taja tace "magana zakuyi da ita"
tashi tayi ta basu waje, mami tace "zauna da kyau"
gyara zama yayi, tayi shiru sannan ta ciro waya ta nuna mishi hoton ibtee, tace "wannan ƴata ce inaso ka sacemin ita, zan baka makullin gida acan zaka kaita ka ɓoyeta, akwai abinci da komai da komai a gidan kasa masu tsaronta dayawa, ka kula da ita sosai zan biyaka makudan kudaɗe"
yace "an gama Hajiya"
hoton ta tura mishi a waya sannan tace "gargaɗi ko sauro ka bari ya ciji ƴata zanyi maka abinda baka taɓa zato ba"
yace "babu abinda zai sameta hajiya na saba irin wannan aikin"
tace "to ga makullin sannan zan kawo kuɗi gobe wa hajiya rabi kazo ka karɓa"
ya karɓi makullin ta faɗa mishi location na gidan sannan ta karɓi number ɗinshi ta bashi nata, tashi tayi ta shiga ciki sukayi sallama da hajiya rabi kana ta tafi gida ranta fes.
ibtee tun daga ranan a tareda Ammi take kwana bata yadda tayi nesa da ita abinci ma itace take bata a baki, alluran yana tasiri shiyasa bata faɗa yanzu saide tayi ta kallon mutum idan sun shigo, nawal abin ya tsaya mishi a rai kullum cikin kuka yake ibtee na lallashinshi, da kyar yake shiru, har sukayi sati biyu a haka, yauma kamar kullum tana zaune a gefen gado ta jingina kanta da jikin gadon tayi shiru hannayenta da kafafunta ɗaure da chain, gashinta ya rufe mata fuska cikin ya kara girma sosai, ibtee ta shigo da sallama, plate na abinci a hanunta tazo ta zauna kusa da ammin, murmushi tayi mata tace "Ammi kiyi hakuri ban gama girki da wuri ba"
kallonta takeyi babu magana, a kullum idan tazo bata abinci kallonta takeyi kamar taga sabon fuska, ta ɗibo abincin ta kai bakinta, bata buɗe ba, ibtee ta turo baki a shagwaɓe tace "kici mana Ammi ko dai fushi kike banyi da wuri ba?"
kara matsarwa bakinta tayi bata karɓa ba, yi ibtee tayi kamar tana kuka, a hankali ta buɗe bakin tasa mata, haka take mata idan tayi kamar tana kuka saita buɗe baki, saida ta koshi kafin ta fara cin ragowan, ruwa ta bata itama tasha tace "yawwa mun koshi ko Ammi?"
shiru tayi sai binta da kallo, kwanciya tayi ta ɗaura kanta akan cinyar ammin, duk abinda ya faru akan idon nawal, wani so da kaunan ibtee yake ji a ranshi yadda bata kyaman Amminshi yake kara rura wutan sonta a ranshi, a hankali yayi sallama, tashi tayi tazo da gudu ta rungumeshi, ɗagata yayi sama yana juyi da ita, kullum idan ya dawo daga office haka take tarbanshi, kiss ya mata a kumatu cikin sanyin murya yace "na gode my love"
shafa sajenshi tayi tace "karka kara godemin amminka Ammina ce"
ya kara rungumeta tace "sakeni to haka, bara na kawo maka abinci"
yace "nooo ni ke nakeso"
tace "to ai bakaci komai ba na sani"
cikin kunnenta yace "i want to eat you"
waro ido tayi tace "kai Ammi fa tana nan"
da bangon ya mannata ya fara kissing nata, tureshi take tana cewa "ka barni Ammi na kallonmu"
a hankali ya zame bakinshi daga kunnenta da yake kissing, cikin kasa da murya yace "ammi bata cikin hayyacinta"
zatayi magana ya rufe bakinta da nashi, shiru tayi tana shafa gashinshi a hankali take responding.
akan gadon ya kwantar da ita ya kashe wutan yana r*m*ncing ɗinta, rufe ido tayi tana jinshi kamar ta haɗiyeshi, a kunnenta da wani irin murya dashi kanshi baisan yana dashi ba yace "kimin duk abinda nayi miki"
gyaɗa kai tayi sabida ta kasa magana.
sunyi nisa musamman nawal da yake breathing slowly, eye's nashi sun koma red, lips nashi kuma tsaban s*cking na duk jikinta da yake sun koma red sosai, gashin kanshi mai laushi da tsantsi take cusa yatsunta ciki tana wasa dashi.
ihu ammi tayi ta fara birgima a kasa, ture nawal ibtee tayi ta tashi da sauri tana maida numfashi, kunna wutan tayi da sauri ta sauka a gadon tana duba ammi, gani tayi hanunta akan cikinta, bata yadda sun haɗa ido da ammi ba sabida kunya, ammi hanun ibtee ta damƙe tana nishi tana jujjuya kanta, janna tace "inaga haihu zatayi"
saita kanshi yayi ya sauko yana kallon ammi, hanunta damke dana ibtee, waya ya kira ganin wahalan da takesha dama dr tace idan ta kusa haihuwa ya kirata za'a mata c's sabida ciwon kafa da take dashi zai iya kawo wani matsalan, tana ɗauka a ruɗe yace "tana naƙuda"
dr tace "ina zuwa"
katse wayan yayi Ibtee sai sannu take yiwa Ammi, shi kuma ya kasa zama, har dr tazo da wasu nurse biyu suka shiga, tace Ibtee dashi su fita, allura aka yiwa Ammi suka fita suka tsaya a bakin kofa, ganin yadda ya ruɗe tazo ta rungumeshi tana patting biyanshi tace "karka damu za'ayi komai lafiya"
suna tsaye a wajen har suka jiyo sautin kukan jariri, murmushi tayi tace "Ammi ta haihu"
shima murmushin yayi zai shiga ta rikeshi tace "no ba yanzu ba ka bari su fito sabida zasu gyara ta"
tsayawa yayi taga yana ta farin ciki, tanason ganin haka taga yana farin ciki, da haka har suka fito da yara biyu a hanu, waro ido tayi tace "twins ne?"
dr tana dariya tace "tabbas twins ta samu ɗaya namiji ɗaya mace"
nawal ya karɓi ɗaya Ibtee ta karɓi ɗaya, farin ciki suke suna jin kukan jariran, Ibtee ta karɓi ɗayan ta rungumesu duka a hanunta ya biyasu kuɗin su, dr tace ibtee ta rinƙa bata ruwan zafi da abu mara nauyi, kalan abincin da zata bata ta faɗa mata Ibtee cikin jin daɗi tace "to"
yace zai rakasu harara ta aika mishi ta yadda ba zasu gani ba, ya sani ibtee akwai bala'in kishi sam bataso ya raɓi mace koda a wajen aiki bataso ya zauna kusa da wata, sunkuyar da kai yayi ya fasa rakasu, shiga ciki sukayi ammi tana bacci a kasan, hawaye nawal ya fara Ibtee ta rungumeshi da yaran tana lallashi.
~Ibtee ce take kula dasu abinci ruwan zafi goyo duk itace take yi, bata hutu kuma har yau Alhaji Alhasan bai ko kara kallon yaran ba, nawal ne ya raɗa musu suna AARIF da ARIFA Ibtee tayi musu wanka me kyau tasa musu sabon kayan da nawal ya siya musu, masha Allah twins ɗin kamar larabawa suke sunbi kyawun Ammi, sannan suna tsananin kama da nawal, ibtee ta zama kamar itace uwarsu ammi jiki sai gaba yake yi babu sauki kullum yimata allura ake, ibtee yau ta gama bawa ammi abinci ta goya Arifa Arif kuma a hanunta, tayi kyau cikin abaya mint green ta yafa siririn mayafin a kanta, jaka ta ɗauka da abinci a flask sannan ta rufe ammi da makulli ta fita, bakin titi ta nufa ta tsayar da mashin ta shiga, office na nawal zataje sabida baici abinci ba ya tafi da wuri Abba ne ya kirashi, a kofan company aka ajeta ta fito ta biya me mashin kuɗinshi sannan ta fara tafiya a hankali, ji take kamar ana binta tunda ta shiga mashin taga kamar binta ake da sauri ta fara tafiya ta faɗa company ba shiri, Abba ya fito zai shiga motarshi ya tafi ya hangota, murmushi yayi har ta iso ta durkusa kasa yace "tashi tashi mana"
tashi tayi yace "ya kike?"
tace "ina lafiya"
yace "masha Allah, ki kara hakuri ki rungumi kaddara nawal ya faɗamin komai kuma ki godewa Allah mijinki ya miki kyakkyawan shaida"
tace "to Abba na gode"
kuɗi ya bata dayawa tayi godiya ta karɓa, shiga mota yayi har ya tafi kafin taje kofan office na nawal tana knocking, wata me aiki ce ta buɗe ta fito daga office ɗin rike da laptop, tace "sannu madam"
harara ta aika mata sannan ta ɓata rai ta shiga ciki, nawal yana ganin yadda ta shigo yasan taga wacce ta fita ne, Ibtee matsalanta kishi ne bata iya controlling na kishinta, abincin ta dire mishi a gabanshi ta juya zata tafi, hanunta ya rike ya tashi, zuwa yayi ya tsaya a gabanta, shafa fuskanta yayi ta ɓata rai kamar bata taɓa dariya ba, kallon Aarif dake hanunta yayi sannan ya kalli Arifa ya rungumesu duka yayi shiru, itama shiru tayi, a hankali yace "I'm sorry wifey ina sanki sosai banason ranki yana ɓaci please ki daina"
shiru tayi, ya ɗago yana kallon bakinta data turo, a hankali ya fara kissing nata a bakin, kallonshi take shima yana kallonta, saida ya tabbatar ta huce kafin ya saketa yace "kiyi hakuri nawal bayason fushinki"
tayi murmushi ganin ya rike kunne alaman sorry, ta mareshi kaɗan a fuska tace "kasan banason ganinka da kowace mace idan bani da Ammi da ba ko? kasan ko jannah kanwata banason naga kana kallonta, har Arifa kishi nake idan naga kana kallonta, nawal ban san dalilin da Allah ya ɗauramin kishinka ba, nawal ina kishinka sosai wallahi zan iya yin komai a kanka, zan iya yin komai sabida soyayyan da nake maka, dan Allah nawal kada ka ci amanata"
hanunta ya rike ya zaunar da ita a inda ya tashi, arif ya karɓa ta sauke Arifa, abincin ya buɗe bayan ya zauna kusa da ita sosai, ya fara ci saida ya koshi yace "ba zan taɓa cin amanarki ba ibtee amma ki rage kishi sabida bakisan me ƙaddara ya kaddara ba"
tace "banaso ko ƙaddara yasa ka auri wata bayan ni nawal zan iya yin komai idan na ganka da wata idan nace komai ina nufin komai"
murmushi yayi yace "abinci yayi daɗi"
hira suka fara, cikin hiran tace "ina fatan ni kaɗai ce nasan kayi sata a baya? bayan ni ko kamal bai sani ba?"
ya girgiza kai yace "babu kowa shima bai sani ba"
murmushi tayi tace "na gode Allah"
matsowa yayi yace "na koshi da abinci me zaki bani?"
shagwaɓa fuska tayi tace "ruwa?"
dariya yayi yace "no nikam banason ruwa"
tace "to me?"
knocking akayi yace "shigo"
kamal ne ya shigo, yana ganinta yace "lalala yau madam ce da kanta a office?"
tayi dariya tace "yau zuwan bazata nayi muku sabida naga me kuke toyawa a office"
yace "Allah yasa dai bataga komai ba nawal"
nawal yace "ban gane ba dama me zata gani?"
kamal cikin son haɗa rigima yace "ƴammatanka da suke zuwa mana"
wani kallo Ibtee ta fara yiwa nawal, yace "wallahi tallahi na rantse da Allah karya yake min"
tace "karya shine a gabanka?"
ganin ta hau yace "dan Allah kamal ka faɗa mata wasa kake"
kamal ya ɗauki Arifa da Aarif yace "ba wasa nake ba ai gaskiya na faɗa"
fita yayi dasu yana dariya kasa kasa ganin yadda Ibtee ta hau masifa dama nawal yana faɗa mishi tanada bala'in kishi idan ya motsa mata kunyanta tafiya yake.
duk yadda yaso ya mata bayani ta kasa fahimta, rungumeta kawai yayi cikin sanyin murya yace "ba zan iya betraying ɗinki ba Ibtee, ko a mafarki banaso na kasance da wata idan bake ba, nasan kinada kishi ba zan taɓa yin abinda zai taɓa miki zuciya ba ibtee"
shiru tayi domin gaskiya yake faɗa.
yace ta jira zuwa dare su tafi tare tace a,ah zata tafi sabida Ammi, ya rakata a hanya take faɗa mishi kamar ɗazu wani yana binta, yace "ki kwantar da hankali ki daina tsoro babu abinda zai sameki ina miki addu'a koda yaushe"
ta shiga napep ɗin tace "to saika dawo"
karɓa yaran tayi suka tafi yana kallonta har sukayi nisa.
har kofan gida ya kaita, momy yanzu ta dawo ko daga ina oho, cikin haushin ibtee da takeji wanda take shirya abu gagarumi a kanta, ganin babu kowa tayo kanta da motan da kyar Ibtee ta tsira da ranta, tana haƙi ta shiga cikin gidan, ta buɗe Ammi taga idonta biyu tana zaune, yaran ta aje mata akan kafarta sannan tace "bari naje na dafa miki abinci"
da kallo kawai ammi take binta, saida ta fita kafin ta fara kallon yaran da suke wasa.
kulawa me kyau take bawa Ammi, yau ta faɗawa nawal zataje gidansu ta duba su janna, yace taje sannan ya karɓi yaran yace zai tafi office dasu idan ta tashi ta biya ta office saisu tafi, tace "tom"
bai tafi da itaba sabida zata yiwa Ammi allura da karfe goma, shi kuma takwas zai tafi, saida ta shirya Ammi kamar kullum tayi mata alluran kafin tayi wanka ta shirya cikin shadda tayi masifan kyau, ɗakin Ammi tazo ta rungumeta sannan tace "zanje gida yau ammi ke kaɗai zaki zauna"
ji tayi itama Ammi tayi mata kamar yadda tayi a hankali ta maimaita abinda ta faɗa tace "zanje gida yau Ammi yau ke kaɗai zaki zauna"
murmushi tayi ganin ta maimaita maganan da tayi tace "na tafi"
ammi ma tace "na tafi"
tana murmushi kawai ta rufe kofan ta tafi, yau babu mashin tafiya take tana juya baya ko zata ga taxi ta shiga, saida ta kai bakin titi abin mamaki duk wanda ta tsayar baya tsayawa, da kyar ta samu wani ya tsaya ta shiga, rufe marfin tayi tana gyara riganta ta ɗago kai tace "malam low-cost zaka kaini"
ganin yadda yake rufe kanshi da bakin hulan rigan sanyi tace "malam kaji me nace?"
hanunshi me ɗauke da hangloves baki taga ya ɗaga mata, yaja motan, gabanta yayi mummunan faɗuwa ganin irin dressing ɗin data fara ganin nawal dashi ne, addu'a ta fara a ranta tana kallonshi, zuciyanta ya kasa yadda dashi tace "malam ajeni anan zan siyi abu"
ya girgiza kai, tace "ka ajeni nace malam"
kara gudu yayi, cikin tsoro tace "zan maka ihu ka saukeni"
wayarta ta ɗauka zatayi kira ya fizge wayan ya wurgar sannan ya fara gudu sosai da motan.
jaad da gudu ya fito daga ɗaki yace "mami ibtee ta kira yanzu wai zatazo gidanmu harma ta shiga hanya"
murmushi tayi tace "tom jaad Allah ya kawota lafiya"
ɗakinta taje ta kira numbern reza, yana ɗauka tace "reza yanzu Ibtee na hanyan zuwa ka tabbata kayi wannan aikin"
yace "gaskiya hajiya na fasa wannan aikin kullum bana ganinta yauma ina nan banga fitowanta ba na gaji gaskiya na fasa zan maida miki kuɗinki"
kafin tayi magana ya katse kiran, tace "na shiga uku na lalace meyasa wannan ɗan kwayan zai min haka?"
momy tsaye take tana kiran waya, tsaki taja tace "ka ɗauka mana ka ɗauka dan Allah"
saida ya kusa yankewa aka ɗauka, cikin sauri tace "yau ta fita ka tabbata ka rabata da duniya kada ka bari ta sake dawowa gidannan, tasa shadda ash color da mayafi ja, kayi sauri yanzu ta fita"
jin yayi shiru tace "bello baka jina ne?"
cikin muryan maye yace "naji"
katse wayan yayi ya shiga mota yazo ya tsaya a kofan yana jiran fitowanta, yanada hotonta shiyasa zaiyi saurin ganeta, ya jima a wajen bata fito ba, tsaki yaja ya kira hajiya naja tace "ka sameta?"
yace "gaskiya ba zan iya jiran wannan abin ba tun ɗazu ina nan ba zata fito ba?"
tace "already ai ta fita bello binta zakayi ka sameta a hanyan gidan nasu"
yace "gaskiya na fasa wannan aikin kada ki kara kirana"
kafin tayi magana ya datse, ta yarfa hanu tace "shine matsalan aiki da balidi ai"
tsaki taja tace "tsinanne yasa plan ɗina ya ɓaci"
Jaad ne ya shiryawa ibtee abu me daɗi ya aje mata yana jiran zuwanta sai kallon time yake, shiru bata zo ba, ya kira wayarta yana shiga bata ɗauka, aje wayan mamin yayi ya fita ya tsaya a bakin gate yana jiran zuwanta dan yayi missing nata, janna ce ta fito daga ɗaki sanye da sleeping dress yanzu ta tashi a bacci, tace "jaad? jaad?"
mami tace "yana waje yana jiran zuwan ibtisam"
murmushi tayi tace "zatazo ne?"
a takaice mami tace "eh"
tace "naji daɗi dama nayi missing nata bari naje nayi brush na jira zuwanta"
komawa ciki tayi, jim kaɗan ta fito sanye da dogon riga marar nauyi, zama tayi a kujeran parlour tana jiran zuwan Ibtee.
shiru batazo ba jaad jiki a mace ya dawo ciki, janna tace "ya akayi jaad kanina? ta karaso?"
ya zauna yace "bata zo ba har yanzu kuma lokacin data kira tana hanyan zuwa gashi ina kiranta da wayan mamin bata ɗauka"
janna tace "comon darling karka damu kanka she will definitely come"
yayi yace "I pray"
suna zaune a wajen tun suna jiranta har suka gaji kowa ya kama aikin gabanshi, jaad yace "may be taje wajen mijinta kin san unty ibtee da mijinta kamar cingum basa rabuwa"
ɓata rai janna tayi batace komai ba.
har dare batazo ba nawal wanda su arifa suka isheshi da kuka yanata kiran numbern Ibtee bata ɗauka, wayan Abba ya kira cikin respect ya gsisheshi sannan ya tambayeshi ko ibtee tana kusa, yace ai batazo ba tace dai zatazo amma bata zo ba, yayi godiya yace zai koma gida may be bata samu daman fitowa bane, a ranshi yace ko tana tare da Ammi, rufe laptop yayi ya ɗauki yaran sannan ya fita dasu ya rufe office, a mota ya sasu ya shiga ya kama hanyan gida, yana isa ya shiga ɗakin Ammi ya buɗe, yaga Ammi zaune tana ganinshi ta fara dariya, shiru yayi ya aje yaran kusa da ita sannan ya fita, a ɗakinsu ya duba ibtee bai ganta ba, yaje kitchen babu ita, abinci ya dafawa Ammi sannan ya haɗawa twins madara ya fito da plate babba a hanu, abincin ya bawa Ammi taci ya basu madaran suka daina kuka, yace "Ammi ina ibtisam?"
tana kallonshi tace "Ammi yau zanje gida zaki zauna ke kaɗai"
tana ta maimaita kalman yace "shine kalman da Ibtee ta faɗa mata kafin ta tafi"
yace "ta fita tunda Ammi ta faɗi haka, to ina taje?"
tashi yayi ya fita a ɗakin yana kara kiran numbern, bata ɗauka ba kuma batada ɗabi'an rashin ɗaukan kira ko tana cikin fushi bata kin ɗaukan waya, tashin hankali ya shiga, take ya kira kamal ya faɗa mishi halin da ake ciki.
babu jimawa kamal yazo, nemanta suka fara gadan gadan basu faɗawa kowa ba, har dare babu ita babu labarinta.
Nawal banda Innalillahi wa inna ilaihiraji'un babu abinda yake iya faɗi, duk inda suka san zasu samu ibtee saida sukaje har gidansu yusra babu ita, nawal cikin tashin hankali ya dawo gida, kamal yana bashi hakuri ya daure zasu sameta nawal yayi shiru kawai yana jin yaran suna kuka itama Ammi tana kwaikwayon kukansu, hanunshi yasa a kanshi yana jin kamar jiri, tashin hankali goma da ashirin yake ciki, kamal yace zai kai police station