mishi, shiga mota sukayi ta shiga mazaunin driver da wani speed taja motan ta bar gidan, rabonta da driving ta jima sabida Abba baya bari suyi driving, hasalima janna tafi jansu idan zasu fita driver ɗinsu baya nan, asibitin kashi ta kaishi aka fara duba kafar tana tsaye ta kasa zaune, nawal sai kallonta yake yadda ta ruɗe Ammi ce kaɗai take irin wannan ruɗewan idan baida lafiya, ya samu targaɗe a kafar suka gyara mishi tareda shafa mishi magani, tace "zaka iya takawa?"
gyaɗa kai yayi ya lumshe ido alaman eh zai iya, tashi yayi da kanshi ya fara takawa amma har yanzu tafiyan ba normal ba, murmushi tayi tace "Alhmdllh"
a hankali take driving bini bini yana satan kallonta, ji yayi zuciyanshi yana harbawa da sauri da sauri, a hankali ya sunkuyar da kai data juyo, murmushi tayi tace "meyasa kake satan kallona"
cikin sanyin murya yace "na gode"
murmushi kawai tayi, har suka isa gida kafin jaad ya buɗe mishi ya fito, har ɗakinshi suka rakashi kafin ta rike hanun jaad suka shiga ciki, janna tana zaune a dinning har yanzu ta kasa tashi ganin irin ruɗewan da Ibtee tayi, suna shiga Ibtee ta nufi inda janna take tace "kin kyauta?"
ta taɓe baki tace "me nayi?"
cikin tsawa tace "janna kiji tsoron Allah ki daina wulaƙanta ɗan adam, janna me ya miki?"
tashi tayi tace "nifa ban gane me kike faɗa ba, sabida yaji ciwo shine zakizo kina min tsawa"
tace "idan ban miki tsawa ba me zan miki?"
mami tace "kai kai me kuke yi haka? abinda bakwayi shine zaku fara yanzu?"
Ibtee cikin ɓacin rai tace "mami itace fa..."
ɗaga mata hanu mami tayi tace "banason jin komai abinda nakeso ku sani shine ba zan ɗauki faɗan da zaku fara ba yanzu"
rai ɓace Ibtee ta bar wajen, mami ta bita da kallo har ta shiga ɗaki, taɓa baki tayi sannan itama ta shiga kitchen, janna har cikin ranta take jin zafin yadda Ibtee take kare wannan driver ɗin.
jinyan kafar har ya gama Ibtee kullum saita kai mishi abinci, har ya warke ya fara fita dasu, Abba bai san abinda ya faru ba har yau.
yau weekend zasu fita shopping tun safe sai murna suke sabida Abba ya yadda suje, janna tana shiri Ibtee already ta shirya, subhanallah kayan kamar a jikinta aka ɗinka, shadda fited gown light purple, hannun manya sannan aka jiƙa da stones, mayafi dark purple tasa shima yaji stones, flat shoe ne a kafarta domin bata saba da high ba, janna kuma wani bakin shadda tasa itama fited ne irin ɗinkin Ibtee tasa mayafi siriri red da takalmi red me tsini, glasses tasa me faɗi a idonta, cingum ta tsoma a baki sabida ta saba ci, turare ta fesawa Ibtee me kamshi sannan ta fesa, jaka karami ta rike a hanu red sannan tace "let's go"
Ibtee tace "kinyi kyau sosai jaan"
tace "thank you unty Ibtee kema kinyi kyau kamar na saceki"
suna fita tace "to ki saceni mana"
dariyan daya karawa fuskanta kyau tayi sannan tace "ai zan saceki lokaci kawai nake jira"
itama dariya tayi suna tafiya gwanin sha'awa, jaad ne ya fito shima yayi kyau cikin shadda baƙi sunyi anko da janna, ɓata rai tayi tace "gaskiya jaad kaje ka canja kaya"
yace "a,ah nikam nafison black sabida nafi yin kyau cikin black dress"
cikin masifa tace "kenan anko zanyi da kai?"
yayi shiru, ta daka mishi tsawa tace "kaje ka canja nace"
"idan yaki fa?"
cewar Abba daya shigo yanzu, shiru tayi kanta kasa, yace "sabida kunsa kaya iri ɗaya shine zaije ya cire tunda ke kika siya mishi?"
girgiza kai tayi, yace "zaku wuce ku tafi ko kuma?"
fuuu ta wuce kamar zata tashi sama, jaad kasa kasa yake dariya, rankwashi Ibtee tayi mishi aka, yace "wayyo"
hanunshi ta rike suka fita, janna a fusace take tafiya, nawal daya shirya cikin black suit yayi kyau yana tsaye a jikin mota ya harɗe hanu, yana kallonta har tazo kamar zata ciji motan tana huci, buɗe mata yayi ta shiga ta zauna, Ibtee ce suka fito, bai san time daya fara smiling ba sabida ganinta, jaad ne yace "yaya p.b mu tafi ka tsaya kana kallonmu"
da sauri ya ɗauke kai baima san yana kallonsu ba, Ibtee dariya kaɗan tayi ganin yanda ya daburce, zata buɗe ta shiga yayi saurin buɗe mata with respect ta shiga ta zauna, jaad ya zauna a gaba, shiga yayi suka tafi, janna tana huci tana jin wani irin haushi kallon Ibtee taga nawal yana yi ta madubi, karkata madubin yayi ta yadda zai ganta sosai, Ibtee kanta a kasa batasan yana kallonta bama, janna wani abu ya tsaya mata a wuya, taji wani tsananshi yana karuwa a ranta, ko kaɗan batason alakanshi da yayarta, ya zama dole ta aikata abinda tayi niya domin yaji haushi ya aje aikin gaba ɗaya ya bar gidan kuma yau zatayi hakan, a hankali ta faki idonsu ta buɗe karamin jakan ta ciro wani katon farin paper tayi rubutu da manyan harufa sannan tayi murmushin da ita kaɗai tasan nufin yi, ta shafa gum a jiki jaad ne ya kalleta tayi saurin ɓoyewa a kasanta tace "me kana kallona?"
ɗauke kai yayi ta ciro ta gama shafa gum ɗin sannan ta ɓoye, ShopRite ɗin da yake tara dandazon mutane sabida sabon ShopRite ne kuma kayansu da sauki gasu da iya kula da customers a farfajiyan yayi parking, ATM a hanunshi Abba ya bada idan sun siyi abu ya biya kuɗin, jaad da Ibtee wacce take saurin fita idan sunje waje sabida kada ya buɗe mata marfin mota suka fita tare, shima nawal ya buɗe marfin motan ya raba bayanshi da kujeran zai fita, janna ta manna takaddan a jikin kujeran sannan tace "ji mana"
dawowa yayi ya kalleta, tauna cingum take tana kallon Ibtee da jaad wanda har sunyi gaba, saida ta tabbar gum ɗin ya kama riganshi kafin tace "it's okay"
buɗe motan tayi ta fita, taku take kamar batason taka kasa, kawarta ta school suka haɗu a kofa tazo da sauri ta rungumeta tace "classy janna kinyi bala'in kyau"
murmushi tayi cikin sanyin muryanta da babu hayaniya sai tsantsan raini tace "thanks"
hira sukayi kaɗan kafin tace "zan wuce rauda sai mun haɗu"
tace "to classy janna bye"
tace "bye"
wucewa tayi suka shiga, Ibtee da jaad suka fara zaɓen abinda suke so jaad yana rike da basket Ibtee na zubawa yana tura musu, janna ma zaɓa ta fara tana sawa a basket ɗin, nawal ya tsaya a gefe yana jira su gama, nunashi aka fara, bai damu ba ya zaci ko dan suit na jikinshi daya nuna shi guard ne yasa ake kallonshi, ɗan matsawa yayi daga inda sukafi kallonshi zai koma gefe, ji yayi wani yace "GAY?"
kallonshi yayi yaga shi yake kallo, ya maimaita kalman "gay kuma?"
zuwa yayi zai yiwa mutumin magana yaga mutumin ya matsa da sauri, yace "karka zo kusa dani"
da mamaki yake kallon mutanen da suka taru suna kallonshi, wata mata ta tofa mishi yawu tace "abinda Allah ya haramta shine zai zama abin ado a wajenka? abinda ya hallakar da mutanen Annabi lud shine zakazo kana tallanshi? lalle bakayi albarka ba kaiba ɗan halak bane"
da mamaki ya nuna kanshi alaman dashi take?
ta kara cewa "tirr da haihuwan ɗa irinka"
bai gane me suke nufi bafa, zuwa zaiyi wajensu domin gane me yayi, gani yayi kowa yana gudunshi.
~Kallon jikinshi ya fara, so yake yaga me suke kallo suke mishi wannan maganan, idonshi ya cika da hawaye Ibtee duk abinda ya faru akan idonta, ma'aikatan wajen suka kira security sukazo inda yake rikeshi sukayi ta karfi suka fara fitar dashi waje "bama son ɗan luwaɗi a cikin shagonmu sabida zaka iya zabar mana da darajan ShopRite"
gani yayi an fara ɗaukanshi hoto mutane sun kewayeshi, fizge jikinshi yayi da ihu yace "wai me nayi? me nayi muku kuke kirana ɗan luwaɗi? sabida an haifeni babu aure? shine kowa yake min abinda yaga dama? laifi nane dan an haifeni babu aure? laifi na ne....?"
kuka ya fara, Ibtee jakanta ne ya faɗi ganin kukan da nawal yake yi, sam ya kasa rike zuciyanshi yau, yana jin ya tsani duniya da abinda ke cikinta, yaji bayason kowa a kusa dashi, Ibtee ta karaso a hankali jikinta kamar an zare laka, ya haɗa kai da gwiwa yana kuka me taɓa zuciya, wani saurayi yace "haka dama suke ai masu aikata irin wannan zunubin sai su rinƙa taɓawa mutane zuciya da acting nasu a fitar dashi kuma bakayi kasuwa ba dan babu ɗan luwaɗi anan"
tashi yayi a fusace zai kama saurayin da duka rikeshi Ibtee tayi, kallonta yayi idanunshi sun jiƙa da hawaye, girgiza mishi kai tayi tana jin har numfashinta yana ɗaukewa, a hankali ya motsa bakinshi cikin baƙin ciki yace "me nayi? mena musu suke jifana da waɗannan munanan maganganun? sabida Ammina ta haifeni babu aure? itama bada sonta hakan ya faru ba..."
a hankali ta jashi jikinta, kankameta yayi yana kuka, dama jira yake ya samu inda zaiyi kuka da kyau, abinda ke zuciyarshi yayi yawa, patting bayanshi take yi a hankali alaman yayi hakuri ya daina kuka, ji tayi tana taɓa abu a bayanshi, da sauri ta kalli bayan taga abinda aka rubuta "I'M GAY"
ma'ana "NI ƊAN LUWAƊI NE"
zaro ido tayi a razane take kallon rubutun dake manne a bayanshi, tace "nawal meka rubuta a bayanka?"
girgiza kai yayi ya kasa magana sai cusa kanshi da yake a jikinta yana ji baida inda zai samu yayi kuka sai jikinta, a hankali ta cire paper sannan ta ɗago kanshi ta kalli fuskanshi daya koma jajur sabida kuka, takaddan ta nuna mishi, karɓa yayi yana karantawa, ya kalleta tace "ya akayi haka?"
girgiza kai yayi ya saki takaddan kawai ya fita waje, ɗauka tayi ta yayyaga sannan ta bishi, jaad ya kalli janna dake harɗe da hannu a kirji tana kallonshi ta taɓe baki alaman ko oho, ganin kallon da jaad yake mata ta watsa mishi harara sannan ta mishi alaman idan ya faɗa saita yankashi, gama shopping ɗinta tayi duk abinda takeso ta ɗauka taje ta biya kuɗin ta fito rike da manyan leda.
Ibtee tana fita taga ya shiga mota ya haɗa kanshi da stairy yana kuka mara sauti, a hankali ta buɗe ta shiga, kallonshi take tana jin zafin kukan a ranta, a hankali tasa hanu akan suman kanshi cikin sanyi take shafa gashinshi da jijiyan kanshi ya tashi tsaban kuka, tana ji har shesheƙan kuka yake yi, a hankali ta buɗe baki cikin lallashi tace "nawal..? kayi hakuri ka daina kuka...."
rungumeta yayi yace "ya zanyi? kullum ina cikin damuwa bana samun kwanciyar hankali a duk inda naje kyamata ake, sabida me? sabida babu aure aka haifeni tun ina yaro nake fuskantar kalubale tun ina yaro babu me zuwa wajena, banada aboki babu me sona sabida ni shege ne"
a hankali tace "ba haka bane nawal Allah ne ya kaddara maka haka"
janna ce tayi knocking kana ta buɗe ta shigo, kafa ɗaya ta ɗaura akan ɗaya, jaad ya shigo jikinshi a mace, a hankali ya saki Ibtee ya share hawayen sannan yayi murmushi yace "na gode"
shiru tayi tana wasa da yatsanta, itama kamar tayi kukan take ji.
cikin sanyin jiki yaja motan ya fara tafiya, janna taunan cingum take, har suka isa gida batace musu komai ba, fitowa tayi ta kwashe kayanta ta shiga ciki, jaad da ibtisam suka shiga jikinsu a mace, Abba yana falo yana safa da marwa ya kasa zama, suna shigowa janna taga Abba tsaye jikinta ya fara rawa, Abba ya kalli jaad yace "jeka kiramin nawal"
yace "to"
fita yayi yaje yace "yaya p.b Abba yana kiranka"
saida gaban nawal ya faɗi, yace "to kace ina zuwa"
shiga ɗaki yayi ya cire uniform ɗin yasa personal, bindigan da Abba ya mallaka mishi ya ɗaura akan kayan sannan ya kama hanyan falon, sallama yayi duk suna falon harda mami wacce take aika mishi wani kallo da saida ya sunkuyar da kai, a hankali ya karaso gaban Abba ya durkusa yace "Abba gani"
Abba yace "nawal dama kai ɗan luwaɗi ne?"
girgiza kai yayi, cikin tsawa Abba yace "ka buɗe baki kamin magana"
yace "A,ah"
Abba yace "to meyasa kace kai gay ne?"
hawaye ya fara ranshi yana ƙuna, Abba yace "ba kuka nace kamin ba amsa zaka bani ka buɗe baki ka bani amsa"
shiru yayi, mami tace "shirun da kayi ya nuna kenan da gaske ne?"
girgiza kai yayi, Abba ya dafa kai yace "Innalillahi wa inna ilaihiraji'un meyasa nake ɗaukan wrong mutane nake basu aiki a gidana? meyasa ka bari na yadda da kai? meyasa ka zama innocent a fuska amma a zuciya ba haka abin yake ba?"
shiru yayi hanunshi rike da kayan kanshi kasa hawaye yana jiƙa kayan, Abba yace "meyasa duk da abinda kayi amma bana jin tsanarka a raina nawal? meyasa kayi haka bayan kasan ba zan iya bari kayi nesa dani ba? ka ceci rayuwata shiyasa ka kwantamin a rai"
juya baya yayi dan bayason kallon nawal ɗin hawaye yake sashi, yace "tashi kaje na sallameka"
a hankali ya aje kayan a kasa sannan yace "na gode Abba, amma inaso ka sani niba ɗan luwaɗi bane, Abba na taso cikin wahala sabida rashin mahaifi Ammina ta haifeni ba aure, ni ɗin shege ne kuma Alhaji Alhasan medara ya auri Ammina, tana shan wahala ba kaɗan ba shiyasa naso aikin da nakeyi tare da kai sabida ina taimakawa Ammina, na faɗa maka hakane sabida banaso na ɓoye maka komai kamar yadda kaima ka ɗaukeni ɗa baka ɓoyemin komai"
tashi yayi yace "na tafi kuma na gode Abba koba komai kaine ka fara jana jiki ka nuna min nima ɗa ne"
buɗe kofa yayi zai fita jaad wanda ya saba dashi sosai bayason rabuwa dashi yace "Abba dan Allah kada ka barshi ya tafi wallahi yanada hankali kuma da dagaske ne zaka gane Abba"
ibtisam ta juya baya batason ganinshi zai tafi, kuka takeyi, jaad ganin da gaske zai tafi yace "Abba wallahi unty janna ce ta manna abin a bayanshi"
ledan hanun janna ya faɗi, jikinta ya fara ɓari, kallon jaad take kamar idanunta zasu zubo, abba yace "wait nawal"
tsayawa nawal yayi, Abba ya kalli janna da jikinta yake rawa yace "me kace jaad?"
yace "wallahi ina ganin lokacin da take shafa gum a jikin takaddan dana kalleta tace idan na faɗa saita yankani"
Abba ya kalli janna da take komawa baya tana girgiza kai, jakan ya fizge ya buɗe, gum ya gani, matsota yayi zata gudu ya damke hanunta ya fara duba gum ɗin, shinshina hanunta yayi yaji warin gum, jikinta kamar mazari bakinta yana rawa tace "Ab..ab..Abba na tuba wallahi na tuba ka yafeni"
da wani irin mari Abba ya ɗauketa saida ta faɗi a jikin mami, tsaban ɓacin rai Abba ya kasa cewa komai, juya baya yayi yace "janna ki bar falon nan kafin na kasheki"
da gudu ta saki mami zata gudu yace "tsaya"
tsayawa tayi, yace "ki bashi hakuri"
a hankali taje gaban nawal tace "kayi hakuri"
kafa Abba yasa mata ta baya sai gata a kasa gaban nawal, rufe ido tayi a azabce tace "wayyo Allah na mutu"
taka ta Abba yayi a gaban nawal ɗin yace "haka ake bada hakuri?"
cikin azaba tace "kayi hakuri nawal ka yafemin"
nawal da sauri yace "na hakura Abba ka barta"
cire kafa Abba yayi a bayanta, tashi tayi cikin azaba tace "na gode"
jan kafa ta fara domin ta tafi Abba yace "ibtisam"
da karfi yayi maganan jijiyoyin kanshi sun tashi, idanunshi sunyi jajur, a tsorace Ibtee tace "na'am Abba"
yace "kina son nawal?"
gyaɗa kai tayi tace "eh Abba"
yace "zaki aureshi nan da sati ɗaya"
murmushi jin daɗi tayi, ya kalli nawal yace "juma'a aurenka da ibtisam ka sanar da Amminka"
kanshi kasa yana hawaye ya durkusa kasa gaban Abba yace "na gode Abba"
hanunshi Abba ya rike ya ɗagoshi sannan ya rungumeshi yace "daga yau kada ka kara kiran kanka mara uba, kaima ɗa ne"
murmushin farin ciki yayi, Abba yace "zan baka aikin da yafi wannan zaka zama manager ɗin company ɗina sannan kaine zaka rinƙa kula da dukiyana, daga yau ka zama ɗana"
hawaye masu zafi suna wanke mishi fuska yace "na gode Ab..."
kuka yaci karfinshi ya kasa karasa maganan, jaad share hawaye yayi yana jin dadi ya fara murmushi, janna kunnuwanta sun jiye mata munanan maganganu, ji take kamar ana zuba mata ruwan dalma me zafi a kirjinta, idanunta suna rufewa tsaban tashin hankalin maganan da taji daga bakin Abba, dukan da yayi mata bataji zafinshi kamar maganan da take ji ba a halin yanzu, taka kafa tayi zata haura stair case, faɗuwa tayi kasa a sume, da gudu Ibtee tazo ta riketa tana kiran sunanta, mami ta kalli nawal ta kara mishi wani kallon me kama da kallon tsana, sunkuyar da kai yayi, abba tsallakata yayi ya wuce, ɗagata sukayi tareda mami da jaad suka kaita ɗakinsu, ruwa suka sa mata ta buɗe ido a hankali tana kallon Ibtee, hanunta ta rike tace "kin yadda zaki auri wanda baida uba? kin yadda zaki auri wanda aka haifa ba ta hanyar aure ba? kin yadda zaki auri wulaƙantacce?"
a hankali ta zame hanunta ta juya baya, mami tace "tambaya fa ake miki Ibtee ki bada amsa mana, kin yadda zaki auri shege?"
gyaɗa kai tayi tace "na yadda"
salati mami ta fara tace "na shiga uku ibtee, zaki zubar mana da mutunci Ibtee, ki rasa wanda zaki aura Ibtee sai mara uba? basu haifeshi ta hanyan aure ba ina zai san darajan aure?"
juyo da ita tayi tace "ki kalleni da kyau Ibtee baki isa ki aureshi ba, na baku tarbiyya me kyau baki isa ki auri wanda aka haifa kafin aure ba kinyi kaɗan"
hawaye ta fara wallahi ba zata iya rabuwa dashi ba, Allah saita aureshi ko anki ko anso, kwace hanunta tayi ta bar wajen, mami